You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Dan ita saima
taji tafi jin dadin MAJEED daya aure Inayah Dan kuwa da tun farkoma sun San bashine
ya haifetaba baida alaqar Jini tako Ina da ita da tuni sun matsanta Masa ya aureta
yafi fashe fashen aurenta da akaita Yi shima Kuma ga lokaci yaja Bai taba aureba
ace haryanzu matsayin saurayi yake Dan haka Kai tsaye ya bayyanarda farin cikinta
ana fada saidai Kuma ta tausayawa Inayah sosai ta yanda Rana tsaka Zata karbi
zamanta ba 'yar mahaifintaba datake tsananin so da kauna amatsayin ubanta ita daya.
Kusan Banda Inayah data kasa fahimta bare yarda har lokacin
Sun Gama fahimtar dai Abbi bashine ya Haifa Inayah ba Kuma shine mijinta a yanzu.
Duk sun gane wannan abinda basu ganeba shine meya Hana a daura auren da Abdulsamad.
Alhaji babbah na dawowa daga masallaci suka dunguma palonsa lokacin har CM ma ya
iso Yana gidan.
Zama kowa yayi jiki a sanyaye Musamman Inayah da kusan komai Bata ganewa Takoma
kaman wata mutum mutumi.
Ita Alhaji babbah yafara kalla cikeda tausayawa da kulawa kafin ya maida kallonsa
kan umma yaganah datake Babba zatafin fahimtar komai Kuma idan ta fahimta komai
zaifi tafiya daidai Dan itace Zata ringa dorata a hanya akan auren da haqqoqinsa
tunda tare suke rayuwa gida daya.
Gaisawa suka fara Yi kafin ya Dora da fadar"
Haj yaganah ya fama da hidima da jama'a?
Allah yasa angama lafiya yakuma sanya Alkhairi.
To wani babban Al'amari yafaru tsakanin shekaran jiya zuwa jiya da Kuma yau din
kafin daurin aure Wanda yasa aka samu sauyi cikin qurarren lokaci.,
Shi aure nufine na Allah Dan haka kada kuyi Wani mamaki da Al'amarin ubangiji,
Inayah dai kaman yanda a da MAJEED shine jigonta yanzuma shine jigonta Kuma
ma'ishinta Dan kuwa shine mijinta haryanzu yafi kowa iko akanta.
Basai an tsaya tone toneba anan ko dogon bayani Wanda Zata samu daga baya idan
ansamu komai ya lafa
MAJEED dai bashine mahaifinta ba Kuma yada alaqar Jini tako Ina da ita bamu kadaiba
duniyama Bata taba sanin da hakanba sbd riqon Amana da Gaskia da yayi Mata da
zuciya daya Kuma a wannan duniyar abune Mai wuya samun irinsa Dan kuwa ko 'dan
jininka baka riqewa ba Amana irin hakan Amma shi ya riqeta ya reneta da Amana da
kauna bai taba barin tasan bashine mahaifinta ba idanba yanzu da hakan ta bullo ba
Rana tsaka shima Kuma hakan da yayi yayine duk akanta sbd har gobe itace kulawarsa.
Shi Dr Abdul dai anfasa aurensane sbd uwarsa daya ubansa daya da Inayah Wanda shi
wannan bayanin ba hurumin shigata bane
Dan hakan Ina fatan Kun fahimci yanayin da aka shiga dakuma wandama zaa Shiga Nan
gaba sbd Koda Wasa karnaji anyi wata fitina kokuma tashin hankali akan wannan
auren,
Shima MAJEED din danasan yafi kowa shiga mugun yanayi akan wannan auren nai Masa
nasiha Kuma Inshallah Ina fatan ya dauka.
Dan hakan Haj yaganah sai anyi kokari gurin fahimtar dasu wasu abubuwan aure ya
wuce mutum yayi Masa daukan dayaga dama,
Allah ya sanyawa auren albarka,
Suma can Allah yabasu ikon warware komai lafiya.
Waiwayowa yayi zaiwa Inayah nasiha akan itama saita dauki qaddara sbd da tashin
hankali samun kanka irin wannan yanayin sai ganin sukai tana Jan numfashi alamar
attack Zata samu
Kafin suyi wani yunqurin tasamu attack take Dan haka a rikice suka dauketa zuwa
cikin gida.
