gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading NI’IMATULLAH Sirrin Wata Rayuwa by HAAJARA ABLA Chapter 8 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

isa ka dakatar dani.”
“Kai dakata min kai wanene kai gaskiya zamu samu matsala dakai yanzu nan ranka sai ya b’aci indai har baka janye ba to sai kayi danasani.”
“Karya kake kaine zakayi danasani bani ba kaine zakayi danasani....

Wanan fad’an da aljanun suke tsakanin su shine ya d’aga min hankali ya rikita min lissafi na toshe kunnuwana na saki wata k’ara mai mutuk’ar k’arfin cikin tashin hankalin da tunda nake ban tab’a sintsar kaina ciki ba saboda cece kuce na aljanu ba wani abu bane mai sauk’i nima ina ga dan inada shan ruwa agaba ne shiyasa har izuwa wanan lokacin ban rasa rayuwata saboda yanda rayuwa take watan gaririya dani.

Yanzun nan zan daura aurena da ita idan ka isa ka dakatar.”
Canza harshe ya dawo yafara wani yaran dan kuwa yanda suke d’aura auren su da banbanci duk da kuwa shid’in musulmi ne,bangane mai yake cewa ba kawai sai naga wash fararen mutane da fararan kaya sun bayyana a take yace”Nazrin. Nazru kune shedata zan d’auara aure da sarauniya kuma d’aurawa tahar abad.... cikin zafin hannu ya kawo masa bugu i cikin bajinta ya goce ya tashi tsayenanfa suka ja da baya sukayi carko carko indayace”Nazrin kaita gida zanyi maganin wanan k’aramin Alhakin k’armin mara mutunci..

Nidai kuka nake tayi saboda magana ma ta gagareni,to ina ma zan iya wata magana....


Baccin datake ne har safiya baya farka ba yasa baba jummai shigowa d’akin taga ko tana lafiya.. surutan dataji tana farfad’ a bacci shine ya tada hankali baba tayi suri ta kira malam shima zama yayi yana jin abin da take da fad’a Allah sarki malam har kwalla yayi saboda tausayin rayuwar NI’IMATULLAH tunda ta taso a rayuwrta bata hutaba take garari suke fafutuka ita da mahaifiyar ta gashi yanzu babu mahaifiyar ta sai ita idan daman tasha fad’a masa, wallahi baba malam bana jin dad’in rayuwar danasani inda zanje mutuwa ta riskeni wallahi baba malam dana tafi can...

Cikin lallashi yake mata nasihohi masuratsa zuciya yakan fad’a mata cewa”daman ita duniyar nan da muka zo ta bak’uwa ce duk iya adadin shegarun da zamuyi a cikin ta bazai wuce shegaara d’ari ta hamsin ba idan mafa munyi da yawa,haka zamu koma gidan mu Na gaskiya anan zamu san cewa tabbas wance gida da muka zauna a cikin sa na aro ne kuma duk daran dad’ewa daman ance zamu koma gidan gaskiya shiyasa kullum nakeso kada ki shagala da duniyar nan kar ki shagala da kyalekyalanta kinga abubuwa da dama a rayuwar ki tabbas idan kika zauna kika maida lamarin ki da Allah kika daina sab’onsa tabbas Allah zai saka miki sanan zai miki tukuici da sakamako sakamako mai kyu,wanda bikizo duniya a banza ba inda zaman lahira shine zama zama ne na dawwama ba mutuwa rayuwace ta har abada babu mutuwa...
Share kwalla yayi yana shirin tashi yaje ya nemi wasu saiwa akwai maganin da yakeso ya fara gwada mata sai gashi ta farka da kuk wiwi.
Babah jummai ce ta matsa kusa da ita tare da lallashin ta”kiyi hakuri kinji NI’IMATULLAH ke a haka taki k’addarar tazo,amma insha Allah malam zaiyi k’ok’ari dan ganin ya rabaki da wad’ancen shed’anun.”
Batace komai ba sai kukan datake. Malam ne yayi gyaran murya yace”kiyi hakuri NI’IMATULLAH ki daina wanan kukan naki kada su Abba ma zuji ki,a kullum ina miki nasiha da cewa kiyi hakuri idan kikai hakuri tabbas watarana sai labari za’a wayi gari tamkar wad’anan abubuwan duk basu faru ba,sanan ki k’ara jajur cewa a wajen ibada nasanki kina da ibada amma ki k’ara jajircewa sosai sin ringa da sun bud’e miki ido dole sai munyi da gaske wajen rabaki dasu,bara naje na kawo miki wani tofi da rubutu sai kisha.”
D’aga kanta tayi alamar ta gode sanan ta sunkuyar da kanta ta koma ta kishinkid’a akan filon katifar...

