gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu Chapter 23 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a saka sannan ya koma wurin aikinsa. Washi gari ya kama juma'a, shima sai da muka zaga unguwarmu sannan na dawo, kayan da aka kawo machine"

"ne na Exercise, Ya Ado yana dawowa daren jiya ya haWa ya gwada aiki da shi a daren jiya."

"A ranar bayan sun fita nima kusan a kai na wuni, dadare kuwa abincinsu suka ci ni kuma na ci nawa"

"tuwon alkama zalla miyar ayoyo, daga nan kuma na sha fruit na kwanta, ranar asabar karfe goma na tafi Gym, sugar kuwa tuni na yi bye bye da shi, wunin ranar Yorghurt na sha daga kuma sai ya rike min ciki. Karfe biyu na bar gym din zuwa gida yau nayi rayuwa da ban tab'a yi ba, sai nake gani kamar mafarki. Ina typing har na iso Unguwarmu, na karasa gida, a harabar gidan na hango Ya Umar wani murmushi ne ya kwace min na isa gare shi, ya dan rungume yana faWin.. ""Auta manya an zama yan gari. Daga Gym ko?"" Gyada kai nayi ya ce min. ""Shiga bari na gama waya na shigo."" A parlourn na samu Mamana, wani ihu da nayi na isa wurinta da gudu na rungume ta, tana buga bayana. ""Sannu Autana, sannu yar jinjirana! Ai tunda suka ce ba zaki zo biki ba nace ban isa ba, zan zo na ganki kada na mutu ban ga autana ba!"" ""Mama me yasa kike kiran mutuwa? Mama me kika kawo min? Mama ina Yadiko?"" ""Suna lafiya tana ta"

"shirin bikin Sani!"" ""Allah sarki!"" Na ji dadi sallah ya tashe mu na ja ta sama, tayi ta mita ita bata son sama, ai kuwa tunda ta hauro tace ba isa da ciwon kafa ba, karshe Abinci ma sama aka kawo mata, ni kuwa dad'i kamar na nutse kasa, tun a daren na gayawa Nasiba ta gayawa Mamanta Mamana tazo daga Bauchi. Kwana muka yi da Mama muna hira tana bani labarin abinda ya faru, hakuri nayi ta bata, karshe"

nayi barci na barta tunda na fara Exercise barci ya daina min wahalar yi.

"Washi gari Lahadi sai ga Aunty Nuratu Kafaya, ita da Mijinta, Mama ta ji dadi nima na ji dadi gashi"

"an hadu ana ta hiran arzikin, sai la'asar Mijinta ya zo ya dauke ta. Koda na zauna ina cikin ganye Mamaki Mama take ta kasa hakuri ta ce. ""Wannan wacce irin rayuwa ce? Yarinyar da rayuwa da ganye ita ba akuya ba ita ba tsutsa ba, Auta dole aka miki ne?"" ""A'a yana cikin kayan karin lafiya ne, idan ina ce kibar"

"zata ragu ko ta tafi bakiWaya."" ""Aiho yanzu na fahimci yadda lamarin yake. Allah ya kara lafiya shi yasa"

"idan na zoma zan ta dafa miki zogale ina shanyawa da rama da yakuwa."" Haka Aunty Zakiyah tayi ta"

"mana dariya, satin Mama biyu ta koma Bauchi ta bar ni da kewarta sai waya kawai muke."

"Bikin saura wata gudu muka fara jarabawa, na kara mai da hankali sosai sai fa muka sha wuta na"

"tsawon wata guda sannan muka samu hutu, rayuwa tana cike da darasi na musamman Ya Ado da Aunty Zakiyah sun tafi, ni kuma na cigaba da kula da kaina, da taimakon Aunty Nuratu Kafaya, sati daya suka yi wanda aka sha biki da karamin gurmi aka dawo aka bamu labarin wai Yan uwa Ya Hafiz da Yan uwanmu ana ta habaici an tura ni karuwanci suna jiran sakamakon bariki, shine fa Yadiko ta rufe Aunty Nana"

"Asma'u da fada ta ce mata. ""Har kina da bakin magana? Karuwanci ai ya kare tunda tana gindinku!"""

