gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading NI’IMATULLAH Sirrin Wata Rayuwa by HAAJARA ABLA Chapter 9 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara ciwo sosai shina ban ma tsaya mun gaisa da momy ba natawo.”
“Ayya Sannu ubangiji ya k’ara sauki yanzu idan kin samu lokaci ai saikije.”
“Insha Allah babah.”
“To Allah ya k’ara sauk’i ki tashi kibar ma aikin haka kinji tunda baki da lafiya.”
“Aa babah mucigaba ai aikin ne yake sawa naji nasamu sauki sosai ma.”
“To shikkenan Allah ya kara lafiya mai daurewa..
Haka sukayi aikin suka gama sanan ta koma d’akin ta ta kwanta kawai taji sha’awar barin tahau online dan kwana dayawa ta shiga cakwakiya ta manta da wani chat......



Sak’onni masoya na fatan Alkhairi take ta gani masoya suna ta tambayar yaushe za’a sa musu wani littafin mai dad’i haka dai sak’onni kala kala ta amsa wanda zata iya sanan ta koma ta kwanta ta cigaba da chat d’inta. Sak’onsane ya shigo ta whatsapp d’in nata.....



Vote
Share
nd comments fisabillilah.🙌🏻
NI’IMATULLAH



By haajara abla



ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(Annuri is the best).




SHAFI NA ASHIRIN DA HUD’U 24

Da kamar bazata duba ba kawai sai ta tsinci hannunta dakaiwa ta bud’e sak’on nasa”Assalamu alaiki,NI’IMATULLAH nashiga mutuk’ar damuwa sosai sanan mun kira wayar ki bata tafiya,bayan na koma gida ni kad’ai nayi ta kiranki taga k’arshe kika sani a call waiting,na shiga damuwa saka makon abin da ya faru yau NI’IMATULLAH kamar akwai abin da yake d’auke miki hankali,dan Allah idan bazaki damu ba ki daure ki sanar dani maike faruwa dake?” Tana dubawa taga kuma yana online dan haka bata yi masa banza ba sai dai kawai ta fahimta abin da tayi d’in dan ita sam batasan ma tayi ba wallahi saida suka fad’a mata,typing tafara yi masa kamar haka”babu abin da yake faruwa dani paris?”
“Ba haka bane,nifa ba yarobane duk da kina daukata wani daban wanda baisan mai yake ba amma nasan abin da nake.”
“Bahaka bane paris nidai kam ada na d’auke tamkar wani mafad’aci wanda baisan darajar mata ba sai na gano cewa a duk sanda muka had’u mukayi rigima to tabbas ka ceceni ne ko kuma ni na ceceka.”
“Mai kike nufi da hakan NI’IMATULLAH saidai bangane abin da kike nifi ba?”
“A rananr da muka fara had’uwa na tawo a mota na bigeka sosai a wanan yanayin I know that I’m not comfortable na tasan tuk’in ganganci nayi maka ka tsayar dani kafin nakai daf da yan ma’aikatan tsaro na kan titi wanan tsaayarwar da kamin tabbas ta na k’arasa gaban su a wanan yanayi zasu iya kamain,secondarily mun had’u a restaurant indan na shak’e Alhaji dan gaske agaban ma’aikatan sa da bodyguard d’in sa without my sense da bakazo kayi abin da kayi ba tabbas da wani daga cikin su ya harbeni k’arshe ma na rasa raina,sanan had’uwar mu a school na bige ka ka bigeni munyi karo Na fad’a kan k’irjinka a time din da banyi maka tijara ba,babu wanda zaice mudin bama sane mukayi haka,sanan a gidan rawa tabbas daban nuna maka k’iyayyya ba da inaga ba labarin ka ake a wajen SAHEED ba.”
“SAHEED kuma wane SAHEED wane shi maine had’in ki dashi.”
“Wanan babu ruwanka just my personality issue ne.”
“Amma mai yasa ni bazan jiba.”
“You are not my personal at all,maiyasa kake son jin abin da bazai amfane kaba.”
“Nasan duk maganar da zata fito daga bakin ki mai ma’ana ce sanan duk a maganganun ki akwai amfanuwa mai yasa bakya son naji.”
“Uhm paris dare yayi kaga har k’arfe d’aya na dare good nyt bye bye.” Tafad’ar haka ta kashe datar ta d’aura wayar bisa k’irjinta. Kawai ji tayi a ranta tana son magana dashi tana son suyi fira tamkar dai wasu wad’an da suka saba taji hankalin ta ya kwanta da paris sakamakon duk abubuwan da suka faru lallai paris mai k’aunar tane amma dai kamar ita wani lokacin matsaloli da rashin mafita suna jefa mutum a wani hali idan baiyi da gaske ba,amma shi paris ai bashida matsala tunda babanshi attajiri.”
Amma sometimes mainkud’i yafi kowa matsaloli da tarin damuwa Allah yasa mu dace.....


