ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwarsu tunda dama dole Inayah zatai rayuwarta da
friends.

Ahakan suka dauki tsawon lokaci har suka samu 2 weeks break a lokacinne Zaid yafara
takura mata sosai akan maganar aurensu.

Kai tsaye yafito yake matsar da ita akan sosai yake buqatan aure sbd shi buqatarsa
tafara zuwa na Neman mace.

Da farko fada sukayi sosai ta nuna Masa ya rabu da friends dinsa da basu dauka sex
abakin komaiba sbd yanayin rayuwar turai dasuke dakuma kusan dukkaninsu tashin
turai dinne.
Shawararta ya dauka ya daina biyewasu zacks kwana biyu sbd dama sune suke tada Masa
da shaawar hakan,
Da yawa yan matansu a gida suke kaisu suna wasu abubuwan gabansa gashi dama babban
gidane suke zaune su ukun kowa da babban bedroom dinsa da fadeden bathroom aciki
harma da closet room.

Su ukun friends ne tare suke kusan tun yarinta,

Zacks bama musulmi bane black American ne,
Sai Sufian shikuma kusanma 'dan uwansa ne sbd fmly friends ne ahalinsu.

Tare suke lafiyayyar rayuwa a gidan sbd kowannensu yanaji da kudi da gata ba laifi,
Yan mata kuwa kusan kullum cikin sauyawa sukeyi babu ranarda mace Bata kwana gidan
Idan zacks Bai kawoba Sufian zai kawo Dan hakan yau da gobe suka ringa saka Zaid
cikin yanayi na damuwa gashi yanzu tsakani da Allah yakan ji shaawar mace lokuta da
dama.
Kwana biyu yafara kasa daurewa shine yafara takurawa Inayah maganar aurensu.

Yauma kusan fadan sukayi akan maganar cikin yanayi na takaicinsu zacks tace Masa"

Baby nafada maka Abbi bama zai kalleniba naje da maganar Kuma shikenan nice zanje
na rokesa akan ayi aure yanzu?
Kana tunani kuwa?
Please ba Abbi ba Nima banajin na shiryawa auren yanzu idan har sbd wannan maganar
kakeson auren yanzu...bazan iyaba please baby mubar maganar Nan banason jinta tana
damuna ma.

Shima ransa Dan baci yayi Dan haka Bai Kuma tayar mata da maganarba saiya koma
kiran dad dinsa yana matsa Masa sosai akan maganar auren Dan hakan dole dad din
nasa ya nema A MAJEED da maganar idan da hali suna son ayi auren yanzu.
##MAMUH#
#INAYAH#
#RIBA BIYU#
#LOVE/ROMANCE#



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/3, 11:07 AM] MG: *_Mamuhgee 12_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Dad din zaid yasan Sarai waye A MAJEED Dan hakan Bai tsaya nemansa a wayaba sbd
sanin babu abinda zai gane a wayar tunda A MAJEED din ba wai son auren yanzu yakeba
yakuma sanar dasu hakan batareda ya fada dalilinsaba saidai Kuma kusan duk Wanda
yasansa yasan dalilin nasa ba boyayye bane duba da yanda yake Da zurfi da ilimin
boko sosai daya Gama ratsasa sunsan babu yanda mutum irinsa zai aurar da yarsa
qwalli daya dazata gadi tarin dukiya da companies dinsa batareda tasamu ilimin
itama Mai zurfiba Amma ya suka iya tunda sunaso dole haka ya tattara ya tsaro
tafiya ya taso zuwa qasar.

Shi dad din tun farko bakin rai bakin fama yakeson auren tsakanin 'yayan nasu sbd
burinsa nason qulla alaqa Mai qarfi da A MAJEED,

Babu wani Mai son abun duniya da kudi daba zaiso shi ko 'dansa su auri 'yar A
MAJEED qwaya daya tal ba wadda zai iya bada duk tarin himilin dukiyarsa akantaba
Dan haka ba dauki bare wasa shi kam so yake ayi auren kota yaya Dan Inayah idan
tana hannun 'dansu tamkar suna riqene da mukullin dukiyar A MAJEED da Baya tabuwa
bare juyiwa ga kowa,Dan banzan naira da dollar sungama zauna Masa tako Ina,sun
girmesa Sbd har lokacin baiyi shekarunsuba badan yanada zuqeqiyar budurwar 'yaba ai
yanada sauran lokaci a cikin matasa Amma dai koma menene yaro da kudi abokin manya
dama abokanan huldarsa manyan ne na gaske.

