gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading NI’IMATULLAH Sirrin Wata Rayuwa by HAAJARA ABLA Chapter 4 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba sauri tayi ta ciro wayarta tasan dai NU’AIMA tasan da exam d’in nan dan kuwa ita ta fad’a min za’a fara yau amma why basu zoba har yanzu,tana wanan tunanin tana kiran NU’AIMA ta baya taji ta sak’alo wuyanta tana magana”sabahul khair Habibty”
“Sabahul nur,amma ya naga sai yanzu maike faruwa ne.”
“Um wallahi na makara ne cos kiya na kwana ina karatu.”
“Ahhhh kice na dawo bayan ki dan kuwa bansamu nayi karatu ba sai yanzu.”
“Kai dan Allah NINU bana fad’a miki ba”
“Kin fad’a min kinsan dai halin kayar ki sai kina min uzuri.”
“To sarkin masu uzurin duk duniya.”
“Ahhh badai ta duk duniya fa.”
“Hhhhh ke NINU akwai labari fa mai zafi ma kuwa bari mu fito daga exam na baki kar naje saboda dad’in labari na manta da karatun danayi.
“Hhhh dan kuwa tsaf idan labari yayi dad’i zaki manta ne....


Suna cikin firar aka shigo aka fara shirye shiryen jarabawar haka akayi cikin sa’a kuwq da yake suna da k’ok’ari sosai nan danan sukayi suka gama sai sukaji ma jarabawar tazo musu da sauki sosai ba kamar yadda sukayu tunani ba tun da ta k’arshe ce suna gama bayan sun fita farfajiya sun zauna ne NU’AIMA ta kalli NI’IMATULLAH tace”gaskiya jarabawar nan tayi min dad’i sosai amma daga gani tafi miki dad’i kalli yanda kika shiga cikin farin ciki.”
“Hhhh kedai bari tayi dad’i sosai fa.”
Tana magana wayarta ta fara ringing zuwa yau d’in nan ya kirata yafi sau ta irga amma tak’i d’agawa kawai sai yanzu da ya sake kira akaro na uku sanan ta d’aga tare da sallama cikin nutsuwa...
“Assalamu alaikum.”
“Wa’alaikumussalam ya abar alfahari ta.”
“Uhmm.”
“Ina fatan kina lafiya ni mai laifi ne nasan nayi laifi amma ki gafarce ni kinji hajjaju na.”
“Ok shikkenan ya wuce amma banji dad’i ba ta sanadin haka ne har wani yazo wajen sabaoda ya ganni zaune ni kadai yaci zarafina.” Tafad’a kamar zatayi kuka. Ai cikin zanura yace”who si he wane ne shi dazai bata miki rai ko cik zarafi ki fad’a min wane ne shi d’an gidan wanene dazai ci miki mutunci wallahi saina sa an kamosa idan kuma ubansa wani ne wallahi sai munyi shari’a akan mai.”
“Ohhh Alhaji mai yasa ka b’ata ranka haka dan Allah kada ka damu ai nima nayi maganin sa kuma ya gane kuskurensa. Kawai ta tsinci kanta da fad’a masa haka dan tasan tabbas zai aikata abin da yace amma ita tafiso abarta itama yaudai ta d’auki fansa da hannunta...
“Ok hajjjaju na yanzu a ina zancen mu ya kwana yaya za’ai mu had’u dan magana ce bata waya ba.”
“Ok babu damuwa a inda muka saba had’uwa ok kizo wanan restaurant d’in.
“Gaskiya Alhaji bazanzo wanan ba ashifa yaci mutunci na.”
“Aa bashi ba nake nufi ai ina da restaurant anan Nasara G.R.A ok babu damuwa ka bani address dinsa idan natashi sai na biyi tanan anjima.”
“Ok babu damuwa zan turo miki.”


