gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading FAHIMAH Gaskiyar Da Aka Ɓoye book 1 By Takori Kabara Chapter 2 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hudu Amrah, i see them like eternity. To Amrah ta ya ya zan amince ni ina nan goho ina jira, wani a can ba zai min shigar sojan badakkare ba?. Ya fada sounding emotionally worried. Amrah ta yi murmushi, ta ce, Tunda Daddy ya amsa maka, to ka kwantar da hankalinka ya tsumma a randa, domin Daddy ba ya magana biyu. Sannan ni wa zan kula? Karatun da ke gabana kadai ya ishe ni, ka yarda da ni Habib-Qalby...(sunan da ta rada masa) a Hausance yana nufin 'masoyin zuciya ta'.."

"Ya ce, Na yarda da ke Amrah, in na ce yarda ina nufin yarda ta har abada cikin aminci. Ki yi karatu mai yawa with me in mind and our next coming babies."

"Amrah ta kai tafukanta ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Ba ta ga lokacin da Uwais ya taso daga kujerarsa ba, sai tsinkayarsa ta yi tsaye a gabanta, hannayensa duka biyu zube cikin aljihu, ya ce,"

Amrah kin amince min kafin ki dawo in tura magabatana wajen Daddy su kara rokonsa a gabatar da neman aurenmu?

"Na yi alkawarin za ki cigaba da karatunki ko da kina Malaysia ni ina nan Kano. And I promised you eternal love Amrah, jiran ne ba zan iya ba."

"Amrah ta kai hannu ta rufe fuskarta, kyakkyawan murmushin da ke kan fuskarta kadai amsa ce ga Uwais, na ta amince ya tura neman auren ta. Don haka da karfin gwiwarsa ya koma gida duk da yana cikin alhinin rashin Amrah da zai yi a kwanakin. Ta riga ta zama wani bangare na"

ruhinsa cikin dan lokaci kalilan.

"Ya shigo gida misalin karfe goma na dare. Tuni Ammi ta dade da kwanciya. Har ya shiga bangarensa. Ya yi wanka ya canza kaya zuwa Pajamas farare sol ya ankara da yana jin yunwa, yunwa sosai da ke bukatar tallafi, ya san yanzu Talatu ta jima da komawa Baskwata, Ammi kuma ta kwanta, don haka ya yanke shawarar zuwa kitchen ya nema wa kansa dan abin da zai"

iya ci ko ya yi barci cikin nutsuwa.

"Ta juya baya tana fasa kwai a cikin tangaran, ita ma yunwar daren ce ta taso ta, kawai sai ta jiyo takun mutum a bayanta, ta juyo da sauri duk da kamshin turarensa ya riga ya gaya mata ko waye. Ya sunkuya ya bude firji ba tare da ya lura da tsayuwarta ba, Fahima ba ta kara mallakar kanta ba daga lokacin sabida rudewa da bugun zuciya wanda ke faruwa da ita a duk sanda ta ga Uwais."

"Kwan hannunta ya subuce ya fashe a kan kafarta, daidai lokacin da ya dago da gorar ruwa a"

"hannunsa sai idonsa cikin na Fahimah. Wani haushi ya kama shi da karfi ya ce,"

"What are you doing here? You Goddam Black, mai idanu irin na kyanwa! Ganinki cikin dare sai ya firgita mutum get out from here."

Ya fada da tsawa.

"Jikin Fahimah na mugun rawa ta juya ta bar kicin din, ko kamin ta kai dakinta hawaye ya jika fuskarta. Ta tsani tsawa, ta tsani kyara da hantara. Amma inda sabo ya kamata a ce ta saba da su daga bakin Yaya Uwais, don tun tana karama duk wata haduwa da za su yi in dai ba'a gaban Ammi ba ne to irin haka ce ta ke kasancewa."

