You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
koina Yana zazzare idon Neman Hadiza.
Daukan babyn yayi dan Dole ya rungume Yana sake jujjuyawa Neman Hadiza.
Fara tashi hankalinsa yayi dayaga dagaske yakasa ganin uwar babyn.
Kokarin komawa yakeyi gurin motar dasuka iso sai kawai ya hangota tana sauri
zatabar tashar tana zazzare idon kada ya ganta.
Da sauri ya bita
tana ganinsa ta sake sauri ba Shiri ta tare Mai mashin ta haye suka bar gurin da
sauri.
Tashin hankali da tsananin mamakine da firgici yasashi Neman wani mashin din ya hau
Amma tuni Hadiza da me mashin dinta suka bace Masa.
Me wannan matar tayi ne?
Me take nufi?
Da gangan tana sane ta bar Masa babyn ta gudu fa.
Innalillahi wainna ilaihrrjiun..
Meyasa zatayi haka?
Dama mahaukaciyace Basu luraba?
Meyesa Zata gudu tabar Masa baby ?
Ina zai Kai babyn to?
Yawo ya ringa Yi dame mashin hankaki tashe Amma sun kasa ganin hadiza ko Mai Kama
da ita.
Dukkanin qwaqwalwarsa tsayawa tayi cak shima
Ya tsaya rungume da baby ajikinsa Yana Jin jiri na Neman zubar dashi,
Ya zaiyi da wannan babyn?
Bazai iya komawa tashaba sbd baisan wazai bawa babynba,
Baimasan wazai fara tunkaraba a tasha da babyn sbd Babu ruwan kowa babuma Kuma
Wanda zai karba.
Innalillahi wainna ilayhirrajiun" yafara maimaitawa dukkanin jikinsa na saki.
Mai mashin ya fadawa Inda zai kaishi
Wata qaramar police station yaje da babyn suka qi karba sukace yace babban station
kawai.
Wata station din yakuma zuwa sukuma sukaqi karban 'yar suna zargin kodai yarda Yar
kawai yakeson Yi.
Wata sabuwar masifar yakuma Shiga lokacinda yagama yawo da babyn Babu wata mafita
ko daya.
Yanayin babyn kawai ya tabbatar masa da babyn sosai tayi nisa batada lafiya Dan
haka ya tattara a nufi wani private asibiti yakaita su duba.
Suna karbanta take sukai dakin jarirai da ita.
Fada suka fara yimasa sosai ganin yanayin datake ciki.
Duk abubuwan zasuyi Mata sunyi suka sakata a kwalba sbd ma sai allah Kam idan Zata
rayu.
Tashin hankali sabo yakuma Shiga lokacinda suka zayyano Masa cututtukan dasuke cin
babyn.
Biyan komai yayi kafin ya samu ya wuce gida yabar babyn anan sbd akwai masu kula da
babies a dakinsu.
Koda ya Isa gidansu mahaifiyarsa na ganinsa cikin tashin hankalin rashin daukan
wayarsa da rashin ganinsa da driver yayi har kusan qarfe daya da rabi na daren
yayi.
ABDULMAJEED..Ina ka shiga daga isowarka?
Lafiya kuwa?
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali idanuwansa na qanqancewa da tashin hankali da
damuwa yace"
Hajiya umma kaina kaman zai fashe
Zanshiga nayi sallah tukuna.
Cikeda kulawa tace"
Jeka kayi wanka da sallar ka huta da safe mayi magana.
Juyawa yayi Yana hada hanya ya nufi hanyar dakinsa Yana jin kansa na sake tsananta
ciwo.
Zubewa yayi qasa tsakiyar dakin Yana dafe kansa,
Daqyar ya tashi ya qarasa isa ya tube kayansa ya shafa toilet.
Wanka yayi ko zai samu kansa ya Dan sake tareda alwala yafito.
Jallabiya da gajeran wando kawai yasake yayi sallah ya miqe a daddafa ya Isa kan
gadonsa ya hau ya kwanta tareda rufe fararen idanuwansa dasuka qanqance sbd tashin
hankali da damuwa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/30, 11:50 AM] MG: *_40_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Babban tashin hankalinsa shine a yanayinda babyn Nan take ciki bazai iya bada ita
ga Yan sandaba kokuma gidan marayu sbd tana cikin mawuyacin hali,
Haka Kuma mahaifiyarsa a yanda ya santa mace ce Mai tsananin kishin 'yayanta
Musamman shi ta tsani wani ya rabesa Dan haka yasan bazata taba yarda da abar
babynba hannunsu harta danyi wayo tukuna akaita gidan marayun
Idanma baa ga uwar babynba kenan Dan zuciyarsa takasa yarda da uwa Zata iya jefar
da 'danta ta gudu duk tsananun rayuwa kuwa..
