gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu Chapter 30 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

elevator, ""ya daina aiki!"" Wucewa stair nayi na fara"

"haurawa a hankali, dama ai haurawan ba sabon abu ba ne."

"Ina isa office din na samu tarin aiki, na bude table tap din, na fara aiki kamar yadda na gani, na shigar"

"da bayanai, na tura mishi office Winsa, na turawa Taj da Jasminah, sai karfe biyu na samu kaina."

***

"Yana zaune duk yan uwan babanshi sun taru ana son dalilin kwatsamawa Khamis mari da Lubnah tayi,"

"yadda yake shan fruit hankalinsa kwance, sai da ya sha ya koshi, ya mike yana faWin. ""Daddah ke da Dattijo ban san dalilin kiran da kuka min ba, gashi nazo babu wani bayani sai tambayar da ni dai nasan da yarinyar bata mare shi ba, sai na karya mishi hannun da ya tab'a da shi, tsalle tsallensa ya tsaya inda yake da iko idan ya shigo wurina ya tab'a min ma'aikta!"" Mikewa yayi bayan ya gama daure takalminsa, ya dauki jacket dinsa ya saka yana mai kallon Uncle Auta ya ce mishi. ""Wallahi sai na kwashe mishi kayan aiki!"" Daga haka ya fita abinsa bayan ya saka Black prada a idanunsa ya nufi waje.. har ya fita sai ya dawo ya ce musu. ""Yaran da kuka turo min na mai da su Office din Uncle Mudansir ina ga zasu dacewa da can!"" Daga haka ya yi tafiyarshi idan kana niman hayaki fidda na koko to Bilal ya kai wannan matakin"

"wai sun zo gaban Alhaji ELYakub amma bai hana yayi yadda yake so, kuma ba yadda suka iya."

"Don ya zame musu kadangare bakin tulu a karka, a kar tulu. A barka ka b'ata ruwa."

""" Baffa kana ganin abinda yayi ko?"" Mikewa Uncle Auta yayi yana faWin. "" Me ya aikata? Ni ban ga wani"

"abin da yayi ba. Ku jawa Khamis kunne ya san limit Winsa."" Daga haka ya juya ya fita, "" ka godewa Allah da ita yarinyar tana wurin, shi din yasan darajar jini da ace bata wurin daga abinda ka yi ta fita tow wallahi inda zaka yi fitsari na sai an daura maka leda! Kayi kazamtarka a idan aka baka dama banda inda yake karewa domin mutuncin kansa. "" Inji Ubaid, sannan ya fita daga cikin gidan. WaWannan mutane"

biyu sun yi kaurin suna wurin kare Turaki.

*

"Karfe uku da wani abu suka shigo, bata nan bai wani damu ba. Haka ya wuce Taj yana bin bayansa koda"

"ya shiga office ya samu ta ajiye mishi printing din da ya da ce duk wani abinda ya dace tayi. Cire jacket din yayi taj yana me amsa ya rataye mishi ya ce mishi."" Oga na ga ta gama aikin saura kaWan ne?"" Tsayawa yayi yana kallon aikin da tayi. "" Daga ina aka turo wannan abin? "" Ya d'aga wani bunch na white paper, wanda har da pin Winsu tayi. Dauka Taj yayi ya fara dubawa. "" Oh My God! Daga office din Badr ya fito ba sakon nan ba ne?"" "" Kira ta"" ya fada a hasale, fita yayi da sauri yana zuwa ya samu har lokacin bata dawo ba. Shi kuwa sai cira yake ya Wan zauna a gaban table Winsa tare da harde hannu a kirjinsa yana kallon kofar. Yana jin wayarshi yana ringing amma bai dauka ba, asalima dauke kai yayi yana kallon"

kofar.

"Taj kuwa haka yayi ta bi yana nimanta, bai same ta ba sai da ya fito waje ya hangota rike da ledar"

"abinci da kuma daya ledar kamar abu ta sayo mr muhimmanci, a hankali take takawa."

"Murmushi nayi lokacin da na ga taj yana jirana, amsar ledar yayi tare da cewa. ""Me kika aikata haka? Na"

"bar miki kome amma kika yi shirme haka, yau Allah kaWai zai kwace ki, domin Oga yana can yana jin rigima a ransa. Hadiye yawu nayi na ce mishi.""Me ya faru?"" ""Muje!"" Hannu ya kai zai dauki daya ledar nayi baya da shi. ""Wannan dai!"" Na fada ina murmushi, amma ni daya nasan yadda nake ji, a hankali nake tafiya saboda zuwan al'adata bazata, kuma nasan yau da gobe zan shiga wani irin tasku ne. ""Don Allah ki yi tafiya da jikinki."" Kamar ance na d'ago kai, yana tsaye yana kallona, da sauri na sunkuyar da kaina ina tsoronshi sosai. Lokacin da na shiga, cikin building na kamfanin sauran abokan aikin sai dariya"

"suke min, ni ban kula su ba. Haka na wuce na shiga elevator."

