gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FAHIMAH Gaskiyar Da Aka Ɓoye book 1 By Takori Kabara Chapter 11 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kashe ma waya, alhalin na gaya masa na yo tattaki musamman tun daga Malaysia har Kano don kawai na faranta masa? Na tsallako karatuna cikin hadari mai yawa? Ba don za ki"

"karyata ni ba, wallahi sai in ce miki jiya da daddare da muna waya na ji tsakin MACE"

"tsuwww cikin kunnena, ya yi sauri ya kashe wayar ba tare da mun yi sallama ba."

Yau kuma very shortly ya amsa min ya kashe wayarsa ?.

Mu karasa a littafi na 3. Sumayyah Abdulkadir 07030137870

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Suna shigowa get maigadi ya bude musu suka shiga. Tun bai gama parking ba Fahimah ta bude kofar za ta fice da niyyar ta yi ta kanta. Wannan Uwaisun bata gane masa ba da murmushin sa akai-akai. Ta sa a ranta in ta shige daki yau Uwais bai kara ganinta sai Ammi ta dawo. Amma me? Ta-yi ta-yi ta bude kofar ta ki buduwa. Ya kulle ta automatically."

Juya idanu ta yi tana kallonsa da sigar tambayar dalilin kulle mata kofa. Ya wani lumshe ido a cikin kallonta.

Saurin me ki ke haka? ?

"Fahimah ta dafe goshinta da ke sarawa, ta ce, Ka san ba ni da lafiya, ina so na je na kwanta ne, don Allah ka bude min kofar ?."

" Ba ki ji likita ya ce, I can take care of you ba? Ni kadai ke da maganin ciwonki ?. Fahima ba ta san sanda ta kwalalo ido ba tana kallonsa."

Ciwo na? Wane irin ciwo ne da ni? Zazzabi fa kawai nake yi da ciwon mara ?. Duk ina da maganin su ?.

" To ba ni insha in je in kwanta, wallahi kaina sarawa yake yi, kuma kana ta sa ni magana ?. Biyo ni mu je, magungunan suna daki na ?."

"Ya saki locks din da ya kulle motar da su, wata zuciyar na cewa ta je ta karbo wata na gaya mata wayo zai yi mata, ba shi da wasu magunguna a daki, gara ma ta duba first aid box din Ammi, ba za ta rasa kowanne irin magani ba."

"Uwais din nan sai ta yi a hankali da shi, shegen wayonsa da son kansa ya fi karfinsa."

"Suna shigowa falo ta nufi dakin Ammi ba tare da ta kalle shi ba, shi kuma ya bi ta a baya, first aid box din ta nufa ta bude tana duba magungunan ciki. Sai jin Uwais ta yi a bayanta, sassanyar numfashinsa na dukan wuyanta. Sannan ya rungume ta ta baya."

Me ki ke nema ne haka? ?

"Ba tare da ta juyo ba murya na rawa kamar yadda jikin ta ma ke yi, ta ce, Magani ?."

" Amma na ce miki ina da su, mu je part dina in ba ki ko? ?"

"Fahimah ta soma hawaye, because he is dragging her closer, and he began caressing her gently, and the touches are irresistable amma haka ta jajirce ta soma kokarin kwatar kanta. Yaya Uwais, dakin Ammi ne fa? ?."

" Abin da Ammin ke so kenan, shi ya sa ta bar min ke, ta bar mana gidan daga ni sai ke, don"

"tana so mu zama abu guda. Na tabbata ita ta hana Talatu dawowa. Look Fah-himah, today I disregard all your clumsy excuses ?...""."

"Fahimah ta wara fararen idanunta gaba daya tana kallonsa da mamaki, sannan ta kankance su"

"cikin tsiwa ta ce,"

" Wallahi sai dai ka yi raping din nawa Uwais (as you earlier said), don na san ka fi ni karfi."

Amma da amincewata da yardata ba zan taba bada alfarmata ga mijin da na tabbata ba ya

sona ba! ?.

"Tamkar wanda ta kwara wa kankara haka ya ja birki ya saketa. Tunda kuwa ta yi rantsuwa ya san da gaske take. Kwakwalwarsa gaba daya ta rikice, Fahimah na so ta zauta shi, ta yi amfani da wannan damar ta raba shi ta fice cikin hanzari."

