ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli farar dattijuwar dake tsaye gefe cikin ash Australian lace da
lafaya baqa a nade da ita yace"
Hajiya ku qarasa Bara na dauko Alhaji idan kafin Ku huta.

Gyada Masa Kai kawai tayi ahankali tareda maida kallonta kan Inayah data kasa
daukewa Ido.

Cikin nutsuwa Inayah ta kalli matar wadda itama tsura Mata Ido yayi sosai sbd
haskenta sosai da Kuma ganin kamanninta sosai da Abbinta Dan kuwa kusan Tama fisa
kyau sbd tana mace saidai kawai manyancin datai sosai.

A natse cikin kasa boye mamakinta sosai tace"

Ina wuni?
sannu da zuwa.

Sam hajiyar Bata amsaba Wanda ita Inayah Sam Bata luraba juyawa tayi Takoma ciki
tana sake saka Kiran Abbi a wayarta.

Cak hajiyar tayi agurin taqi saka kafarta a palon.

'yarta dake gefenta wadda a shekaru tafi anty Hafsat shekaru sosai ta kalli hajiyar
zuciyarta na quna kaman yanda ta hajiyar ke quna Kai tsaye ta bude Baki ba boye
boye tace"

Hajiya inaga mu koma gida kowai kokuma kokuma muje gidan Alhaji babbahn shida
kikazo sbd alfarmar daya nema ta zuwan naki.

Batareda hajiyar tace komaiba kuwa suka juya
Anty Hafsat ta juyo da sauri tareda binsu a rikice tana bawa hajiyar hakurin su
dawo.

Hajiyar tafiyar kawai takeyi Amma zuciyarta a rufe take....

Ciwon hawan jininta Dana zuciya daf yake da tashi sbd dacin da zuciyarta ke dauka..

Kasa jurewa tayi ta tsaya cak tana Dan dafe kirjinta.

Da sauri anty Hafsat da 'yar tata wadda anty Hafsat takira da Anty juwairiyyah suka
riqota suna Kiran sunanta da cikin kulawa.

Ganin tana neman faduwa agurin yasa ba yanda anty juwairiyyah ta iya suka Jata suka
koma cikin gidan.

Umma yaganah data fito palon Jin ance sunyi baqi Bata ga kowaba tana Shirin juyawa
suka shigo da hajiyar a rirriqe.

Da sauri cikin kulawa tace"

Subhanallh,
Hafsat baqin namune ba lafiya?
Bari Akira Dr farhat da sauri kafin Nan Bari Neesah ta fara dubata.

Ciki umman tayi takira Neesah saidai Ashe Neesah din ta fita Dole sai dr farhat
suka kira da gaggawa.

Agurin wayar anty Hafsat tace"

Umma yaganah ki sanar da ita umman AA MAJEED ce da kanta da Allah ta iso da
wuri........
Wuta umma yaganah ta dauke tareda bude dukkanin idonta tana kallon hajiya.

Sai alokacin taga zallar kamannin MAJEED atareda hajiyar dan haka take jikinta Dana
Inayah data fito lokacin mutuwa sbd tsananin farin ciki.

Umma na aje wayar kuwa ta kalli anty Hafsat tace"

Mahaifiyar MAJEED ce kikace?

Eh umma itace.

Maida kallonsu kan hajiya sukai itada Inayah lokaci daya fuskar Inayah daukeda
farin ciki Batasan lokacinda ta furta"

Yau Naga daya da cikin kakannina kenan...
Ashe munada dangi muma,
Abbi na ummansa na raye..

Da sauri umma yaganah ta Dan kwabeta kada ta sauka layi
Cikin sakin fuska da bayyanan farin ciki tafara yimusu sabuwar sannu da zuwa tana
miqewa Anty juwairiyyah ruwan roba da aka kawo Mara sanyi tace"

Bata Tasha Zata Dan ji dama Dama kafin Dr farhat din tazo.

Daga hajiyar har anti juwairiyyah Babu wanda ya iya magana har lokacin sbd Babu
Wanda zuciyarsa Bata cikin dacin rai na shigowa gidan.

Ganin yanayinsu yasa umma datake Babba ta fahimci akwai damuwa Dan haka tace Inayah
tayi ciki har hajiyar ta samu nutsuwa tukunna.

Babban dakin bakinsu dake gefen na umma yaganah aka gyara take duk da Baya buqatan
wani gyaran sbd komai na dakin fes yake Kuma Babbane da toilet.