A bangaren sa kuma yau akaro na farko sun zauna sunyi magana ta fahitar juna shida ita sunyi magana ba cikin fad’a ko masifa ba,gaskiya he enjoyed the mood,saidai bata amsa masa tambayar saba wane SAHEED.. yaso ya damu akan naganar SAHEED amma a karo na farko NI’IMATULLAH tabashi dama sunyi magana dole ya godewa Allah sai yaji yana jin wani kalar sanyi wanda yake ratsa masa zuciya,yasan tabbas yana son NU’AIMA amma kuma yanzu irin son da yakewa NI’IMATULLAH bazai iya kwatantashi ba yana jin zai iya bada rayuwarsa akanta,yasan insha Allah a hankali a hankali zata fahimce sa..”





Washe gari da misalin k’arfe shida na yamma aka aiko wai ana sallama da NI’IMATULLAH cike da mamaki take kallon yaron sanan tace”kaje kace inji wa.”
Komawa yayi yaje yace dashi”wai tace injiwa?” Shiru yayi dan yasan idan yace inji shi is hardly ta fito dan haka sai ya tsinci kansan da cewa kace inji SAHEED.”
Komawa yaron yayi yace mata”wai inji SAHEED. Cike da zumud’i tace kaje kace masa gani nan. Tashi tayi ta d’aukko hojab dinta har kasa tasa sanan ta fita yana cikin mota kuma motar da tin dan haka bata tab’a tunanin cewa wanine a ciki ba SAHEED ba. Bud’e k’ofar gaba tayi ta shiga ta zauna tanjuyawa tare da cewa”kaine da wanan lokacin prin.... sai ta tsaya tayi shiru ganin paris ta saki baki.”
Murd’a k’ofar tayi zata fita ya rik’e mata hannu tare da marairaicewa”plsss NI’IMATULLAH dont do that to me dan Allah kia saurareni banazo dan na b’ata miki bane.”
Ajiyar zuciya tayi sanan ta dawo ta zauna tare da fad’in”maine ya kawo ka k’ofar gidan mu paris,mai yasa dan Allah mai yasa kake so naci amanar k’auna naci amanar zaman tare?”
“Subahanallah dan Allah wannan wace kalar magna ce kinsan ceww kotare da NU’AIMA zamu iya zuwa nan amma mai yasa kike ganin kamar cin amanane,yesss of course cin amana ne cin amanane mana paris,ta d’auki yardar ta tabani amma mai yasa kake son kaja mana abin da duniya zatayi ala wadai damu.”
“Bahaka bane dan Allah kada kice haka dan Allah.”
“Shikkenan paris nagode da kulawarka agareni,nagode.”
“Yawwa zan rok’i Alfarma d’aya a wajen ki dan Allah.”
“Ina jinka wace alfarma ce wanan?”
“Inason mu zama a bokai ina nufin best friend.”
Ita dariya ma ya bata tayi Murmushi sanan tace”matar ka tana my best friend nd you too.”
“Yeah of course.”
“To shikkenan amma fa dole rabin raina tasan da wanan amintar.”
“Don’t mind.”
Haka dai ta lallab’ashi sukayi sallama sanan ta sauka tsayawa tayi har ya tafi ta daina ganin sa,sanan ta samu wani d’an dandamali ta zauna a k’ofar gidan su kawai tana ganin mutane masu shige da fice da yara da manya kowa yana abin da ke gabansa,yaran ne suke ta burgeta duk da cewa ita ko a yarintarta babu wani abin jin dad’i amma duk da haka tafi son yarintar tata saboda duk abin da za’a mata tana fita zata manta tayi ta wasan ta na k’asa amma yanzu kam sai hamdala...


