ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyada kai. 
"DAN ADAM kenan, yanzu ke ba abun ki tayani bakin ciki bane Ikram, ba abun ki tayani zubar
da hawaye bane, ko labarin matsayin Ummi ga Abubakar mai iso ga kunnuwanki ba?"
Ikram ta dubeta jiki a sanyaye.
"To ya zamu yi Ihsan banda mu yi hakuri, komai fa na Allah ne, ba yanda zamu yi tunda haka
Ya tsaro za ki auri dan uwan Ummi, ni ai ba zuwan farinciki zanyi ba, ba kyaso ki ga yanda
zasuyi shagalinsu ba?"
Ihsan ta ja tsaki yayinda idanunta suka cika da ruwan hawaye, shikenan fa k'aryarta ta k'are,
wani aji da jijji da kai yanzu saidai ta yiwa wata ba Ummi ba tunda dan uwanta zata aura, ita
kam tasan ko giyar wake ta sha, ba zata tunkari Abbanta ta ce ta fasa auren Abubakar ba,
sannan bayan wannan ma ga sonsa da ta ke ji a ranta. Sam, ba zata iya hakura da shi ba a
yanzun, da ya ya ma ta soma sonsa da har za ta soma tunanin guje mishi? Ita kuwa babu
Gomben da kafafunta zasu taka.
'Ko ba ki je yanzu ba dole ki je a gaba tunda za ki auri dan Gomben.' Cewar wani sashe na
zuciyarta. 
                   ***   ***    ***
  Bayan Azhar su Hajiya Mama suka isa, alokacin Ummi suna dakin Abida suna faman kwasar
hira, Mariya wacce itama Malam Balarabe bai jima da daukota daga gidan kakanninta ba
saboda bikin ta shigo a guje da yaran gidan.
  "Adda Ummi, Adda Ummi!" Haka ta ke fad'a kamar yanda ta ji sauran yaran gidan na fadawa
Ummin. Ta zube gabanta tana numfarfashi, yarinyar gaba daya ta chanja ta yi ki6a kamanninta
da Saude na nan kamar an tsaga kara an karyashi. 
"Meyafaru?"
Cewar Ummi wacce duk kiran ya rudar da ita. 
  "An kawo lefenki."
Ta ja guntun tsaki tana tureta, su kuwa su Amina suka dara, nan suka ja mayafi suka nufi
hanyar fita Amina na fadin.
"Ah, bari muje na gaisa da mutan Abuja."
  Gaba daya kowa ya tafi aka bar Ummi nan zaune ta yi shiru don gani ta ke kamar mafarki ta
ke yi, wai lefenta? Ta yi tsuru tana rarraba ido. 
   Hajiya Mama ta kama baki ganin Amina lokacin da ta ke gaisheta.
"Ke kam ai kin zama 'yar gida shiyasa tunda ki ka kira ki ka ce kunzo lafiya ban k'ara ganin
kiranki ba."
Akayi dariya, Amina ta hau sunkuyar da kai itama tana darawar. 
Masaukin da aka tanadarmusu(wato gidan da ke makwaftaka da wannan, wanda ya kasance
na Aminin Malam, Manu kakan Ummi saidai ba wanda ke ciki sai kuwa bak'i da ake saukewa)
nan aka kai kayansu, saida suka yi sallah sannan aka hau gaggaisawa daga nan suka ci abinci,
nan kuma aka hau buda lefe, ita dai Ummi banda sautin bud'a babu abinda ta ke ji, kaya ne
masu tsada aka sanyamata, akwatinta saiti cif, harma da wani daban na kayan lalle da na budar
kai da sauransu, cikin suturu kuwa har da dinkakku. 
  Ummi na faman zirga-zirga ta yi can ta koma nan ba zato ta ji Amina ta d'ane bayanta tana
tsalle da dariya. A farko ta tsorata don har gabanta ya fadi saidai jin muryar yasa ta numfasawa.
  "Kai don Allah Anti."
Kafin ta kai ga juyowa ta ji Amina na kuka har da sheshsheka, da sauri ta juyo daman itama
karfin hali ta ke yi kawai, nan suka hau kuka babu mai rarrashin wani. Kusan duk abu guda
suke tunawa. Amina ta dubeta.
