gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu Chapter 11 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce mata. ""Maza mu hadu a asibiti gata nan ina ganin mutuwa zata yi!"" ""Waye?"" ""Lulu!"" Ya fada da karfi, yana tallafo ni, kafin mu isa asibitin kowa ya hallara haka aka wuce da ni"

"emergency, ni dai ban kara sanin me ya faru ba."

"Sai after few days, na farka shima din bana magana, domin idan na kalle su sai naga suna komawa Ya"

"Hafiz haka yasa ko na buWe idanun zan rufe da sauri. Maganar da Ya Umar yake na fahimci an kama Ya Sani, wanda shi kaWai aka kama kuma maganar da ake wai Abba ya zare shi cikin Yaransa, ya kara da cewa ko mutuwa nake ina dawowa na koma dakina idan kuwa Hafiz yace ban koma ba tow kuwa wannan karon sai dai Mama da Yadiko su bar mishi gidansa. Wani irin tsoro ya kama ni, sai da na samu"

"sati biyu me kyau aka sallame ni, anan muhawara ya tashi na ce musu. ""Ku bani kuWina!"" ""Me zaki yi da"

"shi!?"" ""Ku bani kawai!"" Haka dai muka wuce banki aka cire dubu dari biyu da hamsin, sannan na dawo"

"gida da shi, ban d'aga idanun nayiwa Ya Hafiz magana ba."

"Ban san ya aka yi na samu wata kwarin gwiwa ba, amma ina buatar hujjar da xan rabu da Ya Hafiz,"

"shi yasa na dawo na gaji da barazanar Abba akan Mama da Yadiko, haka ya cigaba da iskanci kuma har lokacin Ya Sani an wuce da shi gidan gyaran hali, haka na cigaba da zama tsawon kwanaki."

"Ranar da Ubangiji ya kawo min karshen duk wata damuwa, shine ranar Talata na tashi na daura abin"

"karyawa, nawa iya ni cikina ni daya na daura, bayan na gama na zauna ina hutawa, sai ga Karimah. ""Ke ina ruwan zafin da zamu karya?"" Banza na bawa Ajiyarta ta fita a fusace lokacin na hada nawa na fito na wanke cokalin sai ga Ya Hafiz, yana zuwa ya ce min. ""Ba dake ake magana ba yar dangi?"" Ganin naki kula shi, har na shiga daki ya biyo ni ganin yadda na haWa nawa na nufi wurin kofin yana Wauka bai wata wata ba ya watsa min tafasasshen ruwan zafi a gadon bayana, ji nayi kamar dukka jikina ya matsa min, ga rigar jikina irin robar nan ne mai daukar zafi, yaga rigar nayi na watsa garin cire Braz dina na kwaso har da fatar bayana, zama nayi ina haki domin yau kan Allah ya kawo sanadin kenan, a hankali na d'ago kai na kalle shi, yadda nake kallonshi ya razana karshe fita yayi daga daga dakin, na dauki wayata na kira Ya Umar na ce mishi. ""Don Allah ko zaka zo muje asibiti?"" ""Baki da lafiya ne? Gani nan don Allah ki jira gani nan!"" Ai tun kafin ya iso Ya Hafiz ya gudu, yana shigowa yayi ta kwala min kira, a hankali na fito koda na iso gabanshi zubewa nayi a sume, haka yasa saka shi shiga tashin hankali, yadda na kifa tare da faduwa akan hannuna, shi yayi sanadin gocewar kashin hannuna, yadda fatar bayana ta bare jajjur ya bashi tsoro,"

"haka ya riko ni, muka nufi asibiti."