Bayan kwana biyu ne ta shirya zuwa gidan su NU’AIMA dan bata dauki motar taba gashi biki yana ta matsowa tanaso suje sukai ankon wajen d’inki saboda tuni su INAYATULLAH suka fidda ankon dan haka har Na NI’IMATULLAH an riga da an siya sanan daman ga momynsu tana neman ta dan haka ta shirya ta nufi gidan su NU’AIMAN.”

Saida akazo daidai gate d’in gidan mai mai adaidata sahun ya ajje ta ta ciro kud’i ta bashi ta bar masa harda canjin ma ta shiga ciki..
Saida ta shiga palorn momy tayi sallama amma ba kowa nan ta haura sama d’akin NU’AIMA...
“Oyoyoooo rabin raina sai yau.”
“Kedai bari I’m sorry nasan ban kyuta ba,amma kisan nid’ince sai a slow.”
Duka ta d’ala mata a baya sanan tace”aikuwa dai wallahi ga ankon kican na dinner dana mother’s even harda ma na kamu yanzu d’inkin kawai zamuje mukai sakan mu fad’a masa rana ita yau zamu amsa.”
“Tam shikkenan kamar yadda kika fad’a haka za’ai amma kince momy tana nemana.”
“Eh momy tana nemanki amma kibari mu dawo ai sai ku gana ko.”
“Tam shikkenan babu damuwa.”
Tafiya sukayi suka kai d’inki inda ta kira Luv d’in nata tace masa Suna tare da NI’IMATULLAH a wajen d’inki. Aikuw cikinzumud’i yace gashi nan zuwa sai tace masa ya samesu a gida saboda har sun kammala yanzu zasu koma...

Kafin su isa gidan ma ya riga su zuwa haya ya shiga yayi parking ya zauna a wata kujera dake harabar gidan bayan sun gaisa da mai gadi...


Baifi 10mints ba aaiga su sun dawo,kawai NI’IMATULLAH yake kallo ko daukewa bayayi amma saboda hankalin NU’AIMA baya wajen sam bata kula ba,koma ta kula bazata kawo komai a cikin ranta ba...

“Sannu da zuwa luv.”
“Yawwa luv ya kuke NI’IMATULLAH ina yini.”
“Lafiya Kalau Alhmdlh ta amsa sanan tayi hanyar shiga palorn.”
Katseta yayi da tafiyar tare da fad’in “uhm NI’IMATULLAH kizo kimin bayanin yadda abubuwan zasu tafi kuma nawa zan bada kuma wasu hall ya kamata a kama dan shagulgulan.babu yanda zatayi tace bazata dawo ba,dan haka kawai ta dawo ta zauna tana murmushin yak’e...
NU’AIMA ce tace bara naje na d’aukkobiro da takarda ayi lissafe liassfen sai a rbuta.”
Juyawa tayi ta nufi cikin gidan....

