ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


  Tana hawaye ta danna ta kara a kunnenta, ji takeyi inama kada ta d'aga, ita kam ta shiga
tara...!

   
  "Assalamu alaikum." Ta fad'a cikin rarrauniyar muryarta wanda sautin kuka ya ta6a.
  Faruk dake tsaye a barandar dake a sama wajen dakinsa yana duban  farfajiyar gidannasu, ya
numfasa jin muryarta.
  "Waalaikumussalam, Ummi kina lafiya?"
  "Umm, ina wuni Yaya Faruk." Ta fad'a gami da kai gwuiwoyinta k'asa kamar yana ganinta. 
   Murmushi ya yi lura da ya yi na cewar ta tsorata da shi.
"Lafiya lau."

"Wai Ummi dodo na zame miki? Gaisuwa kad'ai na buk'ata fa..."
Sai kuma ya yi shiru kafin ya d'ora maganarsa.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

   32
Ranar juma'a da misalin karfe bakwai, gaba daya yaran Hajiya Babba sun had'u suna hira
kamar dai yanda suka saba, duk juma'a anan suke wuni matuk'ar ba wani aikin ne ya tasowa
dayansu ba ko duka. Wannan lokacin ma Faruk baya tare da su, a haka ya dawo daga aiki ya
samesu suna ta zuba hira suna dariya ga kayan marmari agabansu a babban faranti an
yayyanka suna sha.
    Yana sanye cikin riga kalar sararin samaniya, ya d'ora kwat dinsa bak'i akan hannunsa na
dama, d'ayan hannun kuwa (briefcase) ne, gaba d'aya fuskarsa ta tona gajiyarsa. Suka amsa
sallamar da ya yi ciki-ciki. Cikin dariya Ridwan ya dubeshi.
   "Kaga manyan ma'aikatan banki."
  Gaba daya suka dara, shi kuwa gogan sai ya k'ara marairaice fuska ya karaso ciki ya zube a
saman kujera gami da fad'in.
"Wash!"
  Haidar ya birkita sumarsa.
"Sannu lil, haka muke fama."
Faruk ya murmusa.
"Kai, anya kana aikin da mukeyi?"
Cewar Likita (Ridwan) kenan. 
  Usman ya cafe.
"Mu da ke wuni a shago sai mu ce me?"
  Nan da nan kuma sai hira ta koma musu tamkar wasu abokai kowanne yana k'ok'arin nunawa
sauran zafin aikinsa musamman  Babban Yaya da Likita wanda idan da sabo sun saba. Ikram
na goyon bayan likita ayayinda Baraka ke bayan Barista Haidar kasancewar itama fannin da ta
ke son karanta kenan. 
     Faruk dai sulalewa ya yi zuwa dakinsa don watsa ruwa. 
   Bai fito ba saida ya yi wankansa tsaf ya sanya riga t-shirt bak'a da farin wando wanda da
kadan ya wuce gwuiwa, kasancewarsa farin mutum, ba karamin kyau da haske ya yi ba, ya jona
wayoyinsa a chaji ya fito.
    Alokacin sun nufi masallaci, shima ya bi bayansu.
  Tare suka shigo gaba daya har Daddy dinsu. Bayan an kammala cin abinci ne, kowanne
Daddy ya tambaya ko da wani matsalar. Duk suka tabbatar mishi babu, Babban Yaya ke
sanarmishi zai je Kano ganin wani babban dan kasuwa da ya buk'aci ya shigo mishi da kaya
suyi lissafi.  Daddy ya gyada kai.
  "Allah Ya bada sa'a." Suka amsa da amin. Faruk wani abu ya tuno hakan yasa ya dubeshi.
   "Ko nayi maka rakiya?"
  Babban Yaya ya washe baki.
"Wallahi da ka kyauta, daman banson bin hanya ni d'aya babu abokin hira."
  "Toh kai baka da wani uzurin ne goben?" Cewar Daddy yana duban Faruk. Faruk ya daga
kafada kadan yana girgiza kai.
  "Babu."
  "Ai kuwa da kun biyamin gidan Alhaji Labaran, akwai saurin auren 'dansa ran lahadi, bazan
samu zuwa ba. Kuje a madadina."
  Sukayi na'am har Haidar na fadin ba don yana da abin sabgogi ba a goben da ya bisu.
  Faruk ba murmushi ya karkata wuya zuwa saitin kunnen Haidar.
  "Kaidai fad'i gaskiya, Intee ce zata hanaka zuwa."
  Haidar ya dubeshi ya harara da wasa, hakan ya bawa Faruk dariya, ya saki murmushi mai
bayyana hak'ora.

