gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading NI’IMATULLAH Sirrin Wata Rayuwa by HAAJARA ABLA Chapter 2 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun ba yauba momy daman nasan INAYATULLAH da Yaya NA’EM ba sona suke yiba kalli inda suka rufeni da fad’a yau ai su sunfini ma surutu tabd’i jam,Allah ya kiyaye na biki tab ana ganin ka shiru shiru amma nasan dukana zaka ringayi acan babu abin da zai kaini yasin ina nigeria nida k’awata muddin ni zan fita waje ma karatu saidai nida My NINU.”
Momy ce tayi dariya sosai sanan tace”ki barni dasu NU’AIMATAH kinji zanyi maganin ki,am sanan ni kuwa yaushe zaki kawo min wanan Ninun taki mu gaisa ne.”
Tsalle tayi sanna tace”momy aikuwa zan fad’a mata ta shirya kuzo ku gaisa dan bata tab’a zuwa ba,daman kullum sai nayi nayi da ita tazo sai tace min ita bata son zuwa gidan masu kud’i.” Ta karashe zancen tana dariya.
Momy ce tace”Allah sarki har naji ta burgeni shikkenan Allah ya kawo ta lafiya tashi kije kici abincin kiga su wad’ancan har sunyi gaba sunfara ci.”
“Allah ni momy badan badan ba sai nace ni sai daddy ya dawo zamuci tare kwana biyu fa duk aiki yasa bama cin abinci tare”kiyi hakuri NU’AIMA kinji zakiji yinwa sosai kafin ya dawo dan haka taso muje muci... kamo hannunta tayi suka nufi wajen dinning din....


Momy tana kaunar NU’AIMA sosai saboda tana da Hankali ga k’ok’ari ta b’angaren arabia da boko ta haddace hadisai da dama sanan ta karanta wasu da dama tayi saukar alk’urani har sau uku tayi hardar izu talatin har tafi INAYATULLAH k’ok’ari da jajurcewa sosai,NU’AIMA tana da shiga rai dan kowa ya zauna inda take sai ya sota tana da sauk’i kai sosai ba kamar wasu y’any’an masu kud’in ba haka take rayuwar ta so simple,saidai yan gidan suna mata tsiya da tafiya surutu dan kuwa su basu da yawan magana kamar nata.....

Wanan kenan


Yau kwana uku kenan NI’IMATULLAH tana gida babu inda take zuwa,ta samu sauk’i zaman gidan cos tayi maganin murja dan yanzu murja agaban idonta har sunkuya mata take amma abayan idan ta babu kalar la’antar dabata yi mata,daman ita baba jummai basu fiya samun matsala da ita ba amma fa hannatu ta saka k’afa d’aya da NI’IMATULLAH taci alwashin duk daren dad’ewa sai ta rama abinda NI’IMATULLAH tayiwa mamanta...

Tana zaune kan katifar ta duk abubuwan duniya sun isheta kewa ta dame ta kewar mahaifiyar ta take duk da cewa a halin da suka rabu da mahaifiyar ta hali ne na gushewar hankali hakan baisa taji ta tsaneta ko bata sonta ba saboda lalurar ta kulum tana kuka tana addu’a idan har mamanta tana raye ubangiji ya bayyana mata ita idan kuma ta rasu Allah yayi mata rahma amma tanaji a jikinta cewa mahaifiyar ta tana raye bata mutu ba kawai dai tayi nisa da ita ne...

D’aukko wayar ta tayi ta fara typing cos ita daman babu wani yanayin rubutu da yake mata sai idan tana cikin damuwa indai tana cikin damuwa to a lokacin take rubutu dan haka yau kawai ta ajje wancen littafin data fara rbutawa cos ita sam bataga ya mata ma’ana ba sai ta d’aukko wani labari a take ta sawa littafin suna MARUBUCIYA ta fara rubutu cikin shauki inda a take damuwar datake ciki ta fara gushewa...

