gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DUK ƘARFIN IZZATA Yaƙin Sirrika BOOK 2 By Star Lady Chapter 26 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dawo da kallon sa kanta ta ɗan tsagaita kukan nata yanzu sai shassheka take a nitse ya fara magana "ya isa kukan nan haka zaki iya jawa kan ki wani chiwon kin ji? Bata kula shi ba ganin bata da niyar kula shi ne ya sanya ya miƙe tare da ɗaukan ta chak suka nufi toilet a tsakiyar toilet ɗin ya sauke ta ya haɗa ruwan wanka ya ɗauke ya chak chikin kafaren baff ɗin wankan sa ya sunduma ta shima ya shiga da kansa ya mata wanka da ruwan mai zafi sosai

Bayan ya gama ya naɗota a towel kai tsaye saman sofa ya ajiye ta yau da kan sa ya zuba musu abinci ya ɗauki spoon ya ɗawo kusa da ita ya zauna sai aniyar zuciya take saukewa ɗiban abincin yayi ya kai mata dai dai sai tin ɗan karamin bakin ta,kin buɗe baki tayi kanta na kasa da wata iriyar daddaɗar voice wadda bai ma san yana da ita ba ya fara magana "ki buɗe bakim ki mana ki ansa" make kafaɗa tayi tana faɗin "bana ci na koshi" kwaikwayar maganar tanna ɗazun yayi yace "haba sister yau fa ban ci abinci ba ke nake jira muci tare shine zaki che ke kuma yanzu ba zaki chi ba" a sukwane ta ɗago kai tana kallon sa kashe mata ido ɗaya yayi tare da ɗaga mata gera ɗaya sunkuyar da kanta tayi tana tunani take anya wanna yaya Prince ne? ko dai aljanu sun shiga jikin sane? daman ya san murya tane har da wani kwaikwaya wato ashe duk abun da ka faɗa masa yana jin ka kuma baya mantawa kawai daman rashin mutunci ne ya sanya yake yin banza da mutun kamar bai ji ba

"Wai sister ba zaki ansa abincin ba sai na miki ɗure" a hankali ta buɗe ɗan karami bakin ta ya sanya mata abincin dan daman yunwa take ji sosai da kyar take taunan abincinb dan kukan da ta sha shiko ɗura mata kawai yake tun bata gama chinye na bakin ta ba zai ɗura mata wani yanayi yana kallon face nata yana jin wani irin nishadi da sabon yana yi na shigar sa

