gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading DAN ADAM by Rufaida Omar Chapter 1 | ArewaNovels google.com, pub-8772996913092952, DIRECT, f08c47fec0942fa0
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng    
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
                D'AN ADAM

       @Rufaida Omar

Sadaukarwa....ga....

        
Jiki na rawa take kwankwasa k'ofar d'akin da k'arfi tana fad'in.
  "Habiba! Ke Habiba!"
"Na'am." Ta furta cikin magagin bacci kafin ta mik'e ta bud'e d'akin. Ganin aminiyarta Saude ne
ya sanyata wartsakewa babu shiri. Ta waro ido. "Lafiya dai Saude?"
  Saude ta rage murya.
"Ina fa lafiya? Ga waccan shegiyar tana nak'uda. Ai idan ta haihu na kad'e."
  Habiba ta dafa kafadarta.
"Karki damu, ai idan har ni ce unguwar zoma ba zata haife d'anta da rai ba. Itama muje sai ta
bar duniya."
  Wani sanyi ya mamaye zuciyarta. Habiba ta dauko kayan amfani ta yi gaba Saude na biye da
ita. Lokacin karfe shida na safe.
  Acan suka iske Malam Balarabe yanata faman zirga-zirga a tsakar gidan. Shigowarsu ne ya
sanyashi nufarsu da saurinsa.
   "Yauwa, Habiba don Allah taimaka mata."
  "Ka kwantar da hankalinka Malam Balarabe, in sha Allahu lafiya kalau zata sauka. Ka sama
mana itatuwa dai na dora ruwan zafi.
  Daga haka ta shiga ciki, Saude na gefe tana matsar kwallar munafunci ita a lallai tausayin
abokiyar zamanta takeyi. Da ire-iren kissar da take cin galabar Malam Balarabe kenan. Da sauri
shi kuma Malam ya fice.
    Saude dake tsaye sai jin kukan jariri tayi. Gabanta ya bada ras ras! A gigice ta fad'a d'akin.
Bakinta na rawa ta tambaya. "Ta..ta.." Ina maganar gaba daya ta mak'ale a saman le66anta. 
Habiba ta dubeta tayi mata alama da tayi shiru. Dole ta rufe bakinta ba don ta so ba. 
  Habiba ta kammala yanke cibi ta mik'awa Saude d'iyar. Saude cikin kukan bakin ciki marar
sauti ta kar6eta tana ji kamar ta shak'eta ta mutu.  
  Ga mamakin Saude, Habiba filo ta dauko ta danne fuskarta da shi, tun Hasiya na shure-shure
har tayi lakwas. Saida ta tabbatar da cewar ta cika sannan ta yi jifa da filon ta mik'e tana sharce
gumi. 
   Saude jikinta babu inda baya rawa.
"Ta mutu." Ta fad'a a gigice. 
Habiba ta gyada mata kai sannan ta dubeta.
  "Eh na cika burinki. Yanzu Malam na dawowa mu nuna mutuwa tayi bayan ta haife d'iyarta. Ko
kusa kada ki nuna wata alama ta rashin gaskiya Habiba. Ita kuma wannan k'aramar alhaki ce, ni
nasan yanda zamuyi da ita nan gaba kadan."
   Saude ta amince da batun aminiyarta. 
"Shikenan."
  Ai kuwa sunajin sallamar Malam suka hau salati da koke-koke.
Malam baisan sadda ya yarr da itatuwan da ya riko ba. Jiki na rawa a gigice ya fada dakin yana
tambayar ko lafiya.
  Ya dubi Saude hannunta rike da jaririya tana ta canyara ihun kuka kafin ya kai dubansa ga
Habiba. Bai yi wata-wata ba ya yi kan Hasiya yana kiranta a rud'e.
"Hasiya! Hasiya!!"
  Ina! Ya fahimci abinda ake nufi, Hasiya ta rasu. Ya hau salati yana zubda  ruwan hawaye.
Baice uffan garesu ba ya fita zuwa tsakar gida ya zauna.
                     *    *     *
   Haka yana ji yana gani aka wanke Hasiya aka kaita gidanta na gaskiya batare da 'yan uwanta
sun sani ba saboda nisan dake tsakanin garuruwansu. 
    Malam Balarabe ya shiga tashin hankali matsananci, ya rame yayi bak'i kamar ba farin
mutum ba. Ga duk wanda ya ganshi dole ya tausaya mishi musamman abokansa wadanda
suka riga sukasan irin kaunar da yake yiwa matarsa Hasiya don kuwa baya 6oyemusu irin
yanda take kyautata mishi a rayuwa ta hanyar yin biyayya ga dukkanin umarninsa. 
     Sai ranar bakwai sannan babban yayan Hasiya da kuma mahaifiyarta da sauran yayyunta
uku mata suka iso. Sun koka kwarai da rashin yar uwarsu. Saidai babu yanda suka iya, su
mutane ne wadanda sukasan ya kamata, sam basu zargi komai ba. Toh me zasu zarga? Bayan
sun san irin kaunar da Saude ke nunawa Hasiya a gabansu tamkar ba kishiyarta ba. Wannan
ne yasa koda Saude tace zata rik'e yarinya, babu wanda baiyi na'am ba. Haka suka tattara suka
koma garinsu batare da shakkar komai ba.
                        *   *   *
  Wahala, tsangwama da kyara, babu irin wacce d'iyar Hasiya, wacce ta ci sunan mahaifiyarta
Hasiya suke kiranta da Ummi, bata gani ba wajen Saude. Saidai a gaban idon Malam Balarabe,
babu abinda Saude bata yiwa Ummi na nuna kulawa da kauna. Yarinya ce mai hakuri, haka
take hakura da komai ta shanyeshi, anan ma Mahaifiyarta ta dauko.
  Saida ta kai shekaru goma sha uku a duniya sannan Saude ta samu ciki. Zo kaga murna
wajen Saude da mijinta. Sai ya zamana bayan Saude ta haifi diyarta Mariya. Ta chanja kwarai a
gidan. Ta hanyar asiri da tsafi, ta siye zuciyar Malam Balarabe ya zamana ko kallon Ummi baya
kaunar yi. Komai ya samo, daga Saude sai Mariya. A wannan lokacin ne, Habiba ta zo da
shawarar tura Ummi aikatau. Ba musu ba jayayya, Malam Balarabe ya amince da a turata ko
bangon duniya ne. Duk acewarsa, bashi da matsala ko wata damuwa...!
     DAN ADAM
@Rufaida Omar
  (02)

