You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
bacci 6arawo ne kadai ya saceta shima cike da
mafarke-mafarke.
"Ina kwana..."
Bata kai ga k'arasawa ba ta ji an dauketa da wani zazzafan mari, ta rik'e kuncinta lokaci guda
kuma ta saki bokitin hannunta tana duban Ikram fuskarta cike da tsananin damuwa, tuni
hawaye sun soma sauka a fuskarta.
"Kinyi kad'an a mareni saboda ke ba kasa tararki na rama wallahi! Ke din banza! Sa'arki daya
ma jiya a gaban wadanda suke da daraja aka mareni, da tun jiya na huce. To saidai mu din an
koyamana tsayawa iyakar matsayinmu bamu saba ketarewa ba, ke kuwa da alama ba ki samu
wannan tarbiyyar ba tunda har ya kasance kinyi tsaurin idon kai kanki inda aka fi karfinki. Banza
mai kwadayi."
Ikram ce ke wadannan kalaman tana mai jifanta da wani banzan kallo, ba ta ce uffan ba, ta sa
hannu zata dauki bokitin Ihsan ta buge hannun da k'afarta.
"Aiki kuma a gidannan ya k'are miki, sannan ki sa a ranki muddin yau muka isa Kano zamanki
a gidanmu ya k'are, sai naga ta inda zaki auri Yaya Faruk din. Banza kawai!"
Ummi da ta kasa dagowa daga durkushen da ta yi, ta runtse idonta cikin jin zafin wannan abu.
"Meke faruwa ne?"
Suka tsinci muryar Hajiya, da sauri suka nutsu kamar ba su ba.
"Bakomai Hajiya, k'arewa Matar Yaya kallo mukeyi."
Cewar Ikram tana dariya ta raini. Hajiya ta daure fuska.
"Ku bar wajen nan tun ban sa6amuku ba."
Suka juya suna gunguni suka koma daki. Hajiya ta zauna saman kujera ta yi shiru tana kallon
Ummi dake faman goge ruwan da suka zubar suka 6ata mata guganta, tana yi tana hawaye.
Murya na rawa ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa mata. Saida ta kammala sannan ta mik'e da
zummar barin wajen, ta dakatar da ita ta hanyar kiranta, jin yanda Hajiya ta kira sunanta da
sanyin murya, yasa ta dan ji sauki na rad'ad'i da kuma fargabar da ta cikata. Ta amsa a ladabce
tana mai zama a gefe kanta a k'asa.
"Kiyi hakuri Ummi, nasan daman tunda Sadauki ya 6ullo da maganar aurenki, dole irin haka
ta faru koma fiye da hakan kafin a samu fahimtar juna. Ni ban ta6a k'in ki a zuciyata ba, haka
kuma ina miki kallon mutum kamar kowa mai nata darajar ta daban. Ko yanzu hakurinki yasa
kin k'ara samun wani gurbi a zuciyata. Ki sani, ni mai son abinda Sadaukina ke so ne matukar
ba abin assha bane don haka kema na yarda da lamarinki da shi. Kar kice kuma zakiyi amfani
da wannan damar ki cutar da d'ana, bazan ta6a lamunta ba. Idan kin d'ore a yanda kike yanzun
to fa zamu shirya da ke. Sannan Ihsan..."
Sallamar Gogan ya katse Hajiya daga maganarta, suka amsa suna dubansa. Idanunsa shima
a kansu da mamaki, musamman ma na ganin yanda abar kaunarsa ke fidda ruwan hawaye
saidai bayason cewa wani abu don gaban Hajiya ne, fatansa dai kada Hajiya ce ta sanyata
kuka.
Ya karaso cikin shigar kananun kaya wanda ya nuna shaidar ya yi wanka, ya zauna gefen
Hajiya yana mai gaisheta, ta amsa fuskarta a dan sake ba kamar jiya ba da ta daure mishi,
hakan ya dan sanyamishi nutsuwa. Ummi ta gaisheshi batare da ta dubeshi ba, ya amsa yana
bin fuskarta da kallo, yana son ya tambayi dalilin kukanta saidai babu dama.
