gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading ZINARIYA Satar Innocent By Aysha JB Chapter 2 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan na ji wani abu mai Wumi yana bin tsakanin cinyoyina. ""Na shiga uku na! Me zan gani? Wayyo Allah an yanka ni! Wayyo Innarmu an sayar miki da Zinariya."" Ihu nake kurmawa da iya ™arfi na, dukkaninsu suka shigo Wakin a rikice A'isha tana faWin. ""Ke dalla rufewa mutane baki duk kin cika mana kunne... ""An yanka mutum sannan a ce kar ya yi kuka? Na rantse da Allah sai an dawo min da jinin jikina tare da naman da aka Santala a cinyata, na rantse ba zan yarda da wannan muguntar da ake shirin yi mini ba."" Na ™arasa maganar ina hararan su tare da murguWa baki. ""Iko sai lillahi, ke kuma Salima wacce aka Wauko miki kenan? Allah shi kyauta."" Cewar Aunty B, Salima da shigowarta kenan ta ce. ""Ba naman cinya ba, kanki za a cire mayya da idanuwa kamar na mujiya, yarinya duk ta ishi mutane, ni da na san haka kike da hauka ina zan Wauke ki aiki? Ai wallahi ki sauko ki zo ki wuce dan daga nan za a mayar da ke inda aka Wauko"

"ki."""

"""Na rantse da Allah babu me ™arfin halin da ya isa ya cire mini kai, kuma sai an biya ni kuWin albashina na wannan watan dan Innata ta ce ba a tura musu kuWi ba. Ko a ba ni kud ina ko kuma wallahi na hana mutum sukuni."" Tsaki ta yi tare da barin Wakin, Aunty B, ta ce. ""Ke da'alla bar shashancin nan, girma ne ya zo miki... ""Girma? Wane irin girma ne bayan kuma wannan girman da nake da shi? Ke ki kalleni Sakutuwa na ciko ta ko'ina... Tagumi Aunty B ta yi tana kallon Zinariya, ga abin dariya amma takaicin halinta ya hanata darawa. Hannun Zinariya ta kama suka shiga toilet ta ba ta auduga tare da nuna mata yadda za ta yi, da yatsu biyu ta Waga audugar tana mishi kallon mamaki. ""Eyye! Iko sai Rabbu! Wannan bala'in kuma daga ina? Ni ce zan saka wannan a jikina kalan aje a mini satan kayan hanjina? O'o wallahi ba ni iya wa da wannan abar."" Ri™e da haSa Aunty B ta ce. ""In ba ki saka ba haka za ki yi ta yoyo... ""Yo me ye a"

"ciki? Ba gwara jinin ya yoye ba da in tara da wannan abar a zo a yi mini warwason kayan hanji."""

"""Ke fa da kanki za ki yi floshing Win shi idan kin gama.. ""Fulo me? Eh lallai yadda za a ji daWin kwashe 'yan hanjin kenan."" Da Aunty B, ta ga ji da shirmen Zinariya fita ta yi daga toilet Win. ""Ni na rantse ba zan saka wannan abar ba."" Ta ™arasa maganar tare da yin wurgi da shi."

"Šankwalin kanta ta cire tare da rabawa biyu ta cusa Waya tare da mayar da Wayan kanta, tana murguWe-murguWen baki ta fito. Ko da ta yi arba da abinci ba ta tsaya tambayar na waye ba ta Wauka ta fara ci, Aunty B, ta mi™o mata magani tana gamawa suka bar asibitin zuwa masaukinsu. Da yamma suka Wunguma zuwa asibitin da za a yi wa Salima aiki inda likita ya yi mata gwaje-gwaje tare da Wora ta a kan maganin kafin nan da kwana biyar za a yi mata aiki. Ita dai Zinariya an barta da yatsine-yatsine saboda warin asibitin ya ishe hancinta. Da lokacin sallar magariba ta yi ta je ta yi za ta yi sallah, Aunty B ta ce. ""Babu fa halin yin sallah 'yar nan."" She™e™e Zinariya ta kalleta tare da haWa kai da wuya tana faWin.  Kamar ya babu halin yin sallah? Kafurta ni kike son yi?"" Aunty B ta ce. ""Ai ba maraba, duk wanda yake cikin wannan yanayin"

"bambancin shi da kafiri kaWan ne... ""Yanzu kina nufin na fita daga musulunci ko?"""