  "Ki godewa Allah Ummi, ki godemiShi, Ya so ki da rahmarSa, Ya baki matsayin da kudi ko
karfinki bazai ba ki ba har abada. Na ta6a ce miki Yaya Faruk ya fi karfinki, matsayinki da na shi
ya sha bamban, a wancan lokacin ina jiyemiki tsoron shiga wahalar rayuwa ne, shiga cikin
wadanda suka fiki da komai. Ga shi da Allah Ya yi ke din matarsa ce, sai Ya maida komai ba
komai ba, ma'ana tulin matsalolin da muke hange ba wasu matsaloli ba, shakka babu ayau na
k'ara godewa Allah da naga lefenki, na kalli dama da haguna naga dangin Ummina cike a daki,
Ummina 'yar dangi ce! Allah Ya baku zaman lafiya da Yaya Faruk, Ya baku ikon rike juna bisa
amana har abada."
  Ummi ta kasa komai sai murmushi ga hawaye na zuba, Amina ta ja ta suka zauna ta hau
share mata hawayen, kafin waninsu ya ce komai, wayar Ummi ta hau ringing, suka kai dubansu
ga wayar sannan Amina ta dara.
"Bari na koma wajensu Hajiya Mama, ki gyara fuskarki fa don nasan zasu buk'aci ganinki."
Daga haka ta fice, haka ya bata damar janyo wayar, gogannata ne kuwa. Dakyar ta iya dagawa,
tana dagawa kuwa ta ji ya sakarmata gud'a a kunne, batasan sadda ta tuntsire da dariya ba
sosai, shima yana tayata, saida suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita. 
  "Kai don Allah."
Ta fada a shagwa6ance, yanzu kam ta saba da Faruk ta saki jiki da shi. 
  "Kai don Allah me? Ko ba Amaryar Faruk din bace?"
   Murmushi kawai ta yi. 
"Ina zuwa, kiran Daddy na shigowa, zan k'ara nemanki."
  "Toh." Ta fada sannan sukayi sallama, kafin ya k'ara kira su Abu da sauransu suka shigo tafiya
da ita gaisawa da surukai. 
  Haka suka sanya ta lullu6e fuskarta da mayafi sannan suka fita. Ba yanda ta iya dole saida
sukaa budemata fuskarta, kowannensu ya yaba, to idan ma basu yaba din ba ya zasuyi tunda
an riga da an daura?  Hajiya Mama ita mamakin kyawun da Ummi ta k'ara kawai ta ke yi, ashe
rashin samun hutu da gyara ne ya sanya ta koma gatanan? Bayan fitar su Ummi, matasan
gidan suma suka shigo aka gaggaisa, Hajiya Mama bata yi mamakin ganin Abubakar ba tunda
labari ya iso gareta, acewarta ma sai ko baa fada ba za'a ga kamannin Alhaji Kabiru da wasu
cikin yan uwan Ummin. 
   Anan ne kuma sauran abokaan tafiyarta suka ga mijin da Ihsan zata aura, sun yaba kwarai. 
   Dangin Ummi suka hada su da(snacks) da kwalayen lemuka da suka yi musu aka kai
masaukinsu aka ajiye. Washegari wajen daya da mintuna su Ikram su Mami aka iso, Mami ta
dake matuk'a don yanzu jikinta ba karamin la'asar ya yi ba musamman ma ganin kawarta
mahaifiya ga Abubakar, Hajiya Salma. 
A ranar ne kuma ake lalle.Tun zuwansu basu sanya Amaryar a idanu ba sai da aka soma biki.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

114

Ummi ta shirya cikin wata koriyar atamfa mai adon kaloli jiki, ta yi kyau matuk'a a wannan rana,
filin taro sosai Abubakar ya kama, shi ya biya komai, abinka da aikin kudi, nan aka gyare wajen
aka yi kwalliyar kumbo a gefe da gefe inda amarya zata zauna sai kuwa tuntun da aka aka
sanya, da katon darduma inda akai kawayen amarya zasu zauna sai kujeru. 
