You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kissing nata ba tare da ya sani ba, sosai yake kissing nata tare da kara jawota jikin sa sosai duk abun da yake mata tana jin sa dan daman batayi barci ba da gangan ta faɗo jikin sa yaya Khalid ne ya rubuta mata a massage kar ta yarda ta rinƙa barci ba a jikin sa ba tarinƙa nuna masa kamar barci take ta mirgino jikin sa ta nuna kamar bata san ta faɗo jikin na shi ba,kara matse ta yayi sosai a jikin sa yana bata hot kiss tula tulan breast nata dake sokin sa a kirjin sane ya fara damun sa ɗan sassauta rungumar da ya mata yayi dan ya samu su ɗan raba jiki, kaɗan kaɗan yake jin feeling akan ta sai da yayi kissing nata mai isar sa sanna ya zame bakin sa daga nata tare da raba jikin su ya ɗan juya ya lumshe ido shi duk a tunanin sa tana barci bata ji me ya mata ba ita kuwa mutuwar kwanche tayi dan gaba ɗaya ya gama kashe mata jiki ya ruɗar da ita dannewa kawai take tunani ta shigayi anya zata iya biyewa shawarar yaya Khalid da yaya Aryan kuwa? Gaskiya wanna aiki ne mai wahala ba zata iya ba gaskiya sai dai su kawo wani shawarar da wanan tunani barci yayi awon gaba da ita, kusan tare barci ya ɗauke su
KANO NIGERIA
Auty Amarya na kokarin fita bedroom nata dan lokacin chin abinci yayi tasan yanzu gaba ɗaya su Abba sun haɗu a palo dai dai zata fita wayar ta dake bedside drawer tafara rigging kamar bazata je ta ɗauka ba sai kuma ta fasa ta koma taje ta ɗauki wayar sunan hajj sadiya che ta bayyana saman screen ɗin wayar zama tayi a bakin gado kafin tayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen ta
Daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace "Hello hajj ya hajara Ykk"dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace "lfy Ykk" "Alhadulillah daman nakira na sanar da ke ne yanzu gagarabadau ya mutu sai dai na kaiwa malamina dake bayalsa ya yi mana aikin Farida da Aisha" miƙewa tsaye Aunty Amarya tayi tare da dafe kirji chike da raza na tace "yaushe ya mutu!? "Yanzun nan gani nan ma a kofar gidan sa yanzu baafi minti ɗaya ba"komawa Aunty Amarya tayi ta zauna gaba ɗaya jikin ta ya mutu tama rasa me zata che wa haj sadiya "haj ya hajara ina zulaihat ne? Tun shekaran jiya bata kirani awaya ba itama malamin mu na Niger ya kusa kammala aikin ta tsakanin ta da Safras"tsaki Aunty Amarya ta ja kafin tace "zulaihat bata koma wajen ki ba ai ni tun shekaran jiya da na ganta da safe ban sake ganin taba na yi tunanin ta gaji da zama da nine ta koma wajen ki ai" "aa zulaihat bata dawo waje naba kai amma wanna yarinyar yanzu a gidan naki ma sai data fita yanzu tana chan kila wani saurayin nata tabi yarinya kwata kwata bata jin magana ni Allah yasa malamin nan ma ya gama aikin nan da wuri mu sa mu ayi auren nan kila idan ta shiga gidan Safras ɗin ta rage yawon banzan nan,barima na kira layin ta dan uban ta koma ina take ta wuce ta dawo" guntun tsaki Aunty Amarya taja dan ita gaba ɗaya yanzu haushi ma suke bata daga zulaihat ɗin har Haj sadiyar "haj sadiya sai munyi waya yanzu zanje palo muyi breakfast ne kowa ya hallara saura ni zamuyi waya anjima" tana gama faɗin hakan ta katse kiran ba tare da ta jira amsar haj sadiya ba mayar da wayar tayi saman drawer gefen gadon ta miƙe ta fice daga ɗakin tana mai bakin ciki mutuwar gagarabadau
Da sallam ɗauke a bakin ta ta shiga palon Abba gaba ɗaya wayan da suka rage a gidan suna zaune saman table diyana na zaune kusa da Aryan ɗin ta tayi shiru ta kasa chin abinci zama Aunty Amarya tazo tayi a kujerar kusa da Abba tana harara Aryan da diyana