"Kafin ta kai daki hawaye sun jika mata fuska; raunin diya mace, weakness na mace kan wanda ta ke matukar so, da tausayin abin da ta ke kauna, ta san da gaske yake yana cikin wani hali da yake tsananin bukatar taimakon matar sa, ita ma kuma tana bukata, Uwais ne fa! Amma da a yi 'a rashin uwa' da ita ? gara kowa ya mutu da urges ya huta."

"Ta dauka zai biyo ta, shi ne dalilin da yasa ta rufe kofar da mukulli ta kuma bar shi a jiki don ma kada ya dauko safayar na Ammi ya cigaba da damunta, amma har dare ya tsala ba ta kara jin motsin shi ba."

"Sau uku tana lekawa ta taga ta tabbatar yana nan bai fita ko'ina ba, ta hanyar ganin motar sa, sai ta yi ajiyar zuciya ta koma ta kwanta"

"Amma kuma barci ya gagara zuwa ga Fahimah a wannan daren, tunanin a wane hali Uwais yake? Ya hana barcin zuwa ya kuma hana ta zaman lafiya."

"A daddafe garin Allh ya waye da ita, barcin da ta yi yau kwata-kwata bai yi na awanni biyu ba. Da ta tashi duk sammakon ta ba ta ga motarsa ba, tabbacin ya fice ofis ba tare da ya nemi karin kumallo daga gare ta ba."

"Don haka ita ma ta yi shirin shiga makaranta don bada excuse na zuwa Sudan kwana biyu ko uku ga abikan karatunta don su yi mata attendences, amma duk jikinta a sanyaye yake. Tana dai karfafa kanta da cewa hukuncin da ta zartar shi ne daidai, kada ta bari soyayya a inda ba ta da gurbi ta kassara rayuwarta."

Ya jira matar SO ta dawo. Su dora daga inda suka tsaya.

*****

"Ta yi wanka ta shiga kicin domin nema musu abin da za su ci. Duk da ba ta da tabbas ko zai ci din? Tunda fushi yake, fushin da ta ke kira na karfin hali wai barawo da sallama. Kai da ba ka son mace, ka fada ka kara, a idonta da bayan idonta, don me ka ke son auratayya ta kasance a tsakanin ku?"

Haka kawai ita ma a barta stranded din idan matar so ta dawo babu gaira babu dalili? A hakan ma yaya ta kare da sabbin darussan da ya koyar da ita duk da bata san kan dawar garin ba? Ba

"ta taba ganin mutum mai son kansa a duniya irin Uwais ba. To ita ma tana son kanta, kuma za"

"ta yi wa rayuwarta gatan da bata da shi in reality, sai ranar da ya furta mata hakikanin kalmar so daga zuciya da ruhi, da kuma fatar bakinsa. Ya janye mummunan sunan da yake kiranta da shi"

"na gorin halitta ""Goddam Black""."

"Yamma lis Uwais ya shigo gidan, a matukar gajiye ya ke ga yunwa da ya dawo da ita, rabon shi da sanya wani abu a bakin shi tun wani dan hot coffee da ya sha da safe a ofis da bai fi rabin kofin mug ba, inda akwai abin da Uwais ba ya yi wa fulako ko zuciya to abinci ne, ko dazu da safe duk da fushin da yake da Fahimah kafin ya fita sai da ya duba ya ga ba ta ajiye komai ba shi ne ya fita, amma shi zai yi fushi da komai ban da cikinsa, sabida yawan excercise din da yake yi yana saka shi saurin jin yunwa."

"Yana shigowa dining ya nufa. Luckly ta ajiye lafiyayyar sakwara (pounded-yam) da miyan Ugu wadda ta ji naman rago zuqu-zuqu. A gefe ga jug na lemon carrots da ta hada da fresh abarba, ta zuba kananun kankara a cikin sa."

"""Ko da wannan mijin fahimah ya tsira ya tsira"". Uwais ya ce a zuciyarsa, yana mai jan kujerar da ya saba zama akai a dining din. Ammi ta yi mata kyakkyawan raino mai matukar ban sha'awa, tarbiyya ingantacciya da kuma tsayuwa a kan ra ayi guda. Ya fahimce ta tun jiya, ya fahimci"

manufarta as the same time ya kuma yaba da jarumtakar ta.

