gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading NI’IMATULLAH Sirrin Wata Rayuwa by HAAJARA ABLA Chapter 3 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

satin nan ya k’are babu inda zani.” Heeeeeyyyyy suka tashi suna murna suna fad’a goge hawayenta tayi sanan ta tashi tayi sallah ta had’a musu kari sukaci da yake yau babu makaranta haka suka zauana suna ta mata surutu duk da rabin zancen ba ganewa take ba dan nasune na yara.

Fitowa tayi tsakar gida da rana ta zauna akan kujera dan ko wayar ta ma bata kunna ba tunda ta dawo dan yanzu tana buk’atar kad’aicewa ita kad’ai tanaso tajita tamkar ya’ agaban iyayenta hakan yasa ta fito tsakar gida cike da kewa da begen mahaifiyar ta...

Haka ta zauna tana ta kallo masu shige da fice da yaran gidan da kuma iyayen su,yaudai yini akayi murja ko lek’e da ita da y’ayan ta dan kuwa ta tsorata mutuk’a da lamarin NI’IMATULLAH ta dauka yau a lahira zata kwana saboda har taurari ta ringa gani...
Ita kuwa baba jummai har kokin ta kawai take yi tayi abinci rana na siyarwa har ya k’are...

Haka da yamma tayi ta koma d’akinta ta zauna sai taji ta duk a takure tunda bata saba ba duk zaman gidan wani iri duk babu farin ciki a cikin sa gashi tayiwa su Abbas alkawarin bazata futa ko nan da can ba....



Yau kwana bakwai kenan kullum idan tazo school bata ganin NI’IMATULLAH abin yana damunta sosai da sosai san haka tace sai taje gidansu taji ko tana lafiya gashi wayarta akashe ta kira ta kira har ta gaji....

Gashi har yanzu drivan da zai d’auketa bai zoba daman INAYATULLAH bata zoba bata jin dad’i kawai sai ta kirasa awayata tace anjima ya sameta a unguwar su NI’IMATULLAH ita kuma ta tafi a d’an sahu...

Saida mai d’an sahun ya kaita har layin su NI’IMATULLAH sanan ya ajje ta a daidai kofar gidansu inda malam yake zaune da almajiran sa haka ta zo ta tsugunna ta gaida shi sanan ta shiga gidan cikin sa’a ta tarar da ita a zaune tayi tagumi a tsakar gidan da gudu ta k’arasa ta rungumeta tana fad’in” why are u trying to hurt me,mai yasa why kinsan i cant take it any more.”
“Murmushi tayi mai cike da kewar Ninun tata tace”oya oya take it easy tashi mu shiga ciki.”
Tashi tayi suka shiga cikin d’aki ind NI’IMATULLAH tabawa NU’AIMA ruwa da lemo tace it baza tasha ba sai ta mata bayanin mai yasa bata zuwa school kuma wayarta akashe.”
“Dan Allah kisha ruwa then we talk.”
Matsawa tayi ta d’auki ruwan tasha sanan ta koma ta ningina da bangon d’akin ta tankwashe k’afarta akan katifar sanan ta d’aga mata gira alamar”yess ina ji bani lbr mai yasa bakya zuwa school.”
“Ohhhh Ninu na banda lafiya shiyasa biki ga na rame ba.”
“Ayya sorry wallahi bansni ba mai yasa biki kirani kin fad’a min ba mai ya faru mai ya sameki gashi nan duk kin rame sosai jifa yanda kikayi maike faruwa.”
“Ke Ninu jifa inda kika d’aga hankalin ki haba bafa wani ciwo bane kawai zazzabi ne.”
“Zazzb’i shine kawai,to an miki test?”
“Eh an yimin.”
“Cant i see.”
“Nuni ni bansan ma inda na jefa saba ai naji sauki an min allura fa sosai.”
“Shikkenan Allah ya k’ara sauk’i amma wallahi kika sake rashin lafiya biki sanar dani ba haka sai munyi fad’a.”
“Ni na isa nayi fad’ da rabin raina.”
Babu wata rabin ranki gashi har kin manta da wata NU’AIMA ko ki fad’a mata baki da lafiya.”
“Ohhhh ni NI’IMATULLAH,to ninu ko na baki bulala ki dakeni sai ki rage.”
“Rufe min baki ni.”
Hhhhhhh dariya sukayi suka cigaba da fira bayan magrif ta kira driver ya dauketa zuwa gida.