"Je ki sai na nemeki, kin shirya kayanki?"
Ta gyada kai, Faruk ya yamutsa fuska yana duban Hajiyarsa cikin rashin fahimta, bayan fitar
Ummi dauke da bokiti da tsummokarai, ya dubi Hajiya.
"Ina zata?"
"Kano zata koma mana, ko ka manta daga can ta fito?"
Ya daure fuska yana mai kauda kai.
"Idan har a matsayin yar aiki zata je don Allah ayi hakuri Hajiya."
Ya karashe fuskarsa cike da damuwa kwarai. Ta yi shiru tana dubansa, ta gama karantar ba
karamin so ya ke yiwa Ummi ba, tasan halin d'anta, wannan magana har cikin zuciyarsa ya ke
yinta.
"To yanzu Sadauki za'ayita rike musu ita ne? Karka manta fa kawota akayi Kano aikatau
asalinta ba ma'yar garin bace."
Ya lumshe ido kafin ya bude.
"'Yar Ringim ce. Kuyi hakuri har ta cika watanta, idan wacce ta kawota ta zo Kanon, sai aje har
Ummin ayiwa mahaifinta bayani don Allah Hajiya. Amma yanzu ba girma kuma ta cigaba da
aikatau, a duba wannan lamarin Hajiyata."
Hajiya ta gyada kai cike da gamsuwa.
"Shikenan, na ji zanyi tunani."
Bayan fitarsa daga falon ta rasa ma abin yi, mikewa ta yi ta nufi dakinta. Karshe dai ta yanke
hukuncin kiran kanwarta Hajiya Mama, don ita har nauyin Hajiya Madina ta ke d'an ji a yanzu.
Hajiya Mama ta dauka, bayan sun gaisa ta ce. "Sadiya kina jina?"
"Ina jinki Hajiya."
Ta koramata dukkan yanda ake ciki tun daga jiya da Faruk ya zo musu da maganar Ummi har
zuwa yanzun da ya ce shi bayason komawarta aikatau Kano. Ta k'ara da fad'in.
"Ki ban shawara Sadiya, kwakwalwata ta cushe, na rasa abinda zanyi, ina kuma jin tsoron
Madina ta ji maganarnan daga bakin 'yarta."
Hajiya Mama da ta sandare don mamakin wannan al'mari ta numfasa.
"Allah Mai Iko, wannan shine ana zaton wuta a makera. Karki damu Hajiya, ni banga aibu a
aurensa da Ummi ba matukar zai had'a har ita Ihsan din kamar yanda ku ka ce, don bazamu so
wannan abu ya kawo matsala a zuri'armu ba. Amma don Allah kamar yanda Genaral ya ce, ku
daure kuyi bincike sosai akan Asalin yarinyar nan, Ummi dai a halayya bata da aibu daidai
gwargwado yarinyar akwai hakuri da sanin yakamata sannan har gwaje-gwaje ayi ko don
gujewa wani abu da zai je ya dawo. Ki kwantar da hankalinki, daman yau zanje saloon, zan fasa
idan yaso na sanarwa Alhaji na je gidan Madinan. Allah Ya za6a abinda yafi alheri."
Cike da jin dadin kalamanta Hajiya Babba ta ce.
"Kai da kuwa kinyimin babban taimako wallahi, nagode sosai."
"Haba Hajiya, kina gaba da ni ai kin wuce haka, na tabbatar Madina ba zata kawo matsala ba
in sha Allah."
Ta jinjina kai.
"Ina fatan hakan."
A karshe sukayi sallama da zummar duk yanda akayi zata sanarmata.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
73
Ko wanka baiyi ba, hankalinsa na ga abar kaunartasa. Zai so jin amsar da zata bawa Binta.
Hakan yasa shi yin cak yana mai zubamata ido don sun ba shi baya.
Ummi ta yi murmushi wanda har gefen kumatunta ya lotsa. Batasan sadda ta soma
magana ba.