Zuwan dadyn Zaid Sydney yasa damuwar da Inayah tafara shiga ya dan fara raguwa sbd
gabaki daya kwata kwata yanzu itada Zaid din kullum cikin hayaniya suke,

Bazata iya daukan fada bare rabuwa da Zaid ba
Ayanzu din tafison Dad din nasa yayiwa abbin mgn idan ya amince ayi auren Dan gskia
tana tsananin son Zaid dinta koma menene ayi auren zatai maganin wannan iskancin da
yayi mata daga baya.

Yau daga makaranta Saida su biya ta siyo wasu abubuwan wankanta dasu undies da Bata
rabo da siya akai akai,

Sai yamma suka dawo Shima tun acan take waya da abbin akai akai tanaji idan yadawo
gida sbd kada ya rigasu komawa yaga sunyi yammacin dawowa.

Da motan Neesah suka dawo sbd yauma Abbinta ne ya ajeta makarantar Dan dama
haryanzu data girma dinnan idan yana gari yawanci shine yake ajeta school saidai
driver yaje ya daukota kokuma su dawo a motar Neesah.
Neesah Bata shigoba ta wuce Dan hakan itama Kai tsaye tana shigowa bakowa a palo
dakinta ta nufa.

Ajiye kayan hannunta tayi tana ajiye numfashin 'yar gajiya da yunwa datake ji Dan
haka tubewa tahi ta fada toilet tayo wanka tafito ta sanya Abayar sallarta tana
idarwa tayi adhkar ta miqe ta sanya ash riga da wandon Burberry masu kauri saidai
qananun size ne Dan sun zauna daidai jikinta,basu matsetaba hakama basuyi mata
yawaba daidai jikinta.

Sponge resort Slippers ta zuro ta fito tana qamshinta hankali kwance.

Dakin umma yagana take kokarin zuwa saiga umman ta fito.

Cikin shagwabe fuska ta rungumo hannun umman suna juyawa zuwa dakin cin abinci tana
cewa"

Umma yaganah yunwa nakeji sosai.

Murmushi umman tayi tareda Dan janye jikinta daga Inayar tana cewa"

Haryanzu kin kasa iya fara gaisuwa kafin komai ko Inayah?

Sake kwantar da kanta tayi kafadar umman tana cewa"

Umma yaganah kullum fa Ina gaisheki kafin nafita idan nadawoma inayi ranarda na
manta ba sai ayi hakuri Amin uzuriba for God sake,Kuma ma fa na........

Qamshin Turaren Abbinta yasata shanye abinda Zata fada din suka kalla hanyar
palonsa atareda umma yaganah aikuwa shi dinne tafe cikin nutsuwa da kwanciyar
hankali.

Sanye yake da fararen Adidas riga da wando masu kauri hular dake hadeda rigar itace
rufe akansa
Qafafunsa kuma black santoni slippers ne.

Gabaki daya Abbinta idan yayi shiga tamkar matashi yake komawa musamman irin
wainnan shigar da yakeyi idan zaiyi geamin(exercise/motsa jiki) ko idan zai kwanta
ranarda yakejin sanyi kenan,

Yawan geamin dinsa yasa kullum yake sake Zama tamkar wani sabon matashin da yanzune
yake lokacinsa sudaima sun rasa gane irin kyan jiki da kyan siffarsa daya hanasa
manyanta sosai.

Umma yaganah ce tafara bude Baki tana kallonsa tace"

ABDULMAJEED barka da fitowa.

Cikin yar girmamawa ya Dan kalleta kadan tareda dauke idonsa akanta yana cewa"

Mun wuni lfy umma yaganah?