Rigima sosai a gefe guda Matar Hafiz itama ta kashe auren ne ko yana lilo oho amma dai ana ta

"rigima tace tunda ta aure shi ita bata gamsuwa, hakuri take da shi. Aka ce Abba kamar yayi hauka yayi ta fada yana rarrashin Hafiz, wannan ya karawa Hafiz wani irin tashin hankali, yayi ta kuka yana rokon Abba ya dawo mishi da Lubnah shi yasa kaf duniya babu Macen da zata iya rufa mishi asiri kamar Lubnah, yadda ya shiga damuwa sosai Abba shima jininsa yayi ta hawa kafin a gama bikin nan sai da ya kwanta a asibiti sau biyu. Abu fa ba dad'i sai gashi har Abba da kanshi wai ya je wurin Mama yana rokon arziki ta dawo da Lubnah, ai kuwa da Abba da Ya Hafiz Mama ta ce sai ta kai su kotu ta ji Uban da suke bukata da"

Lubnah.

HAFIZ

"Don shi kanshi bai kawo a ransa Lubnah ba zata zo ba, saboda yadda ya santa da Sani, amma wani ikon"

"Allah bata zo ba ya kuma kudira a ransa da ta zo sai ya san yadda yayi dawo gare shi yadda ba zata kara barin Bauchi ba sai da izninsa amma dai gashi bata zo ba abin ya bashi haushi, ga Nana da ta gudu ta fasa auren. Gashi ya ga hoton Lubnah a wayar Rufa'i da yake zolayar Aunty Zakiyah ta dauke mishi First love dinsa wato Lubnan kasancewar dan Goggo Alti ne, yana jin su yayi kamar baya wurin yana ganin lokacin da ya bashi number Lubnah da kuma hotonta. Bai nuna zallamarsa ba sai da washi gari ana hira ya ce Rufa'i ya bashi aron wayarshi, zai yi abu ne ai kuwa yana amsa ya binciko number Lubnah wanda Rufa'i ya saka mata bazawarata Lubnah, sai hotonta da ya tura kusan kala goma tayi shi da gym outfits, wani baki da ratsin pink yayi azabar kyau ga kanta da ta saka wata hula me kyau gargasar gaban goshinta sun kara fitar da kyanta da ya boya behind kibar ya fara fitowa, wani murmushi tayi, daya kuma ta fitar da harshe waje kamar tana gwalo, wani kuma tana kan abin motsa jiki na gidan daga ita sai riga da wando ta tufke gashin kanta, wani irin gigicewa Hafiz yayi kamar zai zauce. Bai taSa kawowa a ransa zata dawo kamar da ba. Wannan abin ya d'aga mishi hankali wani hotonta kuwa wani yatsina fuska tayi tana dariya, alamar magana ake mata tayi haka sai kuma ita da yaran, wani kuma a makaranta. Zufa ke karyo masa yana ji ina zai iya ganinta yasan yana ganinta zata fit hayacinta ta nemi dawo mishi, haka ya mai da wayarwa Rufa'i sannan ya koma gidansa yana kallon Yaranshi da suka ci abinci suka koshi, Hajiya tana"

"gidan ita fa Fido. Zuba mishi idanun tayi ta ce mishi. ""Duk akan matsiyaciyar yar nan ne?"" ""A'a Hajiya"

"Lubnah na gani!"" Ya cire mata hoton ta gwalalo idanun waje kamar tsohuwar mayya tana faWin. ""Ina ka"

"samo ta don Allah dama yarinyar nan zata dawo kamar da?"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Hajiya ki taimaka min ta dawo gare ni!"" ""Ba ga zoben nan ba ai shi ne kankat sai kuma shi wancan uban nata kasan yadda zaka yi da shi."" Nan suka yi ta tsara yadda zasu dawo da Lubnah. A daren ranar ya tashi hankalin Baban Bauchi da kuka da rokon ya dawo mishi da lubnah itace daidai da rayuwarsa kasancewar"

"akwai sauran yan biki, suka yi ta bashi hakuri da cewa idan Matarshi ce zata dawo gare shi.."

