You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
faɗin hakan ya fice daga palon, ajiyar zuchiya Abba ya sauke daman ya san haka zata faru dan dukka yayan sa basu yarda da gargajiya ba a kan boko suka tashi kuma a hakan suke tafiya har yanzu
Kallon Abba malam yayi ya lura Abba ya shiga damuwa sosai chikin ni tsuwa ya fara magana "Ranka ya daɗe karka damu in dai irin yayan nan naka ne mun saba haɗuwa da ireren su yanzu dai zan sanya a kawo maka ruwan addu'a sai ka san yadda zakayi ka baiwa ita yarinyar" sunkuyar da kai Abba yayi dan kwata kwata bai ji daɗi ba ache ya sa a kira masa babban malami kamar wanna Aryan ya masa irin wanna chin fuska haka abun sam bai yi ba
dafa kafaɗar Abba malam yayi yace "karka damu yanzu dai kuyi taka tsan tsan domin masu bin ku da wanan asiri asiri da tsuɓɓace tsuɓaɓan nan dama masu bin family ka da sharri suna tare da kai makusan tan kane yanzu kasan yadda zakayi ka bawa duk family ka ruwan addu'ar nan da zan aiko ma,domin da alama makiyin ku na kusa sosai da ku sanan zan aiko maka da turaren ayi hayaki dukka gidan nan dan na san koda an bawa yarinyar addu'ar ita ta warke zaa iya sake yima wani asirin sai ku shirya" malama na gama magana ya miƙe ya nufi hanyar fita, kasa tashi Abba yayi yaje ya raka malam tunani ya shigayi makiyin mu na tare damu to wanene ke mana wanna abun? gaba ɗaya Abba yayi iya tunanin sa a gidan sa dai bai ga wan da zai iya aika ta wanna abun ba sai dai in daga wajen,jiki ba kwari ya miƙe ya shige bedroom na shi
UK
4pm
Sun gama shiryawa gaba ɗayan su suna zaune a babban palon kasa suna jiran hiyana zasu tafi wajen shakatawa sai murna su Zahra keyi yau yaya Khalid zai kai su yawo,gaba ɗayan su sun shirya chikin dogayen riga sai dai rigar ta kama su sosai Zahra da lamrat sun sanya ɗan karamin hijabi baki a kansu ita kuwa amrat ɗan karamin mayafi ta sanya yaya Ahmad sai tsokanan su yake yana dariya sunyi kyau da su abun su kamar ka sache su ka gudu da su dan kyau wajen 10mins suna zaune suna jiran hiyana shiru shiru tsaki Fahad yaja kafin yace "amrat je ki kira sister tazo mu wuce" da sauri Zahra ta miƙe tana faɗin "bari naje na kirata" bata jira amsar su ba ta haura sama.
Zaune a bakin gado ta isko hiyana ta gama shiryawa chikin wandon jeans baki crazy,da yar t-shirt fara mai laushi rigar tana da ɗan dogon hannu amma bai kai karshen hannun taba ta ɗaure gashin kanta a tsakiyar kai
sai chika take tana batsewa,kallo ɗaya Zahra ta mata ta fahimci abun da ya hanata fitowa dariyar mugunta ta guntse chike da iya shege da tsoka Zahra tace
"Aunty Hiyana yaya Khalid yace karki kuskura ki kara 1mins baki fitoba in kika kara tafiya zamuyi mu barki" wani mugun kallo ta wurgawa Zahra ji take kamar ta shako ta mata duka,ganin haka ya sa Zahra ta kariso chikin ɗakin ta chire hijabin jikin ta ta sanya mata ta kamo hannun ta suka nufi kofar fita,binjikin ta da kallo hiyana tayi kwata kwata hijabi a iya kirji ya tsaya mata bata san ya zatayi ba bazata iya fita gidan nan da wanan shigar ba gashi kuma tana mutuwar son fita dan ta gaji da zaman gida,runtse ido tayi ta rasa ya zatayi ahaka Zahra ta jata har palo, Khalid na ganin su suka miƙe a tare suna faɗin "muje ko? da sauri Zahra ta koma ɗaki ta ɗauko wani hijabin ta sanya ta dawo palo
Jerawa sukayi kowa ya rike hannun matar sa hiyana da yaya Ahmad suka gero daga ƙarshe suna fita harabar gidan dai dai lokacin motocin Bgs ya danno kai chikin gidan, tsayawa su Khalid sukayi suna jiran fitowar sa su gaisa