"""Shakka babu."" Ri™e haSa Zinariya ta yi tana faWin. ""TaSWijam! Lallai sai na yi shari'a da duk wanda ya yanka min cinya."" Zama ta yi shuru tare da rafka tagumi da hannuwa biyu tana tunanin hanyar da za ta bi don ta koma gida, ita gaskiya ba za ta iya ci-gaba da zaman wannan wurin da aka kawota ba. Tana zaune tana mita cikin ranta har ta fara barci a zaune, Aunty B ce ta tashe ta ganin yadda take gyangyaWi. Bayan kwana biyu ta samu tsarki a cewarta ba za ta fara sallah ba sai ta yi wankan shiga musulunci, haka kuwa aka yi domin sai da ta yi wankan kafin ta fara sallah. Yanzu ta tsiri fita farfajiyar hotel Win ne don ta ce ba ta iya zaman wuri Waya, saboda ba™in hali irin na madan Salima haka take saka ta wanke musu toilet da gyaran Waki bayan kuma"

"akwai ma'aikatan da suke gyarawa, amma haka ta hana su ta ce ita tana da mai aikinta."

"""Dan ba™in hali a yi ta saka mutum aiki bayan ga su nan da ma'aikatan su, ko abinci ta ci sai dai ta saka mutum ya zo ya kwashe kwanuka ya fito da shi."" Zinariya ke magana tana tafiya har ta fito wajen hotel Win, lokacin ™arfe tara na dare ta tsaya gaban wani shago tare da harWe hannuwa"

tana kallon yanda mutane ke ta harkokinsu ba mai shiga sabgar wani.

"Gefen shagon ta je ta tsaya tana kallon wuta mai launi da ke juyawa yana haskawa ilahirin kayan shagon, tsawon minti uku tana nan tsaye ba ta ankare ba sai ji ta yi an fisgota da ™arfi tare da toshe mata baki aka tura ta cikin mota, mutsu-mutsu take yi tana ™o™arin ™wacewa daga ri™on da aka yi mata amma ina, ji ta yi an sha™a mata abu a hanci wanda tun da ta sha™a ba ta sake sanin inda kanta yake ba sai bayan kwana uku da aka watsa mata ruwa masu sanyi ta buWe idanuwa a firgice da ihu, na tsinci kaina cikin wani Waki mai girma da faWin gaske. A lokacin da na yi arba da yara tsarata da waWanda ba su kaini ba cikin mummunar shiga hankali na ya yi mugun tashi, ina kallon yanda ake yage kayan jikinsu ana duba halittar su, nan na ji cikina ya sake Wurar ruwa, ""Shi kenan ta faru ta ™are! Ta tabbata dai wannan matar sayar da ni ta yi, wayyo Innata..."" GabaWaya sai suka juyo suna kallona, matar da na ga tana duba ™irjin yaran na ga ta nufo inda nake tana Waga hannu alamar me ya faru? Kafin ta fara magana da harshen da ba zan iya cewa ga abin da na tsinta cikin maganganunta ba. Mannewa na yi jikin bango yayin da"

jikina Wauki mugun kakkarwa.

"""Innalillahi ina aka kawo ni? Ina ne nan?"" Tambayar da nake ta yi kenan cikin ihu da hayagaga, amma duk cikin waWannan matan babu wacce ta yi zarrar ba ni amsar da nake son ji, ita tana nan tana wasu yarukan da ban gane kansu ba, yayin da ni ma nake yaren da na fi ™warewa"

"akanta, ina kallon yanda ake yi wa yara 'yan ™ananu yara alluran da ban san ko na mene ne ba."