Tayi nisa sosai a typing d’inta sai ga kira NINUNTA ya shigo cike da murmushi tayi minimizing ta d’aga kiran cikin farin ciki ta fara magana”Assalamu alaikum Ninuta yakike ya kika tashi yasu momy yasu INAYATULLAH?”
“Wayyo NINU yanzu ni wacce amsa zan fara amsa miki kawai ni kibari naji ya jikin naki ina fatan kin samu sauk’i.”
“Na samu sauk’i sosai har yar tsere zamu iya idan kinaso.”
“Ahhhhh lallai kin samu sauk’i sosai to ubangiji ya k’ara sauk’i kinji.”
“Ameen ya Allah ninu to ya kuke.”
“Duk muna lafiya Alhamdulillah.”
“Masha Allah Amma bani labari maike faruwa naji kina cikin farin ciki kodai kinyi gamo da tauraron maza ne dan kuwa sarki zaifi da cewa da sarauniya kalar ki.”
Dummmm gaban NI’IMA ya fad’i kawa sai taga kamar giftawar SAHEED yana mata murmushi cikin shigar sarauta taban mamaki kyan da bata b’a gani ba a duniya saidai a TV take ganin kalar wanan kyawawan yan india ko larabawa.
“Ninu yadai ko bakya ji ne Ninu hello,hello.
Firgigit ta dawo hayyacinta batasan time d’in data furta nima ina sonsa inason shiga fadar nan.”
“NU’AIMA ce tace ninu ban gane bafa wai wa kike so kuma wace fada.”
“Uhm uhm kinga babu komai Ninu wani d’an k’aramin abu ne amma ya wuce.”
“Aa ninu mai kike boye min akwai abin da ke faruwa mai yasa zaki boye min wani abu.”
“Babu komai ninu ba boye miki nake ba kuma bansan ta inda zan fara fad’a miki bane amma insha Allah na fad’a miki zaki sani nan bada jimawa ba.”
“Shikkenan ninu Allah ya nuna mana kinji,amma yayfa muna da test yakamata kiyi kokari ki shigo anjima.”
Ok babu damuwa insha Allah zan shigo.
“Ok nagode ki gaida su momy.”
“Insha Allah ki gaida mutan gidan.”
“Aha.”
Tana ajje wayar kawai ta fad’a wani tunani tabbas SAHEED tagani ya gifta yana mata murmushi cikin shiga irin ta sarauta da alfarma,a yanzu zuciyarta tana k’ara son ganin sa cos gaba d’aya ita tunda ta gansa taji yayi mata taji ta yarda da abin da ya fad’a mata saidai bata san inda zat gansa b dan dat sanidatuni ba wanan mganar ake ba a yanda zuciyar ta take raya mata....

Tashi tayi tayi wanka ta shirya daman ta shirya su Abbas ta fad’a musu tana da test haka sukace dan Allah ta dawo da wuri ta tawo musu da tsaraba..

Shiryawa tayi cikin atamfa doguwar riga coppee colour tayi mata kyu sosai tasa mayafinta a kafad’a ta nufi garejin datake ajje mota,tana fita ta tadda malam a waje ta fad’a masa zata makaranta yayi mata addu’a Allah ya tsare kuma ta kula da kanta...

Koda tazo school a lokacin su NU’AIMA basu shigo ba malamin da zaiyi test d’inma bai k’arasoba hakan yasa ta nufi library dan ta d’an duba darasin daza’ayi test din.


Ta zauna tana cikin dube duben tane tana karatu kusa da ita wani malamine da wata d’akuba zaune suna magana bata san dai kana mai suke tattaunawa ba amma kunnen ta ya tsinkayo mata maganar budurwar kamar haka”so ni malam banga wani abu ba wai dan karuwa tayi karuwanci an bata kudi sanan banga wani abuba dan b’arawo yayi sata,saboda neman kud’i yake zamanin yanzu idan baka da kud’i ko ciwo kake saidai ka mutu saboda baka dashi so babu wani abun aibu dan na bada jikina an bani kudi it’s just matter of time.”
Juyawa NI’IMATULLAH tayi dan ganin mai maganar wata kyakkyawar budurwa ce tana magana ciki da confidence babu alamar tsoro ko danasanin akan abin da ta fad’a alamun ta ya nuna wanan maganar tana yintane tundaga cikin k’asan zuciyar ta....
Wani dogon numfashi taja sanan ta tashi tabar wajen cike da tunani kala kala a zuciyar ta...

