gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FAHIMAH Gaskiyar Da Aka Ɓoye book 1 By Takori Kabara Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com FAHIMAH

Book 1 Complete Writing by

Takori kabara

arewanovels.com.ng

SHIMFIDA

"Misalin karfe ukku na yammacin ranar, wadda ta kasance Talata, cikin wata Unguwa a jihar Kano da ake kira ''Yankaba, Hajiya SAFIYYAH-BASUDANIYYAH (kamar yadda kowa da ya santa yake kuma alaqa da ita ke kiranta), na zaune bisa Kilishin tsakiyar falon ta, carbi ne dan madina a hannun ta tana ja, lokaci zuwa lokaci tana mai daga kanta zuwa ga tankareren agogon bango dake manne a fuskar gabas maso kudu na falon nata. Ga dukkan alamu akwai abinda take dakon jira, shiyasa tun da ta yi sallahr azuhur bata tashi a gurin ba take yawan kai idanun ta ga agogon bangon."

"Kayataccen falo ne ne da ya ji kayan alatu na zamani wanda kallo daya zaka yi masa ka tabbatar masu gidan suna cikin wadatar rayuwa, daular duniya ta gama zaunawa dai-dai misali da burin kowanne dan adam. Komai dake falon kalarsa ruwan madara ne da ratsin ruwan goro (orange) wanda hakan ya maida falon kalar unique don kala ce da ba'a faya amfani da ita ba wajen tsara falukan zamani."

"Tun Haj. Safeeyah bata damuwa, amma da ta ga yadda lokaci ya ja sai damuwa ta fara nunawa akan kyakkyawar Basudaniyar fuskar ta. Me ya tsayar da FAHIMAH a makaranta har yanzu da ake neman karfe uku na rana???"

"Sallamar mai aikin ta Talatu ya katse mata tunani, ta shigo dauke da butar Shayi irin ta larabawan SUDAN da 'yan kananan kofunan tangaran na shan shayin Sudanai, kai tsaye ta nufo inda uwargijiyar ta ke zaune ta russuna daga gefe ta ajiye, ga dukkan alamu abu ne da ya zamewa Hajiyar al'ada wato shan shayin akai-akai. Talatu tace, tana duban Hajiyar."

"""Hajiya mutuniyata ko lafiya? Tun dazu nake duban hanyar ta har yanzu shiru, ko ta ce miki zata biya wani waje ne yau?"""

"Hajiya Safeeyah ta kai karshe a carbin da ta ke ja, tayi addua suka shafa tare da Talatu, sannan ta ce."

"""Tunanin da nake ta yi tun dazu kenan, karfe daya da rabi yau tace min zata dawo, bari in kira wayar ta mu ji ko lafiya, don Fahimah bata zuwa wani waje ba tare da ta gaya min na mata izni ba""."

"Ta dauki wayar dake gefenta ta lalubo lambar Fahimah ta kira ta kara a kunnen ta, amma har tayi ta katse mai wayar bata amsa ba. Which was very unusual of her (kin daga waya). Wanda hakan ya kara dugunzuma zukatan Hajiya da Talatu."

"Daidai lokacin da ya shigo falon yana balle 'links' din hannun farar rigar shi, gabadaya falon ya dauki kamshin sassanyan turarensa ""Maison Francis (Kurkdjian, Paris)"". Farar shaddah ce kal a jikin shi mai santsi da ake kira (London King) da farar hular Zanna mahadin shaddar jikin shi. Dogo ne, mai fadin kirji (physique chest) amma hakan bai hana ka kira shi siriri, don tsayi har ya rankwafa, kallo daya zaka yi mishi ka tabbatar ba cikakken bahaushe bane; ko dai"

ruwa-biyu (half-caste) ko kuma cikakken Ba-sudane. Sudanan ma irin fararen Sudanai ba

"bakaken cikin su ba, hancinsa don tsayi har lankwasawa yayi kadan, hular kansa ta nitse tsaf a cikin tarin sumar kansa wadda ta kara fallasa jinsin da ya fito daga cikin sa."

