gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu Chapter 32 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu tafi na gaya mishi."" ""Kayi hakuri ba zan bika ba."" Na fada na cigaba da aikina, ai kuwa ya ja kujera ya zauna ya zuba tagumi yana kallona, har kawunsa ya shigo tare da yan uwansa, yadda ya hade rai ya watsa min kallon banza, na rasa yadda zan yi d Tarik haka ya dame ni amma shi Masifaffen duniya gani"

yake ni nake kiran Tarik.

"""Zan dakata da Yaron nan, domin ya hana yarinyar nan aikinta."" Ya fada yana cire tie din wuyarshi sai"

"ga Tarik Win ya shigo office din, "" Uncle B please ka ce Lulu ta raka ni ina jin yunwa ne!"" Yadda yayi rikon"

"sai da yaji kamar ya mutu, domin ya tsani wani da namiji yana like mata kamar wani kaska. ""Ba inda zata bika, kai baka ganta bata cika shiga abinda bai dame ta ba."""

""" Ok tunda kai ka ki bari na kira San na gaya mishi."" Ya fada yana dauko wayarshi ya kira Ya Ado ya"

"koro mishi jawabi. Ya Ado zuciyarshi daya ya ce shi kenan zai mata magana. Ai kuwa ya juya yayiwa kawunsa bye bye, ya bar office Win. Shiru CEO yayi bai san lokacin da ya mike ba, a zafaffe ya nufi waje yana fitowa ya samu suna ta musu, cewa yayi. ""Ku zo muje!"" Y fada kai tsaye haka na hada kayana, na saka a locker na bi bayansu, haka muka je wajen cin abinci na Chinese dish, nan muka je ya kai mu har can VIP aka yi oda, aka jera mana, ni dai ban wani saba cin abinci a gaban jama'a ba, haka Tarik ya yi ta zuba min abinci domin ya ado ya gaya mishi ina kula da abinda Zanci, sai yake zaba min abinda zanci da kuma wanda ba zai yiwu na ci ba, abun sai ya bawa CEO mamaki yana kallon yadda yake cire duk wani abin da ba zan ci ba, har ya kira waiter Winsu ya ce ga irin drinks din da zan sha, sai gashi kuwa an kawo ina kallonshi cike da mamaki. ""Ci wannan tsokar kifi ne, zai fi kici irinsu shrimp da danginsu kaza da sauran danginsu ba naki ba ne. Ci iya mune Uncle ya sayi wurin baki daya."" Tashi kuwa Uncle dinsa yayi ya dauki abincin ya kai wani table din ya ajiye min ya kara zuwa ya dauki juice din da ruwan ya ce min. ""Je can ki ci!"" Tashi nayi na je wajen na basu baya, tashi Tarik yayi ya rike hannunsa. ""Kasan bana wasa a kalmaina!"" Yadda yayi magana yasa ya zauna, ya cigaba da latsa wayarshi ya cigaba da cewa. ""Yarinyar nan matar aure ce. A Muslunce kuwa haramun ne bibiyar matar aure. Ina baka shawarar ka koma Berlin ka ji aiki!"" Gyada kai yayi yadda yayi mishi magana a nutse yasa Yaron ya fahimta. Haka muka gama cin abincin, sannan muka bar shagon, kamfani muka wuce. Haka na cigaba da aiki. Tunda muka fito naga jikinsa yayi sanyi. Har muka tashi, na dawo ban ga kiranshi ba na tab'a shi ya ce min jikinshi ne baya jin dad'i, haka muka yi magana sama sama, da dare kuwa aikin gabana na rage, sannan na cigaba da sabgogina. Ni dai ban san me ya faru ba washi gari na iso na sami Dan uwan CEO, yana ganina ya hade rai. ""Wacece ke?"" ""Ni kuma?"" Daka min tsawa, nayi baya domin a gaban jama'a yake min fada da masifar da na ga kamar gadonta suka yi domin kows a cikinsu Masifaffe ne, ""sir mai nayi kuma?"" ""Ki tafi an dakatar dake!"" ""Me nayi to?"" ""Idan baki min shiru ba sai na mare ki!""dariya nayi na ce mishi. ""Maybe baka san wacece ni ba, idan ka mare ni zan rama no matter how, zan mara kuma da kake min ihu so what idan ka ce na bar kamfanin ni ban fito gidan da ake jin yinwa ba, ba ina aikin nan don cika cikina da yake jin yunwa ba ne, ba zai yiwu kowa ya zo ya ce zai taka ni ba. Kudi ko daukaka muna da shi a gidanmu I'm not beggar da zaka na min ihu,kudin kamfaninku ba zai saka ni nayi arziki ko talauci ba, so ba kai ka Wauke ni aiki ba, amma nasan kana cikin waWanda suka dauke ni aiki."" Na juya na cire ID din da yake makale a wuyata, na juya zan fita bayan na ajiye a kan table din Mrs stalle. Idanuna suka fada cikin na shi, dauke kai nayi, a yau na ga wani abu da ban tab'a gani ba, tsoro da tashin hankali. Haka na gyara zaman jakata na wuce zan bar cikin kamfanin. ""Ban karbi ajiye aikin ba! Kuma ki same ni a office ina"