   Basu jima ba anan, duk matasan suka mik'e. Haidar saida ya tsaya a falon Faruk sukayi
kallon ball kafin ya wuce gidansa bayan waya da Intisar ta dameshi da shi. 
   Faruk haka kawai yakejin nishad'i game da zuwansu Kano. Yana matukar kaunar k'ara
sanyata a idanu.

                   ***   ***   ***
   Washegari kuwa misalin tara suka bar Abuja da Babban Yaya, koda suka isa saida sukayi 
La'asar a gidan kakansu Modibbo suka ci abinci sannan Babban Yaya ya k'arasa ga abinda ya
kawoshi, shi kuwa Faruk waya ya yiwa Adnan ya sanarmasa yana Kano, ba jimawa kuwa sai ga
Adnan suka fice yawo. Idan ka gansu kamar abokai don babu laifi shima Adnan ba dai tsawon
k'afa ba. 
    Saida suka gama zagayansu sannan suka nufi gidansu Adnan domin ya gaisa da Mami.

      Ummi na zaune a inda ta saba, wato can hanyar kicin tana kallon tashar cartoon wanda
Fahad ya sanya, ko kadan kallon ba dadi ya ke mata ba, asalima ba ba fahimtar komai take ba,
wannan dalilin ne yasa ta mik'e gami da nufar hanyar d'akinta. Ya yi daidai da sallamarsu.
Adnan na gaba, yana biye da shi. Ta amsa tana dubansu. Yana sanye da riga T-shirt ja da
dogon wando bak'i. Shima idanunsa cikin nata, ta tsinci kirjinta da bugawa da sauri-sauri. Da
sauri ta zube tana gaisheshi cikin rawar murya. Ya sauke ajiyar zuciya kafin kuma ya amsa.
Daga haka ya bi bayan Adnan, ta mik'e jiki a sanyaye ta karasa dakinta da sauri. Juyowa ta yi a
sadda ta kai kofar shiga, suka had'a ido sa'ilin da yake cire takalmi shima din ita ya waigo.
Alokaci guda suka janye idanunsu bayan da suka ji wani sauyin yanayi na daban a jinin jikinsu.
Ta yi wuf ta fad'a d'aki, tana jin ihun Fahad yana ambaton sunansa. 
   Ihun ne ya janyo hankalin Ihsan da Mami wadanda suke dakin daga cikin falon Mami suna
magana akan dinkin da za'a yiwa Mamin na ankon bikin Baraka. Da sauri Ihsan ta fito, ganin
Faruk ta hau dariya, cikin daga murya tace. "Mami dagaske ya ke, Yaya Faruk ne."
  Jin haka yasa Faruk suka k'arasa ciki, daga lokacin kunnuwanta suka daina jiyo sautikansu.
  Ta zauna a kasan kafet tana mai jingina kanta jikin bango. Haka kawai ta tsinci kanta da
murmusawa. Wani sanyi ya doki zuciyarta. Ta tabbatarwa kanta akwai wani abu a ranta game
da Faruk, tafi danganta abin da kauna ta don Allah irin wacce ta ke yiwa Antinta Amina, haka
kawai Faruk ke burgeta. 
   'Kodai kina sonshi?' Gabanta ya fadi jin tambayar da ya darsu a zuciyarta. Ta zaro ido kamar
wani na ganinta.
  'Ina ni ina Yaya Faruk? Ai ko zan so wani na gwammace ya kasance cikib samari masu
takuramin a hanyar makaranta da dai son abinda bazan ta6a samu ba.'
  Ta ayyana a ranta, tunaninta ya katse sa'ilin da ta ji Fahad ya kwalamata kira.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

