ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baba Malam bari inje yanzu ta kula da Yayan"" Godiya nayi ma Baba malam. Tare suka fita da Ramadan."

Bai jima ba sai gashi da waya Asha harda sabon sim na zain wanda a yanzu ya zama Airtel da can kuma sunanshi Econet.

Shi da kanshi ya saka mun sim Win a wayar ya kunna.

"""Gashi Maman Mardiyya. Nasa miki lambar malam akwai kyautar kuWin kira nera Wari da suke bayarwa zaki iya kiranshi dashi. Sannan dan Allah kiyi ha™uri da abubuwan dake faruwa"""

"Amsar wayar kawai nayi. Babu komai Baban Amina."""

Muna cikin haka Hamida da ³ar Shuwa suka shigo.

Mu dasu babu me kula wani. Sai harare_harare nake yi.

Šigimi har mahaifin ³ar Shuwa saida yazo ya duba Babangida. ˜annenta kuwa da mamanta sun jima sosai sune har azahar.

"A masallacin asibitin mu kai Sallah ni da Labbai. A cikin masallacin na kira Baba Malam yaga number na, ya sake jaddadamun lauyan zai kirani dai."

Godiya nayi mishi na kashe wayar muka koma barandar da muke zaune dukkanmu.

"Muna zuwa muka ga dangin Hamida an taso har mata biyu da wani dattijon da in ba mahaifinta bane, to ™aninshi ne ko wanshi tabbas."

"Ni dai cikin mutumtawa na gaishesu suma kuma sun amsa da daraja harma da tambayar me jiki. ""Sabuwa ina yini ya mai jikin?"""

Hmm kunsan wake wannan maganar?

"˜awata Fiddausi wacce itama tare muka taso daga baya ne suka bar layinmu suka yi gini. Har sunan Malama tazo mun, duk matan da Babangida ya aura a baya duk da ita akayi mun dannar ™irji. Daga baya ne aiki ya mayar da mijinta kaduna ya tarkatasu suka koma sai ya zamana sai dai muyi waya. To ashe itama tana tare da ³ar Shuwa tunda gashi tazo mata"""

"Lafiya lau Fiddausi jiki da sau™i"" Na faWa da fara'ata ™a™as."

"""Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"" Ameen"""

Na faWa a ta™aice.

Ramadan ne ya fito da sauri.

"""Maman Usama, da Maman Fatima Babangida ya farka yana nemanku"" Da sauri suka mi™e suka shiga. Har suna rige_rige"

Niko da idanu kawai na bisu na taSe bakina.

Babangida:.

Yana buWe idanunshi wani irin zafi da tsamin jiki sukai mishi sallama.

Idanunshi ya runtse kawai yana tuno dukan ™irjinshi da Sabuwa ta haukace tayi mishi. Hoton fuskar Khalid kuwa abadan bazai gogu a ™wa™walwarshi ba sam.

Idanunshi ya runtse tare da furta.

"""Kin cutar dani Sabuwa kin ruguza mun zuchiyata. Ashe haka nake kishinki?"" Furucin daya janyo hankalin Ramadan zuwa gareshi."

"""Babangida ka tashi, bari in kira likita dan tace daka farka a kirata."""

"Fita yayi yaje ya kira likita, tare ma suka tawo ta shiga dubashi gami da mai tambayoyi."

"""Yanzu abinda za'ayi shine a nema mishi tea ya soma sha ya warware hanginshi sai yaci abinci. Zai karbi allurai da magunguna. Malam Babangida sannu ko, Ubangiji Allah ya ba da lafiya. Sannan a kula da yawan motsa hannun gudun kada a dawo mana da aiki baya'"

"Tana kaiwa nan ta fita akan in yaci abinci za'azo a yi mishi abinda ya dace."" ""Ina su Malama Babba da su Kawu Manga duk basu zo bane?"""

"Babangida ya tambaya idanunshi a lumshe, hoton yadda Sabuwa ta faWa motar Khalid ya shiga tariyo kanshi da kanshi a ™wa™walwarshi."

"""Sun zo Baba Malam ne yace su koma gida. Kuma yace kada su sake zuwa ma."""

"Bai buWe idanunshi ba. Kuma baiyi mamakin abinda Ramadan ya faWa mishi ba. Sai cewa yayi. ""Wayata tana hannun waye, sannan ina su Hamida?"""

