ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka
gaisa ta fito Zata wuce dakinta saikuma ta juya ta nufi dakin Haj umma itama ta
gaidata kafin ta shige.

Kai tsaye dakin ta shigo tana rufe robar sauran ruwan datasha.

Abbi da Haj umma da Anty juwairiyyah ne suka juyo dukkaninsu atare suna kallonta.

Ba damuwar komai tace"

Haj umma Ina wuni?
Ya jiki jiki?

Anty juwairiyyah Ina wuni?

Tare suka amsa kadaran kadahan.

Gun Abbinta ta maida kallonta tareda sakin qayataccen murmushin farin cikin ganinsa
tayo gurinsa Kai tsaye tana cewa"

Abbi kana gida ashe yau.

Da sauri Haj umma ke kallonta ganin da gaske gurinsa ta nufo din da shegun kayan
dake jikinta Wanda zallan shape dinta suke bayyane Musamman shafaffen cikinta
dayasa kirjinta dake cikin push-up bra fitowa dakyau.

Abbin kuwa Jin yayi kunyar ummansa ta kamasa da sauri ya miqe sbd fita da Inayah
din saidai Yana miqewa tana qarasowa ba damar dakatawa sbd tariga ta qaraso ba
tsammani kirjinsu ya hadu.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
#AA/AYSHATOUH INAYAH.
_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/2, 12:18 PM] MG: *_47_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Firfito da idanuwa Haj umma tayi tana dauke kanta daga kallonsu batareda tasan tayi
hakan sbd rudewa.

Anty juwairiyyah ma dauke kan tayi tana shafawa Al'amarin Inayah Ido Kuma daga Nan.

MAJEED Daya riqe balance dinsa da kyau sbd kiris yarage su Fadi har ita
cikin yanayi na kokarin daidaita kansa da 'dan fada a shaqe yace"

Inayahhh,,,me ke damunki ne?
Ki nutsu mana...

Matsar da ita yayi daga jikinsa batareda ya kalli kowaba yaja hannunta suka fice
dakin.

Itama kasa cewa komai tayi sbd Batasan yariga ya tasoba kodata iso idonta nakan
Neman Inda Zata ajiye robar ruwan hannunta Dan haka ba zato tajisa ya miqe Bayan
tariga ta iso dad dashi.

Suna fitowa Palo su zubbi dake gyaran yamma da sauri suka sauke Kai qasa daga
kallonsu.

Umma yaganah data fito lokacin taci Karo dasu Yana gaf da shigewa da ita dakinta
tabisu da Ido cikeda mamaki sbd ita kanta Batasan Yana gidaba alokacin.
Tsakiyar bedroom dinta ya tsaya da ita tareda dakinta ahankali ya dago Yana dauke
idonsa daga kan jikinta da kayan jikinta suke lafe cikin yanayi na Dan fada yace"

So nawa Zan fada Miki kin girma ki ringa nutsuwa?
So kike Haj umma tayita Miki fada tunda bakya ji ko?
Meye hakan kike sakawa kina yawo cikin gidan bayan akwai mutane yanzu...

Sanyi jikinta yayi shikenan ita yanzu Abbi fada zaita yimata komai tayi tunda Haj
umma bataso,

Ta saba yawo da qananun kayanta na Shan iska acikin gida ko yananan Amma yanzu
shikenan sbd Haj umma Abbi fada yake Mata.

Zuciyarta taji tayi sanyi har idanuwanta suka nuna hakan
Jiki a sanyaye tace"

Kayi hkr Abbi bazan Kuma ba.

Juyawa yayi zaibar dakin saikuma ya dakata batareda ya juyoba sbd yanajin kukan
datakeson yi ajikinsa Dan yasan halinta Sarai.

Ajiyar zuciya yayi Bai juyo dinba sbd tana ganin ya juyon Zata fara hawaye Dan
sauya Masa ra'ayi.

Kofa ya nufa ya fice yabarta da kayan jikinta da dakin dasuka Dan dauki kamshinsa.

Hawayen dataso saukewa agabansane suka gangaro Mata zuciyarta na Mata nauyi Dan
kuwa komai na sake tabbata Haj umma Zata wargaza duk wani matsayinta agurin
Abbinta.

