ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake kenam ke bagidajiyace Allah hakadai sukaita wasa muntaz tace wannan bashi bane dan sanina da haukarshi shekara biyu fa bahijja tace ai nima andade dana ganshi yanada kyaufq wancan bakiga yanda aunty maryam tamutu akqnshiba tanata kallonshi ammashi kodaga ido yakalleta baiyiba kinsan wai waye.... Hum shinefa yariman kano babanshimq yarasu naji ance shi aka nada sarki amma yanzun bansan labarinshiba haka aukaita firarsu har sukayi bacci_

_malam sadiku yashiga garin kano dan nemo labari nan yasamu wani mai tallan rake yazauna gun yasiya rake yana cewa kai yau naji wata karya wai ance yarima yabata??? Mai rake yace kai wai kai sai yanzu kajii malam sadiku yazare ido yace aidayake bana garin shiyasa mai rake yace hummm ai bari kawai abin yaba kowa mamaki wlh mamarshi tananan tunda yatafi yanzun shekara biyu bata magana hakanam take zaune kamar gunki ko daga kanta batayi kullun cikin jan carbi take bata cewa kala mapam sadiku yace ohhhj Allah sarki batada wasu yayan ne hala mai rake yace akwai yaya uku amma dayar karamar saboda batar yarima dama da baban yarasu hawan jini yakamata to da yarima yabata jininta ya hau tarasu bakimciki yama mamqnsu yawa yasa tazama kurmar karfi da yaji sauran yayanta biyu kuma duk sunyi aure dayarma baa jimaba amma nan suke zaune da mijinta tace bazata tafi tabar uwartaba humm aikaidai bari iyalan sarki mahmudu lamido sunga jarabawowi muma nan yan gari munganshi domin kuwa bayqn batqn yarima aka nada kanin mahaifinshi wato sarki samaila lamido wanda baida mutunci ko kadan....mai rake yatsagaita yace kagqnni nam nima bafadene a gidan tun zamanin sarki mahmudu amma tunda aka nada kaninsa nabar gidan nadawo tallar rake dan tafimin muhimmanci dan ma ha inceni na kwarai wlh idan kaga yanda yamaida masarautar zakaji tausayin wayanda kw rayuwa aciki dukda uwar yarima saboda bakin jaama yake tsoro yasa ana kula da ita amma kam akwai gyara malam sabiku da idanshi har yakawo kwallah yace Allah sarkine in Allah ya yarda wata rana sai labari bari indan leka gida gobe zandawo shan rake......._
πŸ’πŸ₯€πŸ₯€ *_MUNTAZ..._* πŸ₯€πŸ₯€πŸ’

*written by MAMAN AHMAD*
*(mardiyya kaoje)*

*DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

Page 21-25

*kuyi hakiri da rashin post dina jiya naje asibiti ne ina godiya da sakon gaisuwa da kuke aikomin luv u all my fans*

_malam sadiku na barin gurin yawuce gida koda yaje yarima yana lambu yana kallon tsuntsaye malam sadiku yayi sallama yazauna bayan sun gaisa yakora mashi bayanin koma ran yarima yayi matukar baci kuka yake kamar mace yanason kanwarshi sosai ta tafi tabarshi ga mahaifiyarshi ba lafita haka zaiyita zama bazai yiwuba gaskiya tashi yayi yace baba kahada kayanka mutafi kano gaskiya bazan iya zama har wani lokacinba inason ganin halin da mahaifiyata take ciki dakatarda shi malan yayi yana bashi baki da nunamashi irin hadarin dake akwai idan yanuna kanshi komai baba samaila zai iyayi don yaga yakawar dashi daga doron kasa dakyar yasamu yareema yayarda amma gaskiya bazai jimaba yace malan sadiku yayi murmushi nan dai yafara bashi magunguna na tsari yakuma bashi magani wanda zai manta koshi waye danso yake yayi bincike sosai saboda susan yanda zasu bullowa lamarin dan yaga yarima yanason basu matsala yarima haka yadowa kamar jinjiri dabaisan komai ba yamanta duk wani abu daya faru dashi tun farko kawai yanzu yasan dai tare yake da babanshi kuma suna fita farauta tare tun yarimq bai sabq ba har yasaba malan kuwa yakan tafi kano dan nemo labari har shirin almajiri yayi dai dai baba samaila yafito haka yasa akama malqn korar kare yacicci mishi mutunci sannu a hankali malan yafara sanin halin baba samaila da kuma abinda zai iyayi dan yaga baida mutunci ko kadan kuma yahada kai da mai raken nam_

