gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FAHIMAH Gaskiyar Da Aka Ɓoye book 1 By Takori Kabara Chapter 14 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta koma Abuja ko da da rarrafe ne........."

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Washegari Amrah ta wuce Malaysia, da ma sati biyu za ta yi. Satin biyu ma cikin lokacin karatunta ne, ta yanke komai ne don ta samu ta gyara tsakaninta da Uwais, kuma ta samu ta gyara dan kadan ko ba duka ba duk da bai samu wata kulawa a tare da ita ba saboda lalura iri-iri na cikinta."

"A daren ranar bayan tashin Amrah daga airport gidan Ammi ya taho. Ammi da Fahimah suna zaune a falo suna kallon shirin Arewa24 Uwais ya yi sallama, hannayensa duka biyun zube cikin aljihu. Idanunsa straight a saitin Fahimah wadda daga amsa sallamarshi ta mike. Ta ba su wuri shi da Amminsa. Ba ta yarda ta kalli Uwais cikin ido ba sabida Ammi, kuma dai ba ta hango komai a tare da shi sai tsagwaron rigima yau, tunda ya koma gwauronsa kamar da."

"Ammi ta amsa mishi, ya zauna suna kara gaisawa, ta ce, Yan Malaysia an tashi kenan? ?"

"Ya ce, Eh Ammi ta tashi yanzu ?."

Sannan ya sunkuyar da kai cikin jin nauyin abin da zai fada.

" Ammi na zo ne tafiya da Fahhima, sai ta zauna gidan Amrah kafin a karasa nata ginin. Ammi kin ce duk ranar da na shirya karbar aurena da Fahimah da hannu bibbiyu ranar ne za ki ba ni ita."

"Yau ga ni da kokon barana Ammi, gwiwa a kasa, ki yi min alfarma ki ba ni Fah-himah ?. Haj. Safeeyah ta gyara zamanta tana kallonshi sosai, kamar mai son hango reality na maganganunsa cikin kwarar idanunsa. Daga bisani ta ce,"

" Uwais, ka gaya wa matarka cewa kana auren Fahimah? ?"

"Ya girgiza kai, ya ce, A ah tukunna Ammi, sabida na ga tana gidan, kuma Amrah ba ta gama samun karfin jikinta ba ?."

"Ammi ta yi wani miskilin murmushi, ta ce, To ba da ni za a yi aikin rashin gaskiya ba, kuma Fahimah ba za ta je gidan matarka da kayanta a ciki da iyayenta suka zuba mata ta yi zaman aure ba."

"Har sai ranar da ka zaunar da ita ka gaya mata cewa tare aka daura aurenta da na Fahimah, sannan ka kammala wa Fahimah ginin gidanta ita kadai, don ba za su zauna tare ba. Sannan zan yarda ta tare."

"Duk wannan yar dadin da ka ga suna yi, ina tabbatar maka don Amrah ba ta sani ba ne, da"

tuni komai ya rushe. Don haka ka je ka gama da wadannan matsalolin na gabanka kafin ka zo

gabana da neman daukar matarka.

"Sannan Uwais, na hana ka shiga dakin Fahimah daga rana irin ta yau, daga lokaci irin na yau,"

"sai kun koma gidanku, don ni ba tsohuwar banza ba ce, da za ka dinga binta daki a gabana ?."

"""Yau dai Ammi tsagwaron mugunta ta ke ji! ?."

"Uwais ya fada a ransa, gumi na karyo masa ta kowacce kafa mai fitar da gumi a jikin dan adam. Gini kam ya yi nisa amma bai karasa ba ai. Amrah kuma in ba ta waya ake so ya gaya mata ba, cikinsa ya zube bai san ta hanyar da Ammi ke so ya je ya gaya matan ba."

"Ya shirya a ransa ne sai ta dawo wannan hutun, nan da watanni hudu, lokacin cikinta ya kusa isa haihuwa."

Ya share gumin da ke faman tsatstsafo masa a goshi. Da dai Ammi zata bari sai gobe ta sa masa wannan takunkumin. Yau ta barshi yayi sallama da matar sa. Yau sati biyu kenan rabon shi da Fahhimah Fahhimar da ta zo ta canza akalar rayuwar shi gabadaya ta juya ragamar ta

"cikin dan lokaci kalilan, gaskiyar magana a yanzu bai iya rayuwa ba tare da ita ba!!!"