"""Uhm wayarka inaga tana hannun Yaya Mustapha tunda shi ya kawo ka asibity. Ko Wazu da safe abokanka duk muna tare anan dazu."

"Su Maman Usama suna waje harda Maman Mardiyya ma"""

Runtse idanunshi kam yayi jin an ambaci sunan Sabuwa sai yaji tamkar an watsa mishi ruwan dalma a kwanyarshi. Cikin hucin kishi yace.

"""Ban yarda a barta ta shigo inda nake ba sam Ramadan. Ka je ka kirawo mun su Hamida su zo"" Shine kiran da Ramadan ya fita yayi musu."

"Suna shiga suka tarar da dabara Ramadan na ™o™arin zaunar da Babangida dan yace duk jikinshi tsami yake yi mishi. ""Maman Usama dan haWa mishi tea mai kauri"""

Cewar Ramadan dake kiciniyar sama Babangida fulo a bayanshi.

"Tea kakkaura hamida ta haWa mishi daidai sha inda bazai ™ona baki ba, amman zai dumama ciki."

"Duk da Babangida baya jn daWi a zuchiyarshi da ruhinshi, da gangar jikinshi hakan bai hanashi shanye tean matanshi nata aukin yi mishi sannu ba."

"""Sannu Jannaty. Naji mummunan labarin abinda ya afku. To ni dama na Wauka ta dena bin maza ne tunda nayi mata faWa a baya sosai"""

Wani mugun kallo Babangida ya feso mata wanda saida yasa cikinta ya Wuri ruwa. Gashi dama amfani take so tayi da wannan damar ta yima Sabuwa sharrin da dole ma ta bar gidan Babangida.

"""Au munafuka ashe ke daman kinsan maza take bi shine kika rufa mata asiri? Ohh wato ke kika Waure mata baya tabi maza da aurena ko?"

"Wallahi harke bazan ™yale ba ke da Sabuwa saina Waureku har igiya sai tayi saura. Tare zan koreku ai in dai Sabuwa ta bar gidan kema ba zama zaki yi ba maras mutunci. Shi kuwa farkan nata kasheshi zanyi da hannuna. Zan yi maganinku duka. Wallahi ba'ayi komai ba akan Sabuwa zan iya mutuwa"""

"Babangida da ihu da faWa yake maganarshi. Wata ma'aikaciyar jinya ce ta karaso"""

"""Amm kuyi ha™uri kuje daga waje sabida ba'ason mara lafiya a dinga faWa mishi maganar da zata Sata mishi rai. Bakwa ganin halin jinyar da yake ciki ne? Da Allah kuje waje"""

Ta faWa a wula™ance. ³ar Shuwa sai zufa take sharewa allura na neman tono garma. Jikinta a sanyaye ta fita zuchiyarta cike da tunanin mafita. Gami da mamakin kalmar da yace akan Sabuwa zai iya mutuwa.

"""Kenan yana sonta dama?"""

Wannan amsar har Hamida ita suke ta son ji.

"Hamida na biye da'ita har zuwa barandar da suke zaune"""

"""Iskanci kawai. ³ar iska ashema tasan tana bin maza bata iya faWa mun ba. Kenan ita ta bayar da ™ofar ayi iskancin ma? To zan kuwa kaWasu tare kenan in huta dan wallahi itama ta fita a kaina."""

Idanunshi ya rufe wasu hawayen mugun kishi da ba™in ciki ya biyo gefen fuskarshi ya zubo siriri dashi. Farfesun da Sabuwa ta dafo mishi na kayan ciki shi Ramadan ya zuba mishi.

"""Bazanci ba tunda dai ba dole bane kaji ko?"""

Kafin Ramadan yace wani Abu sai ga Kawu Manga tare da Wawo da Jibrilu sun shigo. Kai da ganin fuskokinsu kasan cike suke da damuwa mai tarin yawa.

"""Babangida ka samu ka tashi kenan? Gara da Allah yasa idanunka biyu domin kaine kaWai zaka iya warware mana wannan ™ullin ko zamu samu nutsuwa."""

Cewar Kawu Manga dake dafe da kan Babangida.

"""Na farka Kawu. Kaga abinda wan Sabuwa yayi mun akan gaskiya ta ko?"

"Bazan bar maganarnan ba gaskiya Kawu."""

Wawo yace.