Tana fita taga ankawo su NU’AIMA da sauri NU’AIMA tazo tayi hugging nata tare da bata kiss a kumata tace nayi kewarki Ninu how was yiur body.”
“Alhamdulillah ta fad’a.” Ji tayi INAYATULLAH tace”ya jikin Ki NI’IMATULLAH,Naji NU’AIMA tace baki da lafiya ko.”
“Eh band lafiya. Ta fad’a tana kawar dakai gefe.
“Ok wish u quick recover.”
Tanqeu tace sanan tayi hanyar shiga class murmushi dai NU’AIMA tayi sanan tace insha Allah watarana zaku fahimci junan ku kuma zaku so junan ku. Tafad’a a zuciyar ta sanan ta kamo hannun yar uwar tata suka rufama INAYATULLAH baya wajen shiga ajin...

Anyi test lafiya angama lafi duk da cewa NI’IMATULLAH tasan duk amsoshin amma hakan baisai ta rubuta duka ba cos tunanin waccen maganar budurwa ya tsaya mata sosai da sosai tasan a kullum abin da take bata kyutawa rayuwarta amma kuma ita wanan tana alfahari da hakan ohhh Allah daga ganin baiwar Allah nan ta shiga cikin matsanancin hali like me Allah kasa mufi k’arfin zuciyarmu....

Tana zaune a farfajiyar makarantar dan fata tafi ba saboda NU’AIMA basu tafi ba suna jiran driver wani text ne ya shigo wayar NI’IMATULLAH tana dubawa taga dubu d’ari biyu ya shigo account nata,batasan wanda yasa mata ba kawai sai taga an mata message kamar haka...

“Sunana Alhaji d’an gaske in bazaki damuba Ni’ima ga kud’i nan na turo miki kisa mai a mota ina gayyatar ki murnar k’arin shekara ta ga wajen nan plssss kada kice min baza ki zoba domin kuwa kece babbar bakuwa ta a wajen kuma ke zaki yanka mana cake d’in.”

Cike da mamaki ta karanta sak’on nan kawai sai taji a karo na farko ranta ya b’aci, har arhata takai haaka mtwssss sai tayi banza da lamarin ganin yanayin ta ya canza yasa NU’AIMA ce mata”are u okay.”
“Yeah I’m ok.”
Uhmm NU’AIMA tace sanan tayi shiru, can kuma sai tace”ninu inaso muyi wata magana mai muhimmanci kinji in bazaki damu ba.”
Amma plsss ko zakizo gida.”
Zatayi magana kenan NU’AIMA ta k’ara katseta da”kada kice min bazaki zoba dan na fad’awa momy zakizo ki gaisheta.”
“To shikkenan ninu babu damuwa zan fad’a miki idan na shirya kinji.”
“Kai ninu zuwan gidan naku ne har sai kin shirya gidan kune fa.”
“Hmm ninu rigima shikkenan insha Allah zanzo ranar sunday.”
“Yawwa tanqeu very much that’s my bestie.”
Murmurshi tayi soaai haka suka rabu suna tab’a hira sama sama....


Amma ita yarinyar nan har girman kanta yakai haka kamara ni in nemi alfarma a wajenta amma ko reply bata iya yimin ba what is she.” Ya fad’a yana dukan teble dake kusa dashi yana kurb’ar wine...


12/12/2022
NI’IMATULLAH



BY HAAJARA ABLA


ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(Annuri is the best.)