" Ammi, duk abin da ki ka lissafa zan yi. Amma ki yi hakuri sai Amrah ta dawo hutu. Yanzu zan maida hankali a kan ginin, ki taya ni addu a Allah ya hore in gama shi cikin dan lokaci ?."

"Yana gama fadin haka ya mike zai fice ko ganin gabansa ba ya yi, imagining yadda zai karar da daren yau babu Fahhimah, bayan har Allah-Allah yake Amrah ta koma ya samu wannan damar, don kuwa ba ta amfana masa komai tun zuwanta sai tsurfa da korafi irin na masu juna biyu. Na Amrah har da karin sangarta a ganinsa, kamar a kanta aka soma ciki. Allah kadai ya san iya burin da ya ciwa daren yau."

"Don haka washegari ya bude wuta a kan ginin Fahimah kamar zai shiga ayi da shi, wanda ake yi a Unguwar Sulaiman Crescent. Ya bai wa ma aikatan watanni biyu su kammala komai."

Komai da ke account dinsa ya tafi ya shige cikin aikin ginin don so yake a yi mata komai kamar

na Amrah.

"Ammi zuciyarta kal! Ganin yadda Uwais ya gigice da hukuncin ta. Burinta ta saya wa Fahimah martaba kamar kowacce mace a gidan miji, in ta ci gaba da barinsa yana zuwa yana rage dare ba zai maida hankali ga muhimman al amuran ba, gini da sanar da matarsa gaskiyar magana. Ita ba girmanta bane wannan boye-boyen da yake wa Amrah. Gara ayi ta ta kare."

*****

"Fahimah ta ci gaba da zuwa makaranta tare da Ammi, Uwais sabida haushin Ammi ta ce ba zai kara kebewa da Fahimah ba yanzu sai ya yi kwanaki uku bai zo gidan ba. In ya zo kuma ba ya zama, abinci kawai yake ci ya tafi, in Fahimah na zaune a falon su gaisa yana faman kawar da kai, in ba ta falon ba ya nemanta."

"Hakan ya fi komai sauki ga Fahimah don karatunsu ya fara zafi, sai ta maida hankali ga karatu sosai, da tukin mota da Ammi ke koya mata da yamma don ta ce ta fasa na Uwais din, don zai"

iya amfani da damar ya karya umarninta. Don haka ta zage tana koya wa Fahimah tukin da

kanta at her leisure time.

"Allah cikin ikonsa kuma da yake ya sa pressure sosai cikin watanni biyu ginin gidan Fahimah ya kammala, har fenti da komai an gama."

"A ranar da yake shirin gaya wa Ammi, ya samu takarda daga babban bankinsu na kasancewarsa cikin wadanda banki ya zaba ya tura kasar Switzerland yin wani muhimmin course da World Bank."

"Abun farin ciki ne a gare shi domin in ya dawo karin matsayi zai samu, amma da ya tuna tafiyar na nufin nesanta shi da Fahimar da yake ganin ya kusa samu, sai duk murnar sa ta koma ciki. Yaji kadaicin duniya da damuwar duniya sun lullubeshi kamar shikadai ya saura a fadin duniya. Na farko dai ba a ba su damar daukar iyali ba, na biyu ko an ba su Fahimah ba za ta samu binsa ba domin tana gab da zana jarrabawarta ta karshen zango. Kwas din na watanni uku ne, kuma su goma kadai suka samu wannan babbar alfarmar. Za su tashi da zarar visa dinsu ta kammala."

"A ranar ya zo ya gaya wa Ammi, maimakon ta ga yana murna ta fahimci jikinsa a sanyaye yake. Kuma cikin matukar damuwa yake. Ammi is over-excited domin da ma akwai kyakkyawan shiri da ta ke son yi wa Fahimah wanda a baya ba ta yi mata sosai ba. Gara-gara ma a Sudan ta dan karba ta bata a wajen matar Mahdi. Tafiyarshi zai ba ta damar yin komai a nitse, in ya so da ya dawo sai su koma gidansu."

"Ammi ta ce, Wannan ai abun farin ciki ne Uwais, tunda ci gaba ne ta fannin aiki. Allah ya"

"tsare Ya bada nasara. Ita ma Fahimah jarabawa za ta yi, don haka in ka dawo sai ku wuce gidan ku insha Allah ?."