"jiranki!"""

"Sannan ya wuce ba tare da ya cewa Ubaid uffan ba, yadda ya wuce haka abun ta bashi mamaki ya ce"

"mishi. "" N dakatar da ita ka dawo da ita?"" "" Ka rubuto min korafi a takarda sai na san me zan yi."" Daga ya wuce shi, nima da na kame a wurin kamar an dasa ni, haka sai naji kamar ban cancanci zama a cikin kamfanin ba, haka na juya na bi bayanshi yana tsaye a bakin kofar elevator, ina zuwa na amshi jakarshi. Bai ce min kome ba, haka yasa na sunkuyar da kai. Har muka isa office dinmu daga nan ya shiga cikin na kai jakar na fitar da menu, sannan na gama na fito na zo na zauna kenan sai ga Jasminah da Badr"

"kallonta nayi na ga kamar na santa.."" Lubnah me ya faru? "" Nan na gaya mata gaskiya abinda ya faru,"

shiru tayi kafin ta shiga cikin office din Dan uwanta. Ban san me suka yi ba na ga ta fito daga cikin office

"din ta tsaya a kaina ta ce min."" Ki yi hakuri kin ji matsalar akwai munafikai ne! "" Tana barin wurina, Badr ta kalle ni. "" Ke mayya ce? "" Ta tambaye ni, kallonta nayi nima na ce Mata. "" Inda kika ci anan naci nawa"" cikin fusata ya d'ago hannu zata mare ni, ai kuwa na rike hannunta, tare da murda shi, domin ba girma ta tayi ba, na murde hannun da karfi sai da yayi ara arfi, nace mata. ""Kalle ni da kyau ni ba sa'arki ba ce, kika kara zuwa inda nake sai nayi maganinki!"" Na ture hannunta sannan na cigaba da aikina, kiran wayar"

yayi na mike na shiga lokacin har ta bar office din.

"Ina shiga na tsaya a gabanshi, tare da sunkuyar da kaina, ya zuba min idanu ban san tunanin me yake"

yi ba.

_Yarinyar da ya sani a shekarun baya irin yaran nan ne masu hankali kuzari da surutu tare da Rawan kai

"da fitina! Yarinyar da kowa na cikin JIBWIS ya santa saboda oarinta da kuma rawan kanta! Yarinyar da ta juyawa duniyarsa baya tare da cewa tana da wanda take so yau ita ce a gabanshi a matsayin sakatariyar kai da kai! He can believe ita ce, bai yarda ita din ce ba, sai dai sunanta da ya zame mishi daidai da ayar da ya haddace ya kuma bata matsuguni na musamman a cikin wawalwarshi. Me yake shirin faruwa? Me yake dawo da kome baya? Me ya kawo ta nan? A yau tana gabanshi ne sannan a gobe bai san wani matsayi zai ajiye ta ba, amma ya kasance yana jin motsinta ina Mijinta? Me yasa take tare da bro dinta! Shin ko Mijinta ne baya kasar? Me yasa yake jin wani babban al'amari a haduwarsu, shi dai yasan bai yi kome ba amma me yasa kowa yake jin ba dadi shi ba wani ririta yayi ba bare a ce ya ware ta!_ Saboda wani abu can ba, ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta a karo na biyu, kafin ya ce mata. ""Ki"

"duba na tura miki sako bana son kuskure "" ""Ok Sir!"""