NU’AIMA ce taja dogon numfashi sanan ta sake kallon NI’IMATULLAH tace”tunda nake dake ban tab’a jin kina fad’a haka ba mai ya faru wanene wanan wanda yayi gangancin tab’a min ke..
“Uhm wani ne wallahi Ninu kawai Allah ne yake had’a mu batare da sanina ba nake masa laifi na farko na gogesa da motata sanan na biyu na zuba masa shayi kai mutumin nan atakaice dai bashi da mutunci ko kad’an kuma baisan darajar mata ba.”
“Kai gaskiya dai bashi da kirki baisan darajar mata ba har ya iya ci miki mutunci gaskiya bai kyuta ba da zan gansa tabbas dasai na rama miki kuma ya tsigunna da k’afafuwan sa a k’asa ya baki hakuri.”
Dariya NI’IMATULLAH tayi sanan tace”calm down Allah ya huci zuciyar Habibty,yawwa bani labarin da kika ce zaki bani ina jinki.”
“Ai ban baki labari ba masoyiya kinsan yazo fa.”
“Tooo wanene kuma yazo wane mai sa’an ne.”
Rufe fuska tayi alamu kunya sanan ta bud’e tace”yazo shida su daddyn sa harda kannensa da mommyn su bababn Aminin daddy ne NINU tun ina yarinya nake mafarki dashi a matsayin mijina yana da kirki sosai da sosai yana da girmama mutane ina sonshi sosai fatana nidai ya soni kamar yadda nake sonshi duk da cewa shidai baisan ina sonsaba amma ina ji ajikina zamuyu aure kuma zai kaunace ni wallahi zan masa biyayya Ninu zanyi duk abin da ya umarceni muddin bana sab’on Allah bane.”
Babu abinda NI’IMATULLAH take Sai Murmushi sanan tana sake godewa Allah na kasancewar NU’AIMA ta samu zab’in ranta.”naji dadi nayi farin ciki sosai NU’AIMA fatana ki kasance a cikin farin ciki na har abada insha Allah zaisoki fiye da yanda ma kike sonshi zakuyi rayuwar farin ciki kinji zaku haifi ya’ya’ masu kama daku.”
“Aa NI’IMATA ni so nake na haifi y’a mai kama dake kuma idan na haifi mace zan samata sunan ki.”

Dariya sukayi sosai sanan NU’AIMA taci gaba da bada labarin yanda suka ringa wasa da dariya dashi sosai yana ta tsokanarta yana ce mata matarshi dankuwa datana yarinya kafin ya tafi idan akace mata wane zaki aura sai tace yaya salman saboda akwai shakuwa atare dasu tunda aka haife ta yake cewa an haifa masa mata.....


Wanan kenan....


Ko gida dai bata koma ba bayan sunyi exam na yamma duk da cewa tagaji sosai amma batason sab’a alk’awari ta riga ta dauka so idan bata cika ba sai abin ya zame mata kamar wani k’aton nauyu ne akanta....


Address na wajen daya turo mata nan ta nufa infa ta shiga harabar wajen daga nesa ma tana hangosa direct wajensa ta nufa suka zauna suka fara gaisawa”
Hajjajuna mai za’a kawo miki.”
“Uhm kawai ruwa nakeso sai abinci dan yinwa nakeji nagaji sosai kasan muna exam so daga school ma nayo nan.”
“Ohhh hajajjuna ai da kin bari kin huta.”
“Aa alhaji munyi alk’awari dakai so banason sab’a alk’awari.”
“Hakan yana da kyu nagode sosai.”
Sawa yayi aka kawo mata kala kalar abinci haka ta fara ci suka fara yin fira sama sama can taji ya daki kunnenta da wata magana tundaga nan tafara rasa nutsuwarta....
“NI’IMATULLAH bazan boye miki ba hak’ik’a tunda nake rayuwa ban tab’a had’uwa da macen da nakeson mallaka kalar kiba inasonki kuma inaso zan aureki idan kin yarda banki a sati biyu ma a d’aura auren muba....


Ai tana jin wanan batu ta fara fita hayyacin ta ta tahsi tashak’e masa wuya tana fad’in “ni zaka aura ni zaka aura kaga nayi kala da matar daza’a aura ne ka tab’a ganin anyi aure kan aure....

Kasa magana yayi sai neman taimako da yake yi dan yana gangara dan daga ji wanan aikin bana mutum bane koma dai Aljana ce ya kwasota agarin neme nemen matansa...

Yazo zai siya milkshake sai ya zauna suke magana da wani abokin sa dake a dubai suna ta vedio call sai yaji hayaniya tana ta tashi ana magana ana ta salati yana juyowa kawai yaga kamar macece ta shak’e wani k’ato sai kawai ya tashi ya nufi wajen.

Yana zuwa daskarewa kawai yayi a wajen gaskiya ayau ya sake tabbatawa wanan yarinyar bak’aramar mara kamun kai bace...