Washe gari tun kafin kowa ya tashi daga masallaci sallar asuba ya fice zuwa asibiti
da mota Yana Jin rashin nutsuwa matuqar ba zuwa yayi yasan halinda babyn ke cikiba.
Banyi baccin nutsuwaba sbd Jin yake babyn mutuwa zatayi a halinda dai yabarta.
Tunaninsa gabaki daya ya karkata akan uwarta ta gudu ne tabar 'yar sbd rashin
lafiyar babyn da bazata iya daukaba wannda hakan zallar rashin imani da tausayine.
Koda ya Isa asibitin babyn ba laifi tarta fara daidaituwa sbd Madara da aka kwana
ana bata duk Bayan mintuna sbd yunwace da tsananin wahala da sanyi suka Kama babyn
sosai.
Fes aka shiryata cikin kayan sanyi masu tsananin taushi farare tas daya siya tun
jiya a asibitin aka shiryata.
Har Inda babyn take aka Isa dashi tareda kallonsa likita yace"
Ina uwar babyn take ne?
Tayi sakaci da ganganci sosai akan wannan babyn gskia.
Wani irin sanyi yaji zuciyarsa tayi batareda ya dauke idonsa daga kan babynba dake
bacci idanuwanta a rufe murya a sanyaye yace"
Batada uwa.
Dakatawa daga rubutu a file Dr yayi yana dagowa dukkaninsa ya kalli ABDULMAJEED din
da mamaki yace"
Ka kuwa gane abinda na tambaya?
Mahaifiyarta nake nufi,
Wadda ta haifeta.
Wani daci yaji yakuma cika ransa ambatar sunan uwar babyn...
Yana kallonta tana kallonsa da 'yarta a hannu tahau mashin ta gudu tabarsa da 'ya
jaririya Yana yawo tsakar dare nemanta.
Mezaice gameda wannan uwar?
Mezai fadawa kowa gameda uwa irin wannan aduk Inda ze Kai babyn yasan bazaa taba
kaunarta ko kulawa da itaba Kamar uwarta Koda kuwa a halin talauci da qunci ne.
Numfashi ya sauke a boye tareda dagowa ya kalli likitan Kai tsaye yace"
Mahaifiyarta ta rasu.
Numfashi Dr ya sauke tareda tausayawa babyn
Saikuma ya dago ya kalli ABDULMAJEED din dakyau
Dan haihuwa Kam ya Isa ya Haihu tunda matashine Amma Kuma yanayin wayewa da hutun
daya gani tattareda dashi yasan zaiyi wuya ace yayi saurin aure bare harda haihuwa
A qiyasa bazai wuce 300level hakaba zuwa 400 a karatun jami'a.
Duk tunanin dr iya lissafinsane kawai Dan haka kai tsaye yace"
But you are the Father right??
Yes" kawai yace Masa Dan bayason tambayar.
Sauran abubuwan da baayi bane jiyan aka qarasa yi qarshe dai bai baro asibitin ba
sai qarfe goma Sha daya sbd babyn Kam Saida aka hada da Oxygen.
Daga asibiti report yaje yasaka na Neman uwar babyn Wanda yasan zaiyi wuya a sameta
tunda tana sane ta gudu ba wai batane babyn tayiba.
Koda ya dawo gida hankalin hajiya umma yagama tashi hakama duk Inda ranta yake
yagama Kai qololuwa gurin baci.
Musamman su Anty juwairiyyah dasuka Gama qara hawar da ita akan zancen ABDULMAJEED
yafi daukan mutanen waje da mahimmanci akanta.
Hajiya umma wadda asalin sunanta yake AYSHATOUH mahaifiyace ga ABDULMAJEED da
yayunsa Mata guda biyu.
Anty juwairiyyah itace Babba sai Anty safiyyah saikuma shi ABDULMAJEED daya
kasance qarami Kuma auta.
Son da mahaifinsu da hajiya umma kewa ABDULMAJEED sosai ya zarta abinda Yan uwansa
zasu iya dauka sbd bambamci ne afili.
