ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koda ace batasan me ake kira da
hadadden namiji ba, to shakka babu akan Faruk ta sani. Cikin sa'a kuwa shima idanunsa suka
sauka akanta daidai lokacin da yake gyara zaman agogonsa. Haka kawai ta tsinci yanayinta ya
sauya adalilin kallon da yayi mata wanda ta tabbatar haka kwayar idanunsa suke, ba wai da
gayya ya yi ba. Ga mamakinta fuskarsa bata sauya  daga murmushin da yakeyi ba duk kuwa da
cewar sun hada ido da shi, ta numfasa ta kauda kanta har suka shige zuwa Falo wajen
iyayensu. 
  
DAN ADAM
  @RUFAIDA OMAR

      18
   Babu jimawa sosai Amarya ta iso filin da Angonta. Baki bud'e Ummi ta dubi Amina, alokacin
wuri ya hargitse, k'arar kid'a ya yawaita da ihun mutane da masu daukar hoto. Ta so ta tambayi
Amina daman namijin na zuwa kamu? Saidai babu damar hakan sakamakon hayaniyar da tayi
yawa awajen, sunyi kyau matuk'a. Gaba dayansu fararen kaya suka sanya, Haidar cikin farar
shadda, yayinda itama Intisar ta had'e cikin shadda dinkin doguwar rigar da ta sha aiki. Su
Ihsan da sauran kawayen Intisar suna take musu baya, hakanan shima ango, abokansa na
Abuja da na nan Kano kalilan cikinsu sun samu halara, yayinda wasu suka barwa gobe daurin
aure. Ba anko sukayi ba, saidai shadda brown kowannensu ya saka, na wani yafi na wani
turuwa. 
   Sunyi kyau kwarai, sai kirari ake yiwa Ango da Amaryarsa har suka isa mazauninsu. Duk raba
idanun Ummi bata ga yayyun Haidar ba da kuma Faruk. Har akayi nisa da sha'anin, mata ne
kawai da daidaikun matasan wajen wadanda dukkansu yan uwansu ne na Adamawa sai kuma
yan uwan mahaifin Haidar Danzaki da ma'aikata. 
   Sun jima sosai a wajen, an ci an sha, har saida aka kusan tashi sannan ta hangi mota ta faka
daga can gefen na amarya da ango. Su biyar ne suka fito daga motar, Yaya Ridwan ne sai
wasu wadanda suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce
wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad'arsa. Har aka tashi daga wajen babu
Faruk da Babban Yaya. 
     Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta
chanja sutura ta kwanta.
                      ☆☆☆
  Washegari ya kama ranar da za'a daura aure da kuma yini. Tun safe da mutanen dakin Mami
suka farka, babu wanda ya koma bacci. Daga Maigidan har sauran yaransa maza,
shirye-shiryen karyawa sukeyi su wuce d'aurin aure, yayinda Mami itama ke shirin tafiya gidan
biki. Ummi kuwa, ayyukanta ta shiga yi cikin sauri-sauri bisa umarnin Mami, don kuwa a son
Mami, tafiso tana can a daura aure maimakon ace bata isa ba. Itama Ramma sanin da tayi na
cewar Mami da wuri zata fita ne, yasa ta shiryawa da wuri, bata da wani aiki a kanta mai yawa
kasancewar yaranta sun je k'auye. Wannan karon dai Ummi ta ji maganar Amina, don kuwa ta
shafe fuskarta da hoda sannan ta sanya jan baki kalar ja sai kwalli data zizara a idonta. Ita
kanta tasan tayi kyau, irin kyawun da bata ta6a ganin ta yishi ba, ko don ba kwalliyar takeyi ba? 
  Ankon bikin da Mami tayi musu ne a jikinta, ya zauna d'abas kamar a jikinta aka d'inkashi, ya
fito da kyakkyawar surarta wanda ita kanta batasan tana da diri mai kyau ba kamar haka. Har ta
dauki mayafi ta yafa sai kuma ta ga sam ba zata iya ba, hakan yasa ta janyo farin hijabinta
wanda ya hau sosai da atamfarta mai adon fari da koren fulawoyi. Kiran da Mami ta kwalamata
ne yasa ta amsawa da sauri don bata da masaniyar cewa Mamin ta shigo falon domin itace a
fadar Alhajinsu. 