"yaya Prince na koshi" ajiye spoon ɗin yayi ya sanya hannu ya ɗago haɓar ta yana kallon face nata "ok to kwanta nayi binchike a chikin ki dan na tabbatar kin koshi ko da saura" murmushi tayi kafin tace "aa ba sai ka duba ba da gaske na koshi" zuba mata ido yayi ya kasa ɗauke kallon sa da ga kanta "har yanzu fushi kike da yayan ki? Girgiza masa kai tayi alamar aa "to why har yanzu baki saki jikin ki ba ko dai ki na tunanin zan sake maki abun da na miki ɗa zunne? Nan ma girgiza masa kai tayi alamar a'a "no banason girgiza kai open your mouth an talk" "aa bana fushi da kai kuma ina rokon Allah da ya hanani ganin ranar da zan yi fushi da kai" ajiyar zuchiya ya sauke tare da jawota jikin sa "na sani nasan ba zaki yi fushi da ni ba because halin ki iri ɗaya da my Ammi shi ya sanya nake jin daɗi da kika kasance sister a gare ni" shiru tayi tana tunani "wato dai yaya Prince ba zai taɓa ɗauka na a matsayin mata ba kenan wato har yanzu a matsayin sister nake hmmmm ya Allah ka sauyamin wanan bawan nake" "tashi muje ki sa kaya sai mu kwanta" make kafaɗa tayi tare da kara lafewa a kirjin sa kasa kasa chikin shagwaɓa tace "aa sai ka chi abin cin kai ma" mai da kallon sa yayi kan abincin kafin ya dawo da kallon sa kan face mata "zaki bani a baki? Waro ido tayi waje tare da ɗago kan ta daga kirjin sa tana kallon sa kashe mata ido ɗaya yayi ya sanya hannu ya jaa karan hanchin ta sunkuyar da kan ta tayi kasa ba tare da tayi magana ba "ko baki san chan zawar da nayine? ba kin che kina burin na chan za ba ko dai ba irin wanna chan zawar kike son nayi bane? Shiru tayi ta kasa magana dan ita gani take kamar yaudarar ta kawai zai yi yayi amfani da ita "na san komai a kan ki ina son ki san wani abu ni ba mugu bane kawai haka yanayi na yake ban taɓa tunani dai dai da second 1 na chutar da ke ba ina sane Ammi ta fi son ku fiye da kan ta ko dan farincikin ta zan so naku farincikin ni ban san ya ake yin magana da mata ba kullun da maza nake magana kuma duk wayan da nake magana da su sojojine a karkashi na suke umarni kawai nake basu bayan umarni ni ban iya wata magana ba amma tun da kina son na rinƙa yin magana da ke sai ki koyamin yanzu haka maganar nan da nake dake ji nake tankar zan mutu bana son yawan magana idan nayi magana kaɗan sai naji na gaji try to understand me ni ba mugu bane ki dai na kirana da sunan mugu bata min daɗin ji" rungume sa tayi sosai a jikin ta chikine farinciki tace "yaya Prince da gaske zaka sauya? da gaske in koya maka magana? Kallon yadda take dariya kawai yake kamar ba itace mai kunbura kumatu yanzun nan ba "ba shakka zan yi kokari na sauya ko dan wanan farinciki ya zauna a kan face ɗin marainiyar Allah amma fa sai kin kara hakuri dan mutun ya sauya lokaci guda ba abune mai yiwuwa ba sai dai kaɗan kaɗan" "yaya Prince to yanzu ka juyo na baka abincin" ba musu ya juya ita ma ta gyara zaman ta a jikin sa ta zuba wani abincin ta ɗauki spoon ta fara bashi a baki "yaya Prince yanzu a wani matsayi ka ajiye Ni? "A matsayin sister na mana" "amma yaya Prince ya zanyi da Auren ka dake kai na? "Wanna karki ɗauke sa a matsayin wani abun idan kin samu wanda kike so zan baki takardan ki sai na aura miki wanda kike so ɗin ba ma lallai sai kin sanar da su Abba ba" mamaki ne ya kamata wai shi dai maganar mata ce baya so "amma yaya Prince me ya sanya baka so mata? An san spoon na hannun ta yayi ya mai da chikin plate ɗin ya juyo ya fiskance ta da kyau ya fara magana "no ba wai bana son mata bane bana son jefa rayuwar ko wace mace a haɗarine" "yaya Prince ban gane ba? "Eh duk wata mace da nayi tarayya da ita to tana chikin haɗari shi ya sanya" "yaya Prince wlh har yanzu ban gane ba" hanchin ta ya ja kafin yace "ai ba zaki gane ba ke dai yanzu dare yayi sosai kije ki sa kaya ki kwanta gobe karfe 5 na asuba jirgin mu zai tashi zuwa Nigeria" waro ido waje tayi chike da murna ta rungume sa tana faɗin "da gaske yaya Prince gobe zamu koma naija? Kai ya gyaɗa mata alamar eh miƙewa tayi chikin sauri ta nufi wajen trolley ɗin ta ta fito da wasu kayan ta sanya a jikin ta ta dawo kusa ta shi tace "yaya Prince muje" miƙa wa yayi ya kama hannun ta suka wuce saman gado daga ɗan gefe ta kwanta tana satar kallon sa