"my diyana kici abinci mana" chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana,sai lokacin Aryan ya ɗago kai tare da ajiye wayar sa a gefe saman table ɗin ya jawo plate na abincin nata ya ɗauki spoon ɗin ya ɗibo chips ɗin ya kai mata bakin ta, shiru tayi bata buɗe baki ba kuma bata ɗago ba tana kallon kasa, mai da spoon ɗin yayi chikin plate ɗin ya ɗan rungumota da hannu ɗaya yana faɗin "my jidda menene kuma....bai karshen maganar ba yaji ta sake masa jikin ta gaba ɗaya a jikin sa kokarin faɗuwa take dan bai riƙe ta da kyau ba chikin zafin nama ya rikota da kyau yana faɗin "my jidda lfy me ya faru" miƙewa Abba yayi yana faɗin "suma fa tayi Aryan" tun Abba bai gama rufe baki ba Haidar ya miƙe da sauri ya nufi fridge ya ɗauko ruwa, ɗaukan ta Aryan yayi chak suka koma tsakiyar palo ya shinfiɗe ta saman karpet Haidar ya miƙo masa ruwa, chikin sauri ya balle bakin robar ruwan ya tarbo a hannu ya fara shafa mata a face nata gaba ɗaya su Ammi sun kewaye su suna jiran farfaɗo war ta zama saman sofa Abba da Aunty Amarya su kayi Ammi da Ummi kam sun kasa zama suna tsaye Omar Haidar suma suna tsaye,sai kwaɓe fuska Aunty Amarya take
Sau uku Aryan na zuba mata ruwa amma shiru bata farfaɗo ba sai a na huɗun ne taja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuchiya tun bata buɗe ido ba ta fara sambatu "Aunty farida yaushe ne jirgin mu zan tashi wlh na kosa na ga su hiyana ina kewar yaya Aryan kin san me Aunty farida ina zuwa gida Ammi zan fara runguma sai yaya Aryan sai kuma hiyana da Aunty Zahra aa na manta Ammi ce first sai Abba tukun nan yaya Aryan" shiru palon yayi suna sauraron sambatun diyana Allah sarki wato shine maganar ta na karshe tana cikin hayyacin ta lokacin guda Abba yaji idon sa ya chiwo da kwalla ba karamin tausayi diyana ta basu ba,mutun ya zauna chikin fitar hayyaci ba karamin abu bane, amma Alhadulillah dan da alama ta dawo hayyacin ta tun da har tana iya sambatu da sunayen yan gidan
Ji Aryan yayi ba zai iya chi gaba da jin sambatun nan nata ba tana tayar masa da hankali hannu ya sanya ya shafa fuskar ta tare da matsowa kusa da ita ya riƙe hannun ta ɗaya chike da kaunar ta ya fara magana "my jidda buɗe idon ki kallemu ai tun ɗazun jirgin naku ya iso gida" jin muryan Aryan ya sanya ta waro blue eyes nata da sauri tare da miƙawa zaune tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya miƙewa tayi da sauri ta rungumi Ammi tana murmushin tana faɗin "Ammi nayi kewar ki daman na faɗawa Aunty farida muna isa ke zan fara runguma" sosai Ammi ta rungume itama tana faɗin "my diyana nima nayi kewar ki sosai amma yanzu dai duk bamu ya kamata ki fara runguma ba mijin ki ya kamata ki fara nunawa farimcikin ki dan ya fimu bukatar ganin hakan" turun diyana ta tsaya chike da mamaki tace "Ammi miji kuma yaushe na samu miji" Abba ne ya ansa zanchen da chewa "Eh my daughter mijin ki" sakin Ammi tayi ta kariso wajen Abba tana faɗin "Abba wanene kuma mijin nawa? Da hannu Abba ya Nuna mata Aryan dake tsugunne ya kasa mikewa dan gani yake kamar har yanzu bata dawo dai dai ba a wani bangare na zuchiyar sa kuwa farincike yake yana godewa Allah da dawowar matar sa hayyacin ta