Jibga jibgan sojojin sa ne suka fara dirowa kasa daga saman nasu motocin ɗaya daga chikin su ya buɗe wa Bgs kofar motar ɗayan kuma ya buɗewa Abdol ya fito,jeruwa sojojin sukayi suka fara sara masa bai bi ta kan kowa ba ya nufi chikin gida ko kallon in da su Khalid suke bai yi ba ya wuce su
har ya kai bakin kofar shiga palo ya dakata ba tare da ya juyo ba yace "ke zo ki haɗamin fruits da Black tea" yana gama faɗin hakan ya wuce chiki, hiyana kamar zata yi kuka haka ta juya ta koma chikin gidan
Kallon su Yusuf Khalid yayi yace "muje ko" "aa yaya Khalid mu ɗan jira sister mana" chewar Yusuf murmushi Khalid yayi kafin yace "baza tazo ba muje kawai" "kamar yaya baza ta zo ba kuma" Ahmad ya tanbaya yana tsare Khalid da ido,
"Auta kuje wajen mota ku jiramu" chewar Khalid ba musu Zahra lamrat amrat suka wuche suka nufi wajen motocin suka tsaya
murmushi Fahad yayi ya fara magana "daga jiya zuwa yau na lura da wani abu tsakanin yaya Prince da sister, amma ba zan iya fassara menene ba mu dai je zuwa" tsaki Khalid yaja kafin yace "ai tun ranar dana sanya snake a toilet na sister, na fara sanya yakinin akan Bgs zai sauya dole idan suka koma kwana ɗaki ɗaya, sai dai ba yanzu ba sai alluran jikin sa ta sake sa daman 2 weeks alluran ke ɗauka ina ga ayanzu ya kai 10 days da yiwa kansa allura wlh duk ranar da alluran nan ta sake sa zai fara sha'awar sister daga sha'awa kuma sai soyayya ta biyo baya" dogon salati Fahad yayi kafin yace "amma yaya Khalid ka iya shirya kitinurmura daman kai ka sanya snake a toilet na sister?" dariya Khalid yayi kafin yace "ai ba a iya nan na tsaya ba ma nayi abubuwa dayawa sai dai ba zan faɗa muku ba wlh sister tana bani tausayi gashi Auren ta da Bgs babu saki to kunga tun da babu saki dolene a matsayin mu na wayan da suka san wanene Bgs mu tsaya tsayin daka mu taimaka mata dan ta samu fatinciki ni dai yanzu na ɗaura ɗamarar yaki da Bgs wlh ko jiya naso zuba masa magani chikin abinci amma dana tuna wanene Bgs sai na fasa dan idan na kuskura na zuba masa magani yasha tofa inaga zamu iya ɗaukar gawar sister dan bazata iya ɗaukar Bgs a yanzu ba tayi kankanta sai gaba" Yusuf ne ya ansa zanchen da chewa "ni nasan dole Bgs zai fara son sister sai dai matsalar bai san me so ba bai iya so ba,bazai taɓa gane yana son taba dan bai taɓa mu'amala da wata mace ba idan ba iyayen mu ba ko Aunty mardiya bai taba zama yayi magana da ita ba kunga ko ya fara son sister ba zai taɓa gane yana son taba" "kabar wanna maganar Yusuf duk na riga na gama shiri a kan haka yanzu ma na gama shiryawa sister yadda zata masa idan alluran nashi ya sake sa,bazan iya fuskantar sister na faɗa mata baki da baki ba shi ya sanya na rubuta mata massage a waya lokacin da na sai musu waya yanzu dai lokacin kawai zaku jira nan da two days dole Bgs ya fara sha'awar sister dole kuma ya fara kula ta bashi da zaɓi dan ba zan taɓa bari ya sake yiwa kansa allura ba,dani da Aryan mun gama shirya masa kitimurmura ta yadda ba zai sake yiwa kansa allura ba" chewar Khalid ya karisa maganar tare da kama hanyar tafiya "laaaa yaya Khalid wato kai da yaya Aryan kuna munafurtan yaya Prince ko?to sai na faɗa masa" chewar Fahad yayi maganar chikin raha "amma ni ina ganin kamar mujira sister dan wlh naga alamar tana san zuwa sosai kuma daman dole zata so zuwa zama waje ɗaya fa takurace" chewar yaya Ahmad, juyowa Khalid yayi ya dakata da tafiyar da yake yace "sister fa baza taje ba idan kun lura ba Black tea ko fruits yake son shaba kawai shigar da tayi zamu tafi ne bai masa ba lokacin da ya fito daga motar sa wlh