Fita sukayi su biyun babah taci gaba da aikin gabanta sanan ta zuba mata abin karyawa tabawa Abba ya kaimata...
Murja ce ta salallab’o tazo tacew babah”wai kuwa maike faruwa ne a gidan nan kodai mun samu k’aruwa ne.”
Babah ce cikin mamaki dan bata gane inda zancen murja ya dosa ba tace”karuwa kuma wace ta haihu ko kece zaki haihu ko bakuwa kikai.”babah Tafad’a tana Murmushi..
“Habada jummai wace kalar haihuwa kuma ni da ciki ai na gama,amma na dauka ai ita waccen farar shegiyar yarinyar ce tayi ciki naga keda malam sai sunturi kuke a d’akinta.”
“Amma wallahi murna kinjji kunya da bazaki daina wanan mummunan halin naki da kika arabkika yafawa kanki masifa ba,insha Allah baza muga ranar ba,bakin ki ya sarin d’ayan kashi,ina miki nasiha da ki rage irin wanan abun dan kuwa yara mata gareki,kuma inda kikace haka zaki wallahi zaki gani a kanki Allah ya kiyaye amma nidai nasiha nake miki....
“Allag ya kiyayye muguwa mai mugun alkaba’ir ki gani a kanki wallahi ni a cikin ya’yana banu wacce zatai cikin shege daman nasan bak’in ciki kike min dasu saboda ke Allah bai baki ba to Wallahi aniyar ki ta biki li’ilafi wallahi.” Tafad’a tana ta tofe tofen miyo..
Banza babah tayi da ita ta cigaba da aikin gabanta dan taga alama ita murja ba aikin yi garetaba dan haka bai kamata ta biye mata su zama d’aya ba....



Bayan baba ta fita a d’akin ne ta tashi zaune tafara tunani,malam yace zai rabata dasu kenan har SAHEED kenan zai rabata da SAHEED gaskiya idan hakane da sake dan kuwa baza tasha ba dan batason ta rabu dashi bazama ta iya rabuwadashi ba saboda tana sonshi kuma tana k’aunarsa sosai da sosai dan haka ta yanke shawarar koda malam ya kawo mata wani addu’a ko rubutu bazatasha ba saboda iya bata son rabuwa da SAHEED,amma kuma sai wani tunani yazo mata shifa SAHEED musulmi ne Ai addu’ar bazata cutar dashi ba shikkenan sai kuma a k’ona wancen sed’ani damanita yanzu shine tashin hankalin ta shine yaje sata firgit shine yake dagula mata tunani yaje ruguza mata lissafi amma idan akayimata maganin sa ai ta huta...


D’akaur wayar ta tayi taga an kikkkirata wata sabuwar Number ita dai batasan ko ta waye ba an mata wajen 10 misscall a lokuta nabanbanta sai kuma kiran NU’AIMA shina dataga miss call d’insa sai kuma sa’ko da NU’AIMA ta turo mata ta inbox d’inta...

Kiran waccen number tayi amma har ta kaste ba’a d’aga ba sai ta koma kan sak’on NU’AIMA.


“Assalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu fatan kina lafiya rabin raina ina ta kiranki biiki d’aga ba bansani ba ko bakya kusa da wayar inaso im fad’a miki cewa jiya fa su Daddyn dubai sun Kawo kud’in auren sanan an saka tana one month amma NI’IMATULLAH ina cikin damuwa dan Allah idan kin samu lokaci inaso yau kizo gidan mu ina cikin damuwa.”


Kiranta tayi suka gaisa sanan tayi mata Allah yasanya alkhairi kuma tace insha Allah zatazo kada ta damu...


Bud’e email d’inta tayi nan taga an turo mata da sak’o ta cikin sa...