"Haka na fita na bar shi ba shiga aiki ina printing, hayaniya da ake yi yana kusanto inda muke yasa ni"

"d'ago kai, wani farin bafulatani ni ne ya shigo da yayansa. Cikin girmamawa na gaishe shi tare da sauran Yaranshi, dakatar da sauran Yaranshi yayi ya ce min. ""Ina son ganinki."" Tashi nayi na bi bayanshi har stair su kuma suka shiga office Winsa. ""Lubabatu Usman Umar Jama'are ko?"" Da mamaki na kalle shi, murmushi yayi ya ce min. ""Kina da aure ne?"" Da sauri na d'ago kai na kalle shi kafin na ce mishi. ""A'a;"" murmushi yayi sannan ya ce min. ""Oganki ya sani ne?"" Girgiza mishi kai nayi. ""Ina son ki min alawarin Waya."" ""Tow ina jinka, Allah ya bani ikon Wauka."" Na fada muryana yana rawa. ""Don Allah kada ki tab'a"

"gaya masa, ki bari shi ya bincika haka da kanshi kin ji ko....."

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 54"

D'ago kai nayi zan tambaye shi me yasa zan yi shiru? Tow meye alakata da shi? Sai nayi shiru kafin na ce

"mishi ""tow!"" Murmushi yayi yana faWin. ""Na gode sai abu daya da nake son niman alfarmanki akai"" a raina na ce kuma dai, murmushi yayi ya ce min. ""Don Allah kiyi hakuri da shi."" Gyada kai nayi, bayan ya gama min magana ya wuce office din jikanshi, murmushi yayi ya zauna akan daya daya cikin kujerun office din, sauka nayi can kitchen na amso ruwa da drinks na fito zan wuce na ji wata tana faWin. ""Wasu ina ganin ba iya golden digger ba ne, har da can Winsu na zinari ne."" Ban kula ba sai nayi kamar ban ji ba,"

haka na wuce na haura abina ban kula tasu ba.

"Ina shiga office din na ga ya daura kafa akan center table din da zan daura ruwan, kallonshi nayi na ga"

"ya dauke kai, kuma bai dauke kafar ba, a raina nace. *Jarababbe haka dai zaka kare* a fuskata sai na saka a dan gabansu. ""Kece Lubnah kawar Tarik?"" Murmushi nayi na kalli mutumin da yayi magana, duk da baki ne amma na hango yadda suke kama da Tarik. ""Gashi ya ce na baki!"" Ya mika min wata paper Bag, sai da na kalli CEO da yake tari, kamar ya kware dole na dauki goran ruwa na bude mishi, yana sha ya ce min. "" Ki dauki key mota ki ce Ade ya kai ki Chinese dish ku amso musu abinci. "" Nufar wurin nayi na dauka, sakon da ban amsa ba kenan, na bar office din kamar yadda ya ce haka muka amso abincin sai dai abin haushi muna zuwa suna fita, koda muka iso da abinci, wani kallon banza yayi min ya fara faWa a gaban jama'a. "" Wannan rashin kuzarin da kike yi a aiki ta fara isata, akan me baki zasu tafi basu ci abinci"

"ba, wannan ai wulakanci ne. Sai ki je ku raba da mutane."""

"""Haba Turaki kayi hakuri mana, ai nan da inda ka aiketa tafiyar minti ashirin ne, sannan sai da suka tafi"

"ka kira, Yarinyata na var miki sakon abokinki! "" Gyada kai nayi ina godiya, a wani gaggauce suna barin harabar zuwa cikin main building na kamfanin, ina cikin kokarin zama sai gashi. Kallona yayi nima na kalle shi a sace sai na ga ya wuce office dinsa, kiri-kiri ya hana ni sakon, har muka tashi ban san me ya kai ni ga magana ba, ina riga shi fita amma yau na tsaya, yana fitowa na ce mishi. ""Nace ba, sakon nan ya ce ya bari a office dinka?"" Wani irin shiru yayi kafin ya ce min. "" Na zubar a dustbin."" Daga haka yayi tafiyarshi, haushi ya kama ni kamar na koma office dinsa na dauki kayana, ai zai ga rashin mutunci. Haka"

na fito na bar office din nima.

"A gida sai masifa nake ina faWin, ""Fisabiilillahi an bada sako bawan Allah nan ya kama ya zubar sai"

"kace a kanshi aka saka ni dai wallahi ba zan iya yafewa ba."" "" Tow me yasa ba zaki iya gaya mishi a can ba sai a nan!"" "" Ni wallahi kamar dodo yake min ina son na samu dare daya na gurza mishi rashin mutunci."" Dariya Aunty Zakiyah tayi tana faWin. "" Allah yasa ki iya!"" Abin ba dad'i fa, haka suka yi ta manna min"

hauka nayi shiru na kyale su.