"Wai kina ina ne? Baki kammala shirya tsummokaran naki ba?"
  Ummi dake d'aki tana kuka, ta tsinci muryar Baba Saude wacce ta sanyata rud'ewa babu shiri.
Cikin rawar murya ta amsa a tsorace.
  "Na gama Baba, ganinan."
Daga haka ta mik'e da saurinta ta dauki ledarta ta fito har lokacin kuka takeyi sosai.
   Baba Saude na zaune tare da Habiba sai wata mata wacce ita ke dillancin mata zuwa gidajen
aikatau, a gefe kuwa, Mariya ce ke faman cin masara hankalinta kwance, ta yi filo da cinyar
uwarta.
   Wata harara Baba Saude ta watsawa Ummi.
  "Shegen bakin hali, kukan me kikeyi na kinibibi toh? Gwara ki share hawayenki ma, don babu
abinda zai hana yau ki bar gidan nan."
   Ummi ta durkushe a gefe tana share hawaye yayinda wasu ke k'ara kwaranyowa har da
majina tana gogewa da hijabinta.
   Baba Saude ta juya ga dillaliya.
"Ina jinki Yaha, yanzu dai duk wata zaki dunga aiko da albashin nata?"
  Wacce aka kira da Yaha ya gyara zaman mayafinta lokacin da ta mike tsaye.
  "Karki damu, duk wani abin arziki da ta samu ma, naki ne Saude. Komai zan tattaro na
kawomaki. Kedai ki kwantar da hankalinki kamar kin kashe d'an maigari."
  Sukayi dariya sannan Yahanasu ta dubi Ummi tana yamutse fuska.
  "Wannan dogon gashin idan bakiyi wasa ba sai na yankeshi kafin mu k'arasa, yarinya sai
shegen munafunci. Zaki maidashi cikin hijabin ko kuwa?"
   Jiki na rawa Ummi ta ja jelar kitson kalbar da ta jagwalgwala a kanta ta maidashi cikin hijabi.
Don kuwa bata isa ta je gidan kitso ba har ya saka ran samun mai kyau. Ta mike ta bi bayan
Yaha wacce tuni tayi sallama da su ta bata umarnin ta taso. 
   Suna ficewa Habiba da Saude suka tafa suna shewar jin dadi.
  "Ina sonki wallahi aminiya, bani da tamkar ki." Cewar Saude wacce ke jin ranta yayi wani
mugun sanyi. 
  Habiba ta gwaguyi masarar hannunta tana wani rausaya kai.
  "Ni ce fa, sai ma idan kudi sun soma shigomaki a hannu zakisan cewa ba k'aramin gata nayi
miki ba. Ai ba'a saurin illata d'iya mace haka, ita tamkar jari ce, ko zata bi duniya in dai zata
nemo ta kawomaki to kada ki damu kanki, ke dai ki more rayuwarki ta jikinta. Amma fa 'yar
kishiya nake nufi."
    Sukayi shewa da dariyar farin ciki. Koda Malam Balarabe ya iso suka sanar mishi cewar
Ummi ta tafi, ko a jikinsa, karshe ma watsar da zancen yayi ya bi Mariya da tsarabar 'yar tsanar
da ya siyomata.
                      *   *   *
