ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dan
haka Ya tsame kansa ya kame daga hulda da kowa yanzu dama can bamai hayaniyar shiga
mutanen ne Shiba,
Cikin tsananin hali ya kammala sauran watannin dasuka ragewa karatunsa bayan ya
Saida duka agogansa da wayarsa sun qare ga hidimar baby INAYAH wadda yasawa sunan
Da karatunsa.

Yana kammalawa ya tattara sauran abinda ya rage Masa ya fita neman hayar dakin
dazai zauna ya nema aikin dazai kula da kansa da Inayah.

Wata irin qauna Mai tsanani yakewa Inayah a yanzu daya Gama tabbatarda batada kowa
saishi kaman yanda baida kowa sai itan.

Kiransa da metron keyi da abban Inayah yasa kauna da shauqin abin ya shigesa sosai
harya sabarwa kansa da amsa sunan.

Gashi Inayah din tayi girma ta warware kaman kowane Lafiyayyan baby.

metron ce tayi Masa tayin gidan hayarsu
Baida zabi haka ya amince duk tsananin qyanqyaminsa da rashin iya Zama cikin
mutane.

Ganin yanayin gidan da jama'a sosai yasa ya ringa karbo Inayah wasu ranakun tana
wuni hannunsa kafin ya maidata da daddare.

Rayuwa Tai Masa tsanani sosai sbd baida komai baida hanyar koman,

Ga metron tafara gajiya da renon tunda baida abin Bata yanzu saiya samo daqyar.

Rayuwarsa tagama sauyawa tako Ina,
Baya shiga mutane sbd kusan duk Inda yaje zundensa akeyi akan 'yarsa Inayah wasuma
jifansa suke da zargin sai Allah idan ba lalata 'yar tasa zaiyiba.

Girma da tsananin dacin kalmomin ya sanyashi tashi gidan bayan ya hada kudin hayar
daki wani gidan daqyar da aikin wahala.

Dayake yaga alaman metron ma ta gaji da renon Inayah kawai karbota yayi ya dawo
sabon gidan daya samu mai dakunan haya birjik a jere
Mai daukeda mutane dabam dabam masu halaye daban daban.

Dagashi sai tabarma da abun rufa yadawo gidan sai yan kayansa na sawa dasuka Gama
fita hayyacinsu sbd kodewa.

Kayan Inayah ba duka suka basufi kala huduba Dan haka dakin nasu fili fayau ne.

Madara yabata tayi bacci yafara kaida kawon tsakiyar dakin da ita a kafada Yana
tunanin yanda zaiyi da ita yanzu.

Zuciyarsa ta qame ta bushe akan Al'amarin mutanen duniya da basusan komaiba sai
kansu.

Cikin yardar Allah da zashi masallaci yafito da ita a kafada yana tunanin yanda
zaiyi da ita yaje sallah.

Umma yaganah ce ta lura da hakan Kuma tunda ya tare ayau din aka fara tsegumsa
tanaji sunayi abinka da gidan haya gulma ba taushe hannu.

Karban Masa ita tayi tace yaje sallar yadawo.

Ba musu yabata sbd Yana buqatan hakan.

Daga masallaci gurin neman aikin qarfi yadan zagaya yi Amma bai samuba sai daya
dawo yasamu a anguwar ya samu tsaron shago Amma na idan an siya Kaya yakai mota
yace ya amince.

Koda yadawo umma yaganah tayi Mata wanka da ruwan zafi tas ta Goyata sbd itama
tanada tsananin sha'awar Yara Amma Allah Bai bataba ga manyanci haryazo.

Godiya yayi tareda bar Mata Inayah din sbd kada a datse mata bacci.

Tun daga ranar renon Inayah yakoma hannun umma yaganah wadda ta fahimci baya tareda
uwar Inayah tunda dai shine mahaifinta.

Rayuwa taci gaba da tsananta Masa sbd komai ya qarasa juye Masa,

Aikin tsaran shago da aikin gidan ruwa ya hada biyu yanayi dashi yake daukan
dawainiyar Inayah.

Ahaka har lokacin service Dinsu yayi yatafi yabarwa umma yaganah Inayah sati biyu
acikin camp ya fito yadawo yafara bautar qasarsa.

Fara service dinsa ya taimake rayuwarsu sosai sbd monthly allowance dinsa dashi
yake musu komai.

