You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kud’i duk abin da kuke da buk’ata kuna dashi so mai kike nema kuma apart fron this.
“Aa Ninu nagode wa Allah babu abinda muka nema muka rasa tun tasowar mu amma saidai ki gane ni y’a macece kuma ina da rauni sanan ina da wata damuwa.... kuka take hakan yasa NI’IMATULLAH tace tayi shiru tabar kukan datake suka canza wata firar...
Sai yamma sanan NU’AIMA ta koma gida cike da jin dad’in ziyarar data kaiwa aminiyar tata...
Washe gari da safe bayan ta tashi ta fito breakfast taga ana ta shirya abinci kala kala ana ta aikace aikace tambayar momy tayi maike faruwa ne”momy kodai kud’in auren INAYATULLAH za’a kawo da Samir ne naga duk ana ta wani shirye shirye kamar wanda za’ai biki.”
Dariya momy tayi sosai sana ta janyo ta jikin ta tace da ita”yau muna da bak’i Mamana bayan munyi tafiya shi kuma Aminin Abban ki sun dawo garin nan da zama gaba d’ayan su harda y’ay’ansa da matar sa dan haka sukace yau zasu zo an kwana da yawa ba’aga juna ba zai tawo da yaransa da matar sa kinsa d’ansa d’aya Namiji da Allah yabasa sai mata hud’u inda yake san d’anan Salman kamar rayuwar sa babu abinda ya nema ya rasa so muna shirin tarbarsu ne.”
Cike da murna da jin dad’i NU’AIMA tace”momy yaya SALMAN dai kike nufi shine zaizo.”
“Yess saurayinki na yarunta ba shine zaizo tun kina yarinya rabanki dashi tunda ya tafi karatu dubai bai dawo ba har ya fara aiki acen sai yanzu da yazo hutu gashi kuma su Abbanaa sun dawo garin nan..
Lumshe ido NU’AIMA tayi cike dajin dad’i a cikin zuciyarta take furta Alhamdulillah yau mafarkin dana dad’e inayi zai tabbata yaya SALMAN zaiso wayyo Allah na Allah yafara amsa addu’a ta...
Bacci take yi sosai tana ta jin dad’i a cikin baccin tana jin wani yanayi na daban yana shigarta sai wani mik’ewta take she’s very enjoying it.sai kawai kuma taga wani katon mutum a gefenta yana wani shek’a dariya wani farin abune yazo suka kama kamar kokawa dan wancen zabgegen mutumin hardai taga babusu farkawa tayi firgigit ta fara salati cike da tsoro.....
Ta fara shiga cikin damuwa da irin wanan mafarkan gashi tana addu’a sosai amma abin ya fara yawa anya bazata samu malam tayi masa bayani ba gaskiya dai yanzu tsoro take ji sosai kuwa....
Vote
Share
Comments
NI’IMATULLAH
By haajara abla
ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(Annuri is the best).
SHAFI NA SHA UKU 13
B’angaren Momy NU’AIMA ta nufa cike da damuwa a face d’inta take fad’a mata abin da ya faru da masoyin nata,cikin rashin jin dad’i momy tace”Wayyo Allah innahlillahi wa’inna ilahi raju’un Allah dai yasa baiji rauni sosai ba?”,Allah ya sawwake bari nasa rahma ta shiga kitchen ta had’a abinci zuwa yamma in Allah ya kaimu sai mu taci gaba d’aya. Babu yadda NU’AIMA zatayi tana jin nauyi da kunyar momy sosaia shiysa batace komai ba ta zauna suka cigaba da fira sama sama...
Misalin k’arfe biyar NU’AIMA takira NI’IMATULLAH tace ta shirya ta fito gasu nan sun fito to tace da ita sanan ta tashi ta fara shirye shirye kiranta ta sake yi a waya tace wallahi shiryawa take amma kawai ta turo mata da address Na hospital d’in idan yaso sai ta nufi asibitin direct...
Haka kuwa akayi ta tura mata address babu b’ata lokaci bayan ta shirya a cikin nutsuwa cike da kamala ta fito ta fad’awa baba jumma ga inda zata baba jummai tace Allah ya tsare tasa kai ta fita...