"Ni nasan yanda nake jin Yaya Faruk a raina Binta, akwai da yawa daga abubuwa wanda ba
sai ka 6ata lokaci wajen bayyanashi ba, watakil ya nuna kansa wataran. Ina son Yaya Faruk fiye
da kaina, zan iya sadaukar da nawa farincikin don kawai ya samu nasa. Binta me zance ga
mutumin da ya daraja ni ya nunawa duniya ni din mutum ce mai daraja? Ke kuwa idan ban
kaunaceshi ba me zan mishi?"
Binta ta yi dariya.
"Tabbas kinyi gaskiya, kin kuma burgeni matuk'a. Allah Yasa wannan kauna taku ta d'ore har ku
haayyafa ku tara zuri'a guda taku."
Kunya ta hanata amsawa face murmushi da tayi.
"Ameen." Jin muryarsa yasa duk suka juyo a razane, ta zaro ido duk ta bi ta diririce, shikenan
ya ji abinda ta ce kenan? Ji ta yi kamar ta nutse a k'asa don kunya. Ita kuwa Binta tana yar
dariya ta russuna ta gaisheshi, ya amsa fuska a sake yana duban Ummi. Ita dinma gaisheshi ta
yi dakyar sakamakon harshenta da ta ji ya yi nauyi duk don tsabar kunya.
Ya amsa yana ji kamar ya nufeta ya rukunkume don dadin da kalamanta sukayi masa.
"Zo nan Ummi."
Ya fad'a gami da juyawa ya fita. Ta bi bayanshi da kallo, daga shi sai dogon wando da singilet
bak'a.
Ta dubi Binta wacce ke zungurar kafadarta tana mata nuni da ta je. Ta yi murmushi mai
bayyana hak'ora cikin muryar rad'a ta ce.
"Anya bai ji maganarmu ba?"
"Lallai ke dinnan, to meye idan ya ji? Daman kinason fadamishi kin kasa kinga ya hutar da ke."
Ta girgiza kai gami da wanke hannunta da handwash sannan ta mara mishi baya.
A tsaye ta tarar da shi wajen hanyar da zata sada ka da sashensa. Ya kura mata ido kamar ya
hadiyeta. Ta kauda fuskarta ta karasa gareshi.
"Meyasa kike barin wayarki a daki sai nayita kira bakya d'agawa?'
Yana maganar cikin muryar shagwa6a kamar wani k'aramin yaro, abin ma sai ya bata dariya,
idan yana wannan shagwa6ar wani kyau ya ke yi mata, ita dake mace ma bazata iya yinta ba.
"Ka yi hakuri, aiki ne mukeyi."
"Naji, maimaita abinda kika fad'awa Binta yanzu a kicin."
Ta zaro ido tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi, shima murmushin ya yi ya daga mata
gira.
"Kinyi zaton ban ji ba ko? Na ji dukkab tattaunawarku, oya idan dagaske ki ke maganarki ki
cemin 'Ina sonka Faruk' na ji."
'Innalillahi...' Ta karantota har karshe a ranta, gaba daya ta diririce. Shi kuwa dagaske ya ke,
don tsayuwarsa ya gyara yana jiranta.
"Kinyi shiru."
Ta hau wasa da yatsunta, murya a raunane ta ce.
"Ni..ni ban ta6a fad'a ba fa."
"Shiyasa nakeso ki fad'amin, ya zama ni ne farko nine kuma karshen wanda za ki fad'awa
hakan ok?"
Ta runtse ido, yau ta shiga uku, ji ta ke yi kalaman sun yi mata nauyi da tsauri, bazata iya fad'a
ba. Ya dan saka saman yatsansa manuniya ya zunguri hannunta.
"Kin yi shiru Ummina."
Ta ja baya kadan ta hadiyi miyau.
"Ka yi hakuri don Allah."
Ya lura a tsorace ta ke ma, sai kawai ya yi murmushi.
"Ki ka ce ba ki da abinda za ki biyani? Ke kuwa ki ke da shi, kawo kunnenki ki ji."
