You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
tayi game ta gaji ta ɗau ruwa ta sha.
Jin tayi gaba ɗaya ta tsargu kamar wani yana kallon ta, slowly chikin tsoron abun da zata gani ta ɗago blue eyes nata, karaf idon ta ya sauka chikin nashi yana tsaye wajen ɗan karamin pool dake wajen ya harɗe hannu a kirji ya zuba mata ido, a tsorace ta miƙe jiki na kerma tazo ta raɓa gefen sa zata wuce hannu ya sanya ya damko gashin kanta da karfi ya jawota baya ya dawo da ita ta gaban sa suna fuskantar juna, tsuke fuska tayi dan ba karamin zafi jan gashin ta da yayi ya mata ba calmly da sexy Voice na shi ya fara magana "me ya kawoki nan? Bakin ta har bari yake lips nata sai kakkarwa suke tace "kayi hakuri yaya Prince bazan.... Bata karisa maganar ba ya ɗaura yatsa ɗaya a saman lallausan lips nata yace "shiiiiiii" shiru tayi shima yayi shiru ya zubawa tsoratachiyar face nata ido ita kuwa ganin ba zata iya kallon chikin gwayar idon sa bane ya sanya ta runtse idon ta, Almost 3mins suna tsaye a haka da kyar ta iya buɗe baki lips nata sai kerma yake tace "yaya Prince dan Allah kayi hakuri wlh zafin gashin yake min" kasa kasa yace "open your eyes now" chikin sauri ta waro blue eyes nata a kan face na shi tana jiran taji me zai che da ita "wai me nake miki ne da kike yawan kirana da mugu? Kara zaro idon ta waje tayi tana mamakin yaushe yaji tana zagin sa kuma "ba dake nake magana bane" da sauri tace "kayi hakuri yaya Prince ba zan sake ba"
"Nifa ba chewa nayi zaki sake ko baza ki sake ba chewa nayi me nake miki da har kike kirana da mugu kuma kika tsaneni" runtse ido tayi chikin tsoro hukuncin da zai mata idan ta faɗa masa ta fara magana
"kana kyamata kace baka sona baka son ganina komai na taɓa baka so,baka kaunar hanya ta haɗa ka da ni ma bare har jikin mu ya haɗu, ban san me na maka ba kamin irin wanan muguwar tsana duk da tsanar da kamin hakan bai hanani in sauke hankin ka dake kai na ba,hakan baya hanani kyautata maka amma komai nayi maka ba dai dai nayi ba....bata kai karshen maganar ba ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa da murya kamar mai raɗa yace "shikenan abun da ya sanya kike chemin mugu?har kike ikirarin kin tsaneni? Kasa magana tayi dan ji take kamar ba aduniya take ba,chi gaba yayi da magana "ok yanzu mun haɗa jiki kuma bana kyamar ki sai ki dai na kirana da mugu, because kalmar batamin daɗi" nan ma ahiru tayi ta kasa magana,hannu ya sanya ya ɗago habarta ya zubawa face nata ido, idon ta a lumshe dan gaba ɗaya kunyar sa take ji "open your eyes" slowly ta buɗe idon nata a kan face na shi "what is your name? Chikin sanyin murya tace "hiyana"shiru yayi bai sake magana ba sai hannun sa da ya ɗago ya ɗaura saman kanta a hankali ya shiga shafa lallausan bakin gashin kan ta, ya zagayo da ɗayan hannun sa ta bayan ta ya ɗaura saman kugun ta, kwantar da kai hiyana tayi saman kirjin sa ta lafe tana tunanin anya ba aljanin bane wannan ɗayan bangaren zuchiyar tane ya bata amsa da chewa idan ma aljani ne yau dai ba kin kwanta saman kirjin aljani mai kama da mutumin da kika fi so a rayuwar ki ba,tuna haka yasa ta kara lafewa a jikin sa tana shakar daddaɗar kamshin perfume na shi almost 10mins suna tsaye haka, kasa jure tsayuwar hiyana tayi dan ta lura Bgs ko shekara zasuyi a tsaye ba zai damu ba, kokarin zamewa take kasa dan kafofin ta sun gaji jin hakan ya sanya ya sunkucheta da hannu ɗaya ya koma da ita wajen kujerun dake rufar wajen, kwanchiya yayi da ita a saman faffaɗar kirjin sa kwantar da kanta tayi saman kirjin na shi tana ɓoye fuska,chi gaba da shafa lallausan bakin gashin kanta yayi, lokacin guda ya fara fita hayyacin sa dan daman shi mutun ne mai tsananin sha'awa, shi ya sanya dan ya kare kansa daga faɗawa neman matan banza yake allura,