Zuwa yayi saitin ta cikin fushi da zafin nama ya dage ya kifa mata mari tare da fad’in”ke wai acikin dabbobi yaya sunan ki ke wallahi ba akuya bace ke tinkiya ce sam biki san inda yake miki ciwo ba ke tamkar ba mutum ba wanan wace irin kaddara ce ni da nake ta had’uwa ma dake,kin zame min masifa da.........



Vote
Share
And comments.
Haajara Abdussalam Adam arzuka ce✍🏻.
NI’IMATULLAH



BY HAAJARA ABLA


ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(annuri is the best.)




Shafi na bakwai 7


Juyi take sosai akan katifar tata daidai lokacin Abbas ya shigo d’akin yahau kan ruwan cikin ta yana”Anty,Anty ki tashi ki shirya mu mu tafi makaranta zamu makara fa har rana ta fito.”
Sakamakon dukan da yaked’anyi mata ne yasa ta dawo daga duniyar mafarkin data lula dakyar ta iya bud’e idon ta cike da mamakin abin da ya faru ba gaske bane a cikin mafarkina wai wanene wanana SAHEED d’in da ya sace zuciya ta lokaci d’aya ina sonsa sosai kuma ina kewar sa,ta fad’a a fili tare cike da damuwa a face d’inta. Tashi tayi ta gyarasu sanan tayi musu breakfast duk da haka dai sun makara hakan yasa da kanta ta dauke su a mota takaisu makarantar....

Shiryawa take sosai dan kuwa yaune sukayi da NU’AIMA zataje ta gadai momyn ta dan kuwa tun jiya NU’AIMA take fad’a mata a waya tace tana sane fa...

Misalin k’arfe hud’u ta shirya cikin wani lafiyayyen less da yayi mutuk’ar yi mata kyu da taaruwa a jikinta tamkar dan ita akayi tasa mayafinta k’arami ta dauki jakarta da wayar ta ta d’auki mukullin sabuwar motar ta tayiwa baba jummai sallama ta wuce...

Da yake bata san gidan ba daman already NU’AIMA ta tura mata address nasu bata wata wahala ba dan kuwa a nasarawa G.R.A suke hakan baiyi mata wahalar samun gidan nasu ba,tsaya tayi a bakin gate tayiwa NU’AIMA Waya NU’AIMA tace gata nan fitiwo,kamar yadda ta saba da gudu taa fito inda gateman ya bud’ewa NU’AIMA k’aramar k’ofa ta fita waige waige tafarayi dan bata ga NI’IMATULLAH ba dan kuwa taga dai sabuwar farar mota amma ai tasan batata bace,tana cikin wanan tunanin taji an mata horn had’e da zuge glass d’in motar”oyaaa come NU’AIMA kin shanyani fa.”
Da gudu ta k’araso inda take ta zagaya ta shiga motar tana kallon NI’IMATULLAH cike da Murmushi tace”tooo NINU a’ina kuma kika samo wanan motar mai mutuk’ar kyu da tsada gaskiya motar tayi bala’in kyu daga gani ma basai an fad’a ba it’s very expensive.”
“Hhhhhh Allah ne ya bani daga sama.”
“Kai Ninu bangane ba daga sama.”
“Ohhhh ni NINU zaki shigar dani gidan kokuwa tambayoyin ki nazo amsawa.”
Dariya tayi sosai sanan tace”oyahh enter idan kika shiga kika huta kya fad’a min how u gate it.”
Murmushi NI’IMATULLAH tayi sanan tayi horn mai gadi ya bud’e suka shiga cikin katafaren gidan su NU’AIMA mai kama da aljannar duniya.”
Parking tayi a parking space sanan suka sauka daga motor inda NU’AIMA ta mak’ale NI’IMATULLAH tana mata oyoyoooo
“Oya ya isa haka ni kada ki fad’ar dani bari na d’auki abu a boot.”
Bud’e boot d’in tayi ta d’auki wasu kaya a leda sanan ta rufe NU’AIMA ta rik’e mata kayan suka shiga ciki..