    Tun Ummi na kuka a motar kasuwa, har ta gaji tayi shiru tana kallon hanya kafin bacci kuma
mai nauyi yayi awon gaba da ita. 
Cikin baccin kuma ta ji Yaha na tashinta.
  "Ke! Ke!" Firgigit ta farka tana dubanta. "Na'am." Ta amsa a tsorace don kuwa kusan zuwa
yanzu Ummi ta saba da hakan, da wuya tayi bacci a tasheta batare da ta firgita ba. Don sau da
yawa ruwan sanyi ake kwara mata ko kuma a sanya k'afa a haureta, wani sa'in kuwa da bulala
ake tashinta. Yaha ta watsa mata mugun kallo.
  "Sai ki sauko tunda motar bata ubanki bace ko? Shashashar yarinya."
  Ummi ta lura su kadai ya rage a motar, cikin rawar jiki ta bi bayan Yaha suka fito. Sai lokacin ta
lura cewar cikin wani babban gari suke lura da yawan mutanen da ta ga suna faman zirga-zirga.
Haka tayi ta bin bayan Yaha har suka fito daga tashar zuwa bakin titi. Saida gabanta ya fad'i
ganin ababen hawa da yawa saman kwalta. Ta tsorata sosao da yawan mutanen da ke
zirga-zirga awajen. A kauyensu na Ringim babu motoci har haka. Yaha ta tsayar da d'an sahu.
Nan Ummi ta ji tace ya kaisu Gadon K'aya. 
  A hanya Ummi tayi ta rarraba ido tana duban tituna. Abin bai gama bata mamaki ba, saida ta
ga sun hau wani dogon kwalta ta sama. 
  Ta kankame ledar kayanta, basuyi aune ba sai ji sukayi ta fashe da kuka.
  "Wayyo Allah zan mutu!" Ta fad'a iyakar k'arfinta. D'an sahun harda kokarin juyowa.
  "Lafiya?!" Yaha ta rankwashi kanta.
"Ka bar 'yar iskar yarinya mana, "yar kauye. Ta ji ta a titin 'yan birni zata kawomin iskanci.
Yanzun nan zan bubbugeki idan baki rufemin wannan  karamin bakin naki ba mai kama da na
tsutsa."
    Dariya d'an sahun ya kwashe da shi. Ita kuwa Ummi da sauri ta rufe bakinta, tana kuka a
ciki-ciki har suka sauka idanunta a runtse yayinda jikinta ke kad'awa. 
   D'an sahun kuwa har da labarin tsohuwar da tayi makamancin hakan ya shiga bawa Yaha.
Kasancewar Yahar itama ba baya ba wajen surutu, nan ta biyemishi suna tayi tana 6a6aka
dariya. Ummi dai tana jinsu, alokacin ta bar kukan. 
   Sunyi kusan rabin awa suna tafiya sannan suka iso unguwar da ta ji Yaha tayi kira da Gadon
K'aya. Haka ta ji Yaha nayita zuba mishi kwatance har suka iso wani gida d'an flat da shi. Ta
biyashi kudinsa sannan ta dubi Ummi. "Sauka muje."
  Ba musu Ummi ta sauka da saurinta. Yaha tayi gaba ta bi bayanta tana wulk'a idanu tana
duban layin. Yaha ta shiga kwankwasa k'ofar tana sallama. Can ta tsinci muryar maigadin na
cewa. 
"Ana zuwa."
     