Allah yasa akwai likita taredasu Neesah taredasu Amma bada ita akaje palon Alhaji
babbah ba
itace tayi gaggawar fara taimakawa Inayah din wadda takejin kaman zata rasa ranta
sbd yanda numfashinta ke Neman yankewa Neesah na taimaka Mata gurin janyosa da
karfi.
Ganin kaman Al'amarin zaiyi girma sosai Dole suka Kira Dr farhat wadda kafin ta iso
suka dunguma da Inayah din zuwa asibiti sbd tuni umma yaganah takira Abbi ya sanar
Masa yace su wuce asibiti gashinan zuwa asibitin.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/20, 1:34 PM] MG: *_32_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Private hospital din dake anguwarsu Alhaji babbah aka kaita sbd kafin suce sunje AA
specialist wato private hospital dinsu akwai nisa daganan da hakan suka tsaya tanan
kusa.
Cikin gagawa suka karba Inayah din
Neesah ma bata barmusu aikinba su kadai da ita sukayi Dan sunada fahimta tana sanar
dasu itama likitace suka barta ta taimaka musu tunda dama itace kusan tasaba
taimakawa Inayah idan irin hakan ta taso.
Umma yaganah gabaki daya kanta neman sake cakewa yakeyi da wannan Al'amuran daketa
faruwa daga wannan sai wannan,
Har cikin ranta takejin kauna Mai tsafta da tsanani akan MAJEED da Inayah sbd sune
danginta itace danginsu Dan lokuta da dama sukan mantama basuda alaqar jini da
juna.
Badan a yanda yanayin komai ya fallasa kansa ba lokaci daya ba zato ba tsammani da
Babu Wanda zai kaita murnar Auren MAJEED datake addua da fatar gani tsawon shekaru.
Hakama auren Inayah wani babban burinta ne shima datake fatan Allah ya nuna Mata ya
cika a yau din
sai gashi Allah yacika Mata burin Auren dukansu a yanayinda Babu wanda yataba
tsammata,
Ku kansu basuma San farin ciki zasuyiba ko damuwar sanin ba Abbi ne ya haifi Inayah
ba.
Anty Hafsat ma zuciyarta kusan Kashi Kashi take kasuwa tana rarraba Mata tunani sbd
ayanzu Bayan Jin bayanin yanda Al'amarin yake daga bakin Alhaji babbah taji
zuciyarta na farin ciki da auren Dan kuwa Inayah Allah yayimata kyakkyawan sauyin
dayafi duka tarin mazan data rasa abaya sbd Abbinta yakai kowanne level da ake
kwadayin namiji yakai badan tashin hankalin halinda Inayah tashigaba da a fili Zata
fara bayyanarda farin cikinta akan wannan tsintar damu akala da Inayarsu tayi Dan
kuwa Abbi kam Masha Allah.
Sbd wadda tasaba ji da matsalarta na kusa yasa ma'aikatan asibitin Basu Sha wuyar
taro yanayinta ba tadawo hayyacinta saidai take bacci ya dauketa sbd kusan wannan
attack din yafi wainda tasaba samu abaya.
Kwantawa hankalinsu yayi ganin tadawo daidai tasamu bacci Amma kallo daya zakawa
fuskarta ka gano baccin na tattareda yanayin firgici data shiga.
Suna zaune a dakin datake anty Hafsat na kokarin daidaita ACn dakin da yayi yawa
umma yaganah Kuma na zaune tana kokarin amsa wayarta da Mimi ke Kira saigashi ya
iso yashiga dakin cikin nutsuwa sanyeda Lululemon wears har lokacin da alama Bai
tsaya sauyawaba zuwa wasu manyan kayan.
Fresh skin dinsa daya bayyana sosai cikin kayan anty Hafsat da Neesah suka kalla
suna sake tabbatarda kyau da tsarin da Allah yayiwa Abbin
Take suka sake Jin tabbas ta wannan fannin Inayah Dinsu tagama dacen miji illa
kawai baqin cikin dazata Shiga sanin Abbinta datafi so fiyeda komai baida alaqan
Jini da ita
Tsintar yayi,kyautarta akai Masa kokuma tayaya ya sameta Allah ne kawai yasani
saishi da umman Abdul din.
