ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bin maza da take yi da aurenshi. Malama Sabuwa har a hotel take kwana da maza da aure a kanta.

Akwai sanda Babangida ya kamata ita da Khalid wanda ya kasance tsohon saurayin ita Sabuwa ne tun tana budurwa.

Sabuwa a titi tayi dambe da mijinta Babangida sabida kawai ya kama Khalid da dambe.

Wanta kuma ya sari Babangida a kafaWa shi da sabuwa suka haWu sukaita dukanshi.

"A ta dalilin wannan saida Babangida yayi fin sati uku a asibiti, ga rauni a kafaWarshi ga karaya duk a hannu Waya. Ya mai girma mai Shari'a Babangida yana neman a fitar mishi da hakkinshi."""

Zama tayi.

Ni kuwa sai haWiyar zuchiya nake yi zufa na keto mun. Barister Ahmad Ahmad ne yace.

"""My lord ina da ja. Lauyan wanda ake ™ara kwatakwata ya sauka akan layin shari'ar da muke yi . In tuhumarta Babangida yake son yi ™ara zai shigar shima domin a kwato mishi hakkinshi."

"Yanzu muna magana ne akan Sabuwa da ta kawo karan Babangida da tana son ya saketa"" ""Ina da ja ya mai Shari'a """

Cewar baristar Abubakar Ibrahim daya mi™e.

Al™ali ya bashi damar yin Magana

"""My lord Batister Asabe madaki tana kan layin shati'a ta yiwu sabida halin rashin kamun kai da bin mazan banza ne yasa Babangida ya watsar da lamarin Sabuwa. Tunda yasan tana bin maza taya zaici gaba da Waukar Wawainiyarsu. Ya mai girma mai Shari'a wannan shari'ar tana da girma muna bu™atar a bamu lokaci domin gudanar da binciken daya kamata a tsanake. Sannan a duba wanda ake tuhuma bashi da cikakkiyar lafiya kullum yana zuruftun zuwa asibiti wankin ciwone, asalima kwananshi uku da aka sallamoshi daga asibiti. Muna bu™atar lokaci mai tsawo. Nagode my lord """

"Bayan al™ali yayi rubutu, yayi rubutu saiya Wago yace. ""Ko lauyan wacce take ™ara yana da ™orafi?"""

Mi™ewa yayi yace.

"""E akwai ya mai girma mai Shari'a. Muna ro™on wannan kotu mai alfarma da kada taja wannan shari'ar domin Sabuwa tana cikin damuwa sosai. Sannan mara lafiya tunda yana iya zuwa asibiti zai iya halartar zaman kotu. ˜orafina kenan nagode my lord"""

Tunda lauyoyin Babangida suka soma magana nake tsiyayar hawaye babu ™a™™autawa. Zuchiyata har tsalle take yi mun tsabar bugawa. Dana waiga na kalli ´an uwan Babangida matan da Malama Babba saina ga suna cike da farin ciki. ³an uwanshi maza kuma girgiza kai kawai mafi akasarinsu suke yi.

Dubana na mayar kan Baba Malam wanda na kasa fuskantar a cikin irin yanayin da yake.

Ta Sangarensu Maigogul sai naga tamkar sunfi su Malama Babba ma farin ciki. Su Adama kuwa ko wacce ranta a

Sace yake da dukkan halama suna tayani jin zafin abinda ke faruwane.

"""Bayan sauraren ™ara da wannan kotu mai alfarma tayi wannan kotu ta Wage wannan ™ara izuwa Waya ga watan Mayu. La'akari da shi Babangida da ake tuhuma bashi da ishasshiyar lafiya. Kotu ta bashi dama yaje yayi jinya kafin ya dawo aci gaba da sauraren wannan shari'ar. Sannan tuhumar da Babangida yake ma Sabuwa bai shafi shari'ar da muke yi ba. In hakan suke so sai ya shigar da sabon ™orafi. A zama nabiyi lauyoyin Sangare biyun zamu basu damar soma gabatar da hujjojinsu."""

Ya kwaWa gudumar kotu duk aka mi™e.