  Yaha ta rik'e k'ugu tana taunar cingam ta dubi Ummi. Ganin haka yasa Ummi kauda nata
idanun cikin sauri. 
   "Don ubanki saura kiyi min halin kauyenci sai na shak'e ki kin mutu har lahira. Banason yawan
kalle-kalle. Kiyi ladabi so..."
  Sauran maganar ya mak'ale a fatar bakinta ganin an soma k'ok'arin bud'e k'ofar.
   Maigadin ya d'an lek'o da kansa. Farin buzu ne. Ganin Yaha ya sanyashi sakin fuska. 
  "A'a mai yara, kaine?"
  Hakanan yake kiranta. Tayi dariya.
"Ni ce dai Baba. Hajiyar na ciki ko?"
  Ya bata hanya ta shigo yana amsa mata.
  "Eh yana nan. Ina ka samo d'an garinmu?"
   Ya fad'a yana duban Ummi wacce ta durkusa da rawar jiki ta gaisheshi. 
  Yaha ta dubeta tayi mata alamun ta mik'e.
   "Wannan ba 'yar garinku bace. 'Yar Maiduguri ce."
   "Anya? Yana kama da mu." Yaha dariya kawai ta d'anyi batace uffan ba.
   Daga haka sukayi ciki. 
Ummi na bin farfajiyar da kallo a sace don bataso Yaha ta kamata tana kallon bayan ta ja mata
kunne. Babban gida ne sosai, an k'awatashi da shuke-shuke. Daga wajen ka rantse ba shi da
wani kyau ko girma don kuwa ko fenti ba'ayi ba daga wajen. 
   Haka suka isa har bakin wata k'ofa. Yaha ta murd'a ta shiga. Suka cigaba da tafiya a doguwar
barandar dake wajen har suka iso tsakar gidan. Acan bakin rariya, wata babbar mace dattijuwa
ce ke zaune saman kujera irin ta tsakar gida tana wanke-wanke.   Ganin Yaha ta washe baki.
  "A'a, lale marhabin da Hajiya Yaha. Yau kuma zuwan rana ce?"
  Yaha ta numfasa fuskarta na nuna gajiya.
   "Bari kawai Ramma, duk a gajiye nake. Hajiyar na ciki mu k'arasa?"
   Ramma fuska a sake ta amsa tana duban Ummi wacce ke takure jikin bango. 
  "Eh tana ciki." Ummi da sauri ta gaisheta. Ramma ta amsa. Har suka kama hanya Ramma na
binta da kallo, yarinyar da alamu zasu d'asa da Hajiya Madina, don kuwa da alama nutsastsiya
ce
DAN ADAM