"""Kaga duk ba wannan ba. Al'amarin fa daya tunkaroka al'amarine mai girma. Shin kasan Alhaji Abubakar Baban Bola dai ko, sannan kasan da maganar dukiyarshi dake hannunka? Muna son ™arin bayani, dan yanzu haka maganar tana kotu"""

A mugun razane yake kallon Wawo zuchiyarshi da kanshi a lokaci guda ya buga. Ma'aikaciyar jinya ce ta karaso wajen tare da katse musu hanzari da cewa.

"""Dan Allah ku Wan bamu waje, zanyi mishi allura kuma zai sha magani, ba'aso ya fiye yawan magana sakamakon jininshi da ya hau."""

Kawu Manga yaima Ramadan da Wawo nuni da su su fita.

"A sanyaye suka fice. Kawu Manga na tsaye ™yam yana kallon yadda jikin Babangida yake rawa, ita kanta ma'aikaciyar jinyar abun karfinta yafi a guje taje ta kirawo likitan da yayi aikin dare suka dawo tare."

Aunashi yayi jininshi ya yi mugun hawa fiye da kima. Allurar gaggawa akayi mishi bacci ya debeshi luu.

"""Uhm Baba akwai wani abun da aka faWama mara lafiyanmu wanda ya Waga mishi hankaline?"" Kawu Manga ya sharce zufar data keto mishi yace."

"""Akwai Dr karayar arzikice ta sameshi"" Idanu Dr ya Wan runtse yace."

"""Ashsha na tayashi jimami gaskiya. Amman Baba ai asibiti ba wajen tattauna ire_iren waWannan maganganun bane. In akayi la'akari da irin halin da shi marar lafiyan yake ciki. Nan gaba a kiyaye hakan dan Allah. Yaci abinci ne daman?"""

Saida ya kuma ajjiyar zuchiya dan ya riga yaga amsar da suke son ji daga yanayin Babangida tabbas komai ya tabbata duk da dai ga saka hannunshi nan akai.

"""Sai dai a tambayi Ramadan shine ya kwana dashi"""

"Wayarshi ya Waga yayo kiran Ramadan. Yana ganin kiran sai bai Wauka ba ya garzayo da sauri. ""Mara lafiyanmu yaci abinci ne?"""

Dr ya kara tambaya a karo na biyu.

"""A_a ya dai sha tea amman da kauri. Abincin na zuba nayi nayi ya™i yarda yaci"""

"""Ok babu damuwa tunda ya sha tea. A kiyaye domun ba'ason hayaniya. In so samu ne duk kuyi zamanku a waje dan Allah ba sai kun shigo ba, mu zamu dinga dubashi"""

"Tare suka fito da Dr daga Wakin. Wawo ne ya nemi a sake ma Babangida Waki, a saka shi a I P U nan da nan aka maidashi abinka da kuWi harma kulawar da ake bashi aka ninka."

SABUWA:.

Mu dai muna ta zaune mu na Wan taSa hira da Labbai.

"Daga shigarsu Hamida wajan Babangida har fitowarsu, kama zuwansu Kawu Manga da fitowarsu, da sake ma Babangida Waki duk ina zaune ina buga lissafine kawai."

"Bamu muka bar asabitin ba har saida muka yi isha, muka tattare kwanukan abincinmu wanda Ramadan ne kaWai yasha farfesun mukai musu sallama muka tafi."

A nan muka baro Kawu Manga da Wawo.

"Hamida,tun yamma ta dawo gida ita da ba™inta. ³ar Shuwa da ™annenta ™ila nan kwana dan naga basu Waura haramar tawowa ba."

"Ko da muka shiga gida munyi tulis da gajiya tara da kusan kwata muka shigo. Mardiyya ce ita kaWai a zaune a falo tana ta karatun Alqur'ani. Tana ganinmu ta mi™e. ""Ummi kun dawo. Ya jikin Baba"""

"""Jikin Babanku da sau™i. Ina su AWWa'u?"" Labbai ta bata amsa."

"""Allah ya ™ara sau™i. Su Aminu tun Wazu sukai bacci. Ummi Wazu AWWa'u daga zuwa masallaci yabi abokanshi rafi da daddare da ™yar muka ganshi. Dana dakeshi shine ya zageni"""

Kai kawai na girgiza wannan yaro baya ji sam. Kullum ina mishi adda'ar shiriya.

