ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hadamu."
  "Karya ki ke yi uwar kissa." Cewar Fadila. 
  "Ya isa, Intisar me ya hadasu ne?" Cewar Dakta. 
Tiryan-tiryan ta fadi duk yanda aka yi, Faruk ransa ya yi mugun 6aci ya soma magana.
"Ku rike girmanku, ina girmamaku, kada ku janyo abinda zaisa nabar ganin girmanku. Duk
wacce ta kara cin zarafin matata bazan lamunta ba, ko wacece cikinku komin girma da kimarta
da nake gani zan yi watsi da shi wallahi!"
   Jidda da Fadila ba bakin magana, shiru sukayi sai faman harararsa sukeyi amma ba bakin
magana, ko babu komai yana da kwarjini. 
  Haidar ya dubeshi.
"Ka yi hakuri mana. Gaskiya ba ku kyauta ba Maman Ma'aruf,  kune masu laifi ba Ummi ba, sai
ku duba matsayinta a yanzu a Family namu, ku dunga sakaya bakinku."
  Shima Dakta cikin tsananin 6acin rai ya hau zazzagawa matarsa fad'a, Ummi dai ganin mijinta
ya nufi hanyar fita, itama ta yi musu sallama ta bi bayansa. 
   A mota ta sameshi zaune yana jiranta, ta shiga gami da dubansa, idanunsa sun kada bai ko
dubeta ba ya figi motar a guje, ganin Batul yasa ta yin shiru ba don taso ba, duk da haka saida
ta mishi magana.
"Don Allah ka rage gudu."
Ta fada gami da dafa hannunsa dake rike da sitiyari. Ya lumshe idanu yana mai jin zafin abinda
ya faru, ganin ta damu yasa shi sassauta gudu har dai suka isa gida, Batul ta yi shiru tana mai
tausayawa uwar dakinta don kuwa ta ji kadan cikin abinda ya faru.
    Koda suka isa, dakinta ta nufa. Ta cire mayafi kenan ta isa gaban madubi da zummar cire
dan kunne da sark'a ya shigo, ta dubeshi ta madubi suka hada ido.  Murmushi ta sakarmishi a
kokarinta na 6oye damuwarta. Karasowa ya yi da sassarfa ya rungumeta ta baya yana sauke
ajiyar zuciya idanunsa a runtse. 
  "I'm sorry." Ya fada a hankali, ta lumshe idanu, sai lokacin zuciyarta ta raunana, ta ji kamar ta
zubar da hawaye saboda tsananin farinciki na samun miji kamar Faruk mai so da kaunarta. 
   Ta juyo ta dago fuskarsa gami da girgiza kai yayinda hawayen da ta danne suka shatato. 
   "Haba FAR HAS, don Allah ka daina  inajin wani iri wallahi."
Ta rungumeshi tana hawaye yayinda lokaci guda ta ke murmushi mai bayyana hakora na
farinciki. 
  "Ko babu komai wannan kaunar da ka ke yimin ta zarce komai a wurina, ta isa wankemin
dukkan wani 6acin rai dake zuciyata. Wallahi na yafemusu bazan kuma rikesu da hakan ba,
DAN ADAM ajizi ne."
  Ya dago kanta yana murmushi gami da share mata fuska. 
"Shiyasa nake kara sonki Ummina, halayenki sunfi komai burgeni. Na damu ne don nasan koda
ya miki ciwo ba za ki bari na fahimta ba, cin zarafi ne abinda suka yi gareki wanda wallahi Allah
idan suka ce haka za su dunga yi gareki bazan lamunta ba, zan jure komai idan ni ka yiwa
amman banda abinda ya shafi lamuranki. Kema kin sani ko?"
   Tun soma maganarsa ta zubamishi idanu tana murmushi gami da jin tamkar ta hadiyeshi don
so, ya hure mata idanu hakan ya basu dariya.
"Eh mana naga kamar mai shirin hadiyeni, wannan kallo haka?"
Ta bugi kirjinsa tana kukan shagwa6a.
"Kai don Allah."
Ya ja karan hancinta yana dariya kafin ya taimakamata da abinda ta soma kokarin yi.
