gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FAHIMAH Gaskiyar Da Aka Ɓoye book 1 By Takori Kabara Chapter 7 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma ta kasa ce da Ammi komai.

"Idan na yi miki ba daidai ba, idan hukunci na bai miki daidai ba ki yi hakuri ki yafe min Fahimah. Da sauri Fahimah ta juyo, tausayin Ammi wadda tsufa ya soma bayyana a gare ta duk sai ya kamata. Cikin rishin kuka ta ce,"

"Ammi, ba ki yi min komai ba. Sannan ta sa kai zuwa dakinta."

"Burinta a rayuwa komai ya girmansa a yau ya cika. Mafarkanta sun zamo gaskiya, ta zamo wani bangare na Uwais Shagari, amma abin mamaki ta kasa farin ciki da hakan, watakila don girman kalubalen da ta ke hangowa ne, watakila kuma don ta san auren ba zabin Uwais ba ne, in ma ya sani ke nan. Jin kanta ta ke tamkar wadda ta rako dukkan mata duniya sabida rashin saarta a rayuwa. Gabadaya maganar auren da auren kansa ba ta san a ajin da ya dace ta sanya su ba."

"Da me za ta ji ne a rayuwarta? Maraici, rashin asali and finally BORANCI?"

"Kodayake Ammi ta ce ba kai ta gidan Uwais za ta yi ba, sai ranar da dukkansu suka amincewa hakan. Ranar da ta tabbata ba mai zuwa ba ce, sai dai ta dauwama da sunan matar Uwais, amma auren ba zai taba zama reality ba."

"Yadda Fahimah ta ga rana haka ta ga dare a wannan ranar, kitsawa ta ke tana tufkewa sannan ta warware. Ta rasa makomar rayuwarta. A karshe ta sa a ranta cewa, ya kamata ta yarda cewa, duk bakinta da Uwais ke fadi yana gorantawa ita ma mace ce kamar sauran mata, wadda wani namijin bayan Uwais zai iya gani ya ce yana so ya biya sadaki ya dauka ya kai gidansa. In haka ne kenan ya kamata ta martaba kanta Ta daina kallon kanta wulakantacciya. Ba kuma ta"

"kowacce hanya ba face ta yin gefe da UWAIS daga zuciyarta, shi da duk abin da ya shafe shi."

"Ta maida komai nasa a bakomai ba, ta maida hankali kadai ga karatun da Ammi ke so ta yi, ta gina wa kanta future yadda duk ranar da babu Ammi za ta tsaya da kafafunta."

"Ta dauki aurenta da Uwais a matsayin shifcin gizo in ba haka ba ita ce a wahale. Ta tsaya ta nema wa kanta madafa ga rayuwarta ta gaba, wanda ba komai ba ne san yin ilmi da zai ba ta martabar da kyawun halitta ba ya badawa. Kyawun halittar da ta fi tunanin a kansa ne Uwais bai sonta. ""Goddam Black"" kamar yadda yake cewa tana alfahari da bakin fatarta."

"Ammi ta sha gaya mata Black is beauty a duk lokacin da Yaya Uwais ya ce mata Black, kuma"

babu mummuna sam a yaya mata sai wadda ba ta martaba kanta ba.

Da kyar barci ya sace fahimah a wannan daren cike da tunanin da ta kwanta da shi.

******

"Washegari Ammi da Fahimah suka tashi Umrah zuwa kasa mai tsarki. Ammi ta yi haka ne don ta nesanta Fahimah da Uwais na dan lokaci, ya kuma samu lokaci da matar sonsa yadda ya kamata."

"Duk adduar Ammi a Harami da Masjid Nabawy a kan Uwais da Fahimah ne, ita kadai ta san"

adadin abubuwan alkhairin da ta ke roka musu.

"A can Kano, ango da amarya suna ta barzar amarci babu kama hannun yaro. Uwais ya matukar jin dadin tafiyar Ammi da Fahimah, don ba ya so ko da kuskure a samu wanda zai gaya wa Amrah yana da wata matar bayan ita."

"Alhaji Umar Dikko ya zuba dukiya a gidan Amrah kamar bai san zafin nema ba. Gidansu komai ya yi acan-acan, soyayya ruwan zuma gangariya tsakanin Uwais da Amrah ba su taba gundura da juna."

Kafin Ammi da Fahimah su dawo Saudiyyah ango da amarya har wata yar kiba suka hada a kumatunansu sabida kwanciyar hankali da samun contentment in life.