Daqyar ta iya lallaba kanta ta nufi toilet ta tube ta shiga ruwan zafi a bathtub ta
lafe tanajin rashin Dadi a ranta.

Tajima a toilet din kafin ta fito daureda towel blue fuskarta ba wata walwala.

Neu Oil kawai ta shafa tareda spray da mist kadan ta saka free doguwar Riga har
qasa Mata nauyi da qaramin hannu tayi sallar la'asar tana idarwa ta koma kan
gadonta ta kwanta tana Dan dudduba wayarta kafin ta ajiye tana rasa meke Mata Dadi.

Karshe tashi tayi ta nufi dakin umma yaganah acan yayi kwanciyarta tayi baccin
yamma na kusan mintuna arbain zuwa awa daya kafin ta tashi.

Sallar magriba tayi ta sauya kayanta zuwa Rigar sweater da wandon jeans ta saka
babbar jacket coat da qaramar hijab iya wuya ta fito riqeda wayarta sai key din
motarta Zata tafi asibiti Dan tana leqawa wasu lokutan da daddare.

Umma yaganah ce kawai tasan fitarta Dan abbin baya gida Dan haka tana fitowa Kai
tsaye ta wuce ta shiga mota ta fice.

Ta Dan samu wasu patients Dr Abdul dayake asibitin shima yanata fama dasu dayar
anmata aiki Amma kaman ta jiwa kanta ciwo gurin yunquri Mai qarfi dayan Kuma
jininta yayi qasa sosai gashi likitoci da nurses na fama da ita taqi tsayawa a qara
Mata jinin.

Wannan aikin yasa ta tsaya asibitin har kusan qarfe goma batareda Tama lura da time
ba.

Suna gamawa taje ta wanke hannuwanta ta fito tareda zaro wayarta dake aljihun jeans
dinta taga misscalls na Abbi kusan guda shida dana umma yaganah guda biyu sbd wayan
a silent take.

Ya Salam" ta furta a gajiye tana saka Kiran Abbi.

Harta Isa mota ta bude Bata samu Kiran yashigaba Dan haka ta ajiye wayar gefenta ta
tada mota tabar asibitin.

Tana shiga harabar gidan Abbinta tafara hangowa tsaye Yana waya da alama fita zaiyi
sbd harda key din mota a hannunsa.

Jallabiyace milk a jikinsa duk da dare ne tana iya hango yanda jallabiyan tayi Masa
kyau kaman wani Dan matashin black Arab.

Duk wadda ta auri Abbinta tasamu the best miji.....
Au itace matansa ko?
Yanzu Abbinta shine mijinta?

Wani murmushin farin ciki tasaki a fili tana cewa"

Koba komai dai tariga ta alaqantu dashi har abada Dan haka Haj umma matsayinta
daban nata dabam.

Da farin ciki kan fuskarta kan fuskarta ta fito sbd mood dinta daya sauya take sbd
wannan tunanin datai na tuna shi din fa mijintane itace matarsa.

Gurinsa ta nufa tana sake kallon kyakkyawar fuskarsa dako yaushe take cikeda
kwarjini da kaunar 'yarsa akai.

Cikin yanayin shagwaba tace"

Abbi kayi hkr banji kirankaba wayan na silent kuma hankalinmu ya dauki akan wata
patient...
I'm sorry Abbi""'ta qarasa cikin wani yanayi na sangarta.

Kashe wayar dayake yayi batareda ya gamaba sbd can bangaren anajin abinda take
fadan.

Kallonta cikin idanuwanta yayi yaga gajiyan dake tareda ita ya sauke numfashi kadan
tareda cewa"

Idan ba call duty zakiyiba ki Dena kaiwa dare haka a asibiti
Idanma Yakama kinyi daren ki kirani Zan daukoki da kaina..na soke tuqin dare da
fitan daren Nan ke daya.

Murmushi tasake tana kallonsa tace"

Ok Abbi.

Ciki suka nufa tana basa labarin aikin dasukai da daren.

Kaman yanda ta saba suna shiga ta aje wayarta da takalmanta tareda zare Jacket coat
dinta ta miqawa zubbi data bude musu kofa.

Kokarin balle maballan rigarta takeyi sbd tanada singlet aciki sukai Ido biyu da
Abbi Wanda ya dauke kansa Yana Dan kame fuska yayi gaba batareda yace Mata komaiba.