Mahaifinsu justice Abdullahi Isah babban former justice ne a high Court dake Abuja,
Yayi retire tareda barin qasar yakoma South Africa tsawon shekaru kafin yadawo
Nigeria sbd ABDULMAJEED dake shaawar karatu da rayuwarsa a Nigeria.
Dagowarsu da qanqanin lokaci akai auren juwairiyyah da wani babban barrister anan
Abuja haihuwarta daya auren ya mutu tadawo gida itakuma anty safiyyah dama Bata
samu mijinba aikinta kawai takeyi Dan itama aikin mahaifinsu tabi lawyer ce.
Anty juwairiyyah da Anty safiyyah tun ABDULMAJEED dasu suna qanana Allah ya sanya
musu kishinsa Mai tsanani Wanda ta wani fannin yake surkuwa da baqin ciki sbd
fifici da banbancin da iyayensu suke nuna musu sosai akansa Musamman hajiya umma.
Abbansu Yana iya kokarinsa gurin yimusu adalci da Basu iya tasu kulawa da kaunar
Amma Kuma ko yayane baya iya boye fificin kaunar ABDULMAJEED.
Ita hajiya umma nata shine yafi tabasu sosai sbd Babu tunanin illar hakan take nuna
nata fificin.
Sunkoma tamkar wasu 'yayan riqo a hannun iyayensu sbd ABDULMAJEED Wanda hakan ya
Gina rashin kauna tsakaninsu da 'dan uwansu.
Bayan rasuwar abbansu Haj umma sosai ta sake qwallafa ranta akan majeed Bataji Bata
ganin kowa sai shi,
Su Anty juwairiyyah dasuka fara nuna rashin Jin dadinsu a fili sai kawai ta tsana
zamansu a gida kullum cikin musu fadan rashin fidda mijin aure takeyi sun fara
tsufa a gida.
Wannan kalaman nata ya tsananta duk wata tsanar dasukaiwa Dan uwansu sunajin kamar
shine duk wata matsakarsu da baqin cikinsu na rayuwa.
Haj umma tsananin kaunar datakewa 'danta yasa ta kasance cikin irin iyayen dake
tsananin kishin 'yayansu
Kishi Mai tsanani,
Sam batason kowa ya rabi 'danta tafison kulawarsa da komai akanta ita kadai,
Shikuma Allah yayisa Mai tausayi da taimako tareda mutunta mutane Musamman marasa
qarfi kusan sune mutanensa Dan yafison yayi mu'amala da wainda zasu ringa qaruwa
dashi suna samun taimakonsa dan kawar da tasu matsalar.
Mahaifiyarsa kuma hakan ne yasata ta tsani duk wasu marasa karfin dake taredashi
sbd ganin sunason samun kusanci dashi,
Ba abinda yake Basu bane baqin cikinta Dan idan duka zai Basu dukiya batada damuwa
ita damuwarta kada kowa ya samu kusanci da 'danta Bayan ita.
A American University of Nigeria yake karatunsa badan Haj umma tasoba tabarsa yake
karatu a wani garinba sai Dan hakan mahaifinsa yaso,
Burin mahaifinsane ganin yayi karatunda zai mallaki komai nasa ya Gina kansa da
kansa.
Fara karatunsa da yanda yake Dan jimawa baya gida yasa su Anty juwairiyyah suka
fara samun shiga gurin Haj umma har suka fara kawo sabani tsakaninta da ABDULMAJEED
ta hanyar saka Mata zargi Mai girma akan yafara 'yan Mata hankinsa akansu yake Nan
gaba ma mace Zata Raba tsakaninta da 'danta.
Hankalin Haj umma tashi yayi sosai sbd yanda idonta ya rufe akan kaunar da kishin
danta yasa komai aka fada Mata yarda takeyi Musamman da ABDULMAJEED din yayi
budurwa kullum cikin kiransa take Dan tun Kiran Sumayya din na damunsa harya daina
damunsa Dole ya saba.
Soyayyar MAJEED da sumayya ta daga hankalin Haj umma sbd sosai yanzu ta tabbarda
mace Zata rabata da Dan ta Dan haka ta rufe Ido tamasa kaca kaca da fada takuma
hanasa kula Mata saiya kammala karatun ita Zata Nemo masa matanda zai aura.
