gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu Chapter 35 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ji wurin. Ni bayan gabana balle ya ce don kuWinsa nake, ni magana da"

Ubaid ya gaya min ma ya ishe ni.

**

KUMO FAMILY

"Fada Alhaji ELYakub Kumo yake kamar ya mari Uncle Auta, ya ce mishi.""kasan tana tare da Yaron nan ne"

"saboda kai, amma ka gaya mishi wacece Yarinyar bayan ba kaunarshi yake da gaske ba, ina sane da cewa Turaki yana bin ra'ayinka ne yake kula Yaron nan, kada ka kara bawa wani labarin rayuwar Turaki."

"Da shi da aka hada baki aka kore shi a shekarar karshen shi a secondry School, kasan sharrin da ya so a"

"kulla mishi? Kasan yadda ya lalata mishi rayuwa? Ban da Allah yana tare da shi da rayuwarsa tafi haka lalacewar don Allah kada ka kara gaya mishi kome akan Bilal wanda ya mishi a baya ma, ya isa yanzu meye ribar shiga rayuwarsa?"" Yadda yake shiga ba nan yake fita ba, fada kamar zai mari Uncle Auta. Yayi"

fada sosai domin kuwa yana jin zafin abinda Ubaid yayiwa Turaki a lokacin.

"Abu guda biyu da suka lalata alakar Turaki da Ubaid na wani abu ne, duk da kowani mutane yana da"

"hali me kyau ko mara kyau, idan har Turaki yayi kuskure tow ya dace ya samu mutumin da zai tsaya a tare shi, tow har ana niman haka tow Ubaid ya kai wannan matsayin, sai dai tun suna Yara Ubaid baya kaunar Turaki yayi sabon aboki ko kuma ya taimakawa wani, yayi ta fushi da kuncin rai kenan. Duk yadda za'a gaya maka matukar ba faruwa yayi da kai ba, ba zaka gane ba. Ubaid ya bawa Bilal wahala akan wannan lamarin domin Ubaid yana ganin Turaki da sabon aboki yayi ta fushi kenan har sai ya raba shi da abokin, sai da Ubaid ya kai ko me turaki zai yi to bai iya ba shi Waya ya iya. (Sometimes silent pain"

"yana kashe mutane dayawa, lokaci yayi da zaka fadi ra'ayinka lokaci yayi da zaka rusa wancan bond din"

da kake gani kamar sasari ne let move together)

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 59"

"Abinda ya fara faruwa shine kama yara da aka yi suna lalacewa a cikin Makarantar, wnada a lokacin"

"iyayensu suka raye maza sun zo akan case Win, wanda yayi sanadiyar da Turaki ya bar makarantar domin Ubaid ya bada shaidar yana lalacewa irin ta mazan da aka tsinewa, kasancewar akwai kyakkyawar alaka tsakanin kakaninshi na Rasha da kasar Saudiya musamman ta harkan kasuwanci suka kashe zancen ya"

koma Rasha wurin kakarshi sai da ya dauki wata goma ya koma Saudiya yayi jarabawar barin makaranta.

"Daga nan ya koma can yayi jami'arsa a lokacin Ubaid azo suka yi karatun tare, duk da wannan abinda"

"yayi mishi yayi hakuri sai ya kasance duk wani abin asha kiri-kiri Ubaid yake danganta shi da Turaki, amma bai taSa kawowa a ransa yana haka ne don ya cutar da shi ba,"

"A hankali yayi ta amfani da wannan damar yana raba Turaki da duk wanda ya zo gare shi, ana haka"