  Sai awajen taron Mami suka hadu da Amarya Ummi, Ikram tun zuwanta ta ke rarraba idanu na
son ganin inda zata ga rabin rannata saidai bata ganshi ba. 
  Wajen ya burgesu ainun, da ka gansu kaga  zuri'ar Modibbo da ta Danzaki, sunyi kyau har sun
gaji, suma dangin Ummi, sun cekare abinsu. Kowannensu da baiwar kyan da Allah Ya yi mishi
bakake da fararensu. 
   Amarya ta sha lik'i a wajen dangin mijinta hakanan suma danginta ba'a barsu a baya ba.
Mami koda ta je lik'amata har saida ta rungumeta, wannan abu da ta yi yasa Hajiya Mama jin
dadi matuka har batasan sadda ta hau lik'a musu kudi ba. Ummi har hawaye ta yi don dadi,
shakka babu wannan ya nuna Mami ta sauko.  Jidda kam su dai yan bin yarima asha kida ne, to
me zasu ce tunda wacce suke ganin kusan ba'a kyauta mata ba itama ta sauko? Ina ga su 'yan
karan kada miya?
   Sai wajen Magriba suka tashi.

Misalin karfe takwas da dare, Amarya ta kammala waya da Angonnata wanda sai gobe zasu iso
da tawagarsa don budar kai, tana tare da yan uwanta ana hira da dariya, Ikram ta shigo da
sallama. Duk suka dubeta suna masu amsawa, Ummi ta saki fuska saidai can kasan ranta
gabanta ne ke dukan tara-tara to da me kuma ta zo mata?
   "Amaryata ki zo mijinki na kira."
Fuskar kowannensu da mamaki, sauran mamakinsu na zuwan ango, Amina da Ummi kuwa
bayan haka harma da na sabuwar fuska da suka ga Ikram da shi wanda basu saba ganinta da
shi ba akan lamura na Ummin, wato fuskarta a sake saidai idan ka nutsu za ka fahimci a
kunyace ta ke dakewa kawai ta ke yi. To ya zata yi? Tunda tana son dan uwan Ummi ai dolenta
ta sauko. 
"Wai Angon ne ya zo?" Cewar wata budurwa. 
   Ikram ta dubeta tana 'yar dariya.
"Gani nan, ai nima miji ce tunda kanwar mijin ce."
Sukayi dariya gaba daya har Ummi, ta saci kallon Amina, Amina ta yi mata alama da ta je. Ta
mike ta bi bayanta, anan kofar dakin suka tsaya. Ikram ta ga shirun ba zai amfaneta ba ta yi
magana cikin sanyin murya.
"Don Allah Ummi ki yafemin abubuwan da na yi..."
Sai kuma ta ji kunya, hakan yasa ta yin shiru.
'Rayuwa kenan." Cewar Ummi a zuciyarta. A fili fad'ad'a fara'arta ta yi don dagaske ta ji dadi
kamar ta shid'e. Hannunta ta riko.
"Kai haba, ni ban rike ki da komai ba, daman nafi daukar hakan a rashin fahimta, na yafemiki
duniya da lahira nima don Allah ki yafemin."
  Dariya ta yi ta dafa kafadarta.
"Nagode Ummi."
Ummi ta ja hannunta.
"Zo muje kiga yan uwana."
Daman haka ta ke so, ta bi bayanta suka koma ciki. Zama sukayi ana hirar tare, yawanci duk
Ummi suke koyawa yanda ake kula da miji ita kam shiru ta yi don ta ga su babu ruwansu, Ikram
dinma da ta ke kunyar ita dinma ta biyemusu. Sallamar Gidado ce ta katsesu, suka amsa, yana
daga kofa yana dubansu, sanye ya ke da shadda ruwan toka babu hula akansa, gashinsa ya yi
luf-luf. 
   "Me ake tattaunawa ne aka manta da kawomin furata?" Cewarsa yana duban Matarsa Hafsa
dake aikin dama mishi fura, ita kuwa baiwar Allah Ikram tun shigowarsa ta daskare a wajen
gami da k'ura mishi idanu. 
