You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
don yanda gaba daya suka fita hayyacinsu, ya 6oyemasa komai sai
abinda Abba ya yi mishi a yau kawai ya sanarmishi.
Faruk bai ji dadi ba sam, ya sauke ajiyar zuciya, baiyi zaton Abba zaiyi haka din ba koda a
mafarki. Ya dubi Adnan cikin muryarsa sassanya yace "Mami tasan ka taho?"
"No, na barmata takarda dai."
Faruk ya girgiza kai gami da daukar waya ya dannamata kira.
Mami na zaune saman darduma, idar da sallar magriba da gabatar da nafilarta kenan ko
mik'ewa batayi ba ta ji wayarta na k'ara. Ta janyo da sauri, Faruk ta gani ta numfasa, daman tun
dazun take jiran kira daga wani na Abujan don jin ko Adnan ya isa batason tayarmusu da
hankali.
Bayan sun gaisa yake sanarmata da isowar Adnan. Farin ciki ya lullu6e zuciyarta. Fuska a
sake ta yi hamdala a fili, ta cigaba da magana.
"Don Allah Faruk kada ka barshi cikin damuwa, kayi iyakar kokarin ganin ya samu walwala.
Nima ina nan zuwa nan da kwana uku da zarar yarannan sunyi hutu."
Ya murmusa cikin ransa yana mai tausayinsu, ya gama fahimtar akwai wasu al'amura dake
faruwa tare da su duk da suna 6oyewa.
"Karki damu Mami, in sha Allah zan yi yanda kikace."
Ta yi murna da jin hakan har ta sauke ajiyar zuciyar da hatta Faruk saida ya ji.
"Nagode d'ana, Allah Ya k'ara muku albarka."
"Amin."
Ya mik'awa Adnan. Adnan murya a raunane yace. "Maminaa."
Mami ta lumshe ido hawayenta sukq zubo ta bud'e tana murmushin k'arfin hali.
"Na'am d'an Maminsa, ka gujemu ko?"
Adnan ya yi shiru baice komai ba sai huci yake.
"Karka damu, Allah Yana tare da mu. Kayi kokarin 6oyemin sirrin gida, idan ma ka gayamishi
wani abu, to don Allah karka k'ara daga abinda ka fad'a. Kayi kokarin sakin jikinka kada
tambaya ta yi maka yawa."
Adnan ya gyada kai. Haka sukayi sallama bayan tace ya gaishemata da Hajiya Babba.
Faruk ya dubeshi da murmushi.
"To ya? Domino's Pizza ko kuma Jabi Lake Mall?"
Adnan ya dubeshi sukayi dariya, ya kanne mishi ido.
"Kaima kasan inda nafi kauri."
Faruk ma dariyar ya yi kafin ya tashi motar ya harba titi. Bai zarce ko'ina ba sai da suka samu
masallaci sukayi sallah sannan suka karasa ya siyamusu Pizza da ice cream sukayi gida. A
hanya Hajiya Babba ta kira Faruk a waya jin ya dad'e, ya tabbatar mata suna tafe da Adnan
shima yazo. Ta ji dadi kwarai don Adnan yaro ne dan shafta, yanzun sai ya k'ullar da cikinta,
sam baya mata bak'unta.
Saida suka isa dakin Faruk, Adnan ya yi wanka shima Faruk ya yi suka chanja kaya daga nan
suka nufi cikin gidan. Hajiya na falon tare da Ikram da Baraka suna hira. Ganin Adnan yasa
yaran soma ihun murna. Shima a take ya ji ya mance da komai ya washe hakora. Ya karasa ya
gaida Hajiya har tana mishi fadan dalilin da bai zarto gidan ba ya soma zuwa ga Faruk. Ya daga
ledojin hannunsa yana dariya.
"Saboda wannan ne."
Sukayi dariya gaba daya.
"An kammala karatu kuma sai tafiya ko?"
Ya dan yi murmushi bai ce uffan ba.
"Ai nima ji nake kamar na bishi wallahi."
Cewar Baraka. Ya harareta.
"Ki barwa mijinnaki wa?"
