gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading ZINARIYA Satar Innocent By Aysha JB Chapter 1 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþ"[30/11,2025. 3:49 pm] :5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ 5Ø Ü5ØÜ;: *...ZINARIYA*"

_Romantic _

®

AYSHA JB

Farin Jini Writer's Asso..

1&2.

"Alhaji Bilyaminu Saifullahi Pawa, haifaffen garin Lafia Nasarawa stste ne, amma asalinsa fulanin Yola ne sananne Wan kasuwa mai kuWi, inda ya ri™e mu™amai da dama, kuma ga shi sarkin Pawa, ya yi tashen arziki a lokacin da duniya ke kwance lafiya, marigayi Bilyaminu yana da mata biyu da tarin 'ya'ya, sai dai du ka yaran na shi mata ne, yayin da Wakin uwargida Binta ke da yara tara, amariya Fatu tana da bakwai, gidan shi babban gida ne inda yake Wauke da da™una, da dama. Duka matan na shi sun yi aikin Hajji da Umrah shi ya sa yaran suke kiran su da hajiyoyi, inda suke kiran Binta da Hajiya Babba, Fatu kuma Hajiya ™arama. Akwai zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin su, sai da ku san Wan'adam da ajizanci, sai da tsufa ya fara cimma Alhaji Bilyaminu kafin Allah ya azurta shi da samun ™aruwa ta gefen Hajiya ™arama a lokacin har kunya take ji a ga ciki a jikinta, domin yawancin 'ya'yansu duk sun aurar da su. Sai dai duk nu™u- nu™unta sai da aka fahimci tana da ciki inda ya dinga tasbihi ga Allah yana ta addu'ar Allah Ya sa namiji ne za ta haifa. Yayin da Hajiya Babba take jin ba™inciki sai dai ba ta nuna a fili ba ta bar shi cikin zuciyarta. Lokacin da Hajiya ™arama ta haihu kuwa Alhaji Bilyaminu ya cika da murna wanda ya gaza Soye shi. Tsananin murnan ya sa ya raWa wa yaron sunan mahaifinshi Saifullahi, karku tona zuciyar Hajiya Babba ku ga irin ba™incikin da take ji idan ta buWe ido ta kalli Saifullahi wanda ba ta ™i a ce mata ya mutu ba, Saifullahi ya ta so cikin gatan iyaye da 'yan'uwanshi mata musamman ma da ya kasance yaro mai ladabi da biyayya. Ya yi karatu daga boko har mahamadiya yana da shekara sha tara Allah ya yi wa Alhaji Bilyaminu rasuwa bayan ya sha fama da jinya. Saifullahi ya ji mutuwar mahaifinshi sosai kasancewar sun sha™u da junansu hatta abinci Saifullahi ne yake ba wa mahaifinshi a lokacin da bai da lafiya, shi ya sa ya yi kuka sosai. A hankali rayuwa ta dinga tafiya inda ya kammala karatunshi ya yi hidima wa ™asa (NYSC) bayan ya kammala ne ya haWu da Salima Nasir mahaifinta shi ma babban attajiri ne, inda soyayya ta ™ullu tsakaninsu yayin da mahaifin Salima ya kasance Wan'uwa ne ga Hajiya Babba, babu Sata lokaci suka yi aure, auren su ba da jimawa ba Saifullahi ya samu aiki a Abuja inda suka tattara shi da matar shi suka koma sai dai tsawon lokaci Salima ko Satan wata ba ta taSa yi ba, tun abin ba ya damun Saifullahi har Salima ta fahimci rashin haihuwar nata na damun Saifullahi ga 'yan'uwanshi da suka fara janye jikinsu daga nata suna zancen Saifullahi ya ™ara aure tun da likitoci sun tabbatar da matsalar da ga ita Salimar ce ba daga gare shi ba, shi kuma ya nuna musu bai da sha'awar ™arin aure domin matar shi ba ta rage shi da komai ba. Ita kuwa Salima tana jin zafin duk wanda ya ce wa Saifullahi ya ™ara aure domin ba™ar kishi ne da ita, wannan dalilin ya sa suke samun saSani da dangin mijin nata. Ko 'yan aikinta ba ta yarda su zo inda take ba muddin Saifullahi na gida, wannan dalilin ya sa ta kasa zama da ™wa™™warar mai aiki guda Waya."