"Kiran Aunty Hindatu yayi ya gaya mata, itama tazo, kafin kace kwabo Aunty Raliya da take Jos ta iso,"

"babu wanda ya sake ya gayawa su Mama da Yadiko. Kawai anyi shiru an barsu. Aunty Hindatu ta kanta ta koma zango ta dauko kuWina tare da kayana ta kwaso min. Haka kwantar dani tsawon kwanaki ashirin ana wanke ciwon kafin aka sallame ni don ya kame. ""Yanzu ina zaki?"" ""Jama'are na gaya musu shirina."" Dama Ya ado yasan kome don haka ya ce na jira shi Aunty Munah da take River sai gata, don ta ce ba zata sake barin kallo ya wuce ta ba, Ya Abba daga Maiduguri ya dirko, kwana Waya muka kara gaba sai Jama'are. A gidan Goggo Alti muka fara sauka aka muka huta aka yi girki aka yi sallah sannan aka ci na"

"nuna mata bayana da abinda ya faru ba kara da gaya mata gaskiya na gaji dari bisa dari ya goya min baya. Na nufi gidan Kakanmu. Da taimakon Yayuna muka isa gidan, na gaya mishi ya kira Yayansa da Hafiz"

domin nazo a raba auren ne har da Matarsa.

"Kiri-kiri tsohon nan ya shiga fada wai an zuga ni. ""Ba a zuga ni ba, a yzun na samu amsar tambayoyina,"

"kai ne sanadin Hajja bakin cikinka ya kashe Hajja yanzu na fahimci yadda aka samu gawar Hajja, tabbas kai ka kashe Hajja sannan itama Dadah kayi sanadin daina ganinta karshe ta mutu bata gani. Imma ka"

"kira Yaranka, ko kuma na kashe kaina kuma wallahi Yan uwana da hukuma ba zasu barka ba, mutuncin"

"da kake da shi a fada sai ya zube, kimar da ka jima kana karewa zaka rasa. Zuwa gobe ka tara mu anan ko kuma jibi yan sanda su taraka a office Winsu. Kuma zan saka sunanka a cikin waWanda suka kashe ni ba kai ba hatta Abba ba xan kyale shi ba."" Daga haka na fito, ajiyar zuciya nake, amma definitely zuciyata ba"

"zata iya daukar wannan kasadar ba, tsohon da nake ji yafi karfin na fada a fatar baki."

"A daren Abba sai da ya kira Yayuna babu wnada ya dauki wayar, kai abin fa dole yasa aka hadu kamar"

yadda na fada din.

***

"A yau da nake tsaye a gaban Baban Jama'are, rike da jakata na zauna a gaban Baban Jama'are da kuma"

"Malam Babba, tura kudin nayi a hankali. ""Ya Hafiz ya biya sadakina a shekaru goma sha daya Naira dubu hamsin, yau na dawo mishi da dubu dari biyu,kawai abu daya nake bukata SAKI NA!"""

"Mikewa yayi yana faWin. ""Hauka kike? Waye zai aure ki da wannan yanayin naki? Baki ga kina kama da"

"dodo ba ne? Kambu ina ruwan kwatarkwashi, na ji xan sake ki shi waye ya gaya miki akwai wanda zai aure ki "" Tass aka wanke shi da mari, Yaya Adam kallonshi yayi cikin huci ya ce mishi. "" Ni barista Adam"

"Usman Umar Jama'are na tsaya mata, yau na kara yarda da cewa kai mugu ne hafiz laifi ne don ta nemi"

"saki? Ashe dama wannan shine asalinka?"""

"Baban Jamaarae ya ce mishi. ""Na gode Adamu, na gode da ka wanke min raina, yau ba gobe ba ka sake"

"ta ina alkaliya Hindatu?"" Mikewa tayi ta dawo gaban jama'a, ta ce."

"""Baban Jama'are ni ba alkaliya ba ce, amma xan iya kiran alkalin ya shiga lamarin!"""

"""Idan kuka kashe Auren Lubabatu ku sani sai dai ku nima mata wani Uban ba ni ba."" Inji Babanmu. Da"

"wani murmushi yake kallona, yana da wanda ya tsaya mishi. Murmushi nayi ina kallon kwayar idanunsa."

"""Idan ka kore ta, ina da inda zan ajiyeta. Hindatu ki kira mana alkali mu yi maganar da shi."""

"""A'a su koma su sassanta kansu, idan abu ya ci tura sai mu kai gaba inji Baba Malam."""