Wata jarabawa kokuma ace lalura datake kansa tsawon shekaru shine Baya kallon mata
kallon daya wuce daya zuwa biyu,

Sam ya dade da rufe shafin mace ata kowanne fani na rayuwarsa bayan 'yarsa,
Duk huldar aiki dazata hadasa da mata Baya wani maida hankali sosai akansu Wanda
Kuma kusan ba kowane ya fahimci hakanba tunda dama shi ba mutum ne Mai sakewa
mutuneba shiyasa baa wani ganewa
saidai umma yaganah da Inayah dasuka Sansa ciki da Bai sune sukasan babu macen
dayakewa kallon daya wuce biyu zuwa uku,

Umman ma haryanzu idan yayi mata kallo daya zuwa biyu koda suna magana ne Baya
qarawa shiyasa da yawa idan kana Masa bayani saika dauka hankalinsa Baya kanka and
yafi maida hankali kan wani abun daban ko waya haka Amma Kuma ahakan yafi fahimtar
bayanin da ake masa.

Wainda suka 'dan Sansa da kadan daga halayensa idan suna magana dashi sukaga Baya
wani abun daban ya tsaya yana saurarensu to kuwa sun San tabbas Bayada niyar
saurarensu ne,idan kanason Kama mutuncin kanka saika dakata kabar maganar Dan ba
lokacinta zaiyiba.

Zama sukayi dukkaninsu a dining Inayah ta zubawa kowa abincin kafin Takoma ta zauna
itama bayan ta zuba nata,

White rice ce da chicken vegetables with scrambled eggs.

Suna fara cin abincin Inayah ta kalli abbin dayakecin abincin a natse kunnuwansa na
sauraren sautin yanayin cin abincinta take ya fahimci akwai maganar datakeson yi.

"Abbi" ta furta sunan ahankali cikin kulawa da bayyanarda 'yar shagwaban data taso
acikinta.

Kallonta umma yaganah tayi cikin kulawa ya katseta da cewa"

Ba yanzu ba Inayah,
Bakiga Abbinki yanacin abinciba?
Surutu lokacin cin abinci baida amfanin kinmatane?

Marairaice fuska tayi cikin son fadar abinda yaketa nuqurqusanta Kuma tasan Idan ba
fada Masa tayiba Dad din Zaid yayi Masa zuwan Kai tsaye da bazata ransa zai baci
akan da sanin ta akazo maganar,

Bazata iya daukan fushi ko bacin ran abbintaba akanta Dan haka Kai tsaye takuma
kallonsa bayan tayiwa umma yaganah fuskar riqon tabarta tayi magana.

Abbi Dad din Zaid Yana gari yazo fa....

Ahankali ya qarasa hadiye sauran abincin dayake bakinsa ya dauki ruwa mara sanyi
sosai dake gabansa cikin glass cup yasha ya ajiye sauran ya dauki tissue Saida ya
goge bakinsa ya dago da manyan idanuwansa ya kalleta hankali kwance yace"

Yes,Uhum?
Dad din Zaid Yana gari zan Masa wani Abun ne?
Gurina yazo ne?

Abbi dama gurinka ne zaizo kuyi magana,karyazo ne baka saniba ranka ya baci Abbi
shine nafada maka Kuma banice nace suzoba Abb...

Umma yaganah ya kalla Kai tsaye da tambayar

"Kinsan da hakan ne umma yaganah?
Ta sanar dake Zata basu Daman zuwa neman aurenta?

Ajiyar zuciya umman ta sauke cikin sanyin jiki sbd Inayah dai Bata gane kwaba,

Kallonsa take cikin sanyin jiki tace"
Ta sanarmun da mahaifin nasa zaizo Amma na kaina na Kira Zaid din nace su dakatar
da zuwan sbd Jan magana daya koyaushe baida amfani tunda dai anbasu auren Inayar
Yin auren ne dai tunda anfada musu ba yanzuba na rasa naci irin na 'yaran yanzu
tunda ba cewa akai a gaban zaa fasaba...