"Abu kamar wasa sai gashi Baban Bauchi ya tashi hankalinsa sai da ya kwana asibiti, Goggo Alti tayi ta"

"fada. Da Baban Jama'are da Baba Malam suka zo nan suka fara fada ai a dawo da Lubnah. Yadiko da kanta yayi wata ta ce musu. ""Tunda tare aka halicce su ai sai ya je ya dawo da ita, sannan aure babu shi a tsakaninsu tunda har sun karbi khulu'i din da ta bayar, haka maganar ya mutu. Ranar daurin aure a shirin da suka yi akan idan aka zo daurin auren Sani sai a hada da na Hafiz da Lubnah, ai kuwa ana gab da daurin auren Babangida da yazo daga Maiduguri ya same shi yake ce mishi. ""Daurin auren Sani muka zo yi ya nake jin wai za a sake daura auren Lubnah da Hafiz bayan kace ba kai ba ita? A da can ma baka mata dole ba sai yanzu cikarka Uba na gari shine ka dakatar dasu idan ba haka ba wallahi za a kafa mummunar Tarihi a zuriarka domin zan kashe Hafiz idan aka daura auren nan da shi!"" Wannan barazanar da Babangida yayi shi ya dakatar da auren da ake shirin kara daura shi, haushi da takaici ya saka BP dinsa low. Domin yana fama da ita ko ta hau da zaran ranshi ya b'aci zata sauka da gudu, sai dai"

a ganshi yana fari da idanun da jijjiga.

"Hafiz da Baban Jama'are da Baba Malam sun ji haushin wannan lamarin, domin Hafiz saka su yayi a"

gaba da rokon su saka baki amma al'amarin ya koma haka. Wasa gaske haka aka gama bikin Sani babu wata matsaya domin kuwa babu ita shine daga baya aka je rokon Mama tayi tsalle tace abokin mutuwa

take nima akan Lubnah.

A bangaren Hafiz yana son kiranta amma yana tsoron kada ta gayawa Ado ya mishi rashin mutunci

haka yasa ya hakuri da kiran yadda kudirinsa xai cika.

***

"Akwai wani abu da na fahimta, tun da na fara kula da kaina da kuma kula da lafiyata, sai na ga kamar nafi"

samun kwanciyar hankali. Dadindewa gaba nake kamar ana hankad'a ni.

"Kwanaki suna tafiya satika suna gudu, watanin na zuwa daya bayan daya a hankali na gama"

"master dina da gagarumin nasara, ga shi dai na sauka sosai, idan ka kalle ni sai ka kara kallona, sai ka yi ta mamaki kamar ba ni ba a cikin wata shida da wani abu sai gani ina kyauta da kayana. Har Bauchi aka kawo aka kai Jama'are aka rabawa yan uwan Mama da Jikokin Goggo Alti, ai kuwa Goggo Uwani da"

"Talatuwa suka yi ta fada wai ba asan da su ba, shi yasa aka rabawa waWanda ake so, Mama da bata iya"

kyale su ta ce musu ai da na basu kayan sai ta biyo ta kwace yadda basu da mutunci karya su ci arzikin

Lubnah.......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 36"

"Zuwa yanzu ina son kaina, na fahimci duk wnada zai soka bayan kaso kanka ne ka kuma girmama kanka."