ɗayan hannun sa ya ɗaura saman bayan ta yana shafawa a hankali, mutuwar kwance hiyana tayi ita har yanzu ganin abun take tamkar mafarki ne ko kuma aljanine yazo mata a suffar yaya Prince, tayi nisa chikin tunani bata ankara ba sai gani tayi ya juya da ita ta koma saman sofar shi kuma ya mata runfa da faffaɗar kirjin sa, waro blue eyes nata tayi waje ba shiri, tana kallon sa, lokaci guda tsoron sa ya dira mata a rai ganin yadda idon sa suka sauya zuwa jaa sosai chikin tsoro lips nata na kerma tace "yaya Prince in tafi ɗaki? Bai yi magana ba sai ma haɗe fuskar su yayi waje ɗaya a hankali ya kamo lips nata na kasa ya fara kissing, gaba ɗaya duk wani kofa da iska ke shiga a jikin ta ya buɗe domin ansan sakon da yaya Prince ke aika mata duk wani jini dake gudu a jikin ta sai da ya tsaya chan,ya baiwa sakon yaya Prince hanya ya wuce, sosai yake kissing nata tare da shafa gashin kan ta da hannu ɗaya, almost 10mins yana kissing nata kafin ya sake ta tare da miƙewa zaune chikin da sarke war murya yace "jeki kawomin abinci" tun bai kai karshen maganar ba ta miƙe da gudu ta barwajen
Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu
💖The Talent Troupe Writer's 💖
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Wanna page ɗin nakine Hauwa'u jidda maman Abba ina godiya da comments naki ina matikar farinciki da jin daɗi Allah ya bar zumunci
Book 2
Page 20
_______A gigice hiyana ta farka daga nauyayyar barchin da ya take juyawa tayi tana yan waige waige hannu ta sanya a saman lips nata da ɗan karfi tace "daman duk wanan kiss da yaya Prince yamin ma farki ne,ina ma wanna daɗɗaɗar mafarkin ya zama gaskiya ya Allah ka nunamin ranar da yaya Prince zai min kiss" ɗago ido tayi tana bin ɗakin da kallon chikin sauri ta diro kasa daga saman gadon dan tana tabbacin yanzu yaya Prince ya dawo, lallaɓawa tayi ta leƙa wajen hutawar sa chan ta hangosa zaune ya manna waya a kunne da alama waya yake chikin sauri ta juyo ta dawo chikin ɗakin ta ɗauki hijabin ta ta sanya ta fice waje ta nufi kitchen, dan shirya masa abinci
Shi kuwa oga zaune yake yana waya da Aryan
"Ykk Aryan? ya jikin su Aunty Amarya? Daga ɗayan bangaren Aryan yace "Suna lfy nakira na sanar da kai ne zan wuce yola yanzu" shiru Bgs ya ɗan yi kafin yace "aa ba yau ba kuma ba gobe ba zanyi bincike a kai kafin na baka izinin zuwa yanzu dai ka chigaba da bata magani da wanchan wawan ke bata,kafin na tattara bayanai" "amma Bgs kasan fa wannan maganin idan yayi yawa zai ja mata wata matsalar ko" "Aryan baka da zaɓi just kayi abun da nache kawai" yana gama faɗin hakan ya katse kiran dai dai lokacin da hiyana ta kariso wajen hannun ta ɗauke da try abinci
Saman table ta aji masa abincin ta ɗau plate ta fara serving nashi bayan ta cammala komai ta ajiye masa saman table ɗin ta matso masa da table ɗin gabansa,tsugunnawa tayi a gaban na sa daga ɗan gefe chikin raunanniyar murana tace "yaya Prince dan Allah ka kiramin Ammi inason in tambayeta an gane diyana ne,wayar da yaya Khalid ya sai min card ɗin ciki ya kare" shiru yayi bai yi magana ba sai ma ɗaukan spoon da yayi ya fara chikin abinci sa,
shiru shiru bai yi magana ba ita kuma tana tsugunne a gaban sa ko kallon in da take bai yi ba har ya kusa kammala chin abin chin chike da kunan rai ta miƙe da gudu ta bar wajen tana hawaye,ko kallon ta bayyi ba ya chigaba da chin abincin sa