"Ga dukkan alamu cikin sauri ya ke, sauri mai yawa, ya dubi mahaifiyar sa dake zaune nannade cikin laffaya shudiya da carbi a hannun ta, bai taba ganin ta da wata suttura ba ta Sudanese ba, Talatu na duke gabanta tana firfita mata shayi, yayi dan russunawa daga tsaye cikin tarin ladabi ga mahaifiyar sa..."

"""Ammi zan fita, zan koma office, don bamu tashi ba na dawo, amma bazan wuce karfe biyar na yamma ba yau zan dawo, insha Allah. Na baro wasu ayyuka da ban karasa ba nake so inje in karasa, don gobe da safe managern Gyadi-gyadi Branch zai karbe su daga ofis dina""."

"Bai kuma jira cewar mahaifiyar tasa ba ya doshi kofa, ko abincin ranar da aka shirya masa bisa makeken tebir din falon bai kalla ba."

"""Uwais!"""

"Muryar mahaifiyar tasa ta dakatar da shi. Ba tare da ya juyo ba ya dakata a kagare. Ta ce, Fahima ba ta dawo ba tun fitarta makaranta."

"Annurin da ke fuskarsa nan da nan ya gushe. Gabadaya ya juyo fuskarsa a gintse, For Allah sake. Ammi ni ina ruwana? Is she a kid? Ko kuwa ba ta san hanya ba?"

"Hajiya Safiyya ta girgiza kai tana iya karantar tsanar maganar yarinyar da ta yi masa baro-baro a kan kykkyawar fuskarsa. To amma dole ta gaya masa sabida yadda kasar tamu ta koma daukan dan mutum ya zama kamar na kiyashi. Babu kuma wani namiji a gidan bayan shi, shi ne ubansu har ita da ta ke mahaifiyarsa."

"Duk uzurin da ka ke da shi ka ajiye ka bi bayanta, ko in tashi ni da kaina in bi ta."

A matukar fusace ya sa kai ya fita daga falon ba tare da ya ce komai ba.

"Daga yadda yake tukin motar kadai za ka fahimci ransa a bace yake, don dai fuskar sa ta kasance mai boye bacin rai ne, ko kadan ba abin da ya tsana a duniya irin Ammi ta hada sha'anin sa da na Fahimah. Ta ki yarda ta gane har yau shi zuciyarsa ba ta son Faheemah, kuma har abada ba za ta so ta ba! Ba don komai ba sai don ASALINTA Da wasu specific"

"dalilan da suka dade da samun muhalli a ransa tun suna yara shi da Fahimar, muhimmi shi ne son da Ammin sa ke mata, wanda yake ittikafin da kyar in bai zarce wanda take masa shi da ta haifa ba."

"Shi kuma tun asali mutum ne mai kishi akan abinda yake so, musamman Amminsa, wanda"

kishin nasa akan ta ne ya hanata sake aure har yau.

"A daidai lokacin ya karya kan motarsa ya shiga makarantar YAN DUTSE COLLEGE, bayan maigadi ya bude masa kofar makarantar, abin haushi yana shigowa ita ya fara hangowa tun daga nesa suna tafe ita da kawarta Majida suna hira, sai dariya ta ke ba abinda ya dameta. Ta baro masa uwa cikin taraddadi don bata san zafinta ba. Her elegant black skin sai sheki ta ke cikin hasken ranar, babu wani abu mai haske a jikinta kamar fararen idanunta da jerarrun hakoranta. She's dark-skinned yet beautiful. Wasu irin idanuwa masu sparkling cikin idanun duk mai dubanta. Cikakken gashin girar da ya kusa hadewa da dan uwansa yana daga cikin abin da"

ya bambanta ta da sauran mata yan uwanta.

"Uwais dauke kai ya yi yana sakin tsaki, tare da danna musu gigitaccen horn mai karfi don"

"kamar ba su lura da tsayuwar shi ba. A ransa cewa ya ke, ko uban me suka zauna yi a makarantar har yanzu oho! Kwata-kwata su da suka rage cikin makarantar ba su fi a kirga da yatsun hannu ba."