"Sallamar Fahimah da Uwais ta kasance a wani dare na litinin, bayan ya dawo aiki ya zarto gidan, ana i-gobe zai tashi zuwa kasar Switzerland. A kalla ya shafe kwanaki masu yawa bai sanya Fahimah a idanunsa ba, kuma bai neme ta ba, don Ammi gasa shi ta ke ba da wasa ba. In taga lokacin zuwansa ya kusa sai ta tashi Fahimah daga falon ta sata wani aikin. Ita kuma ta"

kasa ta tsare a falon taki zuwa ko nan da can.

"Sun yi sallama da Ammi har zai wuce ba tare da ya tambaye ta Fahimah ba. Ransa a cumkushe. A zuciyarsa yana fadin,"

" Ammi ga yarki nan gabadaya na bar miki har wata uku, sai ki yi ta kullewa a daki. Tunda"

dai duk kawaici na ba a gani ba ?.

"Shi kadai ya san halin da yake kasancewa a ciki duk daren Allah a gidansa ba Amrah ba Fahhimah, kuma ya yanke shawarar kin kiran Fahimah a waya har sai ranar da suka gama masa gashin kumar ita da Ammin ta, don ita ma ta biye wa Ammi ba ta nemansa, ta durfafi karatun makarantar ta, ba ji ba gani."

"Amrah ko ko ya kira ta ma yanzu ba ta iya doguwar hira barci zai yi awon gaba da ita. Ko ta ce masa ita karatu ta ke yi ya bari gobe za ta kira shi, sanda ta ke free din, shi kuma yana ofis yana fama da ayyukansa. Don haka in ka ga Uwais a dan tsukin nan har ramewa ya yi, ya fada sosai, ga kasumba ta taru ya ki ya aske ta. Sosai yake ragaita a zuci da gangar jiki."

"Bayan sun yi sallama da Ammi zai wuce, sai cewa ta yi. Ba za ka shiga ku yi sallama da Fahimah ba? ?"

"Idanun Uwais suka kifta kadan, ta wani fannin tamkar wanda aka aikowa da manzon Rahma,"

"wani kuzari ya da rabon sa da irin shi tun ranar da ya zo daukar Fahimah su tare a gidan sa amma ta gwale shi da takunkumin ta, ya ce,"

Ammi kin yi izni? ?

"Da murmushi a bakin Ammi ta ce, Na yi izni Uwais, ko da ma can ai ban hana ku gaisawa ba a waya ko a falon nan. Na fi so ne dai ta tare a dakinta, sannan ku je ku karata. Amma sallama ai ta zama dole ?."

"Tana gama fadin haka ta wuce zuwa dakinta, ta ce da Uwais, Saduwar alkhiri ?. Ammi na bada baya Uwais ya juya dakin Fahimah da takunsa na sassarfa."

"Tana kwance tsakiyar gadonta ta rufe kanta da pillow, amma ba barci ta ke ba, tunanin Uwais ta ke yi da tsawon lokacin da suka dauka ba tare da juna ba alhalin suna gida daya, kuma suna jin muryar juna sau tari cikin gidan, sannan su kan ga juna jefi-jefi."

"Ba ta san dalilin Ammi na nesanta su da juna har haka ba, amma ta yarda komai Ammi za ta yi akan su, to za ta yi ne for her own betterment. Itama ta fi yarda Amrah ta san me suke ciki in ya so komai ta fanjama-fanjam, kuma tana bayan Ammi na ba za ta shigar wa Amrah gida ba don"

ba ta nan.

Da murda kofarsa da sallamarsa ciki-ciki duka ba ta ji su ba. Sai kwanciyarsa a gadon bayanta. Ya sakar mata dukkan nauyin sa. An ce duk nauyin miji mace na dauke shi tsaf ba tare da ta ji nauyin ba ita. Amma Fahimah har yar kara ta saki sabida nauyin Uwais. Dadi da cewa ba ta tsammaci zuwansa a lokacin ba don ba ta san da tafiyar da ke gabansa ba.

"Daga haka Uwais ya canza akalar komai zuwa irin wadda ya fi so a rayuwarsa (romansiyya), wato kasancewa tare da Fahimah cikin nau ikan soyayya irin nasa mai keta zuciya da ruhin Fahimah. Al amuran da suka biyo baya masu tsauri ne kwarai a tarihin rayuwar auren su. Sai da dukkansu suka samu nutsuwar da suke bukata, Uwais ya maida sittirunsa ya rike Fahimah"

"cikin hannayensa, fuskarta cikin tafukansa."

