gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu Chapter 6 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tafi har Jama'are wurin"

"Kakanmu, suka tawo tare yadda mutumin nan yake da mugun hali na tsane na bude idanun na ganshi, domin shima ya taka rawar lalata min duk lissafina, haka yayi ta fada da nuna kada ya ji kada ya gani domin yaji labarin ana son a kashe auren Lubnah da Hafiz, idan suka kashe auren waye zai aure ni?"

"Sannan ga misali a gabansu Jalilah tunda aurenta ya mutu waye ya zo da sunan zai aure ta, kada ya ji"

kada ya gani.

"Abin da basu sani ba ita Jalilah Ya Hafiz take so kamar tayi hauka, duk aurenta uku da tayi ta kasa zama a"

"gidan aurenta ne domin tana da yakinin wata rana ya Hafiz xai dawo gare ta. Haka abin ya cigaba da tafiya ba dad'i, a lokacin Ya Hafiz ya tsiro da wani hali shi da Matarshi."

"Abinda suke mun ba kome ba ne, sai nuna min da suke ni rayuwata bata da amfani, domin ido da"

"ido ya ce min. ""Lubnah baki da amfani a rayuwata, amfaninki kalilan ne, idan aka cire amfanin rashin"

"amfanin yafi yawa, kin ga wallahi ko bukatarki na dabi'ar da namiji bana ji, ke kanka dube ki, yanzu ace"

"na sake ki waye zai aure ki? Wallahi babu namijin da zai tab'a sha'awar aurenki domin baki da wani abin burgewa mace sai kace saniyar huWa! "" Ire-iren waWannan maganar da yake gaya min ya haifa min da"

wani irin yanayi.

"Yana yawan gaya min cewa a yanzu dangi ma basu bukata na, babu wanda ya damu da ni, itama"

"Hindatu don kudina da yake hannunta ne, idan babu ba zata kara kula ni ba,haka muka cigaba da jin kamar ba ni da wata amfani a rayuwar Ya Hafiz. Tunda ban haihu da shi ba, bani da wani abun da zai burge kowa. Ni kaina nasan be zama dole wani ya bukaci ni a rayuwarsa ba. A hankali na dinga jin kamar"

ni din ba kowa ba ce bani da sauran amfani.

"A haka watan azumi ya karato, ba zata Baba yayi mana, ya biya mana umara ni da Yayuna. Sai dai me?"

"Ya Hafiz najin haka yayi ta kunci da bakin rai tare da rigima da fitina kala-kala, karshe dai ban san yadda aka kare ba Baba ya ce ya cire sunana a cikin masu tafiya yayi replace da Jalilah. Wani irin bugawa zuciyata tayi kamar zata fito, a hankali na kama dariya ina jin kamar ni daya ce bani da amfani a duniyar nan, haka watan azumin nan suka yi shi a can ni ina gida, a lokacin na kara koyan yadda xan bawa kaina nishadi. Sai na fara tunanin sana'a bayan sallah, wanda shima a wunin sallah ya ce ba zan je ba. A Jama'are zamu yi sallah, nan ma na amince muka tafi. Muna dawowa nazo da madaran kuka. Na fara sayar da kankara da Pure water, ta nan bai hana ni ba. Sai dai ya daina bani kudin cefane. A hankali na kara har da zobo da kunun aya da fresh milk. Haka su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka zo min gidan, wuni da Yaransu nayi ta hidima gashi bana iya zama idan nayi baki abu ba abu ba sai dariya. Haka suka yi"

"ta kuka a daki, wunin da basu yi ba kenan."