     
  Su Jidda daidai ga Hajiya saida ta nunamusu rashin dacewar abinda su ka yi, hakuri suka
bawa Hajiyar kasancewa suna ganin girmanta ainun don bata kasance cikin surukai masu
sanya idanu kan abinda ya shafi zamantakewar yaransu ba, ta kama girmanta hakanan bata
daure musu fuska. 
   Bayan wucewar watan azumi aka gabatar da karamar sallah. Ko ranar da suka hadu da sallah
a gidan Hajiya banda gaisuwa babu abinda ya hadasu duk kuwa da cewa basu bita da kallon
banza ba. 
    Nan kuma ta soma shirin zuwa Kano halartar bikin Amina wanda dakyar Faruk ya aminta
ganin tana fama da jikinta itama. Ko su Ikram sun zo zuwa saidai makaranta, itama Baraka na
fama da ciki dan wata biyar babu damar zuwa. Da kansa ya kaita, kai tsaye gidan Mami ta
soma zuwa inda zata yi kwanaki uku sannan ta wuce gidan Hajiya Mama har zuwa gama biki.
Babu tarbar arziki daga Ihsan sai dai ta samu sosai daga Mami da sauran mutan gidan wanda
yanzu suke zaman aminci. 
    Mami sai nan nan ta ke yi da ita, abin ya sanyata farinciki sosai. Ihsan kuwa kallo bata isheta
ba, sai idan ita ta gaisheta ko ta yi mata magana sannan zata tankamata a dakile kamar bata
so. Ga shi kuma daki daya suke kwana, wannan abin na bawa Ihsan haushi don dai ba yanda
ta iya ne.
  Yau Ummi na kwance saman gadon Fahad wanda yanzun ya ke kwana dakin Adnan, tana
tunanin yanda ita ke gyarashi a baya, lokacin sha dayan dare bata jima da gama waya da rabin
ranta ba inda ya ke fadamata tsananin kewarta da ya yi. Ihsan ta shigo dakin daga falo, jin haka
yasa ta yin makwas tamkar mai bacci. Itama duk a zatonta bacci ta ke yi, hakan yasa ta saka
waya a handsfree tana amsawa.  Ita da Abubakar ne wanda rikici ne zalla.
  "Kasan ina sonka shiyasa, kuma kasan bazan iya rabuwa da kaunarka ba amma a yanda na
ke jin labarin irin yanmatanka da tuni na yi watsi da lamuranka."
  Ummi ta yi shiru jin amsar Abubakar wanda ta ke mamakin inda ya bar matarsa a wannan
lokaci.
"Ki kara hakuri da halina, ni nasan ina da son mata, ki yarda kawai wannan kaddar..."
"Kada ka karasa, wannan son zuciyarka ne. Daga waccan yarinyar ta sanka, sai waccan ta dora
hotanka a dp dinta, na soma gajiya Abubakar, kishi na neman fasamin zuciyata."
Kawai sai ta sanya kuka, ya rude yana faman kiran sunanta da magiya kan ta yi hakuri, saidai
ina, tuni ta katse kiran da ta ga bai bar kira ba, kawai sai ta kashe wayar gaba daya. 
Ta jima tana kuka kafin ta kwanta cike da tausayawa rayuwarta, yanzu idan suka yi auren haka
zata dunga fama da shi? 
  Ummi ta ji babu dadi kwarai, tana ganin Abubakar kamar bazai aikata irin haka ba, ashe kusan
jirgi daya ya kwasosu da Kb dan uwan su Faruk, koda bikinsu bata ganshi ba ta ji ance yana
Ghana karo karatu. Ta tausayawa Ihsan ainun, ta dan juya ta dubi gadonta, ta bata baya saidai
ta tabbatar bacci ya kwasheta, juyar da kanta ta yi gami da numfasawa.
'Rayuwa kenan, kowa da kalar jarabtar da Ubangiji zai mishi, Allah Yasa mu dace, amin.' Ta fadi
a zuciyarta kafin ta yi adduoi ta kwanta itama.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  
  127

Kwananta uku gidan Mami har ankon bikin Amina, Mami ce ta bada a dinkamata. Har ta cika
kwanakinta babu wata jituwa tsakaninta da Ihsan duk da ita Ummin bata dauki gaba da ita ba
don duk wayewar gari sai ta gaisheta matsayin yar uwarta musulma, a dakile Ihsan ke
amsawa. 