"Ranar asabar da daddare suka sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano. Fahimah ta yi wa kanta sayayya sosai, haka ta yi wa Talatu tsaraba. Ba yadda Ammi ba ta yi da ita ba a kan ta yi wa Uwais tsaraba ko ta carbi ne, Fahimah ta ki. Yadda ta yi fatali da Uwais daga zuciyarta haka"

ta ke fatan ta manta da ko sunansa.

"Dan halak din shi ya zo daukarsu zuwa gida, ya sha excelcior fara kal, sai walainiya ya ke. Da ganin shi ka ga angon daje kan ganiyar sa. Motarshi kamar a nan ne kamfanin Maison Francis yake. Ga wani farin gilashin PRADA da ya manna ma dogon karan hancinsa. Kallo daya da Fahimah ta yi masa ba ta kara maimaitawa ba, duk da kuwa cewa zuciyarta ta yi mugun raurawa. Sakamakon wata irin ilhama da kamala da aure ya kara wa Uwais, gara ita ta kalle shi sau daya, shi ko sau dayan bai kalle ta ba. Sai da ya mallaki Amrah ya kara gane babu wata sauran diya mace da za ta kara burge shi a duniya."

"Babban tashin hankalinsa a kwanakin nan shi ne in ya tuna Amrah tafiya za ta yi ta barshi shi kadai a gidansu, aikinsa kuma ba irin na yawo ba ne duk lokacin da aka ga dama. Ya soma da ya sanin alkawarinsa na barin Amrah ta ci gaba da karatu a jamiar Limkokwing, sai dai ya san bai isa ba, ya yi kadan, yayi tsararo ya daga wannan alkawarin daga muhallinsa."

"Amrah ta sangarta shi da abubuwa da yawa a sati uku kacal, ga iya girki, ga tsafta ga shagwaba sannan uwa-uba ta iya bi da shi a shimfida. Duk da karancin shekarunta."

"Suna tafe a kan hanyarsu ta zuwa gida daga airport tsakanin shi da Ammi kawai suke hira a motar, Fahimah tamkar ba ta gurin a motar, amma har cikin bargonta ta ke jin tasirin muryar Uwais har tsigar jikinta na tashi, suna isowa gida ko gama parking motar bai yi ba ta bude murfin motar ta yi cikin gida."

"Ta gilashin motarsa ya saci kallonta, sanye ta ke da jallabiya kirar Oman ruwan toka da mayafinsu. Kayan sun karbi choculate colour din jikinta sosai. Sannan ta yi dan haske irin na"

kamawar wanka a jikin mace mai tsafta.

Uwais ya dauke kai daga dubanta yana sakin tsaki a ransa. Mace sai fadin ran tsiya kamar

"diyar qaruna, nan kuwa diyar kwalin taliyar indomie ce."

"Maigadi ya sauke akwatunansu zuwa ckin gida. Da gudu Talatu ta fito tana ""oyoyo uwar dakina"", ta rungume Fahima wadda ke ta murmushi don ita ba ta kyalkyala dariya sam, murmushi kawai ta ke wanda ke maida ita kamar furen fulawa idan ta yi shi sabida bakin dadashin cikin bakinta da ke bayyana a duk lokacin da ta yi murmushi. Da taimakon Talatu suka kimtsa duk kayan da suka dawo da su a muhallinsu bayan Fahimah ta ware mata tsarabarta."

"Fahimah ba ta san cewa Uwais ya gaya wa Ammi washegari zai kawo Amrah ta yi mata barka da zuwa ba. Gajiyar tafiya ya sa ta koma barci bayan sallar asubah, ba ta fito ba sai karfe goma na safe, ta yi wanka ta shirya cikin wasu riga da wando pakistan ruwan dorawa, ta kame kakkarfan gashin ta da ribbon kanta babu kallabi, tana tsaye jikin dining tana decorating wurin da kayan kawata dining area da ta sayo daga Saudiyyah ta ji sallamar mace."

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: A hanyarsu ta dawowa Uwais tuki kawai yake ba ya ko kwakkwaran motsi har suka iso gida. Yana yin parking Fahimah ta fice, har tana tuntube saura kadan ta fadi, Uwais ya bita da kallon takaici, dakinta ta shige ta murza key. Ta jingina bayan ta a jikin kofar tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi."

Me ke shirin faruwa ne da rayuwar ta a yau? Ammi na son actualizing wannan auren a lokacin da daga ita har shi Uwais din ba su shirya ba.