Kallon sa diyana tayi kafin ta ɗago ta kalli sauran jamaar palon chikin nitsuwa tace "Abba ni yaya Aiman nake so ba yaya Aryan ba da yaya Aiman mukayi alkawarin Aure ba yaya Aryan ba" tirkashi gaba ɗaya zuba mata ido jama'ar palon sukayi Aryan jin kalaman nata yake tamkar ana zuba masa garwashi a zuciya ashe Aiman yayi gaskiya shi diyana ke so chije lips nashi yayi lokaci guda idon sa ya sauya jijiyoyin kansa suka miƙe huci ya fara yi kamar wani zaki diyana ta haɗa masa zafi biyu lokaci guda na farko ta tuna masa da Aiman na biyu tace ba shi take so ba zuciyar sa zafi yake masa jiyake tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,chikin zafin nama ya miƙe yana kokarin barin palon da sauri Abba ya dakatar da shi ta hayyar riko hannun sa yana faɗin "koma ka zauna" ba musu ya koma saman sofa ya zauna tare da dukar da kai kasa umarni Abba yayiwa su Ammi akan su zauna zama sukayi gaba ɗayan su, saman sofas
"Kai Omar kaje ɗakin Aryan zakaga wata jaka baka mai ɗan girma ka kawomin" chewar Abba da sauri Omar ya juya ya fice daga palon
Dawo da kallon sa Abba yayi kan diyana dake zaune kusa da Ammi ya fara magana "my daughter kiyi hakuri da Auren da na miki ba tare da na tambayeki ba, abu na gaba Allah ya yiwa Aiman rasuwa inason ki anshi Aryan a matsayin miji domin da Aryan da Aiman duk abu ɗaya ne kuma Aryan ya riga Aiman fara son ki kema kuma Aryan ki ka fara so ba Aiman ba nasan kinche Aiman kike so ne ba dan komai ba sai dan alkawarin da kika masa akan zaku yi Aure nasan da kin san Aiman ya rasu ba zaki che hakan ba,ina jinjina miki da kokarin chika alkawari da ki kayiwa Aiman duk da ba shi kike so ba" shiru palo yayi ba abun da kakeji sai kukan diyana kuka take sosai kukan da take ne ya sanya Aryan ɗagowa baya san kukan ta ko kaɗan idan tana kuka zuciyar sa zafi yake masa
Chikin kuka tace "Abba dan Allah ka chemin wasa kake yaya Aiman bai rasu ba wlh na yarda yaya Aryan nake so ba yaya Aiman ba pls kucemin wasa ne yaya Aiman na ɗakin sa" kuka take sosai kakar ranta zai fita kasa jurewa kukan nata Aryan yayi ya miƙe ya dawo kujerar kusa da tasu ya zauna chikin kulawa ya fara magana "my jidda ya isa kukan nan kiyi shiru" "yaya Aryan kai ma ka yarda yaya Aiman ya rasu kenan? "My jidda dole na yarda dan ba'a wasa da mutuwa yanzu dai ki dai na yin maganar kinji idan ba haka ba zaki sanya zuciya ta ta fashe" rage sautin kukan nata tayi dai dai lokacin Omar ya shigo hannun sa ɗauke da jakar da Aryan ya bawa diyana tsaraba lokacin da ya dawo makka
Ansar jakar Abba yayi ya buɗe ya fido da abubuwan dake chiki wayan nan Box guda biyu da Aryan ya ɓuye bai nunawa diyana ba Abba ya ɗauko ɗan babban ya fara buɗe wa, wani dangareren sarkan gold ne wanda ya ansa sunan shi gold ne awajen,mai matukar kyau da tsada sai ɗaukan ido yake ɗago kai Abba yayi ya kallin diyana da ta kwantar da kanta jikin Ammi tana kuka kasa kasa "my daughter ga sadakin ki 100m shine kuɗin sadakin ki daga mijin ki" hannu Ammi ta sanya ta ansa ta sanyawa diyana a tafin hannun ta tana faɗin "an sa ki gani my diyana" kuka kawai take taki kallon sarkan buɗe ɗayan kwalin Abba yayi ya miƙawa Aryan ansa Aryan yayi ya fito da wasu kananan Fararen box masu bala'i kyau daga chiki buɗe ɗayan yayi dan kareran diamond ring ne wadda ya amsa sunan sa diamond sai kyalli yake yana ɗaukan ido ring ɗin ɗauke yake da harafin A ajikin sa ta tsakiya ajiyewa yayi a gefe ya ɗauko ɗayar box ɗin ma ya buɗe shima ring ne irin ɗaya da wan da ya buɗe da farko komai nasu ɗaya sai dai wanan ɗauke yake da harafin D a jikin sa ɗago kai yayi ya kalli diyana dake ta faman kuka kasa kasa yace "my jidda tashi ki zo"tashi tayi tazo gaban sa ta tsaya dan saman sofa mai zaman mutun ɗaya yake zaune hannu ya sanya ya nuna mata saman chinyar sa akan ta zauna satar kallon su Abba tayi kasa kasa yana kallon chikin idon ta miƙewa Abba yayi yana faɗin "zama chikin turawa ya ɓatamin ƴaƴa basa kunya ta yanzu kwata kwata" ya kai karshen maganar tare da fice palo chikin sauri su Ammi suka bi bayan sa taɓe baki Haidar yayi ya fice shi da Omar suna mamakin yaya Aryan