You goddam black

"Ta saba da wannan kalmar. Shin laifi ne in mace ta kasance baka? Shin kyawun halitta shi ne yake sa wa a so mutum? Ko kuwa dai akwai wani dalili da ya sa Uwais ya tsane ta bayan wannan da rashin asalin ta? Za ta so wani makusancin sa ya samo mata wannan amsar daga Yayanta Uwais. Amma ta san ba za ta taba samun wannan alfarmar ba, ta sanin wani abu da ya danganci wannan kwayan mutum guda daya mafi soyuwa a zuciyarta, sannan mafi munana mata."

Yunwar da ya shiga kicin din da ita sai ya ji ta dauke sabida bacin ran ganin Fahima. Tsaki ya yi ya ajiye gorar ruwan ya koma daki. Ya yi nafilfilin da yake yi kafin ya kwanta sannan ya dauko waya ya kira Amrah don jin muryarta ne kadai zai sa ya yi barci lafiya.

"Sun dade suna hira, planning iri-iri na irin yadda za su gudanar da rayuwar aurensu. Hatta yayan da za su haifa sai da suka kayyade. Sannan suka koma musun da wa suke so yayan su yi kama, shi kuma ya dage da ita yake so su yi kama itama ta dage da shi take so, a haka suka shiririce suka bata lokaci. Hirar da ta kai su har sha biyun dare, sai da Amrah ta soma hamma sannan suka yi sallama."

"Da wani irin nishadi Uwais ya yi barci don in yana gaban Amrah ko yana jin sassanyar muryarta manta kansa yake yi, duk wannan miskilancin da izzar nemansu yake ya rasa in dai yana tareda Amrah, in ka ji shi yana zubo hira da kalaman soyayya ka kuma sanshi a tsumammen"

Uwais dinsa manajan GT ba za ka taba yarda cewa shi ne ba.

"Fahimah a wannan dare ba ta runtsa ba. Ba bacin ran abin da ya yi mata ke damunta ba, aa soyayya ce ta ke nukurkusarta, soyayyah yar usli mara algus daga indallahi wadda ba za ta iya tantance daga lokacin da ta samu muhalli a zuciyarta ba. Abin da ta sani kawai shi ne, ta taso cikin son Yaya Uwais ba tare da ta san hakikanin mene ne maanar feelings dinta a kansa ba. Sai yanzu a hankali da hankali ya soma game jikinta, ta fahimci zuciyarta is infactuated sosai a kan Yaya Uwais, son da ta tabbatar ba zai taba amfana ta da komai ba."

Don haka a wannan dare Fahimah ta yanke shawarar fara adduar Allah ya cire mata Uwais

daga zuciyarta ko ta samu sa'idah. Ya munana shi a zuciyarta kamar yadda ta ke mummuna a tashi zuciyar.

"Har aka yi kiran assalatu ba ta yi barci ba, tana kai wa Sarki Allah kukanta a kan Uwais. Amma ko da ta kwanta barci bayan ta sallaci asubahi, mafarkin da ta yi ya firgitata..."

"9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: *****"

"Washegari da ta gama shirinta tsaf na tafiya makaranta ta cimma Ammi a dakinta tana karatun littafin Bulugul Maram da ta ke yi duk safiya. Ta tsugunna a gabanta ta gaishe ta sannan ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Ammin ta lura akwai magana a bakinta, ta rufe littafin ta"

"ce,"

Ya aka yi autar Ammi? Kina son wani abu ne?

"A hankali Fahimah ta motsa dan bakinta kamar mai tsoron abin da za ta fada. A karshe ta daure ta ce,"

"Ammi don Allah kada ki ce Yaya Uwais ya dauko ni a makaranta, don yau ma muna da practical na food and nutrition. Ammi zan dawo da kaina tunda gobe Surajo (direbanta) zai dawo. Ammi yar ki ta girma, ki bar ta ta dinga yin komai da kanta. Ta karasa da murmushi."

"Murmushi mai sauti Hajiya Safiyyah ta yi, alkunyar yarinyar na sa wa ta kara shiga ranta. Ta tabbata Uwais rashin kirkinsa ya yi mata jiya, sannan ya hora ta da ynwa, amma ba za ta fada mata kai tsaye ba sabida kawaici irin nata. Ta kai hannu ta shafa kan Fahimah affectionately.. I will not send him to pick you again, na lura da yadda ya azabtar da ke da yunwa jiya, amma kansa ya yi wa. Ungo kudin mota ki hawo adaidaita ki dawo gida."