"Hmm barni dashi gobe da safe zaki ga yadda zamu kwashe. Kije ki kwanta muma a gajiye muke."" Sallama tayi mana ta wuce Wakinsu."

"Ni na wuce ciki kai tsaye zuwa banWaki dan in watsa ruwa ko zanji daWi, Labbai kuma kitchen ta nufa dan ta sama"

mana abinda zamu ci.

Ina zaune ina shafa mai wayar da Baba Malam ya bani ta soma ringing. Nadai san lauyan da akace zai kirani ne. Dagawa nayi da sallama a bakina.

"""Ameen wa alaikis salam. Sunana barrister Ahmad Ahmad. Ina magana da Sabuwa ne wacce ta shigar da ™arar mijinta tana neman ya saketa?"""

Idanuna na lumshe a hankali wani irin zazzaSine yake hudani sosai. E nice ina wuni?'

Na bashi a takaice.

"""Lafiya lau. Gobe inaso ni dake mu haWu dan mu tattauna dangane da Shari'ar da zamu soma. Sabida musan yadda zamu bullowa lamarin dan shari'a a tsakankanin mata da miji sharia ce mai rikitarwa."

"Inason jin jawabai daga gareki."""

"To Shikenan a ina zamu haWu, ko zanje gidan iyayena sai ka sameni acan. A unguwar Zai suke"""

"""Yauwa hakan yayi. Kije zanzo da misalin karfe takwas na safiya sai kiyi iya ™okarinki kafin lokacin ki rigani isowa."" A haka muka daddale na sauke wayata."

"""Kixo muci abinci. Indommie da dafaffen ™wai na dafa mana sai tea"""

Bakinta cike da ™wai take maganar. Ni tean kaWai na sha na watsa magungunana.

"""Lolo na fahimci kamar bayan ciwon Babangida kamar akwai wata matsalar kuma. Amman ke me kika fahimta?"" Ta kafeni da idanunta tana son taji ta bakina."

"Toh ni nafi tunanin ciwon nashi ne, ko dalilin ciwon nashi. Amman banyi tunanin wata matsala ba"""

"""Amman da gaske ne Lolo da wano Babangida ya kamaki, ko dai ba™in zargine da jan kishi dake damunshi?"" Numfashi naja tare da cewa."

"Da gaske ne Labbai. A mota yaga an saukeni da ledar shopping. Iyakar abinda kaWai ya gani kenan"" Tambaya take son sake jefo mun na katseta."

"Dan Allah ki barni inji da abinda yake damuna. Koma menene aurenmu yazo ™arshe ko ya ganni ko bai ganni ba ba shikenan ba?"""

Gado na haye na rufe idanuna zuchiyata da jikina nata mu™ur™usata. Bansan sanda nayi bacci ba. Zage_zagen da Labbai naji tana ta yi a wayane yasa na farka naga gari har yayi shaa. Da sauri na shiga banWaki na Wauro alwala sabida tsabaragen jarabar da take ta faman yi a waya ni dai sai a Wakin yara nayi Sallah. Su kuma sunata wanka da shirin makaranta.

"Sai kallonsu nake yi ina tausaya musu. Bansan yaya zasu fuskanci rayuwa ba, ban kuma san wacce iriyar rayuwa zasu yi bayan bani a tare dasu ba. Ban kuma isa cewar a bani yarana ba, domin nasan Babangida na da hujjojin da zai gabatar a kotu yasa a hanani ri™on ´a´an. Nima ina cikin damuwa da tsoron kada in ri™esu tarbiyyarsu ta lalace duk da bazan iya rayuwar gidanmu ba nafi son in kama haya in zauna ko zan nutsa."

"AWWa'u zo nan"""

"Na faWa da murya mai kauri. Da sauri yazo wajena dukanshi nayi niyyar yi, hannuna daya kama yasa zuchiyata tayi sanyi abinka da uwa."

Wato jiya dan bana nan shine AWWa'u kayi tafiyarka yawo har saida aka nemoka ko? Sannan ka zagi Adda AWWa'u na ro™eka da girman Allah kabi Allah kabi duk abinda Adda zata ce maka ka Wauketa tamkar uwa.

"Har da kai Aminu, dake ma Malama da kike muttsuka idanu."" Duk sai akai dariya baki Waya na dinga yi musu nasiha."