_sun hada kai dan malan yakaishi yaga yarima kuma yabashi labarin komai tundaga farko har karshe yakoma a matsayin bafade a gidan ba wanda yatuhumi wani abun dance masu yayi rashin lafiya yayi shiyasa kwana biyu baa ganshiba malan yakan hada magunguna yanaba bafaden yana kqima maman yarima wato umma sosai take samun sauki saidai har yanzu bata magana amma komai takanyi dakanta shidai baba samaila baiso hakaba kuma yqna makikin yanda akayi take samun lafiya dqn duk magungunan da aje rubuta mata asibi canzasu yakeyi tanabata wanda bana kwaraiba ko yasa ayi mata over dose mama kuwa matar baba samaila mulki take zubawa son ranta wani lokacin abincin da bayi keci take cewa akaima umma maryam takanyi kuka sosai itama mijinta yasaketa ashe dama dan sarautarsu ce yake sonta auransu da wata biyu yasaketa wulakanci iri iri da gori bawanda mama bata mata itada malika yarta wato matar yareema maryam kullun cikin kuka take umma kuwa janta take ta rungume tana buga bayanta alamar lallashi amma bata magqna maleeka dukda yareema baisaketa ba shekw ayarta takeyi son ranta ita adole mijinta yamutu koma bai mutuba malamai ai sunce idan miji yqgudu yabar matarsa takanyi wani auren intanaso to itakan bazata tsaya jiran gawon shanu ba iskanci iri iri takeyi har wankinta takesa maryam tamaidata kamar baiwarta kunci sosai maryan tashiga bata samun lokacin kanta sai dare itace share share wanke wanke wanki kaiko bayi basayin abinda takeyi_

**********************************
_*bayan wata biyar*_
_muntaz yanzu suna third term sunkusa zanq jarrabawar shiga jss 2 muntaz batada matsala makaranta harso take hutu yacika takoma dan zaman gidan yanzun yanaso yamata wuya duk aikin gidan itakeyi har abinci da shekarunta shabiyu idan tayi korafi sai mama tace ai itace karama muntaz yarinya mai hazaka gason surutu idan tasamu wanda keyi saidai batacikq haniyaba doguwace fara gashinta saboda tsawonshi ko kitso batayi kashi baki kirim kamar ansa relaxer duka yarinyace dole kasan tanada hips dan har kunyar fita faloma take batada hijab nono daine yanzun tafara kirgan dangi ga idon nam nata kamar zasu fado kai badai sainq wahalda kainaba ku kwatanta da kanku mahaifiyar muntaz balaraba ce yar sudan mahqifinta kuma bafulatani dan usulin yola a daddafe taga hutu yacika takoma domin wahalarda takeshe hoton YAYA JANNU... kullun saita kalleshi tayi murmushi tace ko ina katafi kabarni ibata kewanka Allah yasa suk inda kake kaima kana tunani na ta goge kwallah tamiyar cikin jikka hakadai rayuwa taci gaba itada kawarta bahijjah kowa yasansu gurin kyau da ilimi ga farin jini son kowa kin wanda yarasa danko bahijja badaga bayaba saidai ita batada tsawo sosai kuma tada dan jiki_