"""Wallahi wa Rabbul Ka'aba, ba zan sassanta da shi ba. Idan aka ce dole na koma gidansa zan koma amma"

"ku sani zan mutu kuma zamu haWu a gaban Ubangiji shine alkalin alkalai, ba zaku gane yadda nake mutuwa ba ne? Ba zaku gane yadda nake cutuwa ba ne?"" Cire Hijab dina nayi na nuna musu hannuna da yake makale a wuyata. Na kuma kalli Aunty Inna na ce mata. ""Zuge min zif din rigana!"" Tana zugewa, na juya musu baya ruwan zafin da ya watsa min na shayi ne na ce musu. ""Kace na tafi Baba zan tafi idan ka ce na mutu zan mutu, wannan shine abinda dan sonka ya min!"" Kunya ce ta kama Ya Hafiz ya fara kame-"

"kame yana faWin. ""Ba fa da gayya na mata ba, wallahi kawai na je zubar da."""

"""Habibi kame-kame me kake kai fa kace ka gaji da ita gara ka sake ta, ina dalili mace ba haihuwa ba ka"

"zauna da ita sai ciyar ta da ita kake yi, idan ka dawo da ita kuwa mutuwa zata yi da zama da kai domin an gama zugata. Mace sai kace rumfa. Kai ma dai da son rai kake, kasan ko ka ci gaba da zama da ita ba"

"haihuwa zata yi ba tunda kai ne ka lalata mata mahaifa, gara ka sake ta kara gaba domin nima na sakata"

"na wala"" tana fadar haka ta juya ta bar parlourn, burinta ya cika ta fada fara ya sake ni yadda zata ji dad'inta ita Waya da Yaranta."

"""Alhamdulillahi Ubangiji ya bata miji na gari, zaka sake ko sai na maka Allah ya isa!"" Inji Baban Jama'are"

"mahaifinsa. ""Baba ina son matata, sharrin shaidan ne wallahi ban yi haka don na cutar da ita ba."""

Matsowa yayi gabana domin yanzu yasan tabbas za a raba shi da Lulu Kuma wannan zai kara hankad'o

"wasu abubuwan da ya aikata wanda haka yana fitowa kowa sai ya kusan tsine mishi ""Luluna ki yi hakuri ki amince mu koma zamanmu!"" Yadda yake roko da magiya zaka rantse ba shi ya gama cika baki idan ya sake ni sai na rasa majingina ba. Yadda ya gigice da Babanshi ya kara daka mishi tsawa Kakanmu Baba"

"Malam ya ce mana. ""Ku tashi ta koma dakinta."""

"""Gaskiya ba zata koma ba, domin yanzu haka Lubnah tana ganin likitan wawalwa ne, saboda damuwar"

"da take da shi ya shafi wawalwarta kowani lokaci zata iya haukacewa!"" Inji Aunty Innah, kallona kowa ya koma yi cike da mamaki sai lokacin da hawaye yake zuba min. ""Tabbas a yanzu haka ranar Monday zata ga babban likitan wawalwa anan Bauchi muna saka ran idan ya ganta zai daura ta akan magani!"""

"Inji Ya Umar,"

"Zare idanun Mama take zuciyarta yana wani irin bugawa. ""Wani irin likitan wawalwa kuma?"" Inji"

"Yadiko, . ""Kamar yadda kika ji Yadiko zamu mai da ta ganin likitan wawalwa, domin dole ta ga likita Lubnah da muka bashi ba ita ba ce wannan, idan kun kalle ta da kyau wannan bata da sake koma me yake damunta ba mu da dauka lokaci ya kure da zata kara."" Ya Ado ya fada yana kallon agogon hannunsa,"

"Baban Bauchi cikin isa irin nashi ya ce mana. ""Idan kuka kashe mata aure ba dai gidana ba, kuma zan zare ku a cikin zuriar ta."" ""Kai sake ta, sannan na rungume Yaran Yaya Usman a madadin nawa, wallahi idan baka sake ta ba sai na maka Allah ya isa."" Cikin fushi Hajiya Asiyah ta ce mishi. ""Dalla sake ta, me za"

"ayi da Macen da bata haihuwa me zaa yi da Macen da bata da amfani."""