  "Masha Allah." Shine furucin da Ummi tayi a ranta, duk iyakar yanda take ganin ta fito tayi
kyau, sai ta raina shigarta ganin shigar Mami, ba irin ankonta bane a jikinta. Wani tsadadden 
leshi ne ruwan madara mai duwatsu dinkin doguwar riga da zani ta sanya, anyi aiki a gaban
rigar leshin wajen kirji, banda kamshi babu abinda kakeji yana tashi a falon. Hannunta rike da
jaka da mayafinta. Ta dubi Ummi duban tsaf kafin cikin sakin fuska tace. "Ashe dai kin iya
kwalliya." Abin  ya bawa Ummi mamaki, kodayake dai tasan yau Mami cikin farinciki take.
Ramma dariya tayi kawai, itama tayi tsaf da ita tana rike da karamar jaka na kaya wacce ta
tabbatar na Mami ne.
   "Shiga ki cewa su Hajiya Binta idan sun shirya su fito mu wuce."
  "Toh." Sannan ta kama hanya da mamakin wannan irin iko na iyayen gida irin Mami, wato bata
damu da ta sanarmusu su shirya ba tun farko saida ta tashi tafiya. Sashen Hajiya Binta ta soma
zuwa, a zaune ta sameta tana latse-latsen waya ko wanka batayi ba. Ciki-ciki ta amsa sallamar
Ummi, gabanta na dukan tara-tara, ta durkusa ta shaida mata sak'on Mami. Kamar ba zata ce
komai ba saidai ta dubeta a wulakance har saida ta ji ta muzanta.
     DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
     
     20
  
  Ta sauke ajiyar zuciya, gami da zame jiki ta durkusa a wajen. Yau Faruk ne yayi mata
murmushi? Sai tace tun zuwansu bata ta6a ganinsa cikin fara'a haka ba. Mai yiwuwa saboda
farincikin bikin dan uwansa ne. Jin da tayi ana ihu da shewa daga falon ne yasa ta saurin
mikewa itama ta samu dama dakyar tana lek'e. Turare ta gani wata tsohuwa cikin wadanda
suka zo daga Adamawa tana ta fesawa Ango da Amarya. Masu hoto suna faman yi, Faruk na
daga hannun kujera zaune agefen wata mace da bata fi shekaru ashirin da bakwai ba, wacce
itama cikin bak'in Adamawa take. Sai hira sukeyi suna dariya. Sunyi kama kwarai, kana gani ko
ba'a fada ba kasan jini d'aya suke. Haka dai aka gama hotuna, Ango Haidar da tawagarsa suka
fita. Wannan karon banda yayyun Haidar da Faruk, su kam zama sukayi ana gaisawa da hira da
'yan uwa. Tana ji anata yiwa Faruk tsiya akan shima ya dace yayi aure, abin banda dariya babu
abinda yake ba shi, domin shi dai har kawowa wannan lokacin bai ga matar da ta kwanta mishi
a rai ba har yakejin cewar zai iya aurenta. Duk cikin masu nuna masa kauna da so, duk cikin
masu yi kishi tallar jikkunansu batare da sun buk'aci ko sisinsa ba, babu wacce ya ta6a yiwa
kallon rahma. Asalima wannan d'abi'ar gaba daya haushi take ba shi wai ace mace ke tallatawa
namiji kanta, yana daukar hakan a matsayin rashin aji da sanin darajar kai. 
   Dakyar ya samu ya silale ya fito daga falon, Ummi ta bi bayansa da kallo sannan ta maida
hankali ga tsoffin dake faman shige da fice suna rabon abinci. 
  "Ummi." Ta ji muryar Amina a kanta. Wani sanyi ya mamayeta, ko babu komai zata samu
abokiyar hira. Ta zaro ido tana murmushi.
  "Anti, kinga kuwa yanda kikayi kyau? Masha Allah." Ta harareta kadan
  "Lallai ma Ummin nan, wallahi ban kaiki ba, kinga yanda kikayi kyau kuwa yau?" 