Ta dago kai da sauri ta dubi inda horn din motar ya fito. Mutum na karshe da ba ta taba

"tsammanin gani a makarantarsu ba, da sunan dai ya zo daukanta. A gurguje ta yi sallama da kawar tata ta nufo inda yake kafafunta har hardewa suke don sauri da fargaba."

"Ba yau ta fara ganin wannan moody expression din a kan kyakkyawar fuskarsa ba in dai a kanta ne, don haka inda sabo Fahimah ta saba. Ta bude kofar gefensa ta shiga, ya tada motar a guje ya bar makarantar ba tare da ya dube ta ba."

"Maimakon ya dau hanyar gidansu kamar yadda ta yi tsammani, sai gani ta yi sun dau hanyar Bank Road, ita dai ba ta ce komai ba, amma ganin sun yi parking a wani branch bankin GT ta fahimci inda suka zo din, wajen aikinsa ne."

"Ya bude kofarsa tare da daukar jakar loptop dinsa da wayoyinsa ya yi shigewarsa. Duk inda ya gifta sai maaikata yan uwansa sun kula shi sun gaishe shi, amma hannu kawai Uwais yake daga musu ya wuce, kowa ya saba da rashin walwalarsa shi ya sa shan kamshinsa ba ya damun kowa don farin jini gare shi ba na wasa ba, wanda kyawun surarsa ke sayo masa."

"Yana kokarin zama a kujerar ofishinsa wanda ke zagaye cikin raw gilashi, kowa da ke wajen yana iya hango shi daga waje, wayar Ammi ta shigo, yana jan kujerarshi zai zauna ya amsa mata."

Muna tare.

Kawai ya ce tare da ajiye wayar bisa makeken tebirinsa baki wuluk mai sheki. Ammi hankalinta ya kwanta tunda ya ce yana tare da Fahimar.

"Kai ba za ka ce ya ajiye mutum cikin mota ba, ya kunna kwamfutar kan tebirinsa ya durfafi ayyukan da ke gabansa cikin kwarewa da sanin makamar aikin sa, wadanda da ma su ya dawo don yayi. Ya manta da wata da wata mutum dan adam da ya ajiye a cikin mota, ba tare da ko ya sauke mata gilashi don ta sha iska ba."

"A can kuma Faheema tun tana duba siririn agogon da ke daure a hannunta har ta kwantar da kanta a kan dash board din motar, ta sauke gilassan da ya rufe iska ta soma ratsa ta, wata irin yunwa na sakadarta. Rabonta da abinci tun karin kumallon safe da Ammi ta takura mata ta yi, ta san halin Uwais sarai, duk yadda aka yi Ammi ce ta takura masa ya bi sawunta shi ya sa ya zo ya shanya ta a harabar ofishinsu."

"Ba kowa ya ja mata ba sai Mr. Edward malaminsu na Biology, shi ne ya zaunar da su yin practical na darasin da yake daukarsu bayan normal school hours kasancewar nan da watanni uku za su zana jarrabawar barin makarantar sakandire gabadaya. Ammi ta san Uwais ba ya"

son hada hanya da ita don me za ta sa shi ya biyo bayanta?!

"Allah sarki Fahimah! Tun tana sauraron kidan da akuyar cikinta ke yi, har ta koma ta kwantar da"

"kanta jikin kujerar motar, wani wahalallen barci ya yi awon gaba da ita."

"Sai karfe biyar na yamma ya kammala duk abin da yake yi a bankin, ya tattaro wayoyinsa da"

"kwamfutarsa ya fito. Sai da ya tunkaro motar sannan ya tuna da ita, ya bude gidan baya ya"

"zuba shirginsa sannan ya shiga mazauninsa ya zauna. Kunna motar da ya yi, da reverse hadi da cin taya ya bar harabar bankin shi ya tada Faheemah daga wahalallen barcinta. Barcin"

"yunwa da gajiya. Ta dube shi ta gefen ido, ya nutsu yana tukinsa cikin gwanancewa."