ina kallon sa kallon ta yake ta kasan ido kayan jikin tane bai masa ta fita da su ba shi ya sanya, kuma dai wani lokaci sai ku rinka yin abu kamar baku san shi ba komai da Bgs zai chi a duniyar nan to da time na shi kai bama abun chi ba komai da zai aikata yana da lokacin yin sa baya barin wani lokacin ya shiga na wani yanzu fa karfe 5 ake nema ba zai chi wani abuba sai 12 dare kun san Bgs da bala'i kishi ko ku da kuke yan uwan sa ma yaya bare sister da yanzu tauraron ta zai fara haskawa a zuciyar sa" yana kai karshen maganar chikin raha da tsokana tare da wuche ya nufi wajen su Zahra chikin sauri su Yusuf suka bi bayan sa suna dariya,chikin motocin su suka shiga kowa da matar sa ya zauna yaya Ahmad shi kaɗai,a tare motocin suka fita gidan
A ɓangaren hiyana kuwa tana komawa chikin gida kitchen ta nufa ta shirya masa abun da ya bukata ta ɗauka ta nufi part na su zaune saman sofa a chikin bedroom ta same sa, ya jingina kan sa yana kallon sama chikin nitsuwa ta tako zuwa wajen saman table ta ajiye masa try ɗin ta dawo gabansa ta tsugunna ta fara chire masa ta kalmar kafar sa tana faɗin "sannu da dawowa ya Aiki" bai amsa mata ba kuma bai sauko da kansa ba yana kallon sama, chire masa ta kalmi tayi tare da safa ta ɗauka ta wuce ta ajiye wajen da ya dace, ta dawo tana kokarin tsugunnawa yayi saurin ɗaga mata hannu tare da nuna mata kusa da shi akan ta zauna ba musu ta zauna ba tare da ya kalle taba yace "ya sunan mahaifiyar ku? "Sunan ta Fateema amma yan garin mu suna che mata Ummi dan sunan kakan mune wadda ta haifi baban mu...ba ta karisa maganar ba ya ɗaga mata hannu yana faɗin "iya sunan ta na tambaya ban nemi wani karin bayani ba"shiru ta ɗan yi na yan mintoci kafin tace "yaya Prince in tafi? Sai lokacin ya sauko da kallon sa kanta ya tsare ta da ido tare da ɗaga mata gera ɗaya alamar ki tafi ina, narai narai tayi da fuska chikin dakiyar zuchiya tace "yaya Khalid ne zai kai mu yawo shakawata kuma suna jirana" ta kai karshen maganar kamar zatayi kuka "ba zakije ba" yana kai karshen maganar ya mai da kansa ya jingina yana kallon sama,ji take kamar ta shake sa dan haushi ta gaji da zaman gidan nan,ta gama tsarawa yau zata fita,shiru ta zauna da kamar zatayi kuka amma sai ta danne dan tayiwa kanta alkawari ba zata sake bari yaya Prince yaga kukan taba,da ta tuno ranar Monday zasu fara zuwa school sai tayi murmushi ko ba komai ranar Monday zata fita ai
"Yaya Prince ga tea ɗin fa zai yi sanyi" ta faɗa tana satar kallon sa,shiru yayi na ɗan lokacin kafin yace "ɗauka ki sha" "ni bana shan tea" ta bashi amsa chike da tsoron me zai biyo baya, wani mugun kallo ya gefa mata wadda ya sata ɗaukan cup ɗin tea ɗin ta fara sha tana ɓata fuska dan Black tea ɗin ko sugar babu a cikinta sai lemun tsami miƙewa yayi yama faɗin "ki fitarmin da kayan sawa" ya kai karshen maganar yana shigewa toilet
Yana shiga toilet tayi saurin ajiye cup ɗin tana goge bakin ta tare da fito da harshen ta waje tana gogewa dressing room nashi ta shiga kayan sa ta fara bi da kallo a shesshirye suƙe wajen wandon jeans daban wajen t-shirt daban wajen suit daban wajen takalmi agogo daban kowanne wajen sa daban tasha ruwan mamaki lokacin da idonta ya sauka kan kayan hausawa ashe yaya Prince yana da kayan hausawa gasu dayawa ma hannun ta har rawa yake wajen fito masa da jumpa da wando na wata dakakkiyar shadda mai bala'i tsada da kyau fari tas, chikin sauri ta zaɓo masa farar takalma da dangareren agogon diamond ta fito ta ajiye masa saman gado ta ta koma saman sofa ta zauna.