NI’IMATULLAH parking tayi a palor inda ta zauna ta wani nutsu kamar ba ita ba. Dariya sosai NU’AIMA ta kama yi mata tare da cewa”dallah can taso mu tafi sashen mu momy tana wajen daddy sai an jima zaki ganta dan haka taso muje kici abinci sanan kisha lemo.”
Murgud’a mata baki NI’IMATULLAH tayi sanan tace “zanyi maganin Ki NU’AIMA.”
“Hhhhh maganina ai sai husband d’ina shine kad’ai yake da abin da zaimin na kama kaina.”
“Ohhhh ni NI’IMA yaushe kika zama Haka NU’AIMA.”
“Hhhhh daman can a haka nake ki tawo mu tafi.”
“To Allah ya shirya min ke ta fad’a tana ja mata kunne.
Upstair suka hau inda suka d’anyi tafiya sanan suka shiga wani k’aton bedroom kai kace na matan gidan ne.
Abin da yasa ma NI’IMATULLAH ta gane nasune dan taga INAYATULLAH kwance tana chating.

Sallama tayi”Assalamu alaikum.”
INAYA ce ta d’ago da kanta sanan tace”wa’alikissalam sannu da zuwa bak’uwar mu.”
Murmushi NI’IMA tayi sanan tace”nagode INAYA.”
Daga haka basu sake magana ba inda NU’AIMA ta kama hannun ta ta zaunar da ita gefen gadon sanan tace tana zuwa.. fita tayi inda ta koma kitchen yau da kanta tayi komai da komai saboda murnar cewa NI’IMATULLAH zata zo dan haka da kantata shiga kitchen d’in tayu nata girii kala kala irin su plantain rice,chicken irish,pancake,da lemon datasan NI’IMA naso kunun aya tare da coconut juice ita da masu aikin su sukayi wanan aiki sawa tayi aka jera abincin a dinin sanan ta komo d’akin ta kamo hannunta tare da cewa taso muje.
Binta tayi zarai zarai tana mamaki daman har Haka NU’AIMA ta damu da ita take sonta hak’ik’a taji dad’in yanda take kulawa da ita take sonta sosai kamar hakan hakan yasa itama taji sosai a zuciyar ta cewa tana kaunar NU’AIMA daman tinbayau ba tana kaunarta ita ba ma’a bociyar kawaye bace dan so da yawa har gayyatar ta zama kawayen wasu da take had’uwa dasu a waje maban banta amma ita sam harkar kawaye bata gananta ita kawaiabin da tasa gaba shi take yi amma a karo na farko taji tanason wanan baiwar Allah sosai taji tana jinta a wani b’angare na jikin ta tabbas bata fatan INAYATULLAH ta sake tunanin rabasu dan kuwa zatayi kewa sosai zata kasance cikin kadaici a karo na biyu....


Direct dining suka nufa inda suka zauna. Cike da mamaki NI’IMATULLAH ta kalli NU’AIMA,batace komai ba kawai NU’AIMA ta d’aga mata gira...
“Wanan d’aga girar naki duk na mainene ni ban fahimci abin da kike nufi ba NU’AIMA bak’i zakuyi neda yawa wanan abincin haka naga kin kawo ni ni kadai kin zuban ido mai kike nufi.”
“Kai dan Allah Ninu mai kuwa nake nufi kefa mukayiwa yaufa da kaina na shiga kitchen dan ganin nayiwa Ni’imata abin da ranta zaiyi fari kuma takeso.”
“Amma Ninu wanan ai kamar albazaranci wanan abincin ni ina zan kaishi kinsan dai ba wani abinci nake ciba ko to mesa zaki haka.”
“Nidai wallahi Ninu kawai kice idan zakici idan kuma bazakiciba shikkenan zanje na fad’awa momy bazaki ci komai ba kince.” Ta fad’a kamar zatayi kuka..

“Ke ninu duba kaina fa d’an kwali ne ba hula ba dan haka wanan shagwabar ni tamin yawa bansan inda zan kaita ba.”
Dariya sosai NU’AIMA tayi sanan tace “oyaa muci fara d’iba tayi tana bata itama kuma ta fara ci da kanta har saida cikin ta ya cika ahaka ma saida suka kai ruwa rana akan lallai ita bata k’oshi ba sai ta sake ci.
“Nikam naga ikon Allah wai ni da cikina ace ban k’oshi ba kai NU’AIMA to wallahi idan muka aurar dake kikaje kina masa haka dakuwa zaki.”
“Tab wallahi da na dawo gidan mu ko mumy bata dukana sai wani shi.”
“Hhhhh to maida wuk’ar da wasa nake Allah ma ya tsare,ni wanda zai ringa lallab’amin ke kamar kwai shi zan bawa.”
“Hhhhh Yawwa masoyiya koke fa.”