Ganin yanda ranta ya baci sosai yasa MAJEED din takaita muamalarsa da sumayya kwata
kwata baisake bi takanta.
Amma duk da hakan shikenan Haj umma taringa saka Masa Ido takasa yarda dashi.
Wannan yakawo babban gibin dayasa su Anty juwairiyyah qarasa saka zargi da rashin
sukuni a tsaninin Haj umma da majeed kusan yanzu kullum cikin fitinarta da fadanta
yake akan Yana hulda da 'yan Mata shiyasa yake jimawa a makaranta kafin yadawo hutu
gida.
Wannan ne babban matsalar data fara kunno Kai a tsakaninsa da mahaifiyarsa wadda
kwata kwata Bata yarda dashi sosai yanzu.
Su Anty juwairiyyah kuwa yanzu zancensune abin yardarta
Duk abinda suka fada mata hawa takeyi ta zauna daram tayita fada
Abbansu baya raye bare ya ganarda ita gaskiyar rashin kyautawa da tunani akan
abinda takeyi.
*******Shigowarsa gidan Kai tsaye Palo yashigo lokacin daga hajiyar sai Anty
juwairiyyah da rumanah 'yar anty juwairiyyah suna zaune palon anty juwairiyyah na
bubbude kayanta dasuka iso daga Dubai yau na tsadaddun laces da abayas datake
saidawa sosai.
Ko kallonsa hajiya bataiba lokacinda ya zauna kusada ita Yana riqo hannunta cikeda
kulawa yace"
Umma...
Zare hannunta tayi tana juyowa ta kallesa fuska ba walwala tace"
Meya hadaka da asibiti kake warin asibitin?
Tun asuba fa akace ka fita¿
Ina kaje?
Ajiyar zuciya yayi cikin Hana kansa Jin rashin Jin dadin zancenta sbd takasa daina
saka Masa dokar duk Ina yaje da Inda zashi saiya fada Mata bayan Shiba yaro bane
da girmansa take Masa irin hakan,
Amma Kuma uwace Babu yanda zaiyi da ita bakuma zai iyajin haushintaba sbd yanda
take kaunarsa haka yake tsananin kaunarta shima Dan tafiye Masa komai a rayuwarsa.
Ahankali ya bude Baki zai fada Mata abinda yake faruwa saiya dakata sbd tabbas
yasan atake zatace Bata yafe yakoma gurin babynba yabarta can asibitin Susan yanda
zasuyi da ita.
Ajiyar zuciya yayi tareda sakin murmushin boye damuwarsa yace"
Dubiya naje wani asibiti a kubwa.
Kasa yarda hajiyan tayi tana kallon fuskarsa dake kokarin Tona asirinsa sbd Bai
iya qaryaba baikuma taba yintabama.
Miqewa yayi ya wuce dakinsa yayi wanka ya shirya yakuma sulalewa ya fice gidan
batareda sun saniba.
Har dare Bai dawoba sai guraren 10 yadawo ya shige ya kwanta.
Washe garima daqyar ya iya tsayawa yasha ruwan tea kawai ya Kuma ficewa zuwa
asibiti.
Kwana biyu kowa gidan ya saka Masa Ido ganin duk yabi ya rikice baya wani cikin
nutsuwa gashi sai boye boye yakeyi sbd harga Allah bazai iya barin babynba shima
hakama mahaifiyarsa yasan bazata taba Bari su dauki 'yar ba Dan haka hankalinsa ya
tashi sosai,
Yayi yawon bincike akan gidan marayu Amma Babu Inda yaji bayanin daya kwantar Masa
da hankali Dan haka yasake shiga tsaka Mai wuya.
Ta Bangare Daya ya rikice ya haukace gurin Neman uwar babyn harya gaji Babu labari,
Komai yafara tsananta lalace Masa ne bayanda anty safiyyah ta ringa bin diddiqinsa
tagano asibitin dayake zuwa kullum harma da babyn dayake jinya mai amfani da
sunansa ABDULMAJEEDs.
Hankali tashe cikeda firgici da mamaki takawo labarin gida Inda suka dunguma sukaje
suka ganarwa idonsu Kuma suka tabbatarda babyn dai ta ABDULMAJEED dince ta hanyar
bayaninda nurse Tai musu shine mahaifin babyn.
Uwar babyn suka tambaya tace musu ta rasu gun haihuwa.