    31
  "Ok, daman naji ance ke kika d 'aga waya ne, shiyasa na buk'aci k'anina da ya ba ki mu gaisa.
Fatan komai lafiya?"
  Ta ja ajiyar zuciya wanda ya jishi har cikin ransa, ya tsinci kansa da lumshe idanu.
  "Lafiya lau, ya su Hajiya? Agaishesu don Allah."
  Ta burgeshi, hakan da ta yi ya nuna tana da hankali. Murmushi ya yi mai ban mamaki wanda
da wani cikin yan uwansa zai ganshi da ya zargi koda wata budurwarsa ya ke wayar.
  "Zasu ji, thank you."
"Um."
Shiru ya biyo baya ta cire wayar a kunnenta ta ajiye gefe gami da zuba tagumi.
  "Na shiga uku, meya kaini d'aga wayar Yaya Adnan tun farko? Yanzu wace masifar zan
jawowa kaina?"
Tayi maganar a fili wanda tsaf ya shiga kunnen Faruk kasancewar bai riga ya katse kiran ba, sai
lokacin ya kashe ya sake kira. Har razana ta yi gami da ja baya. Ido waje ta duba ta ga shine
har lokacin, ta d'aga ta kara a kunnenta.
  "Ba..bari na mik'aaa mishi, ya fita."
  Ya girgiza kai tamkar tana ganinsa alokacin da ya koma d'aki ya zauna saman kujera.
  "No, ke nake nema ai. So nake nasan masifar da na jawo miki?"
  Muryarta na rawa yayinda hawayenta suka zubo ta girgiza kai.
"Wal..walla..."
"Ki zama jaruma a komai na rayuwa Ummi, matsoraci bai zama gwani. Duk abinda zakiyi a
rayuwa kiyishi da zuciya d'aya, ki zauna da kowa zaman gaskiya. Komai da zakiyi kiyi don Allah
ba don wani halitta ba ok?"

Ta gyada kai gami da numfasawa, sosai nasihar ya shigeta, haka kawai ta tsinci kanta da jin
wani sanyi a zuciyarta.
  "Nagode Yaya Faruk."
  Ya yi murmushi mai sauti kafin ya amsa.
  "Mu'assalam."
Daga haka ya katse wayar, batayi gangancin k'ara wani tad'in a fili ba sai a ranta. Gaba daya
batasan cewar kiran bai katse ba. Lamarin ganinsa takeyi tamkar a mafarki, wai itace ke waya
da Yaya Faruk? Ikon Allah! Yau kuma meke a kansa? 
  Haka tayi lamo a saman katifa cike da fargaba, sallamar Adnan ta sanya ta mikewa zaune
tana mishi murmushi na yak'e. Fuska a sake ya kar6i wayarsa da take mik'o mishi gami da
fadin.
  "Har an gaisa? Wai daman kun ta6a gaisawa da shi?"
  Ta gyada kai.
"Eh, shi ya taimaka ya kawoni gida ran fatin Yaya Haidar ai."
  Ya dan daga kai alamar tunani kafin kuma ya dan daga gira.
  "Oh, na tuna anyi haka fa. Kinsan Yayannawa ba dai kirki ba."
  Murmushin dai ta k'ara yi sannan ya juya ya fice.  Ta zauna ta yi tsuru cike da tunanin wannan
lamari. A karshe dai da ta ga babu wani abu da ta tsinkayo ta share batun.
           
                    ***  ***  ***
   'Me nayi?' Ya jefawa zuciyarsa tambayar da baisan amsarta ba. Ya jingina kansa jikin kujera
gami da k'urawa talabijin ido. Babu abinda ya yi banda sada zumunci. 
   'Kar ka d'arsawa zuciyarka wani abin daban, kana tausayinta ne kawai.'
  Cewar wani sashe na zuciyarsa. Ya kauda maganar gaba d'aya ta hanyar kunna talabijin.