Ta karbi kudin da hannu biyu ta yiwa Ammi godiya ta wuce.

"Ammi, sai na dawo!."

"Ammi ta ce, Rehlah Saeedah (wato a dawo lafiya)."

Bayan wucewar yarinyar Hajiya Safiyyah ta lumshe ido ta jingina bayanta da bango tana tunani. Anya mafarkin ta zai zama gaskiya? Anya Uwais zai cika mata burinta? Idan kuma ta tursasa shi anya tirsasawar za ta haifar da Da mai ido? A kafiya da miskilanci gami da izza irin nasa da ta dade da sani? To in ba shi din ba wa zai auri Fahimah ya rike mata ita da amana?

"""Babu!"""

Amsar ta kutso da karfi cikin kwanyar ta.

"Ko ta samu masoyi ya ji ko wace ce ita guduwa zai yi, in kuma ya karbe ta a haka tofa babu daraja da martaba. Uwaisun dai da ta haifa shi kadai ne guarantee dinta a kan Fahima, amma baro-baro ya nuna gara kowa da shi in dai a kan ya so Fahimah ne. son ma irin wanda ita ta ke mafarkin ya yi mata, wanda ya kasa karbarta a kanwa ta jini, ta ya ya zai yarda ya karbe ta a matsayin MATARSA?"

Shekaru goma sha biyar a baya suka soma gilma mata tamkar a majigi.

*****

TUSHEN LABARIN!

"Bayan haihuwarta ta biyu ne jini ya tsinke mata, washegarin haihuwar yar ta koma ga mahaliccinta. Ita kuma ta samu matsalar da dole aka cire mata mahaifa bakidaya. Shi kadai gare ta, shi kadai Allah ya bar mata, UWAIS kenan."

"Mahaifinsa Justice Abdulkarim Shagari tsohon alkali ne dan asalin jihar Sokoto, wanda ya taka har matsayin Grand Khadi a lokacin rayuwarsa. Dan asalin Sokoto ne amma a Kano ya rayu sanadin aikin sa da ya samu a Kano, ya yi kuma aure da Safeeyah tun yana dalibin digiri na biyu a kasar ta Sudan inda ya yi dukkan karatunsa."

"Sun zauna a can shekaru biyar, sannan ya taho da ita kasarsa ta haihuwa, Nigeria, ya samu"

"aiki da (Shariah Court of Appeal), ya sanya ta a jamiar Bayero, inda ta yi nata karatun a fannin tsimi da tanadi. Allah ya azurta su da Da guda daya, ko ace daya tamkar da goma, shi ne"

"Uwais, wajen haihuwarta ta biyu ne waccan matsalar ta faru."

"Uwais na girma, sha'awarta da shaukinta ga son haihuwar diya mace na karuwa, bayan already an cire mata mahaifa. Duk inda ta ga baby mace kamar ta zauce, ita ba yan uwa a Nigeria ba balle ta karbo yar riko, cikin yan uwanta kuma da ke Sudan ta tabbata babu mai ba ta, alhalin tana kasar Nigeria. Don auren dan Nigeria da ta yi ma ba da son ransu ta yi shi ba. Larabawa akwai kabilanci. Maigidanta kullum cikin kwantar mata da hankali ya ke, don ta kara kwantar da hankalinta a kan haihuwar diya mace ya samo mata aikin koyarwa a Bayero University, ta zama cikakkiyar assistant lakcara."

Ba ta dade da fara aikin ba Allah ya yi wa Grand Khadi Abdulkarim Shagari rasuwa.

"Mutuwar da ta gigita Safiyyah da tilon danta Uwais. An dauki lokaci kafin su dawo hayyacinsu. Kadaici ya kara yi wa Safiyya wadda danta Uwais ke kira Ammi yawa, daga ita sai danta ta ke rayuwa sai mai aikinta Talatu, wadda ta ke tare da ita tun Uwais na karami."