Bayan ta shiga gida ne tayiwa momy sannu da gida ta haye sama b’angaren su,direct bedroom nasu ta nufa inda ta samu Inaya tana ta chat sallama tayi sanan ta tsaya cire kayanta ta dauki towel ta d’aura ta shiga bathroom yin wanka...

Bayan ta fito ne ta zauna kan stool shafa mai da gyara gashin kanta kamar daga sama taji Muryar INAYATULLAH tana magana”sannu da dawowa ko kema kin fara yawa bin club d’in ne bansani ba ko yau kin rakata.”
Tashi NU’AIMA tayi ta koma kusa da INAYATULLAH ta kamo hannayenta biyu sanan ta fara magana.”yanzu INAYATULLAH kina tunanin zan iya aikata kuskure da zunubi kalar haka,mai yasa zaki min wanan fahimtar mai yasa zaki ringa zargin NI’IMATULLAH kawai fa mu kawayene kuma ina kaunarta sosai.”
“NU’AIMA bafa wai dan banason ki ko kuma banasonta bane kawai alak’ar kuce banaso kin manta illah da k’awa tayi miki kin manta abinda soyayyar k’awa ta janyo miki?”
Kuka sosai NU’AIMA ta fara mai tsuma zuciya dakyar INAYATULLAH ta ringa lallab’ata har ta tsagaita sanan NU’AIMA tace”wallahi ban manta ba INAYA ban manta ba kuma bazan mantaba har abada,zuciya ta tana min zafi sosai idan na tuna amma babu yanda zanyi wallahi ina kaunar Ni’imatullah duk da bansan maine tarihin taba bansan mai rayuwar ta ta kunsa ba amma nasan rayuwar ta abar tausayi ce kuma tana bani tausayi sosai wallahi INAYATULLAH kema zaki iya fahimtar ta,bansa ya zafin rashin uwa yake ba kema kanki biki sani amma ita ta sani tana fama da wanan d’acin ga k’anana yara guda biyu ga zafi talauci dake damunsu idan kika kalli rayuwar ta abin tausayi ne kawai a ciki ba kamar kalar tamu ba dan Allah ki fahimce ni Yar uwata.”...




11/1212022✍🏻
NI’IMATULLAH



By haajara abla


ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(annuri is the best.)




SHAFI NA TAKWAS 8

SAHEED ta fad’a cikin jin dad’in ganin sa datayi a wanan lokacin. Bata k’ara ganin saba dan ya b’ece sai ta b’ata rai ta koma zata zauna kenan taji an ruk’ota ta baya yayi hugging nata ya juyo da ita ta fuskance sa suka fara rawa cikin kid’an da yake tashi,cike da jin dad’i cikin da murna da farin ciki take tunanin ina ma ace kada a gama wanan rawa ina ma ace su dawwama cikin farin ciki kamar haka ita wanan rayuwa tata da SAHEED tana mata dad’i sosai tana jin ta tamkar a rayuwar datayi a cikin farin ciki a baya kafin dagulewar al’amuran rayywarta sosai sukayi rawa ita dai daga k’arshe Sai bud’e ido tayi ta ganta a kwance akan katifar ta ta gama shek’a baccin ta...

Tashi tayi tayu alwala tayi sallar asuba bata bar wajen ba ta zauna tana ta karatun al’qur’ani da istigfari da hailala har sai da rana ta fito....


NU’AIMA kuwa baya ta koma cikin gida d’akinau kawai ta nufa ta haye sama ta shiga bargo ta lullub’a wai maike faruwa ne da NI’IMATULLAH haka gashi dai a yanayin ta da kuma tarbiya da addini irin nata sam tasan abin da take aikatawa bashi da kyu amma kuma ko a jikin ta tana accting kamar ba wani abu bane takeyi wanda bai kamata ba amma tasani ita kanta kuskure take...
“Nashiga kuskure a baya saboda soyayya data rufe min ido amma bana ji zan iya bawa wani d’a na mini damar da har zata kaishi da yq tab’a hannuna bakle kuma ya kasance dani,amma wanan ma duk aikin kawai ne tunda har ina da tabo mai muni da idan na tuna sai nayi da nasani har yau.... haka dai take tunani kala kala har barci ya d’ebeta....