  Ummi ta girgiza kai. 
  "Ban kaiki ba Anti."
Amina ta dara gami da jan hannunta.
  "Taso mu zagaya baya, tun dazu ai ina can."
   Ummi ta mike suka zagaya. Babban fili ne mai shuke-shuke, nan dinma akwai mutane saidai
ba kamar cikin gidan ba, kusan ma yanmata sunfi yawa anan. K'asan wata bishiya suka zauna
asaman kujeru inda wasu yara biyu da Mace rike da yarinya wacce bata fi watanni uku ba suke
zaune. Ummi ta hango kamannin matar sosai da Amina, hakan yasa ta gaisheta, cikin sakin
fuska itama ta amsa. Amina ta dubi yaran. 
   "Ahmad, ja  Kulsum ku tafi wasa Antinku ta zauna."
  Ba musu yaron ya amsa sannan ya mike suka bar wurin, daman sun k'agu su tafi wasansu
amma ta hanasu da cewar sai sun ci abinci. 
   Bayan sun zauna Amina ta kalli 'yar uwarta wacce daga ita sai ita a haihuwa. 
  "Anti Hauwa, wannan itace Ummi da nake baki labarinta. Ummi wannan itace yayata Anti
Hauwa, daga ita sai ni a wajen Innarmu. Babbar yayarmu Anti Fiddausi tana Katsina, acan take
aure. Yaranta biyu, da Kulsum da kuma wannan bebin, Anisa. Ahmad shine auta wajen
Innarmu."
  Bayan ta kai aya, Anti Hauwa ta sanya dariya.
  "Toh 'yar jarida, oh Amina." Ta karashe tana kama ha6a, abin sai ya bawa Ummi da Amina
dariya.
   Anti Hauwa ta dubi Ummi fara'arta ta k'aru don kuwa babu abinda Amina ta 6oyemata
dangane da Ummi.
  "Sannu Ummi, fatan kina lafiya?"
Ummi ta gyada kai gami da sakin kyakkyawan murmushinta. 
  "Lafiya kalau Anti. Ya wajen su Inna?"
  Abin ya yiwa Anti Hauwa da Amina dadi.
  "Inna tana lafiya, taso ta zo amma matar kaninta bata ji dadi ba, ta je dubota. Watakil daga can
tayo nan."
  Ta gyada kai gami da yi mata fatan samun lafiya.  Nan kuma hira sosai ta 6arke tsakaninsu.
Anti Hauwa da Amina suka gangaro kan batun Saurayin Aminan, Bello wanda ya matsa akan
shi zai turo magabatansa. Anti Hauwa ta bata shawara akan ta sanarwa Inna idan yaso sai a
had'ashi da wani ya rakashi har can Nijar su gaisa da yan uwan mahaifinsu. 
  Haka suka tsayar da shawara.
  Sun wuni tare, Anti Hauwa sai bayan la'asar ta bar gidan, Hajiya Mama harda bata kudi tayi na
mota. Dakyar ta kar6a don mutunci da karamci irin na Hajiya Mama har yana so yayi yawa,
mace ce da babu ruwanta. Harda kayan rabo ta had'a ta bata, ta sanya aka yiwa Inna
(takeaway) na abincin biki tace ta kai mata domin ba wani nisa ne tsakanin gidansu Inna da
gidan Anti Hauwa ba. Ta kar6a da godiya. 
  Tafe suke gaba dayansu da Anti Hauwa da Ummi da Amina, wadanda suka yo mata rakiya
don ta samu abin hawa, kasancewar babu laifi akwai 'yar tazara tsakanin gidan da babban titi.
Ummi na rike da Anisa wacce ke faman kalle-kalle idanunta tarr a bud'e. Yarinyar ta shiga ranta,
haka kawai ta ji tana kaunarta ko don bata ta6a ganinta rik'e da yarinya k'arama haka bane?
Oho. 
   A farfajiyar gidan, samari ne da d'aid'aikun yanmata suna hira, daga ganinsu kaga yan uwan
juna. Suka wucesu suka fita. 
   Suna tafe suna hira a haka har suka iso titi, bayan sun samarmata d'an sahu, ta shiga sukayi
sallama. Ta dubi Ummi da murmushi mai bayyana hakora a saman fuskarta.
