ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana rufe idanunshi.

Wasu siraran hawayene suka gangaro mishi masu zafin gaske. Burinshi ya mance da abubbuwan daya gani. Sai dai ina yasan har abada bazai goguba.

"Zama yayi a kujera zazzaSi yana sakko mishi, zuchiyarshi na faman bugawa, wani abu na sakko mishi wanda shi kanshi baisan menene ba."

A ranshi ya ™udure har gaba da abada ya dena mu'amula da matan banza. Kuma da kanshi zaije ya sallami Sumy. To

"Wanshi dake wajenta yayi Yaya dashi, wa zaiba ri™on yaron, me zaice in aka tambayeshi daga ina ya samo Wa? Wannan yana daga cikin illolin bariki."

Idanunshi ya lumshe yana jin tsanar Sabuwa da tsanar kanshi na sakko mishi.

"Ba sallah, babu salati, babu istigifari yana zaune akayi kiran sallar farko. Idanunshi da fuskarshi baki Waya sun yi jawur sun kuma kumbura. Da ™yar ya shiga banWaki ya shasshafa alwala ya fito, raka'atanil fajir ya gabatar yana mai jin kunyar mahaliccinshi a bisa kauce dokikinshi da yayi. Allah ya bashi sani, yasan illolin zina, yasan irin lalacewar da mazinaci yake tsintar kanshi a ciki, shike ma wasu wa'azi amman shi ya™i hankalta."

"Kai ya girgiza ""Kaicona"""

Ya fice zuwa Masallaci jiki babu laka.

Yana ta juyayin hawan jinin da Sabuwa ke Wauke dashi.

SABUWA:.

Jin fitar Babangida yasa na tashi Mardiyya.

"Mardiyya kije kiyi wanka ke da malama. Kafinnan ki soma tashin yaran can su yi alwala su tafi masallaci"" Ina gama faWa mata na ta da kabbara."

"Bayan na idar da Sallah, nayi addu'o'ina saina haye gado dan kaina kamar zai fashe haka nake jinshi, numfashina ma naji yayi nauyi."

"Bani na farka ba sai goman safe idanuna sunyi nauyi sosai. Nasan bani da damuwa Mardiyya tayi ma ™annenta duk abinda ya dace sun kama hanyar makatanta, kafin in kwanta dama na ajjiye musu kuWin mota a saman durowar gado."

A hankali na sakko da naji cikina na wani irin murWamun.

"A falo nake jiyo muryoyin su Babangida, ko da su waye oho. Wanka na wuce nayi na dawo na zura riga mai sau™i na kuma fita."

"˜ofar shiga falon na tura na shiga ban kalli kowa ba nayi ficewata, na dai ji wani Wan kanzagi daga cikin abokan Babangida yana cewa."

"""Sannu Madam"""

Watsin ruwan tsarki nayi dashi nayi fitata.

"Šumamen tuwon jiya su Mardiyya suka ci, ga kari biyu ta ragemun ta barmun a cikin tukunyar miyar. ""Maman Mardiyya yau sai yanzu kika fito dake kece da Oga? Ahh Lallai zamu zo Wiban hadda a wajenki"""

Cewar Maman Sa'idu kenan. Duk matan lungun suna zaune ko wacce a kujera tare da wasu gungun mata da banyi tunanin a gidan suke ba. Ga wani kwangirin kwano a gabansu. Šan murmushi nayi muka gaisa da matan wajen.

"Wallahi bana jin daWine ma shi yasa. Dan ko su Mardiyya bansan sanda suka tafi makaranta ba"" Maman Sa'idu tace."

"""Na tambayesu ma ina kike suka ce kina bacci."

"Sai kika bar Babansu da kiciniyar yi musu kayan kari shi da baida lafiya. Sai daga baya Mardiyya ta karSa ta ™arashe musu."""

Sai naji kaina ya Waure a raina na shiga jujjuya maganar amman dai na kasa fahimta. Wata zabiya ce ta katsemun tunanina da muryarta mai za™i da karaWi kamar ta Šaye manna ( Habibty) dan da wa™a baiwar Allah'nnan zata yi da zata samu a jikin wa™a.