Kafin na mi™e na fita zuwa kitchen dan anan na jiyo Suruntun Labbai.

Doya da ™wai take ta soyawa. Tana yi tana Wure_Wuren ashar harda sharar hawaye.

"""Se me dan kace in yi zamana a gidanmu. Ni da sakina kayi da yafi mun Wan gidan ta™i zama ta zauna kawai."

"Ke kiji mun wannan maras mutuncin Habu, daga na Wan tambayeshi kuWi nera Wari biyar fa. Shine ya zage ya shiga yi mun Wiban albarka, har yana cewa in zauna a gidanmu in ubana ya koya mun tarbiyya na koma."

In kaya ya gaji gammo ma ya gaji. Babu inda zan koma sai dai ya aiko mun da takaddata dukan ya isheni. Nifa yanzu in ba mai kuWi ba bazan kuma aure ba.

Jibeki ko dukanki akeyi zaki ci kuka ki toya ™wai ki kunna ac ga tv ga suturu.

"Mufa a dakemu mu fito mu tu™a tuwo miya lami, da safe kokkone ko sigari babu wacce take da kuWine zata sai masa, kosai, ko ´ar tsala fa"""

"Dariya na kwashe dashi, itama dariyar ta saka."

"Ke dai yi maza ki sallamesu, mu ki juye mana namu a kula maci a gida sauri nake yi kinga har bakwai tayi. A gurguje muka gama komai muka fito tare da yaran"

Karfe takwas saura minti goma muka isa gida.

"Nanma muka tarar maigogul yana yima su Rakiya tujarar daya saba. Duk suna tsaye ya faWa su da faWa, Rakiya ta zageshi tas."

Wani abune ya tokareni a wuyana banko kallesu ba nayi shigewata ciki.

"Su Sadiya duk suna ciki sunata karyawa harda Uzairu zuchiyata. Da magazin. Ko wanne cikinsu da abinda yake ci, dan kowa da kudinshi ya siya."

"""Labbai kafin ki zauna zo ki karSo mun waina"" Cewar Rakiya data le™o."

"""Ga ™wai da biredi da doya Rakiya zai ishemu ki shigo"""

˜wafa tayi ta shigo ta baro Maigogul da Hauwa suna ci gaba dayi.

Mu kuma muna karyawa su Sadiya sunata hirarsu. Uzairu zuchiyata yace.

"""Ashe dambarwar tsiyar da akayi kenan ke Lolo? Uhm ai wallahi Gaza yayi mun daidai. Allah ne ma ya so shi bama gidan wallahi da raunin yafi haka."""

Magazin yace.

"""Wanne rauni? Ai kasan Allah da ace inanan to sai dai gawarshi. Nifa da har ubanshi daya tako gidannan saina tsinke mishi agara Allah"""

Danna ™wai yayi a bakinshi wanda ya gutsura a cikin kular gaban Labbai.

"""Ai ™arshenta Rakiya a gidan gyaran hali zata ™arke rayuwarta in dai bata dena wannan shegiyar sana'ar kayi nayin ba. Mata sai sayen kayan sata"""

Tana jin Maigogul ya faWi haka zuruf ta fita dawa Allah ya haWata in ba dashi ba. Uzairu zuchiyata a guje ya bita yana aikin dariya.

Nidai lauyana daya kirani na rakici Labbai nace tazo muje.

"A lokacin da muka fito har gidan ya soma Winkewa da maza da mata ´an ban hakuri maigogul ya tuSe rigarshi ya doka da ™asa zai doki Rakiya, ita kuma anata ri™eta akan yana dukanta zata rama."

Ficewa muka yi a wajema matan unguwa duk an firfito anata gulma harda mahaifiyar ³ar Shuwa.

"""Mutanen banza gida sai kace karnuka. Ni na taSa ganin jahilai irin wannan gidan kuwa? Kamata yayi wallahi a koresu a wannan unguwar domin zasu lalata mana tarbiyyar yara"""

"Allah sarki inji mahaifiyar ³ar shuwa kenan fa. Wai me bunu a ™un™uru ke kai gudunmawar gobara. Wacce kalar karuwace bata da'ita a gidan nata. Su kansu masu gulmar ko wanne nada guntun kashinshi, sai dai dake ance lefe tudu ne, kahau naka domin kayi le™en na wani. Allah dai ya basu sa'a dan Magazin zai iya fitowa nasan ya watsasu. Wani mutum ne naga ya fito daga farar motarshi, yana saye da surt ba™a™e da ba™in gilashi, ya nufomu."

