You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalin umma yaganah harma da Inayah Dan haka da kanta ta Kira cm din a waya tace Inayah tace Dan Allah abar Mata Hafsat da Safnah har zuwa anjima.

Bai Musa ba yabar Anty Hafsat da Safnah Dan haka gidan yayi tsit daga umma yaganah sai Anty Hafsat da Safnah da Neesah
Dr farhat ma ta tafi gida sai zaa wuce da Inayah din tace akirata.

Babu Mai wata doguwar walwala acikinsu sbd sudai anbarsu a duhu basusan meyake faruwaba sai jiran tsammanin zuwan Ango da jama'arsa suke Amma basuga alamar hakan Zata faruba ga wayarsa da Inayah ke Kira kaman zata zare Amma batama shiga kwata kwata.

Sanin Abbi yadawo yasa ta miqe jiki mace ta nufa gefensa tana sake trying din Abdul.

Kodata Isa knocking daya tayi tabude kofar tashiga daukeda sallama Mara sauti sosai.

Baya Palo da alama Yana bedroom dinsa Dan haka ta zauna kan kujera tana sake trying din Abdul.

Tunanin Kiran ummansane ya shigota ta nema numbern umman aikuwa tafara ringing.

Harta katse baa dagaba Dan haka ta fara rubutawa Abdul text.

Kofar bedroom dinsace ta bude Dan haka ta dakata rubutun tareda dagowa tana kallon kofar.

Sanye yake da ash Lululemon wears navy blue dasuka fidda hasken fatarsa sosai da alama wanka yayi ya shiryo cikin kayan Dan samun nutsuwa,
Qamshinsane ya gauraye palon take ya qaraso da yimata kallo daya yanajin wata qululuwar damuwar auren da aka daura Yana dawo Masa.

Cikin boye damuwarta da Yar sakakiyar murya tace"

Abbi kadawo Ashe tun dazu?
Abbi Ina Heart ya....kasa qarasawa tanajin nauyin qarasa zancen sbd ita wani lokacin mantawa takeyi da kunyar fadan wani zancen.

Dan juyowa yayi kadan ya kalleta ganin damuwa a tattare da ita cikin dan yanayin kawar da zancen Kai tsaye yace"

Abdul na asibiti ya Dan samu attack ne aka wuce dashi asibiti.

Zaro ido tayi cikin tashin hankali da firgici Amma ganin ba fuskar Kuma wata tambayar agurin Abbi yasata miqewa ta silale Takoma.

Koda ta Isa a tsattsaye ta taddasu kowanne ba acikin cikakken hayyacinsaba,
Tashin hankali da firgicin data gani ataredasu duka yasata bude Baki da qarfi cikin firgici tace"

Badai Heart wani abun yasamaba kuma daga asibiti???

Umma yaganah kanta yakasa daukan abinda CM yafadawa Hafsat a taqaice na cewa A MAJEED shine mijin da aka daurawa Inayah aure dashi yau.

Wani irin zufa takeyi tanajin kaman iskar dake gurin Bata isarta Dan haka da sauri Neesah ma dake cikin tsananin shock ta Kama umma yaganah sukai daki taqara Mata AC tareda bude suka windows tana cewa"

breath, just breath kada ki Bari Jan numfashi ya tsaya Miki kiyi kokari kijasa.

Kasawa umma yaganah tayi Saida Inayah tashigo dakin tana kallonsu a haukace tana cewa"

Dan Allah ku fadan abinda yake faruwa,
Wane tashin hankali ne zaisaka umma wannan halin?
Anty Hafsat is crying,
Kema Neesah sai zare Ido kikeyi Kun kasa fadamun komai,

Kuka ta fashe dashi tana cewa"

Idan Heart ne ya rasu Dan Allah ku fadamun.

Kasa riqe maganar bakinta Neesah tayi cikin mamaki da qin yarda da abinda sukaji tace"

Inayah Abbi ne fa ya aureki,
Dashi aka daura auren wai,
Shine mijinki yanzu,
Dama akwai aure tsakanin uba da 'ya??....