kasa kasa yace "why yau ba zaki kwanta a jikin yayan ki ba? Ko dai kin fara tsoro nane? Murmushin tayi tana girgiza kai ta mirgino ta dawo jikin sa ta kwanta rungumota yayi da ɗan karfi tace "wash zafi" da sauri ya ɗan saketa yana faɗin "lfy? Kirjin ta ta nuna masa da hannun ta tana faɗin "ka danne min ne kuma chiwo suke min" "me ya same ki awajen da suke miki chiwo? Waro ido waje tayi da mamaki tace "babu komai" ɗaga mata gera ɗaya yayi kafin yace "yaushe kika fara karya? "Ba karya nayi ba fa babu komai" "karya kikayi mana ba yayan ki bane ya matse su ya sa suke chiwo? Rufe ido tayi da hannun ta tallabota yayi ya zame mata rigar jikin ta ya kurawa tula tulan nata ido yan bakin nipple ɗin sunyi jaa sosai har chikin ran sa bai ji daɗin hakan da ya mata ba amma ba yadda zai yi ne, sai yau ya kara tabbatar wa kan sa hiyana ba macece kamar kowa ba duk wanna abubuwan da ya rinƙa yi mata ashe ita kam ma addu'ar samun rahamar Ubangiji take masa yanzu duk abun da ya mata ɗazun nan hakan bai sa tayi fushi da shi ba ba shakka idan hiyana tayi addu'ar Allah ya saka mata akan abun da ya mata ba makawa Allah zai saka mata dan ya wahalar da marainiyar Allah amma sai batayi hakan ba addu'ar ma take masa mai kyau gaskiya ko dan wanna ya zama dole nayi kokari in rinƙa sata farinciki
"Yaya Prince me kake tunani? "Babu komai Sister" ya kai karshen maganar tare da miƙa wa ya sauka daga gadon ya ya nufi wajen mirror jim kaɗan ya dawo saman gadon hannun sa rike da hotona da kuma robar magani ajiye hoto nan yayi a gefe ya buɗe robar maganin ya ɗibo ya shafa mata a bakin nipple nata bayan ya gama ya rufe robar ya ajiye saman bedside drawer ya ɗauki hoto nan yana kallon su

"Tashi ki nunamin maman ku a nan" chikin sauri ta miƙe ta ansa hoton wanan hoton ne da ranar ta kalla awajen drawer mirror sa jikin ta har rawa take wajen nuna masa maman su,zubawa ummar nasu ido yayi na ɗan lokacin kafin yace "ok to yanzu dai kwanta muyi barci idan Allah ya kai mu gobe in muka sauka naija lfy zamuyi maganar" yana kai karshen maganar ya miƙe ya mai da hoton ya dawo ya kwanta tare da jawota jikin sa yana ɗan bubbuga bayan ta da haka har barci yayi awon gaba da su

Nigeria

A ɓangaren su yaya bello kuwa sai shirye shirye suke da shi da hasana dan gobe Ammi zata turo a ɗauke su kwata kwata yaya bello jikin sa a mace bai san tafiya ya bar innar sa amma ba yadda zai yi ya sa a ransa idan yaje ba jimawa zai zo ya ɗauki innar sa su koma tare a ɓangaren inna habiba kuwa yanzu ta samu saukin laulayin chikin nata ba laifi amma dai har tanzu bata da wani abinci sai gawayi a ɓangaren buba shima ya samu lfy ya warke kamar ba shi ba ya rungumi ɗan uwan sa tare suke zuwa gona da yaya bello tare suke komai yanzu yana taimakawa yaya bello sosai susuka riƙe gidan

A ɓangaren bokan inna kuwa wani kurji ne ya fito masa a gaban sa kan bananar sa kafin yayi fitsari sai ya rinƙa ihu saboda azaban zafin da kurjin ke masa yayi magani har ya gaji amma shiru ba sauyi sai ma kara girma da kurjin ke yi yana fitar da ruwa milk colour mai bala'i wari yanzu ya dai na yiwa kowa aiki fama yake da kansa burin sa kawai ya samu lfy lafiya kuwa taki samuwa