"Amma har gobe yana faman cigaba da lalubawa a fadar zuciyarsa bai ji tsayayyen muhalli ga Fahimah ba, balle yayi mata karya wadda ba halin sa ba. Amrah ta bi ta cike kowanne gurbi ita dai barta da son bokonta."

"Ta karaso wajen yana cikin cin abincin, sanye da riga da wando na Pakistan ruwan zuma, ta kame kakkarfan gashin kanta a tsakiyar kanta wanda bai da tsayi sai cika da kuma karfi na hausawan usli. Ta lulluba mayafin kayan a kanta. Idanunsu suka hadu, duk sai ta ji kunya ta kamata. Data tuna rashin arzikin data yi masa jiya."

"Uwais kallonta kawai yake har ta karaso, ya aje cokalin hannunsa. Ta yi wani fresh da ita, dark-skinned din sai sparkling ta ke yi. Ashe dai a can baya kallon tsoro yake mata, bakin ma, kyau ne, ga wanda ya yi dacen sa."

" Ki dau abinda za ki dauka, gobe za mu wuce wajen Ammi, sai ki je ki ba ta bayani cewa kin"

"ki yarda auren ya dore yadda ta ke so, kuma ba daga gare ni ba daga gare ki."

"Na yi rantsuwa da Ubangiji idan baki sauya ra'ayin ki ba har muka dawo, mata ta uku zan aura muna dawowa daga Sudan ?."

"Yana fadin haka ya ture plate din gabansa ya mike. Murmushi ya kwace wa Fahimah, beautiful serene smiles, ko mene ne damuwarta don Uwais ya kara aure? Ai kishi na matar so ne, ita ke da damuwa. Ita matar shige ina ruwanta? Ammi kuma in ya ga zai iya tarar ta ya fada mata wannan babbar maganar ai sai ya je ya gaya matan."

"Kaya kala biyar ta kara dauka, sai na barci da na amfani, wadanda suka dawo da su daga Lagos ta zuba su a kayan wankin ta, tana shirin kwanciya sai ga Uwais ya shigo."

"Ta yi maza ta maida rigar da ta ke niyyar cirewa ta canza da sleepy, ya yi kamar bai ga abin da ta yin ba, ya zauna daga tebir din jikin madubi."

Pajamas ne a jikinshi farare yan gidan Marks & Spencer. Bakin gashinsa sai sheki yake cikin

hasken farin kwan lantarkin da ya haskake dakin.

"Ya ce, Sorry, I m not here for what you are thinking right now. Na zo ne mu fahimci juna"

"kafin zuwan matata ta uku. Ina son sanin me ye a ranki game da ni Uwais, da har ki ka yarda aka kulla irin wannan auren tsakanin mu ba ki yi kowanne irin protest ba alhalin ba kya sona ?."

"Fahimah ta lumshe idanunta, wai ita yau Uwais ke wa gorin ba ta son sa! Ina ma ana ciro zuciya a nuna, ta tabbata da Uwais ya yarda duk duniya babu macen da ke sonsa kamarta. Ba ta tanka masa ba ta dauki kayan da ta ke son canjawa ta yi toilet, ta sanya sannan ta fito duk Uwais na kallon ta. Ya rasa abin da ke damunsa a wannan dan tsukin a kan Fahimah da"

"har ya biyo ta dakin ta again duk da wulakancin da ta yi masa jiya, wanda babu 'ya macen da ta taba yi masa. Alal hakika ji ya yi kawai yana son ganin ta kafin ya kwanta, ya tsokane ta ko"

" yar kokawar ce ya lakato su yi, it will keep him company tonight. Fah- himah, ina magana shi ne ki ka yi banza da ni ko? ?"

"Ya fada cikin rauni, da muryar da Fahimah ta yi tantamar anya ta Uwais ce? Zama ta yi a bakin gado tana kallonsa da idanun mamaki dafe da goshin ta, kafin ta yi wani kasalallen murmushi. Yaya Uwais ban gane tambayar taka ba ne, protest kamar yaya? ?"

" Irin ki dan nuna wa Ammi rashin amincewar ki da auren, tunda kin san ba son ki nake ba,"

"kema kuma na fahimci ba sona kike ba da baki yimin abinda kika yi jiya ba, amma sai ki ka yi shiru, aka kwaci sadaki daga mijin wata ta karfi da yaji aka baki, kuma an ce ki yi aikin sadakin kin ki ?... ?."