Tunowa tayi da fadan dayayi Mata dazu akan hakan Dan haka ta fasa cirewa ta nufi
dakinta tana karban wayarta da sauran kayanta.
Wanka tayi ta saka kayan bacci masu santsi Riga da wando ta haye gado daga kwance
tayi addua sbd ta gaji sosai take bacci ya dauketa.

Washe gari Bata fita aiki da wuriba sbd ciwon Kai data Dan tashi dashi na lattin
bacci.
Tana fitowa a shirye palon Abbi ta nufa Kai tsaye.

Shima a shirye ta samesa zai fito sai qamshinsa Mai sanyi yake zubawa ta zubawa
fuskarsa idanuwa tana tunani wahalhalun dayasha da gwagwarmaya akansa take taji
idanuwanta na cikowa da hawaye zuciyarta na qara cuduwa da kaunarsa Mai girma.

Jin shiru yasanyashi dagowa daga wayarsa dayake dauka ya kalleta a natse.

Ganin yanayinta da irin kallon datake Masa yasashi Dan kame fuska Yana nufan kofa
yace"

Tsayuwar me kikeyi kina lattin fita aiki.

Bayansa tabiyo tana cewa"

Good morning Abbi.

Dan juyowa yayi ya kalleta murmushin fuskarta Bai tafiba saima qaruwa da yayi
Da mamaki yace"

Are you okay?
Kinada labari Mai dadine kike Jin dadi.

Ba zato ta riqe hannunsa tana cewa"

Abbi farin ciki nakeyi ganinka kawai.

Dakatawa yayi batareda ya juyoba ganin su haj umma dasu umma yaganah dasuka fito
rakiyar anty juwairiyyah da Zata wuce.

Kallonsu kowa keyi sbd umma yaganah batama San ta tashiba harta shirya ta nufi
gurin Abbin,

Itakuma Haj umma mamaki takeyi meyasa haryanzu wannan 'yar batada kunya ko tunani.

Ahankali ya zare hannunsa Yana Dan kokarin basarwa cikin nutsuwa yace"

Harkin shirya kenan anty juwairiyyah?
Muje na ajeki airport din saina wuce.

Haj umma Inayah ta kalla cikeda kulawa asake tace"

Ina kwana Haj umma?
Anty juwairiyyah Ina kwana?
Tafiya zakiyi yanzu?
Bazaki zaunaba kema kaman haj umma.

Janyota umma yaganah tayi gefenta tana matse hannunta qasa qasa tace"

Kiyi shiru idan bakisan abin fadaba Inayah.

Abbin da duk yabi ya rasa abin fada tayi ganin harda Haj umma zaa ta baro gurin
umma yaganah tana cewa"
Abbi zanbiku a ajeni asibiti na kwana akan hannuna ciwo yakeyi bazan iya driving
ba.

Da kulawa ya juyo Yana kallonta a natse yace"

Wat?
Shine kike tsaye anan tun dazu kina surutu?
Umma yaganah ta shafa Miki balm kafin kifita
ki zauna Charles zaizo yakaiki asibitin.

Shiru tayi tana kallonsa Jin bazaije da ita dinba.

Qin kuma kallon Inda take yayi ya nufi kofa Yana cewa su Anty juwairiyyah su fito.

Anty juwairiyyah ce ta kalleta tana cewa"

To saina Kuma dawowa Inayah,
Allah yabada zaman hakuri.

Amin" umma yaganah tace cikeda sakin fuska tana Mata Allah ya kiyaye har kofa.

Suna ficewa tadawo gurin Inayah tana cewa"

Da gaske kike ciwon hannun muje na shafa Miki ko rub kokuwa wani sabon halin kuka
samu keda Neesah na hakan?

A dungure tace"

Kaina ne keyi yanzu ba hannunba
Na wuce saina dawo.

Tun su abbin Basu Gama ficewaba itama ta fito da tata motar ta fice da gudu ta
wucesu
Yana kallo Bai nuna yaganiba Amma hankalinsa ya rabu da tuqin nata kusan zuciyarsa
kasa samun nutsuwa tayi su umma na gani yabi hanyar databi yayi dogon zagaye dasu
har Saida yaga isarta asibiti lafiya ya wuce dasu airport batareda yasan da suna
lureda uban zagayen dayayi dasuba Dan ganin Yar gaban goshinsa ta Isa aiki lfy.