@Rufaida Omar
          04
     
"Sannu Ummi."
Muryar Amina ta katsemata tunani, ta dubeta, sukayi murmushi a tare.
  "Yauwa."
  Amina ta ninke abin sallar ta ajiye a gefe. Zama tayi a gefen katifa kusa da Ummi tana
dubanta.
   "Daga wane gari kuke?"
"Ringim." Ta amsa a takaice. 
"Lallai, baku da nisa sosai."
Ummi zuwa yanzu ta dan saki jiki da Amina ganin irin yanda take janta a jiki.  Wannan yasa
itama bata ji nauyin tambayarta ba.
  "Ke ba anan kusa kike ba?"
Ta gyada kai.
"Anan dai nayi rayuwata, amma mahaifina d'an Maradi ne can cikin jamhuriyar Nijar. Zama da
neman abinci ne ya kawoshi Nijeriya sukayi aure da Innata, amma yanzu ya rasu, ya barmu mu
hudu yaransa. Ni ce 'ya ta uku a cikinsu."

  Ummi ta d'an tallafi kumatunta.
"Kema aiki kike yiwa Hajiya?"
Amina ta murmusa.
"Ni ina yiwa Hajiya Mama aiki ne, kanwar Hajiyarnan ce, abinda yasa kika ganni a gidannan,
sunyi tafiya ne da mijinta da yaransu, shine dalilin da yasa na dawo nan da zama kafin su
dawo."
    Ummi ta jinjina kai cike da gamsuwa. A ranta ta ji babu dad'i, kenan itama wataran zata bar
gidan ta barta? 
   "Ya dai Ummi? Kinyi shiru ina magana."
  Ummi a sanyaye ta girgiza kai.
"Bakomai."
  Jin haka yasa Amina yin murmushi.
"Shikenan, tashi muje mu tattara falo da kicin kafin Hajiya tayi magana, ki dunga lura da dukkan
abinda nakeyi, nasan karshe ke zaki maye gurbina."
   Ummi bata ko damu ba, idan ana sabo da aikin wahala, ai yaci kuwa ace ta saba, ina take
samun damar yin cikakken awa sadda tana gidan babanta batare da an had'ata da wani
nannauyan aikin ba? Gashi anan har gatan da za'a gyara mata kai a bata wajen kwana
tsaftatacce da abinci mai kyau ta samu. Ai babu abinda zata ce ga Ubangiji sai godiya.
   Haka ta bi bayanta zugui-zugui suka fita. A falon suka iske Adnan da kannensa su biyu,
wadanda ta ji Ramma ta ambacesu da Ihsan, Hanifa da Fahad wanda shi ne auta a d'akin
nasu. 
    Adnan hankalinsa kacokam yana kan wayar hannunsa yana faman latse-latse, yayinda Ihsan
ta dukufa wajen koyawa kannenta aikin gida da aka basu a makaranta. Shekarun Ihsan goma
sha uku a duniya zata shiga na hud'u, sa'ar Ummi ce. Hanifa kuwa, tana da shekaru goma sha
biyu bata da tazara tsakaninta da Ihsan, Fahad ne mai shekaru takwas a duniya. Daga kansa
kuma, Hajiya Madina bata k'ara haihuwa ba. 
   Yaranta gaba daya su takwas ne cif, mata uku ne kafin zuwan Adnan duniya, Rahila, Na'ima,
Aisha, gaba dayansu ukun suna gidajen aure.
      Shigowarsu falon ne yasa su d'ago kai su dubesu. Adnan ya k'urawa Ummi ido fuskarsa a
sake sannan ya maida dubansa ga Amina.
  "Ummi sunanta ko?"
Amina ta gyada kai tana murmushi wanda ya riga ya zamto jikinta, ko kusa bata rabo da shi.
   "Itace." Ummi ta durkusa ta gaisheshi da saurinta sannan ta gaida su Ihsan. Ai kuwa  su Ihsan
suka tuntsire da dariya. Adnan ya dauki filon kujera yana dariya ya jefi Ihsan da shi.
  "(See you), mene abin dariyar?  Ai na isa a gaisheni, kune dai daga yau kada ki k'ara
gaishesu, na tabbatar kin girme musu." Ya karashe yana maida dubansa ga Ummin.
   Ihsan ta jinjina kai.
"Tab, wallahi saidai mu tafa, na tabbatar bazata girmeni ba. Kuma idan ma aka ajiye wannan a