  "Toh Ummi, sai na ganki a gidana wataran ko?"
  Ummi ta amsa da toh tana maida martanin murmushin. Suka juya tare da Amina suka kama
hanyar komawa. A hanyar ma hira sukeyi, Amina na yi mata korafi akan ita ko dan fita unguwa
bata tambayar Mami ne? Ummi ta ta6a baki kadan.
  "To Anti wa nake da shi a garinnan?"
  "Kina da mu, wataran ki tambayeta kizo na kaiki wajen Innarmu ku gaisa."
  Murmushi Ummi tayi wanda yayi daidai da giftawar wata farar honda mai bakin gilasai ta
gabansu.
  "Wannan kamar motar gidan su Alhaji." Cewar Amina kenan. Ummi da batasani ba ta bi motar
da kallo kawai wacce ta koma tafiya sannu-sannu tamkar matuk'in baya so. Kafin daga bisani
ya fisgi motar ya k'ara gudu. 
  Ai kuwa kamar yanda Amina ta fad'a haka dinne, don suna isa kofar gidan suka iske motar a
fake, na cikin motar baikai ga fitowa ba saidai kafarsa d'aya da ya fiddo waje. Ta madubin
hannun kofar, Ummi ta hangeshi. Kansa a jingine jikin kujera yana amsa waya. Akayi katari
suka had'a ido, gani tayi ya yafito ta da hannu. Abin ya bata tsoro, gabanta ya hau dukan
tara-tara. Tayi saurin dauke idanunta don bata gaskata hakan ba.  Har zasu shige ciki ya danna
hon.  Wannan ya sanyasu dakatawa.
   "Da ku ake." Cewar Maigadi. Amina ta dubi motar, saidai bata hangi ko wanene ba
sakamakon duhun gilashin. Suka zagaya suka isa ta mazaunin direba, idanunsa akansu, suka
durkusa a ladabce suka gaisheshi. Yaya Faruk ya dago kanshi ya dubesu da idanunsa masu
tafiya da dukkan wata diya mace mai lafiya da zata kalleshi. Ya gyad'a kai kafin ya maida
dubansa cikin motar, hannu yasa ya janyo leda bak'a babba ya mik'awa Ummi.
  "Ki mik'awa Hajiyata." Ta sanya hannunta dake faman rawa don gaba daya wani kwarjini yayi
gareta, ta kar6i ledar wanda bisa kuskure hannayensu suka gogi juna har ta gogi tattausan
gashin dake kwance a hannunsa, a gigice ta dauke hannunta had'i da kar6ar ledar tana mai
amsawa da toh wanda bai fito sarari ba saidai kawai le66anta da ya nuna alamun hakan. Baice
uffan ba har suka fice ya bisu da kallo, ya lura yarinyar kamar a tsorace take da shi. Ya dan ta6e
baki cike da mamaki, mamakin bai wuce na ganin yara kyawawa haka ba ace wai suna aikatau
ba karatu ba, tabbas ya tausayamusu. Ya kuma raina iyayensu wadanda tunaninsa yafi ba shi
cewar kwadayin abin duniya ne kawai yasa suke sakin yaransu sakaka suna yawon gidajen
mutane don bauta da neman kudi wanda duk yawan abinda zasu samu bazai haura dubu goma
ba, aganinsa wannan cutar da rayuwarsu ce kawai. Ya lumshe ido, ya jima a haka kafin ya
maida kafafunsa ciki ya rufe kofar gami da yin ribas yabar unguwar.
              
DAN ADAM
  @RUFAIDA OMAR

  21
   Acan kuwa Ummi kasa shiga ciki tayi haka kawai bata son shiga cikin mutanen gidan, tana jin
nauyinsu. Amina ce ta kar6a ta mik'awa Hajiya Babba sannan suka koma inda suke. Sai misalin
karfe bakwai kowa ya soma shirin tafiya wajen (Party) wanda Ango ya shirya na musamman da
iyayensu da yanmata da samari. Abin har ya bawa  Ummi mamaki, aganinta wannan kawai
rashin sanin abinda za'ayi da kudin ne, ko kuma dai kudin ne suka yawaita garesu. Tana gani
Amina tayi mata sallama suka wuce sakamakon yara da zata kula dasu a gida kafin dawowar
Hajiya Maman. Ummi ta dubeta.