"Nanfa kallo ya koma kanmu gulma a kyauta. ""Kece Sabuwa ko?"""

"Ya tambaya yana nuna ni da manuniya"""

"E nice sannu da zuwa. Ga dakali mu Wan gangara mu zauna"""

"Na nuna mishi dakalin ™ofar gidansu Babayo muka ™arasa muka zauna, muka sake gaisawa. MRS BUKHARI"

Sanya

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA HUŠU

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa

Ko kimin mgn ta 08093932955

"""Zanso insan menene dalilinki na shigar da ™arar mijinki ya sake ki, shin wanne hujja kika ri™a a matsayin babban"

"dalili, sannan in ba'a kotu ba bazai iya sakin ki bane?"""

Kaga lauyoyi duka wannan tambayoyin lokaci guda aka watso mun. Kuma ya kafe ni da ba™a™en idanunshi yana jiran amsa.

"Dalilin da yasa na shigar da ™aran shine bana sonshi, duk kwanan duniya ™ara tsanarshi nake yi. Hujjata shine."

"Ya dena ciyar damu, baya shayar damu, baya mana sutura, baya biyan kuWin makarantar yara, baya mu'amalar aure dani."

"Sannan tambayarka ta uku tsawon shekaru sama da goma ina faWin ya sake ni yana cewa ni dashi mutuwace zata raba, kuma badan yana sona ba sai don mugunta kawai"""

Kanshi ya jinjina yace.

"""Yana cin zarafinki ne, ko zarafin iyayenki, sannan yana dukanki ne?"""

"Babu wanda bayayi daga cikin abinda ka lissafo. Babangida ya wuce tunaninka, wata iriyar ba™ar zuchiya gareshi."" Shiru yayi yana nazari can ya jefo mun wata tambayar."

"""Auren dole kuka yi ko Auren soyayya kuka yi?"""

"Bazan ce auren dole ba, ba kuma zance auren soyayya ba. Babangida yayi mun irin soyayyar da babu mahalukin da zai iya yi mun ita a duniya."

Daga baya ne komai ya lalace.

"Amman karka tambayeni dalilin lalacewar domin bata shafi shari'ar ba"" Murmusawa yayi kawai kafin yace."

"""Iyayenki suna bayanki ne akan shari'ar kamar yadda Baba Malam yake bayanki?"" Kai na girgiza nace."

"A_a basa bayana kona mis™ala zarratin."""

"Mijin Labbai ne yazo ya wuce mu, Labbai tayi tsaki ta bishi da harara. Barrister Ahmad Ahmad yace."

"""Baba Malam menene hala™arshi dake?"" Shine mahaifin mijin nawa"""

Har a jikinshi saida mamaki ya bayyana ba'a iya fuskarshi ba.

"""Ban gane ba. Kina nufin Wanshi kika maka a kotu kuma ya Waukar miki lauya, yake ta jaddadamun inji tsoron Allah in yi iyakar yina a ™wato miki hakkinki Babangida ya sake ki?"""

"Tabbas mahaifinshi ne"""

"""Toh Malama Sabuwa ni zan wuce in ma akwai wata tambayar zan bugo miki waya saimu tattauna. Ki kuma zauna da shirin fuskantar Shari'a ki sani kuma saSanin hankalice, tamkar macece da ciki, kinga sanin abinda zata haifa sai Allah. Na barku Lafiya"""

Ya mi™e da sauri ya tafi.

Nayi shiru a zaune a dakalin Labbai tace.

"""Wai kinsan tunda kuka fara magana da lauyannan ™annen ³ar Shuwa da mahaifiyarsu suke ta faman sunturi kuwa?"""

Baki na taSe nace.

Ina ganinsu sunata wucewa kamar ™awayen Amarya.

"Naga Malam Habu ya wuce"""

"""Malam ko buzuzu? Dallah tashi mu tafi ni. Aurene ni dashi ya ™are"""

Ashe yana tawowa duk abinda Labbai tace a kunnenshi. Yana ™arasowa buWar bakinshi sai cewa yayi.