A baya ta ce ne sai lokacin da suka shirya karbar juna a matsayin ma'aurata don kansu.

Abinda su duka biyun suka tabbatar ba mai yiwuwa bane. Amma yau kwatsam! Ta shammaci kowannen su a lokacin da suka riga suka sakankance cewa auren na su ba mai tabbata bane sannan ba zai je ko nan da can ba.

Yau Ammi ta dauko wata gagarumar rigima wadda baza'a ce rikicin tsufa yayi dalilin ta ba. Don kuwa bata yi tsufan da zata ce ta manta waye UWAIS ba? Kuma kuma yaya matsayin ita Fahimah yake a gare shi?

"Ta riga ta gama sakankancewa cewa auren ta da Uwais suna ne kawai, sannan a suna zai kare. Daga ranar da aka daura shi zuwa ranar da zai gaji da ajiyar sa ya bata takardar saki. Yau ina zata tsoma rayuwar ta idan ta bi Uwais zuwa inda bata san kowa ba? A gaban Ammi"

"ma ya ta kare da shi balle a bayan idon ta, karkashin mulkin sa da ikon sa?"

Kawai sai ta ji hawaye na zubo mata. Hawayen ba na komai ba ne na tausayin kanta ne. Namiji sai ana rarrashin sa ana kalallamar sa ana nusar da shi a kan ya so ta! Don kawai bata da iyaye kamar kowa! Ko da ya ke watakila Uwais na kin ta sabida kalar fatar ta ne idan ta yi la'akari da irin kalaman da ke fita daga bakin sa akan ta duk lokacin da ya bushi iskar izzar sa. Ita wace irin mara sa a ce a cikin mata? Kuma wace irin kaddara ke bibiyar ta? Daga maraici da rashin

asali. yanzu kuma zuwa BORANCI!

A wannan lokacin wani irin determination (kudiri) ya kutso ya shigi zuciyar Fahimah Shagari....

"Determination na self-defence and self-actualization; abin nufi ta tsaya ta san hakikanin kanta, ta kuma kare kanta daga farmakin zuciyarta akan Uwais; kada ta bari soyayyar Uwais dake dankare a zuciyarta ta kassara ta, ta zamo barrier ga farin-cikin ta da cigaban rayuwar ta, ta zubar da kimarta ta diya mace mai daraja a dalilin soyayya."

"Zata yi kokari iyakar yin ta, ta ga cewa ko ta ina aka je aka dawo ta baiwa Yaya Uwais mamaki sabani ga tunanin sa; she is not begging for his love. Hakannan komai nasa yanzu ya koma ba komai ba a idanunta (ya daina burgeta). Sannan duk yadda ta kai da son sa a baya, daga lokacin da aka sanar da ita an yi musu aure duk wani infatuation sai da ya kama gaban sa. Su ci gaba da zama a yadda suke a duk inda za su je ba damuwar ta ba ne matukar zata rike determination dinnan nata. Uwais ya rike duk abinda yake takama da shi itama daga yau ta koyi sarrafa kanta akan sa. Abinda Ammi ke fatan ya kasance insha Allah ba zai kasance ba, karewa ma ita yau ta fara period kuma sai ta yi kusan kwana hudu yake daukewa. Kuma an ce"

tafiyar ta kwanaki uku ce.

Tunanin hakan da ta yi ya sa ta jin wani irin relief a zuciyarta. Ta bar bakin kofar zuwa toilet ta sakar wa kanta shower mai dumi kamar yadda ake a al adarta kullum kafin ta kwanta barci. A duk lokacin da tayi hakan zata yi barci mai dadi ne har da saleba.

To yau ma hakan. Domin kwata-kwata ta cire damuwar tafiyar daga ran ta. Sai sake-sake da kintace-kintacen abinda zai faru.

"Bayan sallahr asubah ta sake wanka ta shirya cikin koriyar atamparta vlisco, ba ta san takamai-mai karfe nawa za su tafi ba, don haka ta kishingide a kan gado da zummar kafin cikar karfe takwas na safe ta sake bincikawa in ma tafiya yayi ya barta ta sani, tayi abinda ke gabanta."

Ai kuwa barci mai nauyi ya sadado ya yi awon gaba da ita. Don jiya tunani da sake-saken

yadda tafiyar ta da Uwais zata kasance kadai bai barta ta yi barci yadda ya kamata ba.

"Can! Cikin barcinta ta ji ana buga mata kofa da dan karfi, kamar za'a jijjigeta. Who is this?"""