Aryan Kamar jira yake su Abba su fita ya jawota jikin sa yana faɗin "my jidda ya isa kukan nan haka kwantar da kanta tayi saman kirjin sa kasa kasa tace "yaya Aryan kukan ne ai yaki tsayawa" hannu ya ɗaura saman face nata yana goge mata hawaye yana faɗin "to ya isa karki bari hawayen ya sake fitowa kinji? Gyaɗa masa kai kawai tayi ta kara lafewa a kirjin sa hannun ta ya riƙo ya sanya mata diamond ring mai tambarin harafin A sanan ya miƙa mata mai tambarin harafin D yace ta sanya masa ansa tayi ta sanya masa a ya tsan sa na kusa da karamin ba karamin kyau ring ɗin ya musu ba kamar dan su akayi shi
Kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace "my jidda tashi muje na baki abinci" maƙe kafaɗa tayi chikin shagwaɓa tace "aa na koshi yaya Aryan" jan karan hanchin ta yayi chikin wasa yana faɗin "idan baki chiba zan miki Allura" chikin sauri tace zanci to amma kaɗan" ba tare da ya sake magana ba ya miƙe ya saɓata a kafaɗar sa tana faɗin "yaya Aryan dan Allah ka sauke ni zan tafi da kafana" bai tan ka taba ya wuche ya ɗauki Box na sarkan sadakin ta da sauran kayan ya fice daga palon kai tsaye part na shi ya wuce
Masu karatu mu damalmale da ku a soyayyar Habibi da jiddan sa gobe idan mai dukka ya kai mu su habibi yau abun nema ya samu 😹😹
Ina muku fatan alkhari masoyana masoyan Duk Karfin Izzata fatan Allah ya chika muku burin ku na alkhari
Ina miko gaisuwa da jijjina gare ku
Aunty Asma'u
Aunty Hauwa'u
Maman Twins
My mum
Dr Aisha
Aisha
Hauwa'u yar adamawa jinin yola
Sister Halima
Sister Deeja
Aunty Amira
Nana farida
Deenat Ahmad
Maman Amir
Hafsat Rabi'u Abubakar
Da duk sauran wayan da ban samu daman kiran sunan su ba ina godiya ina ganin comments na ku ya sanyani farimciki da nishaɗi yana rage min kishin hiyana da nake ki dan na lura hiyana ta fara shisshigewa masoyina 🥲
Pls a bani hot🔥 comments
💋Duk Karfin Izzata 💋
💖The Talent Troupe Writer's 💖
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
Maman Shureim gaba ɗaya wanan page ɗin na kine more love 🥰
Book 2
Page 23
Uk
4:40am ya farka daga barci slowly ya waro idon sa waje kyakkyawar face nata ya fara chin karo da shi ba karamin kyau hasken blue light na ɗakin ya ma face nata ba, barcin ta take chikin kwanciyar hankali ya ɗan ɗauki mintoci yana kallon face nata kafin ya miƙe zaune tare da zuro kafafun sa kasan kagon gently ya miƙe ya fara tafiya toilet ya nufa brush yayi sannan yayi wanka ya fito ya shirya chikin fara jallabiya ya fice daga ɗakin ya nufi masallaci
Yana fita ba jimawa ta farka da kyar ta iya buɗe idon ta dan barci bai ishe taba kiran Sallah ne ya tashe ta mikewa tayi ta nufi toilet jim kaɗan ta fito ɗaure da towel jallabiyar sa ta sanya ta sanya karamin hijabi tayi sallah zama tayi saman dadduma bayan ta idar da sallan ta fara yiwa diyana addu'ar Allah ya bata lfy sai karfe 6am dai dai ta tashi daga kan daddumar ta naɗe ta mai da mazaunin sa