Washi gari

"Ina isa na ga Paper Bag a kan table dina, asalima ya riga ni zuwa, dauka nayi na ga flora gown ce mai"

"mayafi, sai turare masu kyau da tsada da kuma chocolate kwali biyu mara sugar da fat, abaya guda biyu. Bayan flora gown din, ban tab'a ba har zuwa lokacin break na mike zan sauka kasa naci abinci sai ga Mrs stalle ta kawo min jakan abinci, ta min tana min wani irin kallon kurulla, ban kula ta ba na amsa ina zauna a kasa naci. Jakar nan dai anan, ina gama cin abincin na tafi nayi alola na zo na gabatar da sallah, ina idar na ji motsinsa, mikewa nayi naga yana kallon jakar yadda ya kalla nima haka na kalla na cigaba da abinda nake, wucewa yayi abinsa, bayan tafiyarshi sai ga Yan matan family dinsu sun zo tare da Mrs stalle da wasu matan office din, suka zo. Daukar jakar daya da na ji ance mata Batul tayi tare da juye shi a kasa, ashe har da wani box na sakar karamin box kamar Pandora, suka yi ta d'aga kayan ita ogarsu ta"

"ce musu. ""Ku fito min da shegiya na gaji da ganinta tare da shi."" Suna dayawa amma kuma dole na koyo"

"tsayawa kaina, finciko ware din laptop dina nayi dama da kauri. Suna zagayowa na rufe su da bulala"

"karfin hali nake, ganin ina shud'a musu yasa suka fara baya har nayi nasarar kure sannan na juya da gudu na nufi elevator, na danna jin muryansu yasa ni juyawa da baya, daidai kofar ta buWe. Muka yi wani irin karo da shi, na fada mishi bakiWaya. Yadda na rikice ban san tare yake da wasu ba, ni dai burina na ceci kaina. Hannunsa nayi a bayana, daidai gadon bayana, dukkan hannu bibbiyu ya rufe ni da shi, kaina a kife a kirjinsa, da xan kwace amma jin kamshin turarensa yasa na nutsu, na kifa kaina a kirjinsa."" Ya isa haka!"" Ya fada tare da janye ni a jikinsa, ya zuba musu idanu, yana kallon abinda suka yi da kayan da ya kashe kudi akansu. Murmushi yayi ya kalli Ubaid ya ce mishi. ""Ban san sunansu dukkan ba, zaka iya koransu a aiki su kuma waWannan jin da su daya bayan Waya."" Sannan ya rako ni har wurin aikina, sai da ya ga na zauna ya tsuguna da kanshi ya kwashe kayan da aka zubar ya zuba a jakan, ya dauki sakar ya zuba mishi idanun. Kafin ya mai da cikin boxs din. ""Turaki!"" Kallon wnada ya kira shi yayi. ""Ka yi hakuri!"" ""Wallahi sai sun bar kamfanin nan ka ji na rantse!"" Kasa magana nayi na kalle shi, ""sir su bar aikin saboda ni?"" Na fada bakina yana rawa, a fusace ya juya tare da cewa. ""Kema na dakatar da ke. Tunda dambe kika zo yi a kamfanin."" Kafin ya rufe baki na hada kayana, na bar office. A ranshi kuwa haka yake son ganin mace, ba kamar sauran kamar mayyu sai hakuri suke bashi ba. Ina barin wurin shima ya wuce office Winsa, Ni kan ba zan iya wannan halinsa ba, misalin uku da rabi na isa gida na huta ban gaya musu"

me ya faru ba.

Ina samun kaina na kashe wayata su je can da kamfaninsu me shegen matsalar tsiya. Daga nan na

rufe babinsa in sha Allah ranar Monday zan rubuta takardan barin aiki.

**

"Yana tashi don masifa bai wuce gida ba, ya nufi gidan Hajiya Samirah kumo yayiwa yarta duka, sannan ya"

"dawo ya samu Badr itama yayi mata dukar har da ji mata ciwo a hannu, Mimi ma bai kyaleta ba, domin kamar wanda ya sha kwaya haka yake jinsa. Duk yadda Alhaji ELYakub ya so boye b'acin ransa sai da ya yi magana tare da nuna mishi kuskuren da yake aikatawa ai ba a haka, dama already Ubaid ya jima da nuna adawarshi a fili, Uncle Auta ne ya goyi bayansa har ya ce bai ga laifin abinda yayi ba ai ya musu warning me ya kai su wutinsa? Jin haka yasa shi shima yayi zuciya ya bar gidan, kai hatta kamfanin fushi"

yayi ya daina zuwa aikin.