"Wani abin da na fahimta shine Ubangiji ya saka albarka a kayan ruwa, domin lokacin sallah layya, nayi"

"ciniki har na ji tsoro, ana kawo min ruwan pure water har gida ake sauke min rabin mota, a lokacin da Ya Umar yazo gidan ya dauke karamin firji din a ranar aka kawo min babba deep freezer, wnada nake zuba jakan pure water ashirin ga kayan sanyina a gefe. Yadda kudi suke shiga da fita yasa Ya Hafiz ya fara tashin hankali na fara kudi xan rena shi, idan nayi abinci bana saka nama a wadace ai da can ba haka nake ba, nayi ta bashi hakuri ashe zai zare min tallafi da yake ne, domin ya daina kawo abinci gidan. Haka dai na kara tsayawa a tsaye sai Allah ya yaye mun dariyar da nake, sai dai duk niman da nake ina bawa"

Ya Hafiz ne domin bayan na cefane da nake yi kudin kusan shi nake bawa.

"Maman Na'ilah ita ce ta tambaye ni aron kudi, na ji tsoro ban iya bata ba. Karshe kamar wacce ta"

"matse ni na gaya mata ai kudin wurinsa yake, zuba min idanun tayi kafin ta ce min. ""Lubnah da hankalinki kuwa?"" Shiru nayi kafin ta cigaba da cewa.. ""wacce irin soyayya kike yiwa mijin nan naki ne? Kin san mun san kece kike dauke da hidimar gidan?"" ""Ba kome ai dan uwana ne."" ""Na ji ba wannan ba,"

"daga yau zaki na kawo dubu uku akwai adashe da muke yi zaki shiga ai zaman tare ta wuce haka, ga"

"yayarki nan wata siririya muna haduwa a asibiti ba karamin taimako take min ba, don Allah ki na kawo kudin! "" "" In sha Allah!"" Na fada tun daga ranar ban yarda na kai mata ba, domin kamar wanda aka"

"gayawa Ya Hafiz, kullum sai ya kirga abinda nayi yasan na kudin da yake ciki, idan ya dawo zai tambaye ni."

"Haka zan dauki kudin cinikin na bashi na mishi lissafin abinda aka kashe, ita Matarshi bata kome ni ce"

"dai akansu, haka dai muka ta mikewa abin ba dad'i, kwatsam aka tashi wani biki, Aunty Innah ta kawo min aikin Kunun aya da zobo, domin suma ina bayarwa a kai musu har gida, a lokacin aikin zai min yawa na shiga gidansu Maman Na'ilah na roka su zo su tayani. Haka muka yi aikin dasu. Sannan ka zo aka dauka, washi gari muka sake yi sai da muka yi kwanaki uku muna aikin kafin aka kawo mana kudin aikin naira dubu hamsin, na dauki 20k na basu talatin, Maman da tazo ta kwace ashirin din ta tafi da shi, ban san me yasa matar nan take min karan tsaye ba, amma naji haushi, wasa wasa sai ga Mamansu Na'ima ta saka ni a gaba da amsar kudina ko ina so ko bana so zata dauka, haka muka yi ta fama da ita daga baya da kaina nake tura mata kudin ma, ta daina zuwa. Ban san manufarta ba amma tabbas ta wani"

gefen tayi min abinda jinina suka gaza min.

"Haka watan azumi ya kara zuwa, ita ta bani shawarar na ajiye kayan zai na koma sayar da anara. Ba"

"sai ya Hafiz yayi tsaye ya ce bai yarda ba. Sai dai idan zan sayi generator, na ce mishi. ""Ya Hafiz tow ka ba Ni a cikin kudin wurinka mana!"" Ai kamar ya rufe ni da duka. ""Ba zan bayar bada wutar gidana kike amfani."" A lokacin na rasa yadda xan yi ina jin kunyar amsar kudin wurin Maman Na'ilah, sai na kira Ya Sani na tambaye shi nawa ne kudin generator? Tunda sune suke sayarwa. Ashe nayi wayar a kusa da Ya Albashir, sai cewa yayi me zanyi da shi? Na gaya mishi gaskiya washi gari sai ga Mikano daidai da zata"

dauki freeze na har da karin freeza.