SHAFI NA SHIDA 6

D’aukar waya yayi ya kira wasu bodyguards d’insa yace yana buk’atar suje gidan su NI’IMATULLAH su tawo masa da ita ko tana so ko bata so..
Cike da bin umarnin uban gidan nasu suka nufi unguwar su NI’IMATULLAH inda Alhajin nasu ya basu address d’inta,mota biyu bak’ak’en jib suka d’auka suka shiga sukayi unguwar su NI’IMATULLAH dasu daidai kofar gidan nasu sukayi parking kowa kuwa su yake kallo almajirin malam gaba d’aya hankalin su ya koma kansu fitowa sukayi da bak’ak’en kaya da bak’in glass a jikin su fuskar nan tasu babu alamar imani a tare da ita jikin kowa ya fara b’ari a wajen nan an d’auka cewa yan kidnapping ne. Daya daga cikin sune yayiwa d’aya daga cikin almajirin malam d’in alamar yazo,kamar yayi fitsari yakasa ko motsawa dan gaba d’aya kowa a firgice yake saida suka daka masa tsawa sanan ya matso yana salati da sallalami. Kai dakata mu babu abin da zamuyi muku dan bakune agaban muba muna so ka nuna mana ina ne gidan su NI’IMATULLAH.”
Kasa magana Almajirin malam yayi saboda tsoro saida sukaga bashi da alamar tanka musu d’ayan ya sharara masa mari ai tuni ya fara bayani. “Nan ne gidan nasu.” Ya fad’a yana nina gidan Malam “oyaa jeka ka kira mana ita idan kuma bazatazo ba zamu shigo ne mu dauketa mu tafi da ita. Cikin sa’a kuwa tana nan babu inda taje dan kuwa safiya ce ma time din.
Cike da rud’ewa almajirin malam ya shigo yana sakin fisari a wando baba jummai ce tace”lafiya kuwa bala maike faruwa ne naga kana fitsari kana wani rawar d’ari duk a firgice.” Cikin wata gigitar yace”baba jummai NI’IMATULLAH tana nan wasu ne suka zo nemanta da bindigu kamar yan kidnapping.”
“Yan mai kace baka innahlillahi wa inna’ilahi raju’un su kuwa mai NI’IMA tayi musu.”
Sam batasan maike faruwa ba saboda bacci take yi amma ta jiyo muryar bala yana kwad’a mata kira”NI’IMATULLAH ki fito ki fito idan biki fito ba sunce zasu shigo da kansu su kamo ki.”
“Ahayyeeee heheheee yau Allah ya kawo wad’an da zasu ramamin cin zarafi da cin mutuncin da wanan yar abin da malam ya hanani fad’ar tayi min kai Alhamdulillah amma Naji dad’i kina ina bak’ar ashana ki fito tun kafin a dawo miki da wanan farar fuskar taki ja hahhhhehhhhh.”

Tashi tayi firgigit ta fito tsakar gidan inda baba jummai take ta zuba salati ita kuma murja tana zuba mugun alkaba’er adaidai nan malam ya shigo cikin tashin hankali ya farawa NI’IMATULLAH magana kamar haka”NI’IMATULLAH maike faruwa mai ya had’a ki da mutane marasa imani kalar wad’ncen dan daga ganin fuskokinsu babu imani ko kad’an mai ya had’aki dasu.”
“Malam wasu irin mutane kuma.... bata k’arasaba su biyu suka shigo gidan da bindiga a hannun d’ayan d’ayan kuma bulala.”
“Zaki wuce mu tafi ko kuwa sai jikin ki ya fad’a miki.”
“Ku su wanene mai nayi muku mai yasa zaku tafi dani.”
“Idan mukaje zakiji amsar tambayar ki dan abu d’aya zamu iya fad’awa su malam da baba shine suyi hak’uri mu aiko mu akai kuma babu abin da zai faru arziki ne yake bin su malam dan haka su kwantar da hankalin su, su Abbas kuwa kuka suka fara dan ganin mutanen daga gani ba mutanen kirki bane.
Zatayi magana sukece karta sake tayi magana ta daukka gyalenta su tafi ko kuma ta tafi a haka.”
Haka ta d’aukko hijab tasa har k’asa sanan sukayi hanyar fita.
Murja ce tace”Allah ya sauki tsiya lafiya.”
Malam ya juyo ya kalleta yana fad’in”haba murja haba murja abin da kike bakya kyutawa mai yarinyar nan ta tsare miki bata shiga harkarki hasakima ke kike shiga tata murja kiji tsoron Allah.”
“Aa malam dakata min wane kalar murja kiji tsoron Allah ni zakacewa inji tsoron Allah ko kuwa karuwar daka ajje..... bata k’arasaba taji saukar lafiyayyen mari sanan ya k’ara daja mata kunne haka baba jummai ta lallashi su Abbas da cewa Antynau babu abinda zai sameta kuma bazata dad’e ba zata dawo...
Murja dai duk da haka jikinta baiyi tsami ba ta murgud’a baki tace”ai daman tsintacciyar mage bata mage mtwssss ayi dai mugani intusa zata hura huta...
Baba jummai bata kulata ba taci gaba da aikin ta dan harga Allah NI’IMATULLAH tana bata tausayi rayuwarta cike take da k’alubale kala kala da abin tausayi k’addara kala kala Allah yabawa yarinyar nan ikon cinye k’addarar ta ya bayyana mata danginta da mahaifinta... ta fad’a a fili tana share hawaye....