  Shi kam sau daya ya kalleta kallo na ganin bak'uwar fuska daga nan bai k'ara dubanta ba. 
  Hafsa ta bishi da murmushi.
"Na gama yanzu zan kawo."
"To saiki hanzarta, kinzo kin biyemusu kun samin kanwa a gaba kuna cikata da surutu ko?"
Aka dara, Ikram murmushin yak'e ta yi gabanta na bugu da sauri-sauri jin wai Gidado na da
mata, ta dubi matarsa, babu laifi bata daga sahun munana amma a diri na halittar jiki ba zata
nunamata ba, babu gaba balle baya. Ta kara satar kallonsa. Ta ko'ina ya kere matarsa saidai ta
kula kallon ma da ya ke jifar matartasa da shi wacce ta ji a dazun sun ambata da Hafsa, kallo
ne na musamman mai  nuni da tsantsar so da kauna. Ta sauke ajiyar zuciya yayinda ta ke ji
kamar ta dora hannu aka ta hau rusa ihun kuka.
  "Kai Yaya Gidado, ba kunyar idanu irin wannan kallon?"
Cewar wata Maimuna abokiyar wasansa, ya kai mata duka ta kauce.
"Kefa kin raina ni yarinyarnan, kinga taso ki ji zan dan fita ne da Abubakar."
   Ba musu Hafsa ta mike ta bi bayan mijinta, su kuwa yan dakin aka sanya dariya banda Ikram.
Duk zaman ya gundureta, ji ta ke kamar ta bar wajen, ai kuwa da sauri ta mike.
"Bari na tafi na kwanta na gaji."
Ta yi maganar a sanyaye tana duban Ummi, Ummi bata kawo komai ba bayan rashin sabo don
kuwa ita kanta bata sake da ita ba ganin abin ta ke banbarakwai wai namiji da suna HAJARA. 
     A nan soron gidan ta yi kici6us da Gidado da Hafsa, ya wani kankance murya yana magana
kamar saurayi gaban budurwa, suka dubi juna ya jefeta da murmushi.
"Sannu da bakunta." Ya bata haushi saidai ta danne.
"Yauwa." Ta amsa a dakile kafin ta wuce da saurinta zuwa wajen yan uwanta.
   Koda ta shiga su Jidda ke kwasar hira akan yan uwan Ummi kowacce na tofa albarkacin
bakinta,  sam basu dauka zasu gansu kai a waye ba, sun yi zaton kauyen da zasu je yafi haka
muni sai kuma abin ya basu mamaki ganin komai tsaf. 
   "Ke kuma daga ina?" Cewar Baraka. 
Ta yamutse fuska.
"Wajen matar Yaya mana."
Mamaki yasa su sakin baki kafin su hau dariya.
"Shishshigi ko?" Cewar Fadila.
Ta daure fuska gami da kwanciya saman katifa ta basu baya.
"Ba ruwan mutum."
Suka shareta. Wannan daren har hawaye ta zubar na tausayawa kanta haka kuma bata ji komai
na digon son Gidado ya ragu a zuciyarta ba...!
       
        WASHEGARI BUDAR KAI....!

Karfe biyu Ango ya iso da tawagarsa saidai a Otal suka sauka....!
         
       DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Wannan naki ne yar uwata...
Sis Aisha Samarou...
115
Ranar ko waya bai samu damar yi da amaryartasa ba.
Dukkan wani masoyi ga Ummi zai so ganinta a wannan rana don kuwa ta yi kyau ainun, har
wani kumatu ta ajiye, kasancewarta fara k'al, sai kunshinta ya yi kyau ainun, hakanan siraran
kitson da akayi mata shima ya taimaka kwarai wajen fiddo da zahirin Hasiya Abdullahi. Karfe
hudu aka sanya na yin Budar Kai saidai ba'a soma ba sai karfe biyar harda mintuna, anan kofar
gidan zaayi.
Ummi ta hade cikin wata hadaddiyar shadda kalar sararin samaniya wacce ta sha aiki, suka
sanyamata Alkyabba, duk a cewarsu itama jinin sarauta ce don kuwa jika ce gidan Lamidon Jar
Kwami. Shima angonnata ya sanya riga da wando sai kuwa babban riga ta shadda kalar na
Amaryartasa. Hular nan ta zauna d'abas a kansa, shi kansa Angon wani kamshi da annuri
kawai ka ke gani saman fuskarsa.
