You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
zaka iya tafiya.”
Zaiyi magana sai kuma yayi shiru yace”tam shikkenan nasan ai wataran ko nan nazo za’a nuna min gidan naku.”
D’aga kafad’a tayi har zai sauka sai tace dashi”am dakata mana,inaso in maka gargad’i inaso ka kula da NU’AIMA sosai da sosai kada ka yarda tayi kuka dakai saboda ta d’auki duk wata yardar ta tabaka dan haka kakula min da Yar’uwata bisa aman kada kayarda wanan zafin kan naka ya bata matsala I told u,u better gate it,if not hmm.”
Shi dariya ma takusan bashi amma ya daure ya cije tare da fad’in”anagama rankishi dad’e ai duk yanda kike so haka za’ai.”
D’aga kafad’a tayi sanan tace”it’s better.”
Fita yayi sanan ta gyara parking itama ta fita ta shiga gida..
Bayan ya koma gida babu abin da yake tunawa sai zancen NI’IMATULLAH ikon Allah wato daman itace wanan k’awar NU’AIMAN datake bashi labarin ta ako da yaushe ashe ma shi yana jin labarin ta ako da yaushe akai akai baisani ba,agaskiya shifa yanzu san yarinyar nan yake yi gaskiya kuma yana jinta tamkar wani b’angare na jikinsa yana jin cewa bazai iya rayuwa ba tabbas idan ya rasata zai samu matsala amma kuma ya zaiyi da NU’AIMA,wanan fa shine ana dara ga dare yayi....
Bacci takeyi hankalinta kwance momy ce ta hauro saman ta shigo d’akin da sallama.
INAYATULLAH ce ta amsa mata sanan tace sannu da zuwa momy.”
“Yawwa wanan kasar tana nan tana aikin nata data saba.”
“Kedai bari momy gashi nan tana nan tanayi ko gajiya ma batayi.”
“Ok to ki tasheta yanzu ku sakko daddyn ku yana k’asa yanaso zaiyi wata magana mai muhimmanci daku.”
“Shikkenan momy bari ma natashe ta.”
D’aka mata duka tayi firgigit ta tashi tana murza ido taga momy tana shirin juyawa sanan tace”momy kikallah fa kiga yanda INAYATULLAH take min kallo yanda take tashina a bacci nidai wallahi momy banason kalar haka wanan tashin daga bacci kamar tashin k’iyama.”
“Hhhhhh kai NU’AIMA kinsan kuwa tashin k’iyama.”
“To kalli fa dan Allah momy abin da take min.”
“Ok sorry my baby,INAYATULLAH kina takurawa y’ata.”
“Ai daman nasan momy haka zakice daman kinfi sonta.”
“A’a fa INAYATULLAH kinsan gaba d’aya ina sonku sosai,bazan kuma iya banbance wacce nakeso a ciki ba.”
“Heeeeee ta fad’a tare da rungumo momy.
Momy ce tace“yanzu dai ba wanan ba kuyi sauri ku shirya daddy yana jiran ku a k’asa.”
Tashi NU’AIMA tayi ta shirya suka sakko a tare daddy yana tare da momy suna fira sai gashi sun sakko.
Sallama sukayi musu suka samu waje suka zauna tare da gaishe da daddy.
Amsawa yayi sanan ya tambayi ya suke suka amsa masa da lafiyar su kalau.
“Am abin da yasa nasa aka kiraku shine,kunsan cewa yanzu kun gana school dan haka yanzu babu abinda ya rage min illah naga na aurar daku dan haka inason nayi magana dasu wad’an da suke zuwa wajen naku,sanan ke NU’AIMA momy tace min d’an SALMAN ne yake sonki ko d’an wajen daddyn turai?”
“Eh daddy.”
“To shikkenan ki masa magana akan inason ganin sa.”
“Kema INAYATULLAH kiyiwa HISHAM magana yazo duk ina son ganin su ranar juma’ar nan.”