  "Nima na tabbatar yanzu zamu wuce ko don Ramma."
  "Wace Ramma? Ramma ai ta tafi gida tun dazu tare da su Hajiyar Iklima. Baki ga su Iklima
sunzo dazu ba?"
  Ummi ta zaro ido.
"Aa banma gansu ba wallahi, na tabbatar Mami ta manta ne da ta had'a tafiyata da su. Toh
yanzu wa zan bi?"
Amina ta jinjina kai.
"Mamin ce zata barki ki tafi da kishiyoyinta? Wasa kike ma. Na..."
  "Ummi, kizo inji Mami." Suka tsinci muryar Fahad wanda yayi sanadin katse Amina daga
maganarta. Ta dubeta.
"To saida safe, nasan kuma mu da kara haduwa ba yanzu ba." Sukayi sallama Amina ta wuce. 
  Ummi tana d'ari-d'ari haka ta daure ta shiga falon, Mami na daga zaune wata tana d'aura mata
d'ankwali.
Ta gaida mutanen falon sannan ta koma gefen Mami. 
  "Gani Mami." Mami ta dan dubeta.
"Ramma ta riga ta tafi, nikuma da wuya idan zan dawo ta nan gaskiya don gaba d'aya zamu tafi
can wajen party, ki zauna a inda zan ganki idan mu  fito."
  "Toh Mami."
  Daga haka tayi gaba, tana ji wata tana zolayar Mami wai da alama ita bata iya rayuwa saida
'yar aiki, har sauran suna dariya. Suna tsokanarta wai sai kace itace autar innartasu.
    Ummi ba haka taso ba, don alal hakika ita zuwa wajen wani party ko waje mai hayaniya baya
burgeta, da ace Mami zata barta anan da ta zauna har zuwa lokacin da zasu ci su cinye su
dawo su tafi. Ta dubi jikjnta bayan wucewar wasu yanmata da suka dauki ado cikin wani leshi
yellow da nadin kai ja, ta yaya ma zata shiga taron jama'a da kayan nan? Ta tabbatar ita kadai
zata bambanta acikinsu. Ta langa6ar da kanta, kodayake daman ita din ba kowa bace face 'yar
aiki. Bata da wani daraja, babu wani wanda zai ra6eta da sunan kauna ta jini ta yan uwantaka,
shiyasa take matukar kaunar Amina, ta tabbatar su Amina  suna kaunarta saidai bata da sa'ar
'yan uwa. Batasan halin da suke ciki ba a yanzu, da ace ma zatasan dangin mahaifiyarta, lallai
da ta kai kanta garesu komin nisan dake tsakaninsu. Ta sauke ajiyar zuciya kafin kuma da
saurinta ta share hawayen da suka zubomata.
  Ko mintuna biyar batayi ba awajen, Mami ta aiko kiranta, kaya ta dunga kwasa tana kaiwa
boot din motarsu, sannan ta zauna a motar tare da Fahad da wasu iyaye matan, Mami na fitowa
suka wuce wajen party. 
     Tun a farfajiyar otel din Ummi tayi bala'in raina kanta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da sakin
baki galala tana kallon yanda wajen ya k'ayatu, anyiwa wajen adon fulawoyi wadanda sai buso
sanyi sukeyi, hakanan kuma wajen sai kamshi yakeyi. Daga can ciki kana jiyo tashin kid'a.
Wadanda basu shiga ba suna tsaitsaye a farfajiyar wajen. Haka suka dunguma zuwa ciki. Sanyi
ba bak'on Ummi bane don tun bata saba shan sa ba a falon Mami, har ya zamana yanzu ta
saba. Wajen kowa ya dauki kwalliya. Matasa masu ji da ilimi da gayu sai kuma iyaye wadanda
kallo daya zakayi musu ka tabbatar cewa kud'i sun riga sun gama jik'asu. Zugwui-zugwui take
bin bayansu Mami, gaba dayanta a d'arare take, gani takeyi kamar kowa awajen ita ya zubawa
ido. Idanunta suka cika da kwalla, bata saba da irin haka ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji an
damki hannunta. Ta juya da sauri, Ihsan ta gani ta ci ado har ta gaji da haduwa, saidai fuskarta
a murtuke. Bata ce mata uffan ba ta soma janta, gaban Ummi na faduwa haka ta bi bayanta har
zuwa d'an (Corridor) na shiga dakin taron. 