Dubari su Anty Hafsat suka ringa yiwa hajiyar ana mata firfita duk da sanyin AC sbd
asamu Dr farhat ta iso.

Dr farhat na isowa aka Kama hajiyar aka Kai dakin da aka Gama gyara musu sanyin AC
da qamshi sai tashi yakeyi.

Ba wata matsalar bace kawai jinintane ya hau take.
Maganinta da batazo dashiba shi Dr farhat tasa aka kawo suka Bata
Cikin Yan mintuna kuwa sai gashi tadan samu tafara dawowa daidai.

Fita akai aka bawa hajiyar da Anty juwairiyyah guri su but suyi sallah da sauransu
tukuna.

Bayan fitarsu ganin yanayin hajiyar yasa Anty juwairiyyah data Gama cika da baqin
ciki aranta tun na shekarun Dana yanzu datake gani gabanta yasa bataiwa hajiyar
maganar komaiba ta nufi toilet tashiga Dan yin alwala.

Hajiyarma saita huta Zata iya sallar sbd tanajin jiri har lokacin da bugawar zuciya
da sauri Dan haka rufe idanuwa tayi daga kwancen tanajin zuciyarta na karye fiyeda
shekarun data debo bada ABDULMAJEED dintaba sbd Bata saniba Ashe Yana Nan ya Gina
sabuwar rayuwa da sabuwar uwa...Jin tayi hawaye na taruwa acikin idonta Amma kaman
koyaushe Bata barin su gangaro sbd zubda hawayen uwa akan danta matuqar bana farin
cikiba babbar masiface ga 'da.
Inayah kuwa cikin farin ciki take Neman wayar abbin Amma still Bata samuba sai taji
murnarta ta Kai sbd duk Wanda Zata samu a rayuwarta matuqar Bata daidai da Abbinta
Bata cikin farin ciki da nutsuwa Dan haka take murnar ta sace Mata ta zauna daki
tareda zubawa wayarta Ido.

Umma yaganah kuwa hidima tashiga kitchen da kanta tafara yiwa su hajiyar MAJEED din
sbd tasan matsayinsu sun wuce abar 'yan aiki da hidimarsu Dan haka tahau aikin
abinci Lafiyayye Mai lafiya.


Saida akai Kiran magriba aka Gama komai aka kwasa a jere da kuloli aka Kai dakinsu
har lokacin daga hajiyar har Anty juwairiyyah Babu Wanda ya saki fuska ko nuna
sakewa Amma hajiyar taji sauki tana zaune tana waya a sanyaye da babbar yarta.

Umma yaganah Bata damu da rashin sakewarsuba bil haqqi take musu hidima tana sake
bayyanar musu da mahimmanci dasuke dashi Mai girma a gidan duk da yau suka fara
zuwa.

Acan Kuma Inayah nason magana da anty Hafsat Amma anty Hafsat din ta hana sbd Dr
farhat na gidan Bata wuceba Kuma Batasan da MAJEED aka daura aurenba a qataice
bakowane yasan meye dalilin fasa auren Inayah da Dr Abdul ba hakama bakowa yasan da
waye aka daura aurenba sbd duk har lokacin a uban Inayah suka Sansa.

Dr farhat na tafiya saiga su Alhaji babbah sun iso daidai tareda motarsu umma
Hadiza da 'yan uwanta.

Dunguma sukai suka shigo ciki gabaki daya babban palonsu umma yaganah.

Tunda umma Hadiza tashigo take rarraba idon Neman ganin Inayah cikin gidan.

Inayah tunda taji su umma Hadiza sunzo gidan taqi fitowa ko Alhaji babbah tanason
fitowa ta gaidar Amma batajin Zata iya barin umma Hadiza ta ganta matuqar bada
izinin Abbinta ba sbd shine kawai yakeda iko akanta na yanda zaiyi da alaqarta da
Hadizan.

Umma yaganah ma Gaisawa kawai tayi dasu Alhaji babban ta miqe Zata komawarta ciki
sbd yanzu da mahaifiyar MAJEED take Nan ba buqatan zamanta agurin dama can Dan tana
matsayin uwa ne.

Cikin nutsuwa Alhaji babbah yace"

Yaganah dawo ki zauna ai komai dake zaayi kece MAJEED yanzu tunda Baya Nan.