"Cikin faWa Yadiko ta ce mata. ""Kike fadar haka Hajiya Asiya? Kike fadar haka Hajiya Asiya? Rashin"

"haihuwar waye sanadin mata haka? Ke Lubnah waye ya kawo miki maganin hana daukar ciki?"" Kaina wani irin sarawa yake, hayaniyarsu saka min kaina juyawa yake. Kallon bakinsu nake domin motsinsa nake gani bana jin me suke cewa bakiWaya. Lumshe idanuna nayi na bude a hankali, tare da dafe kaina."

"Jijiga Aunty Hindatu da nake kusa da ita tayi, na koma zan zube ta riko ni......."

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAAR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500*

"*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105"

ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita*

Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

SHA BIYAR

"Wannan sumar ya haifar da abubuwa dayawa, domin Mama ta tsaya a gefena tsawon wunin da nayi a"

"gadon tana tare ni. Tashin hankalin da Ya Hafiz ya shiga abin har ya wuce tunanin kowa. Abu kamar wasa sai gashi lamarin ya wuce yadda ake tsammanin domin hajiya take kara jagula take al'amarin ta hanyar da aka yi wani rikici a cikin family akan aurena, sai da ta kai an rabu gida biyu wasu suna ganin kamar naki Ya Hafiz ne saboda Yan uwana sun zuga ni, Yayinda wasu suke tare da ni saboda ciwon da yake jikina suka ce ai tunda ya yarda da ya aikata ,sai gashi haka ya kawo rabuwar kuma kowa ya amince"

"da a rabun, banda Abba da ya kafe shi da Baba Malam sai na koma."

"Wasa wasa har tsawon kwanaki uku ina asibiti, yau Mama ta shirya tare da faWin. ""Zan tafi karbo"

"takardanki, na gaji da ganin yadda kome yake faruwa shi Babanku ya dage ni ma kuwa ina tare dake babu wanda ya isa miki dole!"" Gyada kai nayi ina mai cigaba da kwanciya, nasan cewa ina cikin tashin hankali, amma a kasan zuciyata ina jin kamar ban mishi adalci ba, anya Ya Hafiz ya cancanci haka? Bayan"

"fitar ta sai ga Abba ya shigo, wani irin tsoro ne ya cika ni nayi baya ina zare idan, zama yayi."

"Gyara zama Babanmu yayi yana kallon yadda nake zaune a wurin guda, tunda ya shigo dakin, ya ga na"

"kurawa window din idanu. ""Lubabatu!"" Ya kira sunana, a hankali na juyo ina kallonshi. ""Nasan lafiyarki lau me yasa kike bawa Yan uwanki da mijinki wahala!"" Kura mishi idanu nayi ina kallonshi. Turo kofar dakin Ya Ado da Ya Umar suka yi a tare, ""me yasa kike bawa zuciyar kowa wahala?"" ""Baba bata da lafiya ka bar wannan maganar idan mun dawo ayi ta!"" Inji Ya Umar da yake yana da zafin rai sosai. Rike shi Ya"

"Ado yayi yana girgiza mishi kai. ""Lubabatu Y'ata ce, akan me kuke kokarin shiga tsakaninmu?"""

"""Saboda ka fifita zumunci akan Rayuwarta, ka rabata da Mahaifiyarta kada tazo ta ga halin da take ciki."

"Ka nisantata da kowa nata, Abba idan ka sake ta mutu a wannan yanayin Allah sai ya nuna maka iyakar...."" Tass ya tsinkawa Ya Ado mari, a zuciye yayi waje."" ""Abba zan koma gidansa!"" Juyawa yayi yana kallon yadda nake murmushi. ""No Lulu kada ki mana haka."" ""A'a zan koma Ya Ado, zan koma saura me ya rage a rayuwata? Farin ciki sai dai wasu su yi, amma ni na san nayi hannun riga da shi, Ya Ado na"

"gode sosai ka ce likita ya sallame ni kawai na koma dakina."""