Ni kam saida Adama ta tallafamun kafin na iya tashi. Bana ko ganin gabana Adamace ta zame mun garkuwa. Da muka fito harabar kotun lauyana da Baba Malam ne suka tareni.

"""Sabuwa ki kwantar da hankalinki ki dena Waga ma kanki hankali. Ko wata nawa aka saka na sake zaman kotu zaizo ne. Kuma duk yadda azzaluman lauyoyi suka kai da iya sharri dole za'a kai ™arshen wannan shari'ar dole. Barister Ahmad zai nemo wani lauyan suma su zama su biyu. Shari'a yanzune za'a soma."

"Adama ki daure tunda naji labarin mutuwar aurenki kije ki zauna da Sabuwa ko dan Webe mata kewa. Ramadan anjima zan aikoshi da kuWin cefane da kayan abinci ya kawo muku."""

"Godiya nayi mishi kawai Sama da Uzairu zuchiyata ne suka ™araso inda muke tsaye, su Maigogul kuwa suna keSe da Babangida."

"""Lolo wannan tonon sililin har ina, kinji fa abinda lauyan mijinki yake cewa a kotu. Wai hotel_hotel kike zuwa mu'amala da mazan banza. Wai shine nace wai dama baku watsar da rayuwar da kuka gudanar a baya ba. In da anji talaucine ya sakaku kaucewa yanzu da kike gidan aure kuma me yasa kika kauce?"

Adama kinsan Allah nakai zuchiyata nesa ne da muna fitowa zan cukume Babangida ayi wacce za'ayi. Allah yasa Gaza bayanan yana canma a kulle me yau da anyi batacciya.'

Adama tace.

"""Sama duk fa abinda yake faruwa Sabuwa fa akan daidai take. Abinda kaji lauya ya faWa sharrine. Ina Khalid tsohon saurayin Lolo?"""

Ta tambayeshi Uzairu zuchiyata yace.

"""Wannan baban nacin zaki ce mun"" Adama tayi dariya tace."

"""Shifa. To a asibitin da ita Lolo take kai yaranta yake ranar taje asibiti saiya ganta ya rago mata hanya ya kawota gida. A bakin titi a cikin mota fa ya gansu shine yayi mata wannan sharrin. Dake shima Wan iskane shi yasa tunaninshi ya tafi can."

"Mu faWama kanmu gaskiya Babangida fa taceccen Wan duniya ne fa. Maigogul da Rakiya suma kuWi suke yima. Mu bi bayan ´ar uwarmu kawai Sama"""

Kai Sama ya girgiza yace.

"""Wallahi hakane wai duk basu suka SalSanta rayuwarmu ba, sun haifemu sun watsar damu muna gantali a titi ba. Ai shi yasa ni aure ma zanyi ciniki harya faWa Lolo muje gidan naki sai mu tattauna acan ance kun sake gida ana muku gyara a wancan gidan naku."" Duk wannan bayanin da yake yi zaku ce faWa akeyi yanayi yana ihu da wauware hannaye."

Šunguma muka yi dukkanmu muka nufi gidana.

"A bakin titi wajen samun abun hawa muka tarar da su Sa'a suna tsaye kome suke jira ohon musu, sai wani kallon ™yama suke yi mana sabida dattin da Sama yayi. Niko a raina ina faWin ai kallon ™yamar auroni ya kusan zuwa ™arshe tare da Malama zamu zama zaurawa."

"Muna tsaye motar da zata Webesu ta fito suka shige,motarsu Baba Malam na binsu, sai ta su Malama Babba, sai ta samarin gidan."

Mu kuma muna dai tsaye duk abin hawan da muka tare sai suce banan zasu yi ba. Daga ™arshe sai hawa muka yi muka rage tafiyar muka sake shiga wani abun hawan.

Su Rakiya tun muna neman abun hawa suka zo suka wuce mu a mota Maigogul ke tu™in motar wata haWaWWiyar mota ko kallonmu shi kan baiyi ba ga kiWa ya sakar musu Rakiya mandiya tana gaban mota.