Dan murmushin yaqe tayi tareda dawowa ta zauna tana dan kallon Inda hajiyar MAJEED
take zaune fuskarta ba walwala ko kadan.

Kusan kowa ya zauna ya nutsu,

Alhaji babbah ne da CM a gefe daya
Sai umma Hadiza da Haj balaraba a dayan gefen
Alhaji buhari dasu malam Umar ma dasuka matsu dason ganin Inayah duk suna zaune sai
Dr Abdul daya rakube cikin yanayi na tausayi da ciwon dake damunsa.

Hajiyar MAJEED ma da Anty juwairiyyah da umma yaganah sai Anty Hafsat gefensu daya.

Cikin nutsuwa Alhaji babbah yafara magana da cewa"

To dukkaninmu dai kusan bamusan junaba anan MAJEED da INAYAH ne ya hadamu anan,
MAJEED yayi tafiya wadda Nima ban hanasa duk da nasan zaayi wannan zaman sbd Yana
cikin yamutsin Kai Dana zuciya
Yaron Yana buqatan nutsuwa sbd abubuwan duk sun taru sun ratayane akansa Dan haka
gwara abarsa ya samu nutsuwa kada pressure da damuwa din mahaifiyarsa gatanan data
matarsa data hajiya Hadiza dama Tamu duka ta sanyasa cikin wani hali.


Hajiya Asma'u wannan itace hajiya Hadiza da 'yan uwanta gasunan mahaifiyar Inayah
'yar MAJEED da kuka sani a baya matarsa Kuma a yanzu.

Hajiya Hadiza wannan Kuma itace mahaifiyar ABDULMAJEED data haifesa.

Ayanzu wannan taron dai na fahimatar junane dakuma warware duk wata damuwa da
qaddarar data Riga ta wuce.

Inayah dai ba 'yar MAJEED bace hajiya kaman yanda kike tunani
Amma dai yanda tazo hannunsa ne Babu Wanda yasani sai Allah saikuma MAJEED din da
Hadiza gatanan zaune.

Hadiza ki warwarewa hajiya komai sbd kawarda zargi da Kuma damuwar qaddarorin
dasuka gifta abaya data rabu da 'danta akan hakan.

Dagowa Hadiza tayi jiki a sanyaye ta kalli hajiyar cikeda kunyar Zama mugun sanadin
daya kawo abubuwa da dama.

Kan su Yaya Umar da Yaya kabiru ta maida kallonta sbd kusan suma sune sanadin
komai.

Inayah data tsaya bakin kofar dakin umma yaganah sbd tanason taji yanda tazo hannun
Abbinta da kunnenta batareda wani ya fada Mata ya rage Mata wani abun....

SHEKARUN BAYA....
#MAMUH##
#LOVE/ROMANCE/LOADING


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/29, 6:24 PM] MG: *_38_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tana fitowa gidansu rungume da jaririyar tata dake lafe kirjinta tana bacci taji
qafafuwanta na Neman sanyi Amma sukasa riqeta sbd wani irin nauyi da kirjinta
kemata tareda radadi a maqoshi..

Sake rungume jaririyarta tayi da kyau ahankali kafin ta dago ta kalli hanya da
idanuwanta dasuka qafe sukai jajir sbd kuka tuni ya qafe daga Idanuwanta.

Ahankali ta daga qafafunta tafara tafiya tareda kauke kanta qasa sbd Yan anguwa
wainda suka lura da ita suke kallonta da ma'anoni da maganganun zunde da zagi.

Bakowane yasan tadwo daga Lagos dinba da ciki saidai sukaji haihuwar tareda rasuwar
mahaifiyarta shiyasa kusan duk Wanda ya bude Baki tir da Allah wadai yake furtawa
gareta da jaririyar 'yarta.

Ahankali take takawar sbd rashin qarfin jiki dakuma qarin data samu agun haihuwa
gakuma rashin abinci ko abinsha Dan haka batada wani babban kuzarin takawa da sauri
harta fice daga layin batareda ta waiwayo ba Dan tanajin idanuwan mutane akanta
Wanda tasan mummunan fatar rashin ganin me kyau suke Mata a duniyar da Zata shiga.

Kasa hawa titi tayi sbd Batasan Inda ta dosaba,
Batasan gurin waye Zata ba a wannan mummunan halin datake ciki,

Batada uwa Bata uba batada miji waye gareta Mai tsaya mata?