Kauna sosai ta tsakanin uba da 'da yakewa Inayah,
Duka a lokacin burinsa na inganta akanta yaqare,

Baida abinda yafi Masa Inayah sbd kaunarta ta taimaka gurin danne Masa radadi da
ciwon dake daskare cikin zuciyarsa.

Ahaka yagama yake fita aikinsa na service Yana dawowa kuma ya hada Dana aikin gidan
ruwa.

Koda ya kammala service dinsa Inayah tayi wayo sosai tasan mahaifinta wasu lokutan
daqyar ma take komawa gurin umma yaganah.

Haduwarsu da yagana yazama wani babban taimako daga Allah dan kuwa badan itaba
baisan tayaya zaiyi renon jinjirar 'ya shikadaiba.

Bayan Gama bautan qasa komai yasake tsananta alokacin ne yafara aikin wahala da
qarfi kala kala Dan inganta rayuwar 'yarsa wadda yanzu a hannunsa take tabar hannun
umma yaganah.

Tare suke cin abinci tare suke kwanciya
Wani lokacinma tareda ita yake fita aikinsa na wahala tana zaune cikin inuwa yake
aikin yagama sudawo gida.

Ganin kaman sanyin dakin zai Mata yawa yasa yasiya mata karamar katifa shikuma Yana
kwanciya a tabarma,

Duk wani abun buqata da Zata buqata baya sanya koda wahala saiya Nemo ya ajiye
Mata.

Ita kanta tunda tayi wayo tasan mahaifinta wata irin kauna da shaquwa Mai tsananice
ke tsakaninsu,

Batada abinda yafi Mata Abbinta a rayuwarta sai umma yaganah data sani,

Sam Bai taba barin tayi kuka ko kewan rashin uwa ba,
Shine uba Kuma shine ya maye gurbin uwa,
Mata wani irin kallo yake musu na rashin tunani da rashin tausayi da imani shiyasa
duk wata mace ta fice Masa arai,
Mahaifiyarsa data qyamacesa sbd wannan qaddarar Bai tabajin ya tsanetaba Amma Kuma
yasan tabbas Bata kyautaba Dan batai aiki da ilimin da Allah ya Bata.

Inayah itace tazamo sanyin idanuwansa Kuma qarfin gwiwarsa sbd duka gwagwarmaya
dayayi a halin dasuka samu kansu yayisune sbd inganta rayuwarta,

Yayi alqawarin ingata tasa rayuwar da tatane sbd su rayu kaman kowane 'yaya marayu
sbd daga shi har ita marayin Allah ne.



**********
Hadiza bayan barinta gidansu majeed hanya tabi tana Jin kanta na juyawa sosai ga
uwa uba tafiyar datakeyi kaman Mai koyan tafiya Dan kuwa gabanta tuni yafara
zubarda Jini sosai na yamutsin dayake ciki.

Batai doguwar tafiyaba taji tana Neman haukace tuburan Dan haka ta nema bakin wata
hanya ta zauna tana rusa kuka sosai tana tasa Inda ke mata sauki a jikinta.

Kukan datakeyi ne tana yagar jikinta yajawo hankalin mutanen dake kusa suka fara
kallonta suna tausaya mata wasu Kuma Mai Mata video sbd ganin haukacewa zatai
alokacin da alama asiri akai mata suke zargi.

Kayan jikinta take kokarin yagawa wata Mata dake kokarin Shiga motarta tayi saurin
zuwa ta tareta tana masifa da masu Mata video.

Cikin kuka da azaba sosai Hadiza ta bude Baki daqyar tana cewa"

Dan Allah ki taimakeni kikaini asibiti su ciremin gabana wlh azaba,
Ciwo,zafi,radadi duka inaji.

Kallonta matar tayi da mamaki tana sake riqe Dan kareta da handbag dinta masu sbd
daukanta.

Da mamaki tace"

Me yake Miki azabar?
Me kikeji?

Kasa magana Hadiza tayi tana sake bubbuga gabanta cikin ficewa hayyaci tace"

Dan Allah ku taimakeni.....

Da sauri matar ta tari taxi ta cewa Hadizan ta shiga batareda ta kamataba sbd tsoro
da tsaro.

Tata motar tashiga tacewa taxi driver din yabiyota.