gefe ai 'yar aikinmu ce dole ta girmama mu."
   Ta karashe tana jifan Ummi da kallon eh sun isa. Ummi dai ta kara sunkuyar da kanta. Amina
batace komai ba don kuwa bata fiye shiga harkar Ihsan ba, sanin da tayi mata na cewa ta tsani
wasa da duk wani wanda yake karkashinsu. A ganinta, bai kai har a zauna a sakar mishi fuska
ba. 
  Abin yakan bawa Amina mamaki, yarinya tun bata tafasa ba tana neman k'onewa? Ta tabbata
nan gaba idan Ihsan tafi haka za'a ga abu.
   "Zaki fara ko?" Cewar Adnan lokacin da ya mike tsaye.
  Ihsan ta dara a karo na biyu sannan ta dubi su Hanifa.
  "Malamai ku maido hankalinku mu cigaba. Nasoma jin bacci wallahi."
  Wannan yasa su Hanifa nutsuwa don suna d'an shakkarta kasancewarta itama wani sa'in
akwai masifa. Hakanan ta iya kaiwa mutum bugu, kodan ita din tana da jiki kamar kazar gona. 
   "Muje Ummi."
  Sai lokacin Ummi ta mike, Amina daman tana tsaye bata russuna ba. Tasan Ummin itama don
yau ta zo ne, amma ita kam tuni an wuce wajen, don wani lokacin bata daukar rainin Ihsan,
saidai duk randa ta biyemata suka yi cacar baki ko yaya ne, toh fa tana shan zagi da gori wajen
Hajiya Madina. Sam, bata daukar cin mutunci akan yaranta, komin girmanka, muddin ka ta6a
mata yara toh fa zatasan yanda tayi ta rama. Idan kuwa daga matan gidan ne, acan fadar
maigidan ake k'ulla musu k'ullalliya. Shi kuwa ya hau ya zauna.
      Haka Ummi ta taimaka suka kammala gyara komai na kicin sukayi wanke-wanke. Lokacin
ana gabatar da sallar isha'i a masallacin unguwa. 
  A gurguje suka fito suka tattara falon, Ummi na lura da komai, a karshe bayan sun kammala,
Amina ta fiddo dukkan abinda tasan zasu bukata wajen cin abinci ta jera bayan ta shimfid'a
babbar ledar cin abinci a tsakar falon. Daga nan ta dubi Ummi.
  "Jeki kiyi sallah, zan sanarwa Hajiya mun kammala."
"Toh."
  Daga haka Amina ta mik'a wani d'an (Corridor) ita kuwa ta nufi dakinsu. 
  Har ta idar da sallar Amina bata dawo ba, nan kuma ta zauna ta soma gyangyadi don kuwa ba
karamin gajiya tayi ba. Ta kwanta saman katifar dake shimfide ta mutum d'aya, wani dadi taji ya
ratsata, yayinda iskar fanka ke kad'ata.
  "Ashe nima zan kwana saman katifa wataran?"
  Ta fad"a a fili. Tana nan kwance ta ji shigowar Amina. Da sauri kuma ta mik'e zaune tana
mutsistsika ido.
  "Har kin soma bacci wai? Taso mu ci abinci."
  Ta mike ta bi bayanta, falon wayam, kadan-kadan ta dunga jiyo sautin dariya da hirarrakinsu
daga can cikin da batasan iyaka zurfi da yanayinsa ba. 
  Amina ta kammala kwashe komai ta wanke na wankewa, tayi mamakin yanda bata nemi
tayinta ba. Suka zauna suka ci tuwo da miya sukayi nak, a karshe suka sha ragowar romon kifi
wanda duk an jagwalgwalashi da k'ayoyi, haka suka dan tsinci na tsinta suka zubda sauran. 
  Bayan sun kammala, Amina ta rufe kicin din bayan ta kashe fitila, ta rage fitilun falon sannan
suka shige dakinsu suma.
  "Bazasu dawo falon ba?" Cewar Ummi.
Ta gyada mata kai. "Ai kuma shikenan, acan babban falon Hajiya suka fi zama, matukar kinga
sun shige, toh sai kuma wata safiyar, don daga nan kowa makwancinsa yake nufa."
   Ummi ta jinjina kai kawai. 
DAN ADAM
     @Rufaida Omar