Cikin girmamawa anty Hafsat da Neesah sukai Masa sannu da isowa
Da qaramin sauti ya amsa Yana dan kallon Inayar kafin ya kalli anty Hafsat sbd umma
yaganah na waya yace"
Doctors din sungama dubata ne?
Neesah ya nisan yanayin nata?
Firgici ne kawai data shiga ya daketa sosai Amma Inshallah lafiyanta kalau yanzu
anmata allura ne sbd tayi baccinda kanta zai Dan warware ya rage Mata tashin
hankalin.
Gyada Kai yayi ahankali tareda sake kallon Inayah datai wani iri cikin lokaci
qanqani.
Dan gajeran numfashi ya sauke tareda juyawa yafita zuwa ganin likita Dan bayason ta
kwana a asibitin gida zasu koma tunda suna tareda qwararrun likitoci a gidan.
Fitarsa da mintuna biyar sai gasu Mimi sun iso asibitin a gigice sbd tashin hankali
biyu,
Na farko Jin auren MAJEED da Inayah dakuma Jin uwarsu daya ubansu daya itada Dr
Abdul ga qarin halinda Inayar tashiga.
Jigum jigum sukai a dakin wasunsu na sake Dan jajanta wannan alamari da masu godewa
Allah da baa Riga an daura aurenta da Dr Abdul dinba dan da abin yafi lalacewa.
Umma dai bayan taga Inayah ta tashi babu abinda take fata Dan ita kanta yanzu
tanajin dacin da Inayah Zata Shiga,.
A sanin dataiwa Inayah kuka da baqin cikin dazata Shiga na zaman Abbi ba
mahaifintaba zaifi Mata ciwo da radadi fiyeda auren Dan kuwa tafi buqatan ace
alaqar jini suka hada Bata auratayyaba.
Har yamma lis suna asibitin Inayah Bata farkaba sai magriba.
Tana farkawa takasa kallon kowa a dakin sbd yanda duk sukai jigum jigum yabata
tabbacin abinda yafaru kafin zuwanta asibitin Gaskia ne haqiqanin Gaskia Kuma Dan
haka Batasan ta Ina Zata fara bayyanarda babban abinda takeji tokare da zuciyarta
da maqoshinta.
Cikin kulawa da sanyin jikin yanayin da Inayah din ta nuna umma yaganah da Anty
Hafsat suka fara kokarin magana saiga shigowar Abbi Wanda Yana shigowa qamshinsa ya
gauraya dakin suka tsit suna jiran abinda zai faru Kuma ga Inayah din ga Abbi a
amatsayin ma'aurata.
Yanayinsu yasashi basarwa tareda Dan kamewa ya kalli Inayah data dago ta zuba Masa
Ido tana Neman fashewa da kuka yace"
Kina farkawa Kuma Zaki fara wani kuka agurin.
Neesah dake gefenta ya Dan kalla yace"
Ku shirya gida zaa koma da ita yanzu.
To" Neesah tace tana kallon Inayah din dake kokarin fashewa da kuka Amma takasa sbd
abun datakeji ya girma qwaqwalwarta.
Juyawa yayi ya fice suka biyo bayansa.
Anty Hafsat motar CM zatabi itada Mimi da Safnah
Su Kuma su Inayah din motar Abbi zasubi Dan haka suka nufa motar Kai tsaye umma
yaganah na riqe da hannun Inayah dake kokarin zubewa sbd tangadin datake na Bata
cikin cikakkiyar nutsuwarta.
Kaman yanda suka Saba fitarsu da Abbin idan takama Inayah ce a gaba Dan haka yau
dinma itace agaba sai umma da Neesah a baya.
Bayan sanyin Ac na motar da qamshinsa daya cika motar Yana zagayawa Babu Mai ko
motsi acikinsu kaman ba kowa a motar kowa da tunanin daya shiga Banda Inayah da har
lokacin qwaqwalwarta Bata fara aiki daidai ba dif take Bata ji Bata gane komai
yanzu.