“Hiiii dear I don’t know what really happened to me I don’t know what my heart really feels nd the only things I know is I’m in love,i fall in love with the best nd the most beautiful girl NI’IMATULLAH no matter what,i don’t care about anybody saying,just let anybody to say anything i don’t care, I’m in my neel please i beg u to understand me nd to have me special space in your heart i love u nd I can’t hidden u bcos it’s paining me,i love u ndi will marry u....
Daga masoyin ki paris.


A zabure na mik’e ina k’ara bin sak’on da karantawa yanzu paris saboda bashi da kunya bashi da mutunci shi basan annabi ya faku ba shine zaice yana sona?
Wai yana sona?,is he out of his sense,tabbas he is drunker zaiyi abin da yafi haka ai na d’auka ya daina shaye shayen amma ashe har yanzu da sauran shi,ohhh wato shine yayi min wad’anan kiran to bari ni nakirasa i will go nd meet him,zai fad’a min idan ni muna wasa dashi har da zaizo min da wanan maganar banzar wai zai aureni how dare he is ma mtwssss.”
D’aukko wayar ta tayi ta sake bin layin da kira aikuwa ya d’aga cikin salo da murya mai kashe jiki yace mata”Assalamu alakium babyna......





Vote
Share
Nd comments fisabilillah🙏🏻.
NI’IMATULLAH



By haajara abla




ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(Annuri is the best).




SHAFINA AISHIRIN 20


Gumi ne yake karyo masa ta ko ina duk da kuwa sanyin A.C dake wajen.
Daddy ne yace dashi”lafiya SALMAN maike faruwa ne?”
“Uhm ahh babu komai babu komai.”
“Babu komai look at u,gaskiya akwai abin dake damunka look nifa Abban kane so idan zaka b’oyewa kowa da muryarka nasan bazaka b’oye min dan haka inason inji maike damunka?”
“Am daddy daman babu komai,hakane muna soyayya da NU’AIMA.”
“Ok idan madai da akwai wani abun ka fito ka fad’a min na baka nan da 2days idan kana da magana sai kayi dan banason auren nan ya haura wata biyu.”
“To to shikkenan babu damuwa Insha Allah.”
Acikin zuciyar sa kuwa shi kad’ai yasan halin da yake ciki.”
Thesame abinda ya tambayi SALMAN shi ya tambayi HISHAAM cikin farin ciki da gan d’auki ya nuna shima hakan yayi masa daidai.

Yana fita direct wani joint ya biya gaskiya maganar gaskiya shi bazai iya auren NU’AIMA ba saboda harga Allah shi yanzu NI’IMATULLAH yake so yanzu yaya zaiyi,gashi baisan yanda zai tunkari NI’IMATULLAH da zancen soyayyar saba zata so kokuwa akasin haka kuma idan ta amince zai aureta ne yabar NU’AIMA?”
Wad’anan tambayoyi sune suka hana zuciyar sa sakat ya rasa ta ina zaisa ranshi da rayuwar sawa yayi aka kawo masa wine ya zauna yayi ta d’urka kamar an aikosa...