Wani asibiti suka nufa tasa aka shigo da Hadiza wadda ta fice hayyacinta tini bayan
gurnanin azaba da wahala Babu abinda take.

Da gaggawa suka karbeta zuwa ciki suka fara dubata.

Gaban nata dataketa duka suka fara budewa suka duba.

Wata qara suka ringa saki cikin tashin hankali da tsoro.
Dayake wadda ta kawota asibitin likitace take suka taru suka gano haihuwa tayi
gabanta yasamu matsala.

Cikin gaggawa da tashin hankali suka fara taimakonta.

Dayake gurin ya lalace sosai Saida aka hada da yimata Yar qaramar tiyata.

Bayan taimakon data samu sun Gama Mata komai an maidata dakin dazata kwanta tana
bacci batareda tasan waye akantaba.

Dr iklimat itace ta biya komai na Hadizan tukuna ta wuce gida.


Kwananta uku a asibitin kafin yadawo cikakken hayyacinta ta zauna daidai tana Jin
komai Yana dawo mata sabo yanda yafaru.

Tashi hankalinta yayi tafara kuka Mai tsanani na Dana sani da Neman 'yarta.

Da farko Dr iklimat ta dauka Hadizan nada ciwon qwaqwalwa ne Amma data zaunar da
ita ta rarrasheta ta sanar da ita komai sosai hankalin Dr iklimat ya tashi Dan haka
Hadizan na samun sauki suka dunguma Neman gidansu MAJEED.

Kasa gane anguwar tayi bare gidan Dan haka suka ringa yawon stations suma Kai
report Amma ba wani labari.

Tashin hankalin da Hadizan tashiga yasa take Neman rasa nutsuwa da lafiyarta sbd
ahankali yafara taba qwaqwalwarta.

Dr iklimat data fara tsorata da Al'amarin haka ta samu ta lallaba Hadizan takaita
Inda tafara ganinta tace tayi tanuni daganan ko Zata iya game gidansu MAJEED din.

Kaman qwaqwalwarta bazata tunaba sai gashi ta tuna suka ringa bin Inda take tunawa
har Allah yasa suka Isa kofar gidan.

Basuga tashin hankali ba Saida aka tabbatarda MAJEED da babyn baasan Inda sukeba.

Take agurin Hadiza ta suma,
Haj umma ma Jin maganar dake bakin Hadiza yasata zubewa itama tana dafe kirjinta
dake kokarin tashewa da tashin hankali Mai tsanani.

Daqyar su Anty safiyyah da taimakon Dr iklimat ta Dan dawo daidai.

Kuka tafara tana yiwa Hadiza Allah ya Isa akan abinda tayiwa MAJEED ta rabasa da
uwarsa akan 'yarta Mara uba da asali.

Hadiza Kam saidai akai asibiti da ita.

A asibiti tana farfadowa Bata iya kukaba sbd zuciyarta dake barazanar daina bugawa.
##MAMUH#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/31, 12:19 PM] MG: *_43_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Daga gidan Dr iklimat Hadiza sake komawa tayi gidansu hajiyar MAJEED wannan karon
tana kuka tana komai Amma irin wulaqanci da tozarcin dasu anty juwairiyyah sukai
Mata baisa ta hakuraba haka ta ringa zuwa rokonsu su fada Mata Inda MAJEED ya tafi
da yarta.

Tun tana zuwa tana samun ganinsu har takai idan tazo Mai gadi ke yimata korar
wulaqanci yana zaginta.

Daga qarshe police suka saka aka kamata daqyar tasamu Dr iklimat ta karbota bayan
ta sanar dasu Hadizan nada matsalar qwaqwalwa.

Tun daga lokacin tashiga wani mawuyacin hali na ciwo da nauyi a zuciya.

Gabaki daya bata gane komai batajin komai sai kukan jaririyarta,
Kuka tuninya Dena zuwan Mata ya qafe..

Ta dan samu lokaci ahakan cikin masu aikin gidan Dr iklimat kafin Dr iklimat tafara
janta ajiki Dan ta warware tafara dawowa daidai.

Da fari Al'amarin yayi wuya Amma da dr ta dage sosai Kuma lokaci yaja sai gashi
tafara sakewa sbd kyautatawa Dr iklimat dataketa dawainiya da ita.