A jere take Watso kalaman sbd takai kololuwar kasa danne mamakin firgicin dake ransu ita nata kalaman ne suka Riga na kowa fitowa a hargitse.

Kallon rashin fahimta Inayah ke Mata kafin ta kalli umma yaganah da duk tayi wani iri Dan kuwa CM bazai musu qaryaba,
hakama tafi kowa sanin MAJEED ba jahili bane bakuma mahaukaci bane da iliminsa
Idan harya auri Inayah hakan na nufin bashine ya haifetaba kenan tun asali....to wannan wane irin masifa ce Zata sakasa auran yarinyarda take matsayin 'yarsa Koda ba shine ya haifeta ba tasan Dole ba auran dadin Rai ne yayiwa Inayah ba.

Anty Hafsat ce tashigo tana sake samun tabbaci daga uban mijinta Alhaji babbah cewa Inayah dai ba 'yar MAJEED bace Kuma shine dai mijin daya aureta yau Dan haka suyi kokarin ganin sun tausar da ita batareda taqara Masa tension ba akan Wanda yake ciki yanzu.

Da rikitaccen yanayi Inayah ta maida kallonta kan Anty Hafsat data shigo dakin cikin kosawa tace"

Anty Hafsat meke faruwa dan Allah?Bazan iya daukan wannan shirun da kowa kemun ba,
Maganar Neesah ma Ni Sam bangane itama me take nufiba.

Ahankali Anty Hafsat takama hannunta suka nufi Inda umma yaganah take ta zaunar da ita itama ta zauna suka sakata tsakiya itada umma yaganah ahankali ta kalleta cikin sanyin murya tafara cewa"

Inayah bamusan komai dayasaba kokuma yazama sanadi komai for now Amma dai abinda yake gaskiyar zance shine aurenki da Abdulsamad Bai yiyuba Amma aure kam kaman yanda aka sanar Mana tabbas andaura Miki aure da...

Dan shiru tayi tareda kallon umma yaganah dake saurarenta itama Dan Hafsat din tafisu sani da fahimtar komai da kyau tunda itace tayi waya da mijinta yayi Mata bayanin komai hakama Alhaji babbah yayi Mata bayanin komai qarshema yanzu driver na hanyar zuwa daukansu su duka zuwa gurin Alhaji babbah din Dan shine kadai zai iya yiwa Inayah bayaninda kila Zata fahimta.

Kaman daga sama sukaji Inayah din tace"

Da aka fasa aurena da heart sai aka daura mun da Abbi???
Right?
Shine abinda kikeson fada mun?

Shigowar zubbi da sakon isowar driver daga can family house yasa Anty Hafsat dojewa amsa tambayar Inayah din Dan haka ba Bata lokaci takama hannun Inayah din Umma ba Bata jira komaiba ta sauko gadon tareda miqewa ta zari mayafi suka fito Dan kowa matse yake da a wayar Masa da Kai akan wannan sauyin lamari Mai wuyar ganewa.

Koda suka Isa gidan Alhaji babbah na masallaci sallar la'asar Dan haka Saida suka jira ya dawo a babban Palo Haj mama na sake yimusu nasiha a fakaice Dan ita saima taji tafi jin dadin MAJEED daya aure Inayah Dan kuwa da tun farkoma sun San bashine ya haifetaba baida alaqar Jini tako Ina da ita da tuni sun matsanta Masa ya aureta yafi fashe fashen aurenta da akaita Yi shima Kuma ga lokaci yaja Bai taba aureba ace haryanzu matsayin saurayi yake Dan haka Kai tsaye ya bayyanarda farin cikinta ana fada saidai Kuma ta tausayawa Inayah sosai ta yanda Rana tsaka Zata karbi zamanta ba 'yar mahaifintaba datake tsananin so da kauna amatsayin ubanta ita daya.