Ya fada yana kallonta kai tsaye cikin idanunta da narkakkun kwayan idanunsa. Wani kallo ne mai nuna tsananin bukatuwar miji zuwa ga matarsa.... wanda Fahimah ba ta san ma anar sa ba.

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Daga lokacin da ya taso zuwa lokacin da ya iso gare ta, Fahimah ba ta farga ba. Ta dai tsinci kanta ne a tsaye nannade cikin hannayen Uwais. And he began to kiss her, first softly, sannan gently, kafin ya maida shi a urunce (abruptly), kafin kuma ya dakata yana kallonta kasa-kasa."

" Karya ki ke Fah-himah, kina sona, kina son Yayanki Uwais ba tun yau ba, bakin ki bai fada"

"ba amma zuciya da gangar jikin sun gama confessing, na tabbata son ne kuma ya sa ki ka amince da aurena babu protest."

"A bisa hakan ,nake rokon ki da ki yi hakuri da ni, mu yi amfani da son da ke dankare cikin zuciyar ki mu gina kyakkyawar mu amala ta aure. Ki manta da cewa wai bana miki so irin na soyayyah. Babu abin da lokaci ba ya canzawa Fah-himah. Ki bar ni in tabbatar da sunnar da ke tsakanin mu, na yi miki alkawarin ba za ki yi da na sanin ba ni rayuwar ki ba."

"Ban yi miki alkawarin SO ba, amma na yi miki alkawarin ADALCI ?."

"Wani haushi ya zo ya tokare Fahimah a kahon zucci, duk da kasalar Uwais da maganganun sa ya saukar mata, amma bacin ran kalamansa na karshe ya sa ta angije shi. Ta juya masa baya tana hawaye."

" Yaya Uwais ka fita min a daki, pls, tunda ni da bakina ban furta maka kalmar so ba, don"

"Allah ka daina furtan kiyayya. Babu adalcin da nake bukata daga gare ka duk ka hada ka baiwa matar so. Ina bukatar sarari wallahi, kasa daki na ya min kadan, kana sa min ciwon zuciya ?. Uwais ya zuba hannayen shi duka biyu cikin aljihu yana kallonta da murmushi a siririyar fatar bakinsa."

Then why are you jeolous? Da matar so da wadda za a karo? ?

"Da sauri ta juyo, ba ta san ya karaso bayanta ba don haka kanta ya bigi kirjinsa. Ta sake ja da baya ta ce, Kishi kamar ya ya fa? Ban gane ba? Na ce kar ka yi aure, ko na ce kar ka koma wajen matar ka? ?"

But you called her MATAR SO ? in ba kishi ki ke ba don me za ki kira ta da wannan sunan? ?

"Fahimah ta gama lura tsab yau Ya Uwais neman magana ya ke ji, ya zo ne musamman don ya yi ta takalar ta, tayi ta hargagi yana murmushin jin dadi, ta fahimci in za su kwana suna yi ba zai gaji ba. Sai kawai ta yi tattaki da baya-da baya ta shige toilet da sauri ta murza key ta barshi a wurin. Uwais ya karaso kofar toilet din ya ce,"

Ni ki ka kulle wa kofa Fah-himah? Ai ba sai kin kulle ba na gaya miki tun shigowa ta I m

"not here for what you are thinking. Na zo ne mu fahimci juna, kuma alhmdulillah na gama fahimtar duk abin da nake son fahimta a kan ki."

"Ya rage naki ki baiwa zuciyar ki salama da abin da ta ke so, ko ki yi ta zaman jiran tsammanin warabbuka (sai ranar da aka so ki kamar matar so). Ci ba daya ba kuwa, ai koshi bai taba zama daya ?."

"Fahimah ba ta tanka sa ba, ta san ta shaka masa. A yadda ta ganshin nan da bata tsere ba abinda zai biyo baya Allah kadai ya sani. Ta ganshi ya koma kamar ranar su ta farko a Lagos. Rabar da period ne kadai ya ceceta. Tsoronta daya ne kada ya fita neman matan kan titin kamar yadda yake ikirari, don haka ta yi ta leke ta tagar bandakin ta tabbatar motarsa tana nan"

"bai fita ba. Ta yi ajiyar zuciya ta fito ta rufe dakin ta ciki, sannan ta yi alwallah ta kwanta."