"""Toh ni dai Mamam Mardiyya zo ga haja kema ki zama memba kafin Maman muklisiyya tazo ta kwace mun ke. Duk matan lungunnan da matan ma™otanku gasu a wajena suke siyayya kuma wallahi nake faWa miki kuWaWe suke tatsa a wajen mazajen nasu shi yasa zaki gansu kullum fes dasu ga cin abinci me kyau. Kiga mace da yamma fes da'ita ta Wau seti network ciki da waje."""

"Shewa suka saka harda tafawa. Nima saida na dara. Ina dai daga kitchen Wina nace. Hmm ni da megida babu lafiya ina ni ina shan kayan harka. A dai bari in ya samu lafiya"""

Carab wata matar tace.

"""To ga ™ananan kaya na gwanjo amman giredi ne sosai zo ki zazzaSa."

Gudun kada su rainani dai yasa na ™arasa wajen inda ta buWe buhun kayan na shiga Wagawa. Gaskiya suna da kyau babu laifi sai dai in ba siye zaka yi ba.

Wata riga mai ruwan hoda na Wauka me hannu Waya da ba™in wandon da suke tare. Sai wata riga mai ruwan makuba ita kuma da dogon siket yadin yayi kyau sosai.

"To na Wauki wannan nawa ne kuWinsu?"" Cikin washe baki tace."

"""Tunda ke sabuwar kostoma ce ba da Waya da Wari biyar na miki ragin Wari biyar."" To nagode bari in kawo miki kuWin."""

"Na wuce na koma kitchen Wina na daura Wumamen tuwona a gas, ina ™o™arin shiga ciki su Mustapha suka fito na basu waje suka fice."

"""Sabuwa zamu je asibiti su Mustapha zasu kaini ni saina dawo"" Ganin yadda matan lungun suka kureni da idanu yasa nace."

"Sai ka dawo"""

"Murmushi yayi mun, ni sabida ba™in ciki ma sai naga kamar kuka yake yi. Shigewata ciki nayi na Wakkoma mai gwanjo kuWinta."

Na gama dumamen tuwona na dafa ruwan bunu nayi shigewata ciki.

Ina karyawa sai ga ³ar Shuwa tayo sallama ta kunno kai tana ™arema Wakin kallo. Sau Waya bisa kuskure dana Waga kai naga itace ban sake Wagowa ba.

"""Sabuwa ina Babangida yake? Kin hanashi ya le™o ya duba mu sabida mugun hali. Ai ni daman nasan ba zaki iya barin gidan Babangida ba. Kinbi kin asirce kab danginshi sai ro™onshi suke yi akan kada ya sake ki. Nace ko kin dawo da bokancinki ne Sabuwa?"""

"Da ™arfi take maganarta indai ma™otana suna zaune a inda na barsu to tabbas suna jinta. Dan na lura a shirye tazo tsab danta sanarma Babangida cewar ni boka ce, ta fasa wani ™wai, shima babban saita fallasashi. Ba tasan a yanzu in ™wayayen sun Kai dubu so nake ta fasa uban kowa ya huta warin ya turni™emu duk mu mutu ma."""

"""Dake nake yi bokanya Sabuwa mai bama mata asirin mallakar kishiya, ko mallakar miji, ko kassara kishiya. Ki sani asirinki bazai taSa tasiri a kaina ba nafi ™arfinki tun da bare yanzu"""

Sama da ™asa Allah bai bani ikon tankawa ba. Har na soma jin matan lungun suna magana.

"Kafin in aune sai naga daga waje an hankaWo ³ar Shuwa ta shigo, tana shigowa sai ga Aisha mutan zango da Sadiya sun shigo harda sa sakata."""

"Ina ganin haka nayi kukan kura na dira a wuyan ´ar shuwa nan dambe ya turni™e a tsakankaninmu, na hana su Aisha saka mun hannu. Ai ita tasan baki ta fini ba dai ™arfi ba. Nayi mata dukan Allah ya tsine uwar mai ™arya."

"Matan gidanne suka bankaWo ™ofa suka ™waceta. Da mugun gudu na shiga ciki. Nayi kata_kata na dawo baya wu™a ko wani makamin nake nema da zan illata ´ar Shuwa tura ta kaini bango, daidai nake da ko wacce ´ar abu ta kazan... Frime Wina me glass na ciro a bango na fito da gudu ."