Jin shirunsa Yana saurarensu yasa dukkaninsu suka Sha jikinsu sbd sanin hakan
abinda yake nufi,

Dukkaninsu sun fahimci bacin ransa akan hakan shiyasa suka sake yin wani tsamo
tsamo.

Cikowa idanuwan Inayah sukai da hawaye batareda ta saniba cikin sanyin murya da
sigar ban hakuri ta taso tadawo gefensa tareda Dafa hannunsa ahankali tana cewa"

Abbi Banice nace suzoba wlh,
Nayiwa Zaid din maganar kada dad din yazo Amma baijiba,
Abbi wlh bani bace...

Batareda ya kalletaba yace

"It's okay saiyaxo Ina jiransa.

Miqewa yayi tareda kallon umma kadan yace"

Mu kwana lfy umma yaganah.

Allah ya tashemu lfy" tafada itama tana bin bayansa da kallo ranta babu Dadi da
yanayin,

Babbar matsalar basa wani gane bacin rai ko fushinsa bare kasan halinda kake ciki
shiyasa koyaushe irin wannan kuskuren yafaru sun ringa Kara kaina kenan gurin samun
sanin yanda ransa ya dauki Al'amari.

Bayan barinsa gurin Kallon umma yaganah Inayah tayi da raunannun idanuwanta zatai
magana umma ta tareta da cewa"

Inayah meyasa kikai maganar Nan?
Maimakon ki dakatar dasu Zaid din shine Zaki Kuma kawo maganar gaban mahaifinki
bayan kinsan bayason maimaicin zance,
Anyita maimaita zancen Nan Kuma kinfi kowa sanin mahaifinki magana daya yakeyi
akanki meyasa bazakiyi respecting hakanba?

Yanzu gashinan zakiwa kanki Dan kuwa Abbin zai iya Hana auren gabaki daya yace su
hakura suje su nema wata su aura idan sunaga bazasu iya jiranba
Kinga kuwa wa garin ya waya.

Batada abin fada sbd jikinta daya Gama mutuwa da yanayin mahaifinta daya qi barin
su gane yanda ya karbi zancen.

Cikin sanyi ta dauki orange juice din dake gabanta ta Sha sosai ta aje cup din sbd
bazata iya cin abincinba Kuma.

Miqewa tayi tareda yiwa umma yaganah Saida safe ta wuce dakinta itama.

Itama umman kammalawa tayi ta miqe tabar dakin ta dauki sauran abincin datasan zai
moru takai fridge ta jera kafin ta wuce nata dakin zubbi tazo ta tattara gurin ta
gyare Takoma dakinta itama.

Bayan isarta daki ta Gama duk abinda zatayi ta hau makeken gadonta ta kwanta tareda
daukan wayarta ta saka Kiran Zaid.

Daukan wayar yayi tun kafin yayi wata magana tace"

Zaid please ka dakatar da zuwan dad gurin Abbi banason cigaba da Bata ransa akan
maganar wani auren yanzu,
Nidai gskia mu haqura abari sai lokacinda Abbina yace koma yaushe ne zamu jira
I don't want to stress him with unnecessary abubuwa kaman hakan tunda yace ajira
kawai ajira
Dad dinka yakoma please...

Inayah are you out of your mind or what?"" yafada cikin Dan daga murya.

Kinajin kanki da abinda kike fada kuwa?
Dad ya taso all the fuckin way from Nigeria yazo kice yakoma sbd kada a dama
Abbinki?
Are you for real?Kinajin kanki kuwa?

Zaid please karmu batawa juna Rai abanza mubar maganar auren Nan yanzu sai gaba....

Datse wayar yayi ya kashe gabaki daya ya jefar gefensa Dan zuciyarsa tafara baci
sosai da yanda koyaushe Abbinta shine gaba shine yafi kowa mutunci,yanaji kaman
mahaifinsa take kokarin ciwo mutunci Dan haka cigaba da wayarsu yanzu zai iya
hadasu fada sosai shiyasa ya kashe din.