Suna Isa airport ba wani Bata lokaci anty juwairiyyah ta shige sbd lokacin zasu
tashi.

Gida yadawo ya ajiye Haj umma ya wuce aiki.

Gidan yau yaqara yin tsit sbd anty juwairiyyah cema keda Yar hayaniyar wayoyinta da
jama'ar kasuwancinta.

Da wuri tadawo yau Dan tare sukaci abincin Rana da ita
Tana Gama cin abincin Rana ta koma daki Dan tanada vid conference call dasu Neesah
da wasu abokan karatunta da zasu qarawa juna sani akan aikin nasu Wanda sukeyi akai
akai sbd da yawan wasu sunfi wasu qwarewa Musamman su dasuke Dan saka shiriritata
itada Neesah.

A daki taqarasa wunin ranar tana conference din da abokanta saidatai sallar magriba
ta fito sanyeda kayan Shan Isa gashinta a daure tsakiyar kai kaman wata Yar baby
sbd fatarta daketa daukan idon hutu da gyaranta na aure da haryanzu yakeda saura.

Palo ta zauna gurin su Haj umma dake Dan fira sama sama da umma yaganah wadda wadda
yanzu Ta Kama kanta a abubuwa da dama gidan sbd Haj umma dake nuna matsayinta na
uwar maigidan.
Suna zaune palon Abbi yadawo yashigo idanuwansa akan Inayah datake kwance jikin
umma yaganah kaman Mara lafiya.

Gaisawa yayi dasu dukan kafin ya wuce palonsa zuwa bedroom dinsa sbd a gajiye yake.

Wanka yafarayi yayi ya saka pradas na Shan iska ya zauna Yana duba sauran aikinsa
acikin iPad Yana Dan amsa waya akai akai.

Lokacin magriba nayi suma duk suka tashi zuwa dakunansu sallah.

Sai qarfe 7 da mintuna suka hallara dining cin abinci.

Yauma kusan Haj umma nunawa tayi baa kulawa da majeed din yanda yakamata Dan haka
da kanta taqara Masa salad akan Wanda Inayah ta zuba Masa Kuma ya nuna Jin dadin
hakan a taqaice sbd haryanzu yakasa sakewa yakoma yanda yake ada gaban mahaifiyar
tasa
itama Bata damuba sbd tasan sai ahankali ko wannan sabo da shaquwar tasu ta dah
Zata dawo sbd shekaru kusan ashirin da hudu zuwa da biyar ba wasaba.

Fira taringa jansa cikin kulawa Yana amsawa shima cikin kulawar,

Inayah da umma yaganah Yan kallo da saurare suka koma
Karshe dai haka inayah tagama ta tashi ta komawarta daki sbd ganin yau ko kallonta
Abbin nata baiyiba hankalinsa nakan Haj umma.

Umma yaganah ma tariga tashi tabar dining din ganin yau Haj umma Dagaske Jin 'danta
takeyi Dan haka kowa ya silale ya shige yabarsu.

Babu Wanda yasan lokacinda suka Gama harsuka koma Palo suka qarasa firar acan suka
shige.
##MAMUH#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
0913484810
[11/2, 9:43 PM] MG: *_48_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Washe gari da wuri ta fita aiki ko Abbi dataje gaidasa bai fitoba wucewa tayi bayan
ta kirasa awaya kashe da alama Bai tashiba.

Ko yau ta hadu da umma Hadiza asibiti sbd umman hankalinta Bai kwanta da barin
Abdul da Inayah dinba batareda ta rakosa tana sake tunatar dashi illar da shedan ke
masaba na maqalar Masa da tunanin Inayah.

Duk da ya tabbatarwa umma Hadizan zai nesanta kansa da duk wani tunanin daban Amma
takasa yarda dari bisa dari dashi,

Tasan bazai aikata abinda yafita musulunciba Amma Kuma batason ya shigewa Inayah
din sosai sbd ko kadan bazata so a shiga haqqin AA MAJEED ba bayan datasan girmansa
da sadaukarwarsa akan Inayah,

Ayanzu ko ita data Haifa Inayah din tayi alqawarin dakatar da kanta daga zuwa gunta
matuqar ba MAJEED din ya Basu Daman hakanba.