Nayi ta godiya aka turo masu aiki suka min aikin tsaf na sauka akan wutar gidan Ya Hafiz shima dai ai

"yana morar generator tunda kowa yasan watan azumi a lokacin nepa suka tadda iskancinsu, ga lokacin ana wani irin agazarin rana."

"Duk yadda xan fada farin cikin da nake ciki, kamar na boye ne. Ganin duk yadda zai Sullo min ina"

"toshe hanyar don bana son muna rigima, ba sai ya tsiro da fitinar cewa sai dai na kama haya dakin da nake ina biyan kudin wata wata da ruwan da nake tarawa a wajen shima ina biya. Haka na amince na ce nawa xan biya? "" "" Duk wata dubu goma! "" Shiru nayi kafin na ce mishi.."" tow Ya Hafiz ba ragi ne? "" "" Sai dai ku fitar min da kayanki a gidana!"" "" Shi kenan! "" Haka na amince ai ba wani abu ne, haka nayi ta niman kudi ya Hafiz yana amsa da sunan nashi, da sallah yayi nayi musu Winkin sallah don ya ce min hakkina ne nayi musu tunda ai ina samu, nayi mishi nayiwa Yaranshi da matarshi da Yan'uwansa na tura"

"har Jama'are aka kai musu, har da Baban Jama'are nayiwa Baba Malam ne ko da wasa ban mishi ba, ai"

"kuwa na sha zagi ya kira Baba ya gaya mishi, Hafiz ya bani kudi nayi musu kayan sallah amma naki, haka"

"Ya Hafiz ya fada. Sannan ya kara da cewa har su Mama da Yadiko nayiwa, amma a kuWina a lokacin sai da na kwashe kome nawa na sayar har da dan kunnen gwal dina, tow bani da kudin ina sana'a kudin na"

hannunsa.

"Bayan sallah ina cikin azumi sitta shawal, na fara sauraron karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i"

wanda ban tab'a jin kalmar ba sai yau. Ba dai na kara nutsuwa ina sauraren dalilan da suke kawowa ayi shi..

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAAR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

PAID BOOK

TAKWAS

"Wato akwai wani abinda hankalinmu baya kai sai wani dalili mai girma ya shato shi cikin rayuwarmu, ban"

"tab'a nazari akan khulu'i ba, amma kuma me yasa na damu? Me yasa nake son sani akanshi? Kawai sai naji abin bai min na cigaba da nazari akai ba, kawai zan cigaba da zama da fahimtar iyayena. A bangaren Ya Hafiz kuwa nadan wata rana zai dawo yadda muke zai kaunace ni sama da baya, amma kuwa zai yi"

haka.

Bayan sallah da sati uku.

Weekend

"Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake ya jima da na sauke amma da yake yana da"

"wuyar sha'anin, sai na ta saka idanun akanshi saboda Yaran nan da zarar na sauke tukunyar fresh milk sun ta kara kaina akai kenan, har sai na hada na basu. Hankalina yana kan zobo wanda nake ta saurin haWawa. Sai naji an tab'a murfin tukunyar, da sauri na juya Yusrah ce rike da kofi ta bude tukunyar fresh"

"milk din zata har ta saka kofin ta dibo da yake na juya mata baya, a matuar razane na kalle ta ina faWin."

"""Gaskiya Yusrah bakya jin magana maza rufe min ki mai da kafin na zo wurin."" ""Ba zan mai da ba."" Ta"

