ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shikam zai
ringa zuwa akai akai sbd huldodinsa wasu dasuke can.

Daga Nan gidansu har familynsu Anty Hafsat da dangin CM Babu Wanda baya cikin farin
ciki da murnar wannan biki sai Mimi wadda baqin cikin datake ciki ya hanata sukuni
sbd bazata iya kallo Hafsat tasamu shiga jikin zuriar AA MAJEED ba fiyeda ita Dan
kuwa ko yanzu akan wannan auren ba qananan arziki taketa samuba daga AA MAJEED
harma da umma yaganah datake Jin Hafsat tagama Mata komai tunda tayi sanadinda
Inayarsu tasamu kamilallan miji dayake sonta sosai.

Safnah kuwa Bata wani damu da damuwar da Mimin take cikiba sbd tadauka kishi ne
irin Wanda Allah ya halitta a zuciyar Mata shine takeyiwa Anty Hafsat na ganin
tasamu shiga a Inda itace taso tasamu shigar.
Neesah kam Dole da qarfi da yaji tazo Nigeria tareda momy Dan haka Murna a gidan
takuma Zama sabuwa.

Ta bangaren Dr Abdul son Inayah Bai taba raguwa acikin ransaba saima Jin dayake
kaman zuciyarsa bazata iya daukaba ganin Inayah ta aura wani tabarsa,

Amma iliminsa na addini Dana bokon daya kedashi Bai barsa ya qullata komaiba saima
nesa nesa daya Dan farayi da Inayah sbd zuciyarsa bazata iya cigaba da daukan
kishinta Mai tsananin gaske dayake ji Amma Inayah Bata iya nesa dashi sbd yariga
yazama tamkar wani babban bangare na rayuwarta a Nigeria,

Tayi sabo da shaquwa Mai tsananin gaske dashi da har kaunarsa ta ginu a ranta
amatsayin aboki Kuma Dan uwan Dan haka idan yaqi kiranta itace da kanta take
kiransa.


*****Bikinta Saura sati uku Dr Abdul yabar Lagos yakoma Adamawa
Farko hankalin Inayah din yatashi sosai da barinsa Amma hidima da shaanin biki yaqi
barinta maida hankali sosai kan tafiyar tasa
Sai kawai tabarshi akan idan angama bikin Zatai magana dashi.

Anfara gyaran Amarya INAYAH tako Ina,
Umma yaganah baji ba gani ta dauko masu gyara daga maiduguri ana gyaran Inayah ta
ciki da waje.

Anty Hafsat ma ba Zama kusan kullum saitaxo gidan da nata kayan gyaran.

Neesah dai kam tana gidan sbd suna sauka Abuja can gidan iyayen momy kwana biyu
kawai tayi ta biyo jirgi zuwa Lagos Dan haka duk sauran shirye shiryensu tare suke
yinsu
Ko Safnah ma kusan kullum gidan take wuni.

Umma yaganah taje maiduguri kusan kwananta biyar acan daqyar daqyar ta iya samun
wasu daga cikin 'yan uwanta Amma sauran kam duk sun rasu wasu Kuma ba'a San Inda
sukeba kaman ita.

Wainda ta sama cikin Yan uwan nata bama irin Yan uwan kusa bane
Kawun malam mijinta ne da iyalansa ta samu sunkoma kauyensu da aka watse sai wasu
daga cikin amininan iyayenta saikuma kishiyar mahaifiyarta da itama ta tsufa sosai.

Tayi musu Sha Tara ta arziki tabaro tadawo maiduguri tasake kwana daya tabi jirgi
Takoma Lagos.


*****A daren da zaa saka amarya lalle saqon wani mugun labarin ya isowa umma
yaganah ta hanyar Mimi.

Rigimace ta barke a gidansu faruk da iyayensa da shi harma da mahaifin dadynsa..

Wannan wata babbar maganace data girgiza umma da ita kanta Inayah sbd basu taba
tsintar wannan mumunar kalmarba sai ranar.

AA MAJEED ya Haifa Inayah bada aureba,
'yar gaba da fatiha ce...

Tashin hankali Mai girman gaske umma yaganah da Neesah suka Shiga sbd kalmar tayi
Muni da yawa.

Inayah kuwa zuciyarta ce taji tana harbawa da sauri da qarfi
Wani irin zufane masu dumi suka ringa tsatsafo Mata.