** ** **

"Dum!Dum!!Dum!!! Haka na ji zuciyata na ba da sauti, cikin sauri na mi™e daga kwancen da nake tare da kunna hasken Wakin na ™arasa bakin ™ofar ina faWin. ""Waye?"" Tsit na ji, shahadar kuWa na yi na buWe ™ofar a tsorace ina kalle-kalle nan na ga babu kowa, shuru na yi ina jin yadda zuciyata ke tsananta bugawa. Yau kwanana goma sha takwas da fara aiki a gidan wanda kusan kullum sai an zo an buga mini ™ofa, da na buWe sai na ga babu kowa, na rasa me ke shirin faruwa da ni, kullum cikin zulumi nake da zaran dare ya yi, na jima a tsaye kafin na koma cikin Wakin sannan na rufe ™ofar na yi addu'a na kwanta. Washegari kamar yadda na sama tashi haka na fito bakwai saura na share farfajiyar gidan na yi moping baranta na goge duk inda na saba gogewa kafin na nufi hanyar cikin domin shi ne hanyar da zai sada ni da falon ™asa, sai da na share falon tare da gyara ges room na wanke toilet Win sannan na haura sama na shiga gyaran main falon tare da gyara gard room da store Win da suke ajiye kayan sakawa, tara saura na kammala komai sannan na sauko na zauna a kujerar da ke jikin window kitchen ina jiran fitowar Hajiyar gidan wanda sai tara da rabi take saukowa. Don yi wa maigidanta abin kari, ina nan zaune na ji wani irin ™amshi na bugi hancina tare da jin motsin kwanuka alamu dai tana cikin kitchen Win. ""Kee...! Ina jin takaicin wannan suna da madam Wina take kira na da shi, haushi ya sa na™i amsa mata na yi tsaki cikin zuciyata tare da yi mata banza. ""Waye a nan?"" Mi™ewa na yi na shiga kitchen Win"

"ina faWin. ""Barka da safiya."""

"Kallona ta yi tare da faWin ""Koma ki saka hijabinki, na faWa miki ki daina yawo haka bana so masu aiki suna zama ba tare da sun lulluSe jikinsu ba."" Ta faWa haka ba tare da ta amsa gaisuwar da nake mata ba, fita na yi daga kitchen Win na je na Wauki hijabi ina ta mita cikin raina dan na lura wannan matar mugun rainin hankali gare ta, ga kitchen Win da bala'i zafi sannan a saka mutum saka hijabi saboda kawai mijinta na nan mutumin da ko gaisuwa ma bai taSa haWa ni da shi ba, to yaushe ma na taSa ganin shi da zan gaishe shi. Ina shigowa ta ce in fito mata da ™ullun ™osai da ke cikin firiza, sai da na buga shi ya sake jikinshi kafin na saka maggi na goga albasa a ciki, ruwan kunu na ta ce na saka a buta, tana suya har ruwan ya tafasa kafin ta ce na zo na duba ™osan ita kuma ta dama kunun, ina kallon yadda take sauri jin mijinta na gyaran murya alamar ya sauko ™asa, kullum a latti take saukowa ta san mijinta na fita da wuri ba za ta fito a yi komai cikin nutsuwa ba sai lokaci ya ™ure za ta zo tana ce wa mutum ya yi sauri. Sai da ta zuba kunun ta ce in zo in haWa tire, haka na Wauko kofuna na Wauraye su sannan na goge kafin na jera a tire tare da tea spoon, da sugar, ""Mi™o min kula."" Da sauri na fito da kula na goge sannan na mi™a mata, tire Win kunnu ta Wauka ta fita da shi, gass Win na kashe sannan na Wauki na ™osan na bi bayanta. ""Ina za ki je?"" Ta faWa cikin rashin walwala tare da karSe tiren a hannuna. ""Ki je sama ki gyara min Waki."" To kawai na ce mata sannan na koma kitchen sai da na gyara inda aka Sata sannan na Wauki sauran abin da aka rage min na je na karya, ina gamawa na Wau tsintsiya da faka, na haWa ruwan moping na haura Wakinta. sai da na yi goge na gyara gado kafin na yi shara da moping na wanke toilet sannan na fito ina mayar da numfashi. Zan wuce in ajiye kayan moping Win na ji ta ce ""Kee.."" Daga falon mijinta, Wan dakatawa na yi ba tare da na amsa ba, ""Ya sunanki ma?"" Kallonta na yi cikin jin haushi domin kullum sai ta tambaye ni sunana. ""Zinariya."" Kallona ta yi sosai sannan ta ce. ""Ki zo ki kwashe kwanukan nan ki wanke su."" Daga haka ta fito daga falon ta haura Wakinta. Aikin fa kenan kullum babu hutu, sai da na gyara falon sannan na kwashe kwanukan na wanke su. Shabiyu da rabi na koma Wakina na kwanta don hutawa saboda"