After 45mins
Ya fito ɗaure da towel a kugun sa kallo ɗaya yayiwa kayan da ta ajiye masa a saman gado ya kawar da kansa kai tsaye ya wuche gaban mirrow ya fara gyara gashin kansa duk abun da yake tana zaune tana satar kallon sa bayan ya gama gyara lallausan bakin gashin kan sa ne ya shafa body lotion nashi masu kamshi da tsada sanna ya wuce dressing room nashi jim kaɗan ya fito shirye chikin wando 3quarter fari da singlet fari tas ya ɗauki laptop nashi dake saman table ba tare da ya kalli in da take ba ya fice daga ɗakin
jiki ba kwati ta miƙe tazo ta kwashe kayan da ta fiddo masa da su ta mai da dressing room ɗin ta fito ta wuce wajen hutawar sa na chikin ɗaki
Gaisuwa da jinjina gareku yan Duk Karfin Izzata paid group Allah ya bar zumunci ina muku fatan alkhari ina matikar miko godiya gareku masu min comments ina magana ne akan yan duk karfin izzata comments section group ina jin daɗin comments naku ina godiya da muku fatan alkhari, masumin addu'oe ina godiya sosai Allah ya saka muku da gidan aljan na, wayan da basa min comments kuma ina gaishe ku Allah ya barmu tare ina kaunar ku love u all lodi lodi
💋Duk Karfin Izzata 💋
💖The Talent Troupe Writer's 💖
💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*
💋I Hate you masoyiya gidan Aunty lodi lodi💋
💋Aunty sadeeya ina kaunar ki lodi lodi💋
💋Mum sayyid ke kam naki kaunar na daban ne love u lodi lodi 💋
Book 2
Page 22
Uk 1am
Tana kwance saman katafaren gadon sa ta kasa barci duk bayan minti ɗaya sai ta duba time shiru shiru Bgs bai dawo ba tun abun baya damun ta har ta fara shiga damuwa miƙewa tayi zaune saman gadon tana tunanin ina ya tafi Allah dai ya sa lfy tun da sukazo gidan nan bai taɓa wuce 12:10am a waje ba shin me ya daɗar da shi yau, gajiya tayi da zama ta miƙe tsaye ta fara kai kawo tunawa tayi ɗazun ta kalli waya a saman table ɗin da yake ajiye ta kardu da system nashi da sauri ta nufa wajen tana addu'ar Allah ya sa akoi sim a chikin wayar,hannun ta har karma yake wajen ɗaukar wayar ta kunna haske screen ɗin,wani Cool murmushi ta saki lokacin da ta ga akoi sim a chiki already ta haddace number sa a kai chikin sauri ta shigar da number ɗin sa chikin wayar burinta kawai ta kira shi batayi tunanin me zai je ya dawo ba, sau biyu tana kiran wayar sa bai ɗaga ba sai a na uku ya ɗaga tattara nitsuwar ta tayi gaba ɗaya chikin sanyin murya tace "ina wuni yaya Prince" shiru yayi na ɗan lokacin kafin yace "me menene!? "Babu komai daman naga baka dawo bane har yanzu shine nace.... Bata kai karshen maganar ba ya daga tar da ita ta hanyar chewa "kawomin black tea ɗakin bincike" "yaya Prince ban san ɗakin ba ai"guntun tsaki yaja kafin yace "ki fito palo awajen da ake ajiye remote ki duba zakiga farin remote ki ɗauka ki sai ta sama ki dan na open stair case zai sauko sai ki haura ina wajen" yana gama faɗin hakan ya katse kiran, murmushi ta saki kafin ta ajiye wayar ta fice daga ɗakin
Kitchen ta nufa ta haɗa masa black tea kamar yadda ya buƙa ta ta dawo palo kamar yadda ya sanar da ita haka tayi, tasha ruwan mamaki lokacin da ta ga wani ɗan siririn stair case na saukowa bayan ta danna remote,mutun ba zai taɓa zaton akoi wani abu a saman nan ba wai shi stair case tsoro hawa taji dan kar ta hau ta makale amma da ta tuna yaya Prince ɗin ta na wajen sai ta samu kwarin guiwa,
Chikin zafin nama ta haye saman stair tana hawa stair case ɗin ya naɗe kansa da kansa