---

"Yau kwana uku kenan da aka dakatar da ni, na rasa yadda zan gayawa Ya Ado, ina Gym na zurfaffa"

"tunanina sai jin wayata tayi ara, dauka nayi na ga alart har na dubu dari uku da hamsin an saka salary,"

"daga KPAN, mamaki nayi albashina na farko kiran Mama nayi na gaya mata ta ce na kira Ya ado na gaya mishi, nace idan na koma gida zan gaya mishi, haka kuwa aka yi ina komawa gida na nunawa Ya Ado shi"

"kuma ya karbi kudin ya turawa Mama dukka, ya tura min dubu hamsin ya ce min. ""Wannan ni na baki,"

"wancan kuma a bar mata tayi yadda take so da shi."" Murmushi nayi ina faWin. ""Allah ya kara budi."""

"Ranar wuni nayi cikin farin ciki, washi gari da safe ina motsa jiki a parlourn aka buga gidan da kaina na"

"fita na duba, Jasminah ce. ""Laa aunty kece!"" ""Eh gani nan sauri nake, don Allah ki taimaka mana Oganki yau kwanansa kusan hudu baya nan baya zuwa office ko zaki tab'a mana shi a waya!"" Sosa kai nayi ina yake nace mata. ""Aunty bani da number shi?"" Zare idanu tayi nima abin sai nayi ya min wani iri, shiga motarta tayi ta rubuta min number ta bani tana faWin. ""Don Allah ki taimaka mana!"" ""In sha Allah!"" Sannan ta juya abinta, ni kuma na shiga cikin gidan ina tunanin yadda xan kira shi. Tow me ya faru da ya bar gida? Mutum sai kace mai aljanu. Parlourn na shiga na zauna ina tunanin, kafin na haura sama."

"Wayata na dauka nayi shiru ina ta tunanin yadda xan kira shi, a hankali na saka number nayi shahadar kuda na kira Number, har ya gama ya tsinke bai dauka ba, haka na kira bai dauka ba, sai da nayi kira na uku sai gashi ya Wauka. Muryanshi very calm kamar bai san me yake faruwa ba. Na ce mishi. ""Dama na ga sakon kudi ne jiya!"" Sai nayi shiru can na cigaba da cewa. ""Dama ina son nayi submit takardan barin aikina ne."" Na kashe wayar, ina kashewa kuwa ya biyo kiran. ""Me aka miki zaki bar aikin?"" Kashe wayar nayi bakiWaya, na sauke ajiyar zuciya ina kallon wayar da nayi switch up dinsa, ina zaune a wurin Adil ya shigo da gudu yana haki. ""Aunty Lulu ki zo kin yi bako!""zare idanun nayi na ce mishi. ""Baba gaya min waye?"" ""Wannan wanda Abba ya ce oganki ne!"" ""Shi kenan!"" Na fada a raina, kafin na saka jalbab na sauko kasa, ina jin wani abu yana yawo a kaina. Wucewa kitchen nayi na dauko kunun aya da sauran breakfast din da aka yi na dumama masa ce fa sauce din kodar saniya, na kawo mishi a hankali na jera mishi. Sannan na ce mishi ""ka kaci!"" Ba musu ya saka sannu ya fara cin masar da yake miyar da dan yaji tari ya fara na bude mishi kunun aya na zuba mishi ya sha, sannan ya kalle ni, kafin ya ajiye ya cigaba da cin masar, har zuwa lokacin bai ce min uffan ba, nima kuma ban ce mishi ba kaina a sunkuye, nayi mamakin da yaci abincin sosai, ya ce min ya koshi, na tattara kayan na kai kitchen, na dawo na zauna a can gefe. Shiru muka yi kafin ya ce min. ""Gobe ki dawo aiki!"" ""Tow Allah ya kai mu!"" ""Amin Ya Allah!"" Daga haka ya mike zai fita ya ce min. ""Yaranki nawa? Mijinki yana ina?"" Bai tsaya jiran amsata ba yayi"

"gaba abinsa, wannan dan renin hankalin, shi kuma haka yake rayuwa kamar me aljanu."

"Bayan tafiyarshi Ya Ado ya fara zolayata, ""wato Lubna baki da mutunci, don kina son ganinsa shine"

"kika kira shi."" ""Ni wallahi ba kiran shi nayi ba!"" Na fada ina tura baki, dariya yayi suka yi ta tsokanata."