Ta yi dariya. Nan suka shiga hira, Hajiya ta tambayi dalilin ramarsa ya sanarmata ya danyi
rashin lafiya ne. Tare suka ci suka sha kayan makulashen sannan Faruk da Adnan suka shiga
wajen Daddy suka gaisheshi ya tambayi yaushe ya iso ya ke sanarmishi daga karshe suka
koma sashen Faruk.
Faruk kwance saman gado yana danne-dannen waya, yayinda Adnan ke sarrafa Laptop din
Faruk yana duba shafin sada zumuntarsa na Facebook, hankalinsa ya kai ga zanen da Faruk
ya yi a jikin sketch board. Ya k'urawa hoton ido yana son tuno inda yasan yarinyar. Zaro ido ya
yi gami da ajiye Laptop din da sauri ya nufi wajen. Wannan ya ja hankalin Faruk ga dubansa,
gabansa ya fad'i. Shaf ya mance bai cire takardar zanen daga jiki ba. Ya kauda kai sa'ilin da
Adnan ya dubeshi.
"My best, wannan ta yimin kama da Ummi sosai. Ya akayi ka zanata?"
Faruk ya daure ya k'ak'alo murmushin yak'e.
"Hobby na kenan, kasan zane babu inda baya zuwa, haka kawai na tsinci kaina da zanata."
Adnan ya yi shiru, zarginsa yana bashi kamar akwai wani abu game da Ummin a zuciyar
Faruk. Ya numfasa, idan ta yi wari watakil shine wanda zai soma ji. A fili kuwa murmusawa ya
yi.
"Wallahi ta yi kyau, kamar wacce aka dauka a hoto. Gaskiya Allah Ya baka."
Faruk ya share maganar ta hanyar jefomishi tambaya.
"Wace k'asa ka za6i zuwa ne?"
Adnan ya baro wajen zanen ya dawo, ransa ya sosu don ya tuno abin haushi. Ya dan daga
kafada.
"Bar wannan zancen my best, ni nafasa anan zanyi."
Faruk ya lura da wani abu, kawai sai ya share.
*** *** ***
KADUNA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
41
KADUNA
Dija gaba daya ta sauya, daga mai surutu da zafi zuwa marar son hayaniya da kuma sanyi.
Komai takeyi muddin Deen zai shigo, to fa zata mance komai ta shagaltu a kallon dukkan wani
motsinsa. Tun Deen bai lura ba har dai ya soma tsarguwa da yawan bibiyarsa da takeyi da
kallo.
A yau juma'a, Munira batanan ta wuce gidan wata aminiyarta da ta haihu, saida ta dauko
yaranta daga makaranta suka wuce tare, gidan babu kowa sai Dija wacce ganin Denn a gida
yasa fir ta k'i binsu ta fake da ciwon jiki. Misalin karfe uku da mintuna, Deen yana kwance a
falonsa yana duban talabijin, ya ji sallamar Dija. Da mamaki ya dubi hanyar falon, yana mai
amsawa. Ganin da ya yi mata cikin shigar mutunci marar mishkila sosai yasa ya dan ji nutsuwa
a ransa. Ya mike zaune yana murmushin yak'e.
"A'a Dija, k'araso mana." Ta dubeshi ta sauke ajiyar zuciya, komai nashi burgeta yakeyi. Ita
kuwa ko zata mutu sai ta sace zuciyarsa, shekarunta sun kai munzalin da ya dace ace tana
gidan miji ba yawon gidajen yan uwa ba. Itama fa mutum ce ba dutse ba, tana da sha'awa, koda
dai takan biyewa k'awarta wacce waya ta hadasu, mai yawan yi mata hudubar banza akan ta
amince ta je Kano su had'u don d'ebewa juna kewa, ta k'i yarda amman takan ta6a hirar banza
da ita a waya(Wa'iyazubillah).
Ta samu wuri ta durkusa gami da gaisheshi. Ya amsa batare da ya kalleta ba yana mai
wayancewa da chanja tasha.
"Ashe sai kai kad'ai, ga abinci can an jera tun dazu."
Ya dan dara.