Samun kanta tayi da zaunawa bakin wata bishiya sbd kwakwalwarta datake neman Dena
aiki.

Jaririyarta tafara kuka Wanda na tsananin zafin ranar dake dukansu ne

Yaye zanin datake dunqule aciki tayi ta Dan kalli fuskarta taga yanda fuskar tayi
jajir take sbd azabar Rana
Sai alokacin taji zuciyarta data daskare tana narkewa da tausayin kanta dana
jaririyar Dan haka batada zabi daya wuce ta tunkari gidansu salisu ko ummansa Zata
karbesu tunda jikartace su taimaketa ta zauna gurinsu ta Rena Ayshatouh idan ko
shekara tayi saita barta takoma gidansu idanma sbd itane su Yaya Umar suka koreta
daga gida.

'yar qaramar jakar kayanta ta bude tafara duba kudin datake dasu.,

Dari uku da ashirin tagani take jikinta yakuma mutuwa saidai halinda zuciyarta take
ciki Batajin akwai abinda zai fisa daci.,

Miqewa tayi ta qarasa bakin titi Anata kallonta sbd Jin yanda jaririya ke kuka
sosai a jikinta Dan haka Bata tsaya juran napep ba ta tsayarda Mai mashin ta hau
suka tafi.

Gabanta tsananta faduwa da shiga qunci yakeyi sbd hajiyar salisu ma batasan yaya
zata karbesuba...
Mai mashin na ajiyeta kofar gidan ta Ciro dari da hamsin ta miqa Masa ta juya ta
shige qaramar kofar gidan tana sake qamqame yarta jikinta.

Tun kafin ta qaraso ciki Yara suka fara Isa gurin hajiyar suka sanar Mata Hadiza
tazo.

Dan shiru hajiyar tayi kafin ta kalli yaran ta korasu waje ta dawo da hankalinta
kansu balaraba dake gidan ta sallamesu suka wuce inda zasu ta kofar baya batareda
sun tsaya Gaisawa da Hadizan ba Dan dama a sama sama suke da ita tun salisu nada
Rai bare yanzu da basuda alaqa da ita.

Da wata irin dasasshiyar sallama ta shigo hankali sbd muryarta ko fita batayi.

Da mamaki hajiya ta kalleta idanuwanta na sauka kan jaririyar dake hannun Hadizan.

Idanuwan Hadizan zuwa fuskarta ta kalla dakyau take tagane jegone tareda Hadizan
Dan haka ta tattaro hankalinta da mamaki a bayyane kan fuskarta tace"

Hadiza¿
Kece nake gani?
Lafiya da Rana tsaka haka?
Ba zaman karban gaisuwar Aishatu akeba.

Kasa magana Hadiza tayi sbd jirin dake dibanta Dan haka a sukwane ta qaraso ta
durqusa gaban hajiyar tareda sunkuyar dakai idanuwanta na sake rinewa.

Sake Shiga firgici hajiya tayi tana qin nuna taga jariri atareda hadizanba tasake
cewa"

Hadiza nace lfy kuwa?
Kiyi mgana kikai shiru kina bani tsoro...

Dagowa Hadizan tayi tana kallon hajiyar sbd tasan bazatace bataga abinda ke
hannuntaba
Idanma Bata ganiba bazatace batajin kukan da Ayshatouh ke tsalawaba.

Sunkuyar dakai tayi tareda bude jaririyar dakyau agaban hajiyar muryarta na a
disashe da tsananin damuwa da qunci Mai daci tace"

Hajiya haihuwa nayi su Yaya Umar sukace nabar gida,
Bansan Inda zaniba sbd ko Abokai banda shine nataho Nan....


Dauke wuta hajiyar tayi daga zaune tana kallon Hadizan Baki sake ko fuskar
jaririyar taqi kalla.

Qofa tafara kalla ta leqa tsakar gida taga ba kowa tadawo da sauri ta kalli Hadizan
cikin tsananin mamaki, firgici da takaici Kai tsaye tace"

Me Zan Miki anan hadiza?
Haihuwafa kikace kinyi?
Haihuwa ba aure fa?
Wace qaddarace wannan takaiki ga wannan mummunan sakamakon? Shine Kuma Zaki zomun
Nan?