Zaman gidan ya ishheta sosai gashi sometimes idan ta zauna sai ta ringa jin kamar kukan jarirai gashi sai taji kamar ana tsotsar nonanta wasu yanayi dai kala kala haka take jin su,gashi ta kwana biyu rabon dataga SAHEED ko mafarkin sa,gashi tana son ganin sa dan ta fad’a masa cewa a shirye take da buk’atar sa amma har yanzu bata gansa ba kawai batasan sadda tasa takalmin taba tacewa baba zata gidan su NU’AIMA.tana fita tahau motar ta direct bata wuce ko ina ba sai wani joint dake kusa dasu cewa tayi akawo mata abinci da lemo tayi order tana zaune tana danna wayar ta dai babu yanayin farin ciki kuma babu na bak’in ciki amma kana kallonta kasan akawai damuwa sosai a tattare da ita. Tana zaune tafara cin abinci ne NU’AIMA takairata,d’agawa tayi da sallama”wa’alakissalam yakike NINU,fatan kina lafiya.”
“Lafiya kalau Alhamdullilah aima kefa yasu momy.”
“Kalau suke,wai kinsan mai yafaru yaufa Salman yazo sunyi magana da daddy,i stay nd expect amma bai kirani yamin sallama ba,i call his phone but it’s swichoff, idont know what’s going on,kodai ya canza shawara ne ya daina sona kuma bazai aureni ba shiyasa yayi min haka da yaji zancen aure daddy yayi masa.”
Tana cikin yi mata magana ne ita kua ta hango sa da cup yana tashan abin sha batasandai mai yake shaba.
“It’s okay dear,babu zancen daina so ko bazai aurekiba dole sai ya aureki?” Tafad’a tana kallon inda yake.
“Rabin ran dole kuma?”
“Ayya sorry i mean he love u more so hakan bazai canza ba,sanan ki masa uzuri may be ko ya tafi kiran gagagawa ne,ina dai so ki zama mai uzuri d’an rik’e waya i will call u back soon.”
Katse wayar tayi ta tashi ta nufi inda yake a zaune yana ta fama.
Zama tayi a d’ayar kujerar datake fuskantar sa tare da fad’in”Asssalamu alaikum.”
Kamar a mafarki ya jiyo muryarta dakyar ya iya d’go kansa yace”wa’alaikumussalam. Cikin maye dakyar ma ya iya fad’a.
“Mtwssss wallahi ka b’ata wayon ka paris maike damunka what’s kind of stupidity is? Ka bani manaki wallahi iskancin naka datashan cin naka anan ya kare kenan.”
Zuba mata ido yayi yana ta kallon ta,baice komai ba sai kawai yace”kaini gida.”
“Gida kuma kamar yaya na kaika gida dani na kawo ka to kamar yadda ka kawo kanka haka zaka koma kuma bari kaji badan dan ance zaka auri NU’AIMA kake wanan abin ba to aure babu fashi kasa a ranka kamar anyi auren nan dakai da ita an gama.”
“Ya zaki ce haka...ni..fa.. ina da wadda nakeso..”
“Kana da wadda kake so bayan NU’AIMA ban gane ba.”
“Ehhh niii...keee..nake.so ke nake kauna..”
Matsawa tayi dabata tabbas yana cikin maye da n kuwa baya cikin hayyacin sa yake irin wanan zan tuttukan bari ta bashi waje. Har ta tashi ta fara tafiya shidai ya langwab’ar dakai yana ina zakije.”
Sai take ganin idan tatafi tabarshi anan anya kuwa tayiwa NU’AIMA adalci tunawa da aminiyar tata da amintar dake tsakanin su tayi sai ta tunda da irin yadda take son paris hakan yasa tayiwa masu aikin wajen magana akan cewa dan Allah d’an uwantane ga motar sanan zata kwana a wajen sanan su sashi a motar ta,ta basu Number waya da address d’inta saboda tsaro...


Bayan ansashi a bayan motar ne ta jata suka fara tafiya,to amma ai ita batasan gidan suba a ina zata ajje sa kenan ya subahanallahi Allah ya had’a ta da wanan bala’in tunda take had’uwa dashi daidai da rana d’aya bata tab’a hutawa ba duk sanda zata had’u dashi saiya sata a bala’i tana fatan cewa wanan shine karo na k’arshen had’uwa dashi a rayuwar ta.... tana cikin tunanin ne ta sake tuna cewa batason fa inda zata kaisa ba. Juyawa tayi ta kallesa tace ina zan kaika wai?”
Kaini sakkoto road ok ba musu kuwa tayi hanyar Nasarawa G.R.A a birnin kano saida suka shiga titin tace to munzo,ok gida mai lamba... aikuwa babu wahala dan a titi yake saida tazo daidai gate d’in gidan tace dashi”yanzu yazan maka kasan dai bazan shiga gidan kuba ko.”
“Babu matsala ki shiga nasan su hajiya na sama babu wanda zai ganki.”
“Ya Allah nifa bazan shiga ba dan haka idan kaga dama ka sakko ko wallahi nayiwa mai gadi sallama yazo yaja ka.”
“Dakyar ya iya sakkowa yaje ya kwankwasa gate d’in mai gadi ya gansa a haka ciikin tashin hankali yajashi ya kaisa ciki saboda bai tab’a ganin sa a haka ba...