Dafa kujera tayi ahankali ta zauna tana Jan numfashi da sauri sauri.

Ruwa zubbi taje da gudu takawo tabawa Neesah dake Kiran sunanta da Dan qarfi tana
cewa"

Inayah karki daga hankalinki please
Wannan labari ne fa kawai aka kawo.

Karban ruwan tayi takai bakinta da Dan sauri ta kwankwada ta miqawa zubbi cup din
tana miqewa tsaye tace"

Faruk yasan wannan zancen shirme ne,
Ina ruwansu data yanda mahaifina ya haifeni,
Idanma Ni shigeyarce an haramta auren shegu ne?
Tunda Ina tareda mahaifi ai banajin zan karba suna kokuma bin layin shegu..

Umma yaganah ma cikin damuwa da tashin hankalin datake dannewa tace"

Menene Kuma na wannan zancen ma Kuma yanzu?
Yarinya da ubanta Dan Allah bamason janye janye da wulaqanci,
Waye yafara kawo wannan zancen?
Wane Mara hankalin ne zai kawo Mana fitina muna shaaninmu cikin Jin Dadi da farin
ciki?

Kuka sosai anty Hafsat keyi agaban Umma yaganah din sbd batama San Mimi tafara kawo
musu zancen basu yardaba sai yanzu datazo da kanta sbd Al'amarin ya tsananta acan
familyn Anata rigima da tashin hankali,

Mahaifiyar faruk da mahaifiyar dadynsa sunyi rantsuwar bazaai aurenba Dan faruk
bazai aura Inayah ba sai mahaifinta ya sanar dasu Gaskiar wannan zancen da aka kawo
musu.

Dadyn Faruk yasan saidai afasa auren har abada Amma AA MAJEED bazai zauna yiwa kowa
bayaniba Dan a aura 'yarsa
Kai tsayema za'a samu babbar matsala dashi Dan kuwa suna shegenta Masa 'ya ne Kai
tsaye da kalamansu.

Shi kansa Alhaji baba kakan faruk din Bai wani goyi bayan faruk da mahaifinsaba sbd
ganin kaman harda kwadayin suna da arzikin AA MAJEED sukeson rufe Ido su hada zuria
dashi koda da gaske Inayah din 'yar gaban fatiha ce.

Dayake maganar a tsakanin mata tafara har lokacin Abbi baisan abinda yake faruwaba
dagashi har CM Dan haka su sun Riga sun Gama rabawa jama'arsu katikan daurin aure
da invitations na special lunch da zaai bayan daurin auren sbd abokanan huldodinsu
Christians da turawan dake Nan tunda su ba daurin aure suke zuwaba.

Wasa Wasa saiga zance dai yazama Babba Dan kuwa Dadyn Faruk yasamu CM da zancen har
gida sbd bazai iya tunkarar AA MAJEED ba,
Ko daya girma MAJEED sosai yanajin kunya da nauyinsa yaje Masa da maganar Dan haka
yasamu CM da zancen.

Sosai cm ya girgiza da wannan mugun sakon, dan haka baiyi saurin isarda sakonba
saiya samu Alhaji baba dasu hajiyar yayi kokarin fahimtar dasu illar abinda zaayi
din Dan tamkar tozarcine Kuma wulaqanci ga AA MAJEED da 'yarsa ace zaa tambayesa
yanda ya Haifa yarsa.

Sam kasa fahimtar juna sukai dasu dashi Dan haka baida wani zabi sai sanarda AA
MAJEED halinda ake ciki.

Shiru yayi bayan yagama sauraron bayanin CM cikin nutsuwa.

Bai bayyanarda bacin Rai ko fushiba saidai kam idanuwansa wannan karon sun
bayyanarda tsananin 'dacin daya Kama zuciyarsa.

Ba'a taba cin fuska ko cin mutuncin Martabarsaba sai wannan karon,

Ko alokacinda yake talakansa baida girma ko qima a idon mutane tunda shi talakane
baa ci zarafin mutuncinsa kaman wannan lokacinba.

Idanuwansa ya Dan juyo ahankali ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya Nemo numbern
umma yaganah ya saka Kira.

Zaune suke gabaki daya gidan yanzu Murna na Neman komawa ciki tunda wannan muguwar
magana ta bayyana.