Itama aikin ta dauketa cikin gidan na abinci data iya.

Ganin qwarewarta a iya abinci yasa Dr iklimat ta maidata restaurant dinta sbd taga
qaruwar da zatai da Hadizan.

Dayake tasaba aikin restaurant sai Bata wani Sha wuyaba tasaba da aikinta sbd Sam
yanzu Babu wani digon farin ciki ko daya a rayuwarta,
Zuciyarta rufe take ruf da tarin baqin ciki da damuwa Amma a fili tana iya
kokarinta gurin mu'amala me kyau da mutane.

Dr biyanta albashinta takeyi Mai kyau ba gayya Kuma kullum ta gamo aiki a can da
daddare gidanta take dawowa ta kwana Saida sassafe ta koma.

Ahaka yayi fiyeda shekara daya a tareda Dr wadda Takoma tamkar wata babbar yayarta
sbd sabo da kulawa,

Fes Takoma tayi fresh abinta sbd nutsuwa da cigaban data samu sosai.

Ana hakan abokin babban yayan Dr wani soldier yaganta yayi shaawan aurenta sbd yafi
shaawan auren macenda batada kowa ganin yakeyi tafi maka biyayya hakama Zata riqeka
amatsayin kowa nata tabika duk Inda kakeda ra'ayin juyata ko kaita.

Dr iklimat tana duba ribar da Zata samu a komai na rayuwa Dan haka MJ Muhammed na
bayyanarda buqatansa na auren Hadiza tasan cigabansu sbd yanada arzikinsa sosai
saidai yawan auri saki Amma yanzu kila ya daina tunda ya samu irin wadda yakeso
wadda bazata iya Musa Masa komaiba sbd batada kowa.

Hadiza batada ra'ayi ko shaawan aure yanzu ko kadan aranta Dan haka Bata boyewa Dr
iklimat ba ya fada mata batada ra'ayi.

Dr batai qasa a gwiwa ba ta ringa lallaba Hadizan tana cusa mata ra'ayin da auren
kawai Zata samu sukuni da nutsuwata rayuwa tareda komawa cikin 'yan uwanta dasuka
gujeta,

Aure ne kadai rufin asirinta Kuma shine zai Bata Daman sakin kudi ta nema majeed da
'yarta duk duniyar daya gudan Mata da 'ya.

Zancen Ayshatouh da Dr tasaka yayi tasirin sauya Mata raayi Akan yin auren.

Ba bata lokaci kuwa Dr tafara karban kudi sosai gurin MJ Muhammed aka fara gyaran
Hadiza daman gata da sauran kuruciyanta.

Gaggawa Dr iklimat tasaka akan auren Wanda yasa Hadizan kejin damuwa Amma Kuma
bazata iya fasawaba tunda tabbas batada qarfin dazata nema 'yarta sai tana tareda
Mai qarfi.

Batada ra'ayin komawa gida Amma Dr iklimat ta dage akan suje gidan a daidaita Yan
uwanta su daura Mata auren da kansu sbd kaucewa wata fitinar gaba.

Bayan ankai ruwa Rana itada Dr da Yan uwanta suka karbeta Bayan sun tabbatarda Mai
kudine sosai Wanda zata aura.

Tunda Hadiza tadawo gida Babu Wanda ya tambayi Inda yarta takeba sai Inna wadda
take fushi sosai dasu kabiru tun Bayan barin Hadiza gidan.

Ita kanta hadiza Bayan dawowar tata bayan gaisuwa Babu abinda yake hadata da Yan
uwanta da matansu da 'yayansu,

Ta kebe kanta ta tsame daga cikinsu sbd tasakawa kanta Bayan Inna da Dr iklimat
batada kowa a duniya.

Wata biyu tayi da dawowa gida akan daura aurenta da MJ Muhammed ta tattara Takoma
Abuja gidanta itada Mai aikinta guda daya.

Tunda akai auren hankalinta baya kan mijinta sai akan Neman 'yarta wadda idan ciwon
rashinta yataso Mata kaman zautuwa takeyi.
Tun mj na daurewa har abin yafara damunsa sosai auren ma yafara fice Masa akai.

Rawa auren yafara tun Bai Gama cika shekara ba
Dr na ganin hakan ta tashi tsaye akan Hadiza da fada sbd idan tayi gangancin rasa
auren tayiwa kanta.