"iyayensu suka rasu mazan sai da Hajiya Amina mahaifiyar Ubaid zata koma gida Alhaji ELYakub ya amshi rikon Ubaid yace idan ya tafi Turaki zai shiga kadaici, a wannan lokacin kowa ya amshi haka amma kuma a ransu basu son Ubaid din da Turaki domin kowa so yake ya rabu Turaki ya cutar da shi, amma an rasa yadda za ayi, ba a san me ya faru ba. Amma lokacin amma wani satar da aka yi a cikin gidan ElYakub kumo wanda ya girgiza ilahirin family ana cikin binciken baa tambaye shi ba, kawai ya ce ai Turaki ne yayi satan wani abin takaici aka nime kudin ba a samu a wurin Turaki, a lokacin fushin da Turaki yayi dakyar aka shawo kanshi yake kula shi, babban rigimarsu shine akan Mimih wanda aka ce zai aikata, a lokacin ya ce zai aikata ya ci-gaba daga maza ya koma kan mata, tun daga wannan lokacin Turaki ya watsar da shi, amma yana kyautatawa Iyalinsa da duk wani dangin mahaifinsa da na Mahaifiyarshi. Amma ya yanke duk wani abu da yake tsakaninsu, ko rike office din Turaki da yayi ai Alhaji ELYakub ya bashi domin kusan"

shima bai da mutunci akan gaskiya zai iya aikata kome.

Yadda alakarsu ya lalace musamman yadda yake zargin Turaki yafi kome bashi haushi.

***

"""Ke bana son rashin hankali, ya zaa yi ace mutum ya zo baki sauko kun gaisa ba."" Tura baki nayi nace"

"mata. ""Wurinki dai ya zo!"" ""Amma kanki daya kuwa!"" Mirgina mata kaina nayi nace mata. ""Kin ga shi Waya ne babu kari!"" Make ni tayi, haka ta fita, na tura baki ina ruwana da shi. Ba dai ga shi bayan isha ba, muna parlour muna kallon super story, da yake Alhamis ne, zare idanun nayi kaina yana cinyar Mama tana zaune a kasa nima na kwantar da kaina akan cinyarta. Lumshe idanuna nayi kamar me barci, ai kuwa cikin ikon Allah barci yayi gaba da ni, nan suka shiga hira har tara tayi, na musu sallama ya tafi yana fita daga parlourn Mama ta zuba min mari a kafada. ""Tashi ja'ira yau kin kunyata ni!"" Sosa wurin nake ina tura baki. ""Allah ya shirya ki!"" Tashi nayi na wuce sama, washi gari ba naki zuwa aiki ba, sai ga Taj da aika tulin aiki kamar nayi hauka Mama kuma taki bani goyan baya, haka nayi ta aiki kamar jaka kwana biyu nayi ina aiki. Dole ranar Monday na koma aiki domin aikin kamar zai hallaka ni. Tun da na dawo sai na ga yayi sanyi ba masifar nan, nima kuma wannan karon sai na kama kaina. BakiWaya satin Mama biyu ta bar Lagos, bamu gaya mishi ba. Haka aka fara azumi, azumi na da kwana biyu muka wuce Umara, ashe ta Bauchi Mama itama ta zo haka muka yi ta ibada tayi min addu'a kamar zata kara haifa na, wani jallabiya me tsadar gaske Mama ta saya mishi da agogon azurfa da zube, ta saya mishi da wani turare wanda kuWinsa zai kai Naira dubu dari biyu, hidimar da tayi mishi kamar wani danta haushi suka bani har da kukana bata saya min ba, haka ta haWa min a kayana, wai na kawo mishi haka nayi ta mita ina kuka, sallah saura kwana tara muka dawo, cike da farin ciki muka iso, kwana uku na dawo aiki yadda zaku san bana gabanshi, kallo Waya yayi min yayi ta wani cin magani. Tsarabar Sarah da Taj, Sai na Jasminah da"

Yaranta. Shi kuwa ko dabino ban bashi ba. Uncle Auta kuwa da ya min barka da dawowa na bashi

"kyautar wani zoben azurfa da turare. Wayyo Allah, ina wutar da za a saka ni. Fushi sosai yayi, ya daina"

"min magana sai dai Taj ya min Magana. Ina sane nayi mishi wannan wulakancin. Sallah saura kwana biyar aka bamu hutu kowa yayi Sallah, wannan shine karon farko da zan zo Bauchi sallah."