Bata motsa ba, tuni shi kuwa ya matso da bakinsa dab da kunnenta. Maganar da ya fad'i ce ta
rud'ar da ita, da gudu ta juya ta koma kicin. Ya bita da kallo yana dariya kafin ya juya ya soma
tafiya. Wayarsa ta dauki k'ara, ganin Haidar ne yasa shi dauka da sallama. Bayan sun gaisa
Haidar ya ce.
"Ya Man, na ji ka shiru, ka kuwa fad'awa su Daddy?"
Faruk yana taka matattakala yana murmushi ya shafi sumar kansa. Kafin ya soma kora mishi
duk yanda akayi harma da rikicinsu da Dakta Ridwan da kuma cewar Hajiya na sai ya auri
Ihsan ma.
"I just don't know what to do brother, ban ta6a son Ihsan ba, ban kuma ta6a yi mata kallon
budurwa ba, ina mata kallon kanwata wacce ban bambanta ta da Baraka da Ikram ba."
Haidar wanda ya yi shiru ya soma magana.
"Duk wannan bai dameni ba, kamar yanda ku ka samu sa6ani da dan uwanka ba Faruk, zan so
ka je ka sameshi har gida ku fahimci juna. Banason akan lamarin aurenka a samu rarrabuwar
kai a family, it's something that never happen, so please don't let it now."
Ya gamsu matuka da zancen yayannasa. Daman shima ya sauko daga fushin da ya yi da
Dakta saidai kunya ce ta hanashi zuwa gidansa ya ba shi hakuri, wai shine ya nemi yi mishi
rashin kunya akan ya ta6a matar da ya ke ji cikin zuciya da gangar jikinsa. Maganar Haidar ta
katseshi.
"Batu kuma na Ihsan, wannan ba yanda ka iya, ka zamo mai biyayya ga umarnin iyaye ko don
ka cika d'a nagari. Ka yawaita addua akan neman za6in Allah ka ji?"
Ya zauna a karshen matattakala batare da ya bude kofa ya shiga ba falonnasa ba, murmushi
dauke saman fuskarsa na jin dadin maganganun dan uwansa ya ce.
"Na ji Brother, zan yi yanda ka ce, bari na yi wanka nayi breakfast, zan je gidan Dakta idan ma
ban sameshi ba zan shiga asibitin."
Ya ji dadin maganarsa.
"Yauwa that's my lovely brother, haka nake son ji. Nasan anjima zai shigo, gwara ka je kafin
shigowarsa, nima ina nan tafe bayan Magriba idan Allah Ya yarda, don na k'ara ganin
surukartamu da akai mana 6oyon fuskarta."
Dariya Faruk ya yi kafin suyi sallama ya mik'e ya fad'a d'akinsa.
*** *** ***
RINGIM
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
72
A farfajiyar gidan suka hadu da Anti Amarya wacce ta dawo daga gidan wata kawarta, ta lura da
yanayinta saidai baki kawai ta saki tana kallonta, Hajiya Mama itama ganinta ne yasa ta dan
saita kanta duk da kuwa bai hana komai 6oyuwa ba. Anan kofar gidan ma Adnan ya dawo daga
yiwa wasu abokansa sallama sakamakon tafiyarsa da ta k'arato nan zuwa kwana biyu ya ci karo
da ita, daga yanda ta amsa sallamarsa ma yasan ba lafiya ba, ta shiga mota direba ya ja suka
bar wajen. Hawayenta ya kasa tsayuwa, wannan wane irin rana ce ta zo musu? Kamar yanzu
ne suke wasa da dariya da kanwartasu, ace har lamari na aure ya had'asu rikici na ban
mamaki. Wai yau Madina ce ke kiran sun ci amanarta, ta nuna suna mata son kai, wannan abu
da me ya yi kama? Har take nuna basu suka haifi Ihsan ba ga da ga.
Ran Hajiya Mama ya k'ara jagulewa, ta kasa hadiye kukanta, haka hawayenta ya yi ta zubowa
tana daukesu da mayafinta. Babu abinda ta fi tunowa sai yanayin shakuwarsu tun suna k'anana
har zuwa girmansu, yau sa6ani ya shiga tsakaninsu akan auren Ummi da Faruk.