Ko kunyar 'danki dake gidan Nan bakijiba kika kwaso jiki da jaririn shege kizomun
anan?
To Kinga Hadiza tun kafin Raina ya baci Kuma tum kafin wani yaji tashi ki fice,

Mune mukafi kowa hauka a duniya ne dazamu Baki gurin zaman renon barna......

Rawa hannuwan Hadiza suka fara hankalinta yasake mummunan tashi tana kallon hajiya
da idanuwanta jajir tace"

Dan Allah hajiya ki yarda Dani ki fahimceni
Kima kaini a dubani idan ana dubawa wallahi tallahi banyi kowace irin barnaba
nasamu cikin Nan,
Wallahi cikin salisu ne......

Wata irin mummunan zabura hajiyar tayi tana kallon Hadiza a gigice sbd mamaki da
baqin cikin zancenta Dan ta Gama raina Mata hankali kokuwa dai mahaukaciya ta
dauketa?
Amma dai Bari ta tabbatar...kallonta tayi a Rikice tace wane salisun Hadiza?


Muryarta Bata fita sosai sbd shaqewar maqoshi tace"

Salisu baban Abdul....

Kasa magana hajiyar tayi ta rufe idonta daya fara sauyawa sbd tsananin bacin Rai da
masifar Rainin da Hadiza tazo dashi Dan haka Bata buqatan ma Jin komai ta nuna Mata
hanya tace"

Fice Hadiza kibar gabana Dan Allah.

Dagowa Hadiza tayi ta kalli hajiyar sai alokacin hawaye suka ciko jajayen
idanuwanta suka fara gangarowa.

Magana takeson yi Amma zuciyarta tayi nauyi bazata iyaba sai wani irin quntataccen
kuka Mai ciwo daya zuwar Mata.

Ganin ba tashi zataiba kada wani yashigo yagantama kokuma yaji haukar datake fada
yasa hajiyar Kama hannayenta ta miqar tsaye tareda janta takaita har waje ta Kuma
gargadeta akan sake zuwa da wata jaririyar gidan da sunan salisu abakinta.

Kuka sosai Hadiza keyi tanajin wani irin azababben ciwo a zuciyarta,
Jin takeyi kaman zuciyarta zata mutu,

Ganin mutanen dake wucewa sunfara Mata kallon mahaukaciya yasata Jan jiki tabar
kofar gidan.

Tafiya kawai takeyi sbd Batasan Inda zataba,

Jin jaririyar tayi baccin wuya itama yasata tsayawa ta goyata taci gaba da tafiya.

Tafiya Mai nisa tayi wadda batamasan tayiba har Saida yamma tayi sosai ta nema
bakin wani gidan abinci ta zauna tareda sauke jaririyarta ta saka cikin hijabinta
tafara Bata nono.

Kasa Shan nono 'yar tayi sbd tuni ciwon zazzabin wahala ya rufeta sbd ba qaramar
Rana sukashaba.

Fara jijjigata tayi tana sake cusa Mata nonon Amma Bata amsaba Dan haka ta maidata
ta goya.

Shagon dake gefen gidan abincin ta qarasa ta siyo ruwan roba na sauran canjinta
dasuka rage Takoma Inda ta baro ta zauna tasake saukoda 'yar ta bude ruwan ta ringa
zubawa a murfin robar tana Bata.

Ruwan ma batasha saidai wasu sun shiga cikinta kadan...

Kuka jaririyar keyi sosai Wanda ya qarasa gigita Hadiza..
Batasan ya zataiba sbd kanta zazzabi da ciwone Mai qarfi a jikinta.

Gabanta radadi yake Mata sbd qarin haihuwa da rashin ruwan zafin gasa gurin ga
doguwar tafiya cikin azabar Rana Dan haka itama take a gigice.

Kukan 'yar yasa Dole tabar gurin ganin hankalin jama'a yafara yawa kanta.

Cikin wasu mabarata dake gaba kadan bakin wasu super market taje ta zauna tana sake
fama da Yar dake kuka har lokacin.

Nanma bata tsiraba sbd anfara Mata kallon zargi da 'yar
Silalewa tayi tabar gurin kafin ayi Mata dukan Satan 'ya takama hanya taci gaba da
tafiya gashi duhun dare yafara Dan har anfito sallar magriba.

Tafiya Mai Dan tsayi takuma Yi taji bazata iyaba sbd radadi da azabar da tsakiyar
cinyiyinta ke Mata,

Azabar datakeji tafi Mata naqudar haihuwar datayi sbd gurin ya goge sosai sbd
tafiya Dan haka tasamu wasu shaguna da Yan gudun hijira suke ta zauna daga can gefe
itama.