"Hankad'o kofar aka yi da karfi Mama ce tsaye tana huci. ""Ba zaki koma ba, kin gama aurensa daga"

"kotu muke ga takardanki."""

"""Salamatu"" ""Sai me? Uwarshi ta kai kotu me ya rage? Ai dama albarkacin zumunci ne zaku kashe min"

Y'a Uwar da tafi arfin Mijinta zaka yi tsammanin zata bar Lubnah ta zauna ne? An bashi kudin wanke

"muni me ake bukata?"""

"Shima kamar wanda aka wurgo shi ya ce mana. ""Wallahi ban sake ta ba."""

"""Kotu ta sake ta!"" Inji Mama tana kara kallonshi. ""Kaci albarkacin Ubanka, da sai na saka an maka abinda"

"baka zata ba, Lubabatu kuwa ta haramta maka. Adamu kasan yadda zaku yi da ita zaman Bauchi ya kare kuma ka kuma kusantar inda Lubabatu take sai na saka an wulakanta min kai, idan kana jin rashin kunya da fitsara wannan cikin ta haifa min, lauya, magatakarda, Soja, da sojar kasa da na sama sun fika kwaya"

"da tijara ahir dinka."""

"""Wallahi ban sake ta ba, ina son Matata kuma babu wanda! Ya isa raba ni da ita Baban Bauchi kana gani"

"sun raba ni da Matata!"" Ya dawo gabana ya ce min. ""Luluna kina ganin sun raba mu? Luluna ki ce wani abu, ni ne Ya Hafiz dinki. Dube ni ni ne Hafiz Winki!"" A hankali na zare hannuna a cikin nashi, zuciyata tana wani irin bugawa na ce mishi. ""Alhamdulillahi Ubangiji da ka samar min yanci! Ka je na yafe maka kai da Karimcy ka je na bar muku kome na cikin gidan hatta suturata na yafe, Alhamdulillahi Ubangiji na"

"gode maka!"" Sai a lokacin na samu damar fashewa da kuka. Kuka nake da dukkan zuciyata."

"Cikin irin haukar da ya saba ya ce min. ""Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare rayuwraki"

"babu namijin da ya isa kallonki!"" Cikin fushi Mama ta ce mishi."

"""Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure kuwa wallahi sai tayi, ka fita kafin na kira a ci"

"mutuncinka."" ""Lubnah ki dawo? Wallahi ki dawo ko kuma kina ji kina gani ki kare rayuwarki a wulakance! "" Dariya Mama tayi tana faWin. "" Alhaji ka ji abinda danka yake faWa? Ka ji yadda yake ihu bari na nuna mishi nima ina da fitsararru irinsa, ta leko waje tana faWin. ""Kai Adamu zo kayi min waje da wannan Wan iskan ka nuna mishi yadda ake rashin kunya!"" Ba Ya Ado ba bakiWaya Yayuna maza suka yo dakin wani irin daukar amarya suka mishi, zuwa waje suka ajiye shi.. ""idan ka sake zuwa inda Lubnah take gara ka"

"kira kanka gawa domin sai munci Ubanka shege mara kunya dan iska!"""

"Suka kore shi sannan suka dawo a lokacin Abba ya mike tsaye, kin yi yadda kike so da Yaranki ku je"