Amsawa sukayi sanan suka tashi suka koma d’akin su cikin zumud’i NU’AIMA ta d’auki wayarta ta kira NI’IMATULLAH tana sheda mata abin da ya faru..
Cikin jin dad’i tace mata”yanzu saiki kirasa Ki fad’a masa kinga sai ayi ayi musha biki.”
“Aiku dai kinsan daddy yace bayaso asa ya wuce wata biyu.”
“Kaiii amma naji dadi wallahi daman mene na tsayetsaye kuna dashi suma haka kuma kunason junan ku.”
“Uhm wallahi naso tare za’ai bikin mu,wallahi da NA’EM zai yarda dana bashi ke saidai shi sam baya kula mata gashi bayaso ace za’a had’ashi da budurwa wallahi da yayi sa’ar mata,kwanani daddy yayi niyyar had’asa aure da wata causing d’in mu wallahy da yake yayan nawa d’ankansa ne sai da yasa ita matar da kanta ta fito fili tace bata so.”
“Hhhhh gaskiya ne kinsan matar mutum kabarin sa babu wanda yake aurar matar wani sanan babu wanda yake shige lokacin sa shi aure lokaci ne tamkar yadda mutuwa take da lokaci idan yazo ka anaso ko ba’aso sai anyi shi.”
“Hakane NI’IMATULLAH ubangiji ya baki miji nagari mijin dazai kula da rayuwar ki.”
“Uhm NU’AIMA kenan idan nakasance nima tagari ce?na dauka saina zamto tagari sanan Allah zai bani nagari ki sani Allah baya cutar bayin sa Allah.... zatayi magana NU’AIMA tace”shi ubangiji gafurun rahim ne dan Allah banason wani zance insha Allah ubangiji zai baki miji nagari wanda ya dace dake.”
“Ameen ya Allah.”
Haka sukayi fira sosai sanan suka katse wayar,tana katse wayar ta kirasa yana office yana ta aiki rabin aikin kuma tunanin mutuniyarsa ne k’arar wayar sace ta katseshi daga abin da yake saidai ta katse wani kiran ya sake shigowa sanan ya d’aga “Assalamu alaikum Luv.”
“Wa’alaikissalam shalele.”
“Yakake luv?”
“Lafiya kalau naji muryar ki kamar kina cikin farin ciki sosai.”
“Uhm kadai bari luv yaudai burin mu ya cika.”
“Name fa,yi sauri Ki fad’a min naji.”
“Eh mana burin mu ya cika daddy yace yanasonganin ka ranar juma’a zakuyi magana dashi.”
Wani dam yaji gaban sa ya fad’i magana kuma tame.”
“Tame kuma fa kace luv?”
Shi baisan tunanin nasa na zuciya ya fito fili ba yayi saurin cewa”Ayya sorry badake nake ba,tam shikkenan dai babu matsala matsala sai nazo.”
“To shikkenan Allah ya kawo ka lafiya...
Shikam saboda tunanin NI’IMATULLAH ya shigar masa kai,bai kawo ko d’aya maganar aure daddyn aima zai masa ba dan haka bai damu sosai ba...
Rana bata k’arya rana juma’a ta sake kira ta fad’a masa idan an sakko daga masallacin juma’a ance suzo.
Bayan an sakko daga masallaci kuwa suka hallara su biyun a palorn bak’i suna jiran sa..
Babu jimawa ya shigo inda daman an cika musu gabansu da kayan marmari da abubuwa kala kala.
Daddy ne ya kallesu bayan sun gama gaisawa yace da SALMAN”am SALMAN inaso ka sanarwa da daddy ka nace kuturo neman auren d’ansa wato kai a wajena saboda na shirya zanyiwa y’arsa aure sai na samu labarin cewa kaine kuke soyayya da ita hakane?”
