gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FAHIMAH Gaskiyar Da Aka Ɓoye book 1 By Takori Kabara Chapter 4 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama ta yi tunani mai zurfi a kan auren Fahimah zai zamo kalubale mai girma ga rayuwarta. Don haka hukuncin Ammi shi ne daidai ko da mata goma Uwais zai aura in dai zai hada da Fahimah hankalinsu ya kwanta."

"Talatu ta zarce matsayin 'yar aiki a gare su don ko kudin aiki ba ta karba, shekara da shekaru"

sai ihsanin da Ammi ta ga damar yi mata. Ta zame musu kamar 'yar uwa ta jini.

******

"Aka ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya. Kwanakin daurin aure na matsowa, soyayya gangariya na karuwa tsakanin Uwais da amaryarsa Amrah talkless of Fahima da ba ta cikin lissafin sa."

"Ya kama gobe daurin aure, wanda za a yi a gidan Alh. Umar Dikko na Kano, tun jiya kawu Shureim da manyan 'ya'yan sa biyu Mahdi da Mohamed da kannen Ammi biyu su biyar kenan suka iso daga Khartoum, sai mutanen Shagari kwansu da kwarkwatarsu. Duk Uwais ya yi musu masauki a gidan saukar baki na Tahir Guest Palace. Yana zaune a kujera gefen Ammi, sanye cikin wani lallausar voyel milk colour kansa babu hula, sumar nan ta kara kwanciya sosai, ta kuma kara cika da yawa domin ya dade bai rage ta ba. Ammi na daga gefensa tana shan shayin da Fahimah ta dafa mata ta kule a daki musamman da ta san Uwais zama zai yi a falon."

"Wayoyin jama'a yake ta amsawa kala-kala, duk a kan shirin daurin auren gobe. Sai da Ammi ta"

fahimci ya tsagaita da amsa wayoyin ta kira sunansa.

"""Uwais!""."

Ya dago lumsassun idanunsa ya dube ta.

"""Gobe nan ne wurin haduwa (meeting point) na daurin aure kafin ku tafi gidan su yarinyar?"" Ya amsa mata da ""Eh, Ammi""."

"Ammi ta ce, ""tam... To aurenka da Fahimah za a fara daurawa, ina nufin Fahimah ita ce za ta zama uwargida, sannan a yi na ita MATAR SO""."

"A yadda ta fadi maganar cikin shagube ya yi bala'in touching dinsa. Sai dai ya yarda da abin da ta ce din, ""Eh, Amrah matar so ce, ta ki 'yar kuwa matar shige wadda anka ce ba ta daraja sam""."

"Bai ba ta amsa ba sai ma tashi da ya yi ya bar wurin. Ta san za a rina, da ma ba ta tsammaci ya tankata ba, umarni ta bayar kuma dole a bi in ana son zaman lafiya."

"Ta kira Kawu Shuraim da madaurin aurensa su Baffa Haruna duk ta gaya musu hakan, su Baffa"

"Haruna sun yi mamaki matuka, amma da Kawu Shuraim ya yi musu bayanin komai sai suka fahimta."

"Washegari kofar gidan Late Grand Khadi Abdulkarim Shagari ya dinke da jama'a ko ta ina, musamman ma'aikata GT na Kano. Aka daura auren Fahimah Abdulkarim Shagari da Uwais Abdulkarim Shagari a kan sadaki mafi kankanta amma mafi albarka. Daga nan suka zarce gidan Alh. Umar Dikko aka daura na Amrah Umar Dikko da Uwais Abdulkarim Shagari."

Daga nan shi da ma'aikatansa da abokansa suka wuce liyafar cin abinci ta bayan daurin aure

"wadda abokai suka shirya karkashin jagorancin Jabeer, a gidan saukar baki na Ni'ima."

"Uwais farin cikin da yake ciki a yau ba zai misaltu ba, biro ya yi kadan ya bayyana shi. At last ya mallaki AMRAH so duk wani kalubale, duk wani bacin rai zai zamanto nafilah."