"Lokacin da na shiga jingina bayana nayi da jikin elevator, bakiWaya naji kamar xan yi amai. Haka muka"

"fita har zuwa kofar office dina, daga shi har ni Dan tsorace muke shi yana tashi ya shiga da ledar hannunsa, nima kuma haka na shiga da na hannuna tare da dunkule shi, kasancewar pad ne a ciki. Ajiye ledar yayi ya dauko min takardun ya ce min. ""Mene ne wannan?"" Ba tare da kome ba nace mishi. ""Sakon da ka bar min na yi printing dinsa shine nayi na turo mishi."" ""Ba shi bane ina wanda na baki?"" ""Kamar Ya? Ban gane ba!"" Na fada a hankali, ina cizon bakina. ""Na bar miki akan table Winki fa!"" ""Ni iya shi na gani wallahi azim ban ga kome ba sai su!"" ""Tow ina kika je?"" Ogan ya jefa min tambayar, kaina a sunkuye"

"nace mishi.. ""abinci na je sayowa!"" Na fada ina rike ledar hannuna da kyau. ""Babu a kamfanin ne?"" ""Bana son na kamfanin ne!"" Sai a lokacin ya zuba min idanu. Kaina a sunkuye, ""ko karfe nawa zata kai i don't care daga kai har ita ku hada min aikina ina jiran ku!"" Daga ya shuri takalminsa ya bar mu a office"

"din. Haka muka fito na kalli Taj nace mishi.. ""kayi hakuri!"" ""Ba kome dauka aka yi domin na Ajiye miki."""

"Shi kuwa yana fita ganinsa ya fito babu jacket dinsa yasa yan mata dayawa binsa da idanu, ga wani"

"tafiyar da yake ya zuba hannu a cikin aljuhun wandonsa, can tsohon office din ya nufa, yana shiga ya hadu da Badr. Zuba mata sirrintaccen idanunsa yayi cikin wani irin tsinannen kallo me cike da tsana da"

"b'acin ran ya ke bin ta da shi, juyawa tayi ba musu ba tare da ya ce mata bani abinda kika dauka ba, ta"

"wuce ya tsaya a wurin ma'aikata sai gaishe shi suke yana amsawa, Alhaji Abbas da yaji labarin yana"

"wurin ya fito da sauri. ""Yallabai shigo mana!"" ""I'm ok da nan!"" Can sai gata nan dauke da takardun, nuna mata hanya yayi ba musu ta wuce ya cigaba da tafiya yana latsa wayarshi. Har office dinsa, kamar yadda ta shiga ta dauka haka ta dawo da shi cike da kunya. ,harde hannunsa yayi a kirjinsa. ""Ke ina wasa da ke?"" ""Am sorry sir! Ba zan kara ba ayi hakuri."" Ta shiga bashi labarin. ""Na dakatar dake har na tsawon sati biyu!"" ""Don Allah Hamma kayi hakuri!"" ""Get out of my sign!"" Da sauri ta fito, ni kuwa bawan Allah nan haka ya kira Taj ya kara jibga min kaya, haka har karshe shida ina wurin ga ciwon ciki, shima don bakin mugunta yana office din yaki fita, fitowa yayi lokacin ina amsa wayar Ya Ado. ""Ya ina hanya ne hau aikin ya min yawa ne, kayi hakuri gani nan zuwa."" Na kashe wayar ina mai binsa da harara ""mugu kawai!"" Na fada ina jin marana yana ciwo. Taj ne ya shigo yana faWin. ""Muje a sauke ki a gida!"" A hankali na tashi na nufi wurin da Abayana yake na saka, zuwa yanzu na san na bata jikina, shi yasa na saka pad din a inda na zauna, lokacin da da muka sauko ina ta Addu'a Allah yasa na zauna a baya, cikin ikon Allah kuwa bayan na zauna kafin na shiga haka na bude sabon pad na saka a inda xan zauna, kamar nayi kuka,"

"bawan Allah nan mugu ne ko saka abin ban yi a jikina ba. Haka na shiga na zauna, ina jin kamar nayi kuka."