Cike da tashin hankali ya rasa amsar dazaibawa daddy kenan wai maganar aure shida NU’AIMA amma shifa yanzu sam NU’AIMA bata lissafin aurensa dan ya gamo gano rayuwar sa shida NI’IMATULLAH to tayaya ma zai fara maganar auren NU’AIMA......
Vote
Share
And comments.
HAAJARA ABDUSSALAM ADAM ARZUK’A CE✍🏻.
NI’IMATULLAH
By haajara abla
ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(Annuri is the best).
SHAFI NA SHA BAKWAI 17
Sun shirya cikin shirgar atamfar da sukayi ta graduation tayi mutuk’ar d’aukar NI’IMATULLAH sosai tayi mata mugun kyu riga da sikert haka ta fito ta nufi school dan sai sun yi exam sanan zasuyi celebration bayan nan sayu nayau sanan zasuyi wani a evant nan da sati d’aya. Tana zuwa bata zarce ko ina ba sai aji nan ta hango NU’AIMA tayi mutuk’ar yin kyu itama tayi kyu sosai da sosai NU’AIMA ce cikin jin dad’i ta k’araso inda tace tare fad’in “wowww gaskiya kinyi mutuk’ar yin kyu sosai rabin raina Wayyo Allah na tabbata wanan da a motar haya kika tawo bansan iyakacin mutanen dazasu tare kiba kinyi kokyu sosai rabi raina atamfar ta amshi jikin ki sosai tamkar danke akayi ta.”
“Kaiii rabin raina wanan surutun naki ya fara yawa har haka ina fa wani kyu kinfi ni yin kyu kali fa yanda kikayi mutuk’ar kyu tamkar yaudai idan luv ya ganki yace shi bai yarda ba a d’aura muku aure kawai ayau d’inan.”
“Kaiii dan Allah NINU kinsan kuwa d’azu na kirasa kuma ya bani tabbacin zaizo.”
“Wowww masha Allah yaudai zanga wanda ya tafarwa da rabin raina zuciya nasan ya had’u tun kafin na fansa mutumin kirki kamar ki.”
“Kai dan Allah ai biki gansa maba wallahi yana da kirki sosai yana girmama mata fiye da tunanin mai tunanni gashi handsome guy bashi da wata matsala rabin raina ina sonshi da yawa wallahi ina ganin idan mafarki na ya rushe dadai yake da nakashe kaina.”
“Haba dai rabin raina mafarkin ki zai tabbata babu batun kisan kai.”
Haka suka cigaba da fira har aka shiga exam d’in,bayan an fito ne aka fara hotuna da yan class na rabuwa sosai sukayi kyu su uku abin sha’awa.
Ana ta abubuwa sakamakon NI’IMATULLAH da bata fiya son hayaniya ba haka ta koma kan wsu kunerun da suke farfajiyar school d’in ta zauna tana dann wayarta...
Shigowa yayi kamar yadda NU’AIMA ta kwatanta masa haka ya shigo ya tsayar da motar sa yayi parking yana jira NU’AIMA tazo dan bazai iya shiga cikin taron mutanen da yagani ta cikin glass d’in motar saba.
Ya d’aukko waya yana shirin kiran NU’AIMA kawai ya hangota zaune tana ta danna Waya hankalin ta a kwance,k’ara rufe idon sa yayi ya bud’e ya k’ara tabbatarwa da kansa itace,murza idon sa ya sake yi a fili yace”ya ubangiji nagode maka daka sake sawa nayi tozali da wanan yarinyar...
Kawai sai ya tsinci kansa da tunani wai to me hakan yake nufi bana bacci saboda ita kullum cikin tunanin ta nake mai hakan yaka nufi ne,nidai ko giyar wake nasha bazan iya soyayya da yar bariki kalar taba amma mai yasa zuciya ta ta kasance bata da burin da ya wuce na ganta mai yasa na kasance kullum cikin baigenta dafatan had’uwa da ita.. yana cikin wanan tunanin yaga ta tashi tana enman tafiya da sauri ya sakko daga motarsa inda kafin ya ankara har tayi wata kwana. Dube dube yake a daidai kwanar ya tsaya yana dubawa ina tayi ita kuma ta dawo hankali ta gaba d’aya yana kan wayar kawai sai ji tashi tayi tuntub’e ta fad’a kansa..