"Shaawarta ga son diya mace bai canza ba bayan rasuwar mijinta, sai ma karuwa da ya yi a dalilin rashin miji mai tattali, soyayya, kulawa da nuna kauna wato Grand Khadi Shagari."

"A wani dare da kadaici ya yi mata yawa, kuma ta yanke shawarar ci gaba da rayuwa a Nigeria madadin ta koma Sudan saboda aikinta, wani tunani ya fado mata....."

"Ita dai ba za ta iya kara yin aure ba, don Uwais baya so, ya fada ya kara, muddin ta kara aure tayiwa Babansa kishiya a bayan ran sa shi Sudan zai koma wajen Kawunsa Shuraim wato Yayanta, wanda ke da da sa'ansa mai suna Mahdi, kuma ko ta yi aure ta san ba haihuwa za ta kara yi ba, don haka ta yanke shawarar dauko ya daga GIDAN MARAYU (Orphanage). Ta hada da Uwais ta rike sun isheta rayuwar duniya, tayi musu raino da tarbiyyah irin wanda take so sannan a karshe ta yi wa kowannen su aure da wuri, su haifa mata jikokin da zasu gina mata"

"extended family mai albarka a kasar mijin ta, Nigeria."

******

"""Tsintarta aka yi, a kofar makarantar firamare ta gidan Galadima, tana jaririya sabuwar haihuwa ko wanka ba a yi mata ba, a cikin kwalin taliyar indomie, ko suttura babu a jikinta, babu wata shaida da muka samu a kanta bayan wannan""."

"Shugabar gidan marayu na Kano wanda ke unguwar Nasarawa ta gaya wa Haj. Safiyya. Ta kara rike yar bakar yarinyar mai kyawun fuska sosai a jikinta, wadda ba ta fi shekaru uku ba. Ta"

cike duk wasu formalities na daukar Da a gidan marayu ta karbe ta cike da so da kauna.

"Tunda suka taho a cikin motar ta babban dan yatsan yarinyar nan yana cikin bakinta tana tsotso, alamu ne na cewa, yarinya ce mai tsananin hakuri. A nan kantinan da ke kallon asibitin"

"Nassarawa ta tsaya ta saya mata sutturun yara masu yawa, sannan suka karaso gida."

Ammi!

Uwais da ke wajen kwallon kwando a kofar gida tare da abokansa ya fada cikin mamaki a

lokacin da ya ga ta fito daga mota dauke da yarinya.

Wace ce wannan? Ina kika samo ta Ya sake tambaya.

"Murmushi ta yi masa tare da kamo hannunsa, amma sai ya janye daga gare ta cikin tsoro. Ammi ina ki ka samo ya?"

"Ta mika hannu za ta sake kamo hannunsa, ya kara ja da baya."

"Haba Uwais! Kanwa ce na samo maka, were living a lonely life, ka ga ka samu abokiyar hira da wasa idan bana nan."

Kai ya shiga girgizawa da sauri da karfi.

"Bana so Ammi, bana son ki da wani Da ba ni ba!. Haushi ya sa ta shige cikin gida ta barshi a wajen."

"Talatu ta fito daga kitchen tana wa Ammi barka da zuwa, tare da karbar yarinyar da ke hannunta. Ina muka samo ya? Tubarkallah haka?"

"Ammi ta ajiye handbag dinta a kan kujera, Kanwa ce na samo wa dan gidanki Talatu, ita ma ya"

ta ce daga yau.

"Bayan wannan har inda yau ke motsi, Talatu ba ta san ina Hajiya Safiyyah ta samo yar ta Fahimah ba. Ta san dai ba sato ta ta yi ba, amma tunda ba ta taba bude baki ta gaya mata ba sai ba ta takura mata da tambaya ba."

"Farat daya yarinyar ta shiga ranta, in Ammi na wajen aiki to Fahimah tana hannunta. Suka zage wajen kula da ita su biyu. Suna karba-karba in Ammi ta tafi aiki."