Bata sha wuya ba wajen gane address d’in mislin k’arfe shida na yamma ta k’araso ciro wayar ta tayi ta kira NU’AIMA tace mata bari ta fito gata nan zuwa,bayan ta fito ne direct suka nufi b’angaren d’akin da aka kwantar da Salman d’in suna zuwa zuka tura k’ofa suka shiga mutane sun ciki a d’akin cos ga yan uwan sa gakuma su Momyn NU’AIMA da suka zo. Tsugunnawa tayi daga can k’asa tafara gaishesu suna amsawa tana yi musu ya mai jiki momy ce ta matso da ita kusa da ita sanan ta mik’a mata seat tace ta zauna....
Shikuwa mara lafiya yana kwance yana tashan bacci abin sa fuskarsa a rufe dan Haka NI’IMATULLAH bata gane ko wanene ba kuma shima baisan NI’IMATULLAH tazo ba....
Haka sukayi musu dubiya suka fito waje saboda NI’IMATULLAH zata koma gida kuma suna yanzu zasu tafi”habibty kin gansa yana ta bacci baku samu kun gaisa ba.”
“Babu komai ai bashi da lafiya biki gani ba dole yayi bacci.”
“Hakane Habibty ubangiji ya bawa luv lafiya Habibty ji nake daman ciwan nasa ya dawo jikina wallahi saboda banson ganin sa a cikin wani hali kin sani saboda ina sonshi ina kunar shi.”
“Babu komai insha Allah zaiji sauk’i dan Allah kada ki damu kinji.”
“Shikkenan bazan damu ba.”
Haka suka dawo gida daga asibitin shi kuma kamar yadda likita ya fad’awashe gari aka sallameahi suka koma gida..
Kwance yake saman gadon sa yayi rigin gine babu wacce yake tunawa sai waccen yarinyar da kuma abin da ya faru,ya dauka cewa idan wata y’a mace ta zagesa sai tayi danasani amma gashi ita tana y’a mace ta zagesa kuma harda mari amma kuma wani abin mamaki ma shi idan ya tuna murmushi yakeyi sosai idan ya tuna tabbas yarinyar bata tab’a burgesa ba sai yau yana so yaji sunan ta agaro na farko yanaso ya zauna suyu magana tare da ita,to amma ba’a nan gizo Ke tsak’ar ba a ina zai ganta shi k’addara ce ta harhad’ashi da ita at kusan 3times yana so k’addara ta k’ara had’ashi da ita a karo nagaba yasan bazata kubce masa ba..
Amma yana tunanin wannen gayen fa a ina ta samosa gaskiya duk yadda akayi ba d’an nan k’asar neba dan gashi nan kanar wani balarabe ko ba indiye amma yasan cewa yan bariki ne babu wanda bazai gani a tare da ita ba amma kuma gaskiya aka ro na farko yana tsoron wanan gayen yana tunanin abin da yayi masa a club tamkar abin siddabaru haka dai yayi ta tunanin sa ya k’ulla wacne ya kwance wance wayar NU’AIMA ce ta katse masa tunani wani d’an tsaki yayu sanan ya d’aga”hello luv ya kake ya jikin naka dan Allah nakasa samun nutsuwa wallahi inason naji ya jikin naka momy tace min kun koma gida ko?”
“Eh luv mun koma gida kuma jiki yayi sauki sosai ki kwantar da hankali kinji luv.”
“Taya hankali na zai kwanta baka da lafiya amma tunda kace na kwantar da hankalin zan kwantar dashi amma ka kula sosa Allah ya k’ara sauk’i.”
“Ameen ya rahman ubangiji yayi miki albarka kinji ya baki miji nagari.”
Batasan sanda tayi dariya ba sanan tace”ai yama bani insha Allah kai d’in na musassamn ne luv.”
Dummmm yayu shidai baice yanason NU’AIMA ba kuma bazai tuna lokacin da yace yana sonta da aure ba kawai dai Yana fad’a nata yana sonta kamar yadda suke wasa da dariya suna chat suna waya sosai kodai yanayin caring da yake bata yayi kama da masoya ita kuma ta d’auka a haka...
“Luv yadai naji kayi shiru lafiya?”
“Am eh am wallahi kaina ne yad’an sara ta gefe.”
“Ayya sorry kayi hakuri na cika ka da surutu bari na barka ka kwanta ka huta.”