D’agowa yayi kawai yaganta a kirjinta sun fad’i kasa ko motsi yayi saboda daskarewar da yayi a wajen,shi tunanin da yake yi shine anya ma ba mafarki yake yi ba...
Zaro ido tayi cikin hanzari ta mik’e tare da d’aka masa duka a k’irji sanan tace “waikai dan Allah wane kalar mara kamun kaine maine kuma haka wanan wane kalar iskanci ne idan so kake ka rungumi mace kaje wajen yan iskan naka mana amma saini ko da yaushe ko wane bala’i naka akaina yake sauka waikai anya makuwa kai mutum ne?”
Kawai tsayawa yayi yana kallon small lips d’inta da yake motsawa very romance way kawai shi ya tsaya yana kallo bai ankara ba yaji hannunsa saman lips d’inta dakyar ya iya cewa”calm down dear what’s wrong with.”
Wani abu ne ya ratsa ta wani yarr taji sai abin yayi mata wani kalar yanayi kawai sai ta sauke kanta k’asa..
Janyo hannunta yayi sanan ya matso da ita kusa yace”what’s your name.”
K’arfin hali tayi saboda ya rungumeta kuma batason wani ya ganta a irin wanan yanayi baya tayi dashi sanan tace”waikai baka gudun abin fad’a ne a tsakiyar school zaka rungumeni kana min wani kallo kalar naku na yan bariki naga alama kai abin kunya gaba ka basa ba baya ba...
“Kin kasa amsa min tambayata sai wani faman surutu kike min kamar kinci aku.... bai k’arasaba wayarsa tahau ringing NU’AIMA ce d’agawa yayi ya kara a kunnen sa duk da har yanzu idon sa bai sauka akan NI’IMATULLAH ba.
“Hlo luv kazo kuwa.
“Eh nazo luv nama yi parking.”
“Bari na k’araso.”
“Ok”
Yana fad’ar haka ya katse wayar ya waiwayo dan ya juya sai yaga babu NI’IMATULLAH babu alamunta...
Ajiyar zuciya yayi ya koma mota ya zauna...
Yana shiga ya hango NU’AIMA ta taho tayi kyu amma shi hankalinsa yanzu sam baya kanta..
K’arasowa tayi ta bud’e k’ofar gaba ta motar ta zauna sanan ta juya ta kallesa suka fara gaisawa...
“Ina yini luv ya kake yasu momy dasu ifra.”
“Sunana suna gaida ki Ifrah ma ta dage wai sai ta rakonj nace mata ni kadai aka gayyata dan ba’agayyace suba kuma bazani da ita ba.”
“Kai dan Allah luv da ifrah dani dakai ai duk abu d’aya ne gaskiya nidai banji dad’i ba dakak’i tawowa da ita bari ma nakirata...
Number ifrah takira aikuwa ta d’aga cikin muryar sanyi tace”hlo Yaa NU’AIMA how are u.”
“I’m fine ifrah shine luv yak’i tawo min dake ko.”
“Wallahi kuwa bari Yaa NU’AIMA nayi nayi yazo dani yak’i zuwa dani kinsan luv d’in naki idan baiyi niyya ba.”
Dariya NU’AIMA tayi suka ci gaba da gaisawa sanan sukayi sallama.
Juyowa tayi ta kallesa sanan tace”sai munyi maganin ka luv.”
“Ai ina jinta kuma zan koma na sameta zatasan idan ni sa’an tane datake gulmata.”
“Kaiii luv daga muyin maganar mu nida yar uwata shine gulma.”