"Suna fitowa daga wajen liyafar ya kebe kansa a gefe, Amrah ya kira."

"9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Cikin wani yanayi ta ganta tare da Yaya Uwais, yanayin da ya fi kama da muamalar auratayya it is something which goes far beyond mere explanation..da"

"fatar baki but extent reality cikin idanunta, kamar ido biyu ba mafarki ba; mafarki ta yi ma ga ta a matsayin matar Uwais, sabida abinda ta gani yana faruwa cikin mafarkin ta sani baya yiwuwa sai da aure. A karshen mafarkinta kuma ta ga yaya rututu zagaye da su, wadanda har ba ta iya"

kirga su ba sabida yawansu ya cika dakin da suke ciki.

"A matukar firgice fahimah ta farka, jikinta ba inda ba ya rawa, a karshe ta mike zuwa toilet ta sakarwa kanta shower ta ruwa mai dumi ko ta samu karkarwar da jikinta ke yi ya tsaya, ko ta samu ta yi regaining consciousness dinta. Barcin da ba ta koma ba kenan har rana ta fito."

"Tana kwance lamo a cikin bargo, ta kasa fita taya Talatu aiki yadda ta saba, kasancewar yau"

"lahadi ba ta da makaranta, kuma ta yi sallar asuba da azkar dinta na safiya, sai kawai ta ci gaba da kwanciyarta."

"Karfe goma na safe Uwais ya fito daga bangarensa zuwa sassan Ammi, ya same ta tana sallar"

"walha, sai ya samu gefen gadonta ya zauna yana tsumayinta har ta idar, ta yi addua suka shafa"

tare.

"A yadda Hajiya Safiyya ta ga fuskar Uwais yau, tana wani irin annuri ta tabbata yana dauke da labarin da ya faranta ransa. Ya sauko daga gefen gadon ya dawo daidai kafafun Ammi ya zauna. Ko daga irin zaman da ya yi Ammi ta fahimci muhimmiyar magana ta kawo shi."

Ya ya aka yi ne ka zo ka sa ni a gaba yau Lahadi ma me ya fiddo ka da wuri haka? Na dauka duk lahadin karshen mako sai sha biyun rana ka ke fitowa?

"Uwais ya gyara zamansa sosai ya ce, Ammi na kasa barcin ne, sabida ina cikin farin ciki, Amrah ta amince min in tura magabatana a yi maganar aurenmu. Ba sai ta kare karatu ba."

"Ammi ta dube shi da sakakken baki, idonta na wani irin budewa ta ce, Wace ce haka?"

"Kansa a kasa ya ce, Yarinyar da na ke nema, kanwar Jabir, na dade da gaya miki ina neman aure."

"Hajiya Safiyyah ta yi masa wani irin sakaran kallo, ta ce, Uwais! Da kakkausar murya. Da sauri ya dago ya dube ta cikin tsananin fargaba."

"Ta ce, Ba kanwar abokinka ba, ko kanwar shugaban kasa ce ban yarje maka aurenta ba. Mace ko da zubarjadu da yakutu aka kera ta haka za ta ganka ta barka, don tuntuni kana da matarka. Kalaman karshe tamkar saukar alburushi ya ji su a kirjinsa. Hajiya Safiyyah ta ci gaba da cewa, Da ma na zuba maka ido ne in ga iya gudun ruwanka, wannan rawar kan da ka ke a kan yarinyar nan kadai zai hana ni yarda da batunta, don na san muddin ka aure ta ba za ka taba yi wa FAHIMAH adalci ba!"

A matukar razane kuma a firgice Uwais ya dago ya dubi mahaifiyarsa. Fahima? Fahimah! Fahima!! A ina ya taba jin wannan sunan???

Kamar kullum yana jinsa cikin gidan nan. Daga bakin Talatu da Ammi. Cikin wani irin rashin kuzari yake kallon mahaifiyarsa.

"Ammi, I didnt get you right, wallahi ban gane maganar da ki ke yi ba."