_yarima yazan dan dawa domin yanzu yakware sosai gurin harbi harda dare fita yakeyi sosai malqn yake jinshi kamar dan cikinshi yana kuma nuna mashi magungunq na gargajiya kadanne yanzu baisanibq wani lokacin dakanshi yake debowa yanasha yayi haske sosai kwarjininshi yafito baida damuwa ko kadan namijine wanda duk wata macce zataso ace mijinta ne dogone sosai yanada faffadan kirji farine wanda farinshi kamar farin yan china yake idanunshi manya ne dogon hanci ga gashi baki sidik kwan kan girarsa da kuma kansa bazakace yarima yana kiba ba kuma bazaka kirashi ramanmeba idanuwanshi sun kasance kamar na mage yarima bayason surutu ko kadan yanada zuciya sosai idan yayi zuciya ko magana baya iyayi yanzun daya yasamu wata shiddah malan kuwa duk wani bincike dazaiyi yayi umma kawai yake jira takara samun sauki koda nan da wata dayane saidai sole zaiyi kewar yarima dabadon kada yayi sonkaiba dabazai taba bari yarima yakoma kano ba yanzunma daji ya aiki yarima yasamoma umma maganinta yahada yace zaiyi tafiya kwana biyu zaiyi yadawo yarima baidamuba dam yanzun yasaba da dajin ba abinda yake tsoro danko tarmani bai isa yatako cikin gidanba balle wasu halittu saboda tsarii haka malan yafita yayi kano dan koba komai dama yanakaima manya magunguna suna biyanshi dasu yakeci yakesha idan zai dowa yayo cafene dayake yaita girkinshi shi keyi hakanan sunaci yarima tun bayajin dadi har yasaba_

************************************
_muntaz anyi hutu tadawo gida kowa yana falo zaune harda yaya najeeb yadowa karatunshi muntaz taji dadi sosai dan tasan zata samu sauki sosai najeeb kallonta kawai yakeyi yanda tagirma sonta yana kara karuwa cikin zuciyarshi danshi yasan ba babansu dayaba auren muneera ne yatashi kanwar najeeb wacce ke bima nasir yanzun saura sati daya shirye shirye kawai akeyi najeeb dayake yafara aikinshi yanzan babban lawyer ne shimasu duk ashoben daakayi kala kusan hudu muntaz kuwa dakin najeeb ma take fira dan ita duk daukanta uwarsu daya ubansu daya har kan gadonshi take hawa shikuma najeeb yanaso tadan kara wayo yagayamata amma yanzun zai fara fadawa abba kada wani yarigashi idavn tafada jikinshi har wani yar yakeji amma ita ko ajikinta har wasan jifa sukeyi da filo hakadai biki yazo aka fara event itadai muntaz batason haniya sosai ko kida haka shiyasa taki zuwa dinner tayi kwancinta falo abbane yashigo shida mama sai banbamin fada yakeyi baima lura da muntaz dake kwance ba cewa yake wai nafisa kinji iskancin yaron nan najeeb ko wai muntaz yakeso kinjifa gaban muntaz ne yafadi har zatayi magana taji abban nacewa so yake yarona mana asiri yarinyar da tariga tayarda mune mahaifanta zaiso mana da wannan shashancin muda mukeso muci dukiya kawai nandai yashi zaiyono duk wani sirri da muntaz bata saniba mama tace ai alhaji kabarni da dan isk...... Bata karasabata hango Muntaz tsaye tana hawaye tana kallonsu tana girgiza kai zare ido sukayi gabadaya kamar sunga fatalwa_