Da Allah ya bani nasara a tsakiyan kan ³ar Shuwa na fasa frime Winnan. MRS BUKHARI

HAYYA HAYYA

³AR SHUWA YA JIKIN KUMA. WUYA A HANNUN SABUWA AN FASA FRIME A KAN ³AR SHUWA

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA TAKWAS

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

SADAUKAR.

NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFI ZUWA GAREKI MRS JAY

NAGODE SOSAI UBANGIJI ALLAH YA BAR ZUMUNCI SON SO

Assalamualaikum brkanku d warhaka hmmmm Wani kaya sai amale tohhh mata masu capacity matan kwarai

ga ramlex Mai kayan daa kayan buje akwae Package na uwargida

Package na amarya Package na mejego Tsimi baure

Tsimi magarya Hadin tattabara Hadin kaxa Hadin ciccibi Gumban Madara Gumban ridi

Gumban waken soya Karin dandano Xuman matsi

Manta uwa Hadin mallaka Hadin bita xaixai

Hadin tsuguno hmmmmm gareku mata akwae adashen gata duk sati 2k hadi Mai kyau xaayi muku duk Mai bukata ga no 07069722234 ko 07044503983 snnn dn Neman Karin bayani ku tuntubi wnnn layukan

"Ji kuke taratsatsa, take jini ya soma zuba kwalbar ta sameta a gefen kunnenta ta yankata sosai."

"""Mun shiga uku Maman Mardiyya zaki yi kisan kai"""

Cewar Maman Sa'idu. Ni kuwa dana ™yalla idanu na hango kwalbar koka kola ai saina surota da sauri.

"Da ³ar Shuwa tana tsaye tana cin Wamarar faWa, jini na zuba mata duk ya Sata wajen. Ganina da wannan kwalba yasa ta fice a guje."

"""Wallahi kuyi ta kanku ´an daba ne dukkansu"""

Matan ma™ota suka runtuma suka bita a guje matan gidanne kaWai suka tsaya sunata bani ha™uri.

"""Muna jiyota tana kiranki da boka kin asirce miji. Wannan ai ba ™aramar magana bace. Yanzu fa da mai gidan yananan sai kiga in ba wani ikon Allahn ba sai kiga ya kama. Kishiya duk yadda kuke burinta ta ganka a ™asa Allah dai ya kyauta"""

"Nan suka gama surutansu suka bamu waje. Aisha ce ta gyara wajen da jini ya Sata ina zaune ina huci. Aisha yaushe a gari zuwa ba sanarwa?"""

"""Wallahi sabida zaman shari'arku ta gobe nazo. To naje gida naji Maigogul yana cewa shi bazai je kotun ba. Rakiya dai tace saita je yana bazata ba. Har Hauwa dasu Layuza wai zasu je."""

Baki kawai na taSe ta kuntomun goyonta ta mi™o mun. Wuni guda muka yi dasu muna hirarmu duk da hankalina baya jikina ma sam wallahi. Saida suka ci abincin dare da na gama girkashi tun biyar na yamma.

Suna fita sai ga su Mardiyya Ramadan ya dawo dasu gida.

Ana magriba Babangida ya shigo da sallamarshi hakan yasa dole na mi™e nayi shigewata ciki. Ina jiyoshi yana cema Mardiyya ta zubo mishi abincin.

Ina goge kaya ya le™o.

"""Sabuwa meya haWaki da maman Fati ta kirani tace wai kin fasa mata bayan kunne saida taje asibiti?"" Kallonshi nayi bance uffan ba na maida hankalina kan gugar da nake yi."

"Shigowa yayi ya zauna a bakin gadona. ""Sabuwa!!"""

Ya faWa da wani irin taushin yaudara. Nasan yasan bazan amsaba shi yasa ma ya soma magana.

"""Ina dai ™ara ro™onki akan shari'arnan dai Sabuwa. Kima Allah Sabuwa ki janye wannan shari'ar Sabuwa ´a´anmu fa zamu jama abun faWe, ki sani wannan abun bazai taSa yi musu daWi ba. Yanzu Sabuwa zaki so ace a kanki Baba Malam ya rabu da Malama Babba?"