"Hajiya Safiyyah ta mike tsaye tana nade sallayarta, In ma ka gane ai cewa za ka yi ba ka gane ba, sabida rainin hankali irin naka Uwais, tunda dai ni da Hausa na yi maganata. In hausar ce ba ka ji sai ka je ka nemi wanda zai fassara maka."

Ta fice daga dakin ta barshi nan a zaune.

"Uwais ya ci gaba da zama a inda ya ke tamkar an kafe shi. Kokari yake ya yi digesting maganganun Ammi cikin kwakwalwarsa abu ya gagara. Allah ne ya kawo Talatu wadda yake kira ""Baba Talatu"" da tsintsiyar kwakwa a hannunta za ta yi wa Ammi shara. Ta ganshi a zaune kamar statue, ta ce, Uban masu gida tunanin me ake haka?"

"Can tsakiyar kansa ya jiyo muryar Baba Talatu, ji ya yi tamkar mai fassarar da Ammi ta ambata ce Allah ya kawo masa."

"Talatu couldnt believe cewa muryar Uwais ce ke yi mata magana, sabida yadda ta sirance ta"

"zaftare, duk wani thickeness da huskness da ke cikinta ya tafi."

Baba Talatu idan aka ce mutum tuntuni yana da mata me ake nufi?

"Tambayar ta bai wa Talatu dariya, ta ce, Ubangidana ana nufin yana da matar aure ko? Abin da ban fahimta ba shi ne, an yi auren ko za a yi ne nan gaba?"

"Uwais ya hadiyi miyau kamar ya hadiyi kunama, ya ce, Baba Talatu wace ce FAHIMAH?"

"Talatu ta kai idonta da sauri ga hoton Fahimah da ke gefen gadon Ammi daidai inda ta ke saka kanta. Ta ce, Uban masu gida, Fahimah ai daya muke da ita, kuma daya muka sani wata ce ban da abokiyar haihuwarka? Ina nufin Fahimah ta gidan nan, autar Ammi."

"A lokacin ne kwakwalwar Uwais ta soma daukan caji, ya ji wani irin bacin rai da bakin ciki sun zo sun tokare shi a kahon zuci. Bai yi aune ba ya ji cikinsa na hautsinawa Talatu ba ta ankara ba sai ganin Uwais ta yi yana kelayo amai a tsakar dakin Ammi. Amai sosai ya yi kamar zai amayar da yan hajinsa. Talatu sai faman sannu ta ke masa ya tashi yana rangaji ya bar dakin ba tare da ya karbi ruwan da ta kawo masa daga firji tana fadin ya wanke fuskarsa ya kurkure baki ba, zai ji dan dama-dama."

"Ta gaban Ammi ya wuce fuuu tana zaune a falo, ko kallon fuskarta bai yi ba ya wuce, abinda bai taba yi ba. Ammi ta kyabe baki ta dauke kanta daga bayan sa. Ba don aikinsa ba yau zai bar garin. Tafiyar da sai Ammi ta janye mummunan furucinta sannan ya dawo. To Banki ba su san excuse ba. Yau yayi nadamar zabar aikin banki matsayin career din sa. Amma ya kudire a ransa cewa Ammi ta samu matsala irin ta cutar dimentia wadda tsofaffi ke fama da ita. Zai yi"

kokari ya nema mata magani.

"Tun daga ranar gidan ya koma wani iri ba dadi, kowa ba ya cikin walwala. Ammi ranta a mugun bace yake da maganar auren da Uwais ya rakito, Fahimah ciwon so ya gama kassara ta, ya karar da kuzarinta, ya tafi da duk wani karsashi da ta ke da shi a cikin gidan ko falo ta daina fitowa."

"Yayin da Uwais yana can yana neman mafita, ga balain da ke shirin tunkaro shi yo bala'i mana! Rashin Amrah ai catastroph ne, haka zancen da Ammi ta yi (abin amai), shi ma babban balaI ne a gare shi. Don in ya tabbata Ammi ba ta da dimentia kuma tana nufin abin da ta ke fadi ne har zuciyarta wace irin mafita zai nema wa kansa ba tare da ya fada fushin Ubangiji ba?"