💋Duk Karfin Izzata 💋29

By Star Lady


💖The talent troupe writer's 💖




Page 29


Uk

Tun da tayi sallar asuba bata mai da barciba take shirye shiryen tafiya Nigeria shiru shiru yaya Prince bai dawo daga masallaci ba har karfe 6 bai dawo ba ta gama duk shirin abun da ya dace sai murna take zata koma naija shiru shiru har 7 yaya Prince bai shigoba ɗaukar hijabin ta tayi ta sanya akan riga da wandon ta ta fito palo baya palo ɗauko remote na ɗakin binciken sa tayi ta sai ta sama ta danna stair case ɗin ya sauko chikin sauri ta haura sama har tana haɗawa da gudu tsaye gaban na'urori ta hango sa ya bawa hanyar shigowa baya daga shi sai Short yana aiki watsawa tayi a guje taje ta haye bayan sa tana murmushin,a sukwane ya juyo tare sauko da ita cikin zafin nama ya damko wuyar da tsawa yace "ke baki da han... Bai karisa maganar ba yayi shiru tare da zame hannun sa daga kan wuyar ta ya rungumeta yana ɗan sosa kai "yaya Prince laifin me na maka yau kuma? Kara matse ta yayi a jikin sa "babu komai Sister na mantane ai daman na faɗa miki ba zai yiwu na sauya lokacin guda ba sai a hankali" "to yaya Prince ya banu yafi Nigeria bane? Ɗan sakin ta yayi tare da juya baya ya goya ta ya chigaba da aikin sa da ita a bayan sa "na sanar da su Abba akoi aikin da ban karisa ba dan haka jirgin mu sai da yamma zai tashi" hannayen ta ta zuro ta wuyar sa ta chigaba da magana "yauwa yaya Prince tun da sai da yamma zamu tafi pls ka kaini yawo naga gari kafin mu tafi" girgiza kai yayi kafin yace "no baki yarda dana cemiki duk macen da tayi tarayya da ni idan ba sojaba zata shiga babban haɗari ba kon? To ko sojojin ma suna chikin haɗari bare dan Kafin nazo wanna matsayin da nake na Brigadier general Safras na kashe mutane da dama na tarwatsa rundunar yan ta'addan da dama a kasashe da dama ta ko ina ina da tarin makiya shi ya sanya bana yarda da kowa kuma dukkan yan uwana nake kula da duk wani motsin su zamanki lfy shine kiyi zaman ki a matsayin baki sanni ba yafi miki" kai ta ɗan ɗaga sama kafin tace "yaya Prince to ya akayi ranar mukaje shopping tare kuma har ka tafi kabar Ni? Sauke ta yayi daga bayan sa yana faɗin "kema ai ba wani motsin da zakiyi ban sani ba da gangan na barki a shopping ɗin dan nasan gaba ɗaya wajen yana karkashin kulawar sojojin mune shopping na matar general dest ne so na san ba abun da zai faru" "to yaya Prince dan Allah ka faɗa min taya akayi kasan yaya Khalid ne ya ɗauke ni" guntun tsaki yaja dan hiyana ta fara bata masa rai baya son yawan magana ganin ta tsare sa da ido ne ya sanya yace "sister nifa bana son yawan magana kai na chiwo yake min idan nayi magana sosai ina da tarin abubuwan da ya kamata na kammala please leave" tsuke fuska tayi ta turo baki chikin shagwaɓa ta fata magana "yaya Prince ka manta kai kace na koya maka magana to me yasa kuma ina koya maka zaka che baka so" jan hanchin ta ya ɗan yi baya so ya mata tsawa dan ya ɗau alkawari ba zai sake hakan ba sai ya zama dole gashi ta kule sa bai san magana tana sanya shi dole ji yake kamar ya sharara mata mari ya koreta a ɗakin amma sai ya danne yace "sister dole ne zan san Khalid ne ya ɗauke ki mana kije kiyi searching akan sunan Brigadier general Safras ba a banza mutun zai taki wanna matsayin ba kuma kin manta ne? nache maki duk wani motsi na yan uwan mu na sani" "yaya Prince to dan Allah ni dai ina son zuwa yawo na kalli kasar nan kafin Mu koma" shiru ya ɗan yi ba dan yazo ba yace "ok to jeki fitar kin da kayan hausawa da face mark ina zuwa sai muje yawon muyi breakfast a chan amma dai gaskiya kin takuramin dayawa" tsalle tayi ta rungume sa sosai tana dariya tana faɗin "nagode yaya Prince" ɗaga ta yayi gaba ɗayan ta ya ɗaura ta saman kirjin sa yana tsaye a miƙe ya sanya hannu ɗaya ya chire mata hijabin jikin ta ya jefar kasa a nitse ya zame ɗan siririn hannun rigar da ta sanya ya ganganrar da rigar zuwa chikin ta zubawa tula tulan ta ido yayi na ɗan mintoci yayin da ita kuma ta runtse ido hannu ya ɗaura saman bakin nipple nata yana dubawa "sun dai na yi maki zafi ko? Kai kawai ta gyaɗa masa alamar eh ba tare da ta buɗe ido ba "why are you closing your eyes? chikin shagwaɓa tace "kunyar ka nake ji" "kunya?" ya mai mai ta kalmar gyaɗa masa kai tayi alamar eh "menene kunya? Yayi magana lokacin da yake mai da mata da hannun rigar ta girgiza masa kai tayi tana faɗin "nima ban sani ba" shiru yayi yana kallon face nata "ok open your eyes" slowly ta waro idon nata a kan kyakkyawar face nashi matso da face nashi yayi ya haɗe da nata kasa kasa yace "duk da ban san me ake nufi da kunya ba amma bana son ta as from today karki sake rufe mun ido idan muna tare" hannu ta sanya chikin gashin kan sa tana faɗin "to"