“Eh mana I heard everything that she said.”
“Kai dan Allah to shikkenan on behalf of her we apologize.”
“Hmmm kindai ja mata.”
“Am luv u look so worried maike damunka naga tun da kazo is not like yarda na saba ganin ka what’s happening luv.”
“Is no thing kawai yanayi ne.”
“Yanayi kuma kodai banda matsayin da zaka fad’a min matsalar ka.”
“Bahaka bane Na fad’a miki babu komai idan da akwai ma ai tunda na ganki naji komai yayi min haske shaleleta.”
Murmushi tayi mai sauti sanan tace”yawwa yaudai zan kira maka NI’IMATULLAH ku gaisa kasan lokacin da mukaje asibiti kana bacci bakuga juna ba dan haka zan kira maka NI’IMATA rabin raina ku gaisa ina k’aunarta sosai luv kuma itama haka zan iya sadaukar da komai nawa akanta tana da kirki sosai mutuniyar arzik’i.”
“Gaskiya ne nasani batun yau ba akwai k’auna sosai mai mutuk’ar k’arfi a tsakanin ki da Ni’imar ki Allah yabar kauna.aikuwa zanso dai ganin ta.”
“Kar ka damu luv yanzu zaka ganta.”
Wayarta ta ciro ta danna kira amma wayar NI’IMATULLAH bata shiga can kuma sai ta shiga d’agawa tayi”hlo aima.”
“Hiii rabin raina kina ina zaku gaisa da luv.”
“Wallahi kin ganni a hanyar gida rabin raina kawai wani banza ne ya b’ata min rai,ina wanda nake baki labari. NU’AIMA ta amsa da eh to shine ya b’ata min rai wallahi yanzun nan muka had’u ni bansan ma ta yadda ake yake sanin inda nake ba wallahi.”
“I’m sorry rabain raina kiyi hakuri kinji,wallahi banji dad’i ba naso ace kun gaisa da luv amma babu komai wataran zaku gaisa insha Allah.”
“Dan Allah kibasa hak’uri insha Allah zamu gaisa watara gama event daza’ai rana ita yau ai babu damuwa ai nasan zaizo basai mu gaisa ba.”
“Yawwa haka ne fa zaizo mana sai ku gaisa babu matsala ma Allah ya kaimu.”
Haka sukayi sallama ta katse wayar.
“Lafayi luv mai yafaru naga kin canza fuska.”
“Wallahi kaidai ka bari luv wani shashasha ne ya b’atawa rabin raina rai shine fa ta tafi gida yana takura mata Tafad’a min mutumin aikuwa ta tsanesa wallahi koni ma na tsane sa Allah kuwa.”
“Calm downs may be irin mazajen nan ne da basusan mutuncin mata ba,barin daman yan makarantar nan taku sai a hankali.”
“Aikuwa dai wallahi bari na kira INAYATULLAH kawai mu wuce gida muma sai evnt d’in da za’ai rana ita yau ai zakazo tace ma sai ku gaisa anan.”
“Sosai ni kuwa zanzo har gidan kwlliya zan kaiki ranar.”
Haka ta kira INAYATULLAH inda Salman d’in ya kasu har gida sanan ya wuce gidn su cike da tunanin yarinyar nan..
Yana kwance yayi wanka ya zuba tea a cup yana sha yana tunanin a karo na gaba kuma a ina zasu had’u amma tabbas inda suka had’u akaro nagaba kodamai damai sai yasan wacece ita sai yasan sunan ta yasan kuma address d’inta dan kuwa wanan yarinyar ta jefasa a tsaka mai wuya ta tafi ta barshi da tunanin ta...