" I m going to Geneva Fah-himah, sai bayan watanni uku zan dawo. It will not be easy kin sani. Amma as a man dole in je in nemo muku abinci. Ki kula min da kanki. I will surely miss you and everything of you... this luscious lips ? I m gonna miss them ?."

"Fahimah ta janye fuskarta daga tafukansa cikin tsananin damuwa, sannan ta kwantar da kai a"

"kafadunsa sai ga hawaye suna zuba tarara! Wata uku! Babu Uwais! Na nufin komai a gare ta ,"

"Uwais ya sanya dan yatsar sa ya lakato hawayen ya ce, Better, bayan muna gari daya ma kin biye wa Ammi kun sanya ni a kwandon shara, shi ne yanzu ki ke wani kuka, how dare you want me to believe you cewa hawayen a kan tafiyata ne??? ?"

"Fahimah ta ce, Yaya Uwais ba za ka gane ba. I love you so much ?! ? Ta sake kankame shi tana kuka."

"Amrah ta sha gaya masa wannan kalmar, amma yau da Fahimah ta fada wani madaukakin farin ciki ne ya lullube shi, wani excitement ya bakunce shi, ya yi mata kyakkyawan muhalli a cikin physique kirjinsa yana shafa kwantaccen gashin kanta. Sun dauki lokaci mai tsawo a haka kafin Uwais ya dago fuskar Fahimah cikin tafukansa, ya soma magana cikin taushin murya."

" I m sorry for all the past inconveniences, I m sorry for the rest of our lives. Fahhimah I"

hurt you so much cikin ajizanci irin na dan Adam. Da Ubangiji ya tashi hukunta ni sai ya hukunta

ni ta hanyar sanya min sonki da kaunarki lokaci daya. Ba tareda na shiryawa hakan ba.

"Today .... i must confess ban sani ba ko in na tafi bazan dawo ba, I want to use this medium"

to tell you aloud that I LOVE YOU very-very much ?!!! ?

"Suman wucin gadi Fahimah ta yi a tsaye, Allah ya so ta jikin Uwais ya yi mata garkuwa, ba don haka ba sulalewa za ta yi a kasa ta narke domin farin cikin is over-estimated."

"Cikin yanayin da Uwais da Fahimah suka kasance kenan na lokaci mai tsawo ba tare da sun ankara da tafiyar lokaci ba, sai kiran assalatu suka ji a tsakar kansu. Dole tare suka yi sallar asuba bayan sun yi wanka. Sannan ne Uwais ya yi haramar tafiya amma ko ya tafi idan ya je bakin kofa sai ya dawo, kamar ba za su rabu ba, ganin watanni uku suke tamkar shekaru uku. Sai da alarm din gefen gadon Fahimah ya buga karfe bakwai na safe sannan Uwais ya iya tafiya."

"A wannan yanayi Fahimah ba ta yi barci ba, ta karar da ranar wajen addu a ga Uwais da"

nema masa sa a a wannan tafiya tashi da nema masa albarka a cikin nemansa.

"Ko da Uwais ya shiga jirgi kafin su tashi, sai da ya fara kiran Fahimah. Da ta dauka muryarta"

rawa ta ke da alama ta ci kuka ta koshi.

Yaya Uwais kun tashi? ?

"Ya ce, Are you crying Fahhimah? Me ya sa ki kuka? ?"

"Ta share hawayen ta ja hanci, sannan ta ce, Gani nake kamar in ka tafi ba za ka dawo ba as you said ?."

"Ya canza positon na rikon wayarsa, ya ce, Fah-himah, in kin ga ban dawo gareki ba, to na mutu acan, wanda bana fatan hakan yanzu. I would like to cuddle your black beauty babies in my arms.. ?."

"Wani hawayen ya zo wa Fahimah, amma this time around na farin ciki ne. Yaya Uwais kana son ya yana? Idan suka yi baki kamar ni fa? ?"

"Uwais ya ji duk ya muzanta, nadama ta kara lullube shi, shi ya sa ba a son gorin halitta don ba"

ka san me gobe za ta haifar ba.