Nan cikin unguwa aka ringa yayata cewa yan kidnapping sunzo sun tafi da NI’IMATULLAH.


Wani katafaren gida suka nufa daga gani daman kasan na wanda yaci ya tada kai ne,haka suka wuce cikin gidan inda mai gadi ya bud’e musu gate suka shiga na farko suka shiga na biyu harda sukazo tsakiyar gida hakan suka fito da ita suka fara tafiya suka zagaya ta wani corridor suka nufi wani b’angaren suka shiga wani makeken palorn da ya k’ayatu da abubuwa kala kala na kayatuwa tsayawa ma fasalta kyu da tsaruwa ma irin na gidan kauyanci ne..

Zama tayi akan kujera mai cin two sitter hankalin ta a kwance haka ko a jikin ta tace da bodyguard din su bata ruwa. Cike da mamaki suke binta da kallo daidai nan kuma Alajin d’an gaske ya shigo tare da fad’in”kun kawo bakuwa ba ruwa babu lemo wanan wace irin shiririta ne bna son kalar haka fa ya fad’a yana daka musu tsawa... tashi wani yayi aka kawo mata ruwa da lemo da kayan marmari kala kala..
Bayan tasha ruwan ta juya ta kallo alhajin tare da fad’in “basai ka fad’a nasan kai wane kaine ka turon da kudi ka gayyace ni murnar karin shekarar ka ko.”
“Um NI’IMATULLAH kin canka,nayi mamakin kaina yada nayi mutuk’ar damuwa dake sanan na damu mu kulla Alak’a ko dayake ke d’in bata wasa bace ked’in ta mussaman ce,ki yarda ki amince min zan yi miki duk abin da kike so zan kashe miki kud’i daga naira miliyan d’aya har zuwa miliyan d’ari zan baki motada gida nidai kawai ki yarda mu k’ulla alak’a saboda ke d’in your so special to me.
“Ok alaji naji buk’atunka kuma na yarda amma kuskurenka d’aya daka akaje aka d’aukko ni like this kamar wacce nayi maka laifi.”
Dariya yayi sanan yace”eh mana laifi kikayi min mana babba ma kuwa dan kinyi ignoring d’ina.”
“Ok I’m sorry alajina.”
“Karki damu ai ya wuce tunda har na ganki kuma naji dad’in ganin ki.”
Murmushi tayi tana kallonsa tabbas zata wanki gara kuma sai tayi maganin sa akan abinda yayi mata dan ba’a tab’a b’ata mata kalar nayau ba....
Basuyi sallama ba saida yayi mata kyutar wata lafiyayyar mota dan jibi ne birthday kuma a ita yakeso tazo haka tayi masa godiya sosai lallai wanan za’aje dashi ta fad’a,taji mutukar dad’i sosai dan kuwa yaudai wanan alajin ya gama kasheta da jin dad’i.....


Haka ta koma gida da yammada wanan motar gaba d’aya kowa mamaki yake yi sosai ganin abin da ya faru d’azu yanzu kuma gashi ta dawo da wata sabuwar mota ta kud’i ba d’an kad’an ba,malam ne ya tamabye ta wanene ya bata wanan motar ta fito fili tace wani d’an siyasane ya bani kyutar ta...

Nasiha yayi mata sosai akan da kula da rayuwarta da abubuwa da dama haka dai tace taji insha Allah zata kiyaye. Su baba jummai sosai suka tayata murna itama murja ko kunya haka ta ringa rawar gindi wajen zuwa wajen ganin sabuwar motar NI’IMATULLAH d’in....

Da yake ta gaji sosai kawai wanka tayi ta kwanta dan ta huta ta fad’awa baka kuma yakai motar can inda tata take....