Ga rayuwarta tuni ta sauya tasamu wadata da Jin Dadi Amma zuciyarta takasa nutsuwa
ta rungumi qaddara.

Inna Dr iklimat ta daukowa Hadizan wadda ta zauna tareda ita tana lurar da ita
illar datakeson yiwa rayuwarta idan Bata dauki qaddara ta rungumaba.

Ba kunya hardasu Yaya Umar suka ringa kawo Mata ziyara akai akai suna Mata nasihan
riqe aurenta.

Tayi iya kokarinta gurin danne damuwarta cikin ranta tafara kyautatawa mj Wanda
yake tsananin kaunarta da Gaskia yanzu.

Rayuwar aurenta ta gyaru sbd ganin yanda dangi da Yan uwa kowa nayi da ita sosai
sbd abun duniyar datake dashi yanzu Dan haka saita sake nutsuwa da kulawa da
mijinta sbd koba komai auren yazama rufin asirinta dayasa kowa ka binta a Yan uwa.

Duk yanda taso cire damuwar yarta Bata iya cirewa duka Wanda hakan yasa mj ya
dauketa daga Abuja Inda take tuna babyn ya maidata Lagos yadawo da uwar gidansa
Abuja.

Rayuwarta a Lagos tafi ta abujan kwanciyar hankali da nutsuwa sbd ta rage damuwa
sosai ta fuskanci gabanta.

Kaman yanda ake cewa dukiya daban take to kusan ta tabbarda hakan,

Yayunta dasuka fara aibata 'yarta sundawo sune suke gwagwarmaya sosai gurin bincike
da Neman Ayshatouh wadda suka yarda da cewan ba shegiyar bace yanzu idanma da Allah
suka yarda ko Dan quncin dasuka luradashi kwance qasan ranta Wanda suka tabbatarda
har abada bazai goguba,

Kokuwa Dan kudin datake sakar musu sosai gurin binciken Neman 'yar ne?

Kwadayi da dukiya sunsaka anbata danta Abdulsamad Wanda tasaka a makarantar kudi
anan lagos Yana karatu cikin kwanciyar hankali da wadata,

Yan uwan salisu da dama yanzu zumunci da hulda sukeyi da ita sosai Dan kuwa Babu
qyashi a zuciyarta tana musu Alkhairi,

Yaya Umar da Yaya kabiru sune tsundum aduk Dan abinda ke gareta sbd mj ba mai Zama
bane shiyasa daga ita har uwar gidansa uwar yayansa dukiya yake musu sosai.

Ahaka rayuwarta ta sauya Babu wani labari ko bayanin ganin Ayshatouh da Abdul
majeed.

Shekaru sunja sosai manyanci yazo akan dole ta dangana ta cire ran ganin Ayshatouh
har abada a qarshema ta sanyata cikin adduar datakewa salisu dasu mama na Allah
yayi musu rahama.

Abdul baitaba sanin yanada 'yar uwaba sbd zancen da aka rufe gabaki dayansa aka
barsa amatsayin qaddarar data wuce.

Dr iklimat tazama uwa kuma 'yar uwa gareta Dan haka bayan mj yayi retire tadawo
abuja da Zama Amma sai zaman lfy na Neman gagararta da uwar gidanta Dole aka rabasu
ita Takoma Adamawa nata gidan sbd ta nuna Masa tafi ra'ayin Zama acan sbd Kota koma
Lagos din tunda yabar Lagos yakoma Abuja ba wani amfani Dan haka tafison Adamawa.

Da wannan ta tattara tadawo adamwa qaton gidanta da MJ yasiya Mata Mai girma daga
ita sai Inna da masu aiki sai Dr Abdul idan yazo sbd aiki dayake a asibitin Dr
iklimat dake Abuja.

Yaya Umar da Yaya kabiru ma tuni suka zama cikakkun masu rufin asiri da Yar wadata
ta sanadin mijin Hadizan daya sakasu cikin wasu Yan haurkokinsa na business Kuma
suna samu sosai aciki Dan haka suka sake tsayawa sosai akan duk wata hidimar Hadiza
da iyalinta duk da Bata sake haihuwaba tun tsawon shekarun Wanda Dr iklimat tayi
Mata bayanin tasamu matsala tun wancan lokacin data samu matsalar gaba ba lallai
takuma haihuwaba shiyasa ta dauki tsananin son duniya ta dorawa Dr Abdulsamad sbd
ga dukkan alamu shikadaine Dan dazata samu a duniya.