"Sakonsa na wurina da Mama ta bani yaki zuwa gidanmu, ranar na kira Taj ya zo ya amsa na gaya mishi"

"inji Mama ta turo mishi. Bayan an sha ruwa Mama ta kira ni, ""ke ce kika bashi number na ya kira sai godiya yake min, wato ke dai ba zaki bar halinki ba, sai yanzu kika bashi sakon?"" ""Mama daga shan ruwa zaki fara min faWa."" Murmushi tayi tana faWin. ""Allah ya shirya ki!"" Nan muka sha hira, ban san Ya aka yi yasan zamu je Bauchi sallah ba, koda yake ba mamaki Mama ta gaya mishi. Haka yazo da katon jaka wai na kaiwa Mama kayan sallah da na azumi da bai mata. Kallon kayan nayi na nad'e hannun a kirjina. Lashe baki nayi nace mishi. ""Kayi hakuri ba zan tafi da kayan nan ba!"" Na fada ina me juyawa zan bar wurin ya ce."" Ai ba ke na bawa ba, wa Mama na ce a kai min idan ma baki ba ai shi san zai kai min!"" Takaici ya sa na juya ina kallonshi amma kwarjininsa da cikar halittarsa ya sa ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina cizon bakina. ""Dauka ba naki ba ne!"" Y fada yana shiga motarshi ya bar gidan nan wannan dan renin hankali ne wallahi, dauka nayi na tura mishi da sakon. *Don Allah wannan ya zama last da zaka kara"

"kawo mata kaya because we are not money Morga, min iya da rufin asirinmu*"

"Daga haka na wurga da wayar ina hararan kayan kamar na rufe shi da duka. Haka na wuni da takaici,"

"washi gari muka nufi airport domin da wuri muke son shiga Bauchi, tunda Ya Umar yana hanyar Jos. Abin ya matukar min dad'i sai dai me muna isa airport Win na hango shi. Suka gaisa da Ya Ado a raina na ce *wannan kamar maye* wai ma ya aka yi wancan lokacin na iya biyewa shashancina na kula wannan mutumin, haushin kaina na ji sosai fa. Da gayya na saka airpies a kunne na, har zuwa lokacin da muka tashi tafiya. Ashe shima Gombe zai wuce, tab'e baki nayi har muka bar lagos idanuna a rufe. Karfe daya na rana muka sauka a Jos, muna isowa sallah muka yi a masallacin da yake gefen airport Win, muka yi sallah Aunty Raliyah ta kawo mana kayan lambu da fruit, daga nan muka yi sallama. Bamu tsaya ko ina ba sai a nabardo muka sayi fura da nono, sannan muka wuce Bauchi. Karfe hudu saura muka isa dutsen tanshi, na yi kewar Bauchi sai na zama kamar Bakuwa haka muka isa gidan, da yake cike da yan karban sadaka. Mun samu tarba a wurin Yan uwana da suka zo shan ruwa tunda aka ce zan zo na ga gata sai da nayi kuka don farin ciki. Abba ma ba yabo ba fallasa haka muka gaisa. Ranar sai sha daya Yayuna suka bar gidan na kwana a bayan Mamana, cike da so da kauna nayi kewarta. Lokacin da na tashi sahur na ga sakonshi. _Da fatan kun isa lafiya ya Mamana da Abba tare da Yadiko? Nima na isa lafiya._ share text din naso yi sai na ji ban kyauta ba, kawai sai na tura mishi..*Alhamdulillahi kai ma ya naka tafiyar? Da fatan ka isa lafiya,* can kamar minti Waya zuwa biyu sai ga sakonshi. _Masha Allah, baki ce min akan Mamana ba?_ wani iyayi da shishigi tura mishi nayi da ce. *Oops tana lafiya* daga haka na share wayar na cigaba da abinda nake, bayan na idar da sahur nayi Nafilla, sannan na zauna aka yi sallah asuba, kafin na kwanta ban tashi ba sai karfe daya, muka yi wanka ashe Aunty Zakiyah ta wuce gidanta da yake Ibrahim bako tare da kannenta maza biyu da mata uku, kiranta nayi a waya nace mata. ""Shine baki tashe"

"n?"""