Kusan Banda Inayah data kasa fahimta bare yarda har lokacin
Sun Gama fahimtar dai Abbi bashine ya Haifa Inayah ba Kuma shine mijinta a yanzu.

Duk sun gane wannan abinda basu ganeba shine meya Hana a daura auren da Abdulsamad.

Alhaji babbah na dawowa daga masallaci suka dunguma palonsa lokacin har CM ma ya iso Yana gidan.

Zama kowa yayi jiki a sanyaye Musamman Inayah da kusan komai Bata ganewa Takoma kaman wata mutum mutumi.

Ita Alhaji babbah yafara kalla cikeda tausayawa da kulawa kafin ya maida kallonsa kan umma yaganah datake Babba zatafin fahimtar komai Kuma idan ta fahimta komai zaifi tafiya daidai Dan itace Zata ringa dorata a hanya akan auren da haqqoqinsa tunda tare suke rayuwa gida daya.

Gaisawa suka fara Yi kafin ya Dora da fadar"

Haj yaganah ya fama da hidima da jama'a?
Allah yasa angama lafiya yakuma sanya Alkhairi.
To wani babban Al'amari yafaru tsakanin shekaran jiya zuwa jiya da Kuma yau din kafin daurin aure Wanda yasa aka samu sauyi cikin qurarren lokaci.,

Shi aure nufine na Allah Dan haka kada kuyi Wani mamaki da Al'amarin ubangiji,
Inayah dai kaman yanda a da MAJEED shine jigonta yanzuma shine jigonta Kuma ma'ishinta Dan kuwa shine mijinta haryanzu yafi kowa iko akanta.

Basai an tsaya tone toneba anan ko dogon bayani Wanda Zata samu daga baya idan ansamu komai ya lafa
MAJEED dai bashine mahaifinta ba Kuma yada alaqar Jini tako Ina da ita bamu kadaiba duniyama Bata taba sanin da hakanba sbd riqon Amana da Gaskia da yayi Mata da zuciya daya Kuma a wannan duniyar abune Mai wuya samun irinsa Dan kuwa ko 'dan jininka baka riqewa ba Amana irin hakan Amma shi ya riqeta ya reneta da Amana da kauna bai taba barin tasan bashine mahaifinta ba idanba yanzu da hakan ta bullo ba Rana tsaka shima Kuma hakan da yayi yayine duk akanta sbd har gobe itace kulawarsa.

Shi Dr Abdul dai anfasa aurensane sbd uwarsa daya ubansa daya da Inayah Wanda shi wannan bayanin ba hurumin shigata bane
Dan hakan Ina fatan Kun fahimci yanayin da aka shiga dakuma wandama zaa Shiga Nan gaba sbd Koda Wasa karnaji anyi wata fitina kokuma tashin hankali akan wannan auren,
Shima MAJEED din danasan yafi kowa shiga mugun yanayi akan wannan auren nai Masa nasiha Kuma Inshallah Ina fatan ya dauka.

Dan hakan Haj yaganah sai anyi kokari gurin fahimtar dasu wasu abubuwan aure ya wuce mutum yayi Masa daukan dayaga dama,
Allah ya sanyawa auren albarka,

Suma can Allah yabasu ikon warware komai lafiya.

Waiwayowa yayi zaiwa Inayah nasiha akan itama saita dauki qaddara sbd da tashin hankali samun kanka irin wannan yanayin sai ganin sukai tana Jan numfashi alamar attack Zata samu
Kafin suyi wani yunqurin tasamu attack take Dan haka a rikice suka dauketa zuwa cikin gida.

Allah yasa akwai likita taredasu Neesah taredasu Amma bada ita akaje palon Alhaji babbah ba
itace tayi gaggawar fara taimakawa Inayah din wadda takejin kaman zata rasa ranta sbd yanda numfashinta ke Neman yankewa Neesah na taimaka Mata gurin janyosa da karfi.