"Širka-Wirkan mata ne guda biyar masu ji da ™arfi suke finciko yara tare da danna musu allurori, idan kuwa ka ™i ba da haWin kai da duka ake haWawa, yau ni na ga bala in da ban taSa gani ba tun da nake a rayuwata. Ina kallo da zaran an gama tsikara musu allura zubewa suke yi a ™asa suna ihu da birgima wanda daga ™arshe sai su Singire da barci daga haka sai a Wauki yaran a fita da su zuwa wani Waki inda nan ne za a kula da su a dinga ba su cimar da zai ™ara musu lafiya ya sake fitowa da halittar jikinsu. Cikin sati biyu, kafin a fita da su zuwa wani gida inda a nan ne za a"

baje kolinsu kowa ya zaSi wacce ranshi ya yi masa.

"Cewar matashiyar da ke zaune a gefe na, cike da razani mai haWe da Wumbin mamaki nake kallonta sannan na matso kusa da ita ina faWin. ""Ke Bahaushiya ce?"" Ture ni ta yi da hannunta tare ta sunkuyar da kanta ™asa tana faWin. ""Idan kina son kanki da lafiya karki yarda ki zo kusa da 'yar'uwarki ko ki nuna jin ™ai da tausayinki gare ta."" Idan kuwa aka fahimci mun san yaren juna ko wata sha™uwa ta fara shiga tsakaninmu shi ma wannan wani hukunci ne mai zaman kansa. Dan haka za a wurga ki a Wakin gardawan maza su yi miki wula™ancin da sai kin kai wata kina jinyar kanki, gwara ki ci gaba da yi musu yaren da kika iya kafin ki fahimci nasu yaren."" Shuru na yi ina juya wannan mugun lamarin cikin zuciyata. Sai da mata suka fita kafin ta Wago kai, nan na ™are mata kallo, ita ma dai yarinya ce amma za ta kai 19 zuwa 20. Ga ta fara tass"

"kyakkyawar Bafulata, saSanin ni da nake nan ba™a."

"""Yau kwananki biyar kina cikin barcin da aka saka ki, ke kuwa wane ganganci ne ya kawo ki wannan duniyar da take cike da zalunci haWe da son zuciya? Kin san rashin imanin da ake nunawa 'ya'ya mata kuwa musamman mu da muka fito daga Nigeria? Me ya kawo ki Japan har da za ki faWa harkan karuwanci... ""Ya Subhanallah! Karuwanci? Ni da nake Egypt me ya kuma nake yi a nan? Ni fa daga tsayawa a bakin shago na ji an toshe min baki tare da fisgoni ban"

"sake fahimtar komai ba sai yanzu da na buWe idanuwana na tsince ni a nan."""

"Wani irin dariya ta yi tare da faWin. ""Sayar da ke fa aka yi, kamar yadda ake safara daga Nigeria haka ke ma aka yi miki... ""Ba shakka wannan muguwar matar za ta aikata kamar yanda ta"

"faWa."""

"""Wace ce?"""

"""Madam Salima, matar da nake yi wa aiki, mun zo ne da sunan za ta karSi magani ne ko za a mata aiki ne ni ban sani ba, wato shi ne wannan matar za ta yi safarata zuwa nan, shi ne za ta buga mini tambarin da har na mutu na bar wa dangina da zuri'ata mummunar tabon da ba zai"

"taSa goguwa ba kenan? Wai mai ya sa imani ya yi wa mutane ™aranci ne?"""

"""Ba ki da iyayen da za su tsaya miki ne?"""