wani katafaren ɗaki ne awajen mai chike da computers da na urori da ban daban gaba ɗaya ɗakin gauraye yake da hasken computers, yana tsaye gaban wata makekiyar desktop ya sanya wata na'ura a idon sa kamar glass sai aiki yake tika,tsayuwa tayi tana bin ɗakin da kallon kafin ta mai da kallon ta kansa sanye yake da yar gakeren wando wadda ta ɗame sa sosai babu riga a jikin sa da alama wandon ma dolece ta sanya ya sa dan kallo ɗaya zaka masa ka gane haka asalin kyakkyawar suran jikin sa ta bayyana gaba ɗaya hannayen sa da chinyoyin sa baki lallausan gashi ne a kwance awajen sai sheki yake kai kallon ta tayi saman ɗamtsen hannun sa daƙe murɗe dama dama wani mugun farinciki take a duk lokacin da ta kalli kyakkyawar bakin gashin dake kwance a saman faffaɗar kirjin, Cool murmushi ta saki lokacin da idon ta ya sauka a kan haɗaɗen bakin gashin kansa wadda ke baje har bayan sa kasan chewar bai ɗaure gashin ba ya sake ta har baya
duk da sanyin Ac dake ɗakin hakan bai hana shi zufa ba saboda Aikin da yake tika kusa da shi tazo ta tsaya tace "sannu da Aiki yaya Prince" bai an sa ba kuma bai juyo ba aikin sa yake sosai da alama aiki ne mai muhimmanci
Tana tsaye shi kuma yana ta aikin sa almost 10mins da zuwan ta sanna ya chire na'uran dake fuskar sa ya juyo kallon ɗaya ya mata ya ɗauke kai kayan barcine riga da wando a jikin ta fari tas masu laushi sai ɗan karamin hijabin da bai wuce kirjin ta ba ta sanya a kanta baki
ansan cup ɗin hannun ta yayi ya ɗora saman wasu takar du dake wajen chikin sanyi murya yace "wayace ki ɗauki waya har ki kirani? Banche duk wanda zaki kira sai kin sanar da ni ba!? Baya baya ta farayi tana girgiza kai tana addu'a a zuchiyar ta Allah ya sa kar ya bugeta,takowa ya farayi a hankali yana bin ta tana baya baya, "ba dake nake mana bane? Kasa magana tayi ta chigaba da yin baya tana girgiza yana bin ta kai har suka kure bango,runfa ya mata da faffaɗar kirjin sa chikin tsawa yace "bazaki bani amsa ba sai na ɓallaki"slowly ta ɗago kanta tana kallon saitin wuyar sa ta fara magana "daman naga baka dawo bane shi ya sa na kiraka amma kayi hakuri ba zan sake ba" har chikin ran sa yaji daɗin amsar ta dan duk yan uwan sa ba wanda ya taɓa damuwa ko ya kirasa awaya idan ya wuce lokacin dawowarsa ɗan garama Aryan daman shi duk abun da suke a tare suke duk kuma in da zasuje tare suke zuwa for the first time yau sister sa ta damu da bai dawo ba har ta kirasa awaya wow wanan abu yayi,afili kuwa ɗaure fuska yayi sosai chike izza yace "idan kika saƙe ɗaukan waya kika kira sai na hukun taki!" Ɗago kai tayi sosai dan ya fita tsawo sosai idan suna tsaye tana son kallon face na shi sai ta ɗaga kai sosai kwata kwata tsawon ta bazata wuche kirjin sa ba da kanta da komai
Kallon face na shi tayi kafin tace "In Sha Allah ba zan sake ba amma dan Allah idan ba zaka dawo da wuri ba ka faɗamin kafin ka fita" abu guda ɗaya ne ke burgesa da yarinyar nan koda batayi laifi ba idan ka mata faɗa tana ansan laifin tace kayi hakuri bata damuwa wajen dole dole sai ta sanar da kai ba tayi laifi ba da tayi da bayayi ba zatache kayi hakuri bazata sake ba kuma tana kokarin taga ta kiyaye abun da kayi magana a kai, yana sane ba ita take faɗawa Ammi yana mata mugun taba amma da yace idan tasake faɗa sai ya bugeta duk da ba ita ɗin che ta faɗan ba bata nuna ba ita ɗin bace hasalima hakuri ta bashi ta ansa laifin da ba tayi ba