                     ***  ***  ***
  Sallamar da aka doka ne ya katse hirar da Habiba ke kwasa da mijinta. Ganin mai sallamar
yasa duk suka washe baki, mijinta Yahuza ya mik'e.
  "Kai lale da mutan Kaduna."
  Fad'in Habiba kenan tana kokarin gyara tabarma. 
    Bayan sun zauna aka shiga gaisawa, Habiba ta zari gyale ta fita siyo ruwa. 
   Hajiya Munira kenan, 'yar kanwar Yahuza mijin Habiba, wacce ke auran babban ma'aikacin
gwamnati a Kaduna. Ta zauna suka soma gaisawa da kawunta yana tambayar sadda ta iso. 
  "Kwanana biyu kenan ai Kawu."
  Ya jinjina kai kafin su cigaba da hira a haka har Habiba ta dawo dauke da leda mai ruwan
sanyi da lemu tana fad'in.
  "Um, kaga fa tsabar zumud'i ko kudi ban dauka ba, bari yarinyarnan su zo su mik'a mishi."
    Suka dara sannan aka hau hira. A haka Dija ta dawo ta samesu. Ta ji dadin ganin Munira,
suka shiga hira harma a karshe Munira ta nuna tana gayyatarta Kaduna koda na sati ne. Babu
musu Dija ta nuna zata. 
   Kawu Yahuza da Habiba sunyi murna kwarai, ko ba komai sa dan huta da surutun mutane na
cewar anbar yarinya ba aure sai gantali. Man aka tsaida idan Munira zata wuce, tare zasu tafi.
       Koda ta gama kwanakinta a kauyen, suka shirya tare da Dija da yaranta biyu, direbanta ya
kwashesu zuwa Kaduna.

                   ***  ***  ***
                       ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  33

A kofar dakin sukayi kici6us, ya  sanarmata wai ta zo ta k'aro faranti su Yaya Faruk zasu ci
abinci. Ta amsa da to, a sanyaye ta gyara daurin dankwalin atamfarta sannan ta bi bayansa. A
zaune ta gansu a saman tebur gaba daya, ta dauke kanta ganin shi dinma gogan idanunsa
akanta suke, kicin din ta fad'a ta bi umarnin Mami. Ta dauraye ta goge sannan ta karasa garesu
cikin sassanyar tafiyarta, sam bata da kwaramniya...

     Ta kawo falon, tana kokarin ajiye suka had'a ido da ihsan ta samu tsarabar harara kuwa. Ta
ajiye a gaban Faruk, wani daddad'an kamshi na turare ya bugi hancinta.
  "Thank you."

 Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi bayanta da kallo kafin ya numfasa muryar Ihsan ta doki
kunnuwansa.
"Let me serve you."
  Ya dubeta ya dan murmusa gami da gyada kai, cikin siririyar muryarsa ya amsa.
  "Kar ki cika, ban tare da yunwa."
  
Suna ci suna hira, jefi-jefi yakan dubi hanyar da ta bi, Mami ke faman jan shi da hira yana bata
amsa. Ihsan gaba d'aya ta gama tafiya a kallonsa, sai yanzu take tabbatar da hakikanin
gaskiyar abinda take ji game da yayannata. 
   
  Ummi a d'aki zaune ta yi zugum tana tunani. A karshe ta d'aga rigarta ta shinshina gami da
lumshe ido. Ita kam tana son kamshi a rayuwarta don dai babu yanda zatayi ne ta samu.
Musamman wannan turaren da ta ji awajen Faruk, sai ta ji ya doke duk wadanda ta saba shak'a
wajen masu gidan. 
   'Komai na Yaya Faruk ba irin na kowa bane, komai nasa daban. Ya ji dad'in rayuwa.' Cewar
wani sashe na zuciyarta. 
   'Kada ki kai kanki inda Allah bai kaiki ba Hasiya, babban goro fa sai magogin karfe, a komai
na rayuwa Faruk ya d'ara ki, babu gatan da Allah bai ba shi ba. Yafi karfinki nesa ba kusa ba.'
  Wannan tunanin yasa ta numfasawa, wani hawaye ya taho mata wanda bata iya hanashi
kwaranyowa ba, shikenan su yan aiki basu da gata? 
  A daren dakyar ta iya kokawa da zuciyarta har ta samu ta runtsa domin kuwa bata k'ara fita
falon ba, asalima batasan sadda Faruk ya bar gidan ba, ta dai ji maganar Ihsan na fad'in 
Babban Yaya wanda ya nuna shima yazo daga baya.