"""Ni da nake 'yar talaka, daga dangin uwa har na uba, Innarmu ke Wawainiya da mu domin babanmu ba ruwan shi da sauke nauyin iyali, Innarmu ke fita ta nemo mana abin da za mu ci a haka ta saka mu makaranta mu huWu, kin san hannu Waya ba ya Waukar jinka, dole dukanmu karatun ya tsaya daga Firamare, yayuna mata kowa na neman kuWi don a taru a ruwafa juna asiri wannan dalilin ya sa ni ma na fara aiki fa duk don abin ya yi wa Innarmu sau™i, Innarmu na son mu, haka ma babanmu ba ya ™aunar wani abu ya taSa mu amma hakan fa ba shi zai sa ya saya miki ko da takalmi ba ne idan sallah ta zo, duk ya bar Wawainiyar kan Innarmu. Ban san"

"halin da za su shiga ba idan suka fahimci ba na nan."""

"Numfasawa na yi kafin na ci gaba da faWin. ""Babanmu ba zai taSa barin madam Salima ba"

"muddin ya ji labarin ta sayar da ni, domin kuwa za ta sha terere dan duk inda ya zauna sai ya yi"

"wannan batun."""

"Kallon matashiyar na yi jin ta tuntsure da dariya. ""Ba fa zai iya shari'a da masu kuWin nan ba,"

™arshe ma za ta iya cewa ita ba ta ma san wata mai aiki ba ke dai ki yi addu'ar Allah ya fitar da ke.

Littafin Zinariya na kuWi ne akan ¦ 500. Za ku tuntuSi wannan Number ta WhatsApp domin mallakar naku.

09079740079

Maman Faruk.

"[30/11, 3:49 pm] :5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ 5Ø Ü5ØÜ;: *...ZINARIYA* Romantic "

®

AYSHA JB

Farin Jini Writer's Asso..

7&8

"Gyara zama na yi ina kallonta sanan na ce. ""To ke yaya sunanki? Me ya kawo ki nan? Su kuwa waWannan azzaluman babu hukumar da za ta dakatar da su ne ko ta kama su? Oh ni na shiga uku, shi kenan ba zan sake ganin Innarmu da babanmu ba? Allah sarki yaya Fadila, Allah sarki yaya Radiya shi kenan an Wauke muku 'yar auta... ""Kina da abin dariya wallahi, bari na ba ki labarin wannan ™asar da ta yi ™aurin suna. A Japan, ana fataucin mutane ne da nufin yin lalata da bautar da su kamar bayi a ™asar, Japan ™asa ce ta asali, wadda ake yawan ziyarta, haka kuma ™asa ce da ake safarar 'yammata musamman masu ™ananan shekaru don mai da su karuwai a yi lalata da su ba bisa son ran su ba."

"'Yan ™asar Japan, musamman mata da ake yin safarar su ta hanyar mai da su karuwai da ™arfi da yaji a cikin Japan da kuma zuwa wasu ™ananan ™asashen waje. Ana safarar waWanda suke daga ™asashen waje zuwa cikin ™asar japan. Yara kanana, da mutanen da suka fito daga dangi marasa ™arfi wato waWanda talauci ya musu katutu sun fi fuskantar matsalar fatauci. Ana yaudarar waWanda aka yi fataucinsu da manufar kasuwanci, ana yi musu barazana da tilasta musu yin karuwanci. Masu safarar mutane"

"waWanda suka kamasu suna ™wace fasfo Winsu da takardun banki da duk wasu muhimman takardun da suka shafe su, ana yawan Waura musu basussuka don su biya su fanshi kansu daga halin da suke ciki. Ana raunata su idan suka ™i amincewa, kina kallon yanda ake dukan"

"waWannan yaran, to haka suma manyan ake musu, sannan ana yi musu barazanar kisa kuma"

"da yawa daga cikin waWanda aka yi safarar su suna kamuwa da cututtukan da ake Wauka ta hanyar jima'i, da fyaWe, kuma suna rayuwa a cikin yanayi mara kyau rayuwar ™unci da wahalhalu. Wasu idan suka samu ceto ma'ana idan suka tsira suka gudu suna fuskantar wariya, daga jama'a a dinga ™yamar su. A irin wannan yanayin ba™inciki kan sa har suna yun™urin kashe kansu. Akan Wauke su hotuna a lokacin da suke tsirara sai a watsa hotuna a yanar gizo don muzanta su"". Ri™e haSa Zinariya ta yi tana faWin. ""Bala'i! Lallai ana shege a duniya, abin da muke ji a"

"labarai yau dai gamu cikin yanayin, to su kuma masu fataucin daga ina suke?"""