Da sallama muka shiga gida. MRS BUKHARI

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA TARA

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

Assalamualaikum brkanku d warhaka hmmmm Wani kaya sai amale tohhh mata masu capacity matan kwarai

ga ramlex Mai kayan daa kayan buje akwae Package na uwargida

Package na amarya Package na mejego Tsimi baure

Tsimi magarya Hadin tattabara Hadin kaxa Hadin ciccibi Gumban Madara Gumban ridi

Gumban waken soya Karin dandano Xuman matsi

Manta uwa Hadin mallaka Hadin bita xaixai

Hadin tsuguno hmmmmm gareku mata akwae adashen gata duk sati 2k hadi Mai kyau xaayi muku duk Mai bukata ga no 07069722234 ko 07044503983 snnn dn Neman Karin bayani ku tuntubi wnnn layukan

BABANGIDA:.

Yana bayan motar Mustapha a zaune idanunshi a rufe tun daga cikin kotun har suka fito motarsu ta nausa titi bai

buWe idanunshi ba.

Yana jin su Bashiru suna jinjina rashin mutuncin Sabuwa.

"""Ai ni wallahi Mustapha mamaki Sabuwa ta bani ban taSa tunanin da gaske take yi za'ayi zaman kotunnan ba. Bura uba ni matata ta kaini kotu akan saki wallahi ko da bakin iyaye a kaina saina saketa. Babangida matsala Waya ce tasa bazai taSa iya sakin Sabuwa ba matsalar Malama Babba. Amman da dan bakin Baba Malam ne kaWai wallahi da tuni an saki mitsiyaciya ta kama gabanta muga wanne kamilinne zai fito ya aureta. Yarinyar da aka taimakama ji iyayenta fa da ´an uwanta, ni naga uban harda mota yazo arowa yayi amman dai ko? Kai amman Baban Sabuwa ya mugun iya wanka. """

Gabaki Waya suka fashe da dariya Mustapha yace.

"""Bashiru wallahi kai Wan iska ne. In ba arowa ba a ina zai samu Jeep ce fa ina yaga kuWin mallakar wannan motar.? Ko da yake kawalai wallahi ™asar a hannunsu take"""

Wayar Babangida sai kuka take yi ya™i buWe idanunshi ji yake tamkar inya buWe idanunshi kanshi zai faWo. Bashiru dake kusa dashi ne ya Wauki wayar ya kara a kunnenshi ganin wacce take kiran wayar.

"""Wallahi da baka Wauki wayarnan ba da kaji mummunan labari. Ina son ganinka da gaggawa wallahi awa Waya na baka in ba haka ba narantse da Allah ubanka zai kiraka ya sanar maka Wanka ya koma gidan kakanninshi. Lallai Babangida kaci abinci ka kuma yi wasa da tunanina. Allah Waya kenan sai ka yi dana sanin sanin Sumy a rayuwarka."" Wayar a hands free take duk abokan Babangida suna ji. Babu shiri Babangida ya buWe idanunshi tare da warce wayar."

"""Sumy ganinan zuwa yanzu kiyi ha™uri """

˜it ta kashe waya

"""Hmm bariki kenan. Ku da ba dan bariki ba Sumy ta isa ta faWa mun magana haka? Mustapha dan Allah juya akalar motarnan zuwa gidan Sumy kasanta muguwar mahaukaciyace saita aikata abinda ta ambata."""

Mustapha yace.

"""Amman ya zaka yi da zaman meeting da za'ayi a gidanku kuma a kanka?"""

"Yama mance shaf amman ya zaiyi dole yaje ya soma kashe wutar da Sumy take son sake kunno mishi."" ""Kai dai muje kawai ai ba zama zamu yi ba"""

Bashiru ya harareshi yace.

"""Kai da wa? Wallah ba zamu shiga ba sai dai kai kaWai ka shiga. Kaima da munji shiru sai mun kawo maka Wauki mun kira motar ´an kwana_kwana (fire service) """

"Dariya suka fashe dashi, shi kuma ya koma ya jingina bayanshi a kujerar motar. Har suka isa ™ofar gidan suna surutu."

Wani yaron gidanne yace.

"""Laa ga baban Amiru ya dawo daga tafiya"""

Yana faWin haka ya ruga a guje. Babangida a karon farko daya soma nadamar ajjiye farka daya soma kenan a rayuwarshi.