     Tunanin duniya ya ishi Ihsan, ta gama tabbatarwa lallai tana kaunar Yaya Faruk, a wannan
daren yini ta yi kallon hotonsa wani dad'add'e da sukayi da Adnan da Haidar. Karshe dai ta
kirashi a waya, bayan sun gaisa ya nemi sanin wace don bil hakki ba shi da lambarta. 
  "Ihsan ce." 
  Ya yamutsa fuska cike da mamaki sa'ilin da yake goge fuskarsa da tawul daga shi sai gajeran
wando ya fito wanka.
  "Oh, kanwar Adnan?"
Ta ji haushin kanta, wato ko lambarta babu a wayarsa? Da tasan da haka da bata bayar da kai
wajen kiransa ba. Kamar zata yi kuka ta amsa da eh.
  "Ok, fatan lafiya?"
Ta daure ta had'iye 6acin ranta.
"Daman na kira na ji ya kuka isa gida?"
  Ya dan saki fuska.
"Alhamdulillah. Nagode."
  "You are welcome."
Ya dan murmusa gami da jinjina kai.
"Good night.". Daga haka ya ajiye wayar batare da ya katse kiran ba ya cigaba da abinda yake
yi. Babban Yaya na gefen gado zaune yana tura sak'o email a laptop dinsa.
  Takaici da bakin ciki suka tararwa Ihsan, ta katse kiran don kanta. Duk da ta ji haushinsa,
hakan baisa ta ji zuciyarta ta bar magagin kaunarsa ba. Inama zai aureta? Ta ayyana a ranta,
wani tsalle tayi a saman gadonta gami da kwakwume filo tana murmushi, a haka har bacci ya
soma fisgarta ta yi addu'a ta kwanta.

                    
    Faruk yana kwance, ya zurfafa cikin tunani, a gefe yana dan tsintar hirar Babban Yaya da
matarsa tamkar wasu sababbin aure, ya lumshe ido yana mai fatan bacci ya yi awon gaba da
shi ko don ya daina ganin abinda ya ke gani a kwayar idanunsa, hakanan yabar jin sautin
muryar da ta k'i gushewa a dodon kunnensa ba don komai ba sai don tsoron kada tunaninsa ya
tabbatar da hakan, bayaso yanayin ya sauya zuwa ga abinda ya ke tsananin gudu. 
  Haka bacci ya sureshi cike da tunani da mafarkai masu dadi da ban mamaki.
   Washegari da wuri suka tashi, bayan sun kammala shiri suka dunguma zuwa daurin auren da
Daddy ya turasu, sosai kuwa Alhaji Labaran ya ji dadin zuwansu, a karshe sukayi sallama suka
nufi gidan Hajiya Mama. Basu jima ba suka wuce don a ranar zasu juya zuwa Abuja. 
   Suna komawa gida kuwa suka tattara suka bar garin Kano...!

       [truncated by WhatsApp]
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

35
                  KADUNA
  Mutan Kaduna sun isa lafiya lau, Dija cikin garin ya zamemata bak'o don bata ta6a zuwa ko'ina
ba banda Katsina kauyen k'urfi inda nan ne asalin mahaifinta Yahuza. Ta yi mamakin ganin
k'erarren gidan da Munira ke rayuwa cikinsa a unguwar Malali, ta sauke ajiyar zuciya har ta
kasa 6oye mamakinta ta fito da shi fili.
  "Gidanki mai kyau."
Munira ta murmusa.
"Nagode 'yar uwa."
  
  Bayan shigarsu ciki ne ta gane wajen ba komai bane, domin sakin baki tayi tana karewa falon
kallo wanda ya yi bala'in had'uwa. Zata iya cewa tunda take bata ta6a zuwa gida makamancin
wannan ba. Haka Munira ta rakata har dakin bak'i a sannan ta koma ga yaranta Tasleem da
Haris. 
  Ita dai Dija k'arewa komai kallo takeyi, tsaf, kamar ansan da zuwanta. Gado ne sai aka
shimfida kafet a k'asa, a gefe sif ne maidaidaici na kaya, sai bandaki. Ina zata samu wannan a
kauyensu kuma gidansu? Tunda dai akwai masu ginin zamanin, amma bata ta6a kwana ba.
Tayi tsalle saman gado don dadi saikace wata 'yar shekara goma. 
    Munira ta dawo ta ajiyemata sabulu da soso a bandaki, ta umarceta da tayi wanka. Bayan ta
kammala ta shirya tsaf sannan ta fito suka ci abinci saman tebur abin sai ya yiwa Dija
banbarakwai, hatta yaran and saida sukayi mata dariyar yanda ta dunga nuna kauyenci saman
tebur. A karshe suka tashi sukayi magriba mai aiki ta kwashe komai. 
Suna zaune a falon ita da yaran suna kallo, Munira kuwa na kicin tana shiryawa maigidanta
abinci, suka ji sallamar maigidan.
    Gaba daya yaran suka mike suna ihun murna, hakan yasa Dina kallonsa. Sakin baki ta yi
yayinda gabanta ya hau dukan tara-tara, haka mijin Munira ya had'u?
     