"Eh yanzu zan taso na ci."
Ta narkar da fuska.
"Haba Deen, don Allah ka zo muje, ni kaina sai yanzu zan ci. Na riga na saba da ci da ku ana yi
ana hira, yanzu da basunan bazan ji dadi ba."
Ya jefeta da wani irin kallo har saida ta ji gabanta ya fad'i, tsoro ya cikata, sai kuma ya
numfasa gami da maida dubansa ga talabijin.
"Jeki ina zuwa."
Ya bata amsa a gajarce ta mike jiki babu kwari ta fita. Har ta cire ran zai zo sai kuma gashinan,
wani sanyi ta ji a ranta ta mike zata zubamishi. Ya dakatar da ita.
"No barshi, zan yi da kaina."
Ta girgiza kai.
"Ban ta6a ganin kunyi haka da Munira ba, nima bazan bari ka zuba da kanka ba kada nayi laifi
awajenta."
Jin haka ya kauda kai, ta zuba tana murmushi ta tura gabansa sannan ta zauna saitinsa tana
cin nata. Idanunta a kansa, da zarar ta ga zai kallota sai ta yi sauri dauke idanun.
A ransa ya ji yana mai jin haushinta, da ace yar uwarsa ce da tuni ya korata gidansu, saidai ba
yanda ya iya, baya son ran Munira ya 6aci ya lura sosai take kaunar Dija hakanan tana
tausayinta wai adalilin har yau bata samu mashinshini ba.
Ya rigata mik'ewa ya bar wajen, ta bishi da zazzafan kallo gami da k'ara cin alwashin ba fa
zata barshi ba sai ta cika burinta na aurensa. Babu wacce ta fad'omata a rai sai Baba Habiba,
ta tabbatar ita daya ce zata iya yi mata kokarin shawo kan Deen ko ta wane hali. Idan ma da
hali ya saki Munira ya aureta. (Kun ji butulcin DAN ADAM)
*** *** ***
Bikin Baraka ya iso, komai na shirye-shiryen Mami, ita da kanta ta yi bata saurari Abba ba
balle ta tambayi wani abu a aljihunsa har ya samu damar cin zarafinta. Ta yiwa Ihsan anko,
hakan ta siyawa Fahad shadda tare da Adnan aka dinka musu. Ummi kuwa ta yi mamaki da
Mamin ta bata kudi suka je da Amina bayan isarsu gidan Hajiya Mama ta siyo 'yar kanti da
kuma wani abin idan tana so. Ta yi murna matuka duk da tasan ba da ita zasu je ba.
Hajiya Mama ta jajantawa yar uwarta kwarai na abinda ke faruwa da ita. Ta kuma yi mata fada
sosai akan dalilinta na rashin sanar da ita tun wuri. A karshe tace zata sanya ayi rokon Allah,
suma kuma ba kwanciya zasuyi ba, su dage sosai da addua da sadaka har Allah Ya kawo
makarin koma menene.
Bayan Amina da Ummi sun dawo daga shago suka biya gidan Innar Aminar. Mace mai
mutunci kwarai, ta yi murna da ganin Ummin da duk sadda Amina ta zo saitq bata labarinta.
Sun jima anan sannan suka lek'a gidan Anti Hauwa yayar Amina daga nan suka kamo hanyar
gida. A hanyar ne ma Ummi ke labartawa Amina yanda suka ta6a yi da Hajiya Binta. Amina
sosai ta tsorata, hankalinta ya dan kwanta jin Ummi bata bi turbar shaidan ba ta aikata. Ta k'ara
fahimtar da ita lallai mai yiwuwa yanzun ma da sa hannunsu cikin lamarin Abba da Mami. A
karshe ta kara shawartarta akan ta dage da addu'a akan Allah Ya kareta daga sharrinsu.
Ashe kuwa dai sharrin na tafe, domin a daren da suka koma gida daga gidan Hajiya Mama,
Abba ya kira Mami ya ke fadamata ta gaggauta korar Ummi daga gidansa don labari ya iso
mishi cewar tana biye-biyen maza tana fakewa da zuwa makaranta. Acewarsa, yaransa basu
jawomasa abin kunya ba, to babu 'yar wata can da zata janyomasa. Mami ranta ya 6aci, cike da
mugun 6acin rai ta dubeshi.