Tashin hankalin da Faruk yake cikine ya tabbatarwa dasu Inayah Al'amarin ya
girmama,
Babban tsoro da fargaba tareda tashin hankalinsu shine idan zancen yaje gaban Abbi
yanda zai karbesa.

Sbd farin cikin Inayah sunsan zai iya komai hakama sunsan bazai taba bawa Wainda
suka shegantata suka alqantata da 'yar gaban fatiha aurentaba,
Zancen na zuwa gabansa sunsan maganar bawa su faruk aurenta Kuma ta mutu saidai
wani ikon na ubangiji.

Hakan yasa Kiran abbin na shigowa wayar umma yaganah duk jikinsu yakuma sanyi sbd
sunsan cm na gidan tun dazu suna magana.

A natse ta dauka tareda sallama a sanyaye tace'"

Naam ABDULMAJEED.

Umma kuzo Palo akwai sako.
Ina Inayah?

Gatanan kwance tana fama da Dan ciwon Kai ne.

Kizo harda ita din.


Yana fadar hakan ya kashe wayar a natse tareda ajiyewa Yana cigaba da sauraren
amininsa CM dake fadar rashin dattakon dasu Alhaji suka nuna akan wannan Al'amarin
Magana dai gatanan irinta mata Amma sun biyewa zancen banzan.


Shidai Bai iya cewa komaiba sbd zancen yazo Masa ne a bazata,
Bai taba tunani ko sanin wani zai iya samun guts na aibata 'yarsaba.

Kuma aibatawa mafi muni bafi tozarci Dan kuwa Saida suka kammala komai na ya'da
maganar aure ace an fasa.

Ta wani bangaren Inayah din yakeji,
Tanada rauni sosai
Bata iya saka damuwa ka shiga baqin ciki ba sbd sosai take shiga damuwa,
Da qarancin shekarunta ace itama wannan shine Karo na biyu ana neman aurenta ana
fasawa.
Tabbas su Alhaji baba sun tozartasa
Tozarta mafi muni.

Sallamar umma yaganah ce tasashi Dan rufe Ido ya bude batareda ya juyo ya kallesuba
Dan yasan dukansu Babu Wanda yake cikin yanayi Mai kyau sbd daga Inayah din har
umma yaganah baisan Wanda yafi wani qulafucin aurenba,
Ya rasa meyasa suke tsananin son auren tunda komai lokaci ne dashi.

Inayah na ganin yanayin Abbinta tasan maganar fasa aurence zaai Dan haka ta fashe
da kuka ahankali tana kwantawa jikin umma yaganah da itama nata idanuwan sukai
jajir.

Har lokacin Bai waiwayo ya kallesuba saidai cm ne yafara bayani cikin damuwa da
rashin Jin Dadi yace"

Umma nasan dai kinji bayanin abinda yake faruwa daga bakin Hafsat,

Iyayen faruk dai basu amince da auren faruk din da Inayah ba akan wasu dalilansu da
Babu amfanin ambatarsu yanzu,
Dan haka ayi hakuri maganar auren dai yanzu abarta babuta saidai bamusan abinda
Allah zaiyi agaba ba,
Faruk idan mijinta ne Inshallah duk wainnan tashin hankalin da maganganun zasu
wuce.


Inayah ya kalla cikeda tausayi da kulawa yace"

Kiyi hakuri kinji Inayah
Inshallah Zaki samu mijinda yafi Zaid da Faruk,
Wannan fashin auren wata jarabawace da ubangiji ne kadai yasan tanadin da yayi Miki
a gaba.

Kallonta Abbi yayi da idanuwansa dasuka sauya cikin nutsuwa da Jin zafin abinda
akaiwa 'yarsa yace"

Karkiyi kuka ki dauka hakan amatsayin wani gwaji daga Allah.

Umma yaganah ki kula da ita sosai kada ta saka Al'amarin aranta tajawa kanta damuwa
ko wani ciwon.
Allah ya zaba Mana abinda yafi Zama Alkhairi.

Amin" suka furta CM da umma yaganah
Inayah kam kuka takeyi sosai Wanda kusan Bata taba irinsaba.

Daqyar ta iya Isa dakin umma ta zube jikin umman Yana Jan numfashi zuciyarta na
harbawa da qarfi.