"Albashin Ammi da shi suke rayuwa cikin rufin asiri, rayuwarsu very simple, ta wadanda ilmi ya wadata. A wancan lokacin cikin gidajen malamai na sabuwar jami'ar Bayero suke zaune gidan dajami'ar Bayero ta baiwa Ammi. Sabida ya fi wa Ammi saukin zirga-zirga. Acan ta sanya Fahimah a (staff school). Lokacin Uwais ya gama ya shiga sakandire a Musa Iliyasu wadda itama nan kusa dasu take. Grand Khadi Shagari ya bar musu gadon tankareren gidan da suke ciki a halin yanzu wanda suka dawo cikin sa bayan Fahimah ta fara karatun sakandire a 'Yan Dutse College, ya bar musu gidan wanda ke unguwar 'Yankaba da tsabar kudi a banki, wanda Ammi ta sayi hanun jari da su a bankuna duk wata suna karbar kamasho. A haka ta dauki"

"nauyin karatun yayanta guda biyu, Uwais da Fahimah!"

"Cin zalin na duniya da mugunta iri-iri babu irin wanda Uwais bai yi wa Fahimah ba, wadda har gobe bai san a ina Ammi ta samo ta ba. Sai da ya shekara ashirin ne ya gane Ammi a gidan marayu ta dauko Fahimah, don lokaci zuwa lokaci yana kai su gidan marayu ta gaida wata mata wadda ya fahimci shugabar gidan ce."

"Ita kanta Fahimah ba ta san hadinta da Hajiya Asabe ba, da Ammi ke yawan kai ta ta gaishe ta in ta samu lokaci, kuma hankalinta da dan guntun tunanin ta na lokacin bai taba ba ta cewa gidan marayu gidansu ne ba. Ta fi daukar Hajiya Asabe a matsayin kawar Ammi, don in suka hadu suka tsinke da hira har ba sa son rabuwa. Daga baya Hajiya Asabe har gidansu tana zuwa, Ammi na yi mata alheri sosai. Musanman lokacin da ta zo aurar da diyarta ta fari Ammi"

ce ta dauki nauyin gado da kujeru.

"Tun daga lokacin da Uwais ya gane daga inda Ammi ta dauko Fahimah tsanarshi da ita ya karu,"

"ya nunku. Ya tsani ya bude ido ya ganta gabansa, sabida yawan tsawar da yake mata ko hanyar dakinsa ba ta bi. Haka in yana falo ta leko ta ganshi komawa dakinta ta ke ta rufe kofa har sai ya fita."

"A haka suka taso, Fahimah na mamakin abin da ya sa ita nata Yayan ya tsane ta, bayan ba haka ta ga sauran yayyen kawayenta na makaranta suna treating dinsu ba."

"Duk ranar da uzuri ya sa Ammi ba ta dauko ta a makaranta ba, ta tura shi ya dauko ta sai ta dawo da kumburarriyar fuska, ya mammake ta a motar ko ya rarrankwashe ta. Dalili hakan ya sa Ammi daukar mata direba nata ita kadai lokacin da ta shiga sakandire a Yan Dutse."

"Ammi ta yi nasihar, ta yi lallashin a kan Uwais ya karbi Fahimah a matsayin yar uwarsa da Allah ya ba shi, har ta koma ta zuba ido, domin kuwa Uwais kaifi daya ne. Kuma mai gabadaya. Abin nufi; In zai so abu dukkan soyayya yake masa, haka in zai ki shi, muguwar kiyayyah yake masa bata wasa ba. Ya sha gaya wa Ammi shi ba zai taba son wannan tsintacciyar magen da ta kawo"

musu ba.

"Tun yana yaro Allah ya zuba masa baiwar kyau na larabawan ifriqiyyah, wani irin kyau mai sanyaya idanun duk mai kallon sa, ya hore masa kwakwalwar karatu musamman darasin lissafi, don haka ne da ya zo shiga jamia ya zabi ya karanta aikin banki. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a jamiar Ahmadu Bello, inda ya karanci fannin accountancy. Bai dade da kammala karatu ba ya samu aiki da babban bankin Guaranteed Trust (GT Bank) matsayin akawu (Accountant) sabida kyawun takardunsa."