"Wannan kuma ba halin Ummi bane, da ace Ummi na yi kasan kafin ka gane ka koreta, da tuni
na yi hakan don bana zama da maci amana. To Ummi babu inda zata je, zamanta daram a
gidan nan!"
Ta yi maganar cikin daga murya har kirjinta na bugu da sauri-sauri saboda tsananin 6acin rai,
ba wai don kwatarwa Ummi yanci kadai bane, aa, har ma da gajiyawa da jin zafin yanda ya ke
bayar da ita gaban kishiyoyinta, don a wannan karon ma har hadasu ya yi gaba daya a falon
yana mata korafi akan Ummin. Abin ya soma isarta.
A fusace ya ce. "Sai mu gani idan gidan ke kika ginashi Madina! Amma wallahi kinji rantsuwa
ta musulunci babu yar iskar da zata zauna a gidana, saidai ko ki bita."
Hankalin Mami ya tashi, su kansu matan sun razana da furucin Abba, Anti Amarya wacce bil
hakki ta tausayawa Mamin, ta saka baki.
"Haba Alhaji, ya kake..."
"Kiyimin shiru Malama, bansaka dake ba, daman na taraku ne don na gargadeku da ku jawa
yan aikinku kunne, banaso and iskancin banza da wofi. Ke kuma ki tattara taki ki maida inda
kika amso ta, bazan lamunci iskanci ba."
Takaici ya sa Mami jan tsaki batare da tasan sadda ya fito ba.
"Sai kayi, na gayamaka babu inda Ummi zata je, sa'arka d'aya zan je Abuja da na soma
gwadamaka gaskiyar abinda nake fad'a tun yanzun. Naga ai wasu ma nasu cikin suka ta6a yo
wa aka zubar aka cigaba da zama da su a gidan."
Hajiya Binta ta fahimci da yar aikinta Sa'ade take wacce ta ta6a yo ciki suka zubarmata. Ta
fusata ta yi kwafa batace uffan ba.
Kafin Abba yace wani abu, Mami ta zura silifas dinta ta fice cikin kunar rai.
"Ummi! Ummi!!"
Ummi dake daki ta ji Mami na kwalamata kira cikin daga murya. Ta fito a kidime ta russuna.
"Naam."
Ta tamke fuska.
"Ki shirya kayanki, dake zan tafi."
Ummi gabanta ya fadi don bata ta6a zato ba, ta mike ta wuce bayan ta amsa da toh kawai.
Shigarta da mintuna biyar Fahad yazo ya kara kiranta wai inji Mami. Ta mike ta isa gareta a
can daki. Mamin na zaune gefen gado ta yi jugum tana tunani, bayan Ummi ta durkusa ta
dubeta fuska daure.
"Ki gayamin tsakani da Allah akqn dukkan abinda zan tambayeki Ummi."
Ummi a tsorace ta ce. "Toh."
Mami ta zubamata ido, ita tasan sharri aka yiwa Ummi, saidai dole ne ta tambayeta don amana
ce ita a hannunta.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
42
"Dagaske ne kina...."
Sai kuma ta yi shiru, haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyin maganar, ta daure ta karasa.
"Labari ya iso ga Abba na kina bibiyar maza, ki gayamin gaskiya Ummi."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
Abinda Ummi ta furta kenan a fili kafin wani kuka ya tahomata, kuka sosai harda sheshshek'a.
Mami na kallonta bata katseta ba, bata ta6a jin tausayin Ummi ba aduk zaman da suke sai a
yau, k'azafi abu ne mai matukar cin rai, tasan yanda Ummi ke ji irinsa Adnan ya ji a sadda aka
mishi sharrin sata, hakanan itama irinsa ta ji alokacin. Maganar Ummi ta katse tunaninta.