Neman yankewa numfashinta keyi da gudu Neesah taje takawo ruwa suka Bata suna Mata
firfita duk da sanyin AC daya cika dakin zufa takeyi sosai tana Jan numfashi ga
hawaye nabin fuskarta.

Hankalin umma yaganah da Neesah harma da Anty Hafsat da Safnah da mimi dake gidan
tashi yayi ganin yanda Inayah take cikin yanayin ban tausayi ga hawayen idonta
dasuka qi tsayawa.

Mimi datai wannan mummunan qullin Saida jikinta yayi sanyi tashiga damuwar tausayin
Inayah duk da batai Dan cutatar da Inayah ba tayine Dan lalata Hafsat.
Jiki amace suka watse suka koma gida aka bar ssu umman da Inayah suna fama da ita.

Abbinta dayasan hakan Zata kasance da ita da wuri ya Kira likita akazo gida aka
dubata
Harda drip akai Mata qari sbd tashiga tension sosai na Al'amarin.
##MAMUH#
#RIBA BIYU#
#AYSHATOUH INAYAH#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/14, 1:12 PM] MG: *_23_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da zazzabi ta kwana sosai a daren Dan haka a dakin umma yaganah ma ta kwana sbd
tasamu kulawa da ita yanda yakamata Neesah ma kasa kwana tayi daki ita daya ba
Inayah tadawo dakin umman suka kwana.

Washe gari ba laifi ta tashi da lafiyar jiki saidai rashin ta zuciyata,

A sanyaye take gabaki dayanta,
Damuwa da 'dacin zuciya harma da baqin ciki sune takeji mamaye da zuciyarta tako
Ina,

Ga faruk tun jiya sai kiranta yake hankalinsa ya tashi dajin batada lafiya Amma
bazata iya daga kiransaba ayanzu Dan kukane kawai zatai tamasa,
Sun shirya tareda tsara yanda zasu gudanarda rayuwarsa da tsantsar so da kaunar
juna,
Daga ita har faruk suna tsananin son juna sbd tako Ina suna ganin sun dace da
rayuwarda suke so da burin gudanarwa a rayuwar aure.

To menene yasa iyayensa zasu datse musu buri da kaunar junansu?

Meyesa zasu aibatata Rana tsaka Dan kawai cin zarafi ga mahaifinta
Dan kuwa wannan da gani ba ita sukeson tozartawa da wulaqantawaba sai
mahaifinta...sai dai kuma duk abinda zaa tozarta ko cin zarafin mahaifinta fita
ranta yake.

Tana son faruk kusan ma fiyeda yanda taso Zaid Kuma cire sonsa aranta zaiyi Mata
wuya sosai amma Kuma Dole Zata dauki dangana kodan kada acigaba da cin mutuncin
Abbinta da maganar yanda ya haifeta,

Itadai koma Yaya mahaifinta ya haifeta tunda Bai yar da itaba kokuma ya gudu
yabarta kokuma yamayi denying zamansa mahaifinta to tanason abunta ahakan,

Idanma bada aure ya haifetaba Bata buqatan sani tunda barna ce to Riga ta afku ba
gyara acikinta,
Hakama dawo da zancen kokuma tambayarsa akan Gaskiar zancen kaman cin mutuncin
mahaifintane zatai bayan Babu ta Inda ya gaza a matsayinsa na uba Wanda ya maye
gurbin uwa.

Ko danginsu da kakanninta Bata sake tambayaba sbd tsananin dokar daya kafa Mata
akan hakan shiyasa Bata sake shaawa ko marmarin tambayaba.
Abu daya tasani takuma tabbatar shin,
Koma menene ya Raba mahaifinta da mahaifiyarta harma da danginsu ba abune Mai
dadiba,tashin hankaline.




****Bayan kwana biyu da fashin auren jama'ar da suka sani sunyita yawo da zancen
Wanda har gurin abokan aiki da huldarsa zancen yaje na cewa bada aure ya Haifa
yarsaba,

Da yawa basu wani damuba sbd harkace data shafesa bawai aikinsaba
Haka zalika dukiyarsa da matsayinsa ya hana kowama daga zancen saidai mamaki da la
shakka mutane sunyita fada.
Inda ma zancen yayi sauki bai wani shiga media ba sbd a Nigeria din ba kowane ya
sansaba tunda baa qasar yake zauneba,

Manyan mutane abokanan huldodinsa ne kawai suka Sansa sosai sai jama'ar da baa
rasaba.