"na yi bala in gajiya, ga ™wan™wasona kamar za su Salle"

saboda ciwo.

"'Yar Nokia ta na Wauka tare da kiran Innarmu na gaisheta, ina tambayar ta mutanen gida da babanmu, nan take sanar min da kowa na nan lafiya mun Wan jima muna gaisawa kafin na yanke kiran, sallar azahar na yi na kwanta dan ba wani abu zan yi ba gwara na yi barcin kawai. Haka dai kullum nake aikin wani lokaci da sau™i wani lokacin kuwa aikin sai ya cakuWe mini musamman idan ta yi ba™i ko maigidan ya yi ba™i. Wani lokaci ina kaiwa shaWayan dare kafin na kwanta da zaran barci ya fara Waukata zuwa biyun dare zan ji ana buga mini ™ofa, ni kam yanzu tsoron gidan nake ji har ban ™aunar dare ya yi don katse mini barci ake yi. Yau da wuri na kammala aiki domin ko goma ba ta yi ba, ina shiga Waki na nufi toilet ina cikin wanka na ji kamar an shigo Wakin, amma sai na basar dan ba mai shigowa, babu ma me zuwa side Win da nake."

"Šaure da Wan galen da nake Waurawa na fito. ""Wayyo Allah!"" Na faWa da ™arfi ina neman hanyar guduwa. Šan tsaki ta ja tare da Wauke kanta daga kallona tana faWin. ""Ke tun Wazu da nake kiran ki ba ki ji ba ne?"" Tana gama faWar haka ta fita a Wakin ajiyan zuciya na sauke ina kallon Wakin, cikin raina na ce Allah ya sa na gyara Wakin bare ta ce min na bar wuri babu gyara."

"Doguwar riga na saka tare da himar na fita, na same ta zaune a falo ita da wata, ""Kwashe kayan ki haura sama da su."" Gaishe da ba™uwar na yi sannan na Wauki kayan."

"""Wannan ce me aikin?"" Na ji ba™uwar tana tambayarta. ""Ita ce."" ""Da alama ba irin yara masu hayaniya da rawan kan nan ba ne."""

"""Uhm, to ga ta nan dai."" Ba™uwar ta sake cewa, ""Yaushe ne tafiyar taku Salima?"" daidai zan fita daga falon na ji an kira sunanta wanda sai yau na ji asalin sunan nata, ni dai Madam nake ce mata. Salima ta juyo ta kalli ba™uwar tare da faWin. ""A'isha jibi za mu wuce da yamma tare da Wasila yayar Saifullah, amma gabaWaya ina ji wani iri kamar kar a yi tafiyar nan."""