Washe gari da safe bayan ta shirya tsaf dan kuwa yauma suna da makaranta kuma idan bazata manta ba yaune partyn birthday na d’an gaske so zata kasance a tare da NI’IMATULLAH dan kuwa bataso ta halarci wajen gaskiya...

Shiryawa tayi tsab cikin shirin ta mai kayatarwa yau ta fito a asalinta na shuwa arab tayi mutuk’ar kyu sosai haka ta fito ta nufi shashen momy dan su gaisa...

“Momy good morning.”
“Morning my baby how was your night?”
“Fine momy.”
“Ok ya NI’IMATULLAH taje gida hope lafiya?”
“Lafiya kalau momy.”
“Ok masha Allah yau kuna da school ko?”
“Eh momy but INAYATULLAH fa, naga bangantaba na dauka ma tana nan.”
“Aa taje wajen daddyn kune.”
“Ok nima bari naje na gaida shi.”
Tana zuwa ta tarar dashi suna fira shida INAYATULLAH tsugunnawa tayi ta gaida shi sanan ta nemi waje ta zauna.
“Mamana ki shirya saboda na shirya muku flight zaku tashi da yamma zuwa umra sanan zamuje cyprus amma tare zamuje da momyn ku gabaki d’aya.”
“Wowwww daddy what surprise.”
“Hhhhh yar gidan daddy kenan sai ki tashi kije ku shirye shirye kafin anjima.”
Taji dad’i sosai amma kuma dad’i daya dabataji ba shine babu NI’IMATULLAH a wanan tafiya dan haka kawai dai murna tata ba wani cancan bane tama fi murna da zata umra duk da ba wanan ne karon ta na farko ba....


Wanan dalilin yasa ta fasa zuwa school suka fara shirye shiryen dan gane da tafiyar su dan basu san ma iyakacin kwanan ki da zasuyi ba haka dai suka shirya aikuwa at afternoon jirgin su ya tashi zuwa k’asa mai tsarki.....


Shiryawa tayi tsaf dan kuwa tunda safe Alhaji d’angaske yake mata waya yana tuna mata tace tana sane ai bata sab’a alk’awari haka da daddare ta shirya cikin shiga mai kyu da aji da d’aukar hankali tamkar dai wata amarya ko sarauniya kyanta ya fito sosai iya fitowa wanda duk inda ta gifta sai an kalle ta kuma muddin kana da cikakkiyar lafiya idan ka ganta tabbas sai wani abu ya d’arsu a cikin zuciyar ka....

Address d’in wajen tabi inda ta k’arasa tayi masa waya gata fa tazo kofar wajen. Da kansa ya fita ya shigo da ita mata da mazan dake wajen duk wanda ya kalleta sai ya sake ganin ta tayi masifar yin kyu sosai fiye da yanda ba’a zato,shi kuwa alhaji d’an gaske sai wage baki yake saboda shi wanan shine wanda ya samu dami a kala...


Nan take aka fara gabatr da program akazo aka yanka cake inda ita ta yanka masa cake d’in inda kuwa anan wajen yayu mata kyutar wani gidan sa wan da yake a tudun yola a birnin kano haka cikin jin dad’i aka rak’ashe aka shana aka raba dare ana party saidai yayi yayi tasha drinks tace bata shan wine hakan yasa yace aka wo mata wanda ba wine to abinka da club ne duk anyi miss ita kuma bata sani ba haka ta karba tasha aka ci gaba da casu....


Bud’e idon ta tayi ta ganta a hotel inda alhaji dan gaske ya kama musu d’aki dan shak’atawar su...

Haka suka kwashe kwana biyu suna shoshalewa sanan a rana ta uku da daddare ta d’auki motar ta dan komawa gida...
Tasha shisha ta bugu sosai dan kuwa alhaji a wanan kwana uku ya b’ata ta da kud’in dan haka har yakai da ya koya mata shan shisha ma abin da batayi da yace ita ba komai bace kawai flavor ne...