Inayah ma wayar tabi da kallo cikeda mamaki da Dan takaici,
Ita Zaid yake kashewa waya yau?
Wai kodai bayan matsalarsa ta buqatan aure yanada wata matsalar ne da ita Bata
saniba Dan kuwa wlh bazata dauka wannan wulaqancin tun yanzuba tana magana ya kashe
mata waya.
##MAMUH#
#A MAJEED
#INAYAH



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/5, 8:23 AM] MG: *_Mamuhgee 13_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da 'dacin Rai duka suka kwana a daren ,
Inayah Kuma harda matsuwa tayi garin ya waye ta nemesa taji dalilinsa na kashe mata
waya sbd ko Abbinta baya kashe mata waya shi dayafi kowane namiji daraja agurinta
da rayuwarta.

Duk yanda Abbi yakai ga bacin rai baya taba Bari agane Dan haka da safen koda ya
fito kyakkyawar fuskarsa na ayanda take koyaushe ba damuwa.

Black Armani's ne ajikinsa sosai yayi fresh acikin black kala din,

Cikin sanyi ta kallesa tanason shagwabe Masa Amma tunanin Tayi Masa laifi daren na
jiya yasa ta Dan nutsu duk da hakan cikin marairaicewa tace"

Good morning Abbi" tana qarasowa gurinsa itama shirye cikin milk sleeves riga da
skirt na Balenciaga.

Morning Inayah" ya amsa Yana kallon yanda idanuwanta sukai zuru zuru sbd daren
jiyan da Bata samu bacciba.

Dining suka zauna bayan ya gaisa da umma yaganah yasake kallon Inayah din da itama
taketa qara wani kalar tausayi ganin take ya nuna ya lura da yanayinta na rashin
baccin da Bata samuba Kuma tasan dole zai nuna damuwarsa akan hakan shiyasa take
sake yin kalar tausayi.

Black tea Ginger tea Mai zafi aka fara zuba Masa ya dauka yafara Sha ahankali
tareda Dan sake kallon fuskar Inayah din ya dauke fuska Kai tsaye ya bude Baki
cikin nutsuwa yace"

Inayah¿

A marairaice tace"

Yes Abbi¿

Kallonta yayi bayan ya aje cup din hannunsa fuska a Dan matse yace"

Next abinda zakiyi na soke alaqarki da kowanne namiji sai bayan kin Gama karatu
kwata kwata shine kici gaba da saka damuwar soyayya aranki harya hanaki bacci irin
haka,
Umma yaganah ya kalla cikin jaddada zancensa yace"

Yaushe tasan wani soyayya hakane?
Ki ringa Mata fada sosai idan ba hakanba zan tattara mubar qasar gabaki daya mu
koma Nigeria ko Zata maida hankali a karatun can.

Hawaye takeson yi Amma tunowa da ya Hana yasata maida hawayen cikin sanyi tace"

Abbi Dan Allah kayi hkr,
Ba tunanin komaine yasa banyi bacciba inada test ne yau so I had to study all
night...

Waiwayowa yai ya watsa Mata manyan idanuwansa ahankali Yana sake mamaki da
jinjinawa sauyin sabbin halayenda Inayah ke dauka,
Yaushe Kuma ta iya harda yimasa qarya?

Sauke Kai tayi qasa tana Dan sosa wuyanta gabanta na faduwar kada yagane qaryarta
saidai Batasan ta makaroba.

Qarasa Shan tea dinsa yayi Bai wani Abinci sosai ba ya kammala ya miqe Yana cewa"

Muje zan ajeki school.

Satar kallon umma yaganah tayi tana neman qaryar dazata Kuma shimfidawa yatafi
yabarta ta tafi school din da kanta Dan dole tana buqatan biyawa gurin Zaid suyi
magana.

Rasa abin fada tayi dole badan tasoba ta miqe suka bar gurin umma nai musu adduar
dawowa lfy.

Shi kadaine ya amsa Banda ita data shiga tunanin abinyi Dan yanzu tasan kila Abbin
zai qara Mata tsananin fita akan na dah.

Yau bashine yake tuqa motarba driver dinsa ne yake jansu.