AA MAJEED mutum ne da Baya damuwa da Al'amarin kowa sai Wanda ya shafesa,
Kuma Sam Baya damuwa da abinda kowa zai fada akansa Dan Bai taba damuwaba sbd yasan
iya bayan fage ne bazaa iya zuwa afada a gabansaba sbd iskancinma gurin yinsa ake
samu
Ko su Alhaji baba duk wannan abin daya faru basu iya zuwa sun fada a gabansa ba sbd
kwarjini da cika idon da Allah yayi Masa akan mutane Dan haka shima baiga amfanin
nemansuba ko ji daga garesu tunda sun Kai sakon gurin Aminsa CM Kuma ya isar musu
da sakonsu ga AA din,

Sun dauka zaizo ya rokesu akan janye maganar tunda sunsan Babu abinda bazai iyaba
akan farin cikin 'yarsa saigashi sunga sabanin hakan,
Abinda basu saniba da akan wani dalilin ne suka soke auren zai iya nemansu a
sulhunta Amma Kuma har abada bazai iya bawa Wanda ya sheganta asalin 'yarsa aurenta
ba Dan hakan take ya toshe duk wata sauran hanyar dazata ma tunatar da Inayah
wannan Al'amarin.

Private hospital din da aketa kokarin budewa da sunanta aka sake bada himma sbd ko
aikin tafara sosai yanda hankalinta bazai zauna akan damuwar matsalar da aka
samuba.


Dole ta sakawa kanta dangana da tawakkali sbd ganin Abbinta daya tattara maganarsu
faruk ya watsar duk da tasan abin Yana damunsa tunda shi ubane da aka fasa auren
yarsa Rana tsaka saidai Kuma bayyanarda damuwar batada wani amfani shiyasa basa
gane Inda yanayinsa yake dosa.

Umma yaganah ma haka suka hakura suka dauki dangana suka cigaba da adduar Allah
yakawo Mata wani mijin yasa hakan shine yafi Zama Alkhairi.

Yanzu Bata wani fita asibiti sbd baa kammala tasu asibitin ba gashi Dr Abdul ma
Dole yanzu zai dawo yaci gaba da aiki a asibitin tasu idan angama tare.

Da labarin lalacewar auren ya samesa baiji dadiba sosai sbd tunanin halinda Inayah
Zata shiga Dan haka Saida ya matse ayyukansa yazo Lagos din hankalinsa ya kwanta.

Da farko Inayah na ganinsa daya iso gidan nasu Batasan lokacinda ta fashe Masa da
kuka ba tana sake maimaita Masa abinda yafaru.

Hankalinsa Bai tashi da abinda ya faru dinba kaman yanda hankalinsa yatashi da
kukan datakeyi Wanda taketa riqewa da dannewa cikin ranta sbd gudun daga hankalin
umma yaganah da Abbinta,

Amma tsakani da Allah har cikin ranta tanajin tsananin quncin rashin faruk Wanda
gabaki daya yanzu idanma yakira bayan kuka Babu abinda take Masa harya daina
kiranta sbd kukanta ba qaramin daga hankalinsa yakeyiba,

Kukanta zai iya sakasa bijirewa iyayensa ya dauketa suje suyi aurensu wani gurin
Amma Kuma hakan ba qaramar fitina zai tadaba dan kuwa Yana shakkar mahaifin Inayah
din sosai tako ina.,
Bayason ya jawa iyayensa 'daurin da zai taba tsufa da mutuncinsu Amma badan hakanba
Babu abinda zai hanasa guduwa da Inayah wani gurin a daura musu aure.

Hankalin Dr Abdul ya matuqar dimauta da kukan Inayah wadda yakewa wani irin
boyayyan son da yafara fin qarfin qarfinsa,

Shi mutum ne Mai tsananin zurfin ciki da iya danne Abu shiyasa son nata yake boye
cikin ciki da zuciyarsa Amma irin son dayakejin yanai Mata a yanzu bazai iya barin
wani ya auretaba koda zaaita saka ranar auren nata ana warwarewa har sai ranarda ya
sameta.