"""Fuskar ta salihai, kyakkyawa a ido, amma kamar ta Firauna a zuciya. Fahima ta fada a zuciyarta.A shekaru goma shaf takwas na rayuwarta da ta yi tare da shi gida daya, bai taba kyautata mata ko sau daya ba, sannan ba za ta taba iya fadar wani alkhairi guda daya da ya yi mata ba a matsayinsa na Yayanta a kan dalilin da ba ta sani ba. Duk da kasancewar su biyu ne kacal a wajen mahaifiyarsu Hajiya Safiyya, ta sa a ranta Uwais makiyinta ne na babu gaira babu dalili, don bata san laifin da take masa ba, Ammi ma bata sani ba, don har a cikin kwayar idanunsa tana iya hango tsantsar kiyayyar da yake mata, a gaban kowa kuma ba ya iya boyewa"

including mahaifiyarsu Ammi Safiyyah.

Ita kuma nan duniya babu mai burge ta irin UWAIS ABDULKARIM SHAGARI!!!

"Wani kwayan mutum guda daya da ya yi mata babakere a zuciya.Daga baya ta fahimci shi Ammi ta haifa ba ita ba daga lokacin da ta soma hankali, amma in za a yanka ta ba ta san alakar da ke tsakaninta da su ba."

"Ita dai ta taso ta ganta a gaban Hajiya Safiyyah Basudaniyyah, cikin wata irin kulawa irin ta UWA da duk wata kyautatawa da uwa ke wa danta. Ammi Safiyya is more than a mother a gare ta, she is an ANGEL wadda Allah ya halicce ta a hannunta domin ta zame mata kafadar da za ta kwanta a kai ta yi kuka, ko dariya."

"Yawan kyautatawar Ammi, jin kai da kulawarta gare ta ke hana ta yi mata titsiyen da Ammin ba ta so na ita wace ce uwarta, wane ne ubanta??? In tana son ganin bacin ran Ammi, to ta yi mata wadannan tambayoyin. Don haka ta dade da daina yi mata tun kafin ta kawo munzalin adolscence. Ta yarda da abin da Ammin ke gaya mata kullum, ITA CE UWARTA, ITA CE UBANTA amma ta sani watarana na zuwa da dole Ammin za ta yi mata confessing daga inda ta samar da ita tunda ko makaho ya shafa a halitta ya san Ammi balarabiyar usuli haka ba ita ta tsugunna ta haife ta ba."

"Kodayake ba'a judging haihuwa da kamanni ko kalar fata, amma ita kam ko daga kalar fata, gashin kai da yanayin kirar jiki za ka san Ammi balarabiya ce, yayin da ita kallo daya za ka yi mata ka tabbatar cikakkiyar bahaushiya ce, jikar Barbushe da Tsimbirbira."

"To amma me ta ke nema a iyaye wanda Ammi ba ta yi mata ba? Ta yi mata komai a rayuwa wanda a kullum yake mantar da ita cewa, ba ita ta haife ta ba, sai dai kulafuci irin na dan adam. Musamman akan son tabbatar da legitimacy din ta."

"A duk lokacin da wani tunani makamancin haka ya sarke ta, fuskar Ammi da murmushinta na UWA a gare ta take daukowa ta dora a kan idanunta, sai kowanne tunani, da kowacce damuwa da kowanne bacin rai su bace su kama gabansu. A duk lokacin da Uwais ya yi mata kallon nan nasa na tsana da kyama, murmushin Ammi kadai ke gusar da shi komai girmansa."

"A yayin da ka ke da uwa irin Ammi a gefe, babu wani bacin rai a rayuwa da ya isa ka yi masa"

kuka. Fahimah ta kan yawaita fadar hakan a zuciyarta.

Tana wannan tunanin cikinta kuma na ci gaba da kartawa ta ji Uwais ya kashe motar a parking

"lot na gidan su, sai a lokacin ta ankara sun zo gida. Ya fice ya barta a motar ba tare da ya ce da"

ita ko uffan ba.