"fada tana kallon cikin kwayar idanuna, abin da ya bani haushi da takaici yanzu ta kone Iyayenta su ce na konata. Mikewa da zan yi kuwa ta kwasa da gudu ai kuwa sai gashi ta taka ledar Bevimix ta zame bakiWaya fresh milk din ya kware a gefen kirjinta, abinka da zafi sai kuwa ta fasa ihu wanda yayi daidai shigowar Mahaifinta da fitowar Uwarta a dakin, wani irin bugawa zuciyata tayi na tsaya cak kafin na karasa da sauri nace mata. ""Kin ga abinda nake gaya miki ko?"" Na yi maza na shiga daki na dauko kamun da aka niko min zan yi kunu na sha na watsa mata a kirjinta bayan na cire mata rigar, bakiWaya iyayen babu wanda ya ce min ci kaina. Haka na zaunar da ita na cire mata rigar ba wani tashi wurin ba, amma yadda take kuka da ihu yasa Uban ya karaso ya bangaje ni sai da na fadi, sannan ya dauki yar ya fita da ita, wasa wasa basu dawo ba har dare habaici da cin mutumci babu wanda Karimah bata min ba, ni dai bance mata uffan ba, wajen karfe biyar Mama ta kira ni. ""Kin kyauta Lubnah wacce irin kishi ne haka yake damunki?"" Bata ba ni damar magana ba. ""Saboda kishi zaki kyale yarinya kamar Yusra ta kona"

"kanta?"""

"Ni dai asa magana nayi har sai da Mama ta ce min. ""Saboda mugun nufinki Allah ya hana ki"

"haihuwa domin da ya baki da Yaranki zasu dauki mugun halinki!"" Komawa daki nayi na zauna shiru. Haka Baban Bauchi ya kira ni ya ce sai ya ga wanda ya isa min, wasa wasa sai ga al'amarin ya girma yadda ban zata ba, yusrah kwantar da ita aka yi a gadon asibiti. Sannan wacce take gudun Mama ce. A wannan lokacin na ji duniyar ta min zafi, kaf duniya mutum daya ce ta fahimce ni Aunty Hindatu, dole na bawa Aunty Hindatu special respect a duniyata, ita kaWai sai Ya Ado suka fahimci abin domin abin ya faru da kwana biyu Baban Bauchi ya zo har gida ya saka aka kwashe kayan sana'ar aka fita da su. A wannan lokacin Ya Hafiz ya zata ni yayiwa mugunta. Ya zata ni ya rusa tabbas ya Hafiz ya rusa ni, sai da na kusan zarewa domin babu wnada ya saurare ni, kowa ya juya min baya sai Aunty Hindatu da ita Waya ce take rarrashina, kwana Yusrah biyar a gadon asibiti Hajiya da Baban Jama'are suka iso a ranar Karimah ta"

dauki matakin da Baban Bauchi ya goya mata baya.

"Ina zaune wurin karfe biyu na rana aka yi sallama a gidan, fitowa nayi ina amsa sallamar. Yan sanda ne"

"mata biyu suka shigo. ""Sannunku da zuwa!"" Yadda nayi magana a matuar tsorace. ""Kece Lubabatu Usman Umar Jama'are?"" Jikina ne ya dauki rawa. ""Eh nice!"" ""Ok ko zaki zo muje office din Yan sanda!"" Ji nayi kamar ina yawo a saman iska. ""Akan me zan bi ku Office dinku bayan ban yi kome ba?"" ""Eh tow idan muka je zaki ji abinda ya faru!"" ""Tow bari na kira mijina;"" na shiga kiran Ya Hafiz amma bai dauka ba, haka nayi ta kiran Yan uwana har Baban Bauchi na kira Babu wanda ya dauka, sake magana suka yi na fito ko su shigo dakin. Haka na fito a sanyayye da hijab har kasa. Ina kara kiran Aunty Hindatu. Daidai na shiga bayan motar. Dauka tayi tana faWin ""Auta yi hakuri bana kusa ne!"" ""Aunty Yan sanda sun zo zasu tafi da ni!"" ""Akan me?"" ""Ban sani ba Aunty! Don Allah ki zo!"" ""Shi kenan gani nan zuwa!"" Haka ya kashe wayar muka Office din Yan sanda da yake dutsen tanshi, anan na samu Karimah ashe shirinta kenan ita da Uwanta da iyayenta, muka shiga suka amshi wayata da kome suka tura ni cell suka ki min magana, ina zaune wata yar sanda ta shigo ta d'aga hannu tayi ta kifa min mari, yan uwan Karimah suna faWin. """