"""To mene ne abin jin sanyin jiki ke da za ku neman waraka, kin ga fa idan aka dace da wannan aikin da za a yi miki shi kenan fa ke ma za ki zama uwa, danginsa za su daina goranta miki na rashin haihuwa, daga ™arshe shi ma Saifullah idan ya gaji da zama haka ba yara wallahi aure zai ™ara, ba zai iya jure wannan zaman da kuke yi ba tun da dai ya yi ha™uri ya zauna da ke tsawon shekara sha biyar ko Sari ba ki taSa yi ba... ""Saifullah bai Sata nuna ya gaji da ni don ban haihu ba, 'yan'uwansa ne dai da shegen damuwa suke uzzura mishi suna so lallai sai ya rabu da ni ko ya ™ara aure tun da an gano matsalar da ga ni ce ba wai shi ba. Ni kuma kin san wallahi ina da mugun kishi ba zan iya kallon Saifu da wata mace har su haWa makwanci ba, gaskiya ba zan iya ba."" Salima ta ™arasa maganar tana mayar da ™wallan da ke shirin zubo mata. ""Da kin ha™ura kin bar shi ya ™ara auren, Saifullah yana ™aunar ki, ko da ya yi aure ba zai juya miki baya ba... ""Ko da ya haihu da matar da ya aura? Hmmm! Ki bar wannan maganar kawai don ba zan ma yarda ba."" Daga nan suka rufe zancen, ina kwance a Waki har barci ya fara Waukata na ji an buga min ™ofa, ko da na buWe ™ofar har ta yanki kwanar hanyar kitchen haka na bi bayanta, tana zaune a kujera tana danna wayarta na ji ta ce. ""Ki dafa tea ya ji kayan ™amshi da yaji."" To kawai na ce sannan na haWa kayan tea Win na Waura a gas. Flacks Win maigidan ta sa na juye sannan na Wauka na bi bayanta da shi zuwa Wakinta, a daidai ba™in ™ofar Wakinta ta amsa sannan na dawo na wanke tukunyar da na dafa tea Win na koma na kwanta."

"2:30AM ""Zinariyaa... Na ji murya mai taushi da sanyi ya kira sunana. A hankali na buWe idanuna"

"tare da mi™a mishi hannuwana kamar yadda shi ma ya mi™o mini na shi, ji na yi lallausan hannunsa mai kama da auduga ya kama nawa hannun, haka na dinga bin bayanshi ina ta"

"™o™arin kallon fuskarshi amma ina, na kasa ganin koda haSarshi ne. Kyakkyawan wurin"

"shakatawan da ke bayan gidan ya nufa da ni a nan na ga wasu yara suna wasa yayin da suke ta ™ya™yata dariya, ina ji suka rumgume suna faWin. ""Ummi... Kiran sallar assalatu ya farkar da ni daga wannan mafarkin mai ban mamakin da nake yi. Zaune na yi tsakiyar gado ina ta jin wani"

yanayi na sanyi a cikin jikina.

"Littafin Zinariya na kuWi ne, ba zan yi free pages da yawa ba, domin biya za ku tuntuSi wannan"

Number ta WhatsApp. ¦ 500.

09079740079

Maman Faruk.

"[30/11, 3:49 pm] :5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ 5Ø Ü5ØÜ;: *...ZINARIYA*"

_Romantic _

®AYSHA JB

Farin Jini Writer's Asso..