Shigar fulani mai ban burgewa a jikin su ita tayi shigar mata shiguwa shi kuma SAHEED yayi shigar maza mai mutuk’ar burgewa yayi kyu sosai itama tayi kyu mai mutuk’ar burgewa rik’e take da sanda shima haka yake rik’e da sandar suna tafiya ga shanu suna korawa suna fira sunata dariya...
“Sannu ma b’ingel debbo am(barkan ki da wanan lokacin yar budurwata kuma sarauniya)”
“Use lamid’o am SAHEED(yawwa barkan ka dai mai martaba SAHEED).
“Mid’o yelene dur ngol mai waleni ma(ya yanayin kiwon ya miki dad’i ina fatan.)
“Toni mid’o wondi be mad’a walak’o had’ata am nanugo beld’um(indai har ina tare dakai babu abin da zai hanani jin dad’insa).”
“Kai mi nami beld’um gid’ad’o am.(gaskiya naji dad’i kuma nagode masoyiya.)
“Mimma miyatte gid’ad’o am(nima nagode masoyi).”
“E’n ya e’n dura to e’n hot,mi hokke habaru beld’um gid’ad’o am(kibiyoni mune muyi kiwo mudawo mu huta na baki labarurruka masu dad’i masoyiya.”
“To gid’ad’o am e’n yana koha toi tokkete(shikkenan masoyina mu tafi ka kaini duk inda zakaje zan bika.”
“Miyetti gid’ad’o am(nagode masoyiya.)”
SAHEED ya fad’a sanan suka cigaba da tafiya a cikin jejin cikin nishadi da shauk’i irin Na soyayya....


13/12/2022
NI’IMATULLAH



By haajara abla


ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(annuri is the best)


SHAFI NA HUD’U 4


Shiru tayi cike da tashin hankali jin ko shi wanene amma hakan baisa ta wani firgita sosai ba kai a take ma taji zata iya kasancewa matar sa indai harzata shiga wanan wajen..
“Naa.... zatayi magana kenan ya girgiza mata kai tare da fad’in”badai yanzuba NI’IMATULLAH zan baki lokaci kuma zan baki dama kiyi tunani akai amma ki sani ni SAHEED mai kaunarki ne tun kafin kizo duniya na barki lafiya sai mun sake had’uwa a karo na biyu.... batare data ankara ko ta luraba ta ganta cikin motar ta a kuma k’ofar gidan su ita tasan cewa wanan abu duk da ya faru ba mafarki take ba zahirine amma kuma wanan zahirin yazo mata da bazata tabbas ba yau ta tab’a ganin SAHEED ba bayau tatab’a ganin face d’insaba amma takasa tuna asanda ta gansa kuma a ina... tana cikin wannan tunanin ne malam ya sake kwankwasa glass d’in motar tata da k’arfi firgigit tayi k’asa dashi ganin malam ne yasa tayi saurin fitowa ta tsugunna har k’asa ta gaida sa da alma ya fito sallar asuba kamar yadda ya saba,bai iya ce mata komai ba kawai ya kad’a kai yayi gaba...

Tashi tayi ta shiga cikin gidan ta nufi d’akinta Murja ce tace”hhhh anje club ansha giya ansha casu andawo mtwssss aikin banza wallahi malam yak’i karb’ar shawarata ne kawai ya koreki kibar masa gida ke kanki sai kinfi jin dad’in holewar taki a inda ba ganin idonsa,dan ma dai idon nasa babu abin da yake ragawa kuma babu abin da yake k’arawa anyi asara an biyo halin uwa....
ai jin maganar anbiyo halin uwa yasa har NI’IMATULLAH taje zata shiga d’akinta ta dawo batasan sanda ta d’aga murja sama ta direta a k’asa ba tahau kan ruwan cikin ta ta shak’e mata makogaro Murja sai kakarin mutuwa take sakamakon bakowa a tsakar gidan anyi sa’a da daidai lokacin Baba jimmai ta fito dan ta tace gasarar kokon datake siyarwa da kosai ta hango kamar Murjace a kwance kuma ga wata kamar NI’IMATULLAH tana kokarin kashe ta dan ko numfashi sosai bata iyayi amma baba lami takasa gasgata abin da idon ta ya gane mata tasani cewa NI’IMATULLAH tana da mugun hakuri duk zagin da suke mata bata tab’a tanka musu ba amma mai yayi zafi har haka...
Da gudu ta rugo tana k’ok’arin janye NI’IMA amma abin ya gagara ai sai taji kamar k’aton dutse take ja dan ko motsi alamar sauka ni’ima batayi ba ai baba jammai ihu ta kwala tana mai shela kowa da kowa ya fito ai tuni yan mata da samarin gidan aka cika gida har almajiran malam aka kira dakyar katti suka kwaci Murja a hannun NI’IMA tana ta numfashi sama sama dan har suma tayi ta farka....