Kashe wayar tayi bata kawo komai a zuciyar taba taci gaba da harokin ta....
Bayan kwana biyu ne taji tana so ta ziyarci NI’IMATULLAH dan tunda suka rabu a asibiti basu sake had’uwa ba...
Tana kwance tana chat inda ayaune ta Kammala book d’inta mai suna marubuciya kuma ayaune za’a karramata a d’akin taro dake kano state library. Tana kwance tana ta karb’ar gaisuwa da yabawa akan littafin nata da yazamo bakan damiyar wanan shekara tana jin dad’in sosai nagani addu’o’in da mutane ta ko ina suke mata hakan yana bata nishadi,kamar daga sama taji NU’AIMA ta fad’o kanta tana sallama...
“Kaji mafarki kece yanzu NINU kinsan har kin tsorata ni.”
“Ohhh NI’IMA daman kina da tsoro kinjiki to bani ceba aljana tace.”
“Hhhhh wai aljana.”
“Yawwa NU’AIMA daman yanzu nake son kiranki anjima zamuje wajen taro na marubuta inda za’a karramani saboda littafina na marubuciya shine yazo na d’aya a wanan year.”
“Wowwwww masha Allah hana no wonder ni daman nasani ai littafin yayi dad’i sosai wallah saboda kin zuba basira ai Na fad’a miki kike gani kamar karyane wasa nake.”
“Ba haka bane NU’AIMA na saba tubutu ne inayi ina ji tabbas wanan littafin yayi ma’ana sosai kuma makaranta zasu k’aru sosai a cikin sa zasuyi nishadi,amma a wanan karon kawai dai rubutun nake batare da nasan abin da ke damuna ba.”
“Uhm hakane NI’IMATULLAH Allah ya yaye miki amma dai nayi murna sosai saboda kinyi nasara.”
Haka suka cigaba da firar su sai wajen k’arfe biyu na rana suka shirya suka nufi wajen taro an karrama NI’IMATULLAH sosai an bata award mai kyu da tsada ana ta hotuna da vedio tana jin dad’in wanan d’aukakard Allah yayi mata ko ba komai taji dad’i a karo na ba adadi tayi abinda al’umma suka k’aru kuma har suke alfahari da ita....
Bayan taro ya watse ne suka shiga mota ita da NU’AIMA sukayi hanyar komawa gida..
Suna cikin tafiya daidai wani super market NU’AIMA tace”NI’IMATULLAH d’an mu shiga nan kwana biyu ina san zuwa kuma k’uya ta hanani zuwa.”
“Hhhh tam shikkenan bari mu shiga a siya mana kayan dad’i.”
Bayan sunyi parking ne suka sauka a motar suka shiga ciki suka fara siyayya sosai suka siyo abubuwan kwalam da mak’ulashe sanan suka tawo adaidai k’ofar fita ne NU’AIMA taci karo da k’awarta bestie cike da mamaki tace”bestie.”
“Itama bestie tace mata sanan tace yakike.”
“Lafiya kalau bestie daman kina garin nan NU’AIMA ta tambaye ta.”
“Ina nan NU’AIMA ina zanje yasu mama.”
“Lafiya kalau wallahi.
To agaishe su...
Saidai suka shiga motar NI’IMATULLAH ta kunnata sanan tace”yaudai naga bestien taki.”
“Uhm aikuwa dai.”
Dariya NI’IMATULLAH tayi sanan tace”to mene kuma duk na canza fuska har haka ko bikiyi farin cikin ganin taba ne.”
“Mai yasa zanyi farin ciki dan na ganta.”
“Ohhh ni NI’IMATULLAH itafa d’in bestien kice kuma nasan kinsota fiye da yadda kika so kowa cikin kewayeki d yan uwanki ma.”
“Ada ba amma a yanzu tabbas ni bazan ce insomta b kuma bazance n tsanetaba.”
“Amma miyasa?”
Labarin NU’AIMA at boarding school.....
Ayi min afuwa adakace a shiri nagaba🤗.
21/12/2022
NI’IMATULLAH
BY HAAJARA ABLA
ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(Annuri is the best).