Ta runtse ido.
'Madina ina kika mance tarbiyyar da iyayenmu suka bamu? Yaushe kika chanja daga kyawawan
d'abi'unki? Ya akayi kika bari son 'yarki ya rufemiki ido har haka? Wannan abu abin kunya ne ya
shiga kunnen iyayenmu. Abin kunya ne gareki idan Hajiya Babba ta ji wannan lamari.' Tana
dukkan wadannan maganganun ne cikin zuciyarta. Akan hanya wayarta ta yi k'ara fiye da sau
biyu amman ta kasa d'auka, tsoron dagawar ma takeyi, me zata iya cewa Hajiya Babba? Sam
bazata iya da wannan abin kunyar ba wanda ta ke ganinsa tamkar a mafarki.
Adnan cikin sauri ya shiga wajen Maminsa, saidai bata falo hakan yasa ya nufi dayan
falonnata, nan ma batanan, a karshe ya yanke hukunci shiga dakinta. Gefen gado ya sameta
zaune tana kuka. Hankalinsa idan ya yi dubu to yau ya tashi, ya isa gabanta ya durkusa.
"Mami meke faruwa ne? Ga Hajiya Mama ta fita hankalinta a tashe tana hawaye, kema ga ki
na tarar dake kina kuka, rasuwa akayi ne?"
Ta share hawayenta.
"Da rasuwa ce to da sauki don ansan tana kan kowa, wannan yafi mutuwa k'ona zuciya Adnan.
Yau akan Ummi har Hajiya Mama ta mareni, sai nace tun tasowarmu da ita sa6ani irin haka bai
ta6a shiga tsakaninmu ba."
Kansa ya danyi dum, ya kasa tantance tak'amaiman yanayin da ya shiga.
"Ummi kuma?" Ya furta yana dubanta.
"Kwarai kuwa." Ta kwashe maganat ta gayamishi, ya dan ji hankalinsa ya kwanta, daman ba
yau ya fahimci akwai wani abu a zuciyar Faruk game da Ummi ba, shi yasan daman irin haka
zata faru wataran, Faruk ya ce zai auri Ummi. Saidai Ihsan fa? Bai ta6a kawowa tana son Faruk
ba. Tabbas shi bai ga aibu a had'asu ya auresu ba.
"Kayi shiru?"
Ya dago ya dubi mahaifiyarsa.
"Mami shi fa lamari na aure Allah ne Ya tsara abinsa, babu wanda zai chanja kaddararsa.
Kuma..."
"Tashi ka ficemin! Shashasha kawai da baisan kishin nasa ba."
Sum-sum ya fice don ya lura ta shiga cikin zafi, da alama babu abinda zai iya fadamata a
yanzun ta fahimta. Har ace ta manta irin gwagwarmayar da ta sha a baya wajen Abbansu, har
ace zata mance komai na duniya rubutaccen al'amari ne, idan Allah Ya yi za'ayi, za'ayin?
Ya waigo yana mai dubanta, waya ya ga ta dauka ta na kokarin kira. Gabansa ya fad'i kada fa
ta ce zata kira Hajiya Babba. Da sauri ya isa gareta ya rike hannunta.
"Don Allah Mami karkiyi haka, ki duba zumuncinku, kada a sanadin abinda bai kai ya kawo ba ki
6ata kyakkyawar alak'arku da yan uwanki wadanda kowa ya gani sai ya yi sha'awarta." Sai
kuma jikinta ya danyi sanyi, ta dubeshi fuskarta har lokacin a daure.
"Tashi ka ficemin Adnan tun ban kai ga ta6a lafiyarka ba."
Ya tashi jiki a sanyaye ya fice, bata fasa kiran ba saidai jin da ya yi Ihsan ta kira ta ke tambayar
ko ta taho, hankalinsa ya dan kwanta.
*** *** ***
ABUJA
Hajiya Babba duk ta bi ta damu akan rashin amsa kiranta da Kanwarta Sadiya bata yi ba,
batason kiran Mami tukunna.