"Mazan dake ™ofar gidan ya gaisar sunata kiranshi Baban Amiru. ""HaWari kayi ashe Baban Amiru?"""

"Wani ya tambayeshi, kafin ya bashi amsa Amiru fito da tafiyarshi irin ta yara ya rugungune ™afafun ubanshi. ""Wallahi kuwa Malam Hamza haWarin mota nayi"""

Nan suka shiga jajanta mishi dai. Hannun Amiru yaja suka shiga da sallama cikin gidan. Matan gidan duk suna tsakar gida suna aikace_aikace.

Sannu kawai yayi musu ya shige ciki.

Sumy tana tsaye tana jijjiga dan bala'i da masifa hancinta har hunhuna yake yi.

"""Kai ka Wauka wasa nake yi Babangida, tsawon shekaru nawa ka ajjiyeni ka hana kowa ya raSeni, ka hanani kula kowa sai yanzu inji labarin ka cikace mata huWu?"

"Wallahi Allah saika saki mace Waya dan samamun gurbi a gidanka, wallahi Allah saina rayu dakai rayuwa irinta sunnah ko kuma inje har gidanku in fallasa asirin ka in zaiyanama mahaifinka irin tsawon zamanin da muke tare da"

Irin duk abinda muka aikata kuma in bashi Amiru ya kiraka ya baka Wanka tunda tonon asirin kafi so. ³ar balaja'uce

"ni cikakka. Har bidiyonka saina fitar wallahi"""

Zama yayi babu shiri a kujera yana ta aikin kallonta tace wannan tace wancan.

"""Wata Waya tak na baka muyi aure a gama komai shine magana. Ko ayi haka ko kuma duniya ta sanka"""

"""Amman kinsan ko zan aureki sai kin koma gaban iyayenki kinyi istibiraWi na wata uku kafin muyi aure ko? Kuma ki sani duk matar da zan saka itama dole sai tayi wata uku na idda kafin ta fita a sahun jerin matana, ko nayi saki in dai na mutu kafin ta gama idda dole za'ace matana huWu kuma zataci gado. To kinga batun muyi aure a wata Waya bai taso ba."

"Sannan ke me yasa bakya bin komai a hankali ne kinata ihu so kike matan gidannan su gane irin zaman da muke yi ne?"""

"Murmusawa tayi ta Waura ™afarta Waya a kan kujerar da yake zaune Wayar ™afar tana ™asa ta matso da fuskarta ta yadda suke jin Wumin numfashin juna"""

"""Wallahi baka isa kaimun wayo ba. Naji zanje gida in yi istibiraWi, sai dai ka sani a matar auren da mijinta ya saketa zanje. Iyayena bazan taSa bari su san Amiru shege bane. Ina gama wata ukuna sai kazo a Waura mana aure. Amman wallahi a ranar da zan soma ™irgen istibiraWi a ranar Waya daga cikin matanka zata soma ™irgen idda. In kuwa baka yadda ba in tona asirinka in saki videos Winka da su suka cika wayata in sakarma duniya a dauwama ana tsine maka"" Mi™ewa yayi ya Waga mata hannu."

"""Ya'isheki Sumayya nace miki naji zan aureki. A cikin matana kafin wayewar gari zan sallami Waya. Gobe ki shirya ki tafi garinku, ki bani adireshinki"""

"Dariya Sumy ta saka. Kafin ma tayi magana wayar Babangida ta soma ruri Kawu Manga ke kiranshi anacan an taru za'ayi meeting uban gayyar baya nan."""

"""Assalamu alaikum Kawu ina hanya in sha Allah bada jimawa ba zanzo"". Amsa sallamar tashi yayi tare da cewa."

"""To Babangida ka same ni a gidana acan zamu gudanar da meeting Win Malam fur ya™i mu shiga gidanshi. Kai atakaice dai ya aikata abinda baima kowa daWi ba. Kaga su Wawo suna ciki sai koke_koke suke yi"""

Rararasas gaban Babangida ya tattake yayi mummunar faWuwa. Yana son tambayar abinda ya faru yana tsoron bugun zuchiya.