Ita kanta tanajin Dr Abdul cikin ranta sosai Amma ba amatsayin masoyiba sai
matsayin aboki wanda batada tamkarsa bayan Neesah.

A gidan ya qarasa wuninsa Yana rarrashin Inayah shida umma yaganah daketa qara gode
Masa kan damuwarsa dayake nunawa sosai akan Inayah din.

Yana gidan Abbi yadawo Dan hakama Dole atare dasu yaci abincin dare dukkaninsu a
dining.

Dr Abdulsamad yasamu shiga sosai agurin Abbi Wanda da farko harsu Inayah din sunyi
mamaki sosai tunda sunsan shi mutum ne Mai wuyar sabo da mutane,
Bakowa yake yarda yashiga jikinsaba sosai
Amma Dr Abdul lokaci qanqani yashiga ran abbin ya kwanta Masa sbd sanin kansa
dakuma qaunar Inayah Mai girman gaske daya hanga atareda Dr Abdul din.

Ya jima Yana fira agurin abbin kusanma duk akan aikin asibitin ne nasu da ake gab
da kammalawa,
Sai dare yabar gidan yatafi lokacin INAYAH ta jima da yin bacci sbd yanzu Bata wani
jimawa take bacci.

Neesah Takoma Abuja gurin momy datazo ta jajanta musu suka koma tareda Neesah din
Abuja.



******Ahankali Dr Abdul ya Dage sosai gurin mantar da ita faruk dukda da Kamar wuya
Amma Kuma dagewar tasa da tsananin kulawarsa akanta yafara cin nasarar hakan Dan
yanzu ba laifi tacirewa ranta faruk din ta hakura saima hankalinta data maida sosai
akan Dr Abdul din kan aikinsu.

Faruk yakoma Malaysia qaro karatu Dan haka yanzu wayar tasu ma kusan kwata kwata
sun daina saidai idan sunga juna a social network.



***Lokaci ya 'dan sake ja son da Dr Abdul ke Mata yafara juyewa zuwa wani Al'amarin
daban,
Yanzu gabaki daya ya sauya akanta yakoma kaman ba Natsatsen Dr Abdul din dakowa ya
saniba,

Wani irin so Mai zafin gaske yake Mata Wanda harya fara bawa umma yaganah tsoro
gashi dai Bai fito yafada Mata Sonta yakeba Amma dai kowa ya kallesa yasan yagama
zautiwa a Sonta Dan ko kallonta idan yanayi mantawa yakeyi da kowa.

Ita kanta Inayah lokuta da dama tsananin kulawarsa da abubuwan dayake Mata na kauna
tsoro da shakka suke Bata Amma har lokacin batajin tana Masa son soyayya saina
aboki,yanzuma ya wuce abokinta ya Zama wani bari na rayuwarta.

Abbinta ma ya lurada halinda Dr Abdul yake ciki akan Inayah,

Baida matsala akan bawa Dr Abdul aurenta Amma Kuma Yana shakkar irin son dayake
Mata zai iya cutatar da ita akan kishi kokuma cutatar da duk wanda zai shiga
tsakaninsa da ita Dan haka son shima yake sakasa shakku,
Ta wani bangaren Kuma tausayinsa yakeji Mai tsanani sbd son mace irin haka kaman ba
so bane ciwo ne.

Anty Hafsat koda aka fasa auren Inayah da Faruk Bai taba alaqarsuba saima sake
shaquwa dasukai Dan haka yanzu tazama antyn Inayah tamkar wata qanwar uwa ko qanwar
ubanta
Komai na Inayah tasani da ita suke shawara so da dama
Hakama Umma yaganah ta zamar musu tamkar uwa a gurinta suke wasu shawarwarin.

Anty Hafsat din batai qasa a gwiwa ba takuma hada wani qaninta dasuke uba daya da
Inayah.

Sadeeq qanin anty Hafsat yayi karatun likita shima anan Lagos yatashi Kuma sosai
yakeda abun kansa saidai yayi irin wayewar datai qazanta shima Neman Mata yakeyi
sosai Amma Kuma bazaka kallesa kace yanayi dinba Dan kuwa a kamile yake a
zahirinsa.
Ba laifi ya Dan fara shiga ran Inayah saidai Bata wani zura da yawaba sbd tafara
Jin shakkar Al'amarin maza da aure.