NI’IMATULLAH bayan ta koma gida itama tayi wanka ta huta ta kwanta a kan k’aramar katifar ta kawai sai ta ringa tunanin yau abin da ya had’asu da mutaminta ta rasa wanan wane kalar mutumine tabbas shi ba aljani bane dan da aljanineshi sai ta sani dan da bazai yarda da abin da SAHEED yayi masa ba amma shi d’in wanene da ya shigo rayuwata yakeson ya shiga hancina da k’udu dune gashi abin bak’in cikin irin rungumar da yayi mata da rik’e mata lips da yayi kawai take tunawa sai taji tsikar jikin ta ya tashi maike faruwa ne ta tambayi kanta maike shirin faruwa dani?”
Nasan babu soyayya a tsakanin mu bazan tab’a san wanan yaran ba har abada yakamata ace iyanzu na yanke shawara gaskiya na yanke shawara akan tunanin da SAHEED yace nayi duk sanda na had’u dashi zan fad’a masa na yarda na amince zan zama sarauniyar sa mata agaresa..
Amma kuma tabbas nasan ba’ayin aure tsakanin mutum da aljan amma ni inason sa kuma inason Na aure sa dan haka babu makawa na shirya taaf dan ganin SAHEED ya zama miji agarine saboda shid’in ai musulmi ne...
🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️ANA WATA GA WATA🏃🏻♀️🏃🏻♀️dan ganin yadda zata kaya sai ku cigaba da biyo ni dan jin ciganan labarin haajara abla takuce🤩🥰a nuna min kauna wajen tayani da forwarding dinsa dan Allah🏃🏻♀️🏃🏻♀️🤣atayani da sharing 😘
NI’IMATULLAH
By haajara abla
ANNURI WRITERS ASSOCIATION 💫
(Annuri is the best).
SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS 18
Gobe ne zai kama ranar event din da zasuyi hakan ya basu damar zuwa gidan k’unshi ne wajen saloon dan su gyara kansu,sam NI’IMATULLAH batayi niyyar zuwa ba amma kawai sai taji tana son taje ayi mata aikuwa fararmace alkyabbar mata bak’aramin kyu yayi mata ba,ya tafi da fatar ta sosai daga gidan kunshin suka wuce ta wajen gyaran kai nan ma yayi kyu sosai tamkar dai wasu amare bayan sun dawo ne suka tsaya a gidan su NI’IMATULLAH yaudai INAYATULLAH tazo gidan su NI’IMATULLAH saboda dalili haka suka shiga har d’akin nata sai kawai INAYATULLAH taji ta tausaya mata daman anan take rayuwa Allah sarki shigas bata da girgam kai ko kad’an amma duk da haka wasu y’any’an talakawar bahaka suke ba mussaman daza su samu kyu irin Na NI’IMATULLAH yanzu nan sai su d’aurawa kansu ji dakai da taka’ma da wasu abubuwan amma ita shiyasa take so silent batada da wanan..
Zama sukayi tabasu ruwa da lemo sukasha suka cigaba da fira. Ana haka har drivern su yazo ya d’aukesu sukayi mata sallama da niyyar sai gobe idan sun had’u a wanen event..
Washe gari misalin k’arfe biyu NI’IMATULLAH ta d’auki motar ta sai gidan kwalliya bayan wasu awanni aka mata make’up wanda tadawo tamkar balarabiya jini ba wasa ba tayi mutuk’ar fitowa a asalinta tayi kyu sosai har idan ka tsaya fad’a ma b’ata lokaci ne,time d’in da aka saka yayu harya ma wuce dan haka direct wajen event d’in ta nufa dan tana da gate pass...
Tana zuw ta shiga daidai parking space na wajen ta ajje motar ta sanan ta fito tana taku cike da hankali kana kallonta kasan tasan inda yake mata ciwo..
Gabad’aya wajen sai kallo ya koma sama suka bita da kallo sai tafito tamaakar wata amarya ai kuwa tuni aka bata tafi ta samu seat a gefe ta zauna tana hanga ta inda zataga su Aiman ta dan kuwa bata gantaba..
Wayar ta ta ciro ta danna kira dan batasan zaman ita kadai saboda yan class maza da mata duk d’aga idon dazatayi sai taga suna kallonta.