"Saboda kishi ne ita Allah bai bata haihuwa, koda yake ta kashe mahaifarta da maganin hana daukar ciki"

"shine bari ta kashe yar kishiyarta, Allah ya sa yarinyar ta auna arziki!"" An tozarta ni, an ci mutuncina haka"

"na kasa ko kuka sai sunkuyar da kai da nayi idanuna bana gani. Muryan Ya Hafiz da naji yana ta fada a waje. "" Akan me zaki shigo da hukuma cikin maganar? Ko an gaya miki ban san yadda zan yi ba ne?"

"Gaskiya kin bata min rai yanzu da wani idanun xan kalli iyayenmu?"" Yadda Ya Hafiz yayi ruwa yayi makarbiya yasa ni shiga rud'ani amma ai ya ga kirana. Fada sosai yayiwa Karimah, Aunty Hindatu da Ya Umar da Ya Albashir suka karbi belina, haka na fito kamar wacce ruwa ya mata duka, fuskana ya dan kumbura saboda marin da yar sanda tayi min. A hankali nake takawa har wurin motar Ya Hafiz da ya nuna shi xan bi na je nayi wanka. Haka muka bar office din zuwa gida, a hanya yake cewa. "" Kin san ina sonki, sannan abinda ya faru nasan bakida laifi Yusrah ta gaya min, amma kuma ita mahaifiyarta ba zata ji dadi ba idan na nuna baki da laifi don haka ki amshi laifinki ta haka ne kawai zaki wanke kanki kowa zai gane cewa bada wata manufa kika yi ba!"" "" Ya Hafiz me yasa?"" Na tambaye shi, "" Me yasa ka zabi kuntatta min? Me nayi maka da yake damunka har haka? A sanina ban maka wani abu ba? A sanina ban cutar da kai ba, ina saka ran wata rana zamu koma kamar baya kamar farko-farkon aurenmu, Ya Hafiz duk irin shirun da nayi na cancanci haka daga gare ka?"" Shiru yayi da alamar maganar ya ratsa shi kenan. "" Ka saka kowa ya tsane ni, ka saka kowa yana jin haushina, idan abu ya faru ba zaka gaya musu gaskiya ba sai ka bar maganar a daura min laifi me yasa sai ni? Ya Hafiz rabon da ka nemi ni a shimfidar aurenmu shekara kusan guda dawowarmu zango na gaji wallahi na gaji ka sawwake min nima na gaji!"" Na fada ina kuka domin sai yanzu nake jin kamar bakina ya buWe. "" Ko na sake ki ai baki da wanda zai aure ki?"

"Lubnah ki kalli kanki da kyau har abada babu namijin da zai tab'a jin sha'awarki, Lubnah na ajiye ki ne domin kowa yasan ina oari da mugun halinki, ke har kina da bakin da zaki gaya min magana? Bayan na rufa miki asiri ne, jaka me kama da alade kalle babu abinda wani zai gani na burgewa a tare da ke kazama wawuya, kuma daga hau sai na hana ki farin ciki."" Haka muka isa yana zagina da cin mutuncina har nayi wanka kai karewar masifa kofar ban dakin ya shigo yana cin zarafina. Haka na gama na shirya muka tafi cikin gidan inda Yusrah take da iyayenmu, anan ya min barazanar matukar nayi magana sai ya"

sake Baban Bauchi wato Babanmu ya tsine min shi kuma ya sake ni domin ba zai zauna da tsinanniya ba.

"Lokacin da muka isa gidan Baban Jama'are yana nan haka Hajiya ma, sai Iyayena da yan uwana."