"To bari in ™ara faWa miki duk da nasan kin sani. Baba Malam cewa yayi muddin al™ali yasa na rabu dake, to Malama Babba tasa a ranta tamkar shine ya rabu da'ita. Igiyar data sar™e aurenku yace a haWe take, ba za'a tsinka"

taki nata ya zauna ba. Ko yau Winnan naje dan in gana da Baba Malam amman ya™i. Malama Babba tana cikin gida

"babu lafiya, ya hanani shiga cikin gidan ya haramtamun hakan. Yayu da ™anne duk muna cikin damuwa, ga tsinuwa a kaina Sabuwa. Dan Allah ki zauna kiyi tunani dare Waya kike dashi"""

"A sanyaye ya mi™e ya fice. Ni kuwa mamakine ya kamani. Ohh dama wannan dalilinne yasa Malama Babba take ganin zata siye mu dan ita ta cinma burinta ko, ni kuma ko oho. To ai kuwa saidai mu zama zawarawa dani da'ita shari'a babu gudu babu ja da baya wallahi."

Gugar ma sai naji na kasa tsulum na haye gado nayi rigingine inata tubka da warwara.

Wayewar gari:.

Yara na tafiya makaranta na shiga aikace_aikace shara wanke_wanke da wankin yara duk nayi. Na yi girki na ajjiye a kula dan bansan in mun tafi ™arfe nawa zamu dawo ba.

Tara na safe sai ga Adama da Rahama sun shigo. Babangida yana falo suka shigo.

"Yau dai ya amsa gaisuwarsu harma da tambayar yaransu. Dama a tsaye yake zai fita suna gama gaisawa ya fice. ""Sabuwa jiya fa su Sa'a sukai ayari suka je gida wajen Rakiya da Maigogul. Bakiga kaSakin arzkin da suka kai musu ba. Manja, maggi, shinkafa, taliya harda kuWi."

"Abinda suka tattaunane bamu sani ba jiya ina gidan, amman Maigogul ya kironi waje."" Jikina duk sai naji yayi tulus guiyoyina naji sun sare."

"Wayata ce ta shiga ™ara Barrister Ahmad Ahmad ne yake kirana. Jikina murus na Waga kana na saka a kunnena. ""Assalamu alaikum. Sabuwa ya kamata ace nan da tara da rabi ki ™araso kotu kafin a shiga zama mu Wan ™ara tattaunawa ko?"""

"To barister yanzu ganinan fitowa"""

Kashe wayar nayi na dubi su Adama nace.

"Bari in Wakko mayafina mu tafi lauyanane ya kirani"""

"Mayafi da jakata na shiga na Wakko muka haWu muka fice kai tsaye babbar kotun cikin gari muka nufa. Mun shiga kotun tara da arba'in. Da Babangida na soma haWa idanu suna zaune da abokanshi da wasu da ban sansu ba. Can gefe Malama Babba da Malama ™arama ne a zaune suma harabar kotu dai ta cika har ´an gidanmu ma naga sunzo harda Uzairu zuchiyata da Sama, Gaza dai ban ganshi ba."

KeSewa muka yi da lauyana.

"""Inaso ki nutsu kada ki ruWe duk abinda al™ali ya tambayeki ki nutsu ki amsa mishi a tsanake. Kuma amsa Waya ake bayarwa ko sau nawa za'a tambayeki kada ki canja daidai da kalma."""

Kai na Waga mishi kawai ni magana ma na kasa. Gashi kusan duk harabar kotun ni suke kallo face ragowar mutanen da suma muka shigo muka taddasu da basu sanni ba ban sansu ba.

"""Akwai wani sabon labarine?' E akwai barister"""

"Nan na zaiyana mishi yadda muka yi da Babangida jiya. Da labarin da su Adama suka kawo mun yanzu"""

"""Da kyau waWannan maganganun suna da matu™ar amfani zamu adanasu da akwai gaSar da zamu sokota. Yanzu muje an soma shiga kotu"""

"Wucewa yayi ya barni, ni kuma na koma wajensu Adama. ""Mu jenku Sabuwa anata shiga mu muna tsaye"""

Inji Adama kenan. Sai da su Babangida suka wuce mu kafin muka bi bayansu zuwa cikin kotun.