"Ta kasa barci, sai tunanin maganganun Uwais dalla-dalla. A zahiri ta gane cewa; their relationship is taking another direction. Ta tuno yadda Uwais yake kissing nata a Ikko da dazu babu kyama, a hakan ma don tana zamewa ta ki sakar masa jiki. It was all sudden changes a tare da shi wadanda bata taba tsammanin za su faru da shi ba cikin dan kankanin lokaci irin haka. Sai dai ta lura shi a karan kansa bai san da wadannan tarin sauyukan a tare da shi ba. Da ma an ce mahakurci mawadaci, kuma mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon sa. Idan tafiyar su ta ci gaba a haka, ba ta san iya ina za ta kai su ba, amma dai ko ina ne destination din zai zamanto mai ma ana ne."

Me ya kamata ta yi maimakon kwanciya? Ai kawai ta tashi ta gode wa Sarki Allah. Jallah Wa

"Azza. Wanda cikin mulkinSa da buwayarSa ne yake ta karkato mata da zuciyar Uwais, batare da shi din ya san hakan ce ke faruwa da shi ba. All of a sudden, da ma dai Ammi ta fada,"

" Uwais bai iya rayuwa ba tare da mace ba"", kuma ga zahiri tana ta gani."

****

"Uwais da Fahimah, washegari a cikin jirgin SUDAN AIRWAYS, wannan karon bai kai ta economy class ba, ya barta a first class seats kusa da shi duk da cewa ya ki sakar mata fuska sabida abinda ta kara yi masa daren jiya. Tun da suka taho yake kumburi, ga wani bakin dark spaces ya maka wa kwayar idonsa, wanda ya boye halin da kwayar idanunsa ke ciki."

"Ko abincin da aka ba su a jirgi bai taba ba, duk a cikin fushi ne, fushi yake sadidan da Fahimah, ita kuwa ko a jikinta. Ta ci abincinta ta yi nak! Aka zo aka kwashe kayan, ta soma jin barci, sai ta jingina da kujerar sa barci ya dauke ta."

"Ba ta san ya ya aka yi ba, ta farka ne ta ganta kan kafadun Uwais tana barci. Ko ita ta sulmiyo"

"zuwa jikinsa, ko shi ya gyara mata kwanciyar ba ta sani ba. Da asubahi suka sauka a Khartoum babban birnin kasar Sudan kuma garin su Ammi, Mahdi babban dan Baffa Shuraim shi ya zo ya tafi da su zuwa can main house din su Ammi, inda a can ne ake zaman makoki."

"Ammi baki ya ki rufo, da ganin yadda Fahimah ta yi mulmul cikin 'yan kwanaki kalilan. Wannan ya tabbatar mata suna cikin kwanciyar hankali fiye da tunaninta. Duk da an yi addu ar bakwai an watse dangin Ammi na nan ba su koma ba, nan ta yi ta gabatar da Fahimah matsayin yar"

"ta da ta rike tun tana karama kuma matar Uwais. Wasu sun yaba, masu racism din ciki ba su yaba ba, kin san balarabe da kabilanci. Matar Mahdi sai da ta yi gulmar Ammi a bayan idonta ta ce da mijinta Mahdi cikin harshen larabci,"

Duk matan Sudan Ammi Safeeyyah ta rasa wadda za ta aura wa Uwais sai mara asali mara

hasken fata? ?

"Mahdi ya harareta yace ""to ina ruwan ki? Ita ta ga tayi dai-dai da danta, ko ke kika haifa mata shi?"""

"Da yawa kuma tarin nutsuwar Fahimah da rashin rawar kanta, uwa uba kwarjinin da Ubangiji ya"

yi mata shi ya burge su zuciyar su ta kaunace ta.

"Da daddare Uwais ya shigo yi wa Ammi sallama zai tafi masaukin shi ya kwanta, Mahdi na jiransa a waje cikin motarsa zai sauke shi. Sannan ya wuce nasa gidan. Fahimah na gefen Ammi tana cin abincin dare sanda Uwais ya shigo. Kallo daya ta yi masa ta dauke kai, shi ma ya yi kamar bai ganta ba, amma gani ta yi har duhu ya dan yi sabida gajiyar da ke tare da shi. Ammi fi-amanallah zan je na kwanta ?."

"Ammi ta ce, Allah ya huta gajiya, a ina ku ka sauke shi Mahdi? ?"