"Ammi ba uwa ba ce kadai, Uba ce, dangi ce, abokiya ce komai ce a gare shi, amma ba zai iya yi mata wannan uzurin ba, ko da duk duniya za ta taru a kanshi. Zai iya hakura da Amrah in"

"abinda auren ta zai janyo masa kenan, amma auren Fahimah sai dai ayi da gawar sa."

******

"Walwalar gidan duk sai ta ragu, kowa yana dakinsa kullum, Talatu ce kadai ke shige da fice don tsaftace muhalli, abinci sun daina ci tare a dining yadda suka saba, sai dai ta kai wa kowa dakinsa, ta kuma lura ko ta kai din ba wani cin kirki suke masa ba kamar da, musamman Uwais ko tabawa ba ya yi, in ya fice tun bakwai na safe sai bakwai na magriba ko a ofis coffee kawai yake sha wanda yake hadawa da kansa."

"Amrah ta koma Malaysia tuntuni, kullum suka yi waya tana jin muryar Uwais ba yadda ta saba jinta ba, ko da ta tambayi dalili sai ya ce mata,"

Aiki ne yake masa yawa.

"Yanzu ya rage zuwa gidan Jabir tun bayan komawar Amrah, tsiya iri-iri Jabir ya masa amma sai dai kawai ya yi murmushi ya ce, To me zan zo in yi maka, kai ma ka san ba don kai nake zuwa ba."

Ko kusa bai gaya masa yana da matsala da Amminsa a kan maganar Amrah ba.

"Yau yana ofis kawai wani tunani ya fado masa, Kawu Shuraim. A kasar Sudan, shi ya fado masa a rai, Yayan Ammi da suke uwa daya uba daya, kuma wanda Ammi ba ta iya tsallake"

maganarsa.

"Wata ajiyar zuciya Uwais ya saki, ya mika hannu ya dauko wayarsa a kan tebir din gabansa ya lalubo lambar Kawun nasa."

"Uwais na nan da larabci zam a bakinsa, don Ammi tana yi masa sosai tun yana yaro. Sannan akwai aminci sosai tsakaninsa da Kawun nasa don yana yawan yi masa alkhairi ba tare da sanin Ammi bama. Shi kadai ya rage babba a family din su Ammi, ya manyanta, ragowar duk kannenta ne maza da mata."

"Suka gaisa sosai da Kawun, shi da kansa ya tsinkayi damuwa a muryar Uwais, ya ce, Uwais gaya min ko me ke damunka, insha Allahu za'a samu mafita."

"Uwais ya runtse idonsa ya ce, Kawu, matar aure na samu wadda nake so, daidai da ra'ayi na, mai duk qualities din da nake bukata a matar aurena, ina sonta sosai, kuma ta amince min in turo magabatana yanzu haka."

"Da na zo na gaya wa Ammi, sai ta kawo wani batu wanda har yau na kasa daidaita maanarsa a kwakwalwata. Kawu, na dai fahimci wai ta yi min mata ne already, imagine Kawu da wannan"

tsintacciyar magen da ta dauko a gidan marayu.

Yaa Subhanallah!

"In ji kawu Shuraim cikin kakabi. Ya ce, Ita Safiyyar da hankalinta za ta aura maka wannan bakar yar mara asali? Kamar matan Sudan da na Najeriya sun kare?"

"Uwais ji ya yi kamar Kawunsa ya yayyafa masa ruwa a kan wutar da ke tiriri a kirjinsa, ya ce, Kawu na saya maka tiket, don Allah ka zo a yi ta ta kare. Kai kadai ne last hope dina Kawu, don Allah ka taimaka min ka gaya wa Ammi ta aura min mata hudu a rana daya in dai da Amrah a ciki, amma ta cire wannan yarinyar a cikin su zan iya hadiyar zuciya na mutu."

"Da sauri Kawu Shuraim ya ce, Zan zo cikin satin nan insha Allahu, abin bai kai haka ba, ka"

kwantar da hankalinka.