Tafiya take yi wanda ita kanta bata san yana yin datake ciki ba kawai sai ji kake kikkkkkkkk motarr ta ta bigi wata mota..

Fitowa tayi da sauri inda shima ya fito da sauri cikin fushi yake magana”ke wace kalar dabba ce da zaki shigo kai tsaye kina nema ki haddasa min bala’i.”
“Cike da mamaki da kallon rainin wayo take binsa daga gani kalar y’ayan masu kud’in nan ne data tsana kallon sama da k’asa tayi misa sanan taja tsaki ta koma cikin mota,dan ita ba ma’abociyar rigima bace amma kuma ta tsani rainin hankali.

Shiga tayi ta d’aukko rafa na yan dubu dubu na dubu d’ari ta wulla masa sanan tace”idan na maka b’arna kayi hak’uri ka iya gyarawa.”
Ai baisan lokacin da ya fisgota ba ke wacece da zaki watao min kud’i a yan iskan ke wacece kinsan wanene ni kinsan d’an wanene u are very nonsense idiot i will show u who I’m ya fad’a yana matsowa kusa da ita.

Mutanen da suka fara taruwa a wajen ne suka rik’esa suna bashi hakuri ya wullo mata kudin amma basu shiga motar taba yana ta sababi idon sa yayi jajawur dan b’acin rai ita kuwa komawa tayi cikin motar ta tabar wajen....



Wacece ke da zaki jefo min kud’in kinje kinyi shaye shayenki na banza shine zakizo ki janyo min bala’i....

Abin da take ta maimaitawa kenan tabbas ko wane wanan yaci mata mutunci kuma wallahi bazan yarda ba sai na rama cin mutuncin da ka min niba mai shaye shaye bace mai yasa zaka kirani da yar shaye shaye idan kace min yar iska ban musa ba amma why ta fad’a tana kuka he call me idiot mahaukaciya duk dan na gogesa ban ganin ba Allah ka sake had’ani da wanan bawan naka ka sani ni ba mai san rigima bace amma ya ubangiji ka sake had’ani dashi... ta fad’a tana kuka....

Gida ta wuce ta kwanta cikin b’acin rai da rashin jin dad’i ahaka har bacci b’arawo yayi awan gaba da ita....



“Ya ubangiji ina rok’onka da ka yafe min zunubaina ka rabani da wanan mugayen mafarkan marasa amfani ubangiji ka shiryar damu hanya madaidaiciya ya ubangiji ga baiwarka nan NI’IMATULLAH ya ubangiji ka kareta ka shiryeta ta gane gaskiya ka rabata da wad’an suke san ganin sai sun ruguza rayuwar ta ya ubangiji kada ka basu sa’a ya ubangiji kada ka basu nasara Allah ka cika min mafarki na na samun miji nagari kamar d’an uwana da ake so a had’amu aure ubangiji kasa Alkhairi kasa ya soni kamar yadda nake kaunar shi ubangiji ka bamu zuru’a d’ayyiba ubangiji ka bawa yar uwata da iyayena ka biya musu bukatunsu Na alkhairi ya ubangiji ka karemu daga sharrin mai sharri ubangiji ka yafe mana kurakuran mu kasa mu yan aljanna ne kasa mu cika da kalmar LA’ILAHA’ILLAHLAH Kasa annabi(S.A.W.)ya cece mu ranar alk’iyama...”
Wanan itace addu’ar da NU’AIMA take a duk lokacin da suka shiga harami....


Koda ta tashi Alhaji dan gaske ne ya dame ta da kira akan yana son su sake had’uwa dan gaba d’aya ya kasa hakura da NI’IMATULLAH yayi mutuk’ar kewarta na kwana d’ayan nan ji yake zai iya mutuwa idan bai had’u da ita gaskiya yana so su had’u ne dan yanaso ya furta mata cewa yana so zai aureta ta bashi dama danshi a yanzu bashi da wani buri da ya wuce kawai ace NI’IMATULLAH ta zama matar sa......