SHAFI NA SHA BIYU 12
“Kamar yaya INAYA ban gane ba,yanzu kenan zargina kike zan iya zuwa club ko hotel,to asa misali naje ma maikike tunanin naje yi ko kuma kina tunanin naje iskanci ne,babu komai bance karki wanan tunanin ba kiyi iya tunanin duk abin da zaki tunani idan ma kince min nima nafara yawan club ko hotel kinyi daidai tunda kina min fata a matsayin ki na yar uwata nagode sosai.”ta fad’a tana kuka sosai... jikin INAYATULLAH ne yayi sanyi ta tashi ta dafa yar’uwar tata ta rungumeta tare da fad’in”kiyi hakuri yar uwata kawai na damu dake ne sosai banason abin da zai baki matsala a rayuwa ne kamar baya dan Allah ki yafe ni wallahi dan na damu dake ne shiysa banson ki fad’a a halaka.”
“Insha Allah bazan fad’a ba yar uwata nasan tunda Salman yana sona insha kuma very soon zamuyi aure komai zai wuce kamar tarihi.”
“Hakane ubangiji ya nuna mana sistona.”
Bayan kwana ki biyu ne ta shirya dan kuwa duk yanzu basu da exam din sai next week gaba d’aya gidan ya dameta tamkar tana kan k’aya gaskiya bari taje wanan gidan da alhaji ya bata kota huta.. tashi tayi ta shirya su Abbas da Abba da sauran yaran gidan harda baba jummai ta daukesu suka ga gidan sun tayata murna sosai kuma sun mata fatan samun miji nagari itama ta zauna a gidan aurenta kamar yadda ko wace ya’ mace ke zama a gidan aure gashi NI’IMATULLAH bata da rowa kokad’an daman komai ta samu na mutane neba nata bane ita kadai hakan yasa yara da manya kowa yake sonta cos unguwr su geto area ce duk da cewa ta tara munafukai yan gulma da yawa amma hakan bai hanasu fad’ar Alkhairin NI’IMATULLAH agaresuba. bayan tadawo dasu gida ne ta shirya kawai taji bata son zaman gidan dan haka ta salallab’a ta fita bayan kowa yayi bacci saboda yanzu harga Allah tana jin kunyar fitar datake agabansu kuma babu yanda sukayi iya da ita dan tun kafin tayi karfi a fitar malam yake sawa ana mata duka da yaga hakan bazai ba ya cigaba da yimata addu’a...
Fita tayi ko mota bata d’auka ba saboda yau kawai taji tana son bataso agane ta fitan ya kamata ta ringa boyewa koba komai bakin zai ragu...
Titin unguwar su ta nufa ta dauka zata samu mota amma babu mota ko daya ta haya saidai tsalli tsallin motocin gida tunda alokacin d’aya saura na dare...
Wata motace tayi parking gabanta motar tayi masifar kyu daga gani mai ita ba k’aramin mutum bane sauke glass d’in motar yayi aikuwa ido ta zazzaro sanan ta dafe k’irji tana fad’in”kaine?”
“Yesss nine mana ai kin manta dani.”
Da sauri ta shiga motar ta zauna a gaban tana kallon sa kamar zata cinye sa tace”taya zan manta dakai SAHEED bazan tab’a mantawa dakai ba a rayuwata ni banason ranar da zata zo ace ma na manta dakai sai dai ranar mutuwa ta.”
“Naji dad’in maganar ki sarauniyata,so ykk?”
“Kana tunanin zan zauna cikin lafiya ne bayan bana tare dakai bana ganin ka kayi min nisa mai yasa kayi min nisa na tsawon kwanaki mai nayi maka dan Allah ka jefa zuciya ta cikin halin damuwa da kewa na rashin ganin ka,kana tunanin zan iya rayuwa mai dad’i ta farin ciki bayan kayi min nisa?”
“Bahaka bane NI’IMATULLAH kiyi hak’uri ki saurare ni ba komai ne yasa na miki nisa ba sai wasu dalilai.”
“Wasu dalilai ne wad’anan SAHEED?”
“Nayi tafiya ne can k’asa mai tsarki wajen kakana sanan munyi tafiya nidashi sosai a sararim samaniya inda muka shafe wata d’aya nidashi sanan fa daga nan na dawo fadata inda aka nad’ani sarki kuma aka bani kuyanku da sauran fadawa da wad’an da zasu min hidima,yanzu idan kikaje fada ta zakiga ta cika da hallitun mu saidai kawai abu d’aya yanzu nake jira shine sarauniyata wacce zata kasance a wanan fada na har abada.”