3&4

"GabaWaya na ji yanayin wani iri, ina zaune har biyar da rabi sai da na ji ana shirin ta da sallar subahi kafin na yun™ura na nufi toilet na yi alwala na gabatar da ra'atanil fijir na yi sallar subahi. Ina zaune har hantsi ta yi kafin na mi™e na fito farfajiyar gidan na fara aikin da na saba. Karfe takwas na kammala komai na zauna a ™ofar kitchen ina jiran fitowar hajiyar gidan, yau dai an yi abin kirki an sauko da wuri, ""Ke Zinariya... ""Wai ita wannan madam Win ba za ta iya kiran sunan kurum ba sai ta haWa ni da *ke* ne?"" Cikin masifa nake mita ni ma. ""Mene?"" Na ji ta ce tana kallona. ""Na ce ina kwana?"" Ba ta amsa mini ba sai cewa ta yi. ""Je ki gyara min Waki."" Cikin raina na ce za a fita kenan, domin in har ta ce in je in mata gyara war haka na san fita za ta yi duk da ba ta ce min fitar ne za ta yi ba, don ba na sanin fitarta sai dai na ga ba kowa a gidan. Haurawa na yi na iske ba™uwarta ta fito da ga wanka, sai da na jira na gama shiryawa sannan na shiga Wakin na gyara mata. Ina fitowa na tsaya gaban mirror da ke upstair Win ina kallon fuskata, zaro ido na yi ina faWin. ""Kam bala i haka na yi kumamatu? Kai, wallahi kumatu na yi sosai aikuwa zan kira Innarmu na sheda mata Zinariyarta ta fara zama Sakutuwa, ga jikinta ma ya fara murjewa 'yar ba™a ta fara haske."" Cike da zallar yarinta take maganar tana taSa kumatunta tare da shafo wuyarta, sai da na ga haske ya haskani sanna na tuna ashe da Camera a gidan. Kallon Cameran na yi ina murguWa baki na ce. ""Kalle ni da kyau ™iba na yi jikina"

"ya murje."""

"""Subahanallahi lafiya? Ke da wa kike magana?"" Cewar wannan ba™uwar. Sum-sum na Wauki kayan shara na ™arasa saukowa kamar munafuka, turaren wuta na kunna tare da baWe gidan da ™amshi zuwa lokacin madam Salima ta gama girki ni ina can ina zagaye gida da turare ina haWa wa da shiririta. ""Wannan yarinyar akwai shiririta wallahi."" Cewar A'isha a lokacin da suke yin breakfast ""Wa kenan?"" Salima ta faWa tana kallonta. ""Mai aikin ki mana."" Ba ta ce mata komai"

"ba ta ci gaba da abin da take. ""Wannan yarinyar ba na tunanin ta cika sha bakwai..."

"""Yanzu wai ta shiga sha shida ma."" A'isha ta ce. ""Haba ai dole za a zuba ruwan shiririta mana, amma ya kamata a ce tana makaranta ne yanzu."" Hmm, kawai Salima ta ce sannan ta dubi A'isha tana faWin. ""Suna da halin kaita makaranta suka kawota aikatau? Ai da suna da wannan damar ba ma za su turo ta neman kuWi ba."" A'isha za ta yi magana Salima ta Waga mata hannu tare da faWin. ""Dan Allah ban son surutu."" Ta mi™e ta Wauki na ura tana kallon shirmen da Zinariya ta yi Wazu. Duk wani motsinta tana kallo da yadda ta dinga taSa kumatunta, tsaki ta yi tare da rufe"

wa ta mi™e ta Wauki key Win motar ta suka fita.

"Ina kwance na ji fitar motar ta, taSe baki na yi tare da faWin. ""Zan sha barcina na more."" Sai kusan la'asar na farka, Ina zaune ina jiran dawowarta don na fara jin yunwa wallahi, kuma ta ce na daina girki sai in tana nan saboda ina cika mata maggi da mai cikin abinci ita kuma ba su cin su, ni kuma gaskiya ba na son girki salam-lam don a gidanmu ba haka muka saba girki ba."