"""Ikon Allah Auta ta zo wurin Mamanta taya xan tashe ta, jinjira tana jin dumin Mama!"" "" Aunty"

"Zakiyah gaya min magana mike fa a fakaice fa! "" Dariya tayi tana faWin. ""Allah Yayanki ya ce a bar ki wurin Abba shi yasa ban tashe ki ba, kuma suna bukatar wani a kusa da su. "" Haka na jita, muka rabu na fito n taya su Mama aiki Abba yana tsakar gidan yana jin yadda Mama take waya da Turaki tana ta saka mishi albarka, ta ji dadin wannan sakon da ya aiko mata, bayan ta gama ta kalli Abba ta ce mishi."" Mai gidanta na wurin aikin ta ne ya turo min sako!"" Ina jin ta tana gaya mishi har da wani shadda ya turo bashi yace baya son kayan da sai da aka sabawa Allah sannan aka kawo ni. ""Eh fa haka ne, bayan saSon Allah ya wuce na annobar da aka kawo muku a cikin zuri'a, in sha Allah taraba da yasin zamu cigaba saboda harshenku!"" Inji Yadiko, Mama kan murmushi tayi tana faWin.""Ai shi kenan! Zan turawa Yayana"

"ya samu a mishi dinkin layya."""

Bayan isha ta dauki turmin yadiko ya bata tare da sauran kyaututtukan da ya hada har da madara da

"milo, duk ta turawa Yadiko, kaya ne me tsada. Washi gari ana gobe sallah aka nimo mana mai lalle ni da Yaran Jiddah da Ummu da aunty Zakiyah aka zo aka mana sallah da yake baki suna zuwa daga Jamaare su ne suka yi aikin kome mu kan ana mana lallen hannu da kafa ni kan ja aka min me kyau da Waukar idanu, a daren muka wuce gidan Aunty Hindatu aka mana saloon a can wurin karfe biyu na dare muka dawo. Washi gari tun asuba muka tashi, muka tashi saboda Masallacin Malam Idris zamu bi. Da wuri muka fita domin bakwai yake sallah idininsa, muna idarwa muka iso gida ta saman dutse, muna shigowa"

"gidan aka sake shewa aka rungume juna, nan aka bude chapter yaushe gamo."

"Kusan kowa yayi kewata, Aunty Munah tana azare sun zo itama zasu karaso Bauchi, haka muka yi ta"

"farin ciki. Har dare ana tare sai hoto ake, sai lokacin Mama ta kawo musu tsarabar da Turaki ya turo ni da shi, ta cirewa Yaranta kowa turmi turmi, dakin Yadiko ma ta cire musu, bayan tafiyarsu na shiga wurin Abba da aka ce yana kirana, kaina a sunkuye yayi shiru. Kafin ya ce min. ""Shi abokin shaidancinki, aurenki zai yi?"" Rike zuciyata nayi amma tabbas yadda Abba yake danganta Turaki da wasu irin kalmai yana saka ni jin wani irin yanayi, mutumin da ko hannuna bai taba rikewa ba, me yasa Abba yake yin haka ne?"

"Haka ya gama fadarshi iya hakuri nake bashi ina kara nutsuwar da kai na, har zuwa ya gama abinda yake"

"sannan ya ce na je, lokacin da na koma daki Mama tayi tayi tasan me yake faruwa ban gaya mata ba."

-Washi gari.

Tun safe na ga Mama da Yadiko suna ta aiki kamar zasu yi wani abincin sallah bayan daga gidan Yayuna

"ake kawowa sallah da kwana biyu ake wunin gidanmu, haka yasa nayi ta mamaki. Amma ban tambaya ba don yadda suke aikin cikin nishadi, na fahimci akwai wani abu."