"Har muka isa gida, na dan haska wayata na dauki pad din da jakata na, musu godiya sannan na shiga cikin gidan da sauri, ban tsaya ba ban dakin yara na wuce na wanke jikina na tura Ummu ta dauko min pant da wasu kayan na gyara jikina, ina sauke ajiyar zuciya. Laptop dina gida na dauko nayi login din na"

kamfanin ba fara aiki. ......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 50"

Da yake ke yana gaba ne shi da Taj har suka isa Taj ya dauki jakarshi ya shiga da shi cikin shi kuma ya

"wuce masallaci. Taj na isowa ya bi shi suka tafi. Koda aka yi sallah isha taj ya wuce gida shi kuma ya nufi inda motar yake zai duba abu, yana budewa ya kunna wutar motar ya saka hannu ya dauki file din da yake bayan motar, idanunsa ne ya kai kan jinin da yake manne a jikin kujeran. Mamaki ne ya kama shi. A hankali yayi lissafi yau ya zo mata, shi yasa take kome sanyi-sanyi. Kiran Taj yayi ya ce mishi. ""Kace yarinyar nan ta zauna sai Monday!"" Ya kashe wayar, sannan ya koma cikin gidan ya dauko kayan wankin ya zo ya wanke sit din ya jingina da motar yana nazarin har yau bata daina fama da ciwon cikin ba ne?"

"Shiru yayi yana nazarin lamarinta, duk da yana jin zafinta amma a duk lokacin da ya kalleta sai ya ga kamar tana boye wani abu fuskarta, idanunta yana fadar abinda fuskanta yake faWa daban. Wayarshi ce"

"tayi ara ya saka a kunne. ""Oga ban samu numbeta ba, domin bani da shi."" ""Ok"""

Haka ya wuce gidan Ubaid ganin Nihla suka yi ta wasa da Yarinyar amma zuciyarshi tana wani irin

"yanayi. Bude wayar yayi ya kara bincike ko ya dauki number wayarta yasan gobe zata zo da mood din. Amma bai samu ba abinci ya ci ya nufi gidan Uncle Auta, nan ma fura ya sha yana dawowa gidan ya wuce Gym ya motsa jikinsa. Rabin daren yayi shi akan aiki ne amma bakiWaya Lubnah ce a ransa."

"Kusan har gari yayi tsit ina aiki, tashi nayi na dauko faten da wanke na sha. Sannan na zo na kwanta"

"saboda hajijiyar da nake ji, haka nayi barci a wahale ban farka ba sai karfe shida na safe. Na shiga nayi wanka na wanke jikina duk na b'ata zanin gadon haka na hada na wanke da kayan jiya, sannan na shafa mai da body spray. Na saka kaya irinta hausawa saboda yau juma'a ce, pad dina guda goma na zuba a"

"jakar, domin kada a kara samun matsala."

"Doguwar riga ce ta atamfa, sai hijab da na saka yadi biyu da rabi da na saka, na fito Ya Ado ya ce"