"""Shikenan gani nan zuwa"""

Da mugun sanyi yayi maganar tare da sauke wayar.

"""Ni zan tafi gobe ki tattara ki koma garin iyayenki. Duk halin da ake ciki zamu yi waya."" Har yasa kai zai fita tace."

"""Babangida!"""

Cak ya tsaya ba tare daya ™ara ko ta™i Waya ba.

"""'wallahi Allah bazan yaudaru ba. Kafin in tafi goben sai ka kirani ka tabbatar mun da sakin Waya daga cikin matanka, sannan ka turo mini da copy na sakin ta wayata. In kayi haka ni kuma sai in tafi"""

Baice mata komai ba ya fita. Da sauri ya faWa mota ba tare daya ce uffan ba. Idanunshi ya rufe kai da zuchiyarshi suna harbawa da ™arfi.

"Basu daWe ba suka iso ™ofar gidan Kawu Manga kamar yadda yace nan zasu kawo shi. ""Shikenan ni anan zan wuni da yamma zan le™o majalisa"""

"Mustapha yace"""

"""Amman yaya kuka yi da Sumy Babangida. Karfa ta tona maka asirinka?"" ""Mustapha in nazo majalisa da yamma zaku ji yadda akayi"""

Shiga cikin gidan Kawu Manga yayi da sallama. Babu kowa a tsakar gidan duk suna ciki kenan. Ga takalma birjik a

™ofar falon Kawu Manga harda tashin muryoyin ´an uwa.

"Da sallama Ya shiga tare da neman waje ya zauna kusa da Wawo. Jikin kowa a mugun mace. Kawu Manga yace. ""To kai Wawo buWe mana taron namu da adda'a"""

Da adda'a ya buWe taron kafin Kawu Manga ya soma magana.

"""Abun dai babu daWi Malam ya yanke hukunci yayi tsauri gaskiya. Yanzu idan Sabuwa tayi nasara a wannan shari'ar shikenan Malam ya rabu da Babba kenan? In kuwa da gaske yake yi ha™i™a bai yima Babba halacci ba, Malam bai kuma duba shekaru da ³a´a ba. Ya kori Babangida daga gidanshi a baya, tsakanin Babangida da gidan mahaifinshi sai dai ya shiga ya gaishe da iyayenshi mata. To yanzu yayi mai Wungurungum yace ko mutuwa yayi bai yafe ba muddin ™afarka ta taka zuwa cikin gidannan. Itama Babba yace kada ta koma mishi gida ta zauna a hannun yaranta har zuwa lokacin da sharia zata zo ™arshe. Ga takaddar sallamarka da Malam yayi a makaranya yana hannun Wawo. Babangida duk da dai duk abinda Yaya yake kai gaskiya ce kuma soyayyace yake gwada maka. Kayi abubbuwa a"

"rayuwa masu tarin yawa, har ila yau baka dena ba tunda har ka iya auren mace har kuka haihu babu wanda ya sani a"

"cikinmu. Wa yasan inka warke irin rigimar da zaka sake jajiSowa"" Shiru yayi yayi ™asa da kanshi yana girgizawa."

"""Bazaima jajiSo komai ba tunda yanzu bashi da ko sisin kwabo, babu sana'a koyarwan ma Baba malam ya koreshi. Ai sai yaci sa'a ne in aka gama shari'arshi shi da Alhaji Abubakar Baban Bola zai iya samun ladan juya dukiya in aka cire ma mai hakki hakkinshi. Wallahi Kawu Baba Malam ya fa fimu gaskiya a cikin wannan lamarin."

"Laifin Malama da yake gani shine yana ganin kamar ita kullum a bayan Babangida take. Kuma fa hakanne. Kai ko dan Malama Babba ai ya kamata ka nutsu. Gashi ta dalilinka aurenta yana girgiWi."""

Sa'a tace.

"""Gaskiya laifin Babangida ne duk komai ma. Laifin Baba Malam ri™o shi baya mantuwa, kuma in mutuncinka ya zube a idanunshi babu mai kwaso maka wannan mutuncin. Kai Babangida kana ganin za'ayi nasara akan wannan shari'ar har al™ali yasa Sabuwa tilas ta zauna dakai? Dan naga tana da hujjoji manya wanda zata iya hamSarar damu?"""