Ganin kaman Al'amarin zaiyi girma sosai Dole suka Kira Dr farhat wadda kafin ta iso suka dunguma da Inayah din zuwa asibiti sbd tuni umma yaganah takira Abbi ya sanar Masa yace su wuce asibiti gashinan zuwa asibitin.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/31, 9:43 PM] +234 703 926 9802: *_32_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Private hospital din dake anguwarsu Alhaji babbah aka kaita sbd kafin suce sunje AA specialist wato private hospital dinsu akwai nisa daganan da hakan suka tsaya tanan kusa.

Cikin gagawa suka karba Inayah din
Neesah ma bata barmusu aikinba su kadai da ita sukayi Dan sunada fahimta tana sanar dasu itama likitace suka barta ta taimaka musu tunda dama itace kusan tasaba taimakawa Inayah idan irin hakan ta taso.

Umma yaganah gabaki daya kanta neman sake cakewa yakeyi da wannan Al'amuran daketa faruwa daga wannan sai wannan,

Har cikin ranta takejin kauna Mai tsafta da tsanani akan MAJEED da Inayah sbd sune danginta itace danginsu Dan lokuta da dama sukan mantama basuda alaqar jini da juna.

Badan a yanda yanayin komai ya fallasa kansa ba lokaci daya ba zato ba tsammani da Babu Wanda zai kaita murnar Auren MAJEED datake addua da fatar gani tsawon shekaru.

Hakama auren Inayah wani babban burinta ne shima datake fatan Allah ya nuna Mata ya cika a yau din
sai gashi Allah yacika Mata burin Auren dukansu a yanayinda Babu wanda yataba tsammata,

Ku kansu basuma San farin ciki zasuyiba ko damuwar sanin ba Abbi ne ya haifi Inayah ba.

Anty Hafsat ma zuciyarta kusan Kashi Kashi take kasuwa tana rarraba Mata tunani sbd ayanzu Bayan Jin bayanin yanda Al'amarin yake daga bakin Alhaji babbah taji zuciyarta na farin ciki da auren Dan kuwa Inayah Allah yayimata kyakkyawan sauyin dayafi duka tarin mazan data rasa abaya sbd Abbinta yakai kowanne level da ake kwadayin namiji yakai badan tashin hankalin halinda Inayah tashigaba da a fili Zata fara bayyanarda farin cikinta akan wannan tsintar damu akala da Inayarsu tayi Dan kuwa Abbi kam Masha Allah.

Sbd wadda tasaba ji da matsalarta na kusa yasa ma'aikatan asibitin Basu Sha wuyar taro yanayinta ba tadawo hayyacinta saidai take bacci ya dauketa sbd kusan wannan attack din yafi wainda tasaba samu abaya.

Kwantawa hankalinsu yayi ganin tadawo daidai tasamu bacci Amma kallo daya zakawa fuskarta ka gano baccin na tattareda yanayin firgici data shiga.

Suna zaune a dakin datake anty Hafsat na kokarin daidaita ACn dakin da yayi yawa umma yaganah Kuma na zaune tana kokarin amsa wayarta da Mimi ke Kira saigashi ya iso yashiga dakin cikin nutsuwa sanyeda Lululemon wears har lokacin da alama Bai tsaya sauyawaba zuwa wasu manyan kayan.

Fresh skin dinsa daya bayyana sosai cikin kayan anty Hafsat da Neesah suka kalla suna sake tabbatarda kyau da tsarin da Allah yayiwa Abbin
Take suka sake Jin tabbas ta wannan fannin Inayah Dinsu tagama dacen miji illa kawai baqin cikin dazata Shiga sanin Abbinta datafi so fiyeda komai baida alaqan Jini da ita
Tsintar yayi,kyautarta akai Masa kokuma tayaya ya sameta Allah ne kawai yasani saishi da umman Abdul din.

Cikin girmamawa anty Hafsat da Neesah sukai Masa sannu da isowa

Da qaramin sauti ya amsa Yana dan kallon Inayar kafin ya kalli anty Hafsat sbd umma yaganah na waya yace"

Doctors din sungama dubata ne?