Yauma kaman baqi haka suka gaisa da juna saidai har umma Hadizan ta fice Inayah na
zaune cikin mota tana kallonta.

Fitowa tayi ta nufi ciki tana saka wayarta silent tareda sakawa cikin jaka.

Kaman yanda suka Saba kusan tareda Dr Abdul tayi aikin wunin ranar na duba patients
Dan haka tafara Jin sakewa dashi kaman yanda suke can farko.

Sai yamma sosai yau tadawo Dan haka Bata tsaya koinaba sai bedroom dinta tafada
wanka.

Tana fitowa sallar magriba tayi tareda saka kayan bacci tayi kwanciyarta a daki
tana Jin ciwon Kai na Dan damunta na gajiya.

Ta Bangare Daya jinta takeyi wani sukuku sbd gabaki daya wunin batai magana da
Abbinta ba abinda baitaba Kuma baya faruwa a rayuwarta,

Abbinta shine abokin firarta akoda yaushe kusan da safe da Rana kusanma dai time to
time suke waya idan har baya gari
Idan Yana gari kuwa tunda safe saitaga Abbinta take fita hakama kafin tadawo Zata
kirasa da darema tare sukecin abinci a dining Kuma tabisa palonsa kafin taje ta
kwanta Amma yanzu komai Yana neman canjawa duk sbd auren Nan dakuma zuwan Haj umma.

Da zaaci abincin dare Bayan kowa ya zauna zasu fara baiga tafito Kuma yau duk
baijitaba shima.

A natse ya dago ya 'dan kalli umma yaganah yace"

Inayah Bata dawo daga asibiti bane?
Tadawo,
Batajin dadine kanta na ciwo tun dazu.

Baice komaiba ya ajiye tissue din hannunsa tareda miqewa tsaye zai wuce Haj umma ta
riqe hannunsa ahankali cikin kulawa tace"

Ka zauna,
Ina zaka bakaci abincinba?
Bari a kuma kiranta.

Dan shiru yayi tareda Dan juyowa gefen zubbi dake kokarin ajiye juice data kawo
yace"

Ki kirata ta fito taci abinci.
Idan jikin yana damunta sosai Dr farhat zatazo yanzu ta dubata.

Yes Sir" zubbi tace tareda juyawa ta nufi dakin Inayah din.

Tana zuwa ta taddata kwance idanuwanta a rufe saidai ba bacci takeyiba waya takeyi
da Neesah ahankali sbd batako son doguwar magana yau.

Magana sukeyi da Neesah akan damuwarta na abinda yake sauyawa daga rayuwanta da
Abbi.

Cikin kulawa zubbi tace"

Abbinki yace a kiraki kifito kuci abinci.

Ajiyar zuciya Inayah sauke ahankali zatai magana Neesha tace"

Babes kice bakida lafiya sosai bazaki iya fitaba kodan abbin yanuna Miki kulawansa
dakika rasa kwana biyun.

Shiru Inayah tayi tana nazarin maganar,
Bata yiwa Abbinta Karya sbd Bai koyar da itaba Amma Kuma tanason kulawansa datake
neman rasa sbd zuwan Haj umma Dan haka ta amsa shawarar Kai tsaye tace"

Babes saimunyi mgn.
Kashe wayar tayi tareda ajiyewa gefe ta kalli zubbi a kasalance tace"

Zubbi bazan iya fitowaba kaina na ciwo sosai na koshi da abincin.

Juyawa zubbi tayi abinta ta isarda sakon ta juya ta koma kitchen.

Shiru kowa yayi
Haj umma na jiran ganin idan tashi zaiyi.

Umma yaganah ma jiran take taga abinda zaiyi.

Ajiye spoon din hannunsa yayi yanason miqewa Amma Kuma Haj umma da kanta tayi
serving dinsa cikin tsananin kulawa da kauna da maimaicin yaci abincin.

Katse shirun Haj umma tayi da cewa"

Yaganah Akira likitan dazata dubata Mana tun kafin dare yayi Amma nafisa ran stress
ne na aiki kawai may be idan tayi bacci zuwa safe Zata wartsake.
Dan yakamata ta saba da duka irin wannan stress din tunda likitace,

Kun sangartata shiyasa komai qanqantan Abu take maidasa Babba,
Saiga kuna rufe Ido kuna koyar da ita wani bangare na rayuwar
Ba'a sangarta da shiririta rayuwar Zata qareba
Aure zatayi Batasan kalan rayuwar dazata tadda b......