"Ammi ba ta san me suke kullawa shi da Kawunsa ba. Yanzu ta fara maida walwalarta tana harkokinta cikin gida, amma ta cire Uwais daga shirginta, musamman da ta lura shi ma ya dauki gaba da ita. Damuwarta yanzu a kan Fahima ne, wadda ke ta faman ramewa babu gaira babu dalili, kuma ba ta son cin abinci. Ga jarrabawarsu ta barin sakandire na tunkaro su."

"Wajen karfe goma na dare, Ammi har ta yi barci ta farka, so ta ke ta binciki halin da Fahima ke ciki a daren nan. Ta sauko daga gadon ta a hankali ta daura laffayarta kamar wadda za ta unguwa, sannan ta nufi dakin Fahimah."

Tun daga bakin kofa ta ke jiyo shesshekar kukan Fahimah ta karasa da sauri ta murda kofar ta shiga. Ta kifa kai a kan filo ta dunkule jikinta sai kuka ta ke. Sai jin muryar Ammi ta yi a kanta. Fahimah! Yau sai kin gaya min abin da yake damunki. Wani ke yi miki abin da ba ki so cikin gidan nan ko kuwa kin gaji da zama da ni ne?

"Fahimah ta dago a hankali cikin tsananin faduwar gaba, ba ta taba tsammanin Ammi a wannan lokacin ba, she will never shed tears a gaban Ammi, don haka tashin hankalinta a yanzu shi ne ganin kukanta da Ammi ta yi fiye da damuwar da ta ke ciki."

"Hajiya Safeeyyah ta zauna a gefen gadon ta ce, Fahima ta ba ki da wanda ya fi ni duk fadin"

"duniyar nan, don haka daure ki gaya min ko mene ne damuwarki, na yi miki alkawarin sai inda"

"karfina ya kare wajen sama miki farin ciki, don ke amana ce a hannuna fiye da wannan yaron, kuma amanar ce tsakanina da ke, ki gaya min ko mene ne Fahimah ta."

"Fahima ta riga ta kudire a zuciyarta sai dai ciwon son Uwais ya yi ajalinta, amma ba za ta taba furta hakan ga kowa ba balle mahaifiya a gare shi. Idan ta tursasa shi ya aure ta to ta kai shi ina? Mutum gashinan kamar malaikan daukar rai wane dadi mace za ta ji a aurensa? Macen ma wadda ya fi tsana fiye da kowa a duniya?"

"Don haka ta soma tunanin abin da za ta fada wa Ammi ba tare da ta sanya mata kokonto ba. Abubuwa da yawa na damunta, not only UWAIS SHAGARI. Tana son sanin asalinta, tana son sanin su waye suka yi sanadin zuwanta duniya. Ammi ba ta son tambayar nan ko kankani, amma yau dole da ita za ta bi ta kare kanta da mutuncinta a idanun Ammi Safiyyah."

"Ammi, babu ciwo mafi muni ga dan Adam irin a ce ba ya da asali, bai san su waye suka haife shi ba, bai san shi dan sunnah ne ko shege ba. Ammi ko ba ki fada ba na dade da ganewa, orphanage da muke zuwa shi ne gidanmu, shi ne asali da tushe na, a can ki ka dauko ni."

Ta karasa cikin wani irin kuka da ya keta har cikin zuciyar Hajiya Safiyyah.

"A yau ita kanta Ammi ta rasa da kalaman da za ta lallashi Fahimah, ta fahimci irin ciwon da ta ke ji a ranta, kuma ba ta isa ta warkar mata da shi ba. Kama ta ta yi ta rungume a jikinta ta ce, Fahima, in kin yarda ni ma UWA ce, sannan kokarina ya kai na kowacce UWA, to ki dubi Allah ki cire wannan damuwar daga ranki. Im your mother, father and Uwais is your brother. Ki sani babu wanda rayuwa ta ke cikakka a gare shi, babu kuma wanda Ubangiji ba ya jarraba in one way or the other."