  Saida Mami ta soma biyawa da ita wajensu Hajja suka gaisa, har Hajja ta matsa akan sai ta
kwana, dole ta barta anan ta yi musu kwana daya daman acewar Mamin, ya dace ta
kwanarmusu, a wannan kwanan saida Hajja ta kara neman afuwar Ummi don shakka babu ta ji
kunya musamman jin cewa Ummin na dauke da juna biyu, tabbas idan Rabo Ya Rantse to duk
kiyayyarka da auren sai an yishi. 
    Ummi ta ji dadi ta nunamata babu komai, sun sha hira kwarai har da dariya da su Modibbo
wanda ke jikinsa ya matsa mishi a yan kwanakin, washegari ta wuce gidan Hajiya Mama.  
  Nan ma ta ga kulawa da tarba mai kyau daga iyalan Hajiya Mama har ita kanta. Su Maryam
kamar su hadiyeta.
  Amina Amarya ta yi kyau ta gyaru tsaf, anan gidan zaayi yinin biki, kwarai Hajiya Mama ta yi
musu kara. Acan gidan Innar Amina, yan uwan babansu ne na Nijar da na Innarsu anan Kano
suka cika gidan. Amina ta sha mamaki jin cewa Malam Balarabe da kaninsa Baffa zasu zo
daurin aurenta, ta hadata da Dada ta waya inda ta bata hakuri gami da nunamata ta so zuwa
saidai bata samu dama ba, Amina ta nuna babu komai. 
    Da dare suna zaune a dakin su Maryam gaba daya suna hira da dariya, wayar Maryam ta yi
k'ara, ta mike da sauri ta fita. 
  "Mene na gudun? Ai munsan mai kiran, Adnan ne."
   Cewar Rukayya cikin daga murya. Amina da Ummi suka dara. Amina ta cafe.
"Kai ke kuma ba'a sirri dake." 
  Dariya Rukayya ta yi.
"Ai naga sai wani 6oye-6oye sukeyi kamar bamusan komai ba, gwara mu nunamusu mun
d'agosu."
  Ummi da mamaki ta ce. "Wai don Allah soyayya su ke yi?"
"Ba ki da labari? Gaskiya Amina kinci amanar kauna da ba ki fesamata ba, ai kullum suna
mak'ale da juna ta waya duk da wani 6oye-6oyen da sukeyi munsan komai, daidai da Hajiya
Mama ta sani."
  Ummi fara'arta ta karu.
"Kai na ji dadi wallahi, Yaya Adnan ya yi dace kam, Maryam ba ruwanta halayenta na burgeni.
Sun dace wallahi."
"Karshe ma." Cewar Rukayya daidai lokacin da Maryam ta shigo ta mikawa Ummi wayar.
"Ga Yaya Adnan ku gaisa."
Ta kar6a tana tsuke baki. Ta yi sallama ya amsa gami da fadin.
"Allah Ya kiyayemana ke ranki ya dad'e."
   Ta hadiye dariyarta.
"Ai ni na yi fushi Yaya Adnan, ka daina nemana kuma ko na kira layinka yanzu ba ya shiga."
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Na ji kunya biyu. Na farko kirana da Yaya Adnan da ki ka yi, na
biyun kuma, kiran da ban yi miki da sabon layina ba kasancewar wancan ya fad'i sai na barshi.
Ki yi hakuri Ranki ya dade matar bestie."
  Sukayi dariya a tare, ta girgiza kai.
"Har abada, Yayana ne kai wallahi. To na hakura, ya fama da biro da takarda?"
  "Gashinan sai kuyita tayamu da addua. Kinga surukarki ko? Ta yi ko akwai gyara?"
Ta daga idanu ta dubi Maryam da su Rukayya ke tsokana ta yi dariya.
"Ta yi 100%."
Ya yi dariya cike da mamakin yanda tasan wani 100% domin ko kusa ba shi da labarin ana
mata darussa. Saidai kuma bazai iya tambayarta ba.