"Kotu dai a mugun cike take yau ma™il cikin ™an™anin lokaci kotun ta cika har babu wajen zama dole wasu suka tsaya daga waje, ciki harda Hamida da Amaryar Babangida ³ar Shuwa kam ita da uwarta summa riga mu shiga kunnenta naWe da audiga. Da halama ba shari'armu kaWai za'ayi ba. Dan duk inda na waiga sai inga bansan mutanen ba dan sun fimu yawa sosai."

"Karfe goma dot al™ali ya shigo ta wata karamar kofa. Duk muka zabura muka tashi, bamu zauna ba har saida al™ali ya zauna kana."""

Mai karanta ™arane ya mi™e da takadda a hannunshi ya soma jawabi kamar haka.

""", Ayau ashirin da biyu ga watan maris ne zamu saurari ™ara mai lamba Wari da shittin. ˜arar da Halima ta shigar tana tuhumar mijinta Baballe da handame mata kuWaWen gadonta tare da siyar mata da gidanta data gada."""

"Ashe ba shari'armu za'a soma ba. Kai kawai na girgiza maza da yawa son zuchiyoyinsu kawai suka sani."" Al™ali ya Wago kai yace."

"""Lauyan Halima in yana kusa ya gabatar da kanshi."" Wani lauyane ya mi™e tare da cewa."

"""Cike da girmawa ya mai Shari'a sunana Barrister Buhari Ladan nine lauyan wacce ta yi kara wato Halima. Nagode ya"

mai Shari'a.

Yana zama wani lauya ya mi™e shima yace

"""Sunana barrister Ibrahim Abubakar nine lauyan wanda ake ™ara wato Baballe. Nagode mai Shari'a."" Al™ali yace."

"""Ko lauyan wacce take ™ara yana da shimfiWa da zai ma kotu?"" A zabure da zafin nama ya tashi."

"""My lord Halima matar Baballe ce suna da yara huWu tare dukka mata. Mahaifinta ya rasune shekarar biyu da suka wuce ya rasu ya barma yaranshi su Halima kadarori da ruwan dukiya."

Jin™ai irin na mace akan mijinta da Halima ta nuna ma Baballe shine. Da aka raba aka bata gadonta na gida da ruwan kuWi miliyon bakwai. Kuskuren da tayi saita dam™ama Baballe miliyan biyar a hannunshi tace ya ja jari dasu. Kasancewar yana taya abokinshi saida motoci saita bashi shawarar me zai hana ya dinga bin abokin nashi zuwa kwatano suna Wakko mota tare tuwaris.

Akan wannan dalilin Halima ta ba Baballle kuWinta kuma ba kyauta ba da sharaWin zasu dinga raba duk wata riba da aka samu harya gama biyanta kuWinta.

"My lord kuWinta basu fito ba, a tsakaninta da Baballe babu mutuntawa daga karshe da kuWinta yayi aurenshi ya kama"

"™atotin gida ya saka amaryarshi, ya sai motar zagaya gari da'ita. Ita Halima da yaranta ya barsu a ™unci."

Hakan baiyi mishi ba kuma kwatsam Halima na zaune da yamma a gidanta ranar talata biyar ga wannan watan. Sai taga Baballe da dillalai masu duba gida.

Data tambayeshi lafiya saiya kada baki yace da'ita ya saida gidan harya amshe kuWinshi dan haka shi ya saketa ta tattare kayanta ta bar gidan.

"Akan wannan rashin adalcin da Baballe yayi ma Halima ta shigar dashi ™ara sabida ™ila ya amta da hukuma. Ina neman wannan kotu mai alfarma data dubi halima ta kwato mata hakkinta. Nagode mai Shari'a """

"Kai na girgiza ina kwatanta girman wautar da Halima tayi. Ko da yake bana kira hakan da wauta ba, ita a tunaninta shine mijinta shine makwafin ubanta a wannan lokacin, kuma dashi kaWai ta amince shi yasa ta dan™a mishi ragamar dukiyar tata. Shi kuma ya tata mata wannan rashin mutuncin."

Muryar alkaline ya katse mun tunanina.

"""Lauya mai kare wanda ake ™ara yana da abun cewa ne?"""