Komawa yayi ya zauna ya dubi NI’IMATULLAH yace”NI’IMATULLAH wallahi a kullum inason in cireki a zuciya amma kullum abin dad’a faskara yake... katseshi tayi da cewa”wallahi pariskoda ace soyayya muke dakai NU’AIMA ta ganka tace tana sonka kai zata aura wallahi saina bar mata bazan tab’a auran kaba...


“Dan Allah NI’IMATULLAH ki amince ki aureni,inason zan aureki wallahi ina sonki.”
Tuni jikin ta yafara rawa sosai da sosai idonta ya zazzaro aikuwa tunita shak’esa irin mummunan shak’a wacce har numfashinshi yake d’aukewa....

Daidai nan NU’AIMA ta fito kuma taji abin da yace dan haka kawai faduwa tayi a sume.....


Vote
Share
Nd comments fisabillilah🌹.
NI’IMATULLAH



By haajara abla



ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(Annuri is the best).


Wanan page d’in sadaukarwa ne gareki SHUKRATA🥰❤️😍Allah yabar kauna😍masoyiya kiyi yanda kike so dashi haajara abla takice🤩.



SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU 22

Babyna kuma. Ta sake maimaitawa a cikin zuciyata katse ta yayi tare da fad’in “daman nasan zaki kirani NI’IMATULLAH nayi ta kiran number bakya d’agawa bansan maike faruwa ba amma ina fatan kin ga sak’ona kuma kina cikin k’oshin lafiya.”
“Naga sak’on ka amma ina son insan wane kai kuma mai kake nema a awajena?”
“Kamar yadda kika sani nine Salman saidai mafi yawancin abokaina suna kirana da paris sanan nin....”
“Dakata min ba wanan nakeson jiba ina son insan maine dalilin ka na kirana a waya sanan mai kake nema a gareni da ka hanani tutawa ka hanani sakewa ka shigo min rayuwa da takura mai na tsare maka?”
“Babu abin da kika tsare min nidai nakwai Na fad’a miki soyayyar ki nake nema.”
“Soyayya ta kake nema aikuwa bazaka tab’a samu ba wallahi sanan idan kace zaka soni mutuwa zakayi Na fad’a maka,soyayya ta ba abu mai sauk’i bace da zan amsa a wajen wanan in kaiwq wanan,sanan kai taabar bama kada kunya ka rasa wacce zakace zakaso sai aminiyar wadda akayi muku engage saboda toshewar kwakwalawa irin taku ta masu shaye shaye...”
“Ya isa Haka NI’IMATULLAH kin kirani dan ki cimun mutunci.” Sai a yanzu ma ta tuna cewa ita ta kira saboda tsabar tana cike da jin haushi yasa ta mata aikuwa k’ittt ta kashe wayar nan ya dame ta da kira har saida tayi blocking d’in layin saboda sam ita batama tab’a ganin mutum irin paris ba,gashi a haka kamar mai hankali amma ina ashe babu wanan hankali yanzu banda toshewar basira how did he say that,yasan cewa me nd NU’AIMA are best friend may be dai baisan irin amintar datake tsakanin muba shiyasa... Tafad’a tana jan tsaki dan ya b’ata mata rai bad’an kad’an ba...