Har suka Isa makarantar kame kamen basa hakuri takeyi Amma Bai wani bi takan zancen
nataba saima zancen karatun dayayi Mata daban.

Suna Isa aka sauketa suka wuce sai alokacin yabi bayanta da kallo,
yanajin tausayin 'yarsa fiyeda komai,

Hakama Baya iya hakurin damuwarta,

Ya rasa waye yake gurbata Masa tunani da tarbiyar 'ya akan ire iren hakan,

Kwata kwata haryanzu bayajin sha'awar kowace irin mace bare marmarin ajiyeta
shiyasa yake tsananin mamakin yanda Inayah ta qwallafa Rai a soyayya da son aure
tunda ba ganin tayiba a gidansu ana soyayyar, hasalima shi soyayyarce sam baisan
yama akeyintaba bare harka Gama macewa akan wani kaje kana Hana kanka bacci a wofi.

Motar Abbin na barin makarantar ta fito zuwa coffee shop din dake makarantar ta
samu Neesah dake can ta zauna tareda fidda wayarta batareda ta iya wata doguwar
maganar da Neesarba tafara saka Kiran zaid.

Kasa samunsa tayi dole qarshe tabar Masa sakon murya da cewa idan ya kunna waya
yakirata Kuma ya tabbata Dad baije gurin Abbinta ba sbd zasu iya yiwa kansa Abbin
ya dakatar da soyayyarsu sai gaba din.
Bayan Gama tura Masa sakon muryan aje wayar tayi gabanta zuciyarta ba wani Dadi ta
Dan yamutsa fuska tareda Kiran sunan waiter a tushe tace"

2 Cappuccino's please.

Kallonta Neesah tayi tana cewa"

Kodai zamu samesa ne?

Bazai tsaya sauraren wannan ba namafi zatan Dad din nasa ya riga Abbi Isa office
dinsa jiransa.

Kasa cewa komai tayi Saida aka kawo Mata cappuccino din ta fara Sha ahankali kafin
tace"

Banajin komai sai bacin ran mahaifina,
Zuwan dadyn Zaid zai fusata Abbi Kuma na fadawa Zaid kada yaje Amma Yana banza da
zancen yakuma Dan akan Abbina bana daukan wannan so gwarama ya daina wannan saurin.

Bari naji Inda yake saimu samesa" cewar Neesah tana fidda wayarta daga qaramar
Louis Vuitton handbag dinta.

Kinason Abbi ya daina kulani kwata kwata yayi fushi danine?
Kinsan halinda mahaifina zai shiga kuwa idan yaji naje gidan namiji
Gskia bazan iyaba,
Bari anjima idan Bai kiraba na sake kiransa.

Maida wayar Neesah tayi tana cewa"

Amma dai bafa lallai yazoba Sai sungama magana da Abbin hakan Kuma shine qarshen
Bata komai.

A qasan maqoshi ta furta"

Allah ma yasa Abbi ya gaji da wannan zaryan ya amince musu ayi auren yanzu sbd
Gaskia Ina son Zaid dina sosai,I can't live without him, duk wannan fadan danake na
qarfin haline Ina tsananin sonsa gaskia.


********
_AAM's BUILDINGs_

Zaune Yake kan sofa dake makeken office dinsa hankali kwance ya jingina bayansa
kadan yana sauraren Former Ambi Mukhtar Asheer mahaifin Zaid.

Gabaki daya idanuwansa dake Dan rikata wanda duk ya zubawa sbd kwarjini su ya
zubawa Ambi din Yana kallonsa Yana saurare.

Da gaskiyarsa ta hakika yake sake tsaro jawabansa Dan shawo kan A MAJEED din ya
amince da auren 'yayan nasu a yanzu sbd kaucewa barna tunda yaran sun matsa sunason
ayi.
Amma abinda Bai saniba gameda A MAJEED shine wannan zuba Masa idon da yayi baida
niyar daukan zancen ne.