Dayake suma asibitin sun dade dafara gulmarsa akan kila baasan ya haifi yarinyarba
shiyasa yakasa kawo 'yan uwansa su tayasa hidimar babyn.
Gida suka koma hankali tashe suka zayyanewa hajiya komai.
Kasa yarda tayi da Abdul dinta zaiyi abinda suke fada kula Mata da aikata Zina
harma da haihuwar 'yar gaban fatiha.
Sunsan zaayi hakan Dan haka suka dauketa suka kwasa zuwa asibitin
Cikin saa kuwa suna zuwa suka taddasa rungumeda babyn an jikinsa cikin tsananin
kulawa.
Sallamarsu ake tunanin Yi zuwa gobe dan haka yake Jin sanyi ta wani bangaren Kuma
tashin hankalin yanda zaiyi da babyn.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/30, 7:25 PM] MG: *_41_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Ahankali Haj umma ta qaraso tana kallon babyn hannunsa a Rikice tace"
MAJEED babyn waye wannan?
Da sauri ya dago Yana kallonta dasu anty juwairiyyah.
Miqawa nurse babyn yayi yana kallon hajiyan yace"
Umma muje gida Zan Miki bayani.
Kasa motsawa tayi sbd fargaba da tsoro tace"
Majeed bazan koma gidaba wlh saikamun bayanin Inda kasamo wannan babyn.
Mezan gani majeed?
Mezan ji?
Ta tabbata kenan fasiki ka Zama har kayi nisa haka¿
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun" zuciyarsa dake rawa tafara karantowa.
Cikin dacin kalaman mahaifiyar tasa ya dago ya kalleta Jin sunan fasiqi data kirasa
dashi.
Zuciyarsa na daci ya bude Baki zaiyi magana anty juwairiyyah ta taresa da munanan
kalamai tareda kiransa da sunayen mazinatai kala kala.
Kasa dago kansa yayi cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki ya dakatar da Anty
juwairiyyah da cewa"
Anty juwairiyyah me kika fada?
Sunayen mazinata fasikai kike kirana,
Idanma nine mahaifin babyn akwai yanda zakuyi ne da qaddarar Allah?...
Ba zato sukaji qarar saukan Marin da hajiya tayi sakar Masa tana kallonsa ciki
tsananin bacin Rai da baqin ciki tace"
Wallahi wannan 'yar bazamu taba karbantaba idanma Kaine ubanta,
Idan Kuma wani gurin kasamota kayi gaggawar maida ita..
Kai koma Kaine ka haifeta bazaka karbetaba wuce muje gida.
Jajir idanuwansa sukayi sbd baqin ciki da damuwa,
Su Anty safiyyah kuwa ta Inda suke shiga bayanan suke fitaba take hankalin hajiya
yaqarasa tashi hawan jinin datake fama dashi yayi sama take
Ba Shiri suka Jata zuwa gida har ABDULMAJEED din Wanda jikinsa yayi dukkanin sanyi.
Isarsu gida Bai qarar da komaiba sai sabon tashin hankali Dan kuwa bayanai ne daga
Yan sanda sukazo anga Hadiza Kuma ta tabbatar musu da 'ya 'yarsace.
Kasa yarda da zancensu yayi saida aka kawo Hadiza wadda gabaki dayanta batada
bambamci da mahaukaciya sbd yanayin shigarta da rashin lafiyarta.
Saida aka fara tambayarsa ya tabbatar musu da itace mahaifiyar babyn kafin aka sake
tambayarta itama tace babynsa ce.
Ganin yanayinta na tabin hankali yasa aka sallameta ta tafiyarta dayake yan sandan
sunga gurin samun kudi sai suka Kama MAJEED din akan yayiwa mahaukaciya fyade ta
Haihu.
Take Yan sanda suka sauya zancen Kuma suka tabbatarda Hadiza ta tafiyarta sbd karma
aci gaba da tambayarta tadawo daidai tafada wani zancen Bayan wannan.
Babban tashin hankali yashiga Yana son mahaifiyarsa kadai ta yarda dashi ta
fahimcesa Amma tuni taji tana danasanin fifita sonsa akan sauran 'yayanta.
Kasa danne abinda takeji tayi zuciyarta take tafara Neman bugawa aka kwasheta zuwa
asibiti.
Acan station kuwa ba Imani yan sandan suka rufesa tareda cike Masa laifin dabai
aikataba.