Fahimah Ta tambaya cikin mamaki da mutstsike ido.

"Shiru ba amsa, tamkar da dutse take magana, nan jikin ta ya bata ko waye, saukowa ta yi daga gadon ta bude kofar don ganin wanda ke mata wannan bugun kamar ana binta bashi."

"Uwais ta gani harde da hannuwa a kirji sai huci yake kamar mesa, ya hade cikin jamfa da wando na wani tattausan voyel sky blue, as usual hular kansa ta nitse cikin tsakiyar sumar kansa. Wani kallo ya yi mata kamar fararen kwayar idanunsa za su fado don harara, sannan ya nuna mata agogon hannunsa."

Are you aware ? an lika min ke kuma zaki bata min lokaci ki ka shige daki kina ta barci?

Me za mu ci kafin mu bar gida ko ni ki ke jira in je in girka miki? ?

"Fahimah ta tsuke baki, sannan ta murguda shi gefe ta rabe ta gefensa ta wuce zuwa kitchen ba tare da ta tanka masa ba. Ya saki baki yana kallonta da madaukakin mamaki har ta shige kitchen, shi ta ke murguda wa baki?"

Girgiza kai ya yi ya bi ta kitchen din. Cikin hargagi yace.

" You Goddam Black, 15 minutes na baki ki sama min abin da zan ci, bana hawa jirgi ban ci komai ba, cikina hautsinewa yake yi ?."

"Fahimah dai bata amsa ba, ta baiwa banza ajiyar sa, sai kokarin kunna heater din dafa ruwan zafi da ta ke yi. Da alama so yake ta tanka ya ji dadin bata mata rai, ya ci mutuncin ta a banza bata da mai tare mata, to ba za ta tanka shi ba. Don an ce karfe daya baya amo."

" Irin ga dan iska din nan ko, ina magana kin bai wa banza ajiyata? ?"

"Fahimah ta ga in ba ta amsa ba zai iya yin zuciya ya shigo ya makure ta, ko ya samu ya huce"

"haushin manna masa ita da Ammi ta yi, ga shi su biyu kacal a cikin gida babu mai ceton ta. Sai ta ga gara ta tanka, don ya san ta daina tsoronsa yanzu, kuma tana iya mallakar kanta a gabansa. Sannan ba zamansa take yi ba zaman Ammi take yi."

Don Allah ka sarara min mana! Kafin 15 minutes din ma zan kawo ?. Ta fada ciki-ciki

kamar mai kunkuni. Babu tabbacin ya ji ta ko bai ji ta ba. Tsiwa take so tayi masa amma tana tsoro.

Fatanta ya bar mata kicin din. Ko ta samu ta saita bugun zuciyar ta. Kada tayi abind ta saba yi a gaban sa.

"Tsayuwarsa a wurin na maida ita unease, jikinta ya ki sakewa ya yi aiki yadda ya kamata. Kamar wadda ke cikin sanyin kankara a dalilin kasancewar sa a wurin tare da ita. Daurewa kawai take yi don tsira da determination din ta akan Uwais Shagari."

"Amma ga mamakinta Uwais ya ki tafiya, karewa ma shigowa ya yi kitchen din ya haye kan island ya yi zamansa. So yake ya gargasa mata magana ko yaya ne kafin ya yarda ya dauketa su tafi, wadda har ta koma ga mahaliccinta ba za ta mance ba ya sonta ba."

"""Yanzu ke kin yarda Ammi ta rusa miki rayuwa da mijin da ba ya sonki, bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba? Me ya sa ba ki yi wata hobbasa don kwatar wa kanki yanci ba? Ba ki da masaniyar ina da mata ne, wadda nake matukar so kamar na ba ta raina? ?"

"Tunda ya fara maganar Fahimah ba ta dago ba, firar dankali ta ke, amma da ya zo sentence dinsa na karshe sai ji ta yi ta tafi da tsokar hannunta, wato ta yanke hannunta da kakkaifar wukar da ke hannunta."

" Ina da matar da nake so, kamar na ba ta raina ?."

"Wani statement ne wanda shi a wurinsa ba komai ba. Amma a gare ta tamkar digar ruwan dalma ne a kan fatar jikinta. Tana so ta ba shi amsa, daidai da wadda ta dace da munanan maganganunsa sai ta tuna UWAIS ne. Wani kwayan mutum guda daya da zuciya da ruhinta ke so, wanda ta yi wa kanta alkawarin zama da shi da kasancewa tare da shi against all odds koda zai yi ta yankar tsokar naman jikin ta yana sanyawa a miya albarkacin Ammi Safeeyyah - Basudaniyyah. Balle common bakar magana akan matar da yake so."