Fitowa tayi da d’ayrin kirji ta d’auki bokiti ta d’ebi ruwa ta saka ruwan zafi sanan ta siria ta shiga band’aki tayi wanka. Bayan ta fito ta zauna ta shafa mayukanta masu dad’in k’amshi dasa laushin fata da gyara fata,kanta ta gayara sanan tayi parking d’nsa wata doguwar rigar abaya ta d’auka ta saka tayi mutuk’ar yi mata kyu sosai abin ba’a magana tana cikin shiryaawa babah jummai ta shigo d’akin rik’e da ruwan rubutu da addu’o’i a hannunta ta mik’a mata sanan tace malam yace idan zata kwanta bacci zatasha sanan ta shafe jikin ta”Yawwa NI’IMATULLAH sanan karki manta idan kinzo kwanciya bayan kin gama cin komai kin gama shan komai sai ki d’ebo ruwa a kofi ki karanta ayatul kursiyyu k’afa bakwai ki tofa ya zama shine k’arshen abin da zakisha haka ma inkin tashi daga bacci kafin kici komai ki tofa ta kafa bakwai kisha kinji,Allah ubangiji ya k’ara sauk’i ki dage na sanki bakya wasa da addu’a amma akwaiki da shiririta dan haka ki dage kinji,Allah yace tashi intaimake ka ubangiji ka taimake mu baki d’aya.”
“Ameen ya Allah babah,ameen ya Allah babah nagode sosai da sosai da kulawr ku a gareni yanda kuke kuka dani da k’annena ubangiji ya kula daku ranar tashin alk’iyama ubangiji ya baku aljanna.”
“Ameen ya Allah NI’IMA ameen ya Allah tare dake Allah yayi miki albarka ya baki miji nagari ameen ya Allah..

Tafad’a mata cewa zata gidan su NU’AIMA saboda NU’AIMA tana neman ta sanan ma ansa ranar bikin su wata d’aya mai kamawa.”
“Masha Allah ubangiji ya nuna mana yarinyar kirki,ubangiji ya nuna mana naki haka.”
“Ameen ya Allah babah.”
Tashi tayi ta nufi gidan su NU’AIMA,ba jimawa saigata taje mai gadi ya bud’e nata ta shiga da mitar ta sanan tayi hanyar palorn nasu...
Tana zuw ada sallama ta shiga inda momy ta tare ta tana mata fara’a sosai..
“Inayini momy?”
“Lafiya kalau dota yakuke yasu mamanki?”
“Suna lafiya Alhamdulillah.”
“Masha Allah haka akeso.”
“Momy ansaka kuma ranar su NU’AIMA ubangiji ya sanya Alkhairi ya basu zamn laafiya yasa zamu gani.”
“Ameen ya Allah yarinya ta,kema da zaki fito da miji tare zan had’aku na muku auren ai duk lokaci d’aya.”
Dariya tayi cike da jin dad’in abinda momy tace ta sunkuyar da kanta k’asa....
“Kinga rabin ran taki tana sama tana danne danne waya amma bari na kira miki ita.”
“Tam nagode momy.”
“Ki daina min godiya ki d’auke ni tamkar uwa agareki.”
“Insha Allah momy.”
Wayar ta d’auak ta kira NU’AIMA ta fad’a mata rabin ran ta na jiranta a k’asa fa...

Sakkowa tayi jiki a salub’e NI’IMATULLAH tayi mamakin ganin ta a Haka saboda sam bata saba ganin NU’AIMA haka ba dan kuwa idan akace tazo gidan nan nasu tsalle tsallen da NU’AIMA take sha ke kyace k’aramar yarinya ce.
Kafin NU’AIMA tayi magana momy ta kalli NU’AIMA sanan tace”lafiya momyna what’s wrong with u,are u ok.”
“Yes momy i’m ok.”
“Amma kamar kinyi kuka.” Murmushi ta k’ak’aro sanan tace”eh mana momy kuka nayi fa wani agogona ne danasiya a cyprus na nemesa na rasa sai kuma daga baya na gansa da har na fara kuka.”
“Allah ya shirya min ke ta fad’a.
Direct kusa da NI’IMATULLAH tazo ta zauna tana fad’in sannu da zuwa rabin raina.”
“Yawwa rabin raina sannu.”
“Uhm taso mu fita garding. Ta fad’a tana ruk’o hannun NI’IMATULLAH...

Tafiya sukayi a farfajiyar gidan su suka isa garding d’in daya yalwatu da shuke shuke masu ban sha’awa filawowi kala kala da furranni ga bishiyu na marmari abin gwanin ban sha’awa...