Tissue din daya goge Baki ya ajiye tareda miqewa Yana musu Saida safe gabaki daya.

Umma yaganah ma kasa shiru tayi cikin 'yar Wasa tace"

Aure Kam ai tariga tayi saidai ta muyita fama ta nutsu tasake sanin abinda takeyi,
Inayah kam dama ai akwai shiririta taqi girma indai tana gaban MAJEED.

Aikuwa Dole tasan ta girma tunda majeed din ba zauna zaiyiba zaman jiran tayi
hankali,

Aure yakamata yasan yayi Dan shekarunsa yanzu yakamata ace yafara Tara Yara Amma
gashinan aurenma baisan yayiba Dan shirmen Inayah,
Idanma batai hankaliba ai shikam bazai zauna jiran ranarda Zata hankaltuba aure
zaiyi manyanta yakeyi ba saurayi yake sake zamaba.

Tsit umma yaganah tayi tana sauraron abinda Haj umman ke fada cikeda mamaki da
shakka,

Me kuma yakawo maganar MAJEED da wani auren yanzu ana zaune kalau,

Auren dake kansa yanzuma baigama samun mazauniba a rayuwarsa ake maganar wani auren
yanzu?
Kenan Haj umma Bata dauki auren Inayah din da majeed aureba sai hanyar dakatar da
Hadiza kawai.

Jin tayi jikinta yayi sanyi bakuma gurin sauran gurin shigan abinci acikinta sbd
maganar Haj umma Dan haka ta Dan saki yaqen murmushi tana yiwa Haj umma din Saida
safe ta tashi.

Itama Haj umma tagama Dan haka ta miqe ta nufi dakinta Kai tsaye tana sanarda
Salimat ta hado ruwan zafin gasa Mata qafafunta.


Inayah dake daki tana jiran zuwan Abbinta dubata taji shiru Babu Wanda yazo tsawon
mintuna.

Sanyi jikinta da zuciyarta ke kokarin Yi matuqar Abbinta baizo dubataba to tabbas
yanzu ba kaman dah bane kenan,

A sanyaye ta zame ta qarasa kwanciya tana Jan bargo ta rufa.

Shigowar umma yaganah ce ta sanyata dagowa a sanyaye ta kalleta.

Itama umman jikinta a mace yake Amma Bata Bari Inayah din taganeba ta qaraso tareda
Zama gefenta tana cewa"

Yaya kan?
Ya rage ciwo?

Dago kanta tayi daga kan pillow ta kwantar kan cinyar umma yaganah tana lumshe
idanuwanta.

Ahankali tace"
Umma yaganah Ina Abbi?
Yana gurin Haj umma ne?

Numfashi umma yaganah ta sauke tareda dafa kan Inayahn cikin nutsuwa da kulawa
tace"

Inayah kina buqatan cire duka wani tunanin MAJEED kada ya kusantu da kowa bayan ke,
Haj umma mahaifiyarsa ce wadda duk duniya Babu Wanda yakaita matsayi agunsa,

Duk yanda yake tsananin kaunarki idan kina nuna Jin zafi ko kishin kusancinsa da
Haj umma Zaki iya jawa kanki matsala,

Ki cire tunanin komai ki maida hankali kan aurensa dake kanki Dan yanzu duk wani
shashanci ki ajiyesa ki fara sanin aurene akanki.

Kuma ki koyi hadiye Abu Dan Allah Inayah sbd banson afara samun damuwa tunda wuri
tsakaninki da mahaifiyarsa tunda dai ba zaunawa zatai har abada ananba dole wataran
Zata tafi,
Nima zuwa gaba kuna fara taramun 'yan jikoki Zan barku ayita kaimun renonsu..koba
haka ba?

Ko har shirin auren da kukai keda Neesah ya wargaje sbd Abbi ne mijin ba'a aura
masu rawar Kai ba..

Da 'yar tsokana ta qarasa zancen tana shafa kan Inayah sbd ta sake Dan tasan Zata
iya kwana da damuwa aranta.