Fuskar Amarya a rufe ruf, haka aka riketa har mazaunin da aka tanada mata, Ango na zaune
tare da su Haidar sai kuwa abokan karatu da na aikinsu, sannan danginsa mata a baya suna
fuskantar Amarya Ummi da nata dangin itama daga bayanta.
Algaita kawai ka ke ji ana busawa awajen, nan aka soma inda Ango Faruk ya mike, Haidar da
Jafar wano abokin aikinsa sune a gefensa, haka ya nufi wajen Amaryarsa mata na faman gud'a
da hanci ya bud'e fuskar Amaryarsa kuma matarsa, idanunta a k'asa tana faman doka
murmushi yayinda ta ke kokarin danne kukan da ke son kwace mata. Nan ya soma zuba ruwan
kudi waje ya cika da sowa da gud'ar mata, bayan ya gama nasa suma abokansa suka soma
kafin daga bisani bayan komawarsu danginsa su tashi suma su yiwa Amarya nasu lik'in. Bayan
sun kammala ne, itama Amarya ta mike da Amina da Abu kanwar gidado suka isa ga Angon
wanda ya kasa dauke idanu daga kan Amaryarsa yana ji kamar ya dauke abarsa su gudu.
Durkusawa ta yi suka mik'a mata turare na maza mai tsada da dadin kamshi ta hau fesa mishi,
ya lumshe idanu ya bude yana dubanta, hawayen da ta ke kokarin dannewa saida suka zubo,
ta daure ta daukesu da sauri, sannan ta amshi hankicif a kunyace ta hau goge mishi gumi
kamar yanda aka koyamata, habawa zo kaga sowa da gud'a, su kuwa su Mami, al'adar Gombe
ta tafi da su matuka don abin ya burgesu musamman ganin ba kure kamar yanda Abubakar ya
koyawa Faruk haka din ya yi shima.
Daga haka Amina ta mik'amata bandir na dari-dari, nan ta shiga lik'amishi itama, abin ya burge
matuk'a, bayan ta kammala suma danginta suka dan yi nasu lik'in sannan aka dau hotuna
wannan karon Ango Faruk babu wani batun iyayi na rashin son hoto har yayyunsa na zolayarsa
yana dariya, daga nan kuma aka tashi taro....!
((Ku yi hakuri da wannan ba chaji ne...))
[2/5, 6:52 AM] +234 703 962 5239: DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

116

Ikram zaune ta yi shiru yayinda yan uwanta ke faman danne-dannensu a waya, babu kunya
Jidda da Fadila harma Baraka na aikin sanya hoton Amarya da Ango a dp, harma da aikawa
group na zuri'a Baraka ta yi. Intisar na kwance saman katifa tana shan iskar fanka ga tulelan
cikinta wata shida tana kallonsu da sauraron hirarsu tana dariya jin Aisha na fadin.
"Um su Yaya Faruk ashe shi yasan me ya hango da ya mak'alewa 'yar aikin Mami." Suka kara
darawa. 
   Hankalin Intisar ya kai ga Ikram, ta zunguri bayanta da kafarta. Ikram ta dubeta, da hannu ta
yi mata alamar tambaya na meke faruwa? 
  Ta yi murmushin yak'e sannan ta girgiza kai a nufinta babu komai. Intisar itama murmushin
kawai ta yi duk da ta fahimci lallai akwai abinda ke damun Ikram din, tun zuwansu ta yi sanyi
kamar wata miskila yanzun. 
  Ita kuwa Ikram ganin haka yasa ta wayancewa ta hanyar mikewa ta dubesu.
  "Bari naga Hajiya Mama."