"Wallahil Azim ban aikata abinda ake zargina akai ba Mami, ban ta6a koda tsayuwa na saurari
wani d'a namiji ballantana har ya kai da ta6a jikina ba, ki yarda da ni wallahi Allah ban aikata
komai ba. Na shiga uku."
Ta k'ara fashewa da wani kuka wanda ke k'arawa Mami jin wani mugun tausayinta. Ta numfasa
muryarta a sanyaye.
"Ya isa, nasan ba ki aikata ba daman, kawai don kiyaye amanar da aka ban naki ne yasa ni
tambayar. Na riga nasan kazafi ne na mahassada amma babu komai wataran sai labari. Kiyi
hakuri, kina iya tafiya ki soma shiri, dole dake zamu wuce."
Ummi ta mik'e ta fita, a hanya suka ci karo da Ihsan ta bita da kallon mamaki ganin ta fito daga
dakin mahaifiyarsu kuma tana kuka, da sauri ta karasa dakin don duba Mami. Sai ta tarar ta yi
shiru ta zuba tagumi. Ta karasa gareta. "Mami lafiya? Naga fitar Ummi daga nan ta na kuka."
Mami ta murmusa.
"Bakomai, kin gama shirye kayanki?"
Fuskarta cike da damuwa ta amsa da eh. Bata kaunar ganin Maminsu a wannan yanayin,
Allah-Allah takeyi su bar garin su shiga cikin yan uwansu ko zuciyarsu zata sanyaya. Ta kasa
hakuri saida ta k'ara tambayar Mamin dalilin da yasa Ummi ke kuka. Haka dai ta sanarmata don
ta k'i jinin 6acin ran yarannata. Ihsan duk da tana k'in Ummin itama ta ji babu dadi musamman
jin cewa a gaban kishiyoyin Maminnata Abba ya gasawa Mamin magana. Ta yi kwafa.
"Ai Allah Ya fisu, munanan mugun abinsu zai juye kansu."
Mami ta jinjina kai. Tabbas ayanzun ta soma zarginsu duk da zato zunubi, tana yi musu kallon
munafukai masu fuska biyu.
Ummi ji ta yi duniya ta mata zafi sosai, ta riga tasan makircin Umma ne, ita kadai ce matar da
ta ci alwashi akan lalata rayuwarta, ta barta da Allah domin bata da karfin yin fad'a da ita, koda
tana da shi, bata jin zata iya ramuwar gayya. Allah zai mata sakayya, saukinta ma Mami bata
gaskata hakan ba.
*** *** ***
Ta dubi 'yarta tana mai zaro ido.
"Me kike nufi ne? To wallahi babu inda zakije. Na rabaki da wannan shegen yaron ba kiji, idan
ba kiyi a sannu ba zan mugun sa6amaki."
Iklima ta turo baki ta mike daga saman kujera.
"Wai don Allah inace ni zan zauna da shi? To ni gaskiya ina sonshi kada ki yi yunkurin rabani da
shi. Kuma meye idan naje Abujan? Baraka fa k'awata ce, ana bikinta don kawai wani kishi naki
kice..."
Bugun le66anta da ta yi ne yasa ta yin shirun dole tana sosawa don zafi.
A fusace Umma ke magana.
"Kinyi kadan! Wallahi iklima kinyi kadan, ban haifi 'yar da zata fi k'arfina ba nan duniya. Biki ne
kuma babu inda za ki taka kije, mu zuba ko ni ko ke a gidannan."
Daga haka Umma ta nufi dakinta a fusace kasancewar ranar ba aikinta bane. Kai tsaye layin
bokonsu ta nema ta sanarmishi akan tana so ya raba zuciyar 'yarta da soyayyar Faruk. Ya
sanarmata abu ne mai sauki amman sai ta zo ta amshi wasu magunguna. Ranta ya yi sanyi ta
bishi da godiya gami da tabbatar mishi da zuwanta a goben da kuma kudin aikinsa. Daga haka
suka rabu.