Zafi zuciyarsa da kansa sukeyi kaman zasu fashe,
Wace irin masifaffiyar qaddara ce wannan?
Tayaya mahaifiyarsa da 'yan uwansa zasu yarda da zai iya Koda kallon wannan matar
so ukuma bare iya wani abun da ita sbd tsananin qyanqyamin dayake dashi.
Bai taba kukaba tun girmansa Amma ayau baisan lokacinda wasu hawayen baqin ciki da
qunci suka gangaro masaba.
A rufe ya kwana Saida yakuma wuni a rufen kafin alhj jamilu qanin Haj umma yazo
yayi belinsa shima ransa amatuqar bace da abinda MAJEED din yayi.
Ko sauraronsa baiyiba yayi Masa diban albarka da maganganun dasuke kaman Yana Masa
Baki.
A gidan ma saida ya zubda hawaye ga maganganu marasa Dadi da 'yan uwansa suka ringa
jifansa dasu
Mahaifiyar tasa kuwa ko qaunar ganin batayi hakan ta ringa hawaye tana jujjuyar
dakai batason ganinsa yatafi yabarta kawai.
Nauyi zuciyarsa tayi ta yanda baisan mezaiyiba,
Mahaifiyarsa ta tsanesa Bata son ko ganin inuwarsa,
Yan uwansa ma sun tsanesa,
Yan uwan mahaifinsa Dana mahaifiyarsa sai Allah wadai sukeyi dashi.
Kiransa akai daga asibiti akan yazo ya tafi da babysa.
Baida wani zabi bayan zuwa ya karbota sbd bazai iya barinta acanba ayanzu da kowa
yagama alaqanta shine mahaifinta.
Koda ya karbota ya dade Yana tunanin Inda zai kaita sbd dagashi har ita bazasu taba
karbuwa ba a gidansu.
Hakanan ya daure ya iso gidan da ita saidai tun kafin ya shiga ainihin gidan su
Anty safiyyah suka tabbatar Masa bazai zauna da 'yar ba a gidan.
Zabi zaka dauka ko ka kaita gidan marayu kokuma kasan Inda zakaje ka raineta Dan
bazai taba yiyuba ayi renon 'yar qaddaraba a gaban hajiya sbd baka damu da damuwa
ko baqin cikinka ya kasheta.
Bai tsaya ya sauraresuba ya wuce ciki da 'yar a hannunsa rungume ya nufi dakinsa.
Cikin fada sosai da tsawa anty juwairiyyah tace"
Bakaji abinda safiyyah ta fada bane?
Ina zaka wuce ana magana?
Ka fice kakoma tun dare baimaba kakaita gidan marayu idanma bazasu karbaba ka
maidawa mahaukaciyar uwarta idan taga dama ta Yar da ita...
Tsananin zafi da quncin da zuciyarsa me Masa yasa tafara bushewa a fusace yace"
Duk abinda zanyi da ita da Inda Zan kaita ba ruwan kowa bane matsalata ne tunda
nine nakawota..
Idan sbd wannan 'yar alhakin aketa tada hankali to naji nine ubanta zai raineta
daga Nan har girmanta Kuma Babu Wanda ya Isa ya hana hakan.....
Nima ban isaba Amma Kuma na Isa danace kabar gidan Nan da ita tunda gidan bana uban
nata bane.
Kai yanzu MAJEED har kayi nisan da yannanka suna magana kana mayar masu Kai me 'ya?
To wlh wallhi wannan 'yar dai bazata zauna a gidan banba,
Banason ganinku daga Kai har ita ka tattara ku koma gidan marayun har Kai sbd kaima
kazama marayan daga yau...
A Rikice ya kalli hajiyar idanuwansa na sauyawa
Muryarsa na rawa yace"
umma nabar gida?????
Ban Isa bane?
Ai kakai tunda kazama uba yanzu.
Innalillahi wainna ilaihrrjiun""
Umma........
Daga Masa hannuwa tayi tareda fashewa da kuka Mai ciwo da qunan zuciya tace"
Idan Ina ganinka zuciyata bugawa zatayi MAJEED Dan Allah ka tafi na daina ganinka
da 'yar nan.
Kaci amanar tarbiya da tsananin kaunar dana fifitaka akan 'yan uwankw..
Maganganunta dukan zuciyarsa sukeyi suna yamutsa qwaqwalwarsa tareda zafafa kansa.