  "Uban wa yace ki shigo? Kalleki kiganki, typical 'yar kauye, wallahi kika yi kuskuren shigowa
wajennan sai na miki wulakancin da baki ta6a zato da tsammani ba. Shegiya kawai marar
galihu!" Daga haka ta ja tsaki tayi gaba ganin mutane sun nufo hanyar shigowa. Ummi kuka ya
taho mata, da saurinta ta juya zata fita, ta bawa mutanen hanya suka wuce ta bi ta gefe ta fita
da gudu-gudu. Kai tsaye ta wuce bayan motoci inda babu  mai ganinta ta durkushe ta soma
kuka mai shiga rai. Kuka sosai takeyi, lallai ta k'ara gaskata cewar halayen DAN ADAM sun
bambanta. Ta gaskata cewar ita din ba wata bace face marar galihun kamar yanda Ihsan ta
jaddada mata. Kaiconta! Kaicon rayuwarta! Ace mahaifinka ya bude baki yayi furucin cewa ko
bangon duniya za'a kaika, ba matsalarsa bace, baka da wani makusanci mai kaunarka, daga
dangin mahaifin harma da shi kansa mahaifin. Takan rasa abinda ta yiwa mutane, wai meyasa
dangin mahaifiyarta bazasu nemeta ba? Ta tabbatar koda duniya ta k'i ta, su bazasu ta6a
gudunta ba, ta tabbatar zasu bambanta da sauran 'yan adam din da ta sani kuma ta rayu da su.
Tana fatan su zamto irin Amina da su Anti Hauwa, tana fatan su zamto masu nunamata so da
kauna ta gaskiya. 
   DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

22
   K'arar rufe motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa a firgice. Ido hud'u sukayi, kallonta yake
cike da tsantsar mamaki, yayinda ita kuwa take mishi kallo tamkar wacce ta ga wani dodo.
Gaba d'aya tsoro takeji kada ya bud'emata wuta akan me takeyi anan. Ta sunkuyar da kanta
tana duban motar, sai lokacin ta lura cewa motar da suka ganshi dazu a ciki ce. 
  Kamar yayi mata magana, saidai ya fasa ya juya ya soma tafiya. Ta mike ta bar wajen ta soma
tafiya kai tsaye ta nufi k'ofar fita daga Otel din. Kamar ance ya juyo, ya ganta. 
   "Ke!"
Ya fad'a a sannu yanda yasan zata ji don ba wani nisa tayi ba. Ta juya gabanta na fad'uwa. Sai
lokacin ta lura da shigarsa, ya had'u karshen haduwa, a yanzun yana sanye da shadda ruwan
kasa mai duhu wacce aka yiwa dinkin da ya zauna daidai a jikinsa. Takalmi da hular da ya dora
ma su kansu abin a kalla a k'ara kalla ne. A haka har ta karasa wajensa ta durkusa. Ya bata
umarnin ta mik'e. Bayan ta mike ya kare mata kallo sannan ya jefota da tambaya.
  "Ina zaki?"
  Ta soma rawar murya.
  "Gi..da." Ya yamutse fuska.
  "Ke kika kawo kanki?"
  Ta girgiza kai.
  "To shiga ciki."
  Tunanowa da maganar Ihsan yasa ta soma zubar hawaye ta dubeshi da jajayen idanunta
wadanda kuka ya maidasu hakan, sai lokacin shima ya lura da su. 
   "Kayi hakuri Yalla6ai, bazan iya shiga ba."
  Shiru ya biyo baya ayayinda ya kafeta da ido yana kallon fuskarta. Haka kawai sai ya ja
guntun tsaki.
  "Akan wane dalili?"
"Ih..ih.san tace kada na shiga zata wulakantani."