   "Yauwa Ranki ya dade, ai da kince akwai matsala tuni zan dakata."
"Wace ni da fadin haka?"
Suka dara kafin su yi sallama.

  An soma bikin Amina lafiya, ana gobe daurin aure Malam Balarabe suka zo, sun sha hira da
diyarsa har ya rasa inda zai sakata don tsabar farinciki. Ita ta yi musu jagora har wajen Inna don
yi mata fatan alheri, wani abu ya darsu a zukatan tsoffin sadda suka yi arba da juna. Bayan an
daura auren ne Malam Balarabe ya kasa jurewa har saida ya sanarwa Baffa kaninsa don
daman ya samun labarin cewa yanzu Inna bata da aure, hakanan yana iya cewa tun bayan
Hasiya babu wacce ya kara gani ya ji yana so ya karashe rayuwarsa da ita matsayin mata
kamar Inna Bilkisu. Baffa ya ji dadi kwarai kuma zai so hakan. Abinka da batun manya nan suka
tuntu6i babban Yayan Bilkisu, Mahmuda, nan ya nunamusu jin dadinsa a fili don kwarai ba ya
son zaman kanwartasa haka babu aure duk da cewa ta aurar da yara biyu Fiddausi da Hauwa,
sai Amina ta uku, ga kuma autanta Ahmad mai shekaru goma sha daya a yanzu, ya yi musu
alk'awarin tuntu6ar Inna Bilkisu. A karshe sukayi musayar lambobin waya sannan a karshe
sukayi sallama da kowa suka tafi, Ummi har hawaye ta yi don kewa, shi kuwa babanta dadin
yanayin da ya ganta ya ji don ta yi k'iba ta kara kyau. 
   Inna ta ji lamarin banbarakwai duk kuwa da cewa a ganin farko da ta yiwa Malam Balarabe ya
kwantamata, ba musu ta amince da hakan. Nan ya kira ya shaidamusu, basu yi wata wata ba
suka sanarwa iyayensu, Malam ya ji dadi haka ma Dada wacce ke tausayawa dan nata. Aka
tsaida magana nan da sati biyu za'a je a daura aure. 
  Su Anti Hauwa sun ji abin banbarakwai, wai Innarsu aure. Tun basu ji ko waye mijin ba suka
nuna rashin goyon bayansu, acewarsu da shekarunta na arba'in da takwas me ya ragemata
banda ibada? A bakin matar Kawunnasu suka ji waye manemin auren, hankalinsu ya kwanta
suka ji dadi, kusan Amina ta fisu jin dadin lamarin don a take ta bugawa Ummi wacce ke shirin
komawa Abuja.
    "Albishirinki." Ummi ta ware ido.
"Goro fari k'al Antina."
  "Inna zata zama matar Babanmu."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Anti inace kin cemin Baba ya rasu."
Ta ja tsaki.
"Dallah can, babanmu fa na Gombe."
Daskarewa ta yi a tsaye ta bar ninke kayan. Ita abin kamar mafarki haka ta jishi. 
"Ke ya ki ka yi shiru, wallahi dagaske ne." Tiryan-tiryan ta labartamata abinda ta ji. Hawaye
kawai Ummi ta shiga fitarwa tana kara jin kaunar Amina da yan uwanta. Banda hamdala babu
abinda ta dunga nanatawa a fili. 
   Bayan komawarta Abuja ta sanarwa Faruk wanda shima ya ji dadi ainun, ya sanyawa lamarin
albarka. Kowa ya ji sai ya sanya albarka ciki. Koda ta kira mahaifinta, dariya kawai ya yi ya ce.
"Lamarin Allah kenan Hasiya, a tayamu addua."
Farinciki fal cikin ranta haka suka sha hira suka yi sallama.
                ***    ***    ***
        BAYAN WATANNI BIYAR
Ayau ake bikin yaye su Ikram daga sakandire, acan Kano ma su Ihsan na nasu shagalin don
lokaci guda aka yi bikin yayesu. 