Suna Isa gida Dole Neesah ce ta kamota suka nufi ciki tana kokarin kaita bedroom
dinta ta qwace Takoma Palo tana kokarin bin bayan Abbi cikin dimauta tana cewa"
Abbi ne kawai zaifadamun Gaskia na yarda da abinda duk ake fada,
Abbina ne kawai zan yarda da maganarsa.
Da sauri umma yaganah ta riqota tana cewa"
Ki nutsu Mana Inayah,
Me zakije kice Masa yanzu?
Bakiji anfada Miki yanzu mijinki bane,
Qarya zamu taru mu Miki ne?
Alhaji babbah zai Miki qaryane?
MAJEED din dakikeson saiya fada Miki komai Yana cikin damuwa sosai bakya gani?
Zaki sake daga Masa hankali da kukan Nan nakine idan kikace rikicewa zakiyi.
Rikitaccen Kuka ta fashe dashi Mai tsananin qunci tana cewa"
Ni bazan yardaba wlh abbin ne mahaifina,
Banason kowa a mahaifi sai Abbi,
Har umman Abdul din banaso amatsayin uwa Ni Abbi ne kawai uwa Kuma ubana...
Da sauri umma ta rufe Mata Baki jikinta na rawa sbd jikinta daya fara sanyi itama
da irin kukan da Inayah din fasawa Wanda tunda take Bata taba yin irinsaba sai yau.
Rirriqeta sukai ta zube qasa tana sake tsananta kukanta zuciyarta na Mata wani irin
zafi da radadi...
Idan ba abbine mahaifinta ba ai ita asaran duniya da baqin cikin duniya tana cikin
cikinsa da wannan mummunan labarin da gwara ayita fasa aurenta har abada akan
wannan labari...
Bazata taba yarda da maganar kowaba sai taji daga Abbinta cewa gaske bashine ya
haifetaba.
Dukkanin sautin kukan datake yanajinsu Amma Bai iya zuwa Inda suke dinba Dan kusan
yafita baqin ciki da wannan bankadar,
Dan yaso ya tsaya a ubanta na har abada saidai qaddara Bata bar hakan ba Dan kuwa
Koda warware auren Nan akayi har abada ita zaa Kira da matarsa ta farko wadda
tafara daukan igiyoyin aurensa haka itama har abada shi zaa Kira da mijinta na
farko daya fara riqe martabar aurenta.
Kuka Inayah da tashin hankali sosai tashiga lokaci daya Wanda ya gigita umma
yaganah da Neesah harma dasu zubbi da Salimat sun Shiga tashin hankali da damuwa
sosai ganin halinda Inayah din ke ciki
Ta bangare daya shi kansa Mai gidan babu Wanda yakuma ganinsa har washe gari,
Abincin gidan ranar haka aka daukesa aka fitarwa Bosco ya rarrabawa securities din
anguwar abokanansa sbd Babu Mai nutsuwar cin wani abinci.
Da zazzabi Mai zafi Inayah ta kwana Dan kaman yarinya qarama Takoma musu daqyar
baccin wahala ya daukeda jikinta da mugun zazzabi.
MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/20, 10:13 PM] MG: *_33_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta kwanta sbd
tsananin ciwon Kai Dana kirji,
Ana Gama breakfast umma yaganah ta sallami baqinta aka kaisu aka sanya mota tareda
Dan abin arziki gidan yasake daukan tsit.
Su zubbi tuni suka shirya komai a dining na breakfast kaman yanda suka Saba.
Umma dai a dakinta tayi breakfast din Neesah ma bata fito dining ba Dan a daki
Tasha tea Danma sunyi sunyi Inayah ko tea din Tasha taqi.
Har lokacin bata daina tsiyayar hawayeba,
Takasa yarda da wannan qaddarar lokaci daya wai ace Abbinta shine mijinta,
Tayaya Zata fara fuskantar wannan maganar,
Har abada bazata taba iya karban Abbi amatsayin mijintaba sbd haramun nema agunta
kallon Abbi a matsayin Miji ba uba ba.
Daga Neesah har umma sunyi rarrashi da nasihun harsun gaji Amma Babu sassauci a
lamarin,
Gabaki daya fuskarta ta sauya sbd kuka.
Anty Hafsat ma tazo tayi nata rarrashin Amma Dole haka zasu hakura sbd dama bazai
yiyu ka karbi irin wannan ba lokaci daya.