"Kitchen na shiga na buWe firiza na Wauko ragowar taliyar da muka yi jiya na Wuma na ci kayana na koma Wakina. Sai huWu da rabi ta dawo gidan. Ina ji tana horn alamar ta dawo banza na yi da ita, sai da na ji kamar za ta tashi gidan kafin na nufi parking space Win ina mata barka da zuwa. ""Ke tun Wazu ba ki ji ina horn ne da kika yi zamanki?"" Ta yi maganar tare da nufar hanyar falo bayan ta buWe booth. Da harara na raka bayanta domin haushi ni kam take ba ni idan ta yi magana ba"

ta kira sunana ba.

"Ina cikin gyaran bayan mun kammala girki da dare na ji tana ™wala mini kira. Šan dakatawa na yi ina sake sauraro don sake tabbatar da ni Win ce ake kira ko kuwa, ""Zinariya... ""Na'am madam Salima ga ni zuwa."" Bayan na je ta kalle ni tare da faWin. ""Ki shirya gobe ™arfe shida za mu yi tafiya."" Zaro ido na yi waje ina faWin. ""Tafiya ina? O'o ni dai a kaini gidanmu ba ni zuwa ko'ina wallahi."" Banza ta yi da ita tare da haurawa sama, ""Ni wallahi kar aje a sayar da ni ma a sa na daina ganin Innarmu... Cak Salima ta tsaya tare da juyowa ta yi mata wani irin kallo tana faWin. ""An ce miki ko na sayar da ke kuWi zan yi? 'Yar talaka da ke har kina da bakin da za ki ce kar a je a sayar da ke? Ke ba abin farincikinki ba ne a ce za a keta hazo da ke? Karki kawo mini shashanci."" Tana kawowa nan ta yi shigewarta."

"cikin Sacin rai na gama gyaran kitchen na koma Waki na Wau waya zan kira Innarmu na ga ba ni da kati kamar na fashe da kuka saboda ba™inciki ga shi dare ya yi babu ta inda zan fita a gidan bare har in samu kati. Haka na kwana cikin Sacin rai ina idar da sallar subahi na ji wani mugun ™ararrawa na ™ara kamar za a ta shi kaina, saboda neman fitina kaya kala uku kawai na saka a leda sai himar Wina guda biyu, shi kayan ma doguwar riga ce kawai na saka guda biyu sai fallen zani Waya da T-shert ina isowa ta yi mini nuni da wata mota gidan baya na buWe na shiga nan na"

"ga drive ne sai wannan ba™uwar, ita kuma tare da mijinta suke a mota Waya."

"Gaisuwa ce kawai ya haWa ni da matar dan ita ma na ga alamar irin madam Salima ce ba ta da sakewar fuska, haka har muka iso airport nan muka iske wata babbar mata dan za ta iya kai wa sa'ar Innarmu duk sai na ga suna gaisheta, har shi mijin madam Salima wanda iya bayan rigar shi kawai nake iya kallo, ni kam ina rakuSe a gefe rumgume da 'yar leda ta ina kallon su, haka na ga madam ta shiga jirgi da mijinta ba™uwarta ma ta shiga, ya saura daga ni sai matar nan. Ai tsayawa na yi na ce yau zan ga ikon Allah da gaske ne matar nan so take lallai sai ta sayar da"

"ni, zaman 'yan bori na yi tare da kurma ihu ina faWin. ""Wayyo Allah Innarmu! Wayyo na shiga"

"tara na lalace... ""Subhanallah! ˜alau kike kuwa 'yar nan?"" Wannan babbar matar ta faWa tare da Wago ne. ""Wayyo ni ku bar ni, ni wurin Innarmu zan tafi ni a kaini gidanmu."" Kururuwata ya sa security suka nufo wurin suna tambayar ba'asi, nan take sanar musu da babu komai. ""Yarinya ki nutsu babu wanda zai sayar da ke. Mu je jirgin zai ta shi."""