Qaramin numfashi ya sauke a natse kafin ya Dan dauke kallonsa daga Ambin ya dauki
wayarsa dake gefensa ya ajiye gabansa cikin nutsuwa yakuma nagowa ya kallesa yace"

Kaman yanda nafada last time dakuma farkon zuwanku neman auren maganar dai tana Nan
a hakan,
Hakuri zaa cigaba dayi inshallah babu wani abinda zai faru ko biyowa Baya dangane
da wata barna ko makamancin hakan...

Inayah dai tunda nace nabawa Zaid aurenta bazan fasaba kokuma sauyawa matuqar ba
itace tace ta fasa Dinba kokuma wani dalilin dazai iya hanawar Kuma ba'a fatan
hakan,

Dan haka Ambi Ina sake baka hakuri kuci gaba da hakuri inshallah lokacin ya kusa
sbd tana gab da kammala karatun tunda duka duka shekara dayane ya rage Mata
inshallah...

Amma tunda Kai kana hango wata barna da Zata iya biyo bayan rashin auren da wuri
To inaga na dakatarda haduwarsu kawai su tsaya iya waya zuwa sbd kiyayewa sai a
sanarda shi Zaid din
Inayah Kuma zan fada Mata
Daga yanzu haduwarsu iya wayane ya dakata da zuwa gurinta for now,

Allah yayi Mana jagora duka.

Sake da Baki Ambi yake kallon A MAJEED din Yana sauraron bayanansa dake fitowa suna
zuwa Kai tsaye,
Yasani yakuma ji wainda suka San A MAJEED din suna fadar Kai tsaye yake magana Baya
wani kwana kwana ko lanqwasa Musamman zancen daya shafa 'yarsa dayake ganin baida
abinda yafita.

Jin shiru yasa Ambi ya rufe bakinsa tareda sauke numfashi Yana yaqen dole yace"

Shikenan ba komai zamu cigaba da jiran tunda Shima akwai nasa programs din dazai
kammala zuwa next year din
sai abin yazo musu duk a natse ma,
Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi.

Amin" ya furta Yana kallon ruwa da aka kawowa Ambi din Bai Sha ba yace"

Me zaa kawo maka?
Any drink, coffee or something?

No,no,no I don't think i need anything
Thank you,
Ruwan ma is okay.

Daukan ruwan yayi yasha kadan tareda ajiyewa suka Dan fada wata firar daban wadda
Bata shafi iyalansuba ta business industries ahakan har ya Dan ja lokaci sosai sai
lokacin tashinsa suka fito tare ya maidasa har masaukinsa kafin ya wuce gida da
driver dinsa.


Da daddare zaid yazo masaukin dadynsa Dan jin yanda aka Kai qarshe Dan Shikam ma
wlh yanzu yafara gundura da qaidan abbin Inayah

Lokacinda dadyn Zaid ke yiwa Zaid bayanin komai Shima sai alokacin yake bayyana
zallar bacin ransa da yanda A MAJEED din yaketa ja musu Rai akan 'yarsa saikace
itace 'yar datafi kowa gata a duniya,
Saikace shine kadai Mai arzikin dayake da 'ya.

Cikin damuwa Zaid yace"

Dad inason Inayah sosai Amma gskia bazan iya wannan hakurin ba,
Is either ta dagawa babanta hankali akaina kokuma na barta sai ranarda Abbin nata
ya tashi aurar da ita Amma gskia zan nema wata yanzu.

Cikin takaici dadynsa yake kallon bakinsa dake magana yace"

Bakada hankali ko?
Kasan me ake nufi da auren connection kuwa?
Duk da connecting naku akaiba kune kuka hadu da juna da kanku Amma wannan auren
shine yanzu kowa keson ace 'yayansa sunyi wato auren arziki da samun connections.

Duk tarin arzikinsa da uban dukiyar daya tara 'yarsa 'daya,
Hakama Bayada Mata bare asaka ran zai Kuma haihuwar wasu 'yayan,
Duka wannan arzikin da dukiyar 'yarsa yake tarawa Dan haka duk Wanda zai aureta
shine Mai babban rabo tunda 'yar tasa mace ce wani abun dole saidai mijinta,

Ahakan kake maganar ka nema wata ka bar Inayah din?