            05

  Bayan shigarsu Amina ta dubeta.
"Idan kika bi shawarwarin da zan baki, toh lallai zaki zauna da kowa lafiya a gidannan. Yanzu na
lura kina tattare da gajiya, ki kwanta ki huta, gobe ma yi maganar idan Allah Ya kaimu da rai da
lafiya. Kinji ko?"
  Ta gyada kanta tana murmushi, haka kawai ta ji tana kaunar Amina.
  "Toh Anti." Antin da ta kirata da shi ya sanyaya ranta sosai, itama ta ji tana kaunarta kamar yar
uwarta ta jini. Tana mamakin uwar da ta haifi yarinya kyakkyawa har haka, ta juma iya barinta ta
fito aikatau. Kodayake, rayuwa ce ke sanyawa wani lokacin, ba don rai yana so ba. Ita ta ta6a
zaton zatayi wani aikatau? Ko a mafarki a'a. 
   Ta barwa Ummi katifa; ita kuwa tayi amfani da bargo ta shimfida a gefenta ta kwanta. Ummi
na jin sadda take zuba ruwan addu'o'i, abin ya bata sha'awa. Daga nan bacci ya kwasheta
batare da ta shirya ba.
    
   ■●♣♣♣♣♣▪▲♥♥♥★★★★★
      
Washegari dakyar ta iya mik'ewa saboda dad'in baccin da ta ji. Amina ta jima tana tashinta, har
daga karshe ta hakura tayi sallah sannan ta k'ara dawowa ta tasheta. Sai lokacin ne kuma ta
farka. Ummi harda su miyan bacci. 
  Bayan ta idar da sallah tana shirin komawa ta kwanta Amina ta dubeta tayi dariya kad'an.
  "Lallai Ummi kinaso Hajiya ta bud'emiki wuta. Ai muddin yaranta zasu makaranta to bacci fa ya
k'are mana. Sai an had'a musu shayi an dafawa Fahad indomi don kuwa kullum da shi yake
tafiya. Sauran kuma wani sa'in shayin ma ba shansa sukeyi ba haka suke tafiya basu damu ba.
Sannan akwai gyaran dakunan yara da Hajiya. Sauran ayyukan da ya shafi kicin da falo da
tsakar gida, duk ba namu bane, yana cikin aikin Ramma, sai da daddare ne ma tattara falo da
kicin yake dole a kanmu. A yanda nasani kenan yanzu, bansani ba ko kema haka zata d'oraki
akai ko kuma zata chanja tsari."
  Ummi dai tayi shiru kawai tana sauraronta. Suka fita falon. Amina ta kunna fitilu wanda ta
tabbatar ita da ta kashe d'in, ita ta kunna don babu wanda zai fito. Adnan ko zai tafi masallaci,
zagaye yakeyi ta k'ofar waje ta d'akinsa. Ummi 'yar mik'omin wannan da wancan ce, tana lura
da abinda Amina keyi. Haka kuma tana biye da ita da fahimta. 
   Komai suka hada, Amina ta zuba Indomin a filas din Fahad na makaranta, ta had'a shayin
sannan suka fito. A falon suka iskesu, kowannensu na shiri. Ihsan ta shirya Fahad tsaf cikin riga
ruwan goro da bulun wando na makaranta. Itama ta shirya cikin riga fara da siket ruwan toka,
sai farin hijabi da safa fara, ta saka bak'in takalmi. Shima Adnan irin kayan Ihsan ne saidai
wando ne nashi dogo, da farar hula (Face cap) wanda aka buga tambarin makarantar daga
gaba. Shima bak'in takalmin ne sai farar safa, wanda hakan ya kasance tsarin makarantar.
   Ba karamin kyau da burge Ummi sukayi ba, gaba d'aya sai ta shagaltu a kallonsu tana
murmushin inama itace ta samu wannan gatan na zuwa makaranta. Tana son karatu sosai
saidai bata da mai mata gatan nan. 
  Adnan na kokarin zura (belt) na wando ya ankara da ita. Ya dubeta batare da ya cigaba da
abinda yakeyi ba, bai kai ga magana ba, tayi sauri ta durkusa ta gaisheshi, ya amsa sannan ta
juya ga Ihsan wacce take zura littafi cikin jakarta ta makaranta, itama gaisheta tayi. Ihsan ta
amsa tana hura hanci cike da jin ita d'in ta isa ta kai. Adnan ya girgiza kai ya ja karamin tsaki.
"Na gayamaki ki daina gaisheta ko? Kodayake don kanki zaki bari ai."
   Ihsan ta turo baki. "Nidai wallahi broda kana ban kunya a gaban 'yan aiki. Kaga banason irin
haka, wannan jawomin raini ne fa."
  Harararta kawai yayi baice uffan ba. Ta dubi Amina. "Ki zubomin shayi."
  Amina ta juya bayan ta ajiye na Fahad a gabansa da biredi da bota. Can sai gata ta fito da
kofuna biyu a hannunta. Ta ajiyewa Ihsan d'aya, sai Adnan wanda take yace bazai sha ba. Ta
ajiyewa Fahad filas d'in

Please Login or Register in order to submit comment