Shiru suka tsaya yana kallon face nata, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jiran taji me zai che da ita gaba
saukar hannun sa taji saman kanta zame mata ɗan karamin hijabin jikin ta yayi a jefar kasa shafa gashin kanta ya shigayi tare da jawota jikin sa, jin abun tamkar mafarki Hiyana take, sun daɗe a haka yana shafa gashin kanta kafin ya zame hannun sa daga kan nata ya ɗago habar ta suna kallon juna matso da face nashi yayi dai dai nata chikin sauri ta runtse ido kirjin ta na dukan uku uku kasa kasa yace "ki shirya gobe zan sanya a kira muku masu gyaran gashi" yana kai karshen maganar ya sake ta tare da juyawa ya koma wajen aikin sa ya ɗaukk tea ɗin da ta kawo masa ya koma saman sofa dake a ɗakin ya zauna,ya fara sha chikin nitsuwa
Juyawa tayi zata fita sai ta tuna da massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa idan ya saura kamar kwana biyu alluran ya sake sa kirin ƙa yawan zama kusa da shi kina yawan yimasa magana ko da ba zai amsa ba domin awan nan lokacin duk karfin alluran ya ragu yana gab da karewa ne gaba ɗaya alokacin zai ɗan fara jin feeling kaɗan kaɗan,tuna hakan ya sanya ta koma wajen sofan da yake zaune ta na kokarin tsugunnawa kasa ya nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauƙe kafin ta zauna kusa da shi tana satar kallon sa ta kasan ido, kaɗan ya sha tea ɗin ya ajiye ya miƙe ya koma bakin aikin da yake yana miƙewa ta kwanta a wajen dan daman ta fara jin barci tana kwanchiya ba jimawa barci yayi awon gaba da ita
2am ya kammala aikin da yake gaba ɗaya ya kashe duk wani kayan wuta dake ɗakin nan take duhu ya gauraye ɗakin haske wayar sa ya kunna kasa kasa yace "tashi muje" shiru bata amsa shi ba tsaki yaja kafin ya nufi wajen da take kwance hannu ɗaya ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗa ya nufi hanyar fita da ita sai da ya kai tsakiyar ɗakin ya danna remote stair case ɗin tayi kasa ya sauka yana sauka stair ta koma kai tsaye bedroom ya wuce,saman katafaren gadon sa ya shin fiɗe ta ya wuche ya nufi toilet wanka yayi chikin sauri yayi shirin barci dan dare yayi sosai, saman gado ya dawo ya haye tana kwance yadda ya kwantar da ita gefe ya kwanta ya karanto addu'oe in barci ya shafa sannan ya lunshe ido
Kamar jira take yana lumshe ido yana lumshe wa ta mirgino ta faɗo jikin sa slowly ya waro green eyes na shin karaf sai saman face nata, zuba mata ido yayi yana kallon ta barcin ta take chikin kwanchiyar hankali yauche rana ta farko da ya karewa face nata kallon, shafa nashi face ɗin yayi kafin yace "haka ne fa kamannin mu ɗaya da yarinyar nan" dawo da kallon sa yayi saman ɗan karamin bakin ta ya zuba mata ido zuchiyar sa na ingizashi akan ya sunbacheta ɗayan ɓangaren na zuchiyar sa yace "idan ka sunbace ta ka sunbaci wa keman?" da sauri ɗayan ɓangaren yace "ka sunbaci sister ka kuma zaka iyayin komai da ita a matsayin ta na sister ka, kawai ka ɗauke ta a matsayin abun rage kewar ka,shiru yayi sai tunaninnuka daban daban yake a zuchiyar sa amma ya rasa wanne ɗaya sai kama ji yayi ba zai iya jure kallon lallausan lips nata ba batare da ya sumbata ba
slowly ya kai bakin sa saman nata da niyar ya sumbace ta amma sai ya zarce ya fara
Book Chapters
Chapter 19
Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31