"""Ya mai girma mai Shari'a ina da ja akan dukkan abinda lauyan wacce tayi ™ara ya faWa a matsayin shinfiWa. Sannan ya kamata ya iya harshenshi wajen tabbatar da laifi akan wanda ake tuhuma, domin zargine ba tabbas"""

Al™ali yace.

"""Barister Buhari Ladan a kiyaye jingina laifi kai tsaye ba tare da an tabbatar ba."" Lauyan wanda ake ™ara yace."

"""My lord Halima matar Baballe bata ba Baballe ko sisin kwabonta ba. Asalima shi da kanshi ya ro™i ta taimaka mishi da jari ta™i. Kowa yasan Baballe mutum ne tsayayye ba mai macacciyar zuchiya ba. Babu ko sisin kwabon Halima a hannunshi. Batun gida da take ikrarin ya siyar ya saketa. Ya mai girma mai Shari'a itace ta siyar da abinta sabida kishin auren da mijinta yayi wai itama sai an kama mata hayar tabkeken gida kamar yadda ya kamama Amarya. A wannan gaSarne ya saketa kuma Allah ya baka yawan rai yanzu haka a cikin kotunnan ya dawo da matarshi."

"Nagode my lord """

"Halima dai sai share hawayenta take a kusa da juna muke inaji tana sambatu masu zafi da raWaWi. ""Bayan sauraren ™ara da wannan kotu tayi, da shimfiWa da lauyoyin Sangare biyu suka yi."

"Wannan kotu ta Wage ™ararnan zuwa ashirin da biyu ga wata na gaba. Tana bu™atar lauyoyi na Sangarorin da su kawo hujjojinsu masu ™arfi domin kotu taci gaba da saurarensu. Sai ™ara na gaba kuma"""

Mai karanto ™ara da ake kiranshi da turanci ko mene nadai kasa haWe turanci amman ai kun ganeshi ko? Saiya mi™e yace.

"""Sai ™ara mai lamba Wari da sittin da Waya wacce Sabuwa ta maka mijinta mai suna Babangida a kotu bisa tana neman ya saketa sakamakon kasa cika hakkokinta na Aure.'"

Al™ali yayi rubutu yayi rubutu kana yace.

"""Zamu je hutu na rabin awa in mun dawo saimu saurari ™aran."" Wannan guduma ya buga, yabi ta ™ofar baya ya fice."

"Nan take kotu ta Wauki hayaniya ³an uwan Halima suka shiga tsinema Baballe, da wannan muka runtuma zuwa wajen kotu. A wajenne muka tarar da Baba Malam, da su Rakiya da Maigogul suna zazzaune."

Gefe guda na zauna nayi tagumi. Baba Malam ne shi da Barister Ahmad Ahmad suka karaso inda nake. Gaishe da Baba Malam nayi da girmamawa ya amsa kamar kullum.

"""Sabuwa kar ki karaya naga halamun mutuwar jiki a tattare dake. Zan baki duk gudunmawar data dace."

Dangane da shirin da Babangida da gyatumarshi suke yi bazai yi tasiri ba da izinin Allah. Akan son zuchiyoyinsu da cimma manufofinsu kawai suke.

Kai na gyaWa nace.

"Allah ya bamu nasara Nagode sosai Baba Malam"" Maigogul ya karaso wajen a hargitse."

"""Lolo inaso zanyi magana dake ta ™arshe kafin ayi zaman kotunnan. Gara da Allah yasa kuka fito' Magana zanyi, muka haWa idanu da Baba Malam ya girgiza mun kai halamar kada in musa mishi. Jiki ba laka na mi™e nabi bayanshi har zuwa wajensu Rakiya da Hauwa, dasu Adama."

"""Lolo ashe ba zaki ji maganarmu ba kin dage sai kin tozarta uban ´a´anki ke akan daidai kike ne. Wanne irin iskancine baki tata a gabanmu ba. Kin dace kin auri malami Wan gidan malamai a kab ´an uwanki babu wacce baki fita dace ba. Ki duba irin mazan da suke aure daga ´an iska sai ´an abu ta kazan uba."