Neesah ya nisan yanayin nata?

Firgici ne kawai data shiga ya daketa sosai Amma Inshallah lafiyanta kalau yanzu anmata allura ne sbd tayi baccinda kanta zai Dan warware ya rage Mata tashin hankalin.

Gyada Kai yayi ahankali tareda sake kallon Inayah datai wani iri cikin lokaci qanqani.

Dan gajeran numfashi ya sauke tareda juyawa yafita zuwa ganin likita Dan bayason ta kwana a asibitin gida zasu koma tunda suna tareda qwararrun likitoci a gidan.

Fitarsa da mintuna biyar sai gasu Mimi sun iso asibitin a gigice sbd tashin hankali biyu,
Na farko Jin auren MAJEED da Inayah dakuma Jin uwarsu daya ubansu daya itada Dr Abdul ga qarin halinda Inayar tashiga.

Jigum jigum sukai a dakin wasunsu na sake Dan jajanta wannan alamari da masu godewa Allah da baa Riga an daura aurenta da Dr Abdul dinba dan da abin yafi lalacewa.

Umma dai bayan taga Inayah ta tashi babu abinda take fata Dan ita kanta yanzu tanajin dacin da Inayah Zata Shiga,.

A sanin dataiwa Inayah kuka da baqin cikin dazata Shiga na zaman Abbi ba mahaifintaba zaifi Mata ciwo da radadi fiyeda auren Dan kuwa tafi buqatan ace alaqar jini suka hada Bata auratayyaba.

Har yamma lis suna asibitin Inayah Bata farkaba sai magriba.

Tana farkawa takasa kallon kowa a dakin sbd yanda duk sukai jigum jigum yabata tabbacin abinda yafaru kafin zuwanta asibitin Gaskia ne haqiqanin Gaskia Kuma Dan haka Batasan ta Ina Zata fara bayyanarda babban abinda takeji tokare da zuciyarta da maqoshinta.

Cikin kulawa da sanyin jikin yanayin da Inayah din ta nuna umma yaganah da Anty Hafsat suka fara kokarin magana saiga shigowar Abbi Wanda Yana shigowa qamshinsa ya gauraya dakin suka tsit suna jiran abinda zai faru Kuma ga Inayah din ga Abbi a amatsayin ma'aurata.

Yanayinsu yasashi basarwa tareda Dan kamewa ya kalli Inayah data dago ta zuba Masa Ido tana Neman fashewa da kuka yace"

Kina farkawa Kuma Zaki fara wani kuka agurin.

Neesah dake gefenta ya Dan kalla yace"

Ku shirya gida zaa koma da ita yanzu.

To" Neesah tace tana kallon Inayah din dake kokarin fashewa da kuka Amma takasa sbd abun datakeji ya girma qwaqwalwarta.

Juyawa yayi ya fice suka biyo bayansa.

Anty Hafsat motar CM zatabi itada Mimi da Safnah
Su Kuma su Inayah din motar Abbi zasubi Dan haka suka nufa motar Kai tsaye umma yaganah na riqe da hannun Inayah dake kokarin zubewa sbd tangadin datake na Bata cikin cikakkiyar nutsuwarta.

Kaman yanda suka Saba fitarsu da Abbin idan takama Inayah ce a gaba Dan haka yau dinma itace agaba sai umma da Neesah a baya.

Bayan sanyin Ac na motar da qamshinsa daya cika motar Yana zagayawa Babu Mai ko motsi acikinsu kaman ba kowa a motar kowa da tunanin daya shiga Banda Inayah da har lokacin qwaqwalwarta Bata fara aiki daidai ba dif take Bata ji Bata gane komai yanzu.

Suna Isa gida Dole Neesah ce ta kamota suka nufi ciki tana kokarin kaita bedroom dinta ta qwace Takoma Palo tana kokarin bin bayan Abbi cikin dimauta tana cewa"

Abbi ne kawai zaifadamun Gaskia na yarda da abinda duk ake fada,
Abbina ne kawai zan yarda da maganarsa.