Tashi sukayi suka koma d’aki inda sukayi fira sanan suka sakko palorn k’asa dan momy ma ta dad’e da sakkowa k’asan....

Tun daga nesa momy taga kamar ta shaida fuskar nan kamar ta santa amma data k’araso sai taga kawai asalin kyune da NI’IMATULLAH kedashi yasa yake mata gizo da na fam nasu dan a fisge ma suna kama da NU’AIMA.
Cike da fara’a NI’IMATULLAH ta k’araso wajen momy inda ta tsugunna tana gaida ta.”Ina yini momy fatan kunyini lafiya.” D’ago ta tayi tana mata magana ta rungumeta “haba y’ata kar ki tsugunna taso nan,lafiya kalau ta fad’a sanan ta saketa tace ki zauna mana zama tayi a k’asa momy tace sai ta tashi tahau kan kujera”ki saki jikin Ki NI’IMATULLAH ki d’auka tamkar nan gidan kune kinsan kuwa a kuklum Sai NU’AIMA tayi zancen ki sosai a gidan nan”
Murmushi tayi tai k’asa da kanta batare datace komai ba.
Nagode momy Allah ya k’ara lafiya ni zan wuce dan magrif tayi.”
“Har zaki tafi.”
“Eh Momy saboda unguwar mu da nisa daga nan.”
“Ok Allah ya tsare kinji Allah ya bada miji nagari ki gaida gida ki gaida min da mamanki.”
Insha Allah zasuji haka ta d’auki ledar ta bawa momy.
“Kai amma nagode sosai.”
“Babu komai momy nice da godiya.”
Daidai sanda INAYATULLAH ke sakkowa daga kan benen tayi magana”aa NI’IMATULLAH har zaki tafi.”
“Eh wallahi INAYATULLAH dare yayi.”
“Ok to Allah ya kiyaye hanya.”
Tare suka fita inda tazo daidai fita taji INAYATULLAH adaidai kunnenta ta rad’a mata”daman ke kina tsoron dare ne ko kuwa kinsan dare.”
Murmushi kawai tayi ta wuce batare da tace da ita komai ba ita kuma NU’AIMA daman bataji mai INAYATULLAH tace mata ba..

“Nagode sosai NU’AIMA momynku tana da mutuk’ar kirki sosai da sosai gata kyakkyawa idanuwanta sun birgeni.”
Murmushi NU’AIMA tayi tace”nagode sosai Ninu ai kema momyn kice.”
“Wanan haka yake.”
Saida tazo shiga motar sanan NU’AIMA ta tuna ohhh biki fad’a min wanda ya baki motar nan ba..
“Ohhh ni NU’AIMA wani ne wai Alhaji d’an gaske wai yanaso na halarci birthday nasa nice babar bakuwa yamin alk’awarurruka wanan dai shine k’aramar kyuta ma idan zan bashi had’in kai..”
Jingina Nu’aima tayi da bayan mota
“NI’IMATULLAH abinda INAYATULLAH take fad’a gaskiya ne daman.”
“Gaskiya ne mana NU’AIMA ko kinji na k’aryatata.”
“Amma NI’IMATULLAH why?”
Karii tambaye ni why idan kika kalle ni kika kalli rayuwata zaki gane dalilin NU’AIMA ke baza ki gane ba dan kuwa babu abin da kika nema kika rasa kuma NU’AIMA tawa kaddarar kenan bani da tsumi ko da bara...
“Zancen k’addara kuma amm NI’IMATULLAH ni naga k’addara kuma darasi amma zamuyi magana letter lokaci yana kurewa ki kula da kanki Allah ya kaiki gida lafiya.ta fad’a tare da hugging nata sukayi sallama inda NI’IMATULLAH tace”kuma bance ki zauna kiyi ta shashan tunanin na. Naki ba bance ki damu ba dan Allah kimin alk’awari.”
“Idan nace ban damu ba na miki k’arya amma kuma zanyi k’ok’arin hakan bai cutar dani ba ko ke.”
“Shikkenan nagode amma ki saki ranki kar INAYATULLAH tayi zargin wani abun.”
“To shikkkenan ki gaida gida bye bye...



Jan motar tayi ta fita daga harabar gidan tahau titi tana tafiya cike da tunane tunane tama rasa mai yasa tayiwa NU’AIMA wanan zancen t santa da sa abu acikin ranta tasanta dasa damuwa arai.amma banason in mata k’arya ko kuma wasu su fad’a mata kamar yadda yar uwarta take fad’a mata....