Innahlillahi wa’inna ilahi raju’un kowa yake fad’a saboda kowa ya rasa bakin magana gashi itama kanta NI’IMATULLAH bata cikin hayyacin ta haka Baba jummai tayi d’akin ta da NI’IMATULLAH kafin malam ya dawo aikuwa ba’afi minti biyar ba saiga malam tundaga k’ofar waje yake jin hayaniya a cikin gidan sa ya rasa mai ya kawo ta yana shiga ciki ya tarar dasu Baba jumma a tsaye carko carko kamar zakaru ita kuma Murja har yanzu tana ta juyi a k’asa ita kuma Yarta hannatu tace wallahi bazata yarda ba su za’a fad’awa bariki taje tayi shaye shayenta tazo zata kashe mata mahaifiya tana mata bak’in ciki ita tana da mahaifiya ita kuma batada ita. Malam ne yayi sallama sanan ya fara magana”mai yake faruwa naganku a haka.”
Hanntu ce tayi caraf tace”Allah malam yau saidai NI’IMA tabar gidan nan dan bazata kashe min mahaifiya ina ji ina ganin ba dan ita bata da dan tasan ita yar tsuntuwa....kafin tak’arasa malam ya kaimata wani kyakkyawan mari sanan yace”wane ne ya fad’a miki NI’IMATULLAH yar tsuntuwa ce to bari kiji na fad’a miki NI’IMATULLAH ba yar tsuntuwa bace kuma y’ace kamar kowa dan haka ki fita daga idona in rufe,sanan ya nuna baba jummai yace ke jummai fad’a min maike faruwa. Baba jummai ta fad’a masa iya abin da ta gani ya girgiza kai yace ina ita NI’IMATULLAH tace”ankaita d’akina.”
“To muje na ganta.”

Suna zuwa d’akin suka tana zaune tayi ta gumi kamar babu abin da ya faru. Suna shiga Baba jummai tace da ita”sannu Ni’ima.”
“Yawwa baba mai ya faru naganni anan kuma.”
“Malam ne yace babu komai Allah ya k’ara sauki sanan ya fita yace ta koma d’akinta zai aiko akawo mata tofi tashi.”

Tashi tayi duk jikin ta a mace ta koma d’akinta ta kwanta...

Murja kuwa haka yaranta sukajata d’aki suna mata sannu bak’in ciki kamar ya kashe su.

Washe gari da safe su Abbas da Abba suka hango d’akin yayar tasu a bud’e da gudu suka tawo suna murna.
“Sannu da zuwa Anty.”
Cike da murmushi da jin dad’i ta janyo su jikin ta sanan tace”yawwa Abbana Abbas ya kuke.”
“Lafiya kalau Anty a wanan karan da kika tafi Baba jummai tana bamu abinci,malam ne kuma yayi mata magana.”
“Ayya amma abbas naga kwana jiya ne fa naje makaranta kuma wasu abubuwa suka rik’eni sai dare na dawo lokacin kunyi bacci.”
“Amma Anty jiya fa naji Babar su Aisha da hannatu tana cewa kin tafi yawo yau satin ki d’aya kenan.”
“Sati d’aya kuma ta fad’a a fili cike da mamaki.”
Abba ne yace eh Anty yau satin ki guda fa wallahi ba k’arya tayi ba.”
Subahanallah kenan nayi sati a tare da SAHEED amma ya akayi haka kuma ko kwana d’aya acan ni ban ba,sai wata kuma zuciyar tace to taya ma zaki gane lamari irin na mutanen boye.

Wani dogun numfashi taja sanan tace”kuyi hakuri Abbana ni tawa k’addarar kenan bawa baya gujewa k’addararsa watarana sai lamari kudai kuyi k’ok’ari kuyi karatu tukuru kunji har ku cika burinka ku zama a halin talauci bashi da amfani ko kadan kuma ku ringa addu’a Allah ya rabaku da talauci..”
Shikkenan Anty ai kullum munayi kuma idan na zama likita zan sai mana gida mu koma na sai miki gidan bene da mota mai kyu sosai zan kara sai miki,murmushi tayi sosai sanan tace nagode yan uwana Allah ya cika muku burin ku...
“Amma Anty yau bazaki ko ina ba Abba ya fad’a kamar zaiyi kuka.
Cike da tausayin yaran tace yau bazani ko inaba na muku alk’awarin har

Please Login or Register in order to submit comment