Insha Allah wanan itace had’uwar mu ta k’arshe paris tunda ba Alkhairi a gad’uwata dakai Allh karka sake had’ani dashi Tafad’a tare dajan motar tabar wajen direct gidan su ta nufa....


Tana zuwa ta shige d’aki ta kwanta akan katifarta sai bacci saboda ta gaji da yawa...

Washe gari tabar wayar ta akashe saboda kawai tana son kadaicewa ita kadai dan kuwa yau sai take ji kamar SAHEED zaizo ya dauketa subar wanan duniyar sutafi can dolar su aikuwa tana cikin tunanin taji tayi mata sallama”
Cike da farin ciki mara misaltuwa tace”yakai abin kauna nayi mutuk’ar kewar ka.”
“Nima nayi kewrki sosai abar k’auna.”
“Na shirya abin kauna ka d’auke ni ka kaini dolarka na shirya kuma na amince zan aureka zamu zauna acan muyi rayuwar mu cikin farin ciki babu mai takura mana.”
“Amma naji dad’i sosai kuma nagode abar sona ayau zan ciki burina sanan zaki zama sarauniyar aljanu.”
Yana fad’ar haka kawai ta gansu a wajen k’ofar shiga wanan daula ta SAHEED tana jin k’rar wad’anan tsintsayen ga shuke shuke ga wasu k’amshin furanni da suke tashi abin dai sai wanda yagani.”
“Wayyo dad’i kasheni gaskiya abin kauna inason wanan wajen ina jin dad’in kasancewa a wanan waje mussaman ma idan Na bud’e idi na ganka a tare dani.”
Cike da jin dad’i nake alfahari dake yake sarauniyata...

“Kin amince zaki zama sarauniya ta?”
“Na’amince.”
“Kin amince yanzu a d’aura mana aure?”
Na’a...... kafin ta k’arasa sai wata guguwa mai k’arfi ta gani ta d’ebesu gaba d’aya tayi wani yanki dasu su duka biyun...


Baka isaba baka isaba mai akayi akayi ka a cikin sarauta kai wanene a cikin aljanun kai wanene ka sani wanan yarinyar tun tana jaririya aka bani ita bayan ta girma takai shekarun balaga na aureta kai wanene da zakace zaka aureta kai wanene da zaka aurar min mata......




Vote
Share
And comments.
NI’IMATULLAH




By haajara abla



ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(Annuri is the best).