"min. ""Allah yasa kada a koro ki, kin makara."" Murmushi nayi na shiga muka fita, a inda ya saba ajiye ni ya ajiye ni, na dauki jakata na wuce na jira motar kamr kullum muka wuce, ina isa na biya tare da fita na nufi hanyar kamfanin, a hankali nake tafiya kaina a sunkuye. Har na kusan kamfanin na ji muryan Khamis, gabana ne ya fadi. Na kalle shi dauke kai nayi na cigaba da tafiya, karar horn da aka yi fa karfi yasa ni juyawa. Yau shine da kanshi ba Taj ba. Daina bina Khamis yayi, ya tsaya matsawa nayi a gefen hanyar yayi kan Khamis da motar ya matsa yana ihu da dariya kamar mahaukaci. Da yazo kusa da ni,sai ya rage gudun motar yadda nake tafiya a hankali, bar na shiga kamfanin haka yake bin bayana, ajiyar zuciya na sauke ashe bashi daya ba ne a motar shi kan ma yana baya, daya mutumin nan ne. Fita yayi a motar ya nufi hanyar waje. Mai tuka motar ya ce mishi. ""Kaga ka daina zubawa rauni gishiri."" Zuciya ce take cinsa, bai saurare shi ba haka ya fita can ihun Khamis muka ji, bakiWaya muka fito wajen. Aka yi juyin duniyar nan ya sake Khamis amma fir yaki, sai da nace mishi. ""Don Allah ka kyale shi mana!"" Ture shi yayi ya juya tare da damkar hannuna. Har office dinsa ya kai ni, tare da cewa. ""Daga yau ki tsaya a inda ake sauke ki na gaya miki!"" Ya daka min tsawa, shiru nayi tare da rufe idanuna, haka ya fita ya bar ni kamar mayya a office Winsa, shigowa mutumin da suka tawo tare yayi ya zuba min harara ya daka min tsawa. ""Wacece ke? Me yasa saboda ke yake abinda bai taSa yi ba!?"" Kuka ne ya zo min dai-dai lokacin da ya shigo office, ""Tambayar ki nake ba kuka nace ki min ba!"" Ya daka min tsawa, ""Malam ya isheka haka, ya ishe ka nace!"" Ya fada a masifance. ""Bai isa ba Turaki nima zaka dake ni ne kamar yadda ka dake shi, wace ce ita da kake fada akanta?"" Ture mutumin yayi har waje. ""Kada na kara ganinka a inda nake!"" Daga haka ya rufe kofar. Ai kuwa nima ya juya ya fara min fada tare da cewa na zo ina juya jikina har maza na kai min yadda yake fadar kamar ya rufe ni da duka, sannan ya koro ni waje tare da kiran Taj ya zo ya kawo min aikin, nasha kuka kamar an yi min mutuwa sannan na cigaba da aikin kamar jaka, na jiya ban gama ba, yau aka kara kawo min wani aikin, jikina har ciwo yake abinci kuwa taj ya kawo min faten wake da soyayyar agada, naci sai ruwan tea, wurin karfe biyu ya fito cikin fararen kaya, da hular da ya"

"karya, sau daya na kalle shi na cigaba da abinda nake yi."

"Shigowar wasu yan mata na family Winsu, ya sani mikewa nace musu. ""Sannunku da zuwa, da mai za"

"a taimaka muku?"" ""Mun zo miki kashedi ne ki fita harkan hamma Turaki!"" Kallonsu nake kafin na ce musu."" Ayi hakuri ba zan kara shiga harkansa ba!"" "" Aiki kika zo nan, ba shige mishi ba!"" Yadda suka yi ta min maganar banza ni dai ban ce musu kome ba, sai can na ce musu. "" Mr Turaki ya saka cctv idan kuka matsa dayawa zai dauki mataki! "" Na nuna musu, wurin da camera din yake, sai suka fara baya Baya. Bar suka fita, bayan ya dawo na tattara takardun na kai mishi, ya duba sannan ya watsa min a fuska ya ce"

"min. "" Ki gyara basu yi min yadda nake so ba!"" "" Tow"" na kwashe, haka na dawo na zauna karfin hali"

nake amma ni daya nasan yadda nake ji da ciwon ciki amma mutumin nan ya kara dawo min da aiki ba.

"Hawaye ne ya zubo min, haka na kara zama na fara sabon aiki karshe ya fita abinsa, shigowa Taj yazo ya amshi aikin yana taya ni, ni kuma na zauna ina hutawa, muka yi ta hira da Taj har ya gama min aikin ya"

"ce min. ""Aikin na da wahala amma a madadin sai kin sake type kawai copy and paste zaki yi."" "" Kamar ya? "" Na tambaye shi, ina sani. Mikewa nayi kafin ya bani amsa na wuce ban dakin da aka nuna min, na gyara jikina. Ina dawowa na samu baya nan, sai Masifaffen nan ne a tsaye, "" aiki kika zo ko yawo?"" Kasa"