Kudidi tace.

"""Ni bama wannan ba Baba Malam ashe shi ya Waukarma Sabuwa lauya ma. Ni anya Sabuwa ba lashe zuchiyarshi tayi ba? Ina tuno bayane a lokacin da ko muryar Sabuwa da ubanta baya son ji. Amman yanzu yafi son su sama damu. Mu dai mu tsaya tsaiwar daka dan mu tseratar da auren mahaifiyarmu."

"Malama Babba dai ruwa yana neman ™arema Wan kada. Ita abinda yake damunta a ranta maganar kishi ne, ko a yanzu ˜arama taga wallenta kuma ta cire tuta ita da ´a´anta a idanun Malam. A gabanta Malam ya hanata shiga cikin gidanshi."

Kawu Manga yace.

"""To Babangida gobe shine zaman kotunku kai da Alhaji Abubakar Baban Bola. Duk da ita wannan shari'ace da za'a gudanar da'ita a camba, kuma lissafin dukiya kaWai za'ayi. Shawarar da zan baka kai namiji ne kayi bakin ™o™arinka dan ganin ka shawo kan matarka kasata da kanta ta janye wannan ™arar salin alin duk yadda zaka yi aikin naka nd. In kuma hakan bai samu ba hujjojinta suna da ™arfin da al™ali zai iya umartarka da ka saketa. Ka nutsa sosai ko dan mahaifiyarka, wannan yarinya dai ta zame mana ™arfen ™afa, ko ™adangaruwar bakin tulu."""

"An daWe sosai anata tattaunawa tare da tsayawa akan matsaya guda Waya. Wawo yace zai tafi da Malama Babba zuwa gidanshi akwai Sangare guda da zata iya zama, zai Waukar mata ´ar aiki da zata dinga mata aikace_aikace dan ya riga da yasan matanshi ba lallai suyi abinda ya dace ba."

"Basu tsaya wata wata ba, anayin sallar azahar Wawo ya Wauki Malama Babba da su Sa'a suka wuce gidanshi, Baba malam yana kallonsu yana zaune yana karatu abinshi. Sai wajajen bayan magriba Babangida ya isa majalisarsu nanma akaita tattaunawa akan dai abu Waya. ³ar Shuwa da Hamida sai rangaWa mishi kira suke yi a waya dama ya gaji sai kashe wayarshi yayi dukka."

"""Yanzu wa zaka saka a cikinsu? Ni ina ganin ka saki Hamida tunda kaga itakam ai tama jima kai da baka saba ajjiye mace ta daWe ba"""

Cewar Mustapha kenan.

"""Kaga tashi ka rage mun hanya ka kai ni gida. Wannan sakin wacce tsautsayi ya afkama ce zata sameshi ku dai ku zuba idanu. Ita kuma Sumy da ace tasan bani da komai a yanzu ba Lallai ta yadda zata aureni ba. A tunaninta zata zone ta mi™e ™afarta taci arziki"""

Bashiru yace.

"""Wacce dai Allah ya taimaka ita zaka saka. Kai da baka da ko sisi ka koma gidan haya shine zaka ce wani menene. Itama Sumy ai gara ta shigo ta zauna taci uwar da zata ci"""

"Dariya suka yi dukkansu. Mustapha da Babangida suka mi™e. ""Sai gobe da yamma in na shigo majalisar. Ka gaida matayenka"" Ya saka kai suka wuce shi da Mustapha."""

SABUWA:.

Da sallama muka shiga gidan matan gidan dama ma™ota duk suna tsakar gida anata zuban zance can na hango ³ar Shuwa a tsakiyarsu anata hira harda shewa.

"""Sannunku fa ina kwananmu?"""

"Cewar Adama. Nan suka amsa da fara,arsu muka yi wucewarmu zuwa ciki. A falo muka ya da zango. ""Wallahi Lolo waje yayi kyau sosai. Duk waWannan da muka wuce matan gudanku ne?"""

"A_a Sama harda matan ma™ota hira suke shigowa yi na fahimta"" Uzairu zuchiyata yace."