"Tana fitowa jiri ya kwashe ta, sai da dafa bango sannan ta iya karasawa zuwa cikin gida. Shi tuni ya jima da shigewa part dinsa. Wanda dole sai ka ratsa ta main parlour zaka isa part din nasa. Ammi bata yarda ta ware shi daga can waje ba, sabida tsantseni na tarbiyyah irin nata."

Ammi da Talatu har suna hada baki wajen tambayarta lokacin da ta shigo wujiga-wujiga da ita.

"Fahimah, me ya zaunar da ke a makaranta haka?"

"A gurguje ta yi musu bayani Mr. Edward ya tsare su kan shirye-shiryen su na fara SSCE, da sassanyar muryar ta wadda ta kara sirancewa sabida yunwa da gajiya, sannan ta durfafi dining-table tana zuba abincin jikinta har rawa yake, kuma da ma tana da ulcer."

"9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: A bakin get ya tadda Jabir yana jiransa, a motar Uwais za su tafi, in sun dawo ya ajiye shi a gidansa ya juya. Tunda suka hau kan titin da zai kai su Bompai wuta ta dauke wa Uwais saboda fargabar irin tarbar da kuma amsar da zai samu daga Alhaji Umar Dikko. Jabir shi kadai yake zuba hirarsa ga dukkan alamu shi kam bai da sauran matsala a rayuwa, da ya fahimci halin da Uwais ke ciki, sai ya yi dariya ya dafa kafadarsa."

" Daddy is very friendly, kawai za ka sha tambayoyi, in ya ga dama kuma ya ce ka jira auta for"

6 years ta gama MBBS dinta. This is for sure na tabbata zai fadi hakan.

"Ashe da na tattaro kayana na koma gidansa a Abuja idan yana ganina kullum zai gane ba zan iya jiran ba""."

"Dariya Jabir ya sake yi, ya ce, Kada ka tsorata da dukkan tambayoyinsa, be brave, be yourself,"

sannan kada ka boye masa komai ya tambaye ka.

"Alhaji Umar Dikko na zaune a luntsumemiyar kujerar sitting room dinsa, da ganinsa ka ga bafillacen usli, furfura ta cika a gashin kansa amma fatar jikinsa sumul ta ke, babu tsufan,"

sabida samun hutu. Jabir ya yi musu iso suka shiga already ya san da zuwan nasu.

"Dukkansu a kasa suka zube suka kwashi gaisuwa, irin ta neman iri, fuska sake yake amsawa har yana tsokanar Uwais ya aka yi ya bari abokinsa ya shiga daga ciki shi yana daga waje har"

yanzu? This is kafin ya ji gundarin abin da ke tafe da su.

"Daddy, kamar yadda ka sani Uwais abokina ne, tun a A.B.U, Daddy abin da ya kawo mu shi ne,"

ya zo neman amincewarka ya fara neman auren Amrah.

"Cikin mamaki Alhaji Umar Dikko ya ce, Amrah? Amrah wacce?"

"Jabir ya ce, Autar Mama dai Daddy."

"Ya tsura wa Uwais ido na 'yan dakikai inda ya hango cikar kamalarsa ko ta ina bai ga makusa ba kamar yadda komai da ke jikinshi ya nuna ba karamin mutum ba ne, ilmi da hatimin nasara sun wadace shi. Sannan ga wani irin sassanyan kyau da ya rasa gane daga kabilar da ya dauko shi. Above all Allah ya yi ma Uwais wani irin kwarjini, ilhama da cikar zati da ya wuce ya nemi alfarma wurin mutum a kasa yi mass."

"Amsar da ya so bayarwa sai ta canza kanta ba tare da ya ankara ba, domin da farko so ya yi ya"

"ce su tashi su tafi, ba yanzu zai yi wa yarsa aure ba."

Wane ne Babanka? Kai dan wace kabila ne? Gama na ga ba Bahaushe bane

"Uwais ya muskuta sannan ya kara dukar da kansa in ka ganshi a wannan lokacin kamar bawan da ke neman taimako. Ji yake zai jure komai, zai iya komai in dai Alhaji Dikko zai ba shi auren Amrah a karshe."