Mumini an sanshi da karbar kaddarar Ubangiji da kasancewa cikin godiyarsa ala kulli halin. Wannan damuwar da ki ka sanya kanki babu abin da za ta janyo sai nakasu ga lafiyar zuciya da kwakwalwar ki.

"Insha Allah wata mai kamawa za mu je Umrah mu yi ibada mu nemi kusanci da Ubangiji, za ki"

samu sukunin zuciyarki insha Allahu.

"Haka Ammi ta yi ta lallashin Fahimah, da kalamai masu dadi da nuna kauna har sai da ta sanya"

murmushi a kan fatar bakinta.

******

"9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: Kafin muryarsan nan mai tada tsigogin jikinta ta biyo baya. A yau har wani kauri ta kara mai nuna ya zama cikakken mutum. Wanda ya gama mallakar duk abinda da Da namiji ke bukata a rayuwar sa. Ta juya a hankali ta dube su da fararen idanunta suna shigowa, hannun su cikin na juna sun yi balain dacewa da juna, kyau na bugun kyau. Ko hasidin iza hassada ya kalle su sai ya yaba su a ransa. Wani abu wai perfect match. Da gaske KISHI gaskiya ne a tare da kowacce diya mace, kuma Fahimah ta ji shi a kirjinta har fiye da misali, yau ga ta ga matar Uwais! Wadda ta dade tana kimanta zuwan ranar haduwar su da juna, amma murmushin da Amrah ta yi mata da innocence looks dinta sun sanya Fahimah mayar mata da martanin murmushinta. Ta kuma amsa sallamarta. Sannan ta maida kai ga abinda take yi bata kara kallon su ba."

"Uwais kamar ya fashe don bakin ciki don bai so Amrah ta ganta ba shiyasa ya kawo ta da safe, lokacin da ya tabbata tana barci. Bayan sun wuce falon zuwa falo na gaba Amrah ta juya tana"

"kallonsa da sigar da ta ke kallonsa, wadda ta bambanta da yadda ta ke kallon kowa, ta ce,"

Ina ku ka samo kyakkyawar budurwa haka? Ba ka taba gaya min kana da sister ba. Cikin harshen Turanci ta yi maganar.

"Fahimah daga inda ta ke tsaye tana jiyo shi yana bai wa matarshi amsa da cewa, Mai aikin Ammi ce."

"Suka wuce turakar Ammi, Amrah na waiwayonta tana ta mata murmushi, sai ta samu kanta da kasa maida mata martani sakamakon zuciyarta ta yi bakikkirin da jin amsar da Uwais ya bayar a kanta. Daga bisani ta yi murmushi mai ciwo, cikin ranta ta ce, ban da abun ki Fahimah, don Uwais ya ce ke yar aikin gidansu ce ai ya kara miki matsayi, tunda bai ce da matarsa tsinto ki suka yi a gidan marayu ba. Maganar a ce ita matarsa ce ma ba ta taso ba."

"Ta ci gaba da daukar aure a tsakaninsu a matsayin shifcin gizo, zai fi mata sauki; wato irin almarar nan mai zuwa ta wuce wa dan adam yadda kowacce almara ke zuwa ta wuce, haka aurenta da Uwais zai zo ya wuce ba tare da ya zama actual reality ba."

"A hankali ta zame jiki daga wurin zuwa dakinta tana cewa cikin ranta, ina ma ita ce Amrah? Watakila da ita ce ke da kyan da Amrah ke da shi da Uwais ya so ta. Ta yi maza ta kwabi zuciyarta a kan hakan."

"Shes proud of her own beauty no matter what, watakila ko da ta fi duk matan duniya kyau asalinta ma kadai ya isa ya sa Uwais ya kyamace ta. Don haka Fahimah ta soma kallon aurenta da Uwais a matsayin dabaibayi rather than defensive kamar yadda Ammi Safeeyah ke kallonsa. Anya kuwa tunani da tsinkayen Ammi a kansu daidai ne? Ta yi ta zama da igiyar auren Uwais a kanta kenan don kawai a kira ta matarsa? Anya auren bai zame mata dabaibayi ba ya hana ta yancinta na yammatanci? Ko da ta ke yar gidan marayu in da Ammi ta yi hakuri ba za ta rasa me sonta a duniya ba, ko ta auri orphan dan uwanta a gidan marayun, soyayyar da zuciyarta ke yi wa Uwais da ma mai zaman kanta ce. Da Ammi ta yi hakuri ba ta yi amfani da karfin ikonta na uwa ba wajen ganin Uwais ya aure ta ba, da sannu za ta iya overcoming dinta (rinjayarta)."