“Sauke ajiyar zuciya tayi sanan tace na tayaka mutna sosai ubangijin mu ya tayaka tuk’o.”
Suna cikin firar yaja mota suka tafi batare da ta fad’a masa ba taga ya nufi club d’in datake son zuwa yasan tana zuwa cos anan ya fara ganinta.
Saukkowa sukayi suka fito duk inda suka wuce su ake kalla saboda tsabar kyu mai rikitarwa kalar Na SAHEED abin sai ya bada salo mai d’aukar hankali da kuma shauki haka suka nufi waje suka zauna akabasu drinks suka sha suka zauna suna kallon juna cike da shauki wanda ita bata tab’a jin saba duk lokacin datake tare dashi sai taji wani kalar shauki na mussaman yana shigarta haka suka tashi suka fara rawa cike da so da kauna da kuma burgewa...
Tawowa yayi da drinks na wine a hannunsa yana sha bai ankaraba ya zuba mata a jiki jiiii tayi sanyi abu ya shige ta sosai ta d’ago kai take sukayi ido biyu dashi aikuwa batasan sanda ta sake SAHEED ba ta fuskance shi ta falle masa mari ta sake falle masa mari sanan tace”kai wane kalar dabar d’an shaye shaye ne da zaka watsa min giya kana kallo.”
Kallon ta yayi sanan ya kalli SAHEED aikuwa ya kusa daskarewa yana tunanin ita kuwa a duniyar iskanci nata a ina ta samo wanan ajin k’arshen...
Kama rigar sa tayi saboda shi gabad’aya tunanin sa yabar wajen yana kansu ya rasa ma mai zaice”magana nake maka wane kalar dabba ne kai mashayi da zaka zubamin abin shan ku.”
A wanan karon a maimakon ya biye mata kawai sai abin ya bashi dariya sosai dan haka kawai ya kama dariya baice da ita komai ba.”
“Ohhhh dariya kake.”
“Nayi mamaki tunda nake bantab’a ganin budurwa mai k’arfin hali kalar kiba ko da yake no wonder ai yar bariki ce that’s why.”
“Bai k’arasaba yaji anyi sama dashi an dawi dashi k’asa bai k’ara sanin a inda yake ba sai farkawa yayi ya gansa a gadon asibiti.....
“Naji dad’i masoyi kayi min maganin wanan mara mutuncin nifa bansan saba bansan sunan saba amma ya takura min na had’u dashi duk a rashin sani amma ya shige min hanci da k’udun dune wallahi amma yanzu naji dad’in abin da ya faru ko a haka kabarshi ya gane niba sa’ar sa bace ya gane ruwa ba sa’an kwando bane.”
Dariya SAHEED yayi yace”bazan lamunci naga wni bil adam yana takura miki yana shig tayuwar ki kamar haka ba banyi maganin saba.”
“Haka nakeso masoyi yay ka biya min.”
Dariya sukayu suka cigab da fira yayin da sun ruga sun bar wajen tunda abin ya faru da aka rud’e yan wajen kowa yana ihuuu hakan yasa SAHEED ya dauki NI’IMATULLAH bai ajjeta ko inaba sai saman gadon ta ya tafi sukayi sallama dan asuba tayi...
Tashi tayi tayi sallah ta zauna tana tasbihi har saida rana ta fito sanan ta koma ta kwanta.....
Bud’e idon sa yayi da kyar inda yake ganin dusu dusu,k’arasa bud’e idon yayi tanga raro yaga su daddy da mommy da kannen sa a kusa dashi ganin ya farka ne momy tace”Abba kaga ya farka bari na kira likita.”
Da sauri taje ta kira likitan,inda su kuma suka runga tambayar yayan nasu ya jiki Abba yace”ya jikin kanka son.”
“Da sauki Abba amma mai ya faru nazo nan.”
Kafin ya bashi amsa likitan ya shigo da sallama sanan yayi kansa yana fad’in”paris ya jikin naka?”
“Da sauk’i likita.”