"Tunda na zauna aka bude taron da Addu'a. Aka rufe ni da fada babu wnada ya ji yadda kome ya faru haka na sunkuyar da kaina ina jin Baban Bauchi yana faWin. "" Munafuka ban da kishi da munafunci me kika ajiye ace har degree gare ki ya zama na banza. Sai bakar kishi tow da abinda kike takama da shi na kwashe dama yana gaya min tunda kika fara sana'a kika sauya bakya jin maganarshi, kin yi sabi iyaye masu daura miki mugun abu akanki wallahi kin ji kunya."" "" Amma Baba ya kamata a ji me ya faru? "" Inji Aunty Hindatu, da take wani irin cirra, juyawa yayi a fusace ya zabga mata harara, ya rufe ta da fada da cewa ai ita take zuga ni, haushi ya sa ta bar parlourn ma don bakin ciki haka Baba Malam ya amshi fadar yayi ya ce min. ""Yanzu kin kyauta abin da kika aikata? Da Asiya kike kishi ko da Uwar Asiyah? Yanzu ban"

"da mun fi karfin yarinyar nan ina sai dai kotu ta shiga lamarin nan?"""

"""Malam wallahi ban san cewa haka dai faru ba,.Malam na rantse da Allah ban yi haka domin kona yusrah"

"ba yayi hakuri ba da gayya ba ne!"""

"Zuba min idanu Malam yayi yana faWin..""Allah ya kyauta amma ina amfanin kishi irin naki? Akan ki aka"

"fara kishiya ne?"" Cikin shashekar kuka na ce mishi. ""Wallahi ban san zata shiga ban dakin ba, ka yarda da ni!"""

"""Kai yanzu Hafiz me ka gani?"" Juyawa yayi ya kalli Baban Bauchi wato mahaifina ya ce mishi. ""Duk abinda"

"Baban Bauchi ya ce ai shi kenan!"" ""A'a Hafizillah kada ka cutar da kanka, na ga oarin zaman da ka yi da"

"Lubnah idan ba zaka iya da mugun halinta ba sakota na gaji da kullum ana abu daya a cikin shekaru goma kullum Lubna tana saka ni magana."""

"""A'a Usman, Lubna ko bata auri Hafiz ba, akwai alakar jini balle kuma alaka ce da ta haWa da ta zuci,"

"ai ta ce ba da gayya ta konata ba kuma yadda ake ta ririta al'amarin da na ga ciwon ai ba wani babban al'amari ba ne, lamarin mata ne kawai da ririta lamarin da bai kai ya kawo ba, yi shiru Y'ata share hawayenki. Kul na kara jin wani yayi magana da cewa za a kai batun nan ga hukuma kunar da bai wani tashi ba, ga yadda yayi baki kasan ai ba zai tashi ba, sannan kai Hafiz ka tuna akwai ranar da zamu tsaya a gaban Ubangiji, ka ji tsoron Allah kada son zuciya ya kai ka ya baro ka, kawai jikina yana bani haka kawai"

"Lubna ba zata aikata kome ba."""

"Kunya ce da bori tasa shi, kame-kame amma a cikin ranshi bai so haka ba yasan Baban Bauchi da za a"

bar shi sai ya mari Lubnah shi yanzu yadda zai bakanta mata rai yafi bukata akan wannan abin.

"Duk da an ce yau da gobe bai bar kome ba, Iyayena da dangi babu wanda ya hango mutuwar"