"Muryarshi ta yi rauni kwarai a sanda yake cewa,"

" Dan Adam ya kasance ajizi mai yawan kuskure, kuma Uwais yana cikin su. I m sorry Fahima for the past weird experiences which are all regretful."

"Yau kin sa na yi nadama irin wadda ban taba yi ba. Fahimah ya yanki, jikokin Ammi ne, sabida yar ta ce wadda haifa ne kawai ba ta yi ba ta haifo su, sannan sun fito daga jikin Uwais ? with all these .... and much more....zan so su fiye da yadda nake son kaina! ?."

"Hawayen Fahimah suka ninka na baya, farin cikin ya ninka na baya ta ce, Ya Uwais na yafe"

"maka, na kara yafe maka, ni da ma kullum uzuri nake yi maka. Is not easy da ma a so"

" ya ya kamana sai ga exceptional mutane irin su Ammi, wadanda su kuma tsiraru ne a cikin al ummah."

"Ban taba rike ka ba ko da sau daya a zuciyata sabida an ce so hana ganin laifi, and I blindly"

"love you at the time, fatana kawai shi ne ni ma ka so ni ko da rabin-rabin yadda nake sonka ?. And you got it Fah-himah, halayenki sun sayo miki soyayya fiye da wadda ki ke kintace. Also bazan gaji da cewa ba you are a darling (ke abar so ce) da duk namijin da Allah ya yi wa baiwar samunta, hakika ya ba shi rabin addininsa."

"Ya yi masa boyayyen gata irin wanda kudinsa da zabensa ko mulkin sa bai isa ya ba shi ba. Ba ni da abin da zan ce wa Ammi a yanzu, sai dai in dauwama ina roka mata aljanna ita da mahaifina ?."

A lokacin aka soma shela cikin jirgi cewa a daura belt jirgi zai tashi hakanan. Haka Uwais ya yi sallama da Fahimah jiki a sanyaye don har zuwa lokacin Fahimah ba ta daina kuka ba.

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Ta turo baki gaba, ta ce, Kawai zan yi kewar Ammi ne ?. Ya ce, Uwais fah? ?"

"Ta kyabe baki, Ko kadan ba zan yi ba ?.. ?"

"Dariya ya yi ya ce, Ohk, Amrah, is waiting, I m leaving now, amma ki sani kina gab da tarewa a gidan ki da zarar Ammi ta dawo ?."

Ya mike bayan ya bata kyakkyawar sumba a goshi.

" Kin ce ba za ki yi kewata ba, ni kuma I will undoubtedly miss EVERYTHING da ke faruwa ko ya faru tsakanin mu in these few days... in na ce komai ina nufin KOMAI especially our"

"Dambe, our first night, our Lagos life, our Sudan life, and our past inconveniences. I will still NOT say I love you sai ranar da na samu kyakkyawar sumba daga gare ki, sai ranar da ki ka tare a dakin ki, ki ka karbi girkin ki. In hakan ta faru na fi kowa sa ar zuwa duniya."

"I remain loyal to my mother, thankful and prayerful to her da ta mallaka min ke Fahhimah ?"

"Fahimah ta runtse idonta, kalaman Uwais na ratsa ta, suna gasa kowacce gaba ta jikinta tamkar a cikin oven. Amma kunya ta sa ba ta ce masa komai ba. Ya sake sumbatar goshinta, sannan karan hancinta, ya ja tunga a lips dinta, ganin zai zarme ga wayar shi na ta tsuwwa alamun matar shi ta gaji da jira, sai ta janye kadan."

Please go ?.. ?. Ta fada cikin karfin hali irin nata. Korata ki ke yi Fah-himah? ?

" Ba girkina ba ne, babu kyau ?. Ai ba a raba girkin ba ?."

" Ni dai don Allah ka tafi Ya Uwais ?. Ta fada da iyakacin courage din ta. Cikin shagwabar da ta kara tunzuro Uwais ya kasa tafiyar, sai kallonta cikin tsananin bege."

"Wayar shi ta kara daukar ringing da tune na musamman da ya sanya wa Amrah. Dole ya juya ya tafi a sanyaye, don Fahimah ta juya da sassarfa shige dakin ta."