“Masha Allah duddubasa yayi sanan yace insha Allah zuwa gobe da safe za’a sallame ku saboda ka bugu da yawa dan ma Allah ya tsare da abin yafi haka Allah ya k’ara sauk’i.”
Cike da mamaki ya fara tunanin abubuwan da suka faru kawai sai ya tsinci kansa da yin Murmushi da ya tuna maganar ta ta karshe”sabaoda kai dabba ne dan shaye shaye zaka watsa min abin shan ku.”
Murmushi yayi Abba ne yayi masa sannu da jiki yana ta amsa musu da sauk’i ana haka wayar sa ta fara ringin yana dubawa yaga NU’AIMA luv ce hakan yasa ya d’aga suka fara gaisawa yace mata ai Yana asibiti jiya ya samu accident cike da tashin hankali tace masa gasu nan zuwa,zuwa anjima sallama sukayi ya ajje wayar ya koma yayi lamo yana tunanin waccen yarinyar.....
NI’IMATULLAH ta fara kira tana tsakar gida tana taya baba jummai aiki tazo ta d’aga tare da fad’in”Assalamu alaikum.”
“Waslm Ninu.”
“Ya kike NU’AIMA naji muryarki kamar kinyi kuka.”
“Eh wallahi NINU luv ne babu lafiya yayi accident Yana asibiti shine anjima zamu dubiya inaso ki shirya muje tare.”
“Shikkenan NINU ubangiji ya bashi lafiya mai daurewa ya tsare gaba idan zaku tafi kimin magana sai mu tafi taren.”
“Ok bye tnc dear.”
Vote
Share and comments.
Dan Allah ku tayani sharing cos yanzu banda groups dayawa ngd.....
NI’IMATULLAH
By haajara abla
ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(Annuri is the best).
KO TA INA INA KARB’AR SAK’ONNIN KU MASOYA UBANGIJI YABAR ZUMUNCI.🥰❤️🤩😘
SHAFI NA GOMA SHA HUD’U 14
Cike dajin dad’i da farin ciki na wayi kaina a makarantar kwana da ake kira da boarding school nayi farin ciki mara misaltuwa inda kuma a ta d’ayan b’angaren na shiga damuwa da kewa saboda nayi nisa da iyaye na saidai y’ar uwata data ke kusa dani hakan yakan d’auke min kewar su momy da daddy da na tsinci kaina a ciki saboda rashinsu kusa dani..
Tun da muka kammala aji uku Na junior secondary na takurawa dddy akan akaimu makarantar kwana duk da cewa INAYATULLAH bata so haka na dage akan nidai ina so saboda kawai inaso naje makarantar kwanan saboda hakan yana burgeni haka yasa nayi matuk’ar farin ciki da daddy ya yarda har ya kawo mu makarantar aji biyu aka kaimu wato SS2 inda nanda shekara biyu zamuyi candy...
Haka rayuwa tafara nida yar uwata muke zuwa duk inda zamuje,haka idan zamuje aji karatu duk tare muke tafiya duk da cewa INAYATULLAH ta girmeni baisa an kaita ajin gaba ba an barni a baya dady yace tare muka taso muke komai dan haka tare zamu gama. D’akin mu d’aya ga gadona ga nata...
Zaune nake wajen wata bishiya ina ta kallo y’an makarantar kowa yana abin da yake gaban sa,nayi shiru na shiga tunanin gida da kewar su...
“Assalamu alaikum.”naji an min sallama cikin hankali datarbiyya juyo wa nayi na fuskance ta fara da ita kyakkyawa sosai zama tayi kusa dani bayan na amsa sallmarta sanan tace”sunana RUMA SHU’AIB kefa?”
“Masha Allah ni sunana NU’AIMA MAHFUZ.”
“Masha Allah nice name amma kema sabuwa ce a school d’in nan RUMA ta fad’a tana kallon NU’AIMA.
NU’AIMA ce tace”eh sabuwa ce ranar monday aka kawo mu nida yar uwata.”
“Kai haba no wonder daga nesa sai na hango kamar kece kamar kuma bake ba kinsan nima a ranar aka kawoni kuma ajin da aka kaiku shi aka kaini amma abin da yasa duk ba muga juna ba saboda ba muga juna ba kuma muna ta kukan rabuwa da gida...”