WANNAN SHINE ASALIN ABINDA YAFARU.


***************************
Tsit kowa yayi Banda kukan Haj umma Dana Hadiza saina umma yaganah Babu abinda yake
tashi.

Alhaji babbah da cm dama sauran duka mazan gurin duk jarumtarsu jikinsu saidaya
yayi tsananin sanyi.

Cm da umma yaganah ne suka Dora da irin gwagwarmayar wahalar rayuwar dayaSha iya
wadda suka sani gurin kulawa da Inayah da sauran wahalhalun har arzikinsa.

Duk Wanda yake gurin ya jinjinawa AA MAJEED da irin karfin zuciyarsa.

Ita kanta hadiza jikinta sanyi yayi tareda sabuwar danasani ga girmansa daya cika
Ido da zuciyarta sbd duk Wanda ya riqe 'Yar dabai hada komai da itaba irin hakan
Basu taba tunanin zaa samu Mai wannan zuciyarba.

Tun farko nutsuwar da zuciyarta tayi dashi a ganin farko yasata guduwa tabar Masa
'yarta batareda tunanin komaiba Amma bataba dauka kyan zuciyarsa da karfin
zuciyarsa yakai hakan ba.

Hawayen kunya da damuwar abinda tayi dama na tausayin kanta dana majeed take
tsayayowa tana sunkuyar dakanta qasa sbd Babu Kuma wani abun fada daya ragewa kowa.

Hajiya umma tafi kowa shiga baqin ciki da Dana sani sbd ko a bayan da hadiza tadawo
neman yarta tafada musu gaskiyar su juwairiyyah Basu Bari hajiyar ta yarda da duk
abinda Hadiza ta fadaba shiyasa suka hanata bayyanarda damuwarta akan rashin majeed
dinta da karfi da yaji Amma tun daga wancan lokacin Bata Kuma isashiyar lafiya ba
sbd ciwone da qunci a dunkule ranta na 'danta datafi so fiyeda komai da kowa.

Su Yaya Umar kusan sunfi kowa kunya da baqin cikin abinda suka aikata dan kuwa
kusan sune sanadin komai Dan tun farko dasun rungumi qaddarar Yar uwarsu da duka
baa cutatar da wanda baijiba Bai ganiba aka tarwatsa Masa rayuwa aka rabasa da
iyayensa.

Alhaji babbah yaji tausayin MAJEED da Hadiza fiyeda kowa sbd kusan kowa mafita take
nema a halin matsuwar dasuka shiga Amma tunda kusan komai yazo qarshe Kuma kowa
wahalarsa ta wuce tazama tarihi sai kawai a rungumi qaddara sbd duk wannan
Al'amarin idan anduba rabon aurene dake tsakanin majeed da Inayah yasa komai
yashigo ta hanyar tsanani.

Anty juwairiyyah kunya da takaicin Hadiza harma Dana 'yarta ya hanata cewa komai
har zaman ya tashi kowa ya watse aka bar Yan gidan kawai sai Haj umma da Babu Inda
Zata sai 'danta yadawo Dan bazata iya sake tafiya tabar majeed dintaba sanyin
idanuwanta dayaSha gwagwarmaya da wahalar rayuwar duk tarin arzikinsu.

Ta bangare daya jin tayi zuciyarta na Dan qonuwa da Inayah sbd akanta 'danta ya
zabi ya barta,

Ya bar mahaifiyarsa sbd ita,
Ya fifita kaunarta Mai tsanani da duk duniya tasan da Babu abinda yake kauna sbd
ita duk da tayi imanin da kaunarta na qasan ran majeed dinta sbd bazai taba daga so
da kaunar wani akantaba.