Daqyar ya daga qafafunsa zai matso gabanta ta Kuma fasa kuka tana ja da Baya.
Wani nauyi ne ya danne Masa zuciya ya juya ahankali ya shiga dakinsa ya tattaro
kayan dazai buqata ya zubo a jaka ya fito.
Su Anty safiyyah na kallonsa da mamaki sosai ya fice gidan batareda yasake cewa
komaiba.
Yana fita kuwa hajiya jikinta ya rikice Nan tafara numfashi daqyar
Hankali tashe aka kwasheta zuwa asibiti.
Baitaba sanin haka 'dacin baqin ciki yakeba sai yanzu,
Zafi,ciwo,radadi,nauyi da tiriri zuciyarsa keyi duk lokaci daya,
Gidan Alhaji jamilu ya nufa Amma cin zarafin dayayi Masa yafi Wanda akayo Masa daga
gida Dan haka yana baro gidansa Kai tsaye hotel yanufa yakamata daki ya kwantar da
babyn tareda komawa gefe ya zube Yana riqe kansa dake neman tarwatsewa.
Babban qunci da dacin zuciyarsa yanda mahaifiyarsa da Yan uwansa dasuke jininsa
suka zabi aibatasa da kalmomi mafi muni tareda tsanarsa..
Shin idan da gaske shine qaddarar haihuwar babyn ta sama haka zasu gujesa kenan?
Me yayiwa wannan baiwar Allah dazata ruguza rayuwarsa haka?
Kansa dake Neman bugawa ya juyo ya kalli babyn dake bacci cikin nutsuwa da
kwanciyar hankali..
Wani irin tausayinta yaji tareda qaunarta,
Me tayiwa mahaifiyarta dazata jefar da ita haka ga mutuminda batasaniba,
Batasan halayyarsaba,
Shin idan ga wani mugun mutum ne ta jefarda 'yar Yaya takeson rayuwar wannan 'yar
alhakin tayi.
Kansa da kirjinsa sun toshe baida tunani komai.
Alwala yayo yafito yayi sallar magriba da aka Kira.
Yana idarwa babyn ta farka ya taso ahankali ya tsaya akanta Yana kallon yanda take
motsawa ahankali tana fidda harshe alaman yunwa.
Numfashi ya sauke a sanyaye kafin ya juya gurin jakar kayan madaranta da nurse ta
koya Masa yanda zai hada.
A sanyaye ya hada mata madaran da ruwan roba kafin ya debo ruwan dumi ya saka
madaran yayi dumi.
Ajewa yayi gefe kafin ya dauki babyn yafara Bata ta karba take tana zuqa ahankali.
Qura Mata fararen idanuwansa dasuka sauya yayi Yana Jin tausayin kansa da ita,
Meyasa iyayensu zasu zabi jefar dasu akan qaddara?
Meyasa iyayensu suka zabi rabuwa dasu akan abinda suma basune suka samarwa kansuba?
Uwa mace da akafi sani da qawa zucin 'danta Amma su nasu uwayen Mata ne suka
fincikesu daga rayuwarsu suka 'yar batareda nazari ko tunanin halinda zasu shigaba.
Shi tasa uwar data fincikesa daga rayuwarsu ta Yar yanada girman dazai kula da
kansa Amma ita wannan babyn me tasani.
Har tagama shan madaran tayi bacci bai saniba sbd nisan dayayi a tunani.
Har lokacin sallar ishai tayi Yana zaune rungume da babyn.
Sallar ishai yayi wadda Yana idarwa ya nema guri yazauna tareda rufe idanuwansa
yanajin yanda kansa ke tsananin ciwo.
Babban saukin daya samu babyn bamai rigima bace Dan haka har safe batai Masa rigima
ba sai Madara datakesha sosai Dan haka baiyi wani baccin safeba.
Garin na wayewa guraren qarfe goma Dole cikin ma'aikatan hotel din yasamu wata ta
sauya Masa kayan babyn ta shirya Masa ita ya dauketa suka sake koma gidansu.
Wannan karon Yana Isa babban tsaro yasamu a gate akan kada abarsa ya Shiga gidan.
Kiran wayar hajiyar ya ringa Yi Amma Sam Bata dauka daga karshe aka kashe.
Numbern anty juwairiyyah yafara kira itama bata dauka.
Ta anty safiyyah yakoma Kira itama Bata dauka.
Anan ya kusan wuni da babyn cikin Rana ganin Zata wahala yasa yakoma hotel din.