Da sauri umma yaganah ta riqota tana cewa"

Ki nutsu Mana Inayah,
Me zakije kice Masa yanzu?
Bakiji anfada Miki yanzu mijinki bane,
Qarya zamu taru mu Miki ne?
Alhaji babbah zai Miki qaryane?
MAJEED din dakikeson saiya fada Miki komai Yana cikin damuwa sosai bakya gani?
Zaki sake daga Masa hankali da kukan Nan nakine idan kikace rikicewa zakiyi.

Rikitaccen Kuka ta fashe dashi Mai tsananin qunci tana cewa"

Ni bazan yardaba wlh abbin ne mahaifina,
Banason kowa a mahaifi sai Abbi,
Har umman Abdul din banaso amatsayin uwa Ni Abbi ne kawai uwa Kuma ubana...

Da sauri umma ta rufe Mata Baki jikinta na rawa sbd jikinta daya fara sanyi itama da irin kukan da Inayah din fasawa Wanda tunda take Bata taba yin irinsaba sai yau.

Rirriqeta sukai ta zube qasa tana sake tsananta kukanta zuciyarta na Mata wani irin zafi da radadi...

Idan ba abbine mahaifinta ba ai ita asaran duniya da baqin cikin duniya tana cikin cikinsa da wannan mummunan labarin da gwara ayita fasa aurenta har abada akan wannan labari...

Bazata taba yarda da maganar kowaba sai taji daga Abbinta cewa gaske bashine ya haifetaba.


Dukkanin sautin kukan datake yanajinsu Amma Bai iya zuwa Inda suke dinba Dan kusan yafita baqin ciki da wannan bankadar,
Dan yaso ya tsaya a ubanta na har abada saidai qaddara Bata bar hakan ba Dan kuwa Koda warware auren Nan akayi har abada ita zaa Kira da matarsa ta farko wadda tafara daukan igiyoyin aurensa haka itama har abada shi zaa Kira da mijinta na farko daya fara riqe martabar aurenta.

Kuka Inayah da tashin hankali sosai tashiga lokaci daya Wanda ya gigita umma yaganah da Neesah harma dasu zubbi da Salimat sun Shiga tashin hankali da damuwa sosai ganin halinda Inayah din ke ciki

Ta bangare daya shi kansa Mai gidan babu Wanda yakuma ganinsa har washe gari,

Abincin gidan ranar haka aka daukesa aka fitarwa Bosco ya rarrabawa securities din anguwar abokanansa sbd Babu Mai nutsuwar cin wani abinci.

Da zazzabi Mai zafi Inayah ta kwana Dan kaman yarinya qarama Takoma musu daqyar baccin wahala ya daukeda jikinta da mugun zazzabi.
MAMUH#
#LOVE/ROMANCE


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107*_33_*
*_Arewabook@Mamuhgee_*
Da zazzabin ta tashi da safe Dan haka sallah kawai ta iya Yi Takoma ta kwanta sbd tsananin ciwon Kai Dana kirji,

Ana Gama breakfast umma yaganah ta sallami baqinta aka kaisu aka sanya mota tareda Dan abin arziki gidan yasake daukan tsit.

Su zubbi tuni suka shirya komai a dining na breakfast kaman yanda suka Saba.

Umma dai a dakinta tayi breakfast din Neesah ma bata fito dining ba Dan a daki Tasha tea Danma sunyi sunyi Inayah ko tea din Tasha taqi.

Har lokacin bata daina tsiyayar hawayeba,
Takasa yarda da wannan qaddarar lokaci daya wai ace Abbinta shine mijinta,

Tayaya Zata fara fuskantar wannan maganar,
Har abada bazata taba iya karban Abbi amatsayin mijintaba sbd haramun nema agunta kallon Abbi a matsayin Miji ba uba ba.

Daga Neesah har umma sunyi rarrashi da nasihun harsun gaji Amma Babu sassauci a lamarin,
Gabaki daya fuskarta ta sauya sbd kuka.