Amma Kuma duk da hakan ya fifita Inayah akanta qarshe yanzu karshen rashin rabuwa
ya aureta Wanda ita Sam batajin danta ya cancanta wannan auren sbd tako Ina danta
ya cancanta rayuwar Jin Dadi da farin cikin daya rasa shekaru.
##MAMUH#
#HOT LOVE/ROMANCE
#MAJEED/INAYAH




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/31, 6:01 PM] MG: *_44_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Inayah da kafafuwanta suka kasa riqeta sbd kukan datake Mai tsanani Mara sauti
ahankali ta juya tana dafa bango ta nufi dakinta...
Daqyar ta iya Kai kanta daki sbd ko ganin gabanta batayi sbd kuka hannuwanta na
toshe da bakinta.

Tana Isa bakin gafo ta silale Wasa ta zauna tana sake sabon kuka.

Abbinta kawai zuciyarta kewa wannan kukan sbd sam ita batajin tanada wani abun
tausayi tun jarinta har yanzu sbd Abbinta bai taba Bari ta Zama abar tausayawaba
tun tana cikin zanin goyan da uwarta ta yarda ita ta tafiyarta.

Taji tausayi da kaunar mahaifiyarta saidai Kuma har lokacin kaunar kaunar Abbinta
daban take a ranta Musamman yanzu datake qaunar tasa na qara nauyi da cikin ranta
Dan kuwa har abada Batajin Zata karbi mahaifiyarta matuqar ba abbin ne ya yafe Mata
ba ya hadata da ita.

Neesah ce ta fito toilet taga yanda Inayah din ke kuka ta qaraso tana kallonta
cikin mamaki da firgici tace"

Lafiya?
Wani abin yakuma faruwa ne?
Haryanzu Baki samu abbin bane a waya?

Kasa magana tayi ajiyar zuciya datake jerowa idanuwanta sunyi jajir.

Umma yaganah ce tashigo dakin fuskarta jajir da alamar kukan datasha sbd tausayin
MAJEED datake Jin itama kaunarsa da girmansa sun ninku a ranta sbd ya tabbata Mai
tautasayi da kyakkyawar zuciya duba da yanda itama ya riqeta da Maigidanta kafin ya
rasu har zuwa rayuwarta daya Gama ingantawa yazama gatanta Mai kare mutuncinta da
martabarsu yabasu suna da mutunci a idon duniya.

Tabbas har abada daga ita har Inayah basuda tamkarsa Kuma zasuci gaba da Zama a
qarqashin ikonsa da sunan Daya Basu,
Yazama ubansu gatansu Kuma zaici gaba ra zama hakan har abada da yardar Allah.

Inayah na ganin umma yaganah ta sake fashewa da kuka tana fadawa jikinta tana cewa"

Umma yaganah Abbina nakeson gani kawai yanzu,.bana samun wayarsa Dan Allah ki
kirasa yadawo gida na Dena duk wani rashin jin magana,,,
Ni har aurenma na karba zanyi auren dashi Dan Allah kice ya Dena fushi Dani yadawo.

Umma yaganah data kasa cewa komai bayanta kawai take Dan bubbugawa tanajin kaunarsu
su dukan duk da Inayah tako ina bata Zama abar tausayiba Dan kuwa rayuwarta tagama
samun haske tunda MAJEED ya tsaya Mata.

Umma yaganah Bata sake Jin tsananin kaunar auren MAJEED da Inayah dinba sai yanzu
Da komai ya bayyana.

A duniya Babu Wanda ya cancanta da Inayah dai Abbinta majeed Wanda shi wannan auren
ya zamarwa dukkaninsu RIBA BIYU.

Rarrashinta umma yaganah tayi tareda Neesah wadda take sauraran maimaicin zancen
komai abakin umman wadda ke fadawa Inayah komai batareda tasan taji komai ba.

Sun jima a daki suna rarrashin juna kafin a dakin Inayah din dayafi kowane daki
girma da tsaruwa a gidan Banda na Abbinta daya banbanta da nata ta hanyar
tsarararren palonsa dake hadeda master bedroom dinsa Wanda shima komai na cikinsa
milk ne sbd tsananin tsaftarsa yafison komai me haske bazai bayyanar Masa da komai
qaqantar datti Dan ya rabu da ita.
Gidan tsit kaman ba kowa saisu zubbi da Salimat dake aikin kaida kawon abinci da
maimaicin tsaftace gidan,

Haj umma da Anty juwairiyyah na daki
Anty juwairiyyah sai kame kame takeyi sbd kunyar kanta data mahaifiyarsu saidai
Kuma tana maimaitawa Haj umma girman lefin MAJEED dayaqi waiwayo gida ya zabi 'yar
tsintuwa akan mahaifiyarsa.