"Duk wanda ba zai soka ba babu amfanin zama da shi, amma firstly ka so kanka ka kaunaci kanka yau na ji kaf duniya babu wanda ya dace na so sama da kaina, amma har yau ina jin a raina ya Hafiz shine ajalina yadda nake bala'in tsoronshi har yau ban cire wannan tsoron na a raina. Ina tsoronshi daga kasar zuciyata. Wani irin tsoron shi nake tare da sauran maza bakiWaya. Idan akwai abinda zai hada ni da maza tow na hakura da shi, haka yasa hatta waWanda muke wurin Gym din suma suka kame kansu babu wanda ya tab'a shige min, duk da na sauka amma haka bai hana na cigaba da motsa jikin ba, wani abinda ya fara daukar hankalin mutanen wurin shine ni dai kiba na ke son ragewa amma wani abun mamaki sai ya kasance daga samata na ragu sosai, zuwa kasata sai ya bada shape irin yadda zaka ga wasu suna bukatar domin cinyata zuwa mazaunai na, sai suka fita fess, wanda ya haifar da cikina zuwa kirjina ya wani irin fita kamar dai yadda ke kira coca cola, haka shape din ya fita, a lokacin da na fara yiwa Aunty Nuratu Kafaya magana abinda ta ce min kuwa ya saka ni shiru. ""Ai dama haka halittarki take yanzu kuwa zaki dawo asalin yadda kike, tumbin da ake gani yanzu ba gashi yana ta sauka ba, a hankali kafin nan da shekara daya duk zaki dawo yar cass yanayinki zai fito kamar na yan boko yan yayi."" Kawai sai ban kara damuwa ba, a lokacin aunty Zakiya har da min tsiya wai na koma kamar wata yar Nigeria Film, ni dai ban"

kulata ba.

***

KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY.

"Yau Litinin kusan wata shida da mutuwar Auren Jasminah, mahaifiyarta ta sakota a gaba haka yasa tayi"

"give up bakiWaya take kuma jin rayuwarta bata da amfani, sai dai a yadda Uncle Auta da Ubaid suke tsaye a kanta yasa ta ke samun nutsuwa. Yau aka turo mata da shaidar an dauke ta aiki a kamfanin duk da ba aikin da tayi ba kenan amma kai tsaye Turaki ya ga dacewar ta fara aikin haka zai rage mata"

"damuwa da halin da take ciki, sannan zata nutsu sosai ta kula da Yaranta."

"Karfe takwas yayi mata a cikin kamfanin, kiran wayar aka yi ta dauka tana faWin. ""Na gode sosai, gani a"

"office din."" ""Na baki awa 48 ki fitar min da abinda nake bukata daga cikin yanayin ma'aikata zuwa sauran abinda ake bukata."" ""In sha Allah!"" Ta fada, tana kallon office din, tana mai girgiza kanta. Abinda ta fara dubawa ma'aikata nawa ne a cikin kamfanin? Don haka ta fara fita ta isa office din MD Khamis Abbas Kumo, buga kofar tayi amma baa bude ba. Masinjasa yace mata. ""Hajiya bai isa ba an jima kaWan zai"

"iso;"" ""tow! Ina ne office din shugaban ma'aikata?"" ""Office din Mrs Thomas kenan muje!"" Ba musu ya"

"rakata, ta samu ta zo tana ta aiki ta haWa nan ta haWa can, mika mata hannu tayi suka gaisa nan ta gaya"

mata me ake ciki a kamfanin.

"Murmushi tayi ta ce mata. ""'kamar yadda kika gani ma'aikata dayawa basu shigowa sai lokacin da"