   Duk yayyun Ikram sun je mata banda Baraka dake wankan jego ta haifi danta namiji wanda
ya ci sunan mahaifin Mijinta suke kiransa da Abulkhair. Ummi ma da cikinta dan wata bakwai
katon gaske haka ta zo. Fuskarta duk ta chanja, tana sanye da wata tsadaddiyar abaya Faruk
na rike da hannunta. 
    Ikram duk bata tare da walwala sai lek'e-lek'en wuya ta ke faman yi. 
"Wai me ki ke nema haka?" Cewar Fadila wacce ta kasa shiru. Ikram ta dubeta, kafin ta yi
magana suka ji sallama a gefensu duk suka waiga, mamaki karara ya bayyana a fuskokinsu. 
  Yana sanye da doguwar riga da wando na shadda dark green wacce ta sha aiki, ya dora hula
mai fari da koren din sak'a, ya yi kyau kuma ta haskakashi ainun. Sai murmushi ya ke faman
dokawa.
  "Yaya Gidado?" Ummi ta furta da tsantsar mamaki kafin kuma ta saki fara'a sosai. 
Ya bita da murmushi kafin ya karasa ya soma mikawa Mazajen Hajiya Babba hannu suna
gaisawa. Suma sun saki fuskokinsu, Fadila da Jidda suka yi turus suna kallon ikon Allah, sun
kuwa gane waye shi amman idan ka ganshi saika rantse ba daga kauyen Jar Kwami ya fito ba
tsabar iya daukar wanka. 
  Ikram ta kasa rufe baki, zuciyarta na kara nutsawa cikin kogin so da kaunarsa, babban abinda
yasa ta ke kwadayi da mafarkin zuwan wannan ranar kenan don kuwa ya bata tabbacin zai zo
mata da kyakkyawan albishir duk ranar da ta yi Candy. Toh yau ga ranar ta zo. 
    "Ashe kana tafe ba ka sanarmana ba mu yi maka kyakkawan tarba?"
  Cewar Faruk cikin sakin fuska. Gidado ya danyi dariya.
"A yi hakuri surukina, ai gani yanzu ma bata 6aci ba."
  "Lallai kam, saidai kamar zuwan ba namu bane na kanwarmu ne ko?." Cewar Haidar wanda
ya riga yasan dawan garin daga Intisar., ya fada yana duban Ikram.
   Suka yi dariya, kunya ta kama Ikram.
"Eh to, kusan hakan."
  Cewar Gidado, shi kuwa babban Yaya da Ridwan mamaki sukayi don basu zata ba , hakanan
Faruk shi kansa bai ji daga matarsa ba. Ya dan matse hannunta ta yi karamin kara. 
  "Shine ko ki gayamin?"
Ta waro ido.
"Babu wani abu fa tsakaninsu."
Murmushi kawai ya yi.
  Har aka tashi taron Gidado bai samu ke6ewa da Ikram ba sai bayan sun koma gida, bayan ya
gaisa da su Hajiya suka ke6e da ita a dakin bak'i. 
Ya fiddo wani akwati daga aljihunsa ya mik'amata.
"Ga kyautar da na zo miki da ita, ki yi hakuri babu yawa.". Ta kar6a tana washe baki.
"A wajenka ne babu yawa."
Sukayi dariya. 
  "Ba za ki bini bashin zance ba Ikram, yau zan sanarmiki abinda ban ta6a sanarmiki ba. Haka
kuma zan cika alkawarin da na daukar miki."
  Ta lumshe idanu ta budesu.
"Ina jinka Yayana."
  Shiru ya dan biyo baya kafin ya cigaba da magana.
"Karambanin so ke neman kaini inda aka fi karfina, duk iya kokarin da na yi na dannewa da
kaucewa faruwar hakan, saidai ya gagara, bazan iya hana Allah zartar da hukuncinSa, ban isa
ba ban kuma kai ba. Wallahi na kamu da sonki Ikram, so na gaskiya, a rayuwa ban ta6a zaton
zan kara son wata diya nace ba bayan Hafsa, amma cikin ikon Allah da sannu-sannu
kyawawan d'abi'unki da kuma hakurinki suka rinjayi zuciyata na afka cikin kogin son wacce ta fi
karfin dan kauyen Jar Kwami."