"ash" ya furta lokacin da hannun ta ya sauka chikin gashin kan sa da sauri ta zame hannun ta dan kartaje ta ja masa wani abun da baya so chikin zafin nama ya haɗe bakin su waje guda tare da kama hannun ta ya mai da chikin gashin kan nasa,watsa gashin nasa ta fara yi tana shafa daga kansa zuwa wuyar sa "oh god" kawai yake furtawa ba karamin jin daɗi wasa da gashin sa da take yi yake ji ba kara kankame ta yayi sosai bakin sa na chikin nata yana kokarin zame mata rigan jikin ta ko me ya tuna sai ya fasa slowly ya zame bakin sa daga nata da kyar ya iya sauke ta kasa yana faɗin "muje mu shirya mu tafi ko? Faɗawa tayi saman kurjin sa ta zagayo da hannun ta ta bayan sa tare da kwantar da kan ta a saman faffaɗar kirjin sa tana faɗin "yau kam yaya Prince ba zaka ɗagani zuwa ɗaki bane? "Kin min nauyi ni ba zan iya ba" waro ido tayi waje tana faɗin "kai da kullun da hannu ɗaya kake ɗauka ta kamar yar baby shi ne yau zaka che nayi nauyi" ta karisa maganar kamar zatayi kuka girgiza kai kawai yayi yana danne zuciyar sa yana addu'ar Allah ya ba ni ikon chika mata alkawarin da na ɗauka mata amma gaskiya yarinyar nan tana mani abubuwa dayawa da baya so wayan da ban ma taɓa kwatan tasu ba a rayuwar ta duk yadda muke da Aryan ban taɓa ɗaukan 10mins ina magana da shi ba amma yarinyar nan ta tasani a gaba da tambayoyi da hira haka no dole na san ya zanyi da ita
"Yaya Prince mu tafi mana" hannu ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓa ta a kafaɗar sa suka fice daga ɗakin yana saukowa palon ya chi karo da su Hisham Khalid Yusuf Ahmed Fahad da matayen su suna zaune a palon suna hira bai bi ta kansu ba ya nufi bedroom na shi yaya Khalid ne saurin chewa "Bgs bakaga Hisham bane? gaisheka fa yazo yi" ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce chikin bedroom ɗin sa kallon juna suka fara yi Hisham yana son yin magana amma yana tsoro

saman gado ya kwantar da ita ya wuce toilet chikin sauri ta miƙe ta wuce dressing room na shi ta fito masa da daddakiyar farar shadda mai bala'i kyau da tsada ta haɗo masa da hula fara tas mai kyau almost 5mins ta tsaya gaban glass na gera agogon sa tana tunani ta rasa wanne zata zaɓa masa daga karshe ta ɗauka masa wani dangareren agogon diamond mai matikar kyau da tsada ta fito ta ɗaura masa kayan saman gado ta koma dressing room ɗin ta ɗauko masa takalma mai bala'i kyau tsayuwa tayi ta zubawa takalmar ido mamaki take kafar yaya Prince ɗan karami kamar kafar mace sanya takamin tayi a kafar ta dai dai da ita kamar nata murmushi tayi ta chire ta ɗauko masa face mark ta fito ta ajiye masa takalmin kusa da gado ta ɗaura masa face mark da links a saman kayan sa ta wuce wajen trolley ɗin ta ta chire kayan jikin ta ta duba doguwar riga mai ɗan hankali ta sanya a jikin ta tana kokarin tara gashin kanta ta ɗaure sai jin hannun sa tayi saman gashin nata ya zame hannun ta ta saki gashin ya watse har bayan ta zuro hannun sa yayi ta kugun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna kasa kasa yace "love your hair" murmushi ta ɗan yi kafin tace "to nabaka kyauta" shiru yayi ya sanya hannun sa ya fara tara mata gashin nata "yaya Prince daman ka iya ɗaure wa mutun gashi ne? "na iya ɗaure nawa dai yau shine first time dana fara ɗaure gashin da ba nawa ba ni idan ba Aryan bama ban taɓa taɓa gashin wani ba" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya gama ɗaure mata gashin nata ya zuba mata jelar gashin a bayan ta ya zuba mata ido yana kallon face nata "you look so good" murmushi tayi tace "nagode to kai ma kaje ka shirya mana na" juyawa yayi ba tare da yayi magana ba kayan da ta ajiye masa ya ɗauka ya wuce dressing room