Daga haka ta mike ta fito tsakar gidan, saidai kai tsaye waje ta fito inda matasa da wasu cikin
matan gidan ke tsaitsaye, wata hira ta ke yi wasu kuwa kawai gaisawa da yan uwa. Ta yi ta
faman wulk'a idanu tana mai fatan ganin Gidado, cikin sa'a ta hangoshi saidai hangen nasa
baiyi mata dadi ba don kuwa tsaye ya ke da Hafsa sai wata mace wacce ta kasance Yaya
awajen Gidadon suna hira da dariya, ta kasa dauke idanu daga kan Gidado wanda ayau shigar
fararen kaya ya yi ya dora bak'ar hula akansa. Babu zato ya kallo gefenta, murmushi ne saman
fuskarsa, murmushi ta sakarmishi ba tare da ta san lokacin da ya su6uto mata ba sannan ta yi
saurin kauda kai ta juya ta koma ciki. Ya soma fahimto wani abun a irin kallon da Ikram ke yi
mishi, ya sha kamata tana satar kallonsa daga sun hada ido sai ta kauda kanta, a farko ya
dauka kuskuren fahimta ne saidai zuwa yanzun ya soma saka alamar tambaya ga hakan. Ya
basar da tarin tambayoyin da ke yawo a kwanyarsa ya cigaba da maganar da sukeyi akan 
zuwan Hafsa Abuja inda ya ce babu inda zata je ita kuwa ta kawomishi abokiyar shawararsa
kuma yayarsa Sumayya akan ta lalla6ashi saidai firr ya k'i aminta acewarsa ta ji da karamin
cikinta tunda tana fama da laulayi, dole ta hakura don daman karambani ya kaita matsawa
kanta akan zuwan saninta da Gidado, shi din kaifi daya ne. 
    Misalin takwas da rabi na dare Ummi ta samu waya daga Mijinta akan ta fito yana kofar gida.
Ta nunamishi akan ya yi hakuri akwai mutane ya nuna baisan zance ba. 
"Na baki mintuna biyar karki wuce Malama, gani kofar gida. Mutanen ai sun san mijinki ne."
Ta ajiye wayar a sanyaye ganin ya katse ba tare da ya ko saurareta ba.  Dada ta dubeta, don ta
shigo wajen Dada daukar chajar wayarta.
"Idan kiranki ya ke karki k'i zuwa Boddo, mijinki ne."
  Daga haka Dada ta fice, a kunyace ta mike rike da chajar ta fito, saida ta wuce wajen Amina ta
bata har wayar sannan ta yafa mayafi akan doguwar rigar jallabiya da ta sanya don bacci daga
haka ta fita tana ra6e-ra6e. Ta ci sa'a mutanen kofar gidan sun ragu sosai, ta hau lek'e-lek'e
saidai ko mai kama da shi bata gani ba, sai hon da ta ji wanda ya sanyata duban motar, jeep
bak'a wuluk sai shek'i ta ke, ba ka ganin na cikinta.
  "Bismillah Amarya, angon na ciki." Cewar Jafar kenan abokin aikin Faruk wanda bata sanshi
ba sai a yau ta soma ganinsa.  Ta gaisheshi tana sunkwui da kai, ya amsa, kafin ta isa ya
budemata kofar baya, ba musu ta shiga ta zauna sannan ta rufe kofar. Sanyin Ac da na
tsadadden turaren Faruk Danzaki shi ya soma bugar gangar jiki da kofofin hancinta.  Ta dan
d'ago ta dubeshi, wannan katon sanye ya ke da riga fara k'al da dogon wando bak'i, ganin sun
hada idanu yasa ta saurin sauke kanta.
  "Ina wuni."
"Bazan amsa ba, keda ki ka so ki k'i fitowa wani wai mutane."
  Ta yi shiru tana wasa da zoben hannunta. Ganin shima bai ce uffan ba yasa ta fadin.
"Ka yi hakuri don Allah."
Ya lumshe ido yana murmushi alokaci guda kuma ya tura yatsunsa na dama cikin sumar
kansa. 
   Ba zato kuma ta ji kansa saman kafafunta yana duban fuskarta, yanayin jikinta ya sauya, ta
na mai jin wani iri tun daga tsakiyar kanta har kafafunta. Bata kuma ankara ba, ya kunna
wayarsa hakan ya taimaka wajen ganin fuskarta sosai, ta runtse idanu zata kauda kai saidai
bata samu damar hakan ba don tuni ya ajiye wayar ya janyo fuskarta zuwa tasa. Nan kuma
lamura suka chanja daga gareshi zuwa gareta. Don kansa ya saketa ya na dubanta, ita kuwa
mayafinta ta sha zata rufe fuskarta yayinda ta ke faman sauke ajiyar zuciya. 