Anty Hafsat ma tazo tayi nata rarrashin Amma Dole haka zasu hakura sbd dama bazai yiyu ka karbi irin wannan ba lokaci daya.

Gabaki daya wunin basuga Abbi ba sbd yafita tun safe gurin sallamar baqinsu na nesa dazasu wuce Kuma akwai wainda zaiyi meeting dasu kafin su wuce din.

Da farko mantawa yayi da auren daya rataya akansa jiyan sai daga baya bayanma ya daga waya zai Kira Inayah.

Dan rinte Ido yayi tareda maida wayar ya ajiye Yana fitarda Dan numfashi Mai zafi.

Miqewa yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwan Yana gogawa fatarsa sabulun mountain water soap na Creed.

Sai bayan wasu Yan mintuna yafito daureda blue towel a qugu yafara shiryawa.

Cikin dark blue kaftans yafito da blue hular kube Bai wani shiga can palonsu ya fice daga gidan sbd jiransa da ake.

Sai Bayan azahar Inayah ta iya tashi da daqyar takai kanta toilet tayi wanka.

Sallah tayi tazauna tareda janyo wayarta tana sake saka kiran Heart dinta Wanda yanzu Kuma hankalinta ya karkatane akan taji yanda yake sbd tasan Yana cikin matsanancin halin shima.

Wayarsa har lokacin bata Shiga Dan haka tasake daga hankalinta da wata qarin damuwar.

Dole anty Hafsat da Neesah da umma yaganah sukai Shirin tafiya dubosa asibiti Dan dama suma duk sun damu dason sanin halinda yake ciki din tun iya basuda labarin komai akansa da mahaifiyarsa Kuma mahaifiyar Inayah.

Abbi umma yaganah takira ta sanar Masa zasu tafi dubo Abdul din Bai hanasuba yace suje.

Har Zata kashe Kai tsaye a nutse cikin kamewa yace"

Kar kuje da Inayah ta zauna gida.

Ok shikenan.

Inayah taji lokacinda Abbi yace kada aje da ita Dan haka hankalinta yaqara tashi da sauri tadauki wayarta tareda saka kiransa.

Ringing wayar tafara
Lokacin Yana tareda dasu CM da wasu school mates Dinsu da duk sunzo daurin auren sbd kowa nata kokarin hulda dasu shida CM yanzu sbd ganin sun Zama abokan manya sbd kudi.

Dan waiwayawa yayi gefensa da wayar ke ajiye ya kalli wayar a natse yaga Inayah ce me Kiran yakuma San Sarai roqonsa zatai akan binsu shikuma bazai taba barin ta hadu da Hadiza ba ayanzu Dan haka ya dauki wayar a kame yace"

Yes,Inayah.

A marairaice da alamar kuka tace"

Abbi Dan Allah zan bisu inason dubo Heart Nima,
Abbi Dan Allah kada ka hanani....

Bakida lfy Babu Inda Zaki kina wannan kukan
Kisha magani ki kwanta.

Kashe wayar yayi tareda ajiyewa Yana  maida hankalinsa kan maganar dasukeyi.

Hawaye tafara tana kallon wayar
Su umma na ganin haka suka fice suna cemata saisun dawo.

Zaunawa tayi bakin gadon dakinta Tana cigaba da tsiyayar hawaye sbd tana tsananin buqatan son ganin Heart Dan taga yanayinda yake ciki.

Wurgi tayi da wayarta kan gado tana cusa fuskarta cikin tafukan hannuwanta zuciyarta na radadi.

Hannu takeson dorawa akai ta ringa zumduma ihu da birgima ko zataji sassaucin tsananin qunci da damuwar dake ranta.

Tayaya Zata iya cire soyayyar heart daga ranta bayan yayiwa zuciyarta kyakkyawar Shiga?
Tayaya zasu iya rabuwa da juna sbd kalmar uwa daya uba daya da ake dangantasu da ita?