Zama sukayi akan kujerun da suke a cikin labun sanan NU’AIMAta kalli NI’IMATULLAH tace”yakike fabin ran.”
“Lafiya ta kalau amma ke kam baki da lafiya kuma kinyiwa mama k’arya maike damunki mai yasaki kuka.”
Cikin muryar ban tausayi tace”NI’IMATULLAH ina cikin damuwa sosai kawai k’arfin hali nake banaso mama ta fahimci abin da ke damuna duk da ita uwace mai fahimta nasan zata iya fahimata amma banason ta fahimci matsalar danake fama da ita saboda banason damuwar ta.”
“Subahanallah mai yake faruwa dake ne har haka.”
“Uhm NI’IMATULLAH ina cikin damuwa sosai kinga tunda aka fara maganar auren nan Salman ya canza baya kirana a waya ni zan kirasa sai ya kawo min uzuri yana kaza yana kaza sanan abu kad’an sai ya ringa min fad’a kin sani i cant take it any more ni banason fad’a shiyasa ma Allah bai halliceni da son shiga cikin mutane ba saboda ni bani son fad’a ko kad’an zuciyata tana min zafi sosai da sosai ina tunanin ko na masa wani abu ne yake min haka amma na kasa ganewa.”
Wani dogon numfashi taja sanan tace”amma rabin ran kin tabbata biki masa wani laifin ba.”
“Wallahi rabin ran babu laifin dana masa kinsan ina sosa sosai kinsan bazan iya yi masa laifin dazaiji haushi har haka ba sanan har yayi zuciya,bnsani ba ko dan yaga inasonshi shiyasa yake min haka.”
“Kiyi hakuri bahaka bane kin fad’a min cewa Salman mutumin kirki ne ko so bana tunanin cewa zaiyi miki wani abu kodan ya b’ata miki ki masa uzuri a koda yaushe ki zamo mai yiwa mutum uzuri kinji,sanan kirasa kinji zan masa magana.”
Ba musu ta ciri wayar ta tafara danna kiransa amma har ta katse bai d’aga ba.
“Kin gani rabin raina na kirasa bai d’aga ba kuma idan za’a kwana bazai kirani ba kuma bamu saba haka dashi ba,kin ga dole zanyi zargin ko auren ne bayaso dani.”
“Shittttt karki sake fad’ar haka dabaya sonki da bazai zo gidan ku ya b’ata lokacin sa abanza wajen kiranki a waya da zuwa inda kike da kuma kaiki inda kike buk’ata.”
“Amma rabin raina mazan yanzu ne I’m scared wallahi ina jin tsoro.”
“Calm down everything will be right insha Allah karki damu yanzu bani number tasa na kirasa.”
Karan to mata number tayi,thesame number sa datayi blocking sauri tayi ta bud’e dankar NU’AIMA ta gane sanan ta danna kira tasata a handsfree,aikuwa ringing biyu ya d’aga tare da cewa hello ba.... bata bari ya k’arasa ba tayi maza tace”Assalamu alaikum,sunana NI’IMATULLAH nice aminiyar NU’AIMA daman NU’AIMA ke kiranka baka d’aga shine nace bari na gwada a tana yanzu muna tare da ita gata nan.”
Tana bata wayar tayi mata da alama tayi magana gaisheshi ta farayi yana amsawa yana taso ta bawa NI’IMATULLAH wayar wai su gaisa.bayan tabawa NI’IMATULLAH wayar ne tace masa”yawwa ango daman kai muke nema idan bazaka samu damuwa ba yaushe zakazo muyu maganar yarda zamu shirya bikin da kuma tsare tsaren da zamuyi.”
“Ah aha ai babu damuwa yanzu ma sai intawo babu matsala.”
“Ahh ayi haka kada mu tsareka ko kana aiki.”
“Aa babu damuwa yanzu zanzo insha Allah.”
Haka sukayi sallama cike da mamaki NU’AIMA ta juya ta kalle ta tare da fad’in “rabin raina kinji wani ikon Allah kinga yanda yake ta rawar jiki saboda kin masa magana ikon Allah kenan.”