Murmushi kawai Inayah tayi tana safe lafewa tace"

Umma yaganah ai Abbi ma kila ya manta da cewa nifa yanzu matarsace..

Nidai umma yaganah kiyi Masa tuni nifa yanzu ba 'yarsaceba kawai Ni matarsace Dan
Allah ya......

Buge bakin umma yaganah tayi tana cewa"

Zaki fara ko?
Ba nace ki ringa Kama bakinkiba idan bakisan me Zaki fadaba.

Umma yaganah fa kinaga ko Dan kallon mace bayamun saina 'yar baby Inayah wadda
ta.......

Bazakiyi shirunba kenan?

Shiru tayi tana hadiye sauran zancen Dan ita idan matsayin Mata zaisa kulawan
Abbinta yadawo Mata Zata zabi hakan da sauri.

Zubbi ce tayi knocking kofar dakin tashigo tareda Dr farhat wadda taketa zuba
qamshi Mai Dadi da adonta na doguwar Kuwait Abaya red fes da ita kaman ba dareneba.

Abbi ne yakirata ta taho duba Inayah,

Qarasowa tayi fuskarta daukeda murmushi da kulawa tana gaida umma yaganah kafin ta
zauna gefen Inayah tana cewa"

Oh my baby meke damunki?

Abbinki yakira hankalina ya tashi na dauka sosai ne jikin naki,
Meye matsalar?

Tashi zaune Inayah tayi daga kwancen ta zauna tana cewa"

Ciwon Kai ne kawai due to stress na aiki I think,
So Inaga dana samu nayi isashen bacci I will be ok by morning.

Duk da hakan Bari nai checking pulse naki,
Duka wannnan Zaki Saba ahankali ok?
Ki ringa samun bacci da hutu sosai.

Tea da cake Mai laushi akasa zubbi ta kawo Mata Tasha suna Dan fira sama sama kafin
sukai sallama Dr farhat ta fito.

Umma yaganah ce takaita har dakin Haj umma ta gaidata.

Da mamaki sosai Dr farhat ke sake gaida Haj umma dakyau tana mamakin ba umma
yaganah ceba Ashe ta Haifa AA MAJEED.

Haj umma itama sosai ta saki fuska suka gaisa da Dr farhat din Dan yanda Dr farhat
ta ringa gaidata cikin Jin kunya da girmamawa sosai yasa taga mutuncin Dr farhat
din sosai.

Bayan tafiyar Dr umma yaganah itama wucewa tayi dakinta ta kwanta.

Har Inayah tayi bacci cikin sanyi tana Jin damuwar rashin ganin Abbi.

Da safe haka taqi fita aiki da wuri Saida tayi breakfast da kowa.

A dining tana zuwa da Abbi tafara hada Ido Yana zaune cikin Navy blue Ralph Lauren
suit dasukai masifar yimasa kyau tareda fidda hasken lafiyayyar fatarsa dake cikin
hutu.

Gabaki daya Qamshinsa ya hadu Dana English breakfast din dake jere a dining ya
sauya gurin.

Cikin nutsuwa da kulawa da sanyin murya tace"

Good morning Abbi.

Idanuwanta ya kalla kafin ya dauke idonsa akai anatse Yana cewa"

Morning,
Yaya jikinki?

Complain zatayi umma yaganah ta katseta da cewa"

Yaya jikin Inayah?

Naji sauki umma,
Haj umma Ina kwana?
Umma yaganah good morning.

Zaunawa tayi tana kokarin fara cin abinci Haj umma tace"

Yaya kan?
Yayi sauki ko?

Eh naji sauki alhmdllh.
Fara cin toasted bread tayi tana daukan tea tafarasha.

Itace tafara gamawa ta miqe ta Zata fice Abbinta yace tajira zai ajeta asibitin.
##MAMUH#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/3, 1:04 AM] MG: *_49_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Bai dauki wasu mintinaba ya Gama shima ya goge bakinsa da tissue tareda miqewa
yabar dining din
A natse cikin sautin Mara qarfi yace"

Saina dawo umma.

Umma yaganah ya dan kalla itama yace"

Saina dawo.

Kusan atare sukai Masa adduar adawo lfy.