"yayi musu, haka basu tashi sai a lokacin da ya dace, sannan idan wata yayi aka samu jinkirin albashi su ta korafi! Muje ki gani!"" Haka suka cigaba da tafiya kamar yadda dai ake fama da kowacce irin ma'aikatan da kamfanonin, haka inda ake ajiye kayan ma ya lalace, ga ba ma'aikatar da ya dace. ""Sannan Madam ana sata anan kayan da ake sacewa dole ya baki mamaki!"" Ita dai Jasminah tana rubutawa, tana kara mata tambayoyi har suka isa cikin store din da ya lalace. ""Ko last year an karbi kudin gyaran nan sama da miliyan talatin amma ba a gaya ba, ita kanta kamfanin tana bukatar gyara da asalin ma'aikata masu son aiki ba irin wadanda aka lalata su da rashin son aiki ba. Oga Ubaid yana kokari amma da zai yi wani motsi take za a fara mishi gorin yafi yan gidan kamfanin zakewa, yana son yayi aikin amma da zaran ya fara aiki za a fara magana kai ko dakatar da mutum yayi MD zai dawo da shi ko vice chairman, kamfanin nan ana abubuwa dayawa amma baka da ikon magana, akwai abinda nake son ki sani mu kanmu ma'aikata mata we are not safe daga baragurbi irin MD Khamis Abbas Kumo."" Shiru tayi tana me kawo ta wurin ajiyar kayayyakin da ake kwaso kayan gwanjon ta ce mata. "" Kin ga wannan motar da sauran sun lalace idan har xa'a yi amfani da shi sai mun dauki haya, madadin a gyara mana wannan, sannan zuwa yanzu akwai bankunan da suke bin kamfanin nan sauran cikon kuWinsu. Na gayawa Ubaid ya ce ba ruwansa domin ko na bankin UBA da yayi magana karshe sai da aka samu matsala akace yana da hannu a ciki aka so shi frame dinsa da laifin cin hanci abinda na sani idan har CEO ne a kamfanin nan dole a kawo gyara da sauyi don Allah muna bukatar ma'aikata da waWanda zasu tsara mana yadda kamfanin zai yi gaba ba kullum a baya ba, kaf Nigeria ita ce Waya idan har aka samu na biyu tow tasirin kamfanin zai yi kasa ki duba maganata da idanun basira. "" Haka suka gama zagaye kamfanin sannan suka dawo bakin kofar kamfanin suka zauna suna kallon mutane da suke ta zuwa har suka gama bata ce musu cikanku ba, ta mike ta na me nufar cikin kamfanin, office dinta ta shiga ta fara aiki ba kama hannun yaro, karfe daya Ubaid ya shigo, kallonsa tayi tana faWin. ""Sai na fadawa CEO mukaddashinsa sai karfe daya yake shigowa kamfanin."" ""Ai kuwa da kin kyauta dama ya haWa ni da aiki ne nake son na rabu da shi na ji da aikina ko da aikinsa?"" Murmushi tayi ta ce mishi. ""Zauna Hamma Ubaid!"" Zama yayi ta fara tattara bayanin da ta haWa na yau ta ce mishi. ""Yau na leka kamfanin bakiWaya na ga abinda bai dace ace na gani ba, karfi da yaji ana son kashe kamfanin nan meke faruwa ne?"" Ta mika mishi bayanan da ta hada. Murmushi yayi yana faWin. ""Wannan ai tsohon lamari ne, amma idan kina son ganin yadda rayuwar kamfanin yake ki fara da office din Vice chairman, zuwa office din babban sakatare zuwa na MD kafin ki zo na sauran ma'aikatan, ki yi bincike duk abinda baki gane ba ki tuntube ni."" "" In sha Allah! "" Ta ce mishi sannan ya fita, itama sallah tayi a office din sannan ta ji tana son cin abinci, mikewa tayi a hankali, a saninta lokacin da Babanta yake kamfanin abinci da ake ci kyauta ce don jin daWin ma'aikata, fitowa tayi a lokacin ta ga shigar wata mace office din MD, office din Mrs Thomas ta isa ta ce mata. "" Mrs Thomas ya batun abinci har yanzu ana yi kuwa? Don yunwa nake ji. "" Girgiza kai matar tayi ta ce mata. "" Tunda aka yi gobara a dakin girkin aka rufe bada abinci ga ma'aikatan kamfanin nan."" Shiru tayi tana me jinjina kai, sannan ta juyo tare da nufar office din MD, tana isa kafin Masinjan ya mata magana tuni ta tura kanta. Abin da ta"