"Wurin karfe tara muna gama shirin tafiya kallon hawa da yake a g.r.a muke kallon, Ya Sani dasu Aunty"

"Inna muna dauki wata sienna muka fita bayan Ya Ado ya turo kudi aka zuba a cikin motar. Muka fita sai kudin da Ya Umar ya bamu, haka muka tafi da kular ruwa da kayan ciye-ciye, haka muka kutsa da kyar zuwa old GRA Bauchi daidai alhayat nan muka samu wuri har an fara wucewa. Sanye nake da wata lace"

"mint green wanda aka min dinki Bubu sai daurin da na kafa a kaina mayafina fari ne da takalmi da jakana,"

"sai madubin da na saka. Ruma Mai shadda muka hadu da ita ina tsaye da lema. ""Lubnah Shehu Umar?"""

"Dariya muka saka, na isa inda take ina mai amsar Yaronta alamar sabon haihuwa ce. ""Mai shadda kece haka? Kin zama Mama!"" ""Ke nan ce min zama wata yar 18yrs ba sai ni yar renin wayo!"" Wata yar budurwa Yarta na gani tana mai gaishe ni, ta hado kan kannenta. ""Ruma beautiful familynki kenan?"" Murmushi tayi tana faWin. "" Kema ai naki suna hanya in sha Allah, ki ,zuba idanun suna nan tafe fa wallahi uku uku zaki ya dirke mata duk bayan shekara daya."" Murmushi nayi amma nasan ni ai narasa wanan damar har abada. Haka muka sha hira kafin ta wuce. Sai bayan tafiyarta na nutsu sosai. Ina son Yara, ina son Yara amma ni bani da rabon Yaran domin na gama da mahaifana. Taya xan samu haihuwa ko nayi aure? Ina ga Madadin na sakawa kaina damuwar auren gara na hakura na rike aikina, domin babu namiji da zai aure ne ba tare da ya karu da ni ba. Tab'a ni Aunty Innah tayi na kalle ta. ""Na ga tun kawarki ta tafi kike tunani, shi fa aure da haihuwa na Allah ne idan kika yi hakuri Allah zai baki wanda baki zata ba. Ki kasance mai yarda da addara da kuma hakuri da juriya, wallahi ba kowa Allah yake jarabta ba, sai mai imani a jarabce ka ma Allah yana sonka ne ga mutane dayawa suna saSon Allah kuma suna raye me yafi wannan muni, ki saka a ranki kome ya baki rabonki ne idan bai yi niyya ba Alhamdulillahi ba akanki aka fara haka ba. Ki godewa Allah kina muslma mai imani da addara."

"Alhamdulillahi da Allah ya raba ki da wancan Tsinannen da ko Abba bai bari ba, ke Alhamdulillahi kin auna arziki domin da kina nan tare da shi da kin mutu ba wanda ya san yadda kike cin azaba gashi daga rabuwarku har yau bai kara ajiye mace ba, itama Yarinyar da auro a Gyembu a kotu suka rabu, hmmm yanxu haka a Jama'aren an hana shi aure, domin kuwa cewa suke tunda ya iya rabuwa da ke babu Macen da zai samu ya rike tsakani da Allah. "" Abin sai ya zo min bazata wato idan baka da hakkin mutum sai Allah ya fito da kome sarari, a yadda nake jin labarin kamar a mafarki wai Ya Hafiz ne yake ikirarin sai"

samu wacce zata zauna da shi hm.......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 60"

"A lokacin da ya sake ni yadda yayi ta alfahari da zai samu mata na ribibinsa, sai na ji jikina ya mutu murus."