Itadai Haj umma Bata tankataba sbd yanzu Babu wani Hadi dazai sake rabata da 'danta
ciki kuwa harda Inayah wadda ta tsaya Mata arai sbd kaunar da aketa maimaita majeed
dinta nai Mata.

Sai dare kowa ya fito cin abinci suka hade a dining kowa na kallon dan uwansa Banda
Inayah wadda kafin ta fito sai yawon zuwa kiranta tazo taci abinci kowa keyi daga
umma yaganah har masu aikin da Neesah.

Saida suka fara cin abincin ta fito sanyeda Gucci Riga da wando gajere Wanda ya
bayyanarda fararen qafafunta masu kyau da lafiyar fata.

Rigar batada Fadi sosai Kuma Bata saka bra ba sbd kusan Shirin baccine tayi.

Slippers ne a qafarta da wayarta a hannu tana sake saka Kiran Abbinta Wanda duk
yakira bai shigaba sai idonta yacika da hawaye.

Qamshinta kawai yasa Anty juwairiyyah sake Baki tana kallonta sbd tasan Qamshin
Turaren da tsadarsa tunda tana yawon qasashe.

Haj umma kuwa kayan jikin Inayah din da yanda take wani irin Bata fuska kaman zata
fasa kuka take kalla cikeda mamaki,

Lallai yarinyar tasamu sake fiyeda yanda suke tunani.

Zama Inayah tayi Kai tsaye batareda ta kalli anty juwairiyyah ba ta gaida haj umma
da cewa"

Haj umma Ina wuni?

Ita kadai ta gaida Dan haka kowa yayi tsit,

A natse hajiyar ta amsa itama batareda takuma kallontaba.

Cikin daure fuska umma yaganah tai Mata nuni da juwairiyyah wadda ke juran Inayah
din tawi gaidata Tai mata fada tatas ba ruwanta da gatan dataga yayiwa yarinyar
yawa.

A hankali ta gaida anty wadda ta haifeta nesa ba kusaba Dan kuwa yarta ta fari ta
girma Inayah din sosai.

Wannan auren datakeyi yanzu yayanta biyu Dan haka yayanta uku
Auren ne irin na yayan masu kudi bawani Zama takeyiba kusan koyaushe taso tana
gidansu kokuma yawon wata qasar dauko kayan business,

Anty safiyyah ce kawai take Dan Zama gidanta itama sbd aikinta datakeyi Dan haka
Bata wani yawo ko tafiya sai wadda ta danganci aiki
Itama yayanta uku bayansu Bata qaraba ko yanzu da Alhaji babbah dakansa ya aiko
nemansu Bata samu biyosu Haj umma ba sbd aikinta da Bata Wasa dashi shiyasa sukazo
su kadai.

A taqaice anty juwairiyyah ta amsa gaisuwar tana zuba abincin dazataci.
Zubbi Inayah tafara zubawa tuwon semo da vegetables soup dataji Naman rago da ganda
da kifi.

Tana Gama zuba Mata ta kawo Mata ruwa Mara sanyi dan ita batashan ruwa Mai sanyi
Yana daya daga cikin koyarwar Abbinta tun tana qarama baya barinta da sanyi kowane
iri ne sbd sanyin dayaso shigarta tun tana jaririya.

Da spoon takecin tuwon Dan haka hankalinta ya rabu akan abincin da wayar hannunta.

Dungurar da wayar tayi da qarfi akan dining tana sakin qaramin tsokin rashin samun
Abbinta Dan zuwa yanzu hankalinta yafara tashi da rashin jinsa.

Sudai su Haj umma mamakin duniya yagama cikasu da kallon Inayah wadda shagwabar da
ita da akayi take a fili...

Budurwar yarinya likita guda Amma duka halayyarta da dabi'unta kaman wata qaramar
baby.

Bata Gama cin abincinba ta miqe zatabar gurin umma yaganah ta dakatar da ita cikin
kulawa tace"

Inayah Ina zaki bakici komaibafa a abincin?
Meyasa kike Wasa da cin abinci yanzu?

Shi abbin naki idan yaji bakya cin abinci aikinsan fadan dazaiyi.

Ba

Please Login or Register in order to submit comment