Ihsan ta shigo da sallamarta ta yi shirin tafiya don tuni an fita da kayanta, sam lokacin ma
batasan anfasa tafiyar da Ummi ba. Ganinta yasa Hajiya sakin fuska tana dubanta.
"A'a, d'iyata har an fito?"
Fuskar Ihsan ba walwala sosai ta amsa.
"Eh Hajiya, an fita da kaya ma."
Hajiya ta gyada kai.
"Zo ki zauna mu danyi wata magana."
Ta zauna a gefen Hajiyar kamar yanda ta umarceta.
"Ihsan inaso kiyimin kyakkyawar fahimta akan maganar da nakeson yi dake. Zamanki anan
tare da mu yasa na fahimci kamar kina son Sadauki, ban tabbatar da hakan bane saida naji
daga bakin Ikram. To sai kuma Sadauki ya zo mana da zancen Ummi tashi guda da sunan ita
ya ke so da aure. Saidai ya amince zai hadaku tare ya aura. Ina fatan baki da matsala akan
hakan?"
Takaici ya hana Ihsan magana, lallai ma ta yaya ake zaton za ta yi zaman kishi da 'yar aikin
gidansu? Wannan ma jawowa kai raini ne wallahi. Haushin Hajiya ma ya hanata cewa uffan har
lokacin kanta yana k'asa.
Hajiya ta yi shiru tana karantarta, sai kuma ta numfasa.
"Ki je Ihsan ki yi tunani, bazan matsamaki ba. Ke tawa ce, bazan k'i farincikinki ba kema,
bazan kuma so k'untata miki akan wata ba. Dake da Sadauki abu daya na daukeku, babu
wanda zanso shiga hakkinsa."
Ihsan ta sauke ajiyar zuciya.
'Kedai kome za ki ce daga baya ne kin riga kin nuna son danki fiye da kowa."
Cewar Ihsan a zuciya. Shigowar Binta ce ya katse maganar. Suka amsa sallamarta.
"Ya ce ta fito."
Ta mike Hajiya na mata adduar komawa lafiya itama tana godiyar abubuwan alherin da suka
bata. Saida zata shiga motar ne ta dubi Ikram.
"Wai bada Ummi za mu tafi ba?" Kafin Ikram ta amsa Hajiya ta amsa.
"Ki je zata zo."
Ran Ihsan ya k'ara yin bak'i, kenan plan dinsu da Ikram ya tashi a banza? Niyyarsu da zarar ta
koma Kano a koreta sai aga ta aurenta da Faruk, ranta ya yi wani irin daci, a fusace ta shiga
motar ta banko murfin. Mamaki ya kama Hajiya, anya babu wata a k'asa? Daman ta lura kamar
bata yi na'am da maganganunta ba. Haka ta bi bayan motar da kallo, tuni haushi da 6acin rai
yasa Ikram juyawa ciki. Watakil nan gaba ma Ummi ta zama mai mulkar kowa a gidan, don taga
alama ta samun kar6uwarta wajen Hajiya da Daddy. Acewarta DAN ADAM tara ya ke bai cika
goma ba, zasu ga hali na butulci da Ummi za ta yi musu nan gaba indai akayi auren. Don ta sha
jin labaru na irin hakan.
Ummi duk tana kallon abinda ke faruwa, daman tun jiya da dare Hajiya ta sanarmata an
fasa tafiyar da ita, sannan Faruk ya kira ya bata tabbacin kada ta sake ta shirya da zummar
komawa Kano, ta daina aikatau daga ranar.
Ta saki labulen kicin din gami da sauke ajiyar zuciya ranta ya danyi haske, ko babu komai
alwashin da Ihsan ta ci akanta bazai tabbatu ba. Yanzu ita ina tasan zata ta samu motar garinsu
idan suka korata? Saidai da tambaya kam. Ita har fargabar komawarta Ringim take, ko wane
k'alubalen zata fuskanta a wajen Saude da Babanta?