   "Kimin alfarma daya, kinji?"
Ya yi maganar cikin rad'a, a hankali ta daga kwayar idanunta ta dubeshi, idanunsa a rufe sai ta
ganshi kamar mai shafa mai na k'ara hasken fata sakamakon hasken da ta ga ya yi mata. Bai
saurari amsarta ba ya bude idanu cikin nata ta yi saurin wayancewa da kallon kasa. Murmushi
ya yi.
  "Abinda ki kemin a waya shi na ke fatan samu yanzu."
Gabanta ya buga, ta dubeshi kadan ya shagwa6e fuska.
"Please."
"Ka yi.." 
"Ba za ki bar motarnan ba sai kinyi ko kuma na wuce dake Otal."
Ya fada babu alamun wasa, tasan sarai zai iya aikatawa. Ta runtse ido tana ji kamar ta yi me, ta
daure ta kai hannu ta ja wayarsa ta danne hasken da hannunta, da sauri ta aikata abinda ya
umarceta, dariya ya yi gami da mikewa zaune.
  "Matsoraciyata." Ta hau murza idanu da hannu tana murmushi.
   "Na yi masifar kewarki Ummina, ina kara sonki a kowane rana."
   Shiru ta yi tana mai jin wani dadi a kasan ranta. 
  "Inama zan iya bayyanamaka irin son da nake maka Yaya Faruk?"
Ji ta yi ya dora kansa a kafadarta ya sanyata jikinsa da hannu daya.
  "Mezai hana Ummina, please sanarmin, na jima ina son jin kin furta kina sona da bakinki ba
don bansani ba, saidai ina son ji."
   Ta hau rarraba idanu, ya akayi maganar zuci ya fito fili har ya shiga kunnensa? Ta hadiyi
miyau, anya zata iya? 
'Ki ka yi wancan ma bare wannan?' Cewar wani 6angare na zuciyarta. Ta ji ya kara matsar
hannunta.
"Please Ummi, taimaki Faruk dinki kinji? Ji yanda kirjina ke bugu don kaunarki."
Ya kai hannunta saitin kirjinsa, aikuwa bugun ya ke da sauri-sauri. Ya kai bakinsa saitin
kunnenta.
"Zuciyata zata fashe da sonki."
Ta lumshe ido tana jinta kamar a Aljannah, murmushi saman fuskarta ta yi kasa da kanta.
Dakyar ta bude baki ta yi magana.
  "Ina...ina..." Sai kuma ta yi shiru.
"Say it please."
Ya yi maganar da siririyar murya, ta kasa jure sakonnin da ya ke aikamata, ta kara runtse
idanunta.
"Ina sonka."
"Irin wanda na ke miki?" Ya yi tambayar ba cikin nutsuwa ba, ta rasa bakin amsawa, shi dinma
bai saurari amsar ba ya cigaba da jero tambayoyin kamar a dakin jarabawa. Ita dai Um kawai ta
ke binshi da shi, yanda ya ke mata yasa har hawaye ta ji sun zubomata na tausayi da kuma
tsananin kaunar Faruk, ta ji ko k'uda bata kaunar ya shiga tsakaninsu, ta ji ta kara sallama mishi
zuciya da gangar jikinta, ta ji nan duniya babu abin so da kauna gareta sai Faruk. Shi kadai
tallin tal ta ke so ta ke kauna koda kuwa za'a kawomata wanda yafi Faruk komai da komai, ita
sai Umar-Faruk Danzaki, babu gudu babu ja baya....! So kenan...!!!
   K'arar wayar ce ta firgitasu, ya ja tsaki gami da dauka. Jafar ne, ya soma mishi magana akan
dare ya yi haka kuma ga hadari a garin. Dole ya amsa da toh sannan ya ajiye wayar ya kwantar

Please Login or Register in order to submit comment