jim kaɗan ya fito shirye chikin kayan da ta fitar masa "wow" shine abun da hiyana ta furtawa "tsarki ya kara tabbata ga Ubangiji da yayi wanna halittar yaya Prince kagan ka kuwa innalillahi ni na ma rasa me zance kai wlh kamar dan kai akayi kayan hausawa" harara ya watsa mata kafin yace "dan ke na sa kayan ai nasan idan nayi irin wannan shigar ba wan da zai yi tunanin nine bare su sawa mutane da nake tare da su ido" kwashawa tayi a guje ta faɗa jikin sa tana faɗin "nagode kuma bazan taɓa mantawa da wanna rana ba a rayuwa ta yau yaya Prince yayi abu saboda ni" shafa gashin kanta ya farayi yana faɗin "it's ok tun da kinyi farinciki muje da wuri dan time ya tafi almost 12 yanzu kuma kinga zamuyi tafi anjima kaɗan" sakin sa tayi ta ɗago ido tana kallon sa "yaya Prince to ya baka sanya hulan ba? Ɗagata yayi ta ɗaurata saman gado ya juya mata baya yana faɗin "ɗaure min gashin nawa sai ki samin hulan mugani ko kin iya" duk da ya ɗaura ta saman gado sai da ta ɗaga kafa kafin ta iya ɗaure masa gashin kan na shi

Tana gama ɗaure wa ta diro daga gadon ta shige dressing room nashi yana tsaye awajen har ta fito ta haye gadon tana faɗin "yaya Prince juyo na sanya maka hular" juyowa yayi ya ɗan sunkuyar da kansa kasa ta sanya masa hulan asalin kyan sa na fulani ya sake bayya
face mark ta ɗauko ta sanya masa yana tsaye yana kallon ta yana mamaki da yaba mata a ransa tana da kyakkyawar zuciya sosai hannun sa ta kama ta ɗaura masa agogon
shi dai yau gaba ɗaya mamakin kansa yake ji yake kamar ba shi ba yayi nisa chikin tunanin sai jin ɗan karamin bakin ta yayi saman kumatun sa hot sumbata ta bashi tana murmushin tace "muje to" bai san lokacin da ya rungumota ba yana faɗin "kina da kyan hali sosai" "yaya Prince ai daga wajen ka na koya" kallon gefen ido ya mata kafin yace "a yaushe kika koya awaje na? ɗaura dan yatsan ta tayi saman wuyar sa tana masa yawo da yatsan awajen ta fara magana "awajen Ammi na koya kenan kaga duk abun da Ammi take da shi mu dukkan mu yaran ta muna da shi" first time a rayuwar sa ya saki cool murmushi tare da ɗaukan ta chak ya nufi dressing room nashi da ita yau yana matikar farinciki sosai dan yana bala'i son Ammi duk wan da zai so Ammi to koda makiyin sane ba shakka zai zama masoyin sa

Tsakiyar dressing room ɗin ya sauke ta ya buɗe glass na face mark nashi ya ɗauki ɗaya ya sanya mata ya ɗauko jaket nashi ya sanya mata har guiwa jaket ɗin ya tsaya mata kai kallon sa yayi kafar ta Booth nashi

Please Login or Register in order to submit comment