"na sallame ku ke da ita Yar so dinku!"" "" Alhamdulillahi Masha Allah, na gode katuro min takardar da wuri domin ina gama idda zan yi aure in sha Allah! "" Ashe maza ma na da kishi, cak Abba ya tsaya ya ce mata. "" Uban waye ya ce zaki yi aure a shekarunki nan? "" "" Allah mana ya ce nayi koda ta dauki kwarinka! "" "" Kai Adamu ka gaya mata wallahi na dawo da ita kuma kada ta wuce yau bata koma dakinta ba, ita kuma kanwarku ba dai gidana ba. "" Yadda Abba ya nuna baya bukatar ganina yasa min wani irin kunci, a hankali Mama ta d'ago hannu zata tab'a ni nayi maza na kare kaina, tare da cewa. ""Don Allah ki yi hakuri!"" Sake baki kowa na dakin yayi suna kallona har shi Abba da bai fita ba, juyowa yayi yana kallon yadda na kare fuskana. ""Lubnah meke damunki! "" Inji Ya Ado da ya tako gabana, "" babu! "" Na furta a hankali ina kallon Mama da itama mamaki ya kusan kashe ta. "" Hafiz yana dukanki ne?"" Rufe bakina nayi ina kallon Abba. "" Gaya min dukarki yake yi?"" Fadawa jikin Mama nayi na rufe idanuna, sake magana yayi ma kame-kame Mama ina ajiyar zuciya. "" Wai a haka za a mai da ta wurinsa! Umar muje Bauchi a"

"mai da ita asibiti she need treatment domin basu yadda ya dauka yana azabtar da ita ba. """

"Kiransu Aunty Innah da Hindatu aka yi aka ce zaa koma Bauchi saboda mota daya aka dauko, a ranar"

"aka bar Jama'aren, karfe tara na dare muka isa Bauchi, kai tsaya asibiti aka wuce da ni. Sai da muka isa asibiti bakiWaya sai na kasa fita a motar, sai da suka fitar da ni daga motar, haka aka dauko keken marasa lafiya aka wuce da ni, zan iya cewa tun daga ranar sabon jinya ya same ni, hatta zuciyata sai da ta samu"

matsala.

"Saboda nauyin damuwa dama can kaina ya jima da tabuwa, haka nayi ta jinya har wata guda kowa ya"

"koma wurin aikinsa. Ya Umar da Tahir sai Sani da aka sake shi, Aunty Raliya tana zuwa a kai akai duba ni, da duk abinda tasan zan so."

*

Flash back

"Abinda ya faruwa kuwa, tunda Hajiyar Ya Hafiz ta ga kudin da aka kawo tayi lissafinsa zai kara musu wani"

"abu da yake mugaye ne, ita da Yaranta Nana da Firdausi suka shirya a kai arar Lubnah kotu, yadda dole a amshi kudin da yardan Hafiz ko kada ya yarda idan suka karbi kudin daga baya sai ya ce bai yarda ba, sai kuwa Tijjani yaji maganar shine ya gayawa Baban Jama'are, shi kuma da ya tabbatar an kai maganar kotu, shine ya kira Ado ya gaya mishi, shi kuma ya tura Hindatu, tana zuwa ta tabbatar dama case Win a Bauchi ake son ayi shi, amma tunda sun kawo ba tare da wani dogon magana ba, aka tattauna saboda abin na family ne a office din alkali aka yi magana take alkali ya sake Lubnah tunda uwar shi bata bukatar Lubnah sannan koda ace uwarsa tana son Lubnah dole Hafiz ya kyaleta tunda abin har da irin wannan rayuwar. Ana. Fitowa daga office din Tijani ya kira shi ya gaya masa, sai ga shi har kotun ana ta jajjanta"

"lamarin, ihu yayi ta yi yana faWin bai sake ta ba, wallahi bai sake Lubnah ba. Koda Hajiyarshi ta bashi"

"kudin wanke muni watsi da su yayi ya ce mata. ""Duk abinda ya faru ke ce kika lalata min kome na, ina"

"son Matata kika yi ta saka ni a gaba na cutar da ita, wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba."" Yayi ta rusa kuka har ya zo asibitin."

Wanann shine abinda ya faru.