“Babu wani ikon Allah daman Na fad’a miki may be ko aiyukane suka masa yawa amma ai mutumin kirki ne wanda zaki aura ki kwarara gwiwarki banason ki ringa karya zuciyar ki a wani lissfi na daban kisa a ranki cewa Salman naki ne kuma ke tasa ce da yardar Allah har abada koda kuwa kinga wani suyi to karki manta da Allah kikai kukan ki wajen Allah insha Allah komai zai tafi kamar yadda yakamata.”
“Nagode nagode sosai wallahi zuciyata tayi mutuk’ar yin sanyi sosai da dad’i naji dadin kasancewar ki a tare dani fatana ubangiji yabar mana zumuncin mu har zuwa k’arshen rayuwar mu.”
“Ameen ya Allah ta amsa.”
Da yake gidan su Salman da NU’AIMA babu nisa hakan yasa nan da nan yazo parking yayi sanan ya sakko daga motar,kiran NU’AIMA yayi yace mata ya iso suna ina ta fad’a masa sanan ya nufi wajen.
Yana k’arasawa yaji tamkar an sashi a aljanna saboda NI’IMATULLAH dake wajen sai wani kallonta yake ita kuma basarwa tayi tare da fad’in “sannu da zuwa angon NU’AIMA.” Murmushi yayi sanan yace”yawwa amarya.”
Zaro ido tayi tace amarya kuma?”
“Eh mana amarya,NU’AIMA zata zama amarya ai kinga kema amaryace.”
NU’AIMA ce tace”wanan haka yake luv ina yini sannu da zuwa fatan kazo lafiya.”
“Lafiya kalau luv Alhamdullila yasu momy.”
“Kalau suke.”
Zama yayi suka fara hira dai sama sama Sai NI’IMATULLAH tace”rabin ran kinbar bak’o babu abin sha.”
“Wayyo Allah na sha’afa kinga koke ma haka na barki wayyi duk da cewa kedai ba bakuwa bace.”
“Hhhh fad’a mata dai NI’IMATULLAH.”
Sam batason yana kiran sunan ta har wani k’arawa yake da wata lankwasarsa ta munafinci...
Tashin NU’AIMA tayi ta tafi kawo musu drinks inda NI’IMATULLAH ta maida kallon ta wajen paris tare da cewa” aduk sanda zamu had’u arziki baya had’amu sanan baya rabamu inaso yaudai d’aya kabari mu had’u cikin arziki sanan mu rabu cikin sa.”kallon ta kawai yake yana murmushi yanaji kamar ya had’iyeta...
“Inajin ki madam.”
“Ya kamata yanzu ka tsaya kasan inda yake maka ciwo NU’AIMA tana da hakuri sosai idan ka sameta a matsayin mata kayi sa’a duniya kai har ma da kahira saboda zata iya yi maka silar shiga Aljanna ma,dan haka ina mai maka nasiha dan Allah ka kula da ita kamar yadda kake da koma yafi da kuna shirin aure,shi kuma aure ba abu bane na wasa dan Allah paris ka ajje duk wasu shaye shaye da abubuwanka a gefe saboda Allah ya baka mata mai kyu ga kyan hali ga hakuri....”
“Wai mai yasa kike ta wanan lissafin ne kan NU’AIMA ai a kanki yakamata ki lissafa wanan abubuwan duk wasu qualities da kike fad’a ai kin fita dan haka ni...”
“Ni ban fita ba ai kasan a inda muka tab’a had’uwa dakai dan haka karka kirawoni a matsyin wata mai qualities like that ka manta kalaman ka agarenj ne yar bariki yar shayeshaye duk da cewa ni ban tab’a shan wani abu dan ya sani maye ba amma ganin da ka min a bariki ka fad’i komai a kaina so ka ajje wanan maganar a gefe.”
“Sooo kingani ke yar bariki ni d’an shaye shaye kin gani mumua fi dacewa da juna amma ba NU’AIMA ba......
K’arar plate d’in data d’aukko drinks d’in sukaji a k’asa sun juyawa sukayi ido hud’u da ita.......