Washe gari haka yakoma gidan Amma saiya samu labarin sun wuce Lagos gabaki dayansu
gurin ganin likitan hajiya.
Tashi hankalinsa yayi Dan haka ya ringa Kiran wayar hajiyar Bata Shiga qarshe ya
Kira anty juwairiyyah.
Kalaman data fada masa sune yaka saddaqar da duk wani sauran burinsa na zama cikin
Yan uwansa da mahaifiyarsa.
Ta sanar dashi hajiya umma Bata kaunar jinsa ko ganinsa,
Idan yakuma zuwa ko kiranta Zata iya tsine Masa.
Wainnan kalaman sun girgiza duk wata jarumtarsa da karfin zuciyarsa,
Amma Kuma sun daskarar da zuciyarsa data tarwatse lokaci daya,
Tabbas zaiyi nesa da Inda Haj umma Zata gansa bare yazama sanadin mutuwarta da 'yan
uwansa suke fada.
Yana barin gidan yakoma hotel ya tattara kayansa guri daya,
Yayi wani irin kukan baqin ciki da maraicin rashin mahaifi a duniya,
Yayi kukan rabuwa da uwa wadda yasan itama tana cikin quncin wannan hukuncin nata
saidai Kuma bazai taba Zama sanadin ciwonta ba dakuma tsinuwar data ambata garesa.
gari na wayewa ya nufi Tasha yahau motar komawa Yola.
A motar tun agurin Lodi ya sanar masu mahaifiyar 'yarsa ta rasune zai koma gida
gurin danginsa.
Da wannan ya kawarda kallon zargin da ake binsa dashi fa babyn.
Wasu sun yarda wasu Basu yardaba ahaka dai akai tafiyar Amma saida wata dattijuwa
ta karban Masa babyn sbd ganin yanda yake fama da babyn.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/30, 11:07 PM] MG: *_42_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Wuni cur sukai a hanya kafin suka Isa,
Saida ya sauka mota hankalinsa yayi mummunan tashi sbd baisan yanda zaiyi da
babynba,
Baisan wazai tunkara ba,
Baisan tayaya zaiyi rayuwar makaranta da babynba.
Tunanin farko daya fara zuwa kansa shine ya fara Kama hotel na kwanaki sbd bazai
iya Zama da ita a gidansaba sbd bashi kadaineba tare yake da friends dinsa ashir da
Nuraddeen.
A hotel din daya Kama yakwana da babyn gari na wayeba baida zabi daya wuce yakaita
gurin renon marayu sbd bazai iya yawon makaranta da itaba.
Kudin daya bada sosai ne kadai yasa suka karban Masa ita amatsayin 'yarsa da
mahaifiyarta ta rasu gurin haihuwa.
Kwana biyu yayi yana yawo tsakanin makaranta da zuwa duba babyn,
Sabon yanayi ya shiga na rashin sauki fa sukuni,
Hankalinsa ya rarrabu,
Ga damuwa da quncin dake maqale cikin ransa.
Ahaka yayi kusan sati biyu
Take kudadensa sukai qasa sosai.
Babban abinda ya sake basa tsoro da firgici ga halin mutanen duniya shine duk kudi
da Madara dayake siya na baby metron kashe kudin takeyi Bata siya Mata abubuwan
buqata
Ko gyaran jiki dayace aringa Mata da wipes sbd asibiti dasukai masa gargadi akan
rage yawaita Yimata amfani da ruwa sbd sanyin daya kamata a baya,
Amma sbd rashin tausayi da imani Ashe ruwa suke Mata amfani dashi ko Pampers basa
siya maqale kudin sukeyi ko fitsari tayi ruwa suke saka zuba Mata sosai.
Ciwo yafara Neman kama babyn damuwa tasake kamasa sosai gashi bayajin zai iya miqa
babyn har abada gidan marayu.
Haka yanaji Yana gani ya bar babyn hannun metron sbd watanni kadan suka rage Masa
ya kammala karatun.
Komai nasa yaqare,
Kudin hannu da account dinsa sun qare tas dan haka yafara shiga yanayi sosai.
Babban sauyin daya samesa na rayuwa shine gabaki daya ya rasa walwala da fara'arsa,
Zancen abinda ya samesa tuni ya yadu tsakanin Abokai da jama'ar dasuka sansa
Book Chapters
Chapter 17
Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500