"""Aure kam ya ™are, domin ni ba lusari bane da zan zuba idanu ina kallonki da aurena kina bin maza kamar yadda aka kama Sabuwa ba, yanzu ma ba gashi na kama ku ba."

"Na sake ki saki guda, dama dai kwaWayine irin namu na maza shi yasa na auro karuwa"" Naji zafin maganganun Malam Habu sosai. Musamman karuwa daya cema Labbai."

Kafin in ankara Labbai ta cukumeshi tana ihu tana kwaroroto. Wallahi kafin ™iftawa da bismillah sai ga jama'a sun taru.

Malam Habu ya dinga cauWama Labbai carbi yana jefo manya manyan maganganu marasa daWin saurare a kanmu. Sama da ™asa Allah baisa na iya cewa komai ba.

"Cikin munafukan da suka taru na kutsa na fincike Labbai a wuyan Malam Habu na jata kiyyy har cikin gida. A lokacin ™urar cikin gidan ta lafa, Rakiya ma wanki take yi, Hauwa na kwalima."

"""Wai menene dama daku ake hayaniya ne Labbai."

Ni naji matan Malam Habu sunata Wuma zagi ta katanga. Kafinma mu bada amsa muka jiyo zagin.

Turmi Labbai ta hau sukaita zagi in zaga da iyalan gidan Malam Habu ta karanga Da ™yar na fige Labbai muka shige Waki.

Yaran gidan sukaita jifa daga gidansu zuwa namu.

"Dawowar Gaza yasa komai ya lalace. Yana shigowa aka jefo ™aton dutse ya sauka a ™afar Rakiya. A guje ya shiga gidan Malam Habu, Labbai ta bishi da gudu da wu™a a ™ugunta."

Hmmm abu dai babu arziki duk matan gidan shigewa Waki sukai suka kulle. Gaza ya saka ragunan Malam Habu gabas ya dinga yankasu.

"""³an abu ta kazan uba. Ku shiga ku Webo kayanku mu tafi. Yasin duk matar da muka haWu a hanya sai dai ta canja hanya in ba haka ba saina farWeta."""

Haka mukaita jide kayan Labbai muna ficewa dashi. A guje Rakiya ta shigo.

"""Gaza matsa dale katanga ka wuce ga Malam Habu da kwalawa. Take katanga maza"""

Ragunannan daya yanka ya suri biyu ya yaSa a kafaWa suna yararin jini ya haye turmi ya dire bayan lungu. Yana direwa kwalawan na shigowa a guje.

"Jin muryoyin ´an sanda yasa iyalan Malam Habu fitowa. ""Kaga ta'asar da yayi mun ko?"

"YallaSai ku wuce da waWannan matan dukkansu, kuma wallahi sai an biyani ragunana raguna kusan takwas a yanka mun su sabida rashin tarbiyya Gude a mayar mun da kayan Labbai ciki"""

"""A_a Malam ka rabu dasu kawai tunda dai mai rabawa ta raba. Wallahi ina jiye mana bala'in da zai biyo baya."

"Ni dai Malam ka dangana kawai. Tunda kai ka yayiSo mana dama yaran gidan farare. Meye bamu faWa maka ba? Kar ka bari a tafi dasu, muna da yara mata kada Gaza ya turo yaranshi sui ma yaranmu fyaWe a banza da wofi"" Tana faWan haka sai jikin Malam Habu yayi sanyi."

"Take yaja ´an sandannan waje, ya suka ™are sai Allah. ""Labbai maza kwashe kayanku ku tafi"""

Cewar Gude da ciki ya Wuri ruwa. Rakiya tace.

"""Ai ba sai kince ba. Wallahi kinyi ma kanki Alamnashara Gude da zaman unguwarnan ya gagareku.Yanzunma sai fa mun so rigimarnan zata lafa."

"Labbai ku kwashe kayan mu wuce miji goma ba uba goma bane. Ku Wakko mana ™atuwar tinkiya in dai da Bismillah ya yanka"""

Dukkanmu muka haWu muka kwashe kayannan Labbai kuwa saida ta kinkimi ™atuwar tinkiya ta fice tana ta zage zage unguwa ashe ta cika ta batse sosai da sosai.

"Ohhh Allah rayuwarmu tana cikin garari. Shin haka rayuwarmu zatai ta tafiya babu sauyi ne?"""

Muna shiga gidan muka tarar Adama tazo tana

Please Login or Register in order to submit comment