   Sanye yake cikin farar shadda, bak'i ne kuma dogo, yana da kyau babu laifi. 
  Ya rungume yaransa yana mai farincikin ganinsu, zuwan Munira da sauri ne yasa shi
bud'emata hannu ta karaso ta shiga ya hadasu ya rungume gami da lumshe ido, a hankali ya
yiwa matarsa rad'a ta dubeshi tana murmushi ta sakarmishi hararar wasa shima ya kashemata
ido yana murmushin.
   "Sannu da zuwa."
Maganar Dija ta maidosu hayyacinsu, sukayi saurin sakin juna, ita kuwa tuni ta tafi a kaunar
mijin Munira. Munira ta matsa da sauri shi kuwa ya dake ya amsa yana mai tambayarta
mutanen kauye.
  "Duk suna lafiya, sunce a gaisheku."
  Ya amsa fuska a sake sannan ya maida hankalinsa ga Tasleem da Haris.
  "To, a jira nayi wanka na fiddo muku tsaraba ko?"
  Suka hau tsalle da ihun murna. Ya jinjina kai.
"Kuma ku nemomin tsarabar da ku ka kawomin idan ba haka ba nima zan fasa baku."
  Nan ya yi gaba yana dariya Munira da Dija na tayashi. Yaran kuwa kansu ya dauki chaji don
basu yowa babannasu tsarabar komai ba. Haka sukayita tunani lokacin har Munira ta bi bayan
mijinta, hakan yasa suka koma ga Dija don ta nemomusu mafita.
   Munira na shiga mijinta Deen (Zahraddeen) ya d'agata cak yana juyi da ita gami da fadin.
  "Oyoyo sweetna." Sukayi dariya, dakyar ta zame daga rik'on da ya yi mata ta dan daki kirjinsa.
Cikin muryar shagwa6a tace. "Kaidai wallahi ba ka rabo da abin dariya."
Ya k'ara janyota yana murmushi da nok'e kai.
  "Eh mana, musamman ma idan agaban sweetna nake."
  Tayi dariya ta kwace jikinta gami da fad'awa bandaki don had'amishi ruwan wanka.
   Acan kuwa Dija ta kasa sukuni, hankalinta gaba daya baya wajen Tasleem da Haris masu
tambayarta tsarabar da zasu bawa babansu. Mik'ewa ta yi.
  "Kuje kicin ku nemi wani abun da mamanku ta kawo.".  Da gudu suka wuce, dakinta ta koma ta
zauna tana tunani, tunda take bata ta6a susucewa akan kowane d'a namiji ba kamar wannan,
ta yi murmushi gami da k'udurta mugun abu a ranta.

                    ***  ***  ***
     Da sallama ta shiga turakar mijinta, ya amsa yana mai dubanta fuska a sake, ta ci ado har ta
gaji sai kamshi ke tashi ajikinta. Ya yi ta dubanta itama idanunta akansa ta karaso ta zauna.
  "Barka da..." Maganarta ta katse ganin irin razanar da Alhajinnata ya yi gami da mik'ewa yana
mai saurin toshe hanci. A tsorace Mami ke dubansa da mamaki.
  "Lafiya Abban Adnan?"
  Ya girgiza kai.
"Wane irin turare ne kika fesa haka Madina?"
  Mami ta dubi jikinta kafin ta dubeshi cikin rashin fahimta. 
  "Bangane ba?"
Ya kauda kai gami da k'ara ja baya.
  "Don Allah ki shinshina jikinki, wallahi turaren naki sam babu dadin shak'a, ki tashi don Allah ki
je kiyi wanka kinji?". Ya karashe da muryar rarrashi da kwantar da kai. 
   Mami ta jinjina kai ranta na soyuwa, ba don Muhammad bane ayau da ta gasa mishi magana,
saidai girma da darajarsa a idanunta yafi gaban haka, ga kuma soyayya tsantsa a gefe.
    Mik'ewa ta yi bayan shigewarsa daki da sauri da sauri, ta fice ta koma zuwa sashenta. 
    