14/12/2022
Ablas’glam ce🥰
Comments
Share
And like#.
NI’IMATULLAH





BY HAAJRA ABLA



ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(annuri is the best)




SHAFI NA SHA D’AYA 11

D’aga hannunsa yayi da niyyar ta kifa mata mari sai wani yayi sauri ya rik’e hannun nasa tare da cewa”haba abokina baka ga a halin da take ciki bane Sai fad’a kake ga fama zuba mata kodai ka santa ne?”
“Yeassss na santa na santa mana bata da hankali ni nakasa gane ma maike damunta.”
“D’ayan ne yace”calm down aboki kalli fa a halin data ke ciki bata hayyacin ta tunda kasanta kuma Allah yasa mu rabasu da Alhaji ka d’auketa ka kaita gida mu kuma zamu kai Ahaji asibiti.”
Zaiyi magana kenan wanan d’in ya dafa kafad’ar”plsssss aboki kai musul mi ne kada kace komai dan Allah ka dauke ta ka kaita gida na rok’eka.”
“Akan mai kuke rok’ata har haka ban gane na kaita gida ba gidan ubanwa zan kaita kuma wanan juyewar kwakwalwartata fa ya danganta da abin da tasha so ni bazan iya yin jigilar taaba gaskiya.”
Yarinyar da yake jin haushin ta kamar ya kashe shine za’ace ya d’auke ta ya wani kaita gida ina never wallahi ya fad’a a zuciyar sa...
“Yanzu ka yarda ko ko yaza’ai mu bamusan gidan su ba ko iyayen ta.”
“Ga shawara oya check her phone mana.”
“Matsala da security a jiki.”
Haka dai ya wuce ya barsu samu sukayi suka sata a mota kawai suka wuce asibitin da suka kai Alhaji itama nan suka kaita aka fara bata agajin farko....

Alhaji yasha wuya kafin ya farfad’o dan shi ya d’auka ma ta kasheshi dan sai yanzu ya sake tabbatar wana wanan yarinyat bafa mutum bace Aljana ce...

Bayan ya huta ne wani abokin sa da aka kira yazo shida bodyguard d’in alhajin suke tambayar alhajin cewa yarinyar nan fa tana kwance anan asibitin wane kalar hukunci yake so ayi mata...


Ai yanajin sunce tana kwance a asibitin yayi zumbur ya tashi yace”babu hukuncin da zansa ayi mata ta dawo cikin dare ta kashe ku tashi mu tafi na warke wanan yarinya ba mutum bace Aljana ce.”

Aljaana kuma?”
Suka had’a baki wajen fad’a.
“Eh aljana Na fad’a muku aljana ce.”
“Toooo cike da mamaki suke binsan,d’ayan ne ya kuma cewa”kenana alhajin duk kyututtukan daka mata taci banza kenan.”
“Kai dallah rufe min baki wane yake ta wata kyuta ana ta rai ku tashi mu yafi idan kuma baza ku tafi ba ni nayi gaba kwa sameni a gida.”





“SAHEED ina fad’aa maka ina sake fad’a maka ka fita al’amarin yarinyar nan.”
“Kai acikin ibilisai wane kai kai wanene da zaka zo kana fad’a min wanan maganar arnen aljani ko maine?”
SAHEED sak’o aka bani,kada kaga kai sarkin aljanune kayi gaggawar kwance alak’ar da kake so ka k’ullah Na fad’a maka saboda ita NI’IMATULLAH tunda aka haifeta bata kowa bace sai tashi.”
“Tashi tawa kuma kaiii shed’ani aljanu fito fili kayi min magana.”
“Tun ranar da aka haifi NI’IMA ranar aka bawa Shugaban mu ita a matsayin hadaya har yazo ya k’ulla alak’a da ita yanzu jira yake lokacin da ya kamata ya saudakar da ita yayi dan haka ina mai baka shawara da hakuri da ka nisance ta nisa na har abada.”
“K’arya kake kayi kuskure jinin NI’IMATULLAH d’aci gareshi yayi kad’an yashashi la’ananne kaje ka fad’a masa ni SAHEED na k’aryata sa kuma bai isa ya rabani da NI’IMATULLAH ba mu zuba dashi mu gani idan yana jin shi wani babban shed’ani ne yazo da kansa muyi gaba da gaba dashi sai mu banbance wanda ya dace da NI’IMATULLAH.”
“Shikkenan na barka lafiya sarkin sarakunan musulman aljanu....
Nan take ya b’ace yabar SAHEED a zaune a fada yana ta safa da marwa k’arya yake wallahi ba’a haifesa ba shi wanene mai akayi da shed’ani ma kalar sa mai akayi da uban sa ma balle shi to bai isa ba yana nan yana dakon sa su zuba su gani....