""" Masu fataucin maza da mata a Japan sun fito ne daga wurare dabn-daban. Masu safarar mutane galibin su membobi ne na ™ungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, suna haWuwa ne su cure waje Waya don samun sau™i wajen aikata miyagun Laifuka. suna da ala™a da ™ungiyoyi da dama, suna da Waurin gidi daga fannin manya 'yan ™asan, domin suna ba su kaso mai tsoka daga abin da suke samu. Wannan dalilin ya sa suke gudanar da harkokinsu hankali kwance ba su da haufin komai domin babu wanda zai yi musu shamaki ko karan-tsaye bisa kasuwancinsu. Hatta gwamnatin ™asar muryarta ba ta isa ta yi amo ba... ""To amma ke mai ya fito da ke? Ki ba"

"ni labarin ki, yaya sunanki?"""

"""Hinduu, sanin labari na kuma ba zai ™are ki da komai ba. Don gudu na yi daga gida na shigo duniya saboda za a tilasta ni yin rayuwa da wanda ba shi ne zaSin zuciyata ba, ba nan na fara zama ba. Sai da na yi rayuwa a Thailand kafin ni ma aka sayo ni zuwa nan."" Jinjina lamarin"

"Zinariya ta yi cikin zuciyarta kana ta ce. ""Kuma kema an yi miki allurar ne?"""

"""Ba ki ji na ce miki sai da na fara rayuwa a Thailand kafin na zo nan ba? Ai tun a can an riga da an yi mini komai, har ciki na yi aka cire, daga ™arshe aka yi mini tsarin iyali.. ""Aka cire ciki kuma? Ta yaya? Mene ne kuma tsarin iyali?"" Zinariya ta faWa cike da zallar yarinta. ""Ina nufin ni na yi mu'amula da maza ba so Waya ba ba so biyu ba har na samu ciki na haihuwa, sai aka zubar da shi, aka kuma yi mini allurar da zai hanani Waukar wani cikin."" Shuru Zinariya ta yi domin duk ba ta fahimci abin da Hindu ke magana akai ba. ""Aka yi miki ciki haka na haihuwar yarinya, kuma se aka zubar da cikin?"" Ta faWa tana dafe cikinta tare da Wago hannu tana kwatanta yadda ciki yake idan ya yi girma ya fito. ""Oh ni Zinariya ko yaya ake yin cikin oho"" Kallon Zinariya Hinduu ta yi sosai domin ta lura har yanzu ba ta ma gane kan maganar da take mata ba. ""Ba ki san yanda mata da miji ke kwanciyar aure ba?"" Girgiza kai Zinariya ta yi alamar a'a, ""Kin je islamiyya kuwa?"" Zinariya ta ce. ""Wannan ai tambayar raini hankali ce, ni tun ina shekara sha"

"biyu na yi saukar allo."" Dariya Hindu ta yi sannan ta ce mata. ""Okay."""

"Zinariya ta ce. ""Yawwa na tuna."""

"Hinduu ta ce mata. ""Me kika tuna?"" Zinariya ta ce. ""Kin ce an miki allura a can Telan yake ko"

"ina? Kuma nan Win ma sai an yi miki wani allura?"""

"""Duk cikin maganar iya abin da kanki ya iya ri™ewa kenan?"" GyaWa mata kai na yi, ""Ai nan za su duba kafin su yi min. Idan suka fahimci ni ba cikakkiyar budurwa ba ce, ma'ana na yi sex da"

"wani na miji, za su kaini Wakin 'yanci ne kawai a yi mini gyaran jiki sai su fita da ni zuwa inda za"

"a zo a Wauke ni... ""Me ye six kuma? Idan aka Wauke ki ina za a kaiki?"""