Haka rayuwa ta mika wa wannan family cike da ci gaba da nasarori. Zuwa wannan lokacin Ammi Safiyyah na amsa rank na (Associate Professor) a tsangayar Economics da ta ke koyarwa. Fahimah na ajin karshe a sakandire. Uwais kullum cikin promotion yake daga bankin GT sabida kwazonsa da persevearance. A halin yanzu shine babban manajan Branch din GT da yake kan titin (Bank Road) da ke cikin birnin Kano.

"Ya karbi ragamar kula da komai na nauyin gidansu ban da shaanin FAHIMAH. A wurin sa kam Ammi ce kawai dangin ta. Bai taba cewa wani yana da kanwa ba. Koda dangin su na Sudan. Baya bari ma wadanda suka san shi su san da wanzuwar ta tare da mahaifiyar sa. Ya tsaya kamar shine Grand Khadi Shagari, baka taba gane babu mai gida a gidan sabida tsayuwar"

dakan Uwais akan komai na gidan.

*****

"Hajiya Safiyyah ta nisa a hankali lokacin da tunaninta ya zo nan. Ba ta haifi Faheemah ba, amma yadda ta ke jinta a zuciyarta ba maraba da yadda ta ke jin tilon danta Uwais. Abubuwa da yawa suka yi sanadiyyar wannan kauna; halayen Faheemah da matsananciyar biyayyar da ta ke yi mata. Kafin a samu yarinya nitsattsiya cikin yammata dubu irin Fahimah sai an tona. Sai dai daga ita har Fahimar sun kwana da sanin cewa babu wanda Uwais ya tsana a duniya irinta."

"A shekarun ta na kuruciya Fahimah ta san Hajiya Safiyyah ba ta haife ta ba, amma in za'a kashe ta, ba ta san ta ya ya aka yi ta zo hannunta ba. Ta budi ido ne kawai ta ganta a gabanta"

cikin wata irin kulawa wadda mahaifiya ce kadai za ta yi wa dan da ta haifa.

"Safiya ce mai tsananin hazo wadda matsanancin sanyin watan Nuwamba ya haifar, ranar ta"

"kasance Litinin, aka ce ko Bature yana tsoron ki, tafe yake cikin motarsa Kia Picanto fara sol sanye cikin bakaken suit na maaikatan bankin GT, a nutse yake tukinsa kamar yadda ya saba misalin karfe bakwai na safe. Daidai lokacin da danja ta tsaida su a shateletalen Beirut Road ya rage gudun motar ya tsaya a gefen wata mota Toyota Camry. Hankalinsa na kan danja cike da kaguwar ta ba su hannu domin hakika ya kusa makara, sai ji ya yi daga gefensa an kira sunansa cikin tu'ajjibi.."

"9/23/21, 8:15 PM - Buhainat: UWAIS SHAGARI?!"

"Ya juya a hankali cikin aji irin nasa ya dubi mai kiran nasa, JABEER DIKKO. Ya kira sunan mutumin da yanayi na mamaki. Daidai lokacin da danja ta ba su hannu duk suka gangara gefen titi don su samu damar gaisawa da juna."

"A tare suka fito daga motocinsu suka cafke hannun juna, they have been good friends during their university years a jamiar Ahmadu Bello, bayan sun kammala ne Jabir ya samu tafiya kasar Kuwait yin masters dinshi, yayin da shi Uwais ya ci gaba a nan Ahmadu Bello ba su kara haduwa ba kuma sai yau. A gurguje suka yi musayen lambar waya da alkawarin Uwais zai zo"

"gidansa in ya tashi ofis don shi Jabir ya yi aure ba dadewa, a yanzun yana aiki ne da FCMB."