"""Wallahi ba zan je ko'ina ba..."" Jama'ar da ke wurin suka tsaya kallon ikon Allah, da ™yar aka ja ni zuwa cikin jirgi ina ihu ina fisgewa, duk na haWa gumi da majina. Zaunar da ni ta yi a kujera ta jikin window kafin ita ma ta zauna kusa da ni ta saka min makari, lokacin da jirgin zai ta shi na kuma kurma ihun da ya sa mutanen toshe kunnuwansu ita kanta sai ta ta ce. ""Kai ohooo!"

"Wacce irin yarinya ce ke da babu nutsuwa tattare da ke haka?"" Ajiyan zuciya na dinga saukewa ina jan sheshsheka. A haka barci ya yi awon gaba da ni, yaya B kuwa sai jinjina yarinta irin na Zinariya take yi. Har jirginmu ya sauka a Egypt ina barcina sai da matar nan ta taSa ni don ta tashe ni nan ta ji jikina da zafi alamun zazzaSi. BuWe idanuwana da suka yi mini nauyi na yi da ™yar ina jin jikina na rawa saboda sanyi-sanyi. Motar da zai kai mu masauki ne ya zo ya kwashe mu duka cikin motar kuwa ina kwance jikin matar nan don na lura duk ta fisu kirki so Waya muka haWa ido da madam Salima shi ma ba wani kallon arziki ta yi mini ba. Hotel Win da muka je a Wakin matar da na ji suna kiranta da Aunty B, na zauna ita kuma madam tana tare da mijinta ba™uwarta kuma Wakinta daban. Ko abinci ban iya ci ba, ruwan zafi na sha nan na dinga kwara amai, hankalin Aunty B ya tashi nan ta kira Salima ta shigo Wakin. ""Ko dai yarinyar ta kwaso ciki ne na zo ina yawo da ita?"" Wannan mummunar kalmar ta yi mugun dukar zuciyata, duk da ™arancin shekaruna na san kalmar cikin shege mummunar kalma ce, kallonta na yi da jajayen idanuna da suka rine dan bala i na ce mata. ""Ni ba 'yar iska ba ce."" Salima ta ce. ""In ke ba 'yar iska ba ce amaye-amayen mene ne kike yi wa mutane? Ke ni ba za ki saka ni a masifa ba akwai jirgin da zai juya wallahi zan saka ki mayar da ke inda kika fito."" Aunty B ta ce. ""Haba ya isa Salima wacce irin magana kike faWa haka? Yarinyar nan dai mai aikin ki ce, a gidan ki take"

"zaune ta yaya za ta yi ciki bayan kuna cikin gida Waya?"""

"""Na sani ko tana biye-biye da dare?"" Ni tun da uwata ta haife ni ba'a taSa faWa mini mummunar kalma irin wanda madam Salima take yaSa mini yanzu ba. ""Ni ba 'yar iska ba ce wallahi, ni ba 'yar iska ba ce. Allah sai ya saka min... Ko rufe baki ban yi ba wani aman ya sake ™wace min salati da sallallami suka Wauka. ""Kin gani ko Aunty B? Ni dai wallahi ba za a saka ni a uku ba, gwara tun wuri ta koma inda ta fito."" Ni dai tun da na mi™e da niyar barin Wakin hajijiya ta Wibe ni"

ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance gadon asibiti.

"Littafin Zinariya na kuWi ne, za ku tuntuSi wannan Number ta WhatsApp domin mallakar naku."

¦ 500. 09079740079

Maman Faruk.

"[30/11, 3:49 pm] :5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ5ØÜ 5Ø Ü5ØÜ;: *...ZINARIYA*"

_Romantic _

®

AYSHA JB

Farin Jini Writer's Asso.. 5&6

"Yun™urawa na yi da niyar tashi nan na ji ni shakaf, zaro idanuwa na yi da sauri ina ™o™arin mi™ewa da ™arfi

Please Login or Register in order to submit comment