Saman katafaren gadon sa ta faɗa tare da sakin wani marayar kuka, tana zanchen zuci wai yaushe ne yaya Prince zai chanza a rayuwar sa mutun kamar ba mutun ba baka taɓa gane me yake so me baya so, yana bala'i son su yaya Fahad amma har yanzu ya kasa gane kamar yadda yake son yan uwan sa kowama haka yake son nashi, wlh ina da tabbacin na fishi kaunar yan uwana sune duniyata sune komai nawa wai ni yaushe ne bakin ciki zai kare a rayuwa ta, ya Allah kamin zaɓi mafi alkhari kamin zaɓin da ya dace da ni, ya Allah ka karemin yar uwata a duk in da take a faɗin duniyar nan, tabbas ina ji a jikina diyana na raye sai dai aduk lokacin da na tuna tana raye nakanji gabana na faɗuwa ya Allah kasa ba chikin wata musibar ta faɗa ba,
Sai da tayi kukan ta mai isarta sannan ta miƙe ta nufi toilet ta wanke fuskar ta tayi wanka ta fito ta sake shiryawa chikin wata shegiyar doguwar riga mai bala'i kyau rigar ta kamata sosai rigar bata da hannu launin pink color an mata kwalliya da wasu duwatsu farare masu kwalli daga guiwar rigar har zuwa kasa an tsaga ta ta gaba
gaban mirrow taje ta tsaya tana kallon kanta tsaki taja ganin yadda ta zama kamar wata karuwa ji take kamar taje ta damko Zahra ta mata shegen duka hannun ta na kerma ta ɗauki wani perfume dake wajen ta ɗan sanya a jikin ta kaɗan wai dan karya ji kamshin ya gane, drawer wajen mirrow ta buɗe tana yar dube dube hannun ta sai kerma yake alamar tsoro, wani kyakkyawar hoto ta chikaro da shi awajen jikin ta har bari yake wajen saurin ɗauko hoton sai tagama ashe hotunan biyu ne ba ɗaya ba, tasha ruwan mamaki lokacin da idon ta ya sauka kan face ɗin matar dake chikin hoton matar kamannin su ɗaya da hiyanar kamar an tsaga kara matar na tsaye a kasar wata katuwar bishiyar kuka tana riƙe da kwaryar nono, jikin ta sanye da kayan fulani riga zuwa chibiya da sani an mata manya manyan kitso guda biyu wadda gashin nata ya zubo har kan chibiya bakin kirin sai sheki yake kwata kwata matar bazata wuche 17 years ba, sosai hiyana ta kurawa matar ido tana son sanin wacece wanan mai mugun kama da ita haka,shiru tayi tana tunani to ko dai Ammi ce lokachin da take yanmata dan tasan idan ba Ammi ba ba wacce yaya Prince zai ajiye hoton ta awajen sa ganin tunani da take ba zata samu amsa ba yasanya ta ajiye hoton ta ɗauko ɗayan, ba karamin mamaki ta shigaba lokacin da idon ta ya sauka kan ɗayar hoton, gaba ɗaya Family su Ammi ne awajen tabbas hiyana ta san wasu daga chiki musamman Innar ta dake tsaye kusa da Ammi a lokacin kurawa tsohon da ke tsakiyar su ido tayi tana kallon sa yana ɗauke da yar yarinyar da baza ta wuchi shekara 2 ba murnushi hiyana tayi lokacin da ta gano chewa itace kan kafar tsohon nan domin tana da hoton ta tana karama dawo da kallon ta tayi kan tsohon ta zuba masa ido, na ɗan lokacin kafin ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, bata san lokacin da hawaye ya fara bin kuncin taba lokacin da idon ta ya sauka kan fuskar bappa dake tsaye yana ta murmushi, kallon sa take kamar ta kira shi ya amsa jin motsi takun Bgs ne ya sanya tayi sauri mayar da hoton ta goge hawayen ta chikin sauri ta juya zata barwajen dai dai lokacin shi kuma ya shigo kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai gefe,ya wuche chikin ɗakin da sauri itama ta wuce ta ɗauki hijabin ta, ba tare da ta ɗaure gashin taba ta sanya hijabin ta wuche ta nufi wajen hutawar dan ta kwashe kayan abincin da yaci