"magana nayi ina kasa domin kwarjini ne da shi, baka iya tsayawa ka kare mishi kallo. Kamar nayi kuka haka na wuce bakina yana rawa nace mishi."" Toilet! Banza ya bawa ajiyata yayi gaba abinsa, takaici ne ya kama na cigaba aiki har karfe biyar da rabi, na mike zan hada kayan fitowa yayi fuskarshi a haWe yayi tare da kafe ni da idanu, diriricewa nayi na fara niman inda zan tsaya kawai sai na koma na zauna, ba magana ba zagi amma wannan idanunsa masu kama da na dodanni, sun iya hukunta mutum. Haka na cigaba da aiki har karfe shida ya wuce. Ina wajen, ban san lokacin da hawaye ya fara zuba min ba. Haka na cigaba da aikin ina kuka. "" Lubnah! "" Naji muryan Jasminah, d'ago kai nayi ina kallonta na fashe da kuka. "" Taso muje!"" Haka na taso ina kuka, "" ina zaki kaita?"" "" Bro lokacin tashi ya wuce fa, idan aikin ya mata yawa."" "" Koma ki cigaba da aikinki"" haka na koma na zauna tare da cigaba da aiki ina shashekar kuka, ya juya ya banko mana kofar. Ya cigaba da aikinsa, ina ta kallon wayata ko Ya Ado zai kira ni, amma bai kira itama Jasminah Yaranta suna ta kiranta, haka ta mike tana gaya musu. ""Gani nan zuwa!"" Kallona tayi ta ce min. ""Hankalin Yaran ya tashi."" Cikin dauriya nace mata. ""Ba kome!"" Na fada tana barin wurin na kurawa kofar office Winsa idanun ina jin wani irin haushinsa, haka na dauke kai na cigaba da aikin har na kammala na koma ban daki na gyara jikina koda na fito babu kowa kusa fitilar wurin a kashe office dinsa ma hasken a kashe, da sauri na tafi wurin zamana na kunna wayata, ina d'ago kai muka yi ido hudu da shi, wani irin kara na sake tare da wurgi da wayata. Zube a kasa tare da rike kirjina da amsa min da wani irin ciwo. Ina haki kunna wutar parlourn yayi ya tsaya tare da hade rai. Kuka na saka ina zaune akan gwiwata. ""Ina da abin yi."" Wato yana jirana, da sauri na mike na hada kayan da na zo da shi. Na bi bayanshi da sauri domin ya kashe wutar parlourn, garin binsa haka na yi karo da bayansa cak ya tsaya nima nayi, tare da ja da baya. Ina jan hancina na ce mishi. ""Sorry sir sorry Sir."" Cigaba yayi da tafiya nima na bi bayansa. Har muka shiga elevator, tsayawa nayi can bayanshi ina sunkuyar da kaina har muka fito kasa. Sai da muka fita aka rufe office din bakiWaya. Wurin motarshi muka nufa baya shiga, ni kuma na shiga gaba. ""Har kun taso?"" ""Eh!"" Na cewa Taj da ya tambaye ni, ""kamar kin yi kuka?"" ""A'a ban yi ba!"" Na fada, zai kara magana Masifaffen nan yayi gyaran murya, haka muka cigaba da tafiyar har muka iso gida, fitowa Taj yayi ya bude boot din motar ya ciro min wasu paper Bag har guda uku, ya ce min. ""Inji Oga gobe Saturday akwai meeting din da za a yi a Eko hotel da fatan zaki shirya da wuri."" ""Har Saturday ma akwai aiki ne?"" ""Eh amma ba wai na office ba. Wasu mutane ne zasu sayi kayan kamfanin yana da kyau ki shirya da wuri!"" ""Gaskiya!"" ""Tow ni yau xan tafi Abuja akan meeting, idan ya ji kina musu tura ki kano zai yi!"" Jin haka yasa na ce mishi. ""Tow shi kenan!"" Mishi godiya tare da shiga cikin gidan, Ya Ado na samu yaran sun kwanta, Aunty Zakiyah tana kitchen, gabansa na je na zauna. ""Yaya na gaji aikin nan ba irin nawa ba ne!"" Na fara mishi kuka. ""Mutumin nan bai da imani, kome nayi fada yake min, ba halin nayi mistake yayi ta faWa kamar ni daya ce na fara kuskure."" Murmushi yayi ya ce min. ""Haka kowa yake farawa, sannan ai ya kira ya gaya min yau da gobe kuna da ganawa da wasu yan kasuwan kasashen ketare, shi yasa ba zaki dawo da wuri ba."" Sake baki nayi ina kallon Ya Ado wato Masifaffen nan ya san kan duniya ya kira Ya Ado ya kare kanshi, kada ace na jima har da fada mishi aikin da muke da shi gobe. """

"Ni dai ba zan je ba!"" Na fada ina kuka. ""Tow shi kenan!"" Ya fada yana kallon kayan da ba shigo da shi,"

kusan kayan ci ne sai pad. Da sauri na maida shi cikin na wuce dakina na can sama na wanka na shiga