Toilet ta fara wanke wa kafin ta fito ta gyara masa ɗakin tsab ta sanya wani daddaɗar turare ɗaki mai bala'i kamshi sai da ta gama komai sanna ta wuce dressing nashi ta chire masa jallabiyar sa ta ɗaura towel ta dawo ta tsaya a gaban mirrow kallon kan ta tayi sosai kafin tace "Allah sarki yaya Prince wlh yanzu zan ɗaura ɗamarar ya kar ka a gidan nan domin son ka yana neman halakani dole nayi amfani da shawarar Aunty farida, da wanna tunani ta fara shafa body lotion nashi masu kamshi da tsada bayan ta gama ta nufi trolley ɗin ta sosai ta shiga wargaza kayan nata tana neman kayan da sukafi lallacewa wadda idan ka sanya zatayi kama da karuwar gaske koma abun da ya fi karuwa chan kasan babban trolley ta samu wasu wanduna da ba zasu wuchi chinyar taba da yan rigunan su masu kama da singlet ɗaga rigar tayi tana kallon rigar ba zata wuci chibiyar taba murmushi tayi ta mai da ta ajiye tana faɗin "wanna sai da daddare" kara watsa kayan tayi sosai wani shegen wando ta sake chin karo da shi shima ba zai wuchi guiwar ta ba sai dai shi rigar sa zata saukar mata zuwa marar ta da rigar da wandon duk jikin su robane, miƙewa tayi da su a hannun ta tana murmushin chikin sauri ta sanya su tanayi tana sanyawa Zahra albarka da addu'ar Allah ya bata baby mai kyau kamar yaya Khalid ɗin ta, sai yau taji daɗin kayan da Zahra ta zaɓa mata, sosai kayan suka kamata sunfitar mata da ainihin surar jikin ta ba karamin kyau tayi ba ta zama kamar waruwar gaske
bayan ta gama sanya kayan ta kwashe wayan da ta fitar ta mai da chikin trolley ɗin sanna ta nufi gaban mirrow wow ita da kanta tasan tayi kyau sai dai mugun kunya take ji yayay Prince yazo ya ganta a haka tara gashin kanta tayi ta ɗaure a tsakiya da gangan ta ɗauki perfume nashi ta sanya a jikin ta dan ta lura idan ta taɓa wani abu nasa hakan yana sa yazo jikin ta da niyar hukun tata saman gado ta koma ta kwanta tana tunanin ya kamata a che ya yaya Prince ya dawo yanzu, bata kai ga rufe tunanin nata ba sai gashi ya shigo kallon ɗaya ya mata ya kau da kai ya wuce ya nufi toilet har ya kai bakin kofar toilet ɗin ba tare da ya juyo ya kalleta ba kasa kasa yace "ki fitar min da kayan sawa da suka dace da ni" yana kai karshen maganar ya shege toilet ɗin tunani Hiyana ta farayi ki fitomin da kayan sawa da suka dace da ni kenan yana nufi wanda na fitar masa jiya basu dace da shi ba kenan? to ni ya za'ayi in san wan da suka dace da shi kai dole na tambayi Aunty farida ta faraɗamin wasu kayane sukafi dacewa in rinƙa fitar masa idan ya buƙaci dana fitar masan da wanna tunani ta miƙe ta shiga dressing room ɗin,wandon jeans baki da t-shirt ash ta fiddo masa da shi ta ɗaura saman gado ta wuce kitchen dan ɗauko masa breakfast
lokacin da ta dawo ɗakin har ya fito yana shiryawa godiya tayiwa Allah da ya sanya tafita kafin ya fito ba dan haka ba da zata iya sumewa dan shi yaya Prince ba ruwan shi bai san kunya ba zai iya shiryawa ma a gaban ta,bakaramin daɗi taji ba ganin yau ya sanya kayan da ta zaɓa masa
saman table ta ajiye masa trey mai ɗauke da kayan breakfast ɗin,tana kokarin zama saman sofa sai ta tuna massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa ta rinƙa taya bgs sanya kaya da sauri ta fasa zamar ta miƙe ta karisa wajen sa dai dai lokacin yana sanya buttin ɗin rigar, ba tare da tayi magana ba ta sanya hannu chike da tsoro kirjin ta na dukan uku uku ta fara tayashi sanya wa, kasa kasa yake satar kallon ta mamaki ne ya kama shi wato yarinyar nan ta dai na tsoron sa kenan,amma duk da hakan ya ji daɗi sosai har chikin zuciyar sa da ta taya shi sanya buttin ɗin afili