"""Kada ki sake ayi wannan zaman gulmar dake. Kina ganin ³ar shuwa a cikinsu ta mimmi™e ™afarta itace harda"

"shewa. Baki ga irin wani mugun kallo da take watsa miki bane, ni ko ina ankare da'ita wallahi watarana zamu yi mata babu daWi"""

Adama tace.

"""Ai muna nan daku wata rana Babangida sai yayi mata abinda harta mutu ba zata taSa iya mancewa ba."" Dariya nayi musu nace."

"Ai ko yanzu kasuwar tawatse Wan koli yaci riba. Babangida inaga fa kuWin da yaketa juyawa yake auran mata ya saki kamar ba nashi bane. Shi da kanshi ya taramu yake yi mana bayanin cewar wannan gidan hayan anan za'aci gaba da zama sabida shi ya rasa komai nashi hatta abinci yace musu su jalauta na hannunsu dan saiya warke zai nemi sabuwar sana'a"""

Rahama tace.

"""Kuma Lolo ke kina ganin da gaske yake yi kuwa anya, har gida da motarshi kenan ya rasa, ina ita tata motar to?"""

"A labarin daya bayar komai ya rasa hatta kamfaninshi ya rasa balle wani gida da mota. Akwai dai abinda yake ™asa yana dabo amman ni ba sani zanyi ba gaskiya. Shi kuma dama zurfin ciki gareshi nayi imanin bazai zauna ya tattauna da ko wacce a cikinsu ba. Shi da danginshi ai sun san inda matsalar take."""

Aisha tace.

"""Da badan wani abu ba dana rangaWa guWa a wajennan wallahi. Duk da haka naji daWin wannan labarin ³ar shuwa zata gane shayi ruwane a yanzu"" murmushi nayi nace."

"In bata sa ya saketa ba ko? Ai ba zata iya zama dashi a matsiyaci ba. KuWinshi ta biyo fa ai ko a haka ta tatsa da yawa. Tunda naji labarin gini ma take yi. ³ar Shuwa fa ba zama zata yi ba. Ni kuma zanta ro™a mata Allah akan ta ™arashe rayuwarta a gidan Babangida. Wallahi in batai wasa ba saina kafeta a gidannan"""

Dariya muka kwashe dashi dukkanmu tamkar babu mai matsala a cikinmu. Sama ne yace.

"""Ku tsaya nifa Aure zanyi na samu macen da take sona tsakaninta da Allah. Kuma da gaske aurena take son tayi. Kuma nima a guje na karSeta. Kune ´an uwana naga yafi dacewa in sanar daku farko tukunna tunda su Rakiya faWace_faWacensu suka sani. Ni na rasa dalilin da yasa suke son maigogul har suke faWa a kanshi."""

Nan muka shiga murna da farin ciki marar misaltuwa a mazan gidanmu babu wanda ya taSa aure budurwarma in banda Uzairu zuchiyata wake kula mata cikinsu.

"""Kai wannan abun murnane gaskiya Sama wannan yarinya da abun mamaki take. Kuma ta ganka tasan yadda kake Sama? Kai da baka da sana'a ina kai ina jijjiSo aure kuma ga kanka suru_suru"""

Murmusawa yayi yace.

"""Adama kwantar da hankalinki zata nema mun aiki kamar yadda taimun alkawari. Inma ni ban samu aikin ba ita tana aikinta zata ci gaba da zuwa aiki zamu rufa ma juna asiri."""

Ni dai baki cike da fara'a nace.

"Menene sunanta, kuma ita wannan mata zance dan bana ce yarinya ba a ina take?"" Wayarshi kawai ya zaro ya danna mata kiran waya a lambarta ya rubuta mata Love. ""Hello ki kirani zaki gaisa da ™annena muna tare dasu"""

Yana gama faWan haka ya kashe wayarshi wallahi saiga kira ta biyo shi dashi. Allah mai iko Rahama ya mi™ama itace suke zaune kusa sosai.

"Gaisawa suka yi fes kafin ta mi™ama Adama, daga Adama sai Uzairu zuchiyata ya karSa, suna gaisawa ya mi™omun. Haka dai

Please Login or Register in order to submit comment