Bata wuce gida ba dan tana cikin damuwa hakan yasa tayi wani club direct babu wani tunani...

Tana zuwa ta tarar ba’azazzo ba sosai cos dare baiyi ba kuma ya wanci anfi zuwa tsakar dare amma kuma ita tazo wajen ishsha’i....
Zama tayi akan kunera kawai tana ta tunani tama rasa mai zata tuna a wanan dagulalliyar rayuwar tata sai kawo mata drinks ake amma tak’i sha dan babu abin da ta tsana kalar shaye shaye dan haka ita bazata haukata kanta da kanta ba acewarta...


Kid’ane ya fara tashi a club d’in inda maza da mata sun taru an fara casu kawai tana nan zaune sai taga giftawar SAHEED cikin wasu kaya bak’aken cord masu d’aukar hankali cikin shigar turawa. A filintace SAHEED!!!!





14/12/2022
NI’IMATULLAH



BY HAAJARA ABLA


ANNURI WRITERS ASSOCIATION
(Annuri is the best).



SHAFI NA TARA 9


Yace yanaso tazo wani restaurant anan zasu hadu zasuyi wata magana mai muhimmanci hakan yas atace shikkenan ba danuwa idan ta samu lokaci zata je,ganin babu abin da takeyi a gidan daman kuma ba wani abu take ba hakan yasa tayi shiri cikin shiga mai kyu ta dauki mukullin motar ta tayi restaurant d’in direct..
Tana zuwa ta shiga ciki ta zauna inda ma’aikatan wajen da suke saving d’in mutum suka tambaya mai za’a kawo mata babu komai sai anjima tace dasu sanan ta zauna tana ta danne danne a wayarta yau kwana biyu rabon da suyi waya da NU’AIMA tunda ta fad’a mata sunje umra tayi mata addu’a sosai daga ranar ma basu k’ara waya ba...

Chat suke sosai ita da NU’AIMA take fad’a mata cew suna cyprus suna jin dad’in yanayin wajen daddyn tane yake wani aiki anan amma wani satin xasu dawo. Fatan Alkhairi tayi mata sosai ta tayata kuma murna a haka suka cigaba da fira har ta sauka daga online d’in dan tanaso ta amshi kemo a da shawarma dan taci...

Tashi tayi taje tayi order kafin a kawo mata kuma ta d’aukko lemo a hannunta tana tawowa zuwa inda kujerar data zauna take wayartace tayi k’ara ta duba taga NU’AIMA vedio call d’agawa tayi inda NU’AIMA take ta magana cikin jin dad’i tana nuna mata yanayin garin ji tayi taci karo da mutum inda lemon hannunta ya zube a jikin sa da sauri ta d’ago da kanta shima daidai lokacin ya d’ago da kansa inda take a fili yace”you again.”
Kallon sa tayi sosai sanan tace”kayi hakuri.”
“Ahh daman dole kice nayi hakuri mana wai mai nayi miki kike bibiyata ne wacece ke iyeeee maine had’in dake jibi inda kika b’ata min jiki wai anya kuwa ke mutum ce.”
Innahlillahi wannan wane irin mutum ne ya ilahi ya zanyi da wanan jarabar tasa wanan mutumin Allah ne ya aikoshi dan ya kuntatawa rayuwata yanzu gashi mun kuma had’uwa gashi kuma dai nid’in ce nayi masa laifi,sunkuyar dakai tasake yi sanantace”kayi hakuri ban kula dakai bane.”
NU’AIMA ce tayi mata magana”yadai Ninu maike faruwa ne ina magana bakyaji.”
“Yi hakuri Ninu i will call u back.”

Tsaki yayi sanan yace”kada ki bari mu sake had’uwa a karo na uku dan wallahi bazakiji da dad’i ba.”
Bata dai sake yi masa magana ba ta koma ta zauna ganin ma bazata iya zama ba kawai yasa ta tashi tabar wajen dan kuwa ranta ya b’aci gashi rashin sa’a sun had’u amma ita tayi masa laifi sai bal’i yake zuba mata kamar babanta mtwsss.