gani yasa tayi baya da sauri. Bata yi magana ba ta juya ta bar wurin. Turawa Turaki sako tayi bayan ta

zauna a kujeranta. *Ni dai gaskiya ka cilla ni a uku kamfanin nan sai kai ne kaWai zaka daura shi akan

hanya a yanzu kan kome ya lalace don Allah ka dawo.*

Bai cika reply messages ba amma yau da ta tura mishi sai ga sakonshi ya dawo mata. _Ki yi duk

abinda na zaka ki sannan duk abinda kika ga ya dace ki yi idan na ga abin yayi zan kara tuntubarki_

"Tura baki tayi tana hararan wayar, haka ana tashi ta wuce gida. Koda ta isa gida wasu files ta amsa a"

"wurin Ubaid tayi ta bincike, sannan ta cigaba da tura mishi bayanin halin da ake ciki tare da gaya mishi"

"ana bukatar sabin ma'aikata amma yanzu a fara gyara kamfanin, haka ya turo musu kudi ya ce kada a tab'a na kamfanin domin yana da lissafi akan kudin kamfanin."

"A tsakanin sati biyu aka fara aikin tare da kwashe tsofaffin kayan akayi ta sayar da su ga yan bola jari,"

"wani abin haushi duk an yi sata wasu ma karafunan kamfanin sarrafa mota na kasar Japan aka sayarwa don asarar tayi yawa, haka sai ya bawa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo mamaki tare da Abbas Kumo domin dare daya suka ga ana ta aiki kamfanin ma an sabunta shi, hankalinsu a tashe suka sakata a gaba da tambayar me yake faruwa, karshe har gaban Alhaji ELYakub Kumo aka kaita, ya ce musu. ""Aikin da kuka gaza yi ne take yi kuma Umarni aka bata daga CEO idan zaku iya sai ku dakatar da ita."" Jin haka yasa"

suka sha jinin jikinsu. Nan matan suka fara tambayar dawowa zai yi?

"Kwatsam Badr ta koma gidansa na Lekki da zama, amma bata kwana a gidan gidan Uncle Auta take"

"kwana, ita dai Jasminah bata ce mata kome ba, a can office din kuwa an gyara wurin girki da hall din cin abincin, sannan an hada duk wani abu me muhimmanci kama daga kayan abinci, zuwa sauransu. Tana aikinta tana tura mishi hotuna da bidiyo na abinda take, asalin karatun da Jasminah tayi zanen gidaje wato ita mazanina ce, ya jefota ne domin ta taya shi ganin kamfanin kuma cikin ikon Allah da yake ta san darajar ilminta sai gashi ta kara faWin kamfanin har ta fara bada shawarar a bude sabon kamfanin wannan wurin sai ya zama wurin ajiye kayayyakin kamfanin da za ayi gwanjonsu, ya tambaye ta a cikin wata nawa zata iya aikin? Murmushi tayi ta ce mishi. Matukar akwai kudi a kasa ita bata ganin aikin zai haura wata uku. Jin haka ya gayawa su Mujitafa da Ubaid, tare da Alhaji suka ce sun bata goyan, aka kuwa zuba mata kudi, da mijin Uwarta Baffanta da Mijin Goggonta tare da cousin dinta, da sauran ma'aikata sai gani suka yi an fara aiki babu kama hannun Yaro, haka suka sha bakin ciki, suka kara kai ararta Alhaji ELYakub Kumo ya kore su, ita kanta aiki take kamar wata injin, Uwarta kuwa jin labarin kudin da aka zuba mata ta fara lallabata akan ta kwashe Abinda zata iya ta yi aikin ko oho, blocking Mamarta tayi bata da lokacinta, yanzu da take jin batun kudi shine zata dawo da ita jikinta. Daga masu aikin zuwa kan ita kanta mazaniyar basu zaune basu tsaye duk yadda aka so a mata barazana abin ya ci tura har bibiyarta aka fara yi ta gayawa dan uwanta, tow abinka da miskili bai ce mata kome ba, sai dai yana can sai gashi ya saka an kama waWanda suke binta aka hada su da yan sanda, karshe shi kuma yasa"

"aka karbo su ya saka aka musu kashedi, su kuma take mata baya."