"Adama zawarci, Labbai zawarci, ™annenku duk zawarci Salaha, da A'isha, da Rahama ne fa kaWai suke zaman Aure. A"

Wakin Hauwa kuwa Layuza ce kaWai sai Qamriyya da aka kawo sadakinta za'ayi bikin.

"Dame kike so inji Lolo. So kike ki tozarta kanki ba wani abun ba. In Dai baki janye wannan Shari'ar ba, ki sani ko Babangida ya sakeki ba zaki zauna mun a gida ba saidai ki kama haya kamar yadda su Adama akace sun kama haya suna shirin tarewa. ni dai na faWa miki"""

Tunda maigogul ya soma maganarshi nayi ™uri ina kallon waje guda. Rakiya itama ta kama taita ragargazata da yi mun tone tonen abubbuwan da bana ko ™aunar tunosu ma.

"""Lolo kiyi ma kanki faWa ato. Duk wuyar gidan Babangida kinsan yafi gidan ubanki. Ba'a rageki da ci da sha ba, suturarnan kina dasu yaranki suna karatunsu."

"Duk abinda kika samu mu shi muka rasa muka zauna har saida aka koremu muka ha™ura. Yaranmu duk sun kama irin layinmu na bin maza baka isa ka hanasu ba sabida babu abinci, babu sutura yaya zasu yi suyi rayuwarma.'"

Inji Adama kenan. Ina tsaye nayi shiru har lokacin shiga kotu yayi. Bance musu kuci kanku ba har suka gama. Kai kawai nasa na wuce cikin kotu ko gani banayi sosai sabida jiri.

"Kotu ta cika da dangina dana Babangida, harma da ´an kallo waWanda ba'a fiye rasasu a kotu ba. ""Lauyoyin Sangare biyu su gabatar da kansu."

Barister Ahmad Ahmad ne ya tashi ya gabatar da kanshi. Kafin lauyan Babangida ya mi™e.

"""Sunana barrister Abubakar Shagari nine lauyan wanda ake ™ara tare dani akwai abokiiyar aikina wanda tare zamu yi aiki. Nagode my lord."""

"Yana zama abun mamaki sai wata lauya mace ta mi™e. ""Sunana barrister Asabe madaki. Nagode my lord."""

"Kai na gyaWa wato su Babangida a shirye suke lauyoyi har biyu? Allah ya bamu lafiya. ""Ko lauyan wacce tayi ™ara yana da shimfiWar da zaima kotu?"""

Gabana ya faWi ras. Barister Ahmad Ahmad ya mi™e yace.

"""My lord Sabuwa ta shigar da ™aran mijinta Babangida ne a bisa dalilai masu yawa kamar haka. Na farko Babangida baya ciyar da Sabuwa da ´a´anta."

"Na biyu baya biya ma yaranshi kuWin makaranta. Hatta da sutura baya musu, bai damu da lafiyarsu ba."

Uwa uba ya jingine Sabuwa tsawon lokaci baya sauke hakkin daya rataya a kanshi na mu'amalar Aure. Sai dai duk ranar da yaji sha'awarta yazo ya nemeta ta hanyar ™arfi.

Babangida yasha ya doki Sabuwa ya hakke mata tamkar namijin da ke ma yarinya fyaWe.

Daga baya ma ya ajjiyeta a gefe ta fita daga jerin matanshi a zahiri saidai a baWini matarshi ce. Cin mutunci da cin zarafin iyayenta babu wanda bayayi mata.

"Da wannan ne Sabuwa taga cutuwar tayi yawa take ro™on wannan kotu mai alfarma data kwato mata hakkinta. Sannan ko a musulunci Babangida bai sauke hakkin da Allah ya rataya mishi akan iyalinshi ba. Ba'a aure babu abubuwannan dana lissafo. Nagode my lord"""

Wasu siraran hawayene suka shiga aikin yawo a kumatukana. Barister Asabe madaki ce ta mi™e.

"""My lord duk abubbuwan da lauyan Sabuwa ya faWa zamu iya kiranshi a ™age. Sabida Babangida yana ciyar da Sabuwa yana shayar da'ita kuma yara suna zuwa makatanta. A yanzu haka ma suna makaranta."

Ya mai Shari'a Babangida yana neman hakkinshi a wajen Sabuwa sakamakon

Please Login or Register in order to submit comment