Washi gari.

"Na same shi a office din ne. Ga sabbin ma'aikata, da gaske koran wadancan yayi. Gaisawa muka yi da"

"wata ina ga irin kabilun arewan ko yar Kaduna ko yar Jos, sai dai ban gama tantance ta ba ta ce min. ""Sunana Sarah daga Gombe aramar hukumar kaltungo."" Murmushi nayi nace mata. ""Lubabatu daga Bauchi, karamar hukumar Jama'are."" ""Allah sarki akwai yar uwata Ayrah tana sama wurin CEO!"" Gyada kai nayi nace mata. ""Da kyau bari na isa office din!"" Na wuce sama, kofar dama a rufe take, sai da na"

"ajiye kaina na kunna table tap, na shiga office. Matar da na hango tafi Sarah a shekaru, cikin girmamawa"

na gaishe ta sama sama ta amsa sannan na gaishe ya amsa yana aiki na fara zayyano mishi abinda yake

"da su a a yau, ban gama ba sai ga Tajudeen........"

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 55"

"Murmushi nayi na juya ina kallonshi, a hankali na ce mishi. ""Nayi kewarka!"" Murmushi ya sakar min ya"

"wuce gaban Masifatu ya ajiye document Win da ya kawo, sai lokacin na mai da hankali kanshi ashe ya shaka, wani irin kallon rashin mutunci yake min, yayi shiru rubutu yake a laptop ya rufe ta da karfi tare da mikewa ya fita ya bar ni nan tsaye, anya mutumin nan bai da aljanu? Fitowa nayi na same shi yana magana da Taj, wucewa nayi dan zauna ya ce min. ""Kin gama report din ne?"" Kallonshi nayi cikin mamaki yanzu fa ya fito a office din, ban gama ba sannan ya zo yana tambayar na gama nima share shi nayi kamar ban ji ba, mamaki ya kama shi. Na kuwa hade rai domin ga irin kallon da matar take min na kusa da shi. ""Ina jiranki a mota!"" Ya saka kai ya fita sai da na gama abinda zan na taso na nufi kasa, don ma na bashi haushi stair zan bi ba zan bi elevator ba, kuma a hankali nake sauka ya jima bai kore ni ba. Sai da na shafe minti goma kafin na iso, na hango Taj yana ta leke ta ina xan fito. ""Gani ta nan!"" Na fada ina nufar hanyar waje, ina zuwa na same shi ya cika kamar balloon, sai kallon agogon hannunsa yake, hango matar nan da nayi sai na koma gaba na zauna kuma ai dama gaba nake zama, muka dauki hanyar inda zamu. ""Sir maganar zuwa Japan din yana nan ne?"" Shiru yayi yana kallon table tap din da Taj ya mika mishi. ""Kamfanin Rivers sun tara kayan sosai, dole sai an je da su Japan."" Shiru yayi sannan ya ce mishi. ""Na Kano ma haka, Abuja babu kayan gaskiya."" ""Ka shirya tafiyar har da sakatariya."" Jin an ambace ni yasa na juya na kalli Taj,"" tafiya ina? Har da ni kuma?"" "" Eh ai aikinki har da tafiye-tafiye!"" Yana sane ya fadi haka ya ji ko ya zata fuskanci Mijinta. Hadiye yawu yayi yana kin zuciyarshi kamar aka lugude a kai, wani irin yanayi yake ji a kanshi, yana tsoron kada ta ce tana da miji. ""Amma gaskiya ba zai yiwu ba, domin ko ka tambayi iznin zuwa ba zaa a bar ni ba, ka duba ni mace ce kuma Bahaushiya idan nace zan yi tafiya wata asa da wani namijin ai abin ba zai making sense ba, ina ga a cire sunana a bar ni"

"anan, abinda ya shafi gida Nigeria. """

"""Idan don Mijinki ne, ki bada passport Winsa sai a tafi da shi, but i need you! "" Daga haka ya fita a motar"

"domin har mun iso bankin UBA, gaba yayi na fito airah ta ja min tsaki, kallona Taj yayi yana faWin. ""Kina sa'ar Oga, tunda har da mijinki zaku tafi."" ""Ni fa ba zan bishi ba."" Haka na cigaba da tafiya, ya juya yana kallon yadda nake bawa Taj amsa, tsaki yayi yarinya karamar da ya sani a wancan shekarun bata da wannan kula kowa, amma wannan da aurenta ma, sakewa take da

Please Login or Register in order to submit comment