"Idan akwai kudi da karfin iko uban kowa ma zaka taka, ya nuna musu shi fa yana iya kome da kudinsa"

"yana sarrafa kudinsa yayi yadda yake so, don haka duk abinda zasu zasu gana ba nasara. A wannan"

"yanayin wata ranar lahadi Mrs Thomas ta fito church kuwa da motarta Allah yasa ita Waya ce, aka mata"

"kiran gaggawa daga kamfanin a hanyar zuwa suka saka mota ta buge motar Matar nan, kai abin yayiwa Alhaji ELYakub ciwo yayi fada yayi fada. Kuma yayiwa duk wanda ya mata wannan abin Allah ya isa kuma ko waye asirinta ya tonu sai yayi shara'a da shi, Mrs Thomas tayi aiki da kamfanin tun zamanin Iyayen Turaki ita ba kamar sauran ma'aikata ba ne, kamar yar uwa suka dauke ta.. kasancewar tayi dogon suma"

wanda ake kira coma.......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 37"

"Tashin hankalin da aka shiga a family ba na wasa ba, shi yasa hatta abinda za a kashe KUMO FAMILY"

"suka dauki nauyin abin. Wannan abin da ya faru bai saka Jasminah fasa abinda take ba ai an san suna tare da Mrs Thomas, Kuma anyi haka ne domin durkusar da aikin, kamar yadda Turaki ya gayawa Uncle Auta, kullum Jami'an tsaro suke kaita tare da saka idanu akanta, na biyu kuma aka biyar lafiyar abin hawanta, haka yasa kowa yake tsaye a kanta, babban abinda yasa aka yi haka domin gani ake ai idan da ita Jasmin ce da aikin ya dawo hannunsu, sannan kuma zasu yi yadda suke so amma aba a san waye yayi wannan aikin ba. Kamar yadda ta ce wata biyu a cikin wata biyu wanda yayi daidai da saukar daminar bana, wannan wata biyu da aka diba an samu ban iska idan a damina ne aikin ba zai yi ba, amma ganin yadda aka sha isa ba ruwa yasa ta yi aikin cikin nutsuwa, ba dai ga aiki ya fito fess, Alhaji Mudansir ya ce shi ba zai koma sabon building ba, ai kuwa ya samu sako ta email address dinsa da cewa ai dama building din ba na shi bane na CEO. Abin ya bashi mamaki haka ya kara kai ara Alhaji ELYakub Kumo yayi mishi fata-fata, amma wani abu da ya tsaya musu a rai yadda kowa ya sha jininsa. Bayan an gama aikin aka fara oarin diban saba'in ma'aikata, a wannan lokacin manya mutane sun so lallai a debi yaransu, a wannan bangaren Uncle Auta shi yake da hakkin sabin ma'aikata. Wannan karon masu degree aka nima ba wasu kasa da diploma, haka yasa tsofin ma'aikata da aka same su da laifin rashin gaskiya aka sallame mu, musamman maza matan dama duk ba musulmai ne, a cikin wadanda aka kuma dakatar har da Badr Abbas Kumo, domin bata zuwa aiki kawai albashin take ciki, nan Uwarta tayi tsalle ta dirke bata yarda ba. Alhaji ELYakub kuwa yace ta gode da ba koranta aka yi ba, waWanda basu da dogon laifi an bar su a tsoron ma'aikatan, wannan abin ya bawa kowa haushi wato sune yan iska zasu zauna a tsohon wuri aikuwa suka

Please Login or Register in order to submit comment