Bayan ta kwashe kayan abincin ta mayar kitchen ne ta dawo ta gyara wajen tana gamawa ta dawo chikin betroom ɗin tana kokarin wuchewa palo sexy Voice nashi ya daki dodan kunnen ta "come here" chikin sauri ta juyo ta nufoshi yana kwanche saman gado, tana kokarin tsugunnawa a kasa yayi saurin nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, in da ya nuna mata ta zauna miƙewa yayi zaune shima suna fuskantar juna
Chikin sanyin murya ya fara magana "already an gane yar uwar ki tana gida" ai hiyana bata san lokacin da ta miƙe ta rungume sa tana dariya ba tana faɗin "wayyo Allah na Alhamdulila Alhamdulila" shiru yayi abun ma mamaki ya bashi sai da tayi dariyar ta mai isar ta sanna ta ɗago kai kallon face nashi ba karamin tsoratata yayi ba bashiri ta sake sa ta koma ta zauna a gefe ta nitsu ta manta ɗazun fa mafarki take yanzu kuma gaskiya ne, kara ɗaure fuska yayi sosai chikin izza ya fara magana "idan kika sake min irin haukar nan sai na ɓallaki ki nitsu kiji abun da zan che miki first menene sunan ki? Nitsu ta karayi chikin sanyin murya tace "hiyana"ɗan sakin fuskar sa yayi kaɗan kafin yace "what about your sisters Name" "diyana itace mai bina sai lamrat mai bi mata sai amrat auta" shiru yayi ɗan yi kafin yace "What about Your mother? Narai marai tayi da ido tana kokarin kuka,hannu ya ɗaga mata alamar kar ta kuskura ta fara masa kuka a nan ba tare da yayi magana "wacece maman ki yar ina ce? kuma aina take yanzu?chikin dakiyar zuchiya ta fara magana "ta rasu tun ina yarinya amma bayan rasuwar ta da jimawa bappa ya bamu lbr ta kuma yace zai ajiye mana wani sako ko bayan ranshi idan muka girma mu binciki ɗakin sa zamu samu sakon akan innar mu sakon yake tafiya"
"Ok mahaifiyar ta ku yar ina ce? "Bappan mu yace mana ita yar sudan ce" shiru yayi kafin yace zaki iya tuna a sudan a wani gari? Girgiza masa kai tayi kafin tace "aa bai faɗa mana awani waje bane mu dai yace mana ita yar sudan ce" "tana da yan uwa a nan Nigeria ne?shiru hiyana ta ɗan yi kamar mai tunani chan kuma ta girgiza kai tana faɗin "aa bata da kowa" shiru yayi bai sake magana ba sai chiro wayar sa da yayi ya fara kiran Aryan video call, bugu ɗaya Aryan ya ɗaga
Wani Cool murmushi Aryan ya saki lokacin da idon sa yayi masa tozali da hiyana zaune gefen Bgs yana son ya yi magana akan hakan amma yasan halin Bgs yanzu yana magana zai iya korin ta awajen
"Aryan ina yarinyar nan take? Chewar Bgs
da gangan Aryan yace "wace yarinya kuma" yana magana ya guntse dariya so yake ya ɗan kure Bgs,dogon tsaki Bgs yaja tare da wurga ma sa harara ta chikin wayar "zaka bata wayane ko ko" harara wasa shima Aryan ya wurga masa kafin yace "2dys ba muyi bane shi ya sanya yau nake maka tsiyar" ya kai karshen maganar tare da komawa kusa da diyana dake kwance saman gado tana barchin wahala,mikawa hiyana wayar Bgs yayi hannun ta har kerma yake ta ansa tamkar diyana na jin ta haka tafara surutai
"diyana ina kika shiga kinsan tashin hankali da na shiga bayan tafiyar ki kuwa? dan Allah ki tashi daga barchin nan ko zan samu naji daɗi a rayuwata alhadulillah Allah mai kyauta mai kari ko iya ganin ki kawai danayi ya kawarmin da duk wani tashin hankali da damuwa dana ke chiki, dan Allah diyana ki tashi kimin magana kinji buɗɗon bappa kin tuna sunan ko" tana magana tana kuka hawaye sharɓa sharɓa, shi kanshi Aryan kawar da fuskar sa yayi daga gaban Cameran dan idon sa sun cika da kwalla lokacin guda Bgs yaji mugun tausayin yaran ya kama shi ashe ba shi kaɗai yake son yan uwan sa kaman ran saba Allah sarki marayun Allah first time a rayuwar sa da yaji zai iya tsayawa mace zai iya share mata hawaye.