Washegari Iklima tana ji tana gani su Mami nata shiryen-shiryen tafiya. Rahila da Aisha suma
nan suka zo, dan Aisha, Tahir ya yi wayo sosai. Rahila da yaranta biyu itama, Bintu da Samir
wanda shine karami yana da wayo sosai, cikin ikon Allah bai mance fuskar Ummi ba, hakanan
ya yarda ya je hannunta. Ko kusa Ummi bata da matsala da Rahila da Aisha, babu ruwansa,
sannan basu fiye zuwa gidan ba face da babban dalili. Wannan ne dalilin da yasa basu san
wainar da ake toyawa ba, a wannan zuwannasu ne ma ta tsincesu a dakin Ihsan tana faman
labartamusu komai harda tafiyar Adnan Abuja. Aisha da mamaki tace "Haba, shiyasa kwana
biyu banga keyarsa a gidana ba, ashe baya garin. Bakomai, komai zai wuce."
Abinda ta tsinkaya kenan ta dauki kayan Fahad da Mami ta aiko ta dauka ta fice daga dakin.
Nan su kuma sukayita jajantawa har saida Mami ta gaji ta soma fadan zata tafi ta barsu
sannan suka fito.
Kai tsaye gidan kakansu suka nufa wato Alhaji Atiku Modibbo inda anan zasu hadu har Hajiya
Mama da iyalanta su wuce Abujan. Tafiyar har da Innarsu. Suka yi sallama suka bar dan tsoho
daga shi sai yan aiki da wani dan uwansa na Adamawa suka kama hanya. Ummi na rike da
Samir a gefen Antinta Amina suna shan hira, kowa a Bus din abinda ya shafeshi yakeyi, Mami
kuwa su uku ne a mazauninsu, ita da Hajiya Mama da Innarsu sai hira sukeyi. Nan ma Ummin
ke labartawa Amina kazafin da akayimata, Amina abin ya yi mata ciwo saidai fadan da yafi
karfinka...
Har dai suka isa kowa da abinda yasa gaba kafin a karshe a gaji ayi shiru.
Amina da Ummi wadanda basu ta6a takowa Abuja ba, suka saki baki suna kalle-kalle. Har
suka isa gidan Gen. Ahmad Danzaki inda anan kallo ya koma sabo dal. Suka saki baki suna
k'arewa haduwar gidan kallo. Wannan ko a Turai ne sai hakan.
"Aljannar Duniya." Abinda Amina ta fada kenan cikin rada yanda Ummi kadai ce zata ji. Sukayi
'yar dariya.
"Bari Anti, basu da matsala a fannin kudi."
Amina ta jinjina kai. "Tabbas."
Direban ya hau hon, maigadin da sauri ya budemusu kofa yana washe baki gami da dago
hannu yana musu lale marhabin.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
43
Yana daga samansa yana dubansu da murmushi, ya karasa ga Adnan wanda bayan karin
safe ya yi wanka ya cigaba da bacci ya kai mishi duka.
"Tashi kaga wani abu." Adnan ya mike da sauri yana dubansa ido waje.
"Sun iso?"
Faruk na murmushi ya ja hannunsa zuwa barandar. Ihu ya saki wandq har saida su Mami da
suka riga suka fito suka kallo shi, dariya suka sanya. Da gudu ya fira ya sauka garesu. Shima
Faruk ba shi da za6in da ya wuce na bin bayansa.
Adnan ya kama hannun Maminsa tamkar ya rungumeta don murna.
Baraka da Ikram a guje suma suka fito har Hajiya Babba wacce ta kasa hakurin k'arasowar
yan uwannata ciki. Ta rungume Innarta, su Amina da Ummi suka zagaya domin kwasar kaya.
Tana janye da katuwar jaka, idanunta ya sauka akan Faruk, yana gefe ya hard'e hannuwansa
yana zabga murmushinsa mai burgewa. Sanye ya ke cikin kananun kaya, riga bak'a anyi rubutu
da farin abu, wandonsa ma bak'in ne, ya yi kyau har ya gaji da had'uwa. Cikin sa'a idanunsa ya
kai kanta sa'ilin tuni sauran sun kama hanyar cikin gidan. Murmushi ya sakarmata, itama ta
tsinci kanta da mayarmasa da martani har(dimple) dinta na dama na bayyana. Ya ji wani abu
da bai ta6a ji ba na tsirgashi, ya kauda kansa gami da soma tafiya zuwa ciki. Tana jan akwatin
tamkar bata so sanadin kallonsa da take yi, namiji mai aji kenan, ina ita ina shi? Ta sauke ajiyar
zuciya ta dubi gefenta jin alamun mutum. Amina ce itama rik'e da katuwar jakar Hajiya Mama
tana dubanta cikin nazari, sai kuma bayan sun hada ido ta sakarmata murmushin yak'e.