Gabaki daya wunin basuga Abbi ba sbd yafita tun safe gurin sallamar baqinsu na nesa
dazasu wuce Kuma akwai wainda zaiyi meeting dasu kafin su wuce din.
Da farko mantawa yayi da auren daya rataya akansa jiyan sai daga baya bayanma ya
daga waya zai Kira Inayah.
Dan rinte Ido yayi tareda maida wayar ya ajiye Yana fitarda Dan numfashi Mai zafi.
Miqewa yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwan Yana gogawa fatarsa sabulun
mountain water soap na Creed.
Sai bayan wasu Yan mintuna yafito daureda blue towel a qugu yafara shiryawa.
Cikin dark blue kaftans yafito da blue hular kube Bai wani shiga can palonsu ya
fice daga gidan sbd jiransa da ake.
Sai Bayan azahar Inayah ta iya tashi da daqyar takai kanta toilet tayi wanka.
Sallah tayi tazauna tareda janyo wayarta tana sake saka kiran Heart dinta Wanda
yanzu Kuma hankalinta ya karkatane akan taji yanda yake sbd tasan Yana cikin
matsanancin halin shima.
Wayarsa har lokacin bata Shiga Dan haka tasake daga hankalinta da wata qarin
damuwar.
Dole anty Hafsat da Neesah da umma yaganah sukai Shirin tafiya dubosa asibiti Dan
dama suma duk sun damu dason sanin halinda yake ciki din tun iya basuda labarin
komai akansa da mahaifiyarsa Kuma mahaifiyar Inayah.
Abbi umma yaganah takira ta sanar Masa zasu tafi dubo Abdul din Bai hanasuba yace
suje.
Har Zata kashe Kai tsaye a nutse cikin kamewa yace"
Kar kuje da Inayah ta zauna gida.
Ok shikenan.
Inayah taji lokacinda Abbi yace kada aje da ita Dan haka hankalinta yaqara tashi da
sauri tadauki wayarta tareda saka kiransa.
Ringing wayar tafara
Lokacin Yana tareda dasu CM da wasu school mates Dinsu da duk sunzo daurin auren
sbd kowa nata kokarin hulda dasu shida CM yanzu sbd ganin sun Zama abokan manya sbd
kudi.
Dan waiwayawa yayi gefensa da wayar ke ajiye ya kalli wayar a natse yaga Inayah ce
me Kiran yakuma San Sarai roqonsa zatai akan binsu shikuma bazai taba barin ta hadu
da Hadiza ba ayanzu Dan haka ya dauki wayar a kame yace"
Yes,Inayah.
A marairaice da alamar kuka tace"
Abbi Dan Allah zan bisu inason dubo Heart Nima,
Abbi Dan Allah kada ka hanani....
Bakida lfy Babu Inda Zaki kina wannan kukan
Kisha magani ki kwanta.
Kashe wayar yayi tareda ajiyewa Yana maida hankalinsa kan maganar dasukeyi.
Hawaye tafara tana kallon wayar
Su umma na ganin haka suka fice suna cemata saisun dawo.
Zaunawa tayi bakin gadon dakinta Tana cigaba da tsiyayar hawaye sbd tana tsananin
buqatan son ganin Heart Dan taga yanayinda yake ciki.
Wurgi tayi da wayarta kan gado tana cusa fuskarta cikin tafukan hannuwanta
zuciyarta na radadi.
Hannu takeson dorawa akai ta ringa zumduma ihu da birgima ko zataji sassaucin
tsananin qunci da damuwar dake ranta.
Tayaya Zata iya cire soyayyar heart daga ranta bayan yayiwa zuciyarta kyakkyawar
Shiga?
Tayaya zasu iya rabuwa da juna sbd kalmar uwa daya uba daya da ake dangantasu da
ita?
Batada uban daya wuce abbi Kuma batajin Zata daina daukansa ahakan kokuma daina
kallonsa ahakan.
Abbinta fa ake maimaita Mata kalmar mini agurinta.
Kasa riqe kukan tayi ta kwanta agurin tafara rero kuka tana sake Jin zuciyarta
kaman zata kama da wuta.