"Haka na cigaba da. Kallon amma bani da karsashi har zuwa lokacin da aka tashi karfe daya na rana muka dawo gida amma naji suna cewa zasu wuce kofar fada a can za ayi kallon na gaske. Tunda nayi sallah duhar nake kwance ina jin hayaniyar mutane. Ban kawo baki gidan aka yi ba, domin ina can uwar dakan Yadiko s gadonta. A hankali barci ya fara fisgata sai dai tashina Hashiya tayi na bude idanuna kanta. ""Mene ne?"" ""Wai kin yi baki ne fa."" ""Ni kuma?"" Na tambayi kaina, na juyar da kai na lumshe idanuna barci ya kara gaba da ni. ""Ke tashi baki kika yi daga Gombe?"" Ban san lokacin da dirko daga gadon ba. Na zare idanu kafin na fito da sauri, riko ni Yadiko tayi tana faWin. ""Ina dan kwallinki?"" Da sauri na koma dakin na hada da Hijab dinta da nayi sallah na fito. A parlourn Abba na ji ana ta hira sama-sama, daga yadda gidan ya dauki kamshin turarensa na san cewa wannan mutumin ya zo gidan mu, parlourn Mama na shiga na samu Aunty Kubra Yar Umma Uwani. ""Auta a ina kika samo mana bature? Ya Salam wani hanin ga Allah baiwa ce."" Banza nayi mata na wuce dakin Mama da take sallah, zama nayi ina kallonta idanuna cike da kwalla, taka idarwa tayi ta kwararo addu'a har da hawayenta. Kafin muka shafa da ita na ce mata. ""Dama kin san da zuwansa ne?"" ""Koransa zan yi ne?"" ""Mama zai ga kamar muna mishi ya wani abu ne?"" ""Kuma haka ko? Matsa can ja'ira. Ko ance ban san kuna turowa juna sakon Barka da shan ruwa"

"da kuma Barka da sahur ba?"" Ban kara mamaki ba sai da na ga ashe kayan da muka kawo mata na"

"wurinsa ne a jikin matar nan, rike bakina nayi ina kallon abin mamaki anyi mata Winkin riga da zani, ita da"

"yadiko kayan suka saka, fitowa tayi tana faWin cewa."" Kubra gaskiya Abdulkarim dan albarka ne jiya aka kai kayan nan da darren amma ki ga yadda ya dinka yau kaya sun min cib ni da Yadiko."

"Sake baki nayi wato gidan nan an iya zaga ka ayi abu daga baya ka sani,ji nayi kamar nai kuka. Ina"

"tsaye Yadiko ta shigo da wasu roses irin na da can sai wasu dangaran aka shiga zuba cin-cin da na kiya, tangaran kuma aka zuba cake da donut, ke dai Mama da Yadiko sun ci amanata, asalin cin amanata matan nan dun yi shi, sai na rasa bakin magana Hashiya suka kira tayi ta kwashe abincin ta kaiwa parlourn Abba, ni kuma Mama ta ce min. ""Zaki tashi ki gyara jikinki, ke tafi ka kiyi sabon wanka wannan tsamin ranar da kike yi Allah kaWai yasan hakurin da muke yi da wannan lamarin tsamin."" Kallon kaina nake ina mamakin yadda Mama suka ci amanata, ban gama wartsakewa ba Yadiko ta ce min. ""Auta tsayuwar me kike don Allah je ki yi wanka!"" ""Ni wani wanka xan kara?"" Na fada ina tura baki. ""Ai gara ki nuna musu ke kyakyawar kazama ce."" Inji Mama sake baki nayi anya Mama bata ci amanata ba akan Sir Turaki, tura baki nayi ina fadin. ""Mama cin hancin da ya baku ne zaku mai da ni bare?"" Wani d'ago kai tayi ta kalle ni sau daya sannan ta cigaba da aikinsa, make kaina Yadiko tayi tana faWin. ""Wuce maza kafin na kwala miki murfin nan a katon kanki!"" Daga haka na wuce simi-simi, wankar da ban yi niyya ba, shi suka saka ni nayi bayan na fito na samu Mama bude akwatinta wata riga da zani dinkin born style aka yi mishi, ta ciro min ta ajiye da mayafinsa babba me kyau sai turare wanda Yaranta suke saya mata ta ajiye min, da wani takalmi me kyau ga tsada ta ce min. ""Ibrahim ya turo min daga kasar waje ga jakarshi nan, Munah taso na bawa Innah domin ta hannunta ya fado, ni kuwa nace ba zan bada ba, ita Yadikonku ta bawa matar Sani nata. Na ce autata zan bawa."" Ta fada tana ajiye min, ta cigaba da zaro min kaya daga akwatin tana faWa min wanda suka bata, amma ni ta barwa tasa ayi ta dinka min koda nayi aure dangin miji ba zasu ce suturarsu nake sakawa ba. Murmushi nayi nace mata. ""Na gode sosai Mama!"" Na rungume ta ina jin kuka. ""Ke kada ki bata fuskarki!"" Ta ce min tana murmushi, haka na fito bayan wani lokaci Hashiya ta ce min. ""Aunty ki shiga Abba ya koma parlourn Yadiko!"" Tunda ta fadi haka na kai"