Shima dagewa yayi da soyayyarsa da kulawarsa harma da alqawuransa yasamu yashiga
zuciyar Inayah din.

Wannan karonma ba Bata lokaci ya aiko iyayensa da maganar aure.

Abbin yaso su saurara Kar ayi rushing din Al'amarin Amma Dr sadeeq din ya dage da
iyayensa har abbin ya yarda.

Dr Abdulsamad kusan zaucewa yayi da wannan maganar auren Kuma Saida kusan kowa
yakusa gane halinda yashiga,

Kasa hakuri yayi sbd zuciyarsa bazata iya daukaba yabi ta qarqashin qasa ya lalata
auren ta hanyar tona asalin waye Dr Sadeeq Kuma can ma gidansu anty Hafsat akai
fitinar ta hada 'dan uwanta da 'yar gaban fatiha tunda ba uwarsu dayaba.

Wannan karon har asibiti Inayah ta kwanta ciwo sosai sbd zuciyarta tafara kasa
dauka
Abubuwan sun fara tabata sosai.

Hankalin umma yaganah da mahaifinta ya tashi sosai sbd Saida suka dangana da zuwa
Australia taga likita acan tayi jinya
Ta huta kanta ya Dan sake kafin suka dawo.

Ciwonta ba ita kadai ya taba ba harda Dr Abdul Wanda shima hankalin mahaifiyarsa
yafara tashi da wannan mummunan masifar dake tunkarota 'dan ta namiji guda datake
alfahari dashi Yana Neman samun tabin qaqwalwa akan son mace.
##MAMUH#
#AA MAJEED#
#AYSHATOUH INAYAH#
#DR ABDUL SALEES/HADIZA



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/15, 2:11 PM] MG: *_24_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Alaqarta da Anty Hafsat Bata taba girgiza ba sbd fashin auren da aka samu akaro na
biyu saima tausayin juna dasuke,

Su suna ganin qoqarinta da tausayinta akan yanda taketa kokarin hada Alkhairi Amma
Alamuran na lalacewa,

Itama tausayin Inayah takeji sosai sbd yanda Inayah duk tabi ta sukurkurce akaro na
uku da fashin auren.

Alqawari tayi bazata qara kawo kowaba ya nema auren Inayah tun basu fara tsanartaba
Amma duk mijinta Inayah Zata aura alqawarine ta dauka itace Zata jajirce su tsaya
sosai da umma yaganah suyiwa Inayah gyaran gaske da duk wainda sukaiwa kansu
hasarar rashin aurenta sai sunyi kukan baqin ciki da Dana sani.

Yanzu sosai take tsoron kula mazama kwata kwata basa ranta sunma fice Mata Rai sbd
a matsayin da raunin zuciyarta yakai aka Kuma samun matsalar rashin aurenta komai
zai iya faruwa da ita Dan haka tayi nesa da duk wata alaqar dazata Kuma jefata
soyayya.

Abbinta ma sosai yake data da taka tsantsan akan Wanda Zata Kuma samu yaanzu sbd
kaucewa hadari da damuwa,
Duk aka Kuma samun irin wannan matsalar likita ya fada Masa zuciyarta ba lallai
takuma daukan wani mummunan tashin hankalinba.

A yanayin weak heart irin na Inayah shi baimasan me zatayi da soyayya ba sbd duk
wani disappointment Yana cikin soyayya yake gani.

Haka suketa lallabawa da tunanin ta Inda wani manemin auren zai bullo mata.,

Ita dai umma yaganah fargabarta da babbar damuwarta kada Inayah din itama auren
yafita ranta kwata kwata kaman mahaifinta,

Shi namijine bazaiyi tsufa a aurenba Nan kusa barema kusan yanzu ne yake cikin
shekarun da neman aure agurinsa abune Mai saukin gaske,

Ita Kuma yanzu tanada sauran kuruciya ayanzu ne auren ya kamaceta kaman yanda take
buri da tsananin kaunar yin auren
Dan haka ta ninka roqonta gurin ubangiji Allah yakawo musu abokanan rayuwa masu
albarka suyi auren.