Zaune Inayah take tana chatting sama sama da Neesah dake son Jin labari daga gareta
tana ganin ya nufota tafara kokarin saka wayar cikin aljihun skinny jeans din dake
jikinta da farar doguwar Riga Mara nauyi wadda gefenta yake yanke daga qasa har
gurin qugunta.
Cinyoyinta da wandon ya lafewa ya Dan kalla Yana dauke kai kafin ya dakata daga
shiga motar ya juyo cikin fada yace"

Kije kisa native wear.

Kallonsa tayi da sauri tana kallon kayan jikinta....

Me Kuma kayanta yayi?

Sake dagowa tayi ta kallesa taga harya shige motar Yana zaune
Batace komaiba ta juya Takoma cikin gida ta sauya kayanta zuwa Riga da skirt na
atampa dark green da qaramin medium chantley veil ta fito riqeda qaramar Chanel
handbag.

Gaban motar ta bude tashiga suka wuce.

Suna fara tafiya ahankali ta juyo ta kallesa tareda marairaice fuska ta dafa dayan
hannunsa dake gefen datake cikin wata sanyayyar muryar shagwabar data Saba yimasa
tace"

Abbi idan nayi lefi Dan Allah kayi hakuri bazan sakeba.

Dan juyowa yayi ahankali ya kalleta da idanuwansa dake sake Jin hawayen shagwaba,
Tace please Abbi Dan Allah bazan sakeba.

Hannunta ta qarasa dorawa kan hannunsa
Ya Dan sake kallonta

Tana ganin ya kalleta ta gangaro da hawayen data Tara a Ido tana qara marairaice
Masa.

Rintse idanuwa yayi ya bude ahankali Yana dauke kai daga kallonta....

Besan yaushe Inayah ta iya wainnan abubuwanba na saurin kuka yanzu Musamman idan
tanason Abu daga garesa sbd tasan kukanta shine abu na karshe dazai so a duniya.

Ahankali ya sauke boyayyan numfashi cikin kulawa da sanyin lafazinsa yace"

Meyasa kike Wasa da abinci?
Kina aikin lfy kice bakisan ciwo da dama suna shigaba ta hanyar yunwa?

Karna kumajin zaaci abinci kinbada different story daga yau.
Okay?

Gyada Masa Kai tayi tana sake riqe hannunsa cikin nata.

Zare hannun zaiyi tasake riqewa tana cewa"

Nacefa bazan sakeba Abbi,
Ahaka zamu qarasa ai ni matarkace yanzu Ab....

Wani mummunan burki yaja dasu akan hanya Saura kiris motar bayansu ta dakesu.

Kallonsa takeyi da mamaki batareda ta damu da abinda tafadaba cikin kulawa tace"

Are you okay Abbi?

Juyowa kadan yayi Yana zuba Mata manyan fararen idanuwansa dasuka sata Jin gabanta
faduwa a Karo na farko sbd Abbin nata Bai taba zuba Mata idoba sosai Yana kallonta.

Koyaushe kallonsa akanta taqaitaccene duk da tsananin kaunar da son dayake Mata
amatsayin ubanta.

Sunkuyar da kanta tayi ahankali Jin kallon yayi Mata nauyi da karfi ahankali tace"

Sorry Abbi.

Hannunsa dake cikin nata ya janye ahankali batareda yace komaiba ya ja motar suka
wuce.

Shiru bakinta yayi sbd tasan ta zaro zancen da umma ke cewa idan batada abin fada
ta ringa yin shiru Dan haka tayi shiru Amma Kuma ai Dagaske shi mijintane kodai
Abbinta baya Sonta kenan da auren???

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun" ta furta a fili tareda dagowa ta kallesa tana Jin
kaman hankalinta zai tashi da wannan tunanin.

Har suka Isa asibitin Babu Wanda yasake magana
Yana parking motar Dr Abdul na shigowa harabar asibitin.

Fitowa Inayah tayi tana kallon motar Dr Abdul din kafin tadawo da kallonta kan
Abbinta.

Bai lurada Hadiza ba dake cikin motar ya sauke glass din motarsa Yana amsa gaisuwar
Dr Abdul daya iso cikin girmamawa kaman da can Yana gaidasa.

Ba tsammani sai ganin hadiza yayi tana qarasowa gurinsa.

Inayah ya juya ya kalla itama shi take kallo batareda ta kalli Inda

Please Login or Register in order to submit comment