Ruwan robar data siyawa yarta itama taciro daqyar ta iya karban kadan ta shimfida
zaninta agurin ta kwanta tana fidda numfashi daqyar jikinta na rawar sanyi.

Babu Wanda ya lura da ita sbd suma kowa ta kansa yakeyi Bata wani ba dan kowa
agurin abin tausayine.

Yarta na dungule cikin jikinta itama tayi bacci.

Hadiza Batasan inda kanta yakeba sbd kusan suma tayi saida sanyin asuba da kukan
yarta ya dawo da ita
Ta bude idanuwanta daqyar tana Neman tashi Amma takasa.

Daga kwancen ta sake rungume jaririyarta ta Ciro nono tasaka Mata a Baki.

Ana Gama sallar asuba duka mabarata da Yan gudun hijira dake gurin suka fara
watsewa sbd baa barin Zama gurin da daddare kawai suke zuwa su kwanta da gari ya
waye kowa yatafi gurin bara.

Daqyar ta iya daddafawa ta tashi tabar gurin
Tafiya kadan tayi tasamu guri ta zauna sbd bazata iyaba.

Anan gurin ta Rana ta fito ta sameta
Mutanen dake wucewa suka fara Bata sadaka sbd sun dauka Bata takeyi

Dayake tana buqatan taimakon ana bata haka ta ringa karba har Allah yasa ta hada
400 ta tashi daqyar ta siya ruwan zafi gurin me shayi ta Sha na hamsin ta siya wasu
na hamsin din ta wankewa 'yarta jiki ta gogeta ta maida Mata kayanta da daudarsu da
komai.

Har yamma tana garari a hanya Dan haka tasake komawa gidansu salisu
Hajiyarsa Bata tausayawa mataba tayi Mata korar wulaqanci harda munanan kalamai
akan 'yarta Dan haka ta sake komawa Inda ta kwana jiya anan ta Kuma kwanciya.
Washe gari ma haka ta sake zuwa gidansu salisu a karon karshe hajiyarsa tayi Mata
mummunan gargadin sake zuwa tareda tabbatar Mata da har abada bazasu karbi shegiyar
data haifaba amatsayin 'yar salisu.

Ranar tayi kukan data jima batasamu tayiba sbd maganganun hajiyar dakuma ciwo Mai
tsanani daya sakota gaba da 'yarta.

A ranar ko bacci Bata samu tayiba a zaune ta kwana tana kallon yarta wadda da alama
sanyi ne yayi mummunan shigarta tana numfashi daqyar.

Gabaki daya duniyar tayi mata zafi,
Qunci da nauyi takeji a zuciyarta Mai tsananin gaske..

Washe gari da safe data samu qarfin jikinta ta tallaba takai jaririyarta wani
qaramin asibiti datagani a hanya.

Karon farko ana dubata akace Mata 'yar batada lfy sosai,
Zuciyarta Bata bugawa yanda yakamata hakama sanyi na Neman shigarta.

Gado aka Bata Amma sbd batada ko kudi suka korota ta fito tana bin hanya Ahankali
idanuwanta na tsiyayar hawaye.

Yau Bata samu gurin kwanciyaba sbd yan hijirar dasuka qara yawa Dan haka Nesa dasu
sosai tasamu ta kwanta.

Hankalinta a tashe yake da Inda ta kwanta din sbd itace a nesa qarshe sosai
Wasu irin sauro da cinnaku suka ringa cizonta tanaji Amma Bata ko iya motsawa sbd
zuciyarta data Gama mutuwa.
##MAMUH#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/29, 11:09 PM] MG: *_39_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Koda garin ya waye daga ita har 'yarta gabaki daya jikinsu kurajen cizan sauro sun
bayyana ajikinsu ita hardana cinnaku dasukai Mata kaman Mai wani ciwon take
fuskarta ta kumbura.

Tashi tayi ta nufi Inda suke gyara jikinsu ta gyara ta fito ta miqa hanya goye da
'yar tata.

Kwananta hudu agurin aka rarraba musu kudin sadaka a gurin akan kowa yabar gurin
tana karban nata ta tattara tsumman kayanta ta nufi asibiti takai 'yarta data fara
nisa.