“Ayya wanan haka yake Wallahi.”
“Am to ina yar uwar taki naganki ke kedai.”
“Wallahi tana d’aki bata fito bane tace min kanta yana ciwo kinsan tunda mukazo take a damuwa saboda batason makarantar kwana nice nake so shiyasa tunda mukazo take acikin damuwa babu walwala.”
“Ayya sorry a wane gari kuke.”
“Muna kano kefa.”
“Ai kuwa nima a kano nake,yanzu dai tashi muje na gaisa da ita yar uwar taki.”
Tashi tayi suka nufi inda hostel d’in nasu yake sai taga ai kusa ma da d’akin sune mak’otan sune,shiga sukayi da sallama inaya tana kwance ta fito da wayar ta tana ta dannawa duk da cewa ba’a bari a rik’e waya amma mufa saida muka rik’e waya a boye kuma duk da cewa ana seessing hakan baisa munji tsoro ba mun daina amfani da ita..
Amsa sallamar su tayi sanan ta tashi zaune suka fara gaisawa RUMA yarinya ce mai shiga rai gata da hankali da sanin yakamata hakan yasa sukayi ta fira tana da saurin sabo kamar NU’AIMA hakan yasa suka fi shakuwa da NU’AIMA sosai da sosai duk inda zasuje tare suke zuwa a school d’in bacci ne kawai yake rabasu cikin ikon Allah ubangiji ya had’a zumuncin su na kasance ina saurin sabo da nuna soyayya ga wanda ya soni hakan yasa nake kaunar RUMA sosai saboda tana sona.a kwana a tashi babu wahala a wajen Allah a yaune muka fara zuwa hutu gida ai kuwa INAYATULLAH tayi farin ciki sosai taji kamar karta koma school saboda ita badan RUMA ma da NU’AIMA ba wallahi da tuni bazata kai wanan lokacin ba dan ko za’ayi mai sai an dawo da ita gida saboda ita daman ko a gida ba mai san hayaniya bace balle kuma an dauketa sukutum an sata a hayaniyar...
Har gida RUMA tazo suka gaisa da momy inda momy tayi mata sha tara ta arziki kuma NU’AIMA ma har gida ta raka bestien tata ta gaisar da mom d’insu shakuwa mai k’arfi da k’ullu a tsakanin su hakan yasa basa b’oyewa juna matsalar su....
Bayan sun koma school aka cigaba da darasi ranar nan RUMA batazo aji ba har dare dai NU’AIMA bata ga ruma ba washe gari ma Haka INAYATULLAH ce tace” NU’AIMA yakamata kije ki duba bestien ki ko lafiya kinga yu kwana biyu bata zuwa aji kuma ko a islamiyya ta yamma bama ganin ta ki dubata ko lafiya.”
“Nima abin ya dameni Inaya amma zani yanzu na duba naga ko tana lafiya.”
Tashi tayi ta zura hijab d’inta sanan ta nufi d’akin su RUMA...
Tana shiga da sallamar ta babu wanda ya amsa dan kuwa yan matan suna can suna fira su biyu bama su san ta shigo ba hango Ruma tayi a kwance ta lullub’a da bargo. K’rasawa tayi kusa da ita ta zauna a gefen gadon ta kamo hannunta tana fad’in lafiya kuwa RUMA maike faruwa ne maike damunki baki da lafiya daman?”
“Eh wallahi NU’AIMA banda lafiya tun jiya nake fama da ciwon mara kamar zan mutu.”
“Subahanallahi period ne kinsha magani?”
“Eh nasha magani amma magani babu abin da yake min eh shine kinsan duk wata nake fama dashi.”
“Wayyo sannu kinji Allah ya k’ara sauk’i nima haka nake fama dashi.”
“Wayyo Sannu NU’AIMA.”
“Ke za’ai wa sannu yanzu ya jikin naki?”
“Da sauk’i Alhamdulillah nayi bacci ne ma d’azu ai da na shigo.”
“Ah haba keda baki da lafiya.”
Haka tayi mata sannu sanan ta koma d’akinsu ta fad’awa INAYATULLAH itama taje ta dubata,taji dad’i sosai RUMA kuma yanzu jikin nata ma ya ware daman ta saba...
Wata rana muna chat da