"Haka ta yi ta saka da warwara ita kadai a daki tanajuyejuye akan gado, idan ta ce ta yi watsi da alamarin Uwais, idan tsautsayi ya gifta suka hadu ko yaya ne, tofa dole sai zuciyarta ta motsa. Daga nan ta gane cewa soyayyar gaskiya abu ce da zuciya ba za ta iya kaucewa ba. Saidai ayi mata pretending. Amma daga yau da Uwais ya gaya wa matarsa ita yar aikin gidansu ce, daga yau za ta soma yaki da duk wata soyayyar UWAIS daga zuciyarta, ko da kuwa da karfin"

addu'ah ne.

******

"Amrah ba ta samu wata special reception daga Ammi ba, daga gaisuwa shi ke nan, ta ce, In ce ko ba matsala?"

"Amrah ta ce, Babu Ammi. To Allah ya yi muku albarka."

"Daga haka ta shiga wata hidimar a daki. Ta dai fahimci Amrah za a zauna lafiya da ita daga dukkan alamu, bata da kwaramniya kuma bata da girman kai ba kamar sauran yayan masu kudi"

"irinta ba, shes very simple a cikin muamalarta da kowa."

"Tunda suka dauko hanyar komawa gida, Amrah ke zubo wa Uwais tambayoyi duk kuma a kan Fahimah, shi kuwa komai ta tambaya cewa yake bai sani ba. Yadda ta ga yarinyar shi ma haka"

ya ganta a gidan.

"Amma wallahi Habib-Qalby ba ta yi kama da yan aiki ba. Zubinta irin na matan kasar Sirreleone irin kalar fatarta nake burin ina ma in samu. I hate so much brightness. Ga dasashin cikin bakin ta irin wanda nake shaawa, da a ce ni mazauniya ce da na roki Ammi ta bar min ita, I just like the girl."

"Uwais dai sai ""umh"" yake cewa, yana ci gaba da tukin motarsa cikin nutsuwa har suka isa gida."

"Sun yi shirin kwanciya ya shigo dakin Amrah da zummar yin wani abu, sai ya ganta tana kora magani a bakinta. Da sauri ya idasa shigowa dakin zuwa gabanta."

Lafiya Amrah? Ba ki da lafiya ne?

"Ta ce, No, lafiyata kalau. Contraceptive pills ne nake hadiya sabida su aka min recommending kan cewa sun fi rashin illah ga wanda bai taba haihuwa ba."

"Tunda Uwais ya hadu da Amrah daga dating (soyayya) zuwa aurensu ba su taba samun sabani ba, bai taba jin haushinta a ransa ko miskala zarratin ba. Amma yau ya ce,"

Amrah!

Cikin kakkausar murya.

"Zan amince da komai, karatu a Malaysia, amma ban da a dinga zubar min da kwayayen haihuwata. Ban sani ba ko iya su Allah ya yi nufin ba ni a duniya."

"Amrah ta dube shi tana kankance idanu, Habib-Qalby, me ka ke nufi ne? Ina MBBS student in haihu yanzu? Kwata-kwata nawa nake? Ko shekaru ashirin ban rufa ba, ni karatuna ya fi min komai muhimmanci, wallahi..."

"Uwais ya yi mata wani irin kallo, ya ce, Har da ni Amrah?"

"Ai da abuna ka gan ni ka aure ni, ban ga dalilin da zai kai ni haihuwa yanzu ba."

"Uwais ya yi sake da baki yana

Please Login or Register in order to submit comment