   Ya ji wani abu a ransa, sai kuma ya cije le66ansa na kasa.
  "Ko menene ku kuke jawowa rayuwarku, da ace kun hakura da yanayin rayuwa, kun godewa
kad'an din da kuke samu a gidajenku, da babu abinda zaisa kuzo ana wulakantaku ana baku
tamkar wasu karnuka."
  Batasan sadda ta cigaba da 6ul6ulo da ruwan hawaye ba. Ta so tayi shiru ta barwa zuciyarta
amsa, saidsi ta tsinci kanta da kasa aikata hakan.
   "Ka gafarceni Yalla6ai, saidai akwai lokutan da ba'ason ran mutum yajr aikata abinda ya
aikata ba. Akwai tilastawar rayuwa, wani ba shi da yanda zaiyi ne, sai yaga da yaje ya aikata
abin turr gwara ya gwammace ya rufawa iyayensa da kansa asiri ta hanyar nema ta halal. Wani
kuwa, rashin gata da rashin samun kulawar yan uwa ke sanyashi tsintar kai a halin da yake ciki.
Kowane bawa da yanda Allah Ya tsaro rayuwarsa, ba mu muka za6awa kanmu wannan
rayuwar ba. Akwai KADDARA."
  Daga haka ta juya da sauri-sauri ta bar wajen gami da nufar get, batayi wata-wata ba ta fice
daga wajen batare da tasan inda ta nufa ba, burinta kawai tabar wajen ko ranta zaiyi sanyi....!
       

  Ta dubi sararin samaniya, hasken farin wata ya taimaka kwarai wajen k'ara haskaka unguwar,
hakanan kuma akwai hasken fitili domkn unguwa ce ta manya. Ta numfasa ta soma bin hanyar
da taga Danliti ya biyo da su dazun. Tafiya kawai takeyi batare da tasan takamaiman inda zata
nufa ba bayan nan, hakazalika batajin ko son ta koma wajen walimar. Ta gwammace idan ma
saceta ayi muddin za'ayi nasarar rabata da wajen nan. Ita kam ta tsani cin zarfi da disgi. Tayi
nisa amma ba sosai ba, ta ga mota a gefenta tana tafiya sannu-sannu, wannan baisa ta tsaya
ba ballantana kuma ta waigo. Ta ji k'arar hon da k'arfi, ta runtse ido tana mai cigaba da tafiya kai
ka rantse Ummi tsabar yanga ce takeyi, ga wanda ya santa kuwa yasan tafiyarta ce hakan,
saidai duk da hakan na yau yafi na kullum don tana taku ne jikinta babu laka, gaba daya a
sanyaye yake, zuciyarta banda bugu da sauri-sauri babu aikin da takeyi. 
   "Ummi."
Taji faduwar gaba jin muryar Yaya Faruk. Ta waigo da sauri ta dubi motar, kasa jure kallon
kwayar idanunsa tayi masu kyau da fisgar hankali tayi gefe da idanunta batare da ta cigaba da
tafiya ba. 
   "Shigo."
  Ta daure ta kara dubansa tana mai share hawayen da suka zubomata, girgiza kai tayi.
  "Kayi hakuri Yaya Faruk, bazan iya komawa..."
  "Gida zan kaiki." Ya katseta da fad'in hakan. Ta danyi jim, tana tsoron kada Hajiya tayi fad'a
saidai kuma ta gwammace fad'an Hajiya da dai ta k'ara komawa wajen da ba'a dauketa a bakin
komai ba face wulakantacciya. Jiki babu kwari ta sanya hannu zata bud'e gidan baya, ya rigata
bud'e na mazaunin gefensa.
   "Nan za ki shigo." Gabanta ya fad'i. Ta kasa cewa komai duk kuwa da cewar ta raina aji,
matsayi da kuma girmanta ace wai itace zaune agefen matashin da ya had'a dukkan wadannan
abinda takejin ita din bata da shi, abin kamar dai a mafarki. Da bismillah a bakinta ta shiga ta
rufe a sannu, ajiyar zuciya ta saki jin wani azababben kamshi ga kuma sanyin Ac da ya ratsa

Please Login or Register in order to submit comment