Motsawa tayi a hankali ta gyara kwanciyar ta sai kawai taji kamar dai akan wani anu take ba katifar taba a hankali ta fara bud’e idonta haskem d’akin ya fara haske idon ta a hankali ta gana bud’esu tangararau akan ta...

“NINU kin farka sannu kinji ya jikin naki zaki sha ruwa.”
Cike da mamaki take kallonta sanan take kallon yana yin wajen inda NU’AIMA ta zuba mata ruwa a cup ta bata tace tasha...

“Amma NU’AIMA mai yakawo ni nan kuma mai ya faru dani,nifa lafiyaya kalau.”

“Nima bansani ba NINU nakira waya ma’aikaciyar asibiti ta d’aga tana min bayani daman suna jira a kira ne saboda wayar taki bata shiga ta fad’a min kina nan kin samu ne,gashi cikin ikon Allah ma yau kin farfad’o...
“Wai NU’AIMA kenan bayau nazo nan ba,fad’a min tun yaushe nake nan wajen.”
“Uhm tun jiya ne fa da yamma ai biki dad’e ba.”
“A wajen k’annena kamar nayi shekara ne,wanan rikitarciyat rayuwar tawa NU’AIMA na rasa kuka zan zauna yi ko mai,wataran kawai nakamyi murmushi a wuce wajen saboda idan ma nasa damuwa a raina babu amfanin damuwar babu wani abu da zai sauya fa.”
“Kiyi shiru NI’IMATULLAH komai lokaci ne kuma komai zai tafi zai wuce kamar tarihi kamar ma babu abin da ya faru.”
“Ance min wai fad’a ne ya had’a ki da wani a restaurant kika shak’e masa wuya,nayi mamaki kuma ban yarda ba dan nasan ke ba ma’abociyar rigim bace.”
Sai Yanzu NI’IMATULLAH tayi jigum sanan ta gane ma mai yahad’ata da Alhaji taji yace dai zai aureta tun daga nan kuma ciwon ta ya tashi....

“Ina jinki Ki fad’a min mai ya faru?”
“Uhm ina wanan alhajin da ya bani sabuwar mota da gida a tudin yola.”
“Eh ina jinki.”
“Shine yace nazo mu had’u akwai maganar da zamuyu yana ta so sai mun had’u da muka had’u kuma si yace wai yana so ya aureni.”
NU’AIMA shiru tayi tana sauraronta ganin tayi shiru ta tsaya alamar tagama magana yasa NU’AIMA cewa”to da yace zai aureki mene kuma ya had’a ku fad’a maine yasa kika shak’esa?”
“Wallahi bansani ba NU’AIMA ni bansan na shak’esaba nidai tundaga wanan maganar da yayi min bansake sanin inda kaina yake ba sai yanzu.”
“Nagane kiyi shiru kinji kiyi shiru may be Allah yasan alhaji dan gaske ba Alkhairi bane a gareki shiyasa baisa kun fahimci junan kuba insha Allah very soon Allah zai kawo miki wanda zaku fahimci juna dashi kuma Allah zai baki miji nagari bama irin waccen shed’ani ba daman sam buku dace ba wallahi ke mutuniyar arziki shi kuma na banza.”
“Aa NU’AIMA kada kiso kanki mana nima ba mutuniyar arzik bace mutuniyar banza ce kalarsa shiysa ma ya nemi aurena saboda na dace dashi din,maine a tare dani na mussaman ai bangansaba.”
Ki daina fad’ar haka dan Allah NINU komai naki na mussaman ne kema ta mussaman ce kuma ke ba mutuniyar banza bace nutuniyar arziki ce NI’IMATULLAH bawai ina fad’a bane dan kiji dad’i ina fad’in ai nayin abin da yake gaskiya ne,duk inda kika zauna sai an k’aru dake duk wajen da kikaje sai haske ya bai baye wajen Allah yayi miki tarin baiwa amma kinsan a koda yaushe Allah yafi jarabtar bawan sa mai imani saboda ya gwada k’arfin imanin sa a koda yaushe bawan da yakasance cikim imani shi ake jarabta da k’addara kala kala idan kika cinye ta sai ya yi miki sakayya da gidan Aljanna kece kike fad’a min wanan a duk sanda na shiga damuwa so dan Allah kibar komai ba komaiba watarana sai labari it’s the matter of time.”
“Nagode ya’r uwata nagode da Allah ya had’ani dake a matsayin aminiya nagode ke yar uwatace ina kaunar ki Allah ya cika miki burin ki.”
“Ameen ya Allah,ni ki daina min godiyar nan saboda babu godiya a tskanin mu.”
Dariya sukayi sosai suka cigaba da fira..
“Ina salman kuwa?”
“Allah sarki salman mutumin kirki ko yau ma saida mukayi waya dashi amma har yanzu NINU yak’i yace yana sona kuma duk abin da muke kalar na masoya ne amma sai wani zgaye zagaye yake min.
“Babu komai karki wani damu zai fad’a ne da bakin sa aike tasace shima nakine Maman daddy.”
Tafad’a tana dariya. NU’AIMA fita tayi ta kira likita tazo ta cire mata ruwan sanan ta sallame su duk NU’AIMA ce ta biya kud’in komai da komai a asusun ta na banki.....