***Su umma yaganah kuwa koda suka Isa asibitin da Dr Abdul yake hankalin Yan uwansa
da mahaifiyarsa atashe yake sosai fiyeda tunani Dan kuwa Dr Abdul dai jiki ya
rikice.
A jiyan da aka kawosa asibiti daqyar aka samu ya farfado ya kalli mahaifiyarsa da
hankalinta ya rarrabu cikin tashin hankali masu girma sbd labarin auren MAJEED da
INAYAH ya gigitata sosai,
Zancen ya daketa har Batasan lokacinda itama ta zube qasaba jininta na Neman hawa.
Tabbas AA MAJEED ya nuna Mata shi namijin duniya ne,
Ya Sha gabanta ta hanyar aure Inayah sbd baida niyar bata 'yarta,
Tabbas Babu shari'a yanzu Kam da Zata karbar Mata Inayah daga hannunsa Amma Kuma
idan har Inayah Bata son wannan auren Koda abinda ta mallaka zai qare duniya kowa
ya juya Mata baya saita tsaya Sharia ta raba auren anbata 'yarta.
Su Haj balaraba dasu Alhaji buhari saidai su Alhaji kabiru sukai musu bayanin cikin
daya bayyana jikin Hadiza bayan shekaru Wanda yayi sanadin dasuka koreta daga gida
Saidai yanda komai yafaru Bayan barinta gidan shine Basu saniba saisunji daga
gareta dashi AA MAJEED din Dan yanzu sune kadai zasu qarasa warwarewa kowa wannan
qullin da tunanin dasuka shiga.
Haj balaraba kuka ta ringa rerawa tana yiwa salisu addua suna qara godewa Allah da
baa daura wannan aureba da basusan iya Ina tashin hankalin zai kaisuba.
Hajiyarsu suka kira suka Dan sanar da ita komai a taqaice to dayake tasan da
maganar cikin da haihuwar bayan barin Hadiza gida daga bakin jama'a Amma tayi shiru
ta lafe sbd tunanin ko cikin banzane Hadizan tasamo daga Lagos sbd kada a
dangantasu da cikin Tai shiru taqi Kuma barin 'yayanta ko daya yasani dan kada suce
zasu karba tunda ba tabbas hakama Hadiza ta sameta takanas da jaririyar Amma shedan
yaqi Bari ta amsa.
Tsufa ya kamata sosai yanzu Amma itama haka ta ringa kukan danasani da farin cikin
da aka samu Ayshatouh take zancen yafara fita a dangi saidai halinda Abdul ke ciki
yafi daga hankalinsu akan murnar bayyanar wadda basuma San da itaba a zuriar.
Dr Abdul mummunan shock din daya shiga ya daki zuciyarsa zuwa qwaqwalwarsa sosai
Dan haka ya jima Bai farfado ba Kuma ya a farfadowa ummansa yafara zubawa
indanuwansa dasukai mummunan ja yana kallonta cikin karaya da mutuwar dukkanin jiki
yace"
Umma since Inayah 'yarki ce itama kece kika haife shiyasa bazan auretaba Abbi ya
aureta
Ni nakasa gane komai
So kawai naji daga bakinki idan kece mahaifiyar Inayah tayaya AA MAJEED zai Zama
ubanta?
Umma Dan Allah kicemun ba kece kika haifetaba,
Kicemun bakida alaqar komai da ita sai wadda zamu qulla yanzu ta auratayya,
Umma Dan allah kice bakece uwar Inayah ba bakida alaqan komai da ita...umma bazan
iya rayuwa Babu Inayah ba kinsani akanta zan iya rasa hankalina da nutsuwata,
INAYAH ce farin cikina,rayuwata da nutsuwata.....umma kice wani abun Dan Allah Amma
ki janye maganar kece mahaifiyar INAYAH.
Kakkarwa jikinsa keyi idanuwansa na sake fitowa da tashin hankali.
Saikowa yayi gadon Yana Neman faduwa sbd jiri sukai saurin riqesa umman cikin kuka
ta riqosa tana kallon yanda yake kokarin haukace musu tace"
Abdul hakuri zakayi da wannan kaddarar ka runguma sbd bazan iya goge alaqar jinin
dake tsakaninka da Ayshatouh Inayah ba,
Kai Dan uwantane na Jini,
Nice na haifeta kaman yanda na haifeka,
Uwar daya ubanku daya Babu Mai iya goge wannan sbd rubutacciyar kaddara ce,
Abdulsamad ma dauki danganar rasa Inayah sbd har abada Babu aure tsakaninku
bazaka taba aurentaba Koda ku biyu zaku rage a duniya.