Tana kiranta kuwa ta d’aga tana fad’in”yar halak kenan kaga luv ita ke kirana,hello Rabin raina muna cikin zancen ki sai gashi kinkira.”
“Eh wallahi aima kuna ina ne,wallahi nagaji kinsan bansan zama ni kadai a taro kalar haka.”
“Nasani sorry rabin raina luv ne ya tsayar damukinsan Na fad’a miki shine ya kaimu kwalliya gashi nan dai muna kan hanyar zuwa ma mun kusa k’arasowa.”
“Ok sai kun k’araso.”
Tana zaune haka class mate d’in nata suka runga zuwa suna d’aukar hoto da ita har tagaji sosai ta tashi kenan ta hango INAYATULLAH tashigo sai ta koma ta zauna INAYATULLAH ta d’ago mata hannu ta wuce wajen k’awayenta..
NU’AIMA tare da Salman sun jero suna tawowa cikin ban sha’awa sosai suka dace da juna kamar wata amarya da ango,NU’AIMA Sai dad’i takeji da aka saki tafi,duk da tafin da ake baisa NI’IMATULLAH juyawa ba dan ganin su wanene dan babu haka a d’abi’unta..
Kafin ta zauna ne ta fara kiran number NI’IMATULLAH amma bata d’aga ba,sai kawai ta zauna dashi a wani seat dan ya huta in yaso ta tashi ta nemo NI’IMATULLAH da kanta dan kuwa k’arar sautin kid’an ma indai hankalin ka baya kan wayar bazaisa kaji ba.
Bayan ta zaunar dashi ne tace masa bari taje ta kira NI’IMATULLAH dan tasan zuwa yanzu tak’osa tasan zuwa yanzu tafara tunanin tafiya gida. Tashi tayi ta fara dubu dube itana NI’IMATULLAH tashi tayi ta biyo hanya zata fita kamar ance ya d’aga kansa sama kawai ya hangota komai aka saka mata a fuska Na kwalliya bazai hana ya gane taba dan ya mata kyakkyawan sani wanda koshi bai san ta yarda akayi hakan ta faru in a simple way..
Tashi yayi da sauri tazo fita kenan ya figo hannunta cike da fargabab ta juya ta kallesa.
“Nasani daman zakizo.”
Batace dashi komai ba kawai ta tsaya tana kallon sa na wasu dak’ik’u saida ta gane ma she har yanzu bai sakar mata hannu ba tace dashi”paris ka sakar min hannu ko na sharara maka mari agaban jama’ar nan,saki yayi dan yasan zata aikata amma bawai marinta yake tsoro ba aa kawai dan bayason NU’AIMA ta gano yana da matsala da wata mace ne amma badan haka ba zaizo wanan lallausan hannun nata ya sake kaiwa kan kumatunsa...
Tazo zata fita kenan NU’AIMA ta kwala mata kira”rabin raina kin ganni nan oyoyoooo nasan kinyi fushi daman nasan duk yaddda akayi yanzu shirin tafiya kawai kike.”
“Mtsaas kin b’atamin rai.”
“I’m sorry rabin raina wowwww u look so cute wallahi kamar wata yar india kamar wata balarabiya nama kasa ban bancewa.”
“Zaki fara ko.”Tafad’a tana murmushi tana jan kunnanta..
Shi kuwa yana ganin NU’AIMA ta tawo yayi sauri ya koma seat d’in da yake amma idan ba idon sa gizo yake masa ba shifa kamar da wanan yarinyar NU’AIMA ke magana. Kafin ya k’arasa tunanin s ya jiyo NU’AIMA tana fad’in”taho rabin raina ku gaisa d luv kusan juna kun dad’e kuna jin labarin junanku Allah baiyi had’uwarku ba.”