Vote
Share
And comments fisabillilah.
NI’IMATULLAH




BY HAAJARA ABLA


ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(annuri is the best).



SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI 27


Da sauri ta tashi ta kallesa ta murza idonta sanan ta sake kallonaa ta murza idonta wai maike faruwa ne ya ta ganta anan kuma..
“Sannu NI’IMATULLAH ya kan naki,fatan ya daina ciwo.”
Ohhhhh sai da yace mata ya kanta sanan ta tsaya ta d’anyi tunani a lokacin ne ta tuna cewa ashefa bata da lafiya ta tuna da duk abubuwan da suka faru jiya,aikuwa jikin hanzari ta tashi daga kan gadon tare da cewa”ina NU’AIMA ta farka ya jikin nata. Tana k’ok’arin sa takalmi ya tsayar da ita tare da mik’a mata hijab d’inta ta saka sanan suka fita tare dashi asuba ce dan haka ya nuna mata d’akin da NU’AIMA take ba’a shiga hakan yasa ta lek’ata ta window tana kwance dai kamar yadda suka barta jiya. Wani hawaye ne ya gangarowa NI’IMATULLAH ta koma ta zauna akan seat d’in da yake kusa da room d’in da NU’AIMA take...
Bayan yayi sallah yadawo ya tadda ita a zaune a wajen yace mata tatashi taje tayi sallah ya nuna mata masallacin mata inda ba musu taje tayi sanan ta dawo bacci yana d’aukarta saka makon allurar da aka mata a haka ta zauna a seat d’in har barci ya kwasheta,yayi yayi su tafi gida amma tak’i tace bazata iya barin NU’AIMA anan ba..
Gashi har tayi bacci yana so yaje gida yayi wanka sai ya dawo saboda jikin sa duk yayi tsami.
Juye juye ya fara ko zaiga NA’EM amma bai gansa ba,sai ransa kawai ya bashi yana reception tashi yayi ya nufi reception d’in aikuwa ya hango NA’EM zaune saman seat yana ta danna waya.
K’arasowa yayi inda NA’EM d’in ya d’go da kansa tare dacewa”Paris kaine da safiyar nan haka?”
Waje ya samu ya zauna sanan yace” uhm ai anan na kwana fa,jiya bayan ka tafi gida ni kuma na fita restaurant dancin abinci na ragewa NI’IMATULLAH hanya dan nakaita gida amma ta ringa kuka bazata bar NU’AIMA ta tafi gida ba,sai kuma tafara min ihu wai kanta zai rabe haka cikin gaggawa muka dawo asibitin a lokacin banga momy ba dan haka likita ya bata gado,yanzu haka maganar danake maka tana k’ofar room d’in da NU’AIMA take tace bazata iya tafiya tabarta ba kuma allurar barcin da aka mata bata saketa ba dan haka gashi har tayi bacci.”
“Ohhh Allah gaskiya wanan yarinya tana kaunar Aima sosai kaga fa wani ikon Allah ni bantab’a ganin k’awance kalar nasu ba tabbas wanan kawaye ne abin so Allah yabar musu zumuncin su.”
Ameen Paris ya fad’a tarre d tunanin cewa lallai idan NU’AIMA ta dawo hayyacinta zata fad’awa kowa abin da ya faru sanan zata tsanesa amma ba laifina bane NU’AIMA Ki fahimceni wallahi Allah ne ya jarrabeni da son aminiyar ki bani da yanda zanyi na kaucewa k’addara ta.
“Ya naga kayi shiru lafiya

Please Login or Register in order to submit comment