"""Sunanan Babana Grand Khadi Abdulkarim Shagari, ya jima da rasuwa, na girma a hannun mahaifiya ta, Babana basakkwace ne, mahaifiyata basudaniya ce."

"Alhaji Dikko ya gyada kai, sannan ya kara jifansa da tambaya. Mene ne matakin karatunka? Kuma mece ce sanaarka?"

"Uwais ya zuki numfashi, a ransa ya ce, wannan wane irin mutum ne? Ina da kwalin digiri na biyu, sannan ni banker ne da Guaranteed Trust."

"Alhaji Umar Dikko ya gyada kai cikin gamsuwa, sannan ya ce, Kana da masaniyar cewar Amrah karatun likita ta ke yi a matakin farko? Za ka iya jiranta ta kammala tsawon shekaru shidda?"

"Uwais ya hadiyi yawu da kyar shi fa jiran ne ba zai iya ba, burinsa ya bude ido ya ga ya mallaki Amrah, don haka bai yi kasa a gwiwa ba."

"Daddy, ku yi min alfarma, na yi alkawarin barin Amrah ta yi ta karatunta a dakina har sai ta ce ya ishe ta."

Ya kara dukar da kansa cike da zullumi da fargabar amsar da zai samu daga Alhaji Umsr Dikko.

"Bai san dalilin da ya sa farad daya yaron ya shiga ransa ba. Kamalarsa ce ko kamewarsa? Ba zai iya cewa ba, ga wasu exceptional qualities da ya gani a tare da shi. Shi kansa Jabir a yadda ya san mahaifin su bai zaci tambayoyin Daddyn nasu za su tsaya a nan ba. Sosai Alh. Umar ya"

"dubi Uwais kafin ya ce,"

Na ba ka izni ka nemi auren yata. Idan ta amince da kai dari bisa dari zan iya ba ka aurenta a bisa alkawarin da ka yi min na cewa za ka barta ta ci gaba da karatu a gidanka.

"Besides ni kuma zan yi nawa kyakkyawan binciken a kanka da iyayenka, idan na samu wani mummunan hali a tare da kai zan dakatar da kai. My daughter is innocent ka yi taka tsaftacciyar muamala da ita a cikin neman aurenta."

"Farin ciki ya sa bakin Uwais ya kasa rufuwa, kansa a kasa ya yi godiya tare da alkawarta wa Daddyn insha Allahu zai kiyaye abin da ya fada masa, kuma da yardar Allah ba zai samu wata"

mummunar shaida a kansa ko iyayensa ba.

"Suka fito shi da Jabir, inda Jabir din ya ja shi suka shiga cikin gidan wajen amaryar Babansu Aunty Nana. Suka gaisa tana da kirki sosai. Jabir ya gabatar mata da Uwais matsayin abokinsa, kuma manemin auren Amrah, wanda Daddy ya san da zamansa a yanzu. Aunty Nana ta yi mamaki sosai, don ta san Daddyn ya ce ba zai aurar da Amrah ba sai ta kammala MBBS. Ta karbi Uwais hannu bibbiyu, ta yaba da komai nasa cikin ranta. In Amrah ta same shi, to hakika ta yi dace da miji na nuna wa saa."

"Suka taho gidan Jabir inda Uwais ya sauke shi, Jabir ya yi masa tayin shiga gidan ko zai so yin"

"magana da Amrah. Uwais ya yi murmushi ya ce da shi,"

"Not now, Im not in contentment, tunda na samu licence dina."

"Zuwan Uwais na farko wajen Amrah a wani daren asabar ne, ana tsula ruwan sama, ruwan har ya fara jika shi, a lokacin da ya yi parking ya fito daga mota, ya bi ta garage zuwa falon Jabir inda nan ne ba shi da shamaki, kuma sun yi waya da Jabir ya ce yana gida ita ma Amran tana nan. Amma ya ce masa ya zo da wuri don Amrah in ta fara karatun darenta ba ta so a katse ta. Kuma wannan ne karo na farko da za su ga juna officially, ta sanshi a fuska amma a matsayin abokin Yayanta."