Dan Allah Abdul ka karbi wannan kaddarar da hannu babbiyu sbd zuciyata bazata iya
daukan wannan tashin hankalin dakake saka kanka acikiba Dan Allah Abdul.
##MAMUH#
##KUYI HAKURI AMIN UZURI NASAN CHAPTER DIN IS TOO SHORT.🙏
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[10/22, 8:04 AM] MG: *_34_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Umma Hadiza hankalinta yagama rabuwa daban daban,
Tana buqatan fuskantar MAJEED akan abinda yayi na auren Inayah badan komaiba sai
Dan nuna Mata iko akan Ayshatouh..
Ta Bangare Daya tasan Inayah ma na can cikin matsanancin halin itama,
Babbar damuwar Kuma ganin Abdulsamad na Neman zauce musu sbd yaqi sauraren kowa
bayan zantukan tashin hankali da qin yarda da uwarsa daya da Inayah kaman yanda
itama Inayah batama yarda da tanada wata uwarba Dan ko acikin tarin damuwarta umma
Hadizan Bata shigob ita tashin hankalinta Abbi daya zamana ba mahaifinta ba ko
auren daurawa kawai akayi batajinsa ajikinta kwata kwata.
Zuwansu umma yaganah yasa hankalinsu Haj balaraba tashi sbd mummunan halinda Abdul
yakuma shiga Dan kuka ya ringa yiwa su umman da Anty Hafsat Yana maimaita sunan
Inayah cikin karyewar zuciya.
Umma yaganah dayake tanada saurin kuka take itama tafara hawayen tausayin Abdul
tana cewa"
Abdulsamad sai hakuri
Jarabawar ubangiji ce duk zaa cinye idan anyi hakuri da tawakkali
Inayah tariga ta Zama ta waninka dole dangana zaa dauka abarwa Allah...
Kalaman umma yaganah suka qara Karya zuciyarsa yaci gaba da zubda hawaye Yana
sunkuyar dakai zuciyarsa na Masa wani irin ciwo.
Anty Hafsat ma jikinta mugun sanyi yayi da tausayin Abdulsamad Mai tsanani Dan kuwa
Basu dauka abin yayi tsanani hakanba.,
Abdulsamad din dasuka sani Dan gayu da kwalisa shine ya garare cikin kwana daya sbd
masifar ciwon rashin Inayah.
Neesah kuwa itama jitayi tausayinsa da Inayah harma Dana Abbi yasa hawaye ciko
idonta sbd kowannensu yana cikin matsanancin halin da Babu mafita sai dauka da
dungumar abinda ya samesa.
Irin naci da daga hankalinda Abdulsamad yayi nason zuwa ganin Inayah yasa umma
yaganah miqewa su tafi sbd ko hauka bazata sakata tafiyada abdul dinba ko basa
damar zuwa ganin Inayah ayanzu sbd bayan haqqin mariqi da MAJEED yake dashi akan
Inayah yanzu shine Mai gabaki dayanta Dan haka bazatai wannan wuce gurinba ko
gangancin zuwa dashi Dan haka suka miqe suka fito jiki a sanyaye Koda,
Inayah ma Babu Wanda yayi musu maganarta sbd kowannensu baimasan me zaiceba akanta
Dan haka sukai shiru kafin suga sun fara samun daidaituwar Abdul tukuna ayi zaman
wannan maganar dake buqatan iyaye da manya aciki sbd tsanar da MAJEED yayiwa Hadiza
Saida manya a zancen zai yiyu.
Abbin ne yarigasu isowa gida Kuma yasan Babu kowa a gidan sai Inayah Dan haka daya
dawo direct ta palonsu ya biyo tareda nufar bedroom dinta.
Yana isowa zubbi na fitowa daga dakin daukeda tray din abinci da Inayah din bataci
ba.
Zubbi na ganinsa tayi saurin Dan yi gefe Tana cewa"
Welcome Sir.