Slowly ya kai hannun sa saman face nata abun da bai taɓayi ba a rayuwar sa, chikin nitsuwa ya fara share mata hawaye yana sharewa wasu na zubowa, kamar pampo, shiru yayi yana tunanin ta yaya ake rarrashin mutun ya daina kuka ita kuwa sai surutai take tana hawaye bata ma san Bgs na goge mata hawaye ba idon ta na kan diyana dake kwance ko motsi ba tayi "dan Allah yaya Aryan ka tashe ta ka tashe ta tayi mun magana ko zanji daɗi wlh ji nake kamar in ganni gani gata wayyo Allah" ba karamin tausayin su Aryan ya jiba chike da zullumin abun da zai biyo baya idan ya tashi diyana ya sanya hannu yana ɗan shafa fuskarta yana faɗin "my jidda my jidda" zubur diyana ta mike zaune tana yan waige waige,da karfi hiyana tace "diyana diyana kimin magana kinji? sai lokacin diyana ta kai kallon ta kan wayar da ke hannun Aryan, zubawa hiyana ido tayi tana kallon ta kamar bata taɓa ganin taɓa ita kuwa hiyana sai kuka take tana faɗin "diyana kiyi magana ki faɗamin kina lfy ki chemin in da kikaje ba a chutar da ke ba dan Allah diyana kiyi magana" chikin sanyin murya diyana tace "kamar na san ki kamar sunan ki hiyana ko? a razane Aryan ya ɗago yana kallon ta domin bai taɓa tunanin diyana zata gane hiyana na ba, dafe kai diyana tayi da hannu bibbiyu tana jujjuya kanta da ɗan karfi karfi, chikin sauri Aryan ya rikota yana faɗin "my jidda menene? Shiru diyana batayi magana ba sai juyi take tana kankame da gashin kanta da karfi tana kokarin ta tunano wasu abubuwan, kawar da kai Bgs yayi daga kallon su ya juya gefe chak hiyana ta da katar da kukan da take chikin zafin nama kamar zata chafko diyana ta chikin wayar tace "diyana lfy me kuma ya sameki ko dai baki da lfy ne? Diyana kiyi magana mana" kokari diyana take ta tunano wasu abubuwa na rayuwar ta, tabbas ta tuna wacece hiyana sannan tana jin kamar bayan hiyana akoi wasu da ya dace ta sani, wani marayan kuka hiyana ta kuma saki wadda ya sanya Bgs juyowa yana kallon ta tsabar kukan da ta sha har Voice nata ya dai na fitar da sauti sosai, da sauri ya ansa wayar sa daga hannun ta ya katse kiran ya ajiye wayar a gefen sa dan kukan da hiyana take yayi yawa
Ganin yaya Prince ya anshe wayar sa ne ya sanya ta tattaro sauran sautin Voice nata ta fasa kuka mai sauti ta fika kanta saman guiwowinta tana faɗin "wayyo diyana ni che yau baki gane ba? to meya same ki? me aka miki? waya sa kika manta da ni? shiru yayi yana kallon ta, yana son ya sanya ta tayi shiru amma kwata kwata bai san ma ta yadda ake rarrashin mutun ba wani ɓangare na zuchiyar sa na faɗa masa ya rungumota yace tayi shiru zatayi haka ko akayi chikin sauri da zafin nama ya jawota jikin sa, ya rungume ta sosai da sexy Voice na shi kasa kasa a sai tin kunnen ta yace
"kiyi shiru ya isa kukan" ko jin sa hiyana ba tayi ba sai ma kara sautin kukan nata da tayi dan ji take tamkar zuchiyar ta zai fashe ya fito waje, idan ta tuna ba ta san menene ke damun diyana ba sai ta sake kara sautin kukan nata, Bgs ya rasa yadda zai yi da ita shi gashi bai san fita ya barta a hankalin da take chikin nan dan ba karamin tausayi suka bashi ba gashi bai iya rarrashin mutun ba, iya tsawa da umarni kawai ya iya bawa mutane karo na farko a rayuwar sa da ya sanya ƙwaƙwalwa sa tuna ta yadda ake rarrashin mutun, almost 10 mins suna zaune haka sai kuka hiyana ke karawa taki yin shiru