"Hinduu ta fahimci Zinariya ba ta san ma komai ba a harkar, wannan dalilin ya sa ta yi shuru zuciyarta cike da tausayin Zinariya, dan ta san muddin ta shiga hannun mazan garin Japan fasa"

"ta za su yi, ba su iya bin mace da sau™i ba."

"""Kin yi shuru..."

"""Shh! Yanzu za a kawo mana abinci."" Aikuwa tana rufe baki sai ga shi an buWe ™ofar tare da shigowa da abinci, aka ajiye ma kowa na shi. Ga dai abinci lafiyayye amma ko burge ni bai yi ba. ""Ki dai ci abinci, dan in kika ™i ci haka za ki zauna da yunwa."" Cewar Hinduu, kaWan na"

tsakuri abincin na ture sauran.

"Na so mu ci gaba da hira amma sai Hinduu ta ce barci za ta yi, haka na ™yale ta, washegari ma haka wannan gardawan matan suka zo suka Wibi yara kusan goma dan gaskiya muna da yawa. Ranar da na cika sati cikin yaran da aka Wiba har da ni, lokacin da aka zo Waukar sunana zuciyata ta tsinke, hankalina ya yi mummunar tashi domin na tsani yanda suke yage rigar mutum suna duba ™irjinshi, cike da tsoron na kalli Hindu kafin a zo Wauka na murya na rawa na"

"ce. ""Na shiga uku ina za a kaini?"""

"""Za ki sha™i iskar 'yanci mana, ke kam ki kwantar da hankali za mu haWe ne in sha Allahu da zarar na fito."" Daga haka Hinduu ta Wauke kai ba ta sake min magana ba. Da suka zo Waukana na fara turjewa aikuwa matar ta Waga hannu da niyyar kwaWa mini mari, nan na tsura mata idanuwa tare da tamke fuskata na tsuke baki ina jiran saukar mari, amma sai na ga saSanin haka, cikin zuciyata na ce wallahi da kin mare ni kin ga yanda ake hauka. Yage himar Win jikina aka yi wanda tun da na zo da shi nake nanu™e a jikina, ko wanka na yi ba na yarda na cire shi. Ina ji ina gani aka barke rigar jikina, nan suka ga ™irjin sulum ba komai sai Wan kan da ya fara tasowa. Kallon juna suka yi suna yare ga dukkan alamu sun yi mamakin ganin babu komai a ™irjin. Haka suka danna mini allura har guda biyu, na daWe ina jijjiga tare da jin gaSSai na suna sakewa kamar wanda ake kwance mini su kafin wani wani masifaffen barci ya yi awon gaba da ni. Sai tsakiyar dare sosai na farka nan na tsinci kaina cikin wani ™ayataccen Waki inda na ga 'yammata bila adadin suna ta harkokinsu, ina ta kallonsu ganin yadda suke Waure da Wan ™yallen ™irjinsu yayin da suke sanye da wani Wan mitsitsin siketi, tagumi na yi ina kallon galewar rayuwa dan wallahi ko gama saukowa cinyarsu siketin ba ta yi ba. Wani irin lafiyayyen abinci aka kawo min wanda tun da nake ban taSa ganin irin shi ba, nutsuwa na yi na ci sosai ina karon 'yammatan Wakin, wata mata ce ta zo ta ri™e hannuna zuwa toilet nan aka shiga wanke ni ba ji ba gani, kusan sati biyu ana min wani irin masifaffen gyaran jiki tare da wanke ni da ruwan turaruka. Gashi na da yake tufke aka warware shi, nan shi ma aka gyara min shi duk da ba wani yawa ne da shi ba amma yana da tsayi dan ya sauko har kafaWata. ˜irjina kuwa saboda fitinar shi da aka yi da shafe-shafen mayuka da magungunan dole ya fara fitowa har kana iya ganin"

shi ta cikin riga saSanin da ba a iya ganin komai.