D’aukar ta tayi a motarta suka wuce gidan malam direct...

Suna isa k’ofar gidan suka tarar dashi kad’aine almajiransa sun tafi bara fitowa sukayi su biyun suka zo suka tsugunna suka gaidashi sanan NU’AIMA tafara magana”malam daman d’azu ne aka kirani daga asibiti a waya akace min tana asibitin ta samu suma da naje ma ban dad’e ba ta farfad’o sunce kwana ta d’aya kuma ba’a zo daga gidan suba shiyasa ma na kawota bayan an bamu sallama sanan ta ciro katin tana nuna masa tana k’ara masa bayani....


Salati yayi yace ai basu sani ba,yana ganin ta kuwa yaga rama a indota sosai addu’a yayi masu sosai sanan yayiwa NU’AIMA godiya yace su shiga gidan gashi nan zuwa....


Suna shiga ta tarar dasu Abbas ana ta wanke wanke da gudu suka taso suka rungumeta suna mata oyoyoooo. Malam ne ya shigo ya fad’awa baba jummai abin da ya faru sosai ta nuna damuwarta ita kuw murja ko a tafi silifas d’inta..

D’akin ta ta kaita sanan tayi mata sallama ta tafi gida dan Yamma tayi....

Tana komawa gida ta shiga wanka saboda gajiya tana fitowa daga wanka ta tarar da INAYATULLAH tsaye gabanta tana mata kallon sama da k’asa sanan tace” fad’a min daga wane club kuke ko hotel?”..........




Share it fisabillilah.
NI’IMATULLAH



By haajara abla


ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(annuri is the best).


Bani da bakin da zanyi godiya abisa kwarin gwiwar da kuk e bani NI’IMATULLAH fans tare da sauran makaran ta NI’IMATULLAH a duk inda kuke nagode sosai da sosai kuma sak’onninku suna iso min nagode ubangiji yabar zumunci.❤️🥰😍🤗😘


SHAFI NA GOMA 10

Koda ta tashi taga baccin sai Allah ya mantar da ita mafarkin datayi duk ta sha’afa dan shirye shirye take saboda yaune zasu fara exam d’in k’arshe dan haka babu wasa gashi ko karatu bata samu damar tayi ba shiysa ma take so taje da wuri dan taje library tayi karatun tasan insha Allah zata haye...

Abaya tasa bak’a kawai ta yafa mayafin abayar ta d’auki jakarta tayiwa su Baba jummai sallama sanan ta wuce school d’in tana k’arasawa direct dai library ta nufa inda ta shige ta zauana tayi ta karatu sosai har tam ya rage baifi minti goma a shiga exam d’in ba...


Fitowa tayi ta zauna akan kunerar dake kusa da department d’in nasu har saida lokaci ya kusa ciki sanan ta shiga class d’in juyawa tayi ta sake juyawa amma bataga su NU’AIMA

Please Login or Register in order to submit comment