ko me ya tuna sai yayi saurin ɗago habar ta chikin zafin nama ya haɗe bakin su waje guda, lokaci guda hiyana tayi tsit ta daina kukan waro idon ta ta sukayi jaa suka kunbura saboda kuka tayi waje tana kallon sa yayin da shima ita yake kallo tunani ta shigayi an ya yanzu ma ba mafarki bane kuwa anya da gaskene, tayi nisa chikin tunanin da take sai jin tayi ya sanya ɗayan hannun sa ya rufe mata ido tare da zame bakin sa daga nata kasa kasa yace "kiyi barchi" yana kai karshen maganar ya kwanta da ita a kirjin sa, ita dai hiyana har yanzu ganin abun take tamkar mafarki ne irin na ɗazun,shiru ɗakin yayi almost 30mins suna kwanche haka
ɗago kai Bgs yayi yana kallon face nata idon ta a lumshe tayi barchi, ajiyar zuchiya ya sauƙe chikin dabara ya juyar da ita yanason ya kwantar da ita amma me sai jin yayi ta kankame sa sosai da hannayen ta dukka biyu, guntun tsaki ya ɗan ja tare da komawa ya kwanta da ita a haka tana jikin sa har barchi yayi awon gaba da shi
Chikin barchi yaji zafi ya damesa da kyar ya iya buɗe idon sa, lokaci hiyana ta ɗan sake sa, a hankali ya kwantar da ita a gefen sa ya ɗauki AC remote ya kunna yana kokarin lumshe ido, idan sa ya sauka saman face nata dake ta faman zufa saboda hijabin dake jikin ta,tsaki yaja tare da mirginawa ya matso kusa da ita ya sanya hannu ya ɗan ɗagota kaɗan ya chire mata hijabin
gaba ɗaya tula tulan breast nata a wajen sakamon mutsu mutsun da ta rinkayi a jikin sa ɗazun daman rigan ba ta da hannu shiyasa rigar ta gangaro ta koma chikin ta, zubawa breast nata ido yayi yana kallon na yan mintoci kafin ya mai da kallon sa kan face nata tasha kuka ta koshi hawaye a bushe a kumatun ta, komawa yayi ya kwanta tare da sauke ajiyar zuchiya, ya lumshe ido ya chi gaba da barchin sa
KANO NIGERIA
rungume diyana Aryan yayi sosai a jikin sa yana faɗin "my jidda me ya faru ne? shiru diyana batayi magana ba hannun sa ya sanya ya chire mata hannun da ta kama kanta da shi ya ɗauke ta chak ya wuche da ita toilet tsai data yayi a tsakiyar toilet ɗin ya kunna ruwan zafi sai data ruwan ta kusa tsakiyar baff ɗin wankan sai ya kashe ya kunna na sanyi sai da ruwan ya surku dai dai wanka, sannan ya juyo ya kalle ta tana tsaye tayi shiru kamar mai tunani a hankali ya kira sunan ta "my jidda" ɗago ido tayi tana kallon sa,alama ya mata da hannu akan tazo,ba musu taje riƙe ta yayi da kansa ya chire mata kaya jikin ta tana tsaye bata hana shi ba ɗaukan ta yayi a tare suka faɗa chikin baff ɗin shiru tayi sai kallon sa take kamar mai son tuna wani abun bai bi ta kan ta ba ya mata wanka ya fito ya ɗaura towel sanan ya fito da ita ya ɗaura mata towel ya ɗauke ta chak suka koma chikin ɗakin duk in da yayi binsa take da ido, kwata kwata baya son kallon ta a yadda taken nan dan zata iya jefashi chikin wani hali
zama saman gadon yayi ya zaunar da ita, ya shiga dressing room nashi chikin yan mintuna ya fito sanye chikin jallabiya fara hannun sa na ruke da wata farar jallabiyar, wajen ta ya dawo tana zaune kamar yadda ya barta zura mata jallabiyar yayi tare da zama kusa da ita hannun ta ya riko yana kallon cikin idon ta a nitse ya fara magana "my jidda kiyi magana mana why kika zauna shiru"
Book Chapters
Chapter 17
Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31