Tray din hannunta ya kalla ganin Babu abinda aka taba daga abincin.
Dan rintse Ido yayi ya bude tareda cewa a natse,
"Kiyi warming abincin ki dawo Mata dashi.
Ok Sir" tafada tareda barin gurin.
Dayake kofar abude take Koda suke maganar Dan haka Inayah taji Qamshin turensa
tasan abbi na kusa sai gashi taji muryarsa a hankali.
Da sallama Mara sauti sosai yashigo dakin Yana kallon yanda take zaune kan gado
daga fuskarta har idanuwanta sunyi mugun kumbura gabaki dayama kusan kamanninta sun
sauya sbd kuka da tsananin tashin hankali.
Sofa dake dakin ya nufa ya zauna ahankali tareda Dan takaita kallonsa akanta sbd
ganin fuskarta ahakan damunsa zaiyi sbd baitaba barinta tun yarintaba tashiga
damuwa irin haka.
Yana zaunawa ta miqe tsaye ta nufosa.
Wani kallo yayiwa qafafuwanta dasukai haske sosai ga sai zanen maroon lallen da
akai Mata na aure yafito da Babu safa ko bedroom feetwear a qafafun tana kallon ta
dakata tareda komawa baya ta dauki feetwear dake gefen gadon masu taushi na bargo
ta saka kafin ta nufosa Dan yawo ba feetwear ko safa wani abune da abbinta koyar da
ita tun qanqanuwarta
Duk tsafta da kyan gidansu basa da yanda tsarin gidansu yake na komai fes Bata
tafiya ba takarmin ko safa a qafarta sbd wasu qananun qwayoyin cuta ta qafa suke
saurin shigar mutum.
Gefensa ta qaraso jiki a sanyaye ta zauna tana kokarin yimasa wani kukan Dan dama
tun jiya takeson ganinsa tayi Masa kukan dake cinta Amma taqi barin kowa ya gansa
ya shigewarsa.
Fara hawaye tayi tana kallonsa tace"
Abbi Dan Allah kada kacemun bakaine mahaifinaba,
Ni Kai nasani Kuma Kai zanci gaba da sani a wannan matsayin
Bazan taba karban kowaba amatsayin uwa ko uba
Dan Allah Abbi kabarni da matsayina na 'yarka ta Jini nafison.
Umma yaganah ce ta bude kofar dakin tashigo Kai tsaye sbd dawowarsu kenan.
INAYAH Bata tsaya da abinda take fadaba tacigaba da cewa"
Abbi Dan Allah kada karka bari a sauya mini wani sunan bayan Wanda ka sanyamin,
Ni banason kowa amatsayin jinina sai Kai,
Abbi Ni Kai kadai ne jinina,
Danasan yanda zanyi na hada Jinina da naka ya gauraya daya da naka Abbi wlh danayi
ayau dinnan.......
Umma yaganah dake kokarin juyawa tabasu guri Batasan lokacinda ta tsaya cak ba
tareda dawowa da wuri tana buge bakin Inayah din cikin kunyar zancenta.
Shi kansa MAJEED din Dan muskutawa yayi tareda fuskewa sbd Inayah dai idan zatai
zance ba ruwanta yanko abarta kawai takeyi.
Lokuta da dama Dan umma yaganah na kwabarta ne Amma zantukan datake yankowa gaban
Abbin mamaki suke basa matuqa Dan shi wasu abubuwan na halayen Mata dabai taba
saniba sbd Bai mu'amalantu dasuba sosai a gurin Inayah yake ji da saninsu.
Ahankali ya kalleta Bayan ya kalli umma yaganah da bakin Inayah yake Bata takaici
wasu lokutan.
A natse cikin yace"
Inayah wannan wata Gaskia ce da Dole zamu hakura na dauka sbd nafiki Jin dacin
rashin Zama Wanda ya haifeki Amma hakan Allah ya qaddara.
Wannan kukan kidaina Babu Wanda zai tafi dake koina,
Dr Abdul Kuma idan kin daina kuka kin nutsu zan Bari kije ki dubasa.
Gangaro Mata hawaye sukai tace"
Abbi maganar auren fa?
Da
Book Chapters
Chapter 14
Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500