"Mahdi ya ce, Nan gidan saukar bakin Abbu na gyara masa daki, amma shi ya ce ya fi son Fundaq (hotel) ?."

"Ammi ta dubi Fahimah da ta kasa ci gaba da cin abincin ta ce, Sai ki tashi ku tafi, ni ba zan kwana gado daya da ke ba, hauri ki ke yi da wadannan dogayen kafafun naki in kina barci ?. Fahimah ta zaro ido tana kallon Ammi. Uwais bai ce komai ba ya juya ya fita, yanzu sai ta tsallake kowa da ke cikin gidan nan ta bi Uwais zuwa masauki? Ta bude baki za ta yi magana, Ammi ta jefa mata mayafin ta ce,"

Do as I said ?.

"Tana kunkuni hadi da turo baki gaba ta mike, Duk mutanen gidan nan Ammi? ? Ammi ta ce, Su ba a dakin mazan su suke ba? Bari mu koma gida da ni ki ke zancen,"

"wallahi tarewa za ki yi ko kuma ya dawo da matarsa, ba zan dauki rainin hankali ba, ku zo ku sa ni a tsakiya ina dalili ni ba tsohuwar banza ba? ?"

"Tuni Fahimah ta kai kofa, ga uban horn da Uwais ke antayo mata don ya tsani jira a rayuwarsa. Suna kan hanya shi da Mahdi da ke tukin mota suna gaba, ita kadai tana gidan baya. Uwais ya yi kwafa sannan ya yi magana da hausar da ya san Mahdi bai ji."

" Da ma kin dage kin ki biyo ni, a a ke komai sai ki yi shiru ke ga sarkin biyayya wa Ammi,"

"in kin biyo ni amfanin me kike amfana min? To ni zama da ni DEAL ne kin sani, gara ma ki rufa wa kanki asiri ki bi Mahdi ku koma ?."

"Fahimah ba ta tanka shi ba. Daidai lokacin da Mahdi ya shigar da mota hotel din, shi ya je ya yi musu komai, sannan suka haura dakinsu ta elavator."

"Suna shiga dakin wanka ta shiga ta fara yi sabida tunda suka iso ba ta yi ba, jikinta har"

"danko-danko yake mata, sanda ta fito Uwais na kishingide cikin kujera ya yi rub-da-ciki yana waya. Daga yadda yake magana kasa-kasa da tausasa murya ta fahimci shi da matarsa ne. Sun gama fadan kuma sun shirya."

"Maganganun da ta ji ana yi cikin wayar sun girmi kwakwalwarta, don haka ta ga gara ta fita ta ba su fili kafin ta samu heart attack. Uwais har da gayya yake fadin,"

" Zan iya hakuri mana Amrah? Amma na kwana arba in, daga nan duk yar akwalar da"

"na samu zan yi maneji da ita, da yardar ki ko babu, kada ki ga laifina in ki ka dawo ki ka same ni da sabon aure ?."

"9/23/21, 8:19 PM - Buhainat: Murjanatu ta ce, ""Ki yi wa mijinki kyakkyawan zato Amrah, Uwais mutumin kirki ne a fili da boye as far as i know, bana zarginsa da wannan. Amma lallai ne Amrah in kina son aurenki ya dore, kuma martabarki ta dore a idon Uwais to ki sake shawara a kan karatun ki. Tunda ya fito fili ya nuna miki ba zai iya hakuri ba, bana jiye miki matan waje don"

Uwais ba irin nasu bane. Amma ina jiye miki kishiya da kuruciyar ki ?.

"Gaban Amrah ya yi bala in yankewa ya fadi da kalaman Murjanatu na karshe, wani abu da"

"ba za ta taba iya yarda da shi ba (tarayya da wata a kan Uwais), gara mata ranar mutuwar ta da ganin wannan ranar."

"Amrah ta dubi Antin ta Murja cikin karaya, ta ce, Aunty Murja, ba ni ce abun ji ba, Daddy ne,"

"kuma dai kin san yadda karatun likita yake a kasar nan sai ka yi shekaru goma ma ba su sallame ka ba, sannan gaskiyar magana Uwais yana da takura, mayata har da hayyata. Tafiyata na dan lokaci ba ki ji hutawar da na yi ba da sararawar da na

Please Login or Register in order to submit comment