"tsaye da nake yi saboda Ya Hafiz, Babu wanda ya yarda da cewa ina cutuwa, a'a kowa gani yake kamar ba cuta ba ce ni ce nake cutarsa saboda shi mutumin kirki ne, bayan shi ya shiga rigar mutanen kirki ne. Yayi ado da kwalliya a cikinsa, sannan babu wanda zai kalle shi ya ce mutumin banza ne. Amma bakin maciji ne sanye da tufafi yan adam, haka muka bar gidan, bayan an mana nasiha. Ni dai nasan cewa zuciyata ta gama mutuwa bani da wata amfani. A hankali gidan ya zame mini kamar hell fire, bani da kwanciyar hankali bani da sukuni, idan abin ya dame ni sai na rufe kaina a daki na ki fitowa, a hankali abubuwan suka ta tsanani domin kuwa na daina sayar da kome na daina yin kome, shi kanshi Ya Hafiz da ya fahimci bani da wani amfani sai ya cigaba da azabtar dani da abubuwan da zai saka na ji har na tsani"

"zaman gidan, damuwa ya kara tsananta min domin ba wani abu ba ne su min gorin haihuwa."

"Bayan wata biyu kusan watan Mauludi, Ya Ado ya dawo, ni ya fara kira a lokacin babbar wayar hannuna"

"na sayar domin Ya Hafiz ya zo ya saka ni a gaba yana son kudi haka na hada da wayar da sarkata ta gwal na bashi, kunsan me a duk lokacin da zai same ni yana bukatar wani abu tow ba irin yaudarar da baya min, haka zai zo da soyayya ya cutar da zuciyata, har yau ina da yakinin zai shiryu ya daina abun da yake"

min don na fara tunanin kamar shiga tsakaninmu aka yi.

"Cikin murmushi na ce mishi. ""Barka da dawowa yasu Aunty Zakiya? Kun iso lafiya?"" ""Alhamdulillahi"

"Auta nace ke zan fara kira ki san na dawo!"" ""Masha Allah sannu da hanya madalla!"" Yadda muke wayar"

"naki sake jiki da shi, ya sa shi kashe wayar da zai kira wani lokaci, tunda Ya Ado ya dawo Nigeria kullum"

"zai kira ni, zamu gaisa daga nan zan yi shiru. Haka zai ta ja na da hira, har ya gaji ya kyale ni."

"A hankali abin sai ya zame min jiki, sannan ban kara yarda mun yi tashin hankali da wani abu cikin gidan"

"ba, wani abu daya da na fahimta idan na kashe auren ma bani da wani amfani, haka yasa babu amfanin na gayawa kowa halin da nake ciki, sannan kwasar bakin ciki a wurin Ya Hafiz da danginsa kamar shafa ce ta alola. Haka yan uwansa zasu zo musamman Aunty Nana, haka zata yi ta min kome da gadara da iko"

"iko, idan nayi magana zata ce gidan dan uwanta ne."

"Haka zan zuba musu idanu, kome zai wuce amma idan ban mutu ba zan sha kallo. Idan ka kalle ni"

"bani da matsala sam, amma deep in side ina cikin wani irin mugun yanayi ne. Sai dai ba wanda ya san da haka sai wanda Allah ya jarabta da irin halin da nake ciki."

*

"Yau Dan wake nayi shima dai nice nayi cefanen, musamman duk ranar da ya tashi rashin mutunci ni ce"

"zan yi kome har na gidan, ya daina kawo abinci domin kuwa Karimah ta ce mishi ai idan aka kawo kayan abinci sayarwa nake sai dai idan ya tashi ya auno mudu idan ya gadama idan bai gadama ba zai ce na"

"ranta mishi, yasan bani da kosisi. Haka zan ta kame kame har na hada abincin aci."

"Har lokacin Maman Na'ilah bata bani fuskar da zan tambaye ta kudin ba, abu daya take gaya min. ""Duk"

"ranar da zaki yi aikin alkhairi wa rayuwarki in sha Allah zan baki kudinki amma idan har wa Mijinki ne wallahi kwandala ba zan baki ba, karshe ma zance sharri kika min!"". Murmushi nayi da yake tasan ba zan"

"yi magana ba, shi yasa nima na barta."

"""Ke Yusrah kawo min kular Babanki na saka mishi abincinsa tun dazu

Please Login or Register in order to submit comment