Batada uban daya wuce abbi Kuma batajin Zata daina daukansa ahakan kokuma daina kallonsa ahakan.

Abbinta fa ake maimaita Mata kalmar mini agurinta.

Kasa riqe kukan tayi ta kwanta agurin tafara rero kuka tana sake Jin zuciyarta kaman zata kama da wuta.



***Su umma yaganah kuwa koda suka Isa asibitin da Dr Abdul yake hankalin Yan uwansa da mahaifiyarsa atashe yake sosai fiyeda tunani Dan kuwa Dr Abdul dai jiki ya rikice.

A jiyan da aka kawosa asibiti daqyar aka samu ya farfado ya kalli mahaifiyarsa da hankalinta ya rarrabu cikin tashin hankali masu girma sbd labarin auren MAJEED da INAYAH ya gigitata sosai,
Zancen ya daketa har Batasan lokacinda itama ta zube qasaba jininta na Neman hawa.

Tabbas AA MAJEED ya nuna Mata shi namijin duniya ne,
Ya Sha gabanta ta hanyar aure Inayah sbd baida niyar bata 'yarta,
Tabbas Babu shari'a yanzu Kam da Zata karbar Mata Inayah daga hannunsa Amma Kuma idan har Inayah Bata son wannan auren Koda abinda ta mallaka zai qare duniya kowa ya juya Mata baya saita tsaya Sharia ta raba auren anbata 'yarta.

Su Haj balaraba dasu Alhaji buhari saidai su Alhaji kabiru sukai musu bayanin cikin daya bayyana jikin Hadiza bayan shekaru Wanda yayi sanadin dasuka koreta daga gida
Saidai yanda komai yafaru Bayan barinta gidan shine Basu saniba saisunji daga gareta dashi AA MAJEED din Dan yanzu sune kadai zasu qarasa warwarewa kowa wannan qullin da tunanin dasuka shiga.

Haj balaraba kuka ta ringa rerawa tana yiwa salisu addua suna qara godewa Allah da baa daura wannan aureba da basusan iya Ina tashin hankalin zai kaisuba.

Hajiyarsu suka kira suka Dan sanar da ita komai a taqaice to dayake tasan da maganar cikin da haihuwar bayan barin Hadiza gida daga bakin jama'a Amma tayi shiru ta lafe sbd tunanin ko cikin banzane Hadizan tasamo daga Lagos sbd kada a dangantasu da cikin Tai shiru taqi Kuma barin 'yayanta ko daya yasani dan kada suce zasu karba tunda ba tabbas hakama Hadiza ta sameta takanas da jaririyar Amma shedan yaqi Bari ta amsa.

Tsufa ya kamata sosai yanzu Amma itama haka ta ringa kukan danasani da farin cikin da aka samu Ayshatouh take zancen yafara fita a dangi saidai halinda Abdul ke ciki yafi daga hankalinsu akan murnar bayyanar wadda basuma San da itaba a zuriar.

Dr Abdul mummunan shock din daya shiga ya daki zuciyarsa zuwa qwaqwalwarsa sosai Dan haka ya jima Bai farfado ba Kuma ya a farfadowa ummansa yafara zubawa indanuwansa dasukai mummunan ja yana kallonta cikin karaya da mutuwar dukkanin jiki yace"

Umma since Inayah 'yarki ce itama kece kika haife shiyasa bazan auretaba Abbi ya aureta
Ni nakasa gane komai
So kawai naji daga bakinki idan kece mahaifiyar Inayah tayaya AA MAJEED zai Zama ubanta?

Umma Dan Allah kicemun ba kece kika haifetaba,
Kicemun bakida alaqar komai da ita sai wadda zamu qulla yanzu ta auratayya,
Umma Dan allah kice bakece uwar Inayah ba bakida alaqan komai da ita...umma bazan iya rayuwa Babu Inayah ba kinsani akanta zan iya rasa hankalina

Please Login or Register in order to submit comment