  Ta kasa motsi, ta kasa gaskatawa, ta kuma kasa tantance hakikanin yanayin da zuciyarta ta
fada. Kallonsa kawai ta ke tamkar wata doluwa. Ya kai yatsa kamar zai tsone idonnata ta yi
saurin lumshewa, sai kuma ta yi kasa da kai tana murmushi. 
  "Wannan kallon fa ya tsoratani, ko ba'a sona?" Ya fada don jin ta bakinta kawai bawai don
baisan cewar tana sonsa ba. 
   "Bance ba, saidai na yi mamaki ne kawai ace kamar ka kana sona?"
  "Kina neman ki ce kinfi karfina ko?"
Ya fada a raunane. Ta yi saurin girgiza kai kamar mai shirin kuka ta ce.
"Wallahi aa, ni don Allah ka daina bambanta kanka da ni, kaima cikakken DAN ADAM ne mai
daraja, ina girmamaka hakanan ina sonka tsakani da Allah."
    Ya murmusa gami da sunkuyowa saitin fuskarta cikin muryar rada.
  "Za ki iya zaman aure da ni a Jar Kwami?"
   Ta lumshe idanu gabanta na bugu da sauri-sauri.
  "Yayana ba Jar Kwami ba, koda cikin daji ka ke rayuwa wallahi zan iya binka muyi zaman
aure, ina sonka fa." Ta karashe kamar za ta yi kuka, ai kuwa hawayen da ta ke makalewa suka
kwaranyo.
   "Komai na Allah ne." Ta tuna furucin Ummi gareta a watarana da ta je gidanta da korafin
yanda ta ke kara jin son Gidado a ranta kamar ta mutu. 
   "Idan Allah Ya kaddaro mijinki ne, za ku yi aure." Fadin Intisar a watarana suna hira ta ke
kokawa bisa yanda Gidado kan share kwanaki ba ya nemanta koda ta waya sai idan ta
nemeshi.

  "Na gaji da jin maganar Gidadon nan, don Allah ki hakura ki fiddashi cikin ranki, idan mijinki ne
fa sai kunyi aurennan ko ba ya so." Cewar Hajiya a wataran da ta risketa tana kukan yanda ya
ke yawan yi mata hirar matarsa wanda batasani ba wani zubin da gayya ya ke yi don kawai ya
gwada ko tana kishinsa.

  Ta share hawayenta. Gidado zaune ya cigaba da fayyacemata irin son da ya ke mata ya kuma
tabbatarmata ba da wasa ya zo ba, sonta ya ke yi tsakaninsa da Allah. Koda ta yi mishi batun
Hafsa, ya nunamata wannan ba matsala bace, matarsa nada saukin kai tana son abinda ya ke
so. 
Ranar saida ta yi nafilfilu don nuna godiyarta ga Ubangiji. Daidai da Hajiya ta taya diyarta murna
hakanan duk wani masoyinta da yasan tana son Gidado, ko Ihsan ma ta dan ji sanyi ganewar
ba yar uwarta kadai ke wahala ba, ashe shima yana so. 
  "Allah Ya ba ki sa'a." Shine kawai abinda Jidda ta fadi. 
   Ita kuwa bata biyemusu ba don ta gane yan adawa ne. 
           
   Kamar wasa, aka tsayar da maganar auren Ikram da Gidado wanda takanas iyayensa suka
zo Abuja nema mishi bayan an samu an shawo kan Hafsa dakyar wacce ta dage akan saita bar
gidan Gidado ta ya ya zai hadata kishi da wayayyiya kamar Ikram? Acewarta wannan cutarwa
ce, da dai ya auri Ikram gwara ya auromata yar kauyen Jar Kwami irinta sun zauna. 
   Wasu cikin yan uwa suka goyi bayanta wasu kuwa ba su goya ba, hakanan a cikin dangin
Gen. Ahmad Danzaki, wasu da yawa basu amince ba, acewarsu Ikram ba zata iya rayuwa a
kauye ba da kuma dan kauye, ita kuwa ta dage lallai sai Gidado, to Daddy shima ya goyamaya
baya ko babu komai autarsa ce yana ji da ita. Haka aka tsaida auren Ikram da Gidado wata uku
ba da son ran wasu ba. 