"Tana shiga dakin ta rufe kofarta, ta jingina da jikin kofar tana maida ajiyar zuciya mai nauyi. Ta san barci yau zai yi wuya a gare ta, amma ta sa a ranta gara ma ta saba, Amrah ma na da hakki a kansa, kishi ba nata ba ne ita matar shige, don ta samu Allah ya kankaro mata 'yar"

"darajar da mafarkin ta bai taba bata ba, bai kamata ta yi butulci ba."

"Amrah ta cika fam, ta yi fushin har ta gaji. Lokacin da Uwais ya iso gidan Murjanatu, suna gaisawa shi da Aunty Murja a falo. Aunty Murja ta ce ta dauko jakarta su tafi, sai kumburi ta ke"

haka ta dauko jakar ta bi bayansa.

"A cikin motar ya yi mata side hug sannan ya ba ta hakurin rashin zuwansa da wuri. Ta ce ita ba ta hakura ba, sai ya gaya mata inda ya je."

"Ya maida hankalinsa ga tukin motar, Amrah ki yarda da ni ba inda na je, ina gida ?."

"Ta san ba zai mata karya ba, don haka ta bar zancen."

" Me za ki ci mu tsaya mu saya kafin mu karasa gida? Bana son sake fitowa in na shiga, don a gajiye nake""."

"Amrah ta yamutse kyakkyawar fuskarta ta ce, Ai ni yanzu ba komai nake iya ci ba Habiby, sai abu mai dan yaji-yaji, mu biya Chicken Republic ina son spicy chicken din su ?."

Ya bi umarninta.

"Suna zuwa gida ta zuro kafar ta daya waje tana kokarin fitowa daga motar, sai ta juyo ta ce da shi,"

" To amma fa Habib Qalby, ba za mu hada daki ba, wallahi ko kadan yanzu bana son turaren"

ka ?.

Cikin mamaki yake dubanta baki a sake. Amrah lafiyarki kalau kuwa? ?

Sumul kalau nake ?.

" To kam, ai sai dai in canza kayan, amma abin da ki ke fadi ke ma kin san ba mai yiyuwa ba ne ?."

"Amrah kamar ta saka kuka, ta ce, Wallahi ko ka cire ba ka daina kamshin (Maison Francis) ?."

"Ya ce, Ai kuwa sai dai a yi wacce za a yi, amma ban da wannan yaren ?."

"Sun yi shirin kwanciya, zullumi da damuwa duk sun ishi Amrah, ba da wasa ta ke ba turarensa hawa kanta yake, a baya babu kamshin da ta ke so irin na Uwais amma banda yanzu."

"Uwais na sanya tafukansa a bayan wuyanta ya hada goshinsu zai lallashe ta don ya ji actual abin da ke damunta ta ke ta wannan yamutse-yamutsen fuskar. Ai kuwa ta kelayo masa wani uban amai, mai karni. Ya yi maza ya ja baya ita kuma ta ci gaba da amayar da spicy chicken din da ta ci tas! Sai da ta amayar da ita."

"A daren ya ce su tafi asibiti, ita kuma ta dage ba ta zuwa ko ina. Ai ta gaya masa turarensa"

ne ba ta so ya ki jin magana. Ya ki ya bar mata dakin.

Washegari sai da ya yi mata jan ido sannan ta yarda suka tafi asibitin standard. Awo na fitsari a tashin farko ya nuna ciki na watanni uku.

"Tunda suka dauko hanyar dawowa Amrah ke kuka, kuka kashirban. Kamar ba ita bace a baya ta ce ta yi surrender ba. Bata taba tsammatarwa kanta ciki a wannan lokacin ba. Ta rantse ba ta shirya wa haihuwa yanzu ba, karatunta zai salwanta. Uwais sabida tsananin bacin rai ga"

"kalaman Amrah a kan kyautar da Allah ya yi masa cewa ya yi,"

" Wallahi in ki ka zubda cikin nan da gangan, to a bakin aurenki ?."

"Amrah ta zaro ido tana kallon Uwais, kallon mamaki da tsoro, ina soyayyar da yake ikirarin yana yi mata? Yanzu har ya fi son dan da zai haifa a kanta? Da ma Daddy ya ce soyayya karya ce, ka yi aure kawai don bukatarka ta dan Adam da cika sunnar Annabi, amma ba don soyayya ba, sabida it never exist in nowadays men, even if it exists da zarar sun gano wata za ta yi fading."

"Shin Daddy da gaske yake? Ko dai Uwais ya gano watan

Please Login or Register in order to submit comment