"Muje mana naga bakya daga kafa ne."
Ummi ta gyada kai ta k'ara sauri. Amina mamaki kwarai takeyi na irin kallo da murmushin da ta
ga Faruk na jifan Ummi da shi, da kuma kallon da Ummi ke bin bayan Faruk din da shi har ya
illata tafiyarta. Ta numfasa, 'Idan ma akwai wani abun ya zama dole nasa ido na gano, bazan
bari Ummi ta jefa kanta cikin matsala babba ba, ina mata kallon kanwata kamar ta jini.' Ta
ayyana a ranta. Da taimakon yan aikin Hajiya Babba aka shishshigar da kayan gaba daya ciki.
Tsarin gidan Hajiya Babba wane sauran gidajen yan uwanta, iyakar haduwa ya had'u. Kayan
duk ansaka a inda ya dace, Ummi da Amina daki guda aka hadasu wanda duk na yan aiki ne,
yana daga can bayan(garden) din gidan.
Hira ta k'i ci ta k'i cinyewa tsakanin yan uwan, dakyar sukayi wanka suka chanja kaya sannan
aka gabatar da sallar la'asar akayi zaman cin abinci. Alokacin kuma Haidar da Intisar suka
shigo. Da gudu suka rungume juna ita da Ihsan sannan ta koma ga iyayen kowanne ta hau
rungumarsa don dadi.
"Wai ke bakya girma ne?" Cewar Hajiya Mama kenan alokacin da ta rungumota.
"Kema dai kya fad'a Sadiya, yau kam dole kiban mijina tunda na iso." Cewar Inna kenan.
"Ahaf, mai zuwa gidanmu sai ya shirya fa." Fadin Haidar kenan, akayi dariya gaba daya. Su
Faruk na daga falo suna jiyo caftarsu, shima Haidar bayan gama gaisuwa ya komo wajensu ana
hira. Faruk kusan hankalinsa ya kasu biyu, hakanan ya ji yana d'okin ganin daga inda Ummi
zata 6ullo, fatansa ya k'ara cin karo da kyakkyawar fuskarta. Da zarar ya soma tunaninta, sai ya
yu saurin kwa6ar zuciyarsa, aganinsa babu wani dalili da ya ke da shi da zai dunga tunanin
wata can. Abu ne da tun da ya ke a rayuwa bai ta6a faruwa gareshi ba.
Ita kuwa baiwar Allah, suna can tare da Amina suna cin abinci, saida suka kammala suka kai
komai kicin. Alokacin ta fita wanka, bayan dawowarta itama Amina ta tafi wanko jikinta.
Doyuwar riga ta sanya na kanti marar nauyi na yawon gida, itama Amina doguwar rigar ce
jallabiya. Ummi ta dubeta taba daga rigingine saman katifa
"Anti ashe duk tsaruwar gidajen su Mami bai kama rabin k'afar na Hajiya Babba ba?"
Amina ta murmusa yayinda ta zauna gefenta.
"Haduwa ma ba daya ba kedai, na ji ance fa har wajen wanka akwai(swimming pool)."
Ummi ta zaro ido.
"Haba?"
"Wallahi a bakin su Anti Intisar na ta6a ji, ba don ma kada muyi laifi ba da mun zagaya gidan."
Ummi ta amsa.
"Wallahi kam, zanso ganin wajen wankan kuwa."
Haka sukayita hirarrakinsu, Amina na son yi mata magana akan abinda ke gudana tsakaninta
da Faruk, tana kuma tsoron kada ya kasance zarginta ne kawai,
Book Chapters
Chapter 11
Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500