Bayan ta koma gida gaba d’aya ta kashe wayarta ma wai wanan wanene shine haka itafa tunda take ba’a tab’a na miji saurayi dai da yake yarfata a ko ina ba sai wanan bawan Allah baya ganin kyu ko surar da Allah yayi mata komai ma yazo bakinsa fad’a yake wanan wane kalar d’an girman kan mara mutunci ne,Allah ya sake had’ani dakai kayi min laifi wallahi saina koyi yadda ake rashin mutunci na keta maka rigar mutunci Tafad’a tana kuka dan ita abin kuka baya yi mata kad’an...

NU’AIMA keta kiranta akashe ita tarasa maike damun NI’IMATULLAH amma tana mata addu’a Allah ya yaye mata matsalolinta....


Alhaji d’an gaske baizoba sakamakon wani meeting daya taso masa na gagawa a kaduna haka yahau jirgi zuwa kaduna gashi yana ta kiran ta dan ya sanar mata amma nertwork ya hana wayar tata shiga,dalilin da yasa bai sameta ba kenan...


Yau tsawan kwana biyu kenan ko a mafarki ma bata ganin SAHEED gashi kullum da tunanin sa take kwana dashi take tashi ta rasa maike damunta gaba d’aya kewarsa ta addabe ta gashi shi ba mutum ba batasan ma ta inda zata fara ba idan tace zata nemesa...

Addu’a tayi ta kwanta bacci tana cikin bacci tayi wani mummunan mafarki firgigit ta farka aikuwa bata koma ba tayi alwala tayi sallah sanan taci gaba da istigfari har fitowar alfijir Amma gaskiya ta tsorata sosai da mafarkin ya bata tsoro...


Parking tayi adaidai kofar gidan su inda ta gaida malam sanan ta shiga gidan da kaya nik’i nik’i a hannunta sallama tayi suka amsa sanan ta tambaya NI’IMATULLAH tana nan tayi amsa tana nan dan babu inda taje shiga d’akin tayi da sallama cike da mamaki NI’IMATULLAH ta amsa tare da fad’in “ahhhh wa nake gani haka mutanen saudi arabia mutanen cyprus yaushe kuma kuka sauka shine ba waya.”
“Ni dallah rufe min baki ai wayar nan taki gaba d’aya bata da amfani ko kad’an banga amfanin taba wallahi so nawa ina ta kiranki akashe wani time din ma a kunne nake kira amma sai kin ga dama kike d’auka.”
“Tooooo zubaida na yarda ayi min afuwa ni d’ince kinsan sai a slow,bani labari ya tafiyar taku ta kasance.”
“Hhhh wallahi tafiya tayi dad’i sosai cike da kewarki masoyiya ina ta tunanin ina ma ace tare muka tafi nayi kewarki sosai kinga tsarabar ki gashi kuma abasa su Baba wanan...
Leda guda tata leda guda kuma tasu baba godiya ta mata sanan ta rakata takaisa Baba jummai godiya ta musu sanan tayi musu addu’a haka ta dawo d’akin tana ta bata labarurruka kala kala.”
“Am wai nikam ina INAYATULLAH.”
“Tana gida wallahi.”
“Uhm masha Allah,amma Ninu ki bani labarin rayuwar ki da bestin ki mana ina nufin rayuwar da kukayi a boarding school kafin gida sometimes iajin maganganu daaga bakin INAYATULLAH so idan bazaki damu ba idan kuma har ina da matsayin da zaki bani labarin ki ina so inji bansani ba ko na k’aru.”
Cike da kwalar data cika mata ido tace”babu wani abin k’aruwa a cikin sa babu wani abin ayaba sai abin ashsha a cikin sa,na aikata kuskure a lokacin da nake ganin kamar ba wani abu bane amma yanzu nagane kuskure na nagane kuskurena Tafad’a tana kuka.”
“I’m sorry dan Allah ni bance kiyi min kuka ba munar wanan maganar banason in b’ata ranki dan Allah kiyi hakuri kinji Ninu.”
“Babu komai Ninu bawai bazan iya baki labarina bane a’a kawai dan banason tunowa ne sanan bansan ta inda zan fara ba wallahi Ninu da ace zaka iya komawa baya ka goge wani abu da ya faru daikai a baya dana koma baya na goge abin da ya faru ya kasance babu shi a jerin k’addarata.”
Share mata hawaye ta matsa tanayi sanan ta kalle ta tace”dukkan abin da ya faru dake baikai wanda nake cikin saba kin gani dai kuma kinsani ita kaddara haka take amma ni ina ganin Allah ya baku

Please Login or Register in order to submit comment