"Kamar yadda ya yi alkawari yana tashi daga ofis ya dawo gida ya yi wanka ya sake shiryawa cikin shadda wagambari mai hasken sararin samaniya, inda duk ya gifta sanyin Maison Francis dinsa ke tashi. A falo ya tadda Ammi, Fahimah na murza mata menthol a kafafunta kamar yadda ta ke mata duk dare, kallo daya ya yi mata ya dauke kai, a ransa fadi yake, yarinya kullum kamar ana shafa mata shuni don baki. Ammi ta dube shi affectionately (cike da kauna) ko ita da ta haife shi in ya dau wankan nan kwarjini yake mata. Ta ce,"

Sai ina haka? Bayan ga abinci Talatu ta shirya maka?

"Ya ce ""I'm sorry Ammi, an gayyace ni cin abincin dare, abokina Jabir na Kuwait da na ke ba ki labari yau Allah ya sake hada mu."

"Ammi ta ce, A dawo lafiya, a gaishe shi. Ya sa kai ya fita, Fahimah na satar kallonsa ta gefen idonta, kirjinta na wani irin duka."

"A karshe ita da Ammi suka ci abincin da ya bari din, suna gamawa ta kwashe komai ta kai kicin"

"ta gyara wajen ta yi wa Ammi sallama cewa tana da karatun da za ta yi, sai ta shige dakinta ta kulle kanta."

Fahimah Shagari.

"Kamar yadda ake kiranta a makaranta, budurwa ce yar kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa. A bana ne za ta kare karatun sakandire. A jerin kyawawan mata ba za ka sanya Faheemah ba domin ba ta da artificial beauty irin na yammatan yanzu, komai nata natural daga kalar fata har gashin kai. Baka ce sidik, fatarta mai sulbi da daukar idanu. Tana da manyan ido mai haske da madaidaicin hanci, gashin kanta kakkarfa na asalin Hausawa wanda ba ta taba yi wa relaxing ba sai dai ta yi steaming dinsa. Bakinta dan madaidaici, ba ta a layin dogaye kamar yadda ba ta a layin gajeru, ga ta nan dai yar dagwas da ita, wadda tsafta da wanka suka kama"

jikinta.

"Fahimah ta dauko littafin Food and Nutrition daga jakarta ta makaranta da niyyar karantawa kamar yadda ta yi niyya, don tana da gwaji (test) a kansa a washegari talata. Shine kuma best subject din ta. Amma me? Ko da ta bude shafin farko ba ta ga komai a ciki ba. Shafin ya koma blank, sannan basudaniyar fuskarsa ta maye gurbinsa. Ta bude shafi na biyu don a zatonta a wancan shafin ne kadai Uwais ke yi mata shifcin gizo, sai dai duka sammakal."

"Cikin kowanne shafi da ta bude ba ta ganin komai sai Uwais Shagari, fuskarsa, tsayuwarsa, cin maganinsa da maganarsa cikin seriousness. A duniya ba ta taba ganin abin da ke wahalar da ita da dagula mata lissafi ya hana ta jin dadin rayuwarta ko ta ya ya irin tunanin miskilin Yayan nata, wanda bai san tana yi ba, bai san Allah ya yi ruwan tsirarta cikin gidan su ba. Ita din ba komai ba ce face abar wulakantawa, kuma abar kyama a gare shi, to a kan me ta ke yawan ganinsa cikin idonta? Take jin amsa-kuwwar husky voice din sa? Ta ke kuma jinsa har cikin ruhi da tsokar jikinta???"

"Za ta so a ce tana da wanda za ta iya yi wa wannan tambayar, tsakaninta da kawayenta na makaranta sabgar karatu ce kadai. Ammi kullum na gargadinta a kan tara kawaye da fada musu sirrinta, ta gaya mata ita kadai za ta mayar babbar aminiyarta, komai ta ke son tattaunawa na rayuwarta da ita za ta tattauna shi, amma wannan karon ba ta jin za ta iya gaya mata cewa tana da wani irin feeling a kan Yaya Uwais da ke takura ruhinta wanda ita kanta ta ke neman sani a kansa, ko

Please Login or Register in order to submit comment