Kwantar dasu akai tareda sakasawa 'yar oxygen Wanda ya cinye kudin nata batareda
ansamu na siyan sauran maganiba.

Daqyar takai safe cikin tashin hankali Mai tsanani da qaqa nikayi sbd jikin 'yar
jaririyarta daya sake gabaki daya.

Rashin Imani da rashin tausayin asibitin haka suka sallameta sbd rashin magani da
rashin kudin siyansa ta rungumo 'yarta ta fito tana hada hanya.

Yau kam komai yasake yimata tsananin da takejin mutuwa take buqata Ido rufe.

Uwarta da ubanta da salisu takeson bi Ido rufe sbd ta huta da qunci da baqin cikin
duniyar datake ciki.

Kuka aranar tayisa har idanuwanta basa gani sosai sbd kumbura.

Tahau titi rungume da 'yarta wadda take tsoron dubawa ko ta mutu ko tanada sauran
Rai.

Mutuwa take Kira take Kuma fata sbd Babu Inda takejin sassauci a wannan rayuwar.

Wani azababben ciwon gaba take fama dashi da ciwo ciki Mai tsanani,
Ta bangare daya qwaqwalwarta tafara kasa daukan tashin hankalin da masifar datake
ciki Dan haka wunin ranar attempting kashe kanta kawai takeyi Amma tsananin qaunar
datakewa yarta Yana hanata idan ta kalleta.

Tamkar mahaukaciya tafara komawa sbd taba qwaqwalwarta da abin yafara Musamman
mummunan infection din daya shigeta sosai sbd rashin kulawa da gurinda ta Haihu.

Tun tana iya controlling kanta akan yanayinta dayake son juyar da qwaqwalwarta
haryazo tafara tsoraran yanayinda jaririyarta da itama kusan Rai ne kawai ya rage
Mata Zata shiga idan wani Abu ya sameta.

wani masallaci takai 'yar ta ajiye Zata gudu tabarta ko zaa samu Wanda zai
tallafeta Amma saita kasa barinta agurin tadauketa tana hawaye tana jujjuyar dakai
tabi hanya tana surautai ita kadai.

Batasan ya akaiba sai gata kwatsam takai kanta hanyar Tasha tana tafiya.
Kaduna ne?

Ina zuwa ne?

Kano ne?
Katsina ne?

A kunnuwanta kalmomin ke sauka suna sake yamutsa qwaqwalwarta...

Jikinta rawa yakeyi sosai kanta na sake juyawa sosai.

Ahankali sama sama takejin cikin nutsuwa wani yayi magana a bayanta.

Assalam alaikum,
Malama Zan wuce ko
Zaki Dan matsa.

Waiwayowa tayi da sauri a firgice tareda kallon Mai maganar.

Saurayine matashi Wanda zatai qani dashi bamai tazaraba sosai.

Sanye yake cikin qananun Kaya Riga ash da wandon jeans black.

Cikin sauri Dan tashar masu mota ya qaraso Yana daka Mata tsawa da cewa"

Dalla matsa ki wuce daga Nan
Kinzo kintare hanya
Idan bara zakiyi ki matsa can.

Yallabai Kace gombe Abuja ne ko?

Kallonsa matashin yayi kafin ya kalli Hadiza data Matsa gefe ta rabe rungume da
abinda yake sakaran 'da ne sbd yanda ta rungume zanin cikeda so da shauqi.

Hannu ya saka aljihunsa ya Ciro Dubu daya ya miqa Mata cikeda kulawa batareda yace
komaiba.

Hannu ta miqa a hankali ta karba tareda kafesa da Ido tana zuba godiya Kuma takasa
tafiya.

Cikin qaguwa ya kalli masu lodin motar yace"

Saura mutum nawane motar tacika hanyar kunsanfa bawani kyaune da itaba.

Yallabai Saura mutum uku motar tacika.

Muje zan biya kudin sauran gurin.

Angama ranka yallabai.

Hadiza dake rakube tanajin haka sai kawai tasamu kanta da biyo bayansa tafara
kokarin Shiga motar sbd Jin zaa biya koba komai gwara tashiga duniyar tunda hakane
qaddararta.

Kokarin hanata shiga motar direba yafara yana cewa"

Ke tsaya, tsaya
Ina zaki?
Wane gari Zaki?
Abuja" ta furta Kai tsaye muryarta na 'dan rawa.

Ina kudinki na mota?