SHAFI NA ASHIRIN DA UKU 23

Tasowa aukayi inda NI’IMATULLAH take ta maimaita “Subahanallahi Subahanallahi mai yake faruwa haka Aima ya akayi kika fad’i.”
“Wayyo Allah na,wayyo Allah k’afata nima bansan na fad’i ba kawai santsi ne ya d’aukeni ina daf da shigowa nan najini a k’asa yanzu gashi duk abin shan naku ya b’ata min jiki amma bari na tashi naje na canza kaya kafin nan sai in saka a had’a muku wani..”
“Sannu kinji luv Allah ya k’ara tsarewa.”
“Ameen ya Allah nagode luv.”
“Amma kada iskar tayi muku yawa kodai palor zamu tafi.” Daman sam NI’IMATULLAH batason ta tafi ta barta daga ita saishi dan haka tayi maza tace”eh rabin raina kawai mu tafi palorn gaba d’aya daman har iskar wajen tafara ta kura min.”
“Ok shikkenan taso luv mu tafi.”
Bahaka yaso ba amma cikin dakiya da jarumta irin ta mazan kwarai ya tashi ya fara binsu taku biyu sukayi sai ta hango kamar SAHEED take gani a baki k’ofa da k’arfi ta bud’e bakin ta tare da cewa SAHEED” Tafad’a tana rugawa da gudu inda yake..
Tana zuwa ta dafasa tace SAHEED lafiya kuwa na ganka duk jikin ka yayu ciwo lafiya maike faruwa na ganka a haka?”
“Babu lokaci ki tawo mu tafi a hanya zan fad’a miki duk abin da ya faru,haka ta fita batare dako ta d’auki motar taba.. NU’AIMA ce take ta kwalla mata kira amma ina batajiba ko kad’an hankalin nata yana kan masoyinta,shi kuwa Salman daskarewa yayi dan yaji tana ta magana ita kad’ai kamar dai taga wani haka ta ruga bakin gate kuma tana ta magana gashi kuma ta bude k’ofa sun fita ana ta mata magana bataji ba.. NU’AIMA ce ta katse shi da tunanin sa tare da cewa”innailahi mai yake faruwa ne da NI’IMATULLAH luv kaga motar tafa amma kuma ta fita ta tafi alamun ta kuma kamar wani tagani wanda ta sani amma ai mu bamu ga kowa ba,ko kaga wani Salaman?”
“Nima abin ya bani mamaki wallahi nima banga kowa ba amma shigo mota mu bita muga ko zamu ganta nasan tunda a k’afa ta fita ai ko layin nan bazai tab’a yiyuwa ta wuce ba a k’afa.
“Hakane ta fad’a tare da yin hanzari wajen shiga mota aikuwa tana shiga batare da b’ata loaci ba ya kunna ta yayi wa mai gado horn ya bud’e masa gate d’in da sauri yayi waje,amma abin mamaki babu ita babu alamunta cike da mamaki suke tafiya sai kawai tace masa luv mune gidan su muga ko tana nan. Aikuwa babu musu daman shi haka yake so nan da nan kuwa sai gasu a gidan nasu, wani yaro suka sa yayi musu sallama da ita amma akace bata nan taje unguwa. Wato da alama bata gida to ina ta tafi wa tagani kuma tabi dan da alama akwai wanda ta gani kuma tabi...
“Wai in tambaye ki anya kuwa NI’IMATULLAH batada aljanu?”
“Wayyo Allah Aljanu kuma luv?”
“Eh mana su,ni daman nasha lura da ita tana wasu acting dai sometimes kamar ba ita kad’ai ba.”
Juyo wa tayi ta k’are masa kallo sanan tace”mai kake nufi kace luv kana nufin kace rabin raina bata da hankali ko kuwa maine,amma naga sau biyu kuka tab’a had’uwa amma har kafahimci hakan amma nida nake close da ita ban fahimta ba.”
“Hmmm ke yarinya ce amma tabbas akwai alamar tambaya.”
“Nima dai wallahi abin ya bani tsoro,ubangiji ka tsare min ita a duk inda take.ni babu mayafi a jikina dana shiga na shaidawa mamansu abin da muka gani.”
“Haka ne amma mu koma gida mu tayata da addu’a insha Allah babu abin da zai sameta amma ni in mai tabbatar miki akwai aljani da yake bibiyar NI’IMATULLAH amma insha Allah zai barta ko wanene shi.”
“Insha Allah da yardar Allah tafi k’arfin shi mugu azzalumi.” Sai tafara kuka nan ya ringa lallab’ata sanan ya kaita gida shi kuma ya wuce..



“Mai yake faruwa dakai masoyi mai ya sameka ka jigata haka?”
Kallon ta kawai yake”kuka tafara sosai tana fad’in dan Allah ka fad’a min abin da ke faruwa kafin zuciya ta tabuga plssss tellme what’s happened?”
“NI’IMATULLAH kenan ai kinga abin da yafaru ranar nan daman itace matsalata mun kara sosai dashi munyi da jiki amma ina ni banyi nasara ba sanan shima baiyi nasarar kaini k’asa ba duk dai munyi kan jaki,haka muka sake karawa a karo na biyu abinda muka samu a karo na farko shi ya bamu a karo na biyu yanzu indai har na sake karawa dashi to tabbas d’aya daga cikin mu zai mutu dole ko shi ya mutu ko kuma ni na mutu shiyasa sai a tsya nayi babban shiri dan ganin naci nasara akan abokin gaba.”
“Wayyo Allah nifa wallahi daka hakura karku sake wanan karawar dan idan ka mutu ka sani nima mutuwa zanyi kuma bazan dawo ba na har abada dan Allah kada ka bari k’adddara ta nesan tamu,kada ka bashi damar da zaiga bayan ka dan Allah ni idan so samunane ka rabu dashi wanan fad’an haka ya isa baka ga yanda kayi wa kanka illahba.”
“Ai biki ga illah ba idan kika ganni a siffata ta ainahi dan hakan bazai yiyu ki ganni a siffata ba,saboda zaki mutu ne ki ki haukace,sanan idan na rabu dashi bikiji mai yace ba tun kina yarinya aka bashi ke kuma kuna da y’ay’a dashi.”
“Ni wallahi k’arya yake min babu wani wanda ya basa ni sanan kuma yaran uwar wa nake dasu da shed’ani k’arya yake min la’ananne.” Haka Tafad’a tana ta kuka sosai mai sosa zuciya...