"Sai ta saki wukar da ke hannunta kasa, hade da dankalin ganin jini yana fita. Ta kudire ko dukanta Uwais zai yi cikin gidannan ba za ta soya masa dankalin nan ba, ko dai ya tafi da yunwarsa, ko ya kirawo matar da zai iya bai wa rai ta soya masa daga Malaysia."

"Ta kashe komai ta wuce ta gabansa hannun ta nan digar jini ba tare da ta ce da shi komai ba. Murmushin mugunta ya yi, ko ba komai ya ci nasara, ya yi spoiling mood dinta ita ga amarya zata bi miji Ikko, ta samu miji a bagas sabida ba Amrah, kuma gashi ya janyo ta yanke hannu. Sai yaji bai ji dadi ba daga kasan ransa saboda ko kadan ba ya son ganin jini ko yaya daga jikin dan Adam. Don haka ya sauya shawara ya bi bayanta zuwa dakinta ba tare da ta san ya biyo ta"

ba.

"Toilet ta shige ta sakar wa hannun famfo a sink, tana kalon jinin jikin ta na gudu treda ruwan tana hawaye, sai jin motsin mutum ta yi daga bayanta. Da sauri ta juya a tsorace, ashe har ya iso gab da ita sai da ta bigi kirjinsa. Da sauri ta ja baya. Dan farin bandeji ne a hannunsa na nade ciwo da ruwan hydrogen, daya dauko a dakin Ammi, sabida bata wasa da first aid ita, ba tare da ya ce komai ba ya kama yatsan ya zuba hydrogen a kan yankan, sannan ya soma"

kokarin daurewa da bandejin.

"Fahimah, ta kusa suma a wannan lokacin sabida kyakkyawan closeness din da ya shiga tsakanin ta da Uwais. Wanda hakan bai taba faruwa ba koda da kuskure. Ita da Uwais sai kallo daga nesa. Wani irin sassanyar kamshi yake yi na Maison Francis (Baccarat Rouge) dake tashi a hankali daga jikin sa. Shi kuwa Uwais bai yi don wata manufa ba, sai don tunawa da ya yi da kalaman Ammi."

Fahimah amanar Allah ce tsakaninmu Uwais ? na ba ka amanarta ? idan ka cutar da ita

kai da Allah ?.

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ita in wani ne ya gaya mata a baya cewa Uwais na magana haka ma, ba za ta taba yarda ba. He is not that miskili to such an extent kamar yadda ta dauka a baya, kawai dai magana sai ya ga damar yin ta, kuma in ya so yana yin abar sa sosai ko da bazaka bashi amsa ba. Uwais Shagari, ya fara sassauta wa ransa kiyayyar Fahima a bisa dalilai da dama....."

"Muhimmi shi ne, ganewa da ya yi ita din is a source of geniune happiness na mahaifiyar sa wadda in ya zauna da ita ko da ba ya kyautata mata in disguise Ammi za ta yi ta farin ciki da shi ne, tareda sanya masa albarka."

"Sannan auren su wani abu ne inevitable (wanda ba makawar sa) wanda bazai iya tsallakewa ba, watakila har abada, don ba zai taba iya mikawa Ammi takardar saki ko ta wata mace daban, balle wannan wadda take so kamar ita ta haifa ba."

In haka ne kenan takurawa rai da kiyayyar da babu riba a cikin ta aikin banza ne.

Zai zauna da Fahimah koda har abada ba zaya so ta ba. Sai ta zauna zaman Ladan Noma (as he called it). Tunda haka Ammi ta zaba mata.

"A kullum yana tuna dawainiyar da Ammi ta yi da shi tun yana yaro, da dawainiyar ilminsa a bayan ran mahaifinsa ba tare da taimakon kowa ba. Ita ke kaishi makaranta ta dauko shi tun daga primary har secondary bata yarda kowa yayi mata wannan aikin."

"Yau ga shi yana ta cin gajiyar ilmin ta ko ina, sannan ta bar shi ya auri Amrah duk da yakinin"

"da yake da shi na ba ta sonta, amma ta kwatanta adalci ko a fuska ba ta taba nunawa Amrah ko wani ba."