Kamo hannun ta tayi tazo ta direta akan seat d’in da yake da daskarewa tayi a wajen shima kuwa daskarewa yayi dakyar ta iya cewa”kaine saurayin NU’AIMA daman.”
“Kece NI’IMATULLAH daman.”
“Ehhh nice.”
Tafad’a tana kawar dakai.
“Aaa yadai rabin ran maike faruwa ne kinsan shi ne,luv kasanta ne.”
Cikin ina ina NI’IMATULLAH tace”eh uhm nasanshi mun tab’a had’uwa ne a supy mart yayi min siyayya ma kyuta yana da kirki sosai kinyi dace.”Tafad’a tana mutmushin yak’e tak’asa kuma tana masa wani kallo kawai maganar NU’AIMA take tunawa naceewa.idan mafarkina ya rushe daidai yake dana kashe kaina.innallilahi hakan bazata tab’a faruwa ba tabas mafarkin ki zai ciki..”
Dafata NU’AIMA tayi sanan tace”lafaiya naga kin shiga wani yanayai,naga kinyi wani kala.”
“Uhm kaina ne yake ciwo shiyasa zan tafi gida.”
“Ki tafi gida kuma bayan kanki yana ciwo kiyi tuk’u aa kawai luv ya kaiki a motar taki idan yaso ni yanzu sai na jirasa ya dawo.”
“Hab NU’AIMA baki da hankali shikuma fa kina nufin shi kuma sai ya shiga babut d’in haya yadawo a’a gaskiya kibarni zan iya tafiya ma ni kadai.
Shikam yayi k’ik’am yakasa uhm yakasa uhm ji yake tamkar mafarki yakeyi wai dai ashe wacce NU’AIMA ke bashi labari itace wacce yakejin wani abu akanta babu kanta..”
NU’AIMA ce ta dafasa sanan tace”luv dan Allah kakai rabin ran gida kaga bata da lafiya kuma idan mutum yana irin wanan ciwon kan ba’a fiya son yayi tuk’i bafa luv.”
“Eh eh wanan haka yake,NI’IMATULLAH muje muje kawai na kaiki gidan Ai baza’ai haka ba.”
Da har zatace itafa aa ya barshi kawai kuma sai tayi tunanin wani abu sai tace tam shikkenan tagode Allah ya saka da alkhairi tare da cewa”kina da kyakkyawar zuciya NU’AIMA ta Allah ya faran ta miki kamar yadda kika kasance kina son faranta min akoda yaushe,Allah yayi miki fiye da k’ok’arin ki k’awata aminiyata dan kin wuce k’awa agareni saidai yar uwa ta fad’a tare da huggin d’inta.”
“Shikkenan babu komai dan Allah ki gaida su baba Allah ya k’ara sauk’i mazo dubiya ki kula da kanki ubangiji yasa kaffarace.”
“Ameen ya Allah raibin raina.”
Tana fad’ar haka ta juya ta nufi inda motar taya take bud’ewa tayi ta shiga mazaunin mai zaman bnza shima ya bud’e yashiga inda driver yake zama sanna ya tada motar sai ya juyo ya kalleta sai yaga ta tamke fuska babu ko alamun wasa a tattare da ita shi baitab’a ganin ranta ya b’aci ma kalar nayau ba. Shiru shina yayi sanan ya kunna motar suka bar wajen suka hau titi batare da ta fad’a masa inda suka nufa ba kuma ya kasa tambayar ta....
Vote
Share
And comments#
Abla ce✍🏻.
NI’IMATULLAH
BY Hajara abla
ANNURI WRITERS ASSOCIATION💫
(annuri is the best).
SHAFI NA ASHIRIN DA D’AYA
Kai shed’anin ifiritu kai baka isaba ka rabani da ita ba k’aryarka tasha k’arya kayi kad’an wallahi mai akayi akayi ka to bari kaji babu abin da zai hanani aureta kuma a yanzu zan iya d’aura aure na da ita sai ingani idan ka