“Kiyi hakuri ki daina wanan kukan insha Allah komai zaizo k’arshe insha Allah kada ki damu kuma ki daina wanan kukan kina zubbadda hawayen ki kinji.” Tam Tafad’a tana d’aga masa kai yanzu bari na kaiki gida ki samu ki kwanta ki huta saboda kin gaji da yawa. D’aga masa kai tayi alamar tam.

Gida ya kaita inda ya ajje ta a k’ofar gida ta shiga ciki jikinta a mutuk’ar sanyaye,bayan ta shiga ta tarar da babah tana aiki aikuwa tasaka wasu kayanta na tsakar gida ta zauna tana ta taya babah aikace aikace tana cikin yin aiki ne wayar ta ta ringa k’ara daman Abbas ya shiga d’akin ya d’akko mata da gudu ya kawo mata yana fad’in”Anty ana kiranki,Anty ana kiranki.”
Kab’a tayi tace to sanan ta kalli Number da ake kiran nata.tsaki tayi sanan ta maida wayar ta ajje ita sam ta manta m bata sake yin blocking d’insaba dan kuwa ta gane number..
Babahce ta kalle ta sanan tace”ana kiranki NI’IMATULLAH mai yasa bazaki d’auka ba shifa wulakanci bashi da dad’i.”
“Yanzu baba idan aka kirani ban dauka ba yana nufin wulakanci.”
“Eh mana tunda har kikaga mai kiran ya takura da kiran to wani abu zai fad’a miki mai mahimmanci.”
“Babah shidai wanan babu wani abu mai muhimmanci dazai fad’a min na sauraresa kawai shi wanan burin sa yaga yasani a tashin hankali ne dan haka bari na rufesa.”
“Subahanallah Allah ya raba mu da tashin hankali to ki kula dashi sosai kisan mai kike saboda mazan nn na yanzu suyi mace asiri b damuwar su bace.”
“Innailahi babah asiri fa kika ce.”
“Eh mana asiri ai yanzu ba kowane yake jin tsoron Allah ba wallahi.”
“Wallahi babah har kin tuna min da mamata a gidan baban mu,duk da cewa ni k’aranar tarinya ce a lokacin amma ban manta komai ba sanan ni kaina ai bata k’ayleniba.”
“To kingani dan haka ki yawaita addu’a ubangiji ya shiga tsakanin nagari da mugu,kuma ina miki nasiha da bake babu fad’awa saurayi bak’ar magana ina fad’a miki.”
“Insha Allah babah da yardar Allah zanyi amfani da abin da kika fad’a.”
Wayar tace ta sake yin k’ara tana d’agota taga rain rai ce take kira d’agawa tayi da sallama,ita bata ma tsaya amsa sallamar ba tace”kina lafiya NI’IMATULLAH.”
“Eh ina lafiya Alhamdulillah.”
Ajiyar zuciya ta sauke sanan tace”har hankalina ya kwanta amma kin tafi kin bar motar kifa sanan kuma momy tace idan kina da lokaci kizo zakuyi wata magana da ita.”
“Shikkenan babu damuwa insha Allah idan na samu lokaci zanzo ki gaida min da ita.”
“Ok zataji babu komai ki kuka da kanki.”
“Insha Allah kema haka.”
Sauke wayar tayi sanan ta kalli babah tace”wai NU’AIMA takirani wai momy tanason zatayi wata magana dani mai muhimmanci wanan wace magana ce?”
“To ai bazaki sani ba sai kinje,amma kikace min yau nan zakije.”
“Eh babah naje fa amma idan zan iya tunawa ko sallama bamuyi ba na dawo.”
“To kamar yaya?”
“Am uhm am kaina ya

Please Login or Register in order to submit comment