"kusan minti goma a wurin sai da Mama ta fito na tashi a hankali, na fito waje ina jin gabana yana faduwa. A hankali na tura labulen parlourn na shiga da sallama, idanunsa yana kaina. HaWa idanu muka yi na sunkuyar da kai, ina me shiga parlourn da sallama, na samu wuri na zauna a kasar kafet. ""Barkanku da sallah?"" Muryan mutum biyu na ji sun amsa, shi bai amsa ba. D'ago kai nayi zan kara tambayarsu ya hanya na ga idanunsa a lumshe. Sunkuyar da kai nayi kasa. ""Ya Hanya da fatan anyi sallah lafiya!"" ""Alhamdulillahi!"" ""Lubnah ashe a Lagos yanzu kike aiki?"" Ba zan manta da muryan Malam Hamza ba, cikin murmushin yake na ce mishi. ""Eh Malam!"" ""Jamil ka ji ikon Allah, kuma a kamfanin Malam Bilal"

"take aiki ba"" tabbas yanzu na tuna da asalin shine malam Bilal? A raina na fadi haka daidai bude idanunsa wanda yayi kicibis da d'ago kaina, muka zubawa juna idanun. Wani abu nake ji s cikin idanunsa, wanda har jikina yana amsawa, nayi kasa da kaina ina wasa da yatsuna, shi kuma ya cigaba sauke sirrintaccen ajiyar zuciya a hankali a hankali. Yarinyar nan ta shammace shi fiye da yadda yake"

"tsammanin, ya zata yana da wayo ne amma shi bai san cewa ita din kallonsa take ganga ba rufi ba,"

Two hours ago.

"Lokacin da ya iso Bauchi awa biyu da suka wuce, yana hanyar Gombe har ya kusan shiga alkaleri ya kira"

"Number Malam Hamza duk da sun jima basu gaisa ba, amma akwai wani abu da yayi da har yanzu alakarsu take nan, shine bayan ya bar Bauchi sai da ya bawa Malam Hamza aiki a daya daya cikin kamfaninsu na kano, yanzu haka a can kano yake aiki. Shi kuma Malam Jamil dama karatu zai koma ya mishi hanya ya koma yanzu haka yana koyarwa a jami'ar jahar Bauchi na gadau. Kuma sanadin da suka tsaya da kafarsu, yana kiran Malam Hamza da yake suma basu manta da halaccin da yayi musu ba, yana fada mishi gashi nan a Bauchi shima ya kira Malam Jamil ya gaya mishi, take suka shiga musun inda zai saka, nan suka. Kara kiransa suka gaya mishi rigimarsu, dariya yayi musu ya ce su jira shi zasu tafi gaisuwa ne gidansu Iyayen Lubnah. Mamaki

Please Login or Register in order to submit comment