"Ni kaina ™aunar kaina nake yi wallahi ganin yanda na yi masifar kyau, jikina har wani sulSi yake"

"yi, sai kallon kaina nake ina sake latsa fatata da ta murje ta yi fresh sai ka ce ba™ar baturiya. (Ni kuwa na ce su Zinariya an samu na yi, sai a yi ta latsa jiki) Da dare ina zaune bayan na gama cin abinci na Wauki wani riga mai Wan mutunci daga cikin kayan da aka ba ni na sakawa ina ™o™arin sakawa sai ga matar da take yi mini gyaran jiki ta shigo ta karSe rigar tare da mi™o min wasu kaya, buWe kayan na yi na kalla tare da kallonta. ""Me ye wannan? Me zan yi da ita?"" Da ta fahimci abin da nake faWa sai ta karSi kayan tana gwada mini yanda zan saka. Innalillahi na ce ganin irin mugun kayan da ke jikina wanda ba shi da maraba da gidan sauro. Tsirara ziryan, dafe ™irji na yi tare da kallon madubi ina faWin. ""Na shiga uku ni Zinariya, yau kuma haka na zama?"" Jan hannuna matar ta yi zuwa waje inda aka saka ni cikin wata mota."

**** Egypt.

"Neman duniyar nan a yi wa Zinariya amma ina, babu ita babu labarinta. Hankalin Salima ya tashi sosai amma da ta tuna Zinariyar ba zaman Egypt Win take so ba sai ta lauya zancen tare da faWin dama can ba son zaman take yi ba shi ya sa ta gudu. Da wannan kalaman ta share batun Zinariya. Aunty B kuwa cewa ta yi. ""Amma Salima sai yau na sake tabbatar da ba ki da hankali da imani, ta yaya 'yar mutane za ta Sata sannan ki zauna hankalin ki kwance? Me za ki cewa iyayenta?"" Salima ta ce. ""Me kuwa zan ce musu wanda ya wuce na faWa musu 'yar su guduwa ta yi, ni na Satar da ita? Dan Allah Aunty B ki ™yale ni da wannan maganar."" Mamaki ya cika Aunty B ta kasa yin wata magana, daga ™arshe haka suka dawo bayan gama aikin da za a"

yi wa Salima.

"Dawowarta ba jimawa ta sa aka kawo mata 'yar aiki, amma ko wata ba a rufe ba ta kore ta saboda rashin kamun kan yarinyar, a haka ta dinga canja masu aiki ta kasa samun ™wa™™warar da za ta mata aiki ba tare da sun samu saSani ba. Wani lokaci ta kan tuna Zinariya, duk da tana shiririta amma a hakan take mata aikin da ranta yake so, sai da babu ita take jin takaici, da zarar kuma ta tuna irin rashin kunyar da ta dinga yi musu sai ta ji gabaWaya haushinta ya rufe ta, take kuma take kore tunanin Zinariyar daga zuciyarta."

****

"Uwaisu Sadi, wanda ake yi wa la™abi da Malam Uwaisu haifaffen garin al™aleri ne da ke jihar Bauchi, wanda tun fitowarshi cin rani bai sake waiwayar gida ba, yana da ilimin addini da na zamani wannan dalilin ya sa ake kiran shi malam Uwaisu kasancewar wani lokaci har bugun ™asa yake yi kafin ya yi aure, bayan auren shi da Mardiyya sai ya daina da ya fahimci ba ta son sana'ar. Nan ya shiga 'yan buge-buge yana samo musu abin da za su rufawa juna asiri kasancewar ita ma iyayenta ba masu ™arfi ba ne, amma duk da haka suna tallafa mata musamman da suka lura

Please Login or Register in order to submit comment