Ka kuwa San waye A MAJEED da abin daya mallaka?
Ka kuwa San tarin arzikin dayakedasu a Nigeria ma kawai?

To idan kanka ya daina lissafi Bari na maka budaddiyar wasika,
Idan ka rabu da Inayah wlh ka tabbatada wadda zaka kawo mahaifinta yafi A MAJEED
Jan wuya,

Dama ba sonta kakeba dakaketa ikirarin bazaka iya rayuwa babu ta ba,zaka mutu idan
baka sametaba,
Nonsense,
Uban me kakesha da duk kabi ka dagawa mutane hankali akan son auren yanzu?
Duk ma abinda kake biyewa su Sufian suna baka kanasha da kabi duk da rikice da
Neman mace gwara ka daina Sha sbd Ni Future dinka tsayayya nake hango maka,

Duk tarin nawa arzikin danakeda kaima kakesa nafison ka hada Dana uban matarka
koina yazama kanada connections dinsa da tarin arziki
So idan ma ki fita hankalinka better cm back to your damn senses
Neman Mata ko buqatan mace bashine naka ba yanzu.

Duk abinda dad din yafada Masa yasan hakan ne Amma dai gaskia shi yanzu mace yake
buqata matuqa,

Kuma kaman dai yanda dad yafada akan abinda yake ikirari kan son dayakewa Inayah
gaskia ne
haryanzu tsananin son Inayah na Nan daram a ransa saidai Shima tasa buqatar Gaskia
ce Kuma tabbas wasu abubuwan sukesha taredasu Sufian.

Dan haka zai sama Inayah suyi magana dole ita kadaice Zata iya saka Abbinta yabarsu
suyi aure yanzu.

Koda yakoma gida Bai kirata ranarba sai washe gari da safe.

Tana ganin kiransa lokacin tana taredasu Abbi da umma kan dining Dan haka tsulum ta
miqe tareda cewa ta koshi tabar dining din.

Umma ce kawai tabi bayanta da kallo Shikuwa abincinsa yake cigaba daci hankali
kwance bawai Kuma Dan Bai fahimta komaiba.

Fada sosai tayi Masa a wayar Shima farko fadan yayi Mata kafin ya sauko Yana
rarrashinta.

Kashe wayarta tayi itama tareda jefarwa tana cewa"
Saina Rama Nima kaji yanda naji.

Bai sake kiraba kaman ita yanda tayita yi daya kashe Mata wayar

Sai abin yamata ciwo itama ta sharesa badan tasoba.

Sanin Inayah nayi Masa tsananin so yasa ya daga mata hankali kwana biyu da rashin
Kira kafin Kuma daga baya qarshe Bai Ankara ba yafara mata yar barazanar auren wata
kafin tagama nata karatun saiyayi ta biyu da ita.
#MAMUH#
#RIBA BIYU
#INAYAH
#A MAJEED



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_

_4 BOOKS 4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/5, 1:14 PM] MG: *_14_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Farko Inayah tayi mamaki sosai da maganganun Zaid din sbd Bata dauka Yana fada da
gaske bane kawai dai yanason daga Mata hankaline sai kawai Bata dauki zancen da
wani mahimmanciba tadaiyi mamakin Inda yasamu guts na iya fada Mata hakan.

Shima Zaid din ganin ta watsar da maganar yasan Bata dauka maganan bane Dan haka ya
tattara Shima ya watsar Yafara Dan kula tsohuwar budurwarsa data maqale tanason su
dawo tare dama friend din Sufian ce.


Tunda dad din yazo yasamu Abbi sukai magana da yanda sukai da me ake ciki babu
abinda Abbi ya sanar masu daga ita har umma yaganah,

Maganar dakatar da zuwan Zaid ma shine da kansa ya kirasa ya sanar Masa Dan haka
Inayah Bata saniba Shikuwa Zaid din tuni hakan yasa ya sake watsar da zancen Inayah
yanzu yakama Amal suka bude shafin soyayya duk da ba wani jinta yakeba Inayah ce
kawai a ransa har

Please Login or Register in order to submit comment