   Ummi dake zaune su kadai a falon ita da Fahad suna kallon (Harry porter) sai ji sukayi ana
kwankwasawa, Ummi ta bude, kallo daya ta yiwa Mamin ta fahimci akwai damuwa shimfide
saman fuskarta, itama Mamin zubamata ido ta yi domin ta ga ko zata nuna wata alama na cewa
ta ji wari ajikinta, sai ma ta ga duk hakan bata kasance ba. Wannan yasa ta sauke ajiyar zuciya
ta giftata, ga mamakin Ummi, Mami har waiwayenta ta yi, ko me take son hangowa? Oho.
   Fahad ya mike zaune.
"Lah Mami, ya kika dawo?"
Ta yi yak'e. "Mantuwa nayi ne."
  Daga haka ta shige zuwa dakinta da sauri-sauri. 
  Suka cigaba da kallonsu, can kuma da jimawa, har Fahad bacci ya daukeshi saman kujera,
Ummi kuwa na jiran Mami ta fita ta k'ulle k'ofar, sai ga Mamin ta fito tana zuba wani tsadaddan
k'amshi na ban mamaki. Ummi dai tun kafin Mamin ta karasa fitowa kamshin ya ratsa kofofin
hancinta. Tana mamaki kodai Mami 6arin turaren ta yi. Ta fito sanye cikin doguwar rigar abaya
wanda daga k'asa kayan bacci ne,ta dora hijabi saman doguwar rigar. 
   "A'a, bacci ya yi?"
Ummi ta amsa a ladabce.
"Eh."
Ta jinjina kai fuskarta na nuna alamun bata so hakan ba. Ta dubi Ummi jiki a sanyaye.
"Ki kaishi makwancinsa."
  "Toh." 
  "Saida safe."
"Allah Ya tashemu lafiya." Cewar Ummi tana kokarin cika umarnint. 
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

34
  Ya gama buge-bugensa akan k'asa kafin ya yi wata arniyar dariya ya dubesu.
  "Shakka babu kun hadu da yarinya mai basira da har ta yi muku dabara batare da ta shiga
matsalarku ba."
  Hajiya Binta ta dubi kawarta Luba sannan suka maida hankalinsu ga bokansu.
  "Kamar ya ranka shi dad'e?" Cewar Hajiya Binta kenan cikin rawar murya.
Ya girgiza kai.
"Babu wani k'ulli da ta sanya a k'asan gadon abokiyar zamanki, asalima acan kwatami ta yarr."
  Wani bakin ciki ya turnuk'e zuciyar Hajiya Binta, ta ji wata muguwar tsanar Ummi ya turnuk'eta,
maganar Luba ta katse tunaninta.
"Yanzu ranka shi dad'e ya za'ayi? Tabbas munyi kuskuren saka wata, kada dai ta tona
asirinmu?"
  Ya girgiza kai yana dariya.
"A'a, yarinyar ba haka ta ke ba, kada ku ji ko d'arr, yanzu me kukeso ayi?"
  "A maimaita mana irin wancan."
Fad'in Hajiya Binta kenan tana dubansa da jajayen idanunta wadanda 6acin rai ya kad'a. Nan
take bokan ya turnuk'e fuska yana watsamata kallon banza na baki isa ba. Hakan ya kad'amusu
'yan hanji. Ya cigaba da magana da kakkausar murya....!

    
   "Kafin na baku na gayamaku wuyar k'ara samun aiki irinsa, domin a shekara, sau daya Aljani
Tsingil ya bani damar tambayarsa buk'ata, saidai ko kuyi hakuri har wata shekarar."
  Hajiya Binta ta narke tana rok'onsa ko akwai wani abu da za'a iya yi?
Ya jinjina kai.
"Tabbas, abu mai sauki, zamu sanyamata

Please Login or Register in order to submit comment