***Familyn Dr Abdul hankalinsu yafara tashi akan yanda ya dauko hanyar tabarbarewa
akan mace,

Duk Wanda yake Dan uwansa yasan INAYAH A MAJEED a rayuwar Dr wata babbar
jarabawace,
Abin haushi da baqin cikin shine duk yabi ya lalace akanta Amma wai Bata saniba
hakama iyayenta suna gani sunyi kaman basu ganiba,
Hakan yasa kusan duk wasu Yan uwansa sukaji basa kaunar Inayah din sbd Dan uwansu
daya Zama gwanin tausayi baida zance sai nata.

Ana cikin hakan Inayah ta hadu da wani yayan abokin Safnah.

Mimi da gudu ta ringa Jin Dadi sbd yanzu mijin ta bangarensu ya bullo Dan haka ta
zaqe tanata sake cusa zancen Ahmed din gurin Inayah da umma yaganah saidai Inayah
Sam hankalinta Bai kwanta takuma sakewa sosai akan soyayyaba Dan har yanzu akwai
sauran son faruk maqale acikin ranta.

A karon farko da zancen ya Isa kunnen Dr Abdul sanyi jikinsa yayi ya silale ya
zaune Yana sauraren Inayah din dake fada Masa da kanta.

Bai iya ce Mata komaiba saima kasa kallonta da yayi sbd kada taga yanayinda yake
ciki Dan kuwa Zata girgiza da ganin idanuwansa dasukai jajir.

Bai iya tsayawa yin aiki ba ranar sulalewa yayi ya koma gida sbd ciwon Kai Mai
tsananin gaske daya taso Masa.

Itama haka Takoma gida jiki amace sbd yanayin Dr Abdul din daya sakata damuwa.

Baiyi bacci ba ranar haka ya kwana Yana juye juyen ciwon Kai Mai tsananin gaske da
azaba,

Yasani matuqar Mai samu Inayah ba wlh zai iya haukacewa
Hauka tuburan ta gaske,
INAYAH tazamar Masa jarabawa Kuma qaddara.

Hawayene suka gangaro Masa masu zafin gaske ya miqe zaune tareda nade jikinsa waje
daya Yana fashewa da kuka Mai tausayin gaske.

Washe gari Bai iya fita aikiba sbd ciwo ya kwantar dashi
Haka Inayah tazo tareda Dr Emma ya dubasa.

Ciwon kansa Mai tsanani ne Dan haka yayi requesting suje asibiti ya dubasa acan
Amma yace AA ba buqatan hakan Inshallah maganin ma zaiyi Masa.

INAYAH ce tasaka aka kawo maganin daga asibiti yasha ya shige ya kwanta itama
Takoma gida jiki duk amace.


Kwanansa biyu a kwance kafin ya Dan warware yaci gaba da fita aiki.

Babban abinda ya bawa Inayah tsoro itada umma yaganah da Anty Hafsat shine tun
ba'aje koinaba akan maganarta da Ahmed Al'amarin ya lalace ta hanyar Kama Ahmed a
drugs case.

Haka kawai hankalin Inayah yaqara tashi sbd ta tabbatar yanzu kam koma menene yake
lalata aurenta daga gareta ne sbd shaidu da komai sun nuna Ahmed gskia mutumin
kirkine baya hulda da drugs tako Ina Dan haka akafi tunanin sharri akai Masa.

Kan kace me mutane suka fara canfa daga Inayah ne duk Wanda yazo aurenta to masifu
kala kala na zuwa garesa.

Hankalinta ya tashi sosai da wannan mugun Al'amarin har abin yaso tabata,

Abbinta kuwa take yafara Dana sanin dawo dasu Nigeria,
Da suna can duk da kila Canfi da wasu abubuwan rashin wayewa basu faruba,

A qasar waje da qabilu daban daban anan dinma basu damu da auren Wanda aka Haifa
bada aureba sbd idanma hakane shi ai ba laifinsa bane,
A taqaicema shi abin tausayi ne Musamman ga Wanda hakan ta kasance dashi Yana
musulmi.

Amma duk Anbi an hargitsa Masa rayuwa da tunanin 'ya Bayan duk tattalinsa da
kulawarsa sun qare akan 'yarsa tilo guda.

Fara tunanin maidasu Australia yayi Nan Kuma hankalin umma yaganah yafara tashi sbd
har ga Allah tafison zaman

Please Login or Register in order to submit comment