Waiwayowa tayi ta kalli gefenda matashin yake zaune cikin nutsuwa Yana duba wayar
hannunsa.

Ganin tana kallonsa ya fahimci batada kudin motar Dan haka yacewa drivern tahau
gurin mutum daya cikin kudin mutum biyu daya biya.

Kasa kallonsa tayi bare tasake Masa godia saima sauke kanta datayi qasa tana sake
rungume jaririyarta.

Hanya aka dauka aka fara tafiya Mai nisa kowa yayi tsit a motar Yana aikin gabansa
masu bacci Kuma nayi.

Ahankali ahankali idanuwan Hadiza suke cikowa da hawaye tanajin wani irin
masifaffen ciwon Kai da zabar ciwon ciki.

'yarta take ji,
Ita take tausayi ba kantaba,
Jin kanta na neman juyewa yasa tafara jin kaman tace a tsaya ta sauka.

Yanayin yanda take sake qanqame babynta yasashi Dan dagowa ya kalleta dakyau yaga
tarin tashin hankalin dayake ciki kafin ya maida kallonsa kan babyn cikeda kulawa
yace"

Ki Dan sassauta riqon
Kina matse babyn sosai Inaga.

Da sauri kaman qaramar yarinya tayi saurin sassauta riqon tareda bube jaririyar
gabaki daya Dan Tasha iska.

Wani irin mamaki da firgici ne ya kamasa ganin babyn wadda alamun rashin lafiya
sosai da yin nisa ya bayyana atareda da ita,

Gabaki daya babyn yunwa tagama kamata tako ina.

Dauke kansa yayi daga kallon jaririyar sbd zuciyarsa bazata iya jurewa kallontaba.

Tafiya suka cigaba dayi mai nisa da gudu..
Guri biyu aka tsaya siyan abinci Kuma ya siya Mata yabata sbd lurada akwai yunwa
tareda ita.

Duk abinda ya siya Mata ya bata bataciba suna jikinta dunqule sbd bazata iya ciba
ita kadai tasan tsananin halin azabar datake ciki.

Daga Nan Basu sake tsayawaba a hanya suka cigaba da zuba gudu a hanya.

Qarfe Tara da mintuna arbain da takwas suka isa birnin tarayya.

Kowa fitowa yayi daga motar yana haramar daukan kayansa ya wuce.

Daga shi sai jakarsa dake rataye a kafadarsa ya fito Yana sake saka Kiran Wanda
aka aiko daukansa daga gida.

Ahankali Hadiza ta tako gefensa ta kallesa qafafuwanta na 'dan yin rawa.
Tsalle zuciyarta keyi ga abinda zuciyar tata ke ingizata ga aikatawa.

Jin takeyi zuciyarta ta kwanta data barmasa 'yarta ta gudu sbd yanada tausayi da
Jin qai Dan kuwa ita batada tabbacin zatakai labari ayanda takejin azaba da radadi
cikin jikinta.

Bazataso wani Abu ya sametaba 'yarta ta gararanta...

Jin mutum kusa dashi yashi juyowa da Dan sauri sbd ya Dan firgita.

Kallonta yakeyi da mamaki sosai batareda yace Mata komaiba.

Ganin kallon dayake Mata yasata kallon 'yarta cikin kokarin daidaita kanta tace"

Nagode sosai Allah yasaka maka da Alkhairi.

Amin" kawai ya iya furtawa Kai tsaye Yana cigaba da wayarsa.

Yana aje wayar drivern ya tura aljihun jeans dinsa drivern gidansu yace Saura kadan
ya iso.

Jakarsa ya juyo zai dauka daga qasa gefensa idanuwansa suka sauka kan zani kan
jakar tasa.

Da sauri ya waiwaya Babu kowa gefensa da bayansa.

Sake jujjuyawa yayi Yana Raba idon matar data bar Masa zanin.

Jakar ya riqe zai dauka ya watsar da zanin agurin sai zuciyarsa ta kasa Dan haka
yakai hannu kawai zai janye zanin yaji alamun Abu aciki

Batareda ya taba tunanin ganin komaiba bare 'dan mutum ya bude zanin aikuwa yayi
Ido biyu da babyn.

Zaro Ido yayi da sauri tareda mayarda zanin ya rufe babyn zuciyarsa na rawa.

Da sauri tafara waigawa

Please Login or Register in order to submit comment