"Ammi na da wasu irin principles (doctrines) akan akan karan-kanta, wadanda ta dora Fahimah a kai, wanda su ne ta ke masa kwadayi, amma ya kasa ganewa da gangan. Yana can ga"

"kyale-kyalen da baya lasting. Tana da tabbacin watarana zai gane din, tana raye ko bata raye, cewa Fahimah matar rufin asiri ce kuma babban alkhairi a gareshi, har ma ya zo ya gode mata"

da dukkan godiyar da zai iya. What he needs most is time and closeness ga Fahimah.

"Bayan fitarsa Fahimah ta ga ya dace ta sauya sutturar jikinta ko da ba ta yi kwalliyar da Ammi ke so ba, don haka ta yi wankanta a nitse, da Olay shower gel (goats' milk), ta fito ta zauna shafa, sannan ta fiddo wani jan material da aka yi wa fitted gown ta sanya, yana da ratsin golden da baki a jikinsa. Ta yi daurin kai ya zauna cif, sannan ta matsa gaban mudubi tana duba turarukan da Uwais ya ajiye a wajen har guda uku. Ashe sunan turaren Uwais ke nan (Maison Francis, Baccarat Rouge)."

"Kwarai ta dade tana son kamshin, domin kuwa kamshinsa na mannewa a zuciya ne tamkar maganadisu, musamman ga ruhin diya mace ma'abociyar soyayyar da bata samu martani ba. Ba ta san lokacin da ta kai turaren ga bakinta ta sumbata ba, and it feels like ?.. like Uwais din"

"himself ta ji ta sumbata apparently. Wanda hakan ya aika wani irin sako cikin ruhinta, wanda ta ji"

shi tun daga kwakwalwa har zuwa toe wato babban yatsar kafar ta.

"Something like emotion mai narka zuciya, da sanya wani irin daddadan feeling Fahimah ta"

"shiga waiwaye ko da wanda ya ga abun kunyar da ta yi (sumbatar turaren Uwais). Ga dukkan taimakon Allah, sai ya kasance babu kowa. Daga ita sai Ubangijin ta kadai, sune kuma kadai suka san adadin son da ta ke yi wa Uwais Shagari. Tana kuma rokonSa Azza Wa Jallah a kan in son da ta ke yi wa Uwais, ba alkhairi ba ne a gare ta to ya yaye mata bakidaya ko ya sassauta mata."

Akuyar cikinta ta yi kukan da ke tuna mata rabonta da abinci tun jiya. And cikinta na da nasa hakkin a kanta ba soyayyar Uwais kadai ba. Wadda ta zamo mafi rinjayen abin da ke consuming lokacin ta.

"Idan ta lula a duniyar tunanin Uwais, ba ta sanin cewa lokaci na tafiya, sai ta farga da awannin da ta karar ba tare da ta san me ta ke yi ba. Hormones dinta suna da karfi, da ba su sabbaba mata ciwon tunani a kan Uwais ba."

"She then decided to pray ? wato ta yanke shawarar komawa ga addu'a akan Uwais Shagari, tunda an ce addu a maganin komai ce."

"Addu'ar data dukufa yi a yau itace. Idan son da ta ke wa Uwais alkhairi ne, Allah ya juyo da"

"hankalinsa kanta cikin gaggawa. Idan ba alkhairi ba ne a gare ta, Allah ya nesanta zuciyarta daga kansa Ya raba ta da wannan koshin wahala."

Karfe biyu aka kawo mata abinci mai rai da motsi taci sama-sama daga nan kuma barci mai

"dadi ya dauke ta, barci sosai ta yi wanda ba ta farka ba har Uwais ya dawo."

"Karar sautin talabijin shi ya sanar da ita dawowarsa. Da ta bude ido ta dubi inda yake zaune yana shan lemun power horse daga shi sai farar singlet da dogon wandon suit din da ya cire. Jikinsa ne ya gaya masa tana kallon shi, ya juya ya sakar mata harara a ran shi yana fadin ta kafe shi da ido kamar mayya, ko sun hada jini da maitar ma wa ya sani ne? Kunya sosai ta ji da ya kama ta kane-kane a cikin kallonsa."

Are you not praying ne ke? (Ke ba kya sallah ne)? Tunda muka zo ban ga kin dungura

"goshinki gaban Ubangiji ba, sai kallon mazan mutane kamar kya cinye su? ?"

"Fahimah ta tsuke baki da fuska cikin bacin ran kalaman sa, sannan ta mike daga kwanciyar. Ya dan bi ta da kallo tana wucewa ta gabansa, sai ya ji kamshin turaren

Please Login or Register in order to submit comment