     Aka shiga shirye-shiryen bikin Abubakar da Ihsan, sai Iklima da Musaddik, mijin da Abba ya
za6ar mata akayi sa'a sun hada kansu, da kuma kanwarsu Hassana da Abdullatif. 
   Biki ya yi biki, dukkan yan uwa sun iso Kano, ciki harda KB wanda ya zo hutu daga Ghana,
gaba daya ya chanja ya zamo na kirki kamar ba shi ba. Ummi ce ta samu dakyar Faruk ya
amince da zuwanta, acewarsa cikinta ya tsufa babu yawo....!
    Ansha shagalin biki su Abida da sauran yan uwan Gombe na Jar Kwami duk sun hallara. Sai
nan nan Hajiya Salma ke yi da Ummi, hakanan duk motsi da zata yi sai an tambayi ko akwai
wata matsala. 
   Tana zaune ta sanya kayan ankon Party a gaba tana kumbure-kumburen fuska, Ikram ta
dubeta.
"Allah Sarki Antina, yanzu shikenan ba za ki je ba?"
  Dariya su ka sanya gaba daya wanda ya kara k'ular da ita. 
  "Tana gani zamu wuce amma ba inda za ta je tunda Oga ya hana."
Cewar Baraka kenan. 
"Ke banda abinki, kina fama da wannan katon ciki haihuwar yau ko gobe ina ke ina wani dinner
party?"
  Ta yi narai-narai da fuska.
"Nasan da wanda zan hadashi ai, bari na kira Yayana."
Sukayi dariya, ta kira Abubakar.
"Innota ya akayi na ji muryarki na rawa?"
  Daman kiris ta ke jira kawai ta soma kuka. 
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun, me akayi? Kinga kina ina yanzu?"
"Dakin Ihsan."
"Ok ina zuwa."
Ya katse kiran Faruk dake zaune gefensa a benci ya dubeshi.
"Me ya samu Innontaka?"
"Bari na je na gani."
Ya bi bayansa da kallo kafin ya ta6e baki don yasan zancen bai wuce na party ba.
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

128

Suna daga dakin suka ji falon ya dauka ga Ango ga Ango, da mamaki Baraka ta ce.
"Eh lallai yar gatan yayanta, kiga har ya shigo."
   Ihsan wacce bata jima da shigowa dakin ba batasan me akeyi ba, sai ganin Abubakar ta yi ya
shigo. Tana zaune saidai ban ma lura da ita ba ya yi wajen kanwarsa. Itama tana ganinsa ta
kara turo baki tana murmurza idanuwa. 
  "Ya Salam, meyafaru ne wai kanwata? Hankalina ya tashi wallahi."
  Ganin yanda duk ya rude yasa ta dan sassauta fuskarta, fuska ba walwala ta ce.
  "Ba shine ya ce wai bazan je dinner party ba."
  Ya dan runtse ido gami da numfasawa, hankalinsa ya dan kwanta.
  "Inji wa? Ai ya zama dole ku je don kafarki kafata. Barni da shi, kedai ki tabbatar kin shirya kinji
ko?"
  "Yanzu bayanta za ka goya? Da wannan tulelan cikin ina ita ina wata dinner?" Cewar Rahila
yayar Ihsan.
  Ya dan harareta don sun saba wasa da dariya.
  "Ina ruwanki to? Zuwa kuma ai ta yishi ta gama, atoh."
  Dariya sukayi banda Ihsan da ta k'ulu ganin kamar baisan da ita wajen ba.
  "Idan kaine mijinta ma ji ma gani." Ta kara fadi cikin dariya. 
  "Shima a tafin hannuna ya ke, surukai muke."
  Daga haka ya fice suna mishi tsiya. Ihsan jikinta ya yi sanyi, wane irin Ango ne mai fifita wata
akan matarsa? Haushi ya cika zuciyarta saidai dole ta danne ta mike bisa umarnin Aisha wacce
ta shigo kiranta zuwa kwalliya don Magriba

Please Login or Register in order to submit comment