"Ke!" Ta firgita matuk'a ta juyo idanunta a zare kirjinta a sama don ji tayi har numfashinta ma
kamar yana barazanar daukewa. Ganin Binta yasa ta dafe kirjinta gami da rufe ido tana sauke
ajiyar zuciya. Dariya sosai Binta ta sanya, Ummi ta girgiza kai.
"Wallahi ba ki ji yanda na tsorata ba, kai Binta saiki kashe mutum."
Binta cikin dariya ta daga mata hannu.
"Yi hakuri, daman cewa nayi bari nagani ko za ki tsoratan, na manta yanzu ke fa a tsorace kike
da kowa ma."
Ta yi murmushi tana tattare tafarnuwar da ta zubar a k'asa don kid'ima.
"Na yi zaton Ikram ce ko Ihsan din ce ta dawo."
Sukayi dariya. Kafin kuma Ummi ta cigaba da 6arar tafarnuwa.
Binta ta dubeta sa'ilin da ta janyo robar kifin da ta saka a ruwa don ya yi kankara ta soma
kokarin gyarawa.
"Wai ni don Allah meyasa ban ta6a jin kin fad'i wani daddad'an kalami na soyayya ba game da
Yalla6ai? Sai nake ganin kamar ya fi sonki fiye da yanda ke kika daukeshi."
Wannan tambaya ta Binta, yasa Faruk cin burki daga kofar kicin don ya zo ne daman da niyyar
tuhumar Ummi dalilinta na barin waya a daki ga shi yana ta kira.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
74
RINGIM
Bud'a ne ya cika gidan Baba Habiba sakamakon auren da aka daura na Zahraddeen da
Khadija. Yawanci gaba daya danginta ne suak halarci bikin, daidaiku ne cikin dangin Malam
Yahuza suka zo, wadanda zuwansu ma ba amfani awajen Baba Habiba don acewarta sun zo
kwasar rahoto da gulma.
Ita da aminiyarta Saude sun yi shiga ta sutura har kala uku ana yi ana chanjawa, Amarya
kuwa kusan kala biyar ta yi domin wannan ranar. Da yamma Amarya na cikin taron jama'a suna
gaisawa, wata yar uwarsu ta zo kiranta.
"Kizo kinyi bak'i fa daga Kano." Ta bi bayanta da mamaki don iyakar saninta bata da kowa a
Kano. Gabanta ya bada wani bugu mai karfi ganin Raihana cikin shiga ta wata shegiyar shadda
mai tsadar gaske, daidai da sark'ar da dan kunnenta abin kallo ne, ballantana kuma idan ka
dubi agogo da awarwaronta kasan na gwal ne. Tana da 'yar k'iba hakanan doguwa ce, ba laifi
tana da kyau daidai gwargwado, wacce suke taren itama ta ci nata adon har ta gaji da haduwa.
Murmushi Raihana ke jifanta da shi da wani dan iskan kallo wanda bai kyautu a matsayinta na
yar uwarta mace ta yi mata ba. Ta daure ta k'ak'alo murmushin yak'e ganin cewa cikin mutane
ne.
"A'a, Raihana kece a garinnamu? Sannunki da zuwa."
Raihana da har lokacin bata bar murmushi ba ta amsa.
"Yauwa Dijat , ke kuma haka akeyi?"
Dija ta rude gudun kada ta ce wani abu da mutane zasu dagosu, tana shirin kwa6arta Baba
Habiba ta karaso wajen duk ta had'a zufa saboda shiga da fita. Ganinsu yasa ta washe baki
kamar gonar auduga, ta bisu da kallo daga sama zuwa k'asa sannan ta dubi Dija.
"Wadannan fa?"
'K'awayena ne na yanar gizo, sun zo tayani murna ne."
"A'a sannunku kun ji ko? Ina wuninki?"
Ba kunya ta gaishesu, kasancewar suma yan duniya ne sai suka amsa.
"A'a baza'a barsu anan ba kinga nan a cike yake, kaisu gidan Saude su zauna. Bari na kar6o
muku muk'ulli."
Daga
Book Chapters
Chapter 21
Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500