Yana zaune a falon Jabir yana mai duba agogon hannunsa. Jabir ya ce da shi ya jirata tana

"zuwa, sannan ya gaya wa Murjanatu Amrah na da bako a falo, kuma da sanin Daddy ya zo ganinta."

Bako daga Daddy?

"Amrah ta tambayi Aunty Murjanatu cikin mamaki. Murja ta ce, Haka dai ya ce, kuma ki yi sauri yana jiranki."

"Ko kadan Murjanatu ba ta yi mamaki da zuwan Uwais yau wajen Amrah ba, don ta dade da sa"

wa a ranta in ka ga kare na sunsunar takalmi dauka zai yi.

Amrah ta yi sallama a falon da siririyar muryarta mai kidima nutsuwar Uwais. Mikewa tsaye ya yi ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba. Har sai da Amrah ta shigo suka tsaya suna

"kallon-kallo ta hasken farin kwan lantarkin da ke falon. Zuciyarsu na bugu iri guda a lokaci guda,"

yayin da Amrah ta ji tamkar an sauke mata wani nannauyan dutse daga kirjinta.

"Uwaisun da ta ke kwana da shi tana tashi da shi Uwaisun da ya yi wa zuciyarta babakere ya hana ta sukuni da jin dadin rayuwar ko ta ya ya, yau ga shi a gabanta officially ya kawo kansa matsayin manemin auren ta..Me zata ce? Ko me zata yi? Banda tazbihi ga Ubangiji?"

"Ita ta fara dauke idonta daga cikin na Uwais amma ta yi-ta yi ta furta kalmar ina wuni? Ko sannu da zuwa ta kasa. Zama ta yi a kujera mafi kusa da ita, ta jingina kanta a makarin kujerar don hana kafafun ta kayar da ita daga wadannan kaifafan sexy eyes din na Uwais, tana sauke numfashi a hankalitamkar Uwais ya karanci abinda ke ranta, sai bai wahalar da kansa wajen gabatar da kan sa ba. Kai tsaye ya tafi straight to the point ."

Amrah am I welcome as a husband?

"Uwais ya fada daga karshe, yana mai durkusawa a gabanta a kan gwiwoyinsa wani abu abu"

da bai taba tunanin zai iya yi a kan diya mace ba.

"Murmushin da Amrah ta yi, da fuskarta da ta rufe da tafukan hannunta kadai a matsayin ta na bafullatana tamkar amsa ce ga UwaisUwais Shagari, Uwais Abdulkarim Shagari. and that is"

"the beginning mafari, tushe, sila, na dukkan abubuwan da suka biyo baya Sannan silar data"

zamo hanyar auren UWAIS da FAHIMAH......

****

"Ya dauki lokaci mai tsayi yana zuwa zance wajen Amrah, sun fahimci juna sun yarda da juna,"

"soyayya ta yi kaka-gida, hutun nata da ma na watanni uku ne, har ga shi gobe za ta koma Abuja inda daga can za ta zarce makarantarsu ta Limkwokwing, Malaysia."

"Yau da ya zo sallama ce za su yi, in ka gansu very emotional kamar masu shirin barin duniya don damuwa, Amrah ta shiga ran Uwais yadda ba'a zato haka Uwais ya samu matsayi mai girma a zuciyar Amrah, ta yadda suke jin rabuwar tasu ta yau har cikin bargonsu."

"Ba don kada in yi wa Daddy laifi ba ya ce zan hana ki karatu, da na kawo miki ziyara a Malaysia."

"Amrah ta zaro ido ta ce, Kada ma ka fara 'Habib - Qalby', Daddy bai hada karatu na da komai, za mu kasance a waya koyaushe insha Allah. Abinda zan sake dawowa bayan watanni hudu kuma a nan Kano zan sake yin hutuna?."

"Ke kike ganin watanni hudu kwana

Please Login or Register in order to submit comment