kuwa ɗaure fuska yayi chikin tsawa yace "ke me haka!? Chikin sauri ta chire hannun ta daga saman rigar nashi da cool voice tace "kayi hakuri ba zan sake ba" ko kallon ta bai sake ba ya chi gaba da sanya buttin ɗin sa bayan ya kammala ne ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna da sauri ta karisa wajen ta fara sarving na shi sai da ta gama komai ta tura masa gaban sa sanna ta tsugunna chikin girmamawa tace "yaya Prince dan Allah ka kiramin Aunty farida" da hannu ya mata nuni da wayar sa dake saman bedside drawer ba tare da yayi magana ba miƙewa tayi ta ɗauko wayar ta dawo ta miƙa masa tare da ɗan tsayawa daga gefe layin Aunty farida ya kira wayar na fara ringing ya miƙa mata
Ansar wayar tayi ta nufi kofar fita dan ta koma palo bata son yaji me zatace tsawa ya daga mata wadda ya sanya ta juyowa ba shiri "in zaki je!? "Palo zanje" ta bashi amsa chikin tsoro batare da ya kalli in da take ba ya mata nuni da hannun sa akan ta wuce wajen hutawar sa tayi wayar achan,ba musu ta wuce ta nufi wajen already Aunty farida tayi picking call ɗin tun ringing na farko duk abun da ya faru a kunnen ta ya faru tana jin su, zaman saman sofan dake wajen hiyana tayi kafin ta manna wayar a kunnen ta ta fara magana
"Hello Aunty farida in kwana" "my Hiyana kina ji yanzu ba gaisuwa zamuyi ba kin ga wayar sa ne kuma lokacin tafiyar sa wajen Aiki yayi kawai muyi abun da ke gaban mu yanzu wani chi gaba aka samu"shiru hiyana tayi tana ɗan muku muku bazata iya faɗaqa Aunty farida chewar Bgs yayi kissed nata ba,jin tayi shirune ya sanya Aunty farida tace "my hiyana karki ɓoyemin komai ki faɗa min da wuri kinga bamu da time ko, sunkuyar da kanta kasa kayi tamkar Aunty farida na gaban ta chike da jin kunya ta fara bata lbr duk abun da ya faru tsakanin ta da bgs,murna sosai Aunty farida tayi kafin tace "yanzu bari na faɗa miki kayan da ya dace kirin ka bashi da lokacin da suka dace idan ya dawo aiki kinga yana bukatar ya huta ya sha iska to wannan lokaci kananan kaya zaki fitar masa dan su yake buƙata idan ya shiga wanka da daddare kiyi sauri fitar masa da kayan barci masu laushi kuma Prince ya fison abu fari komai nashi farine yana son kalan fari sosai sai ki kula da wanna ma idan da safene to kayan Aiki zaki fitar masa idan kuma ranar weekend ne to ki karanche sa shin yana fita weekend ne idan yana fita to kaya masu kyau da tsada zaki fitar masa irin jeans da t-shirt ba manyan kaya ba aikema ranar kinyi wauta Prince baya sanya kayan hausawa idan ba dole ba, abu na gaba idan kuma baya fita weekend to jallabiya zaki fitar masa sanan ki rinƙa rigasa tashi sallar asuba dan idan ya shiga wanka ki fiddo masa da jallabiya da zai sanye yaje masallaci,yanzu dai sai mu bari haka sai anjima zan kira ku ta wayar Auta akoi wani shirin da zamuyi kuma ki dage akan shawarar Khalid da Aryan yanzu ki mai da masa da wayar sa dan naga lokacin ya tafi zaije wajen aikin sa kar kije kiyi laifi rike masa waya da kikayi" miƙewa tsaye tayi kafin tace "to Aunty farida na gode sosai" "ba sai kin min godiya ba ke dai ki chigaba da yin abun da na faɗa miki In Sha Allah mun kusa nasara" a chikin zuchiya ta amsa da amin tare da chiro wayar daga kunnenta bata iya komai a wayar san nan ba dan haka bata katse kiran ba ta mai da masa da wayar yana zaume saman sofa kamar yadda ta bashi haka ta dawo ta same sa kusa da shi ta zauna tare da
Book Chapters
Chapter 20
Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31