**

"A kwanakin da nayi ina jinya, babu wanda ya taba kira min sunan Ya Hafiz, nima kuma nayi oarin"

"danne tsoron da nake ji, sai dai kuma irin wannan tsoron baya barin Dan adam, domin abu ne da ruhi ya ginu akanshi, sai da ta kai ta kawo idan za a bude kofa da karfi sai na razana, ga wasu irin nightmare da nake yi,kamar dan mutu tsoro ya gama kassarani, karshe sai aka wayi gari amadadin jini na y sauka a'a jinina hawa yake kamar ana tula mishi gishiri, hatta likitan da yake duba ni sai da ya tambaye Mama ko tana bani wnai abincin da bai dace bane? Ta rantse mishi babu kome, shiru yayi kafin ya shiga tambayarta game da rayuwata kafin yau, bata boye mishi ba, amma yayi mamaki da ji ai ba a jima da kashe auren ba, don haka ya tafi da dare ina kwance ya shigo don Allah ya gani ko magana bana son yi ya shigo ya zauna tare da min tambayoyi, idanuna a rufe nake bashi amsa, abinda yayi matuar daure mishi kai, shine lokacin da ya mike ya matso zai duba ni domin ya ce na tashi zaune, wani baya da nayi saura kiris da na fado kasa. ""Is ok ba zan miki kome ba,.amma ki kalle ni mana!"" A dan tsorace na kalle shi nayi maza na rufe idanuna. ""Hajiya haka take yi ne kullum!"" Shiru tayi kafin ta ce mishi, ""wani lokaci ba, musamman idan muna ta yawan baki masu zuwa gaishe ta!"" ""A dakatar dasu, su daina zuwa domin bata da lafiya sosai da sosai, jinya take bukata kafin ki tafi gida ku daura akan naku."" Tabbas ni kaina nasan"

"bani da lafiya, domin daga yadda nake razana da firgita."

"Koda Yayuna suka zo Mama tayi musu bayani suka ga likita ya gaya musu halin da nake ciki, sai suke"

"ganin kamar ba haka ba sai da Aunty Innah tazo ta fara musu bayani abinka da mai ilimin ta ce musu, ta gyara zama tana kallonsu kafin ta ce musu. ""Lubnah tana bukatar kulawa a kowani irin Yanayi, Lubnah tana bukatar rayuwa me kyau no matter how tana bukatar faWin ciki a ja ta a jiki."" Sauke numfashi tayi tana kallon takardar hannunta ta ce musu. "" Mun yarda da addara mai kyau ko mara kyau, Allah shi ya jarabci Lubnah da wannan laluran amma da ace tun farko da Hindatu ta fara min magana akan Lubnah"

"zata samu wannan matsalar da tun lokacin aka kashe auren! """

"""Dalla Malama ki mana bayani kin sa zuciyata sai tsalle take idan ta dirko ta fashe fa? "" Inji Tahir da ya"

"gaji da maganar da take yana son Isa ga point din. ""*GAD*"""

"Ta furta muryanta yana rawa ta fara magana kamar haka. ""GENERALIZED ANXIETY DISORDER, ake"

"kiranshi a turance, cuta ce da take samun dan adam ta sanadin damuwa da tashin hankali tare da matsin lamba, wanda idan ta kai matakin chronic yake haifar da cutar hauka!"""

""" Bama depression ba?"" Inji Ya Umar, hawaye ne ya zubo mata ta cigaba da cewa ""A yanzu ta shiga"

"mataki na biyu ga cutar, wanda daga shi sai hauka. Yawan razana da miyagun mafarki. Tun ranar da"

"Mama ta kai hannu zata ta b'ata ta razana, ya fara jin shakku, idan kun lura ana bude kofar zata zabura."""

"Kuka ta saka a hankali. "" Tana kokarin fita daga staage ta shiga wancan da shine zata fara hauka. Tun da na ga tana yawan dariya ko tayi ta zama shiru nayi fatan ya tsaya a haka ashe har ya isa wannan matakin."

""""

""" Kin ga ana warkewa ko ba a warkewa? """

"Inji Ya Umar, cikin shashekar kuka ta ce mishi. ""Ana warkewa idan aka hadu da therapy."" Shiru yayi kafin"

"ya ce mata. ""Yanzu taya zamu iya magance matsalar Lubnah amma wancan dan kutumar uban na Ganshi sai na

Please Login or Register in order to submit comment