"nayi sannan na fito na gyara jikina, na fito na ci abinci sannan na dawo na rage sauran aikin na kwanta. Wayyo Allah dad'i nayi barci har karfe tara na safe, don cikin dare da na sauya pad na koma na kwanta ban kara bude ido ba. Sai da na ji ana buga min gadon na bude idanuna."" Kin yi baki suna parlour."" "" Baki kuma? Su waye?"" Na tambaye ta bata kula ni ba tayi tafiyarta, hulata na dauka na saka akan riga da wando na barcin da yake jikina. Ban daki na shiga na yi brush na wanke fuskana sannan na fito,. Na sauko kasa ina faWin. "" Kuma dai weekend din ma ina murna na rabu da jarabar wancan Masifaffen"

mutumin me kama da yan damben turawa.......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 51"

"""Fisabiilillahi ko a gidan gwamnati Asabar da Lahadi hutu ake. Ni yanzu ko Gym na daina zuwa tunda na"

"fara wannan aikin me shegen wahala waye ya sani ko sai na gama aikin ma karshe a ce za a kore, Aunty Mutumin nan ya cika barga, haka ya min shekaranjiya wai zai kore ni, ko jiya oho. Kin ga yadda ke tafiya kamar wani robot"" Na sauko har parlourn, ina kwaikwayar tafiyarsa, kawai kamar ance ns duba kujeran da yake kallon tv, da sauri nayi baya ina faWin. "" Innalillahi! "" Nayi baya ina toshe bakina, kafin na juya da wani Muslimin gudu aikuwa na ji abu ya kwashe ni sama, na hantsila tare da dokuwa da kasa, takalmina kafa daya yayi tsalle sai a fuskarsa, Allah ban san lokacin da na ce. ""Na mutu!"" Na tashi na haura sama da gudu, ina fadin shi kenan. Abin ya zo wani iri amma kuma Ya Ado sai da yayi dariya yana faWin. ""Silly girl, don Allah ka yi hakuri bamu san zata fito tana mocking dinka ba don Allah ka yi hakuri!"" Murmushin yake yayi yana faWin.. ""Muna jiranta."" Ya saka kai ya fita, bai san dalilin da yake son ya ganta a kusa da shi ba. Bai sai me yasa yake jin haushinta ba, amma a duk lokacin da ya ganta yana jin kamar ita din da ya sani can ita ce a gabanshi. Sai dai ita wannan ta sauya dayawa. Fitowa yayi waje, wato asalin yadda aka yi ya shiga cikin gidan, ya zo ya tsaya tare da tunanin wanda zai tura cikin gidan sai ga Ya Ado ya dawo daga Gym da yake weekend yana zuwa, kawai sai ya ganshi a kofar gidan, har zai wuce sai ya dawo ya mika mishi hannu suka gaisa ya ce mishi. ""Kana son ganin Lubnah ko?"" ""Eh"" kawai sabo da a fakaice kallon Ya Ado yake yason ya ga ko mijinta ne amma wani abun mamaki sai ya ga suna kama da Lubnah, sai ya kauda kai har ya ado ya ce mishi zai duba ko ta shirya, yana zuwa ya samu tana barci shi ne ya fita tare da shigo da shi cikin gidan. Shine ta mishi rashin mutunci. Lashe bakinshi yayi yana godewa Allah da iya"

"shi kaWai yazo bai dauko wani ba, balle ya sha kunya."

"Tunda na shiga nake jin kamar zuciyata zata kwace a kirjina, ""wayyo Allah na!"" Na fada a hankali,"

"kamar xan yi kuka. Buga kofar aka yi daga waje Ya ado ya ce min. ""Ki fito yana jiranki, kuma zaki sani ba dai bakinki bai da lizami ba"" bude kofar nayi da karfi ina faWin. ""Ya ado kun san shine ya zo, ba ku gaya"

"min ba."" ""Je ki shirya yana jiranki ai ba zai nuna miki ya ji me kika ce."""

"Kamar nayi kuka haka na haura nayi wanka na shirya tsaf, sannan na dauko abaya na saka tare da"

daura hula kafin na saka gyale na nad'e kaina. Haka na shirya ina fitowa Aunty Zakiyah tana mika min

"wata yar jaka tana faWin."" Baki karya ba, gashi nan ki karya a can."" Kamar nayi kuka haka na fito kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki. Har waje na fito yana mota, ina zuwa na gwada bude bayan mota"

"amma a rufe gaban na zaga na bude na zauna. Kasa kallonshi nayi domin sai yanzu nake jin abin a raina,"

"har ya tashi motar ban iya ce mishi cikanka ba. Ni kaina kamar na nutse kasa, haka ya cigaba da tuki cikin kwarewa. Wani unguwa muka isa wanda yake bakin ruwa. Yayi horn a bakin kofar gidan.

Please Login or Register in order to submit comment