_zurawa tayi da gudu tayi waje dagudu abba yabita yace kada mai gadi yabari tafita nan yasa aka kamota tanata tsulle tsulle tana kuka mai ban tausayi kulleta sukayi a daki ranqn taci kuka harta gaji tana cewa me abbana yamaku dazaku kasheshi kumaidani marainiyq da gatana sai lokacin take tuna irin banbancin da ake nuna mata ashe duk komai natane qmma ake wulakanta ta aiko ko dan kisan da sukama mahqifina wlh bazasu cimma abinda sukesoba nafison ingudu inshiga duniya da inzauna da wayanda suka rabani da duk wani farincikina tashi tayi tana leke leke taga ko akwa hanyar dazatabi abba kuwa harsa masu gadi yadauko mata kofar daki hoton yayanta jannu kawai tadauka sai wayarta tasa dogon wando da riga sai dan karamin gyale tayafa akanta yanda zataji dadin gudu tadauko hijaba tadaura a kugunta sai kudinda najeeb yabata dan tayi siyayya dubu ashirin tasa a aljihu tasan zasuyi mata rana tasamu biro da pepa ta rubatama najeeb yar wasika_

*_yaya najeeb kayi hakuri natafine saboda wani dalili wanda nasan kasanshi nicedai bansani ba sai yau kada ka zargeni inason kayi tunanin komai na aikata ayanzu dai dai ne bazan iyi cigaba dazama cikin gidan namba nima INA SONKA idan harda gaske kakeyi kana sona zankiraka kuma zan aureka kajirani zandawo gareka ALKAWARINE komin daren dadewa zan dawo idan kaga na shekara biyar bandawoba to kayi aurwn isan nadawo daga baya saimuyi aure idan kuma mutuwa nayi ka yafeni nagode da kulawarka gareni da soyayyarka sai watarana I LOVE YOU TOO YAYA NAJEEB daga MUNTAZ....._*
πŸ’πŸ₯€πŸ₯€ *_MUNTAZ..._* πŸ₯€πŸ₯€πŸ’

*written by MAMAN AHMAD*

*(mardiyya kaoje)*

*DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION*


Page 26-30

Jaama kuyi hakurin rashin jina kwana biyu wasu yan uzurine suka hana ku jina da fatar zaku fahinta tanks....

_bayan taajiye wasikar tadauki hoton yayanta JANNU tasa cikin yar karamar akwati tasa yan kayanta kala kusan biyar da sauran abin amfani tashiga toilet tabude window din tajefa akwatin ta katanga ita kuma tahau kan zink tafara zura kafafunta kan katangar sannqn tafiddo kanta tahau katangar ta dira kasa dayake katangar akwai kwalabe daakasaka duk tajima hannuwanta amma ba sosaiba ajwatin tadauka tafara gudu tana waiyaye gurin yayi duhu tunda har anyi ishai kuma bayan gida basuda nisa da daji haka take tafiya tadora akwati akanta tana kuka tarasa tunanin me zatayi tsorone yafara kamata dataga hasken fitilu suna zuwa gudu takeyi tana waiyaye saitaga sunbiyota a guje a can cikin gida kuwa anje kaimata abinci akaga batanam ga inda ta dira nam dan saida tacire net dimm window din hankalin kowa yatashi nan abba yace maza yaranshi subita najeeb yana dawowa yaji munmunan labari saida abba yamashi mari uku sannan yanunashi yace duk kaine sillah kai kajawok komai to tagudu munyi wahalar banza kenam najeeb arikice yawuce dakinta yana sambatu yana cewa haba muntaz ya zakimin haka yana goge hawaye kan gadonta yazauna can yahango takardar yafara karantawa yana hawaye yana murmushi yace ni kuwa zanjiraki koda shekara darine ke kadaice wacce nakeso_

_muntaz gudu takeyi kamar me ga akwatinnan tana cikin gudu taji anjawota da karfin tsiya ta zubaxwani irin ihu wanda yasa duk dajin ya amsa akwatinta tayi wani gefe rungumeta yayi yace yar iska koda zamu maidaki wlh sai mun fanshi gudun dakika samu nan yashiga kokarin cire mata riga yasa hannunshi yabarka rigan daga ita sai bra yafara shafata sai ihu takeyi tana rokansa amma inahh shi yafita hayyacinshi biyun suna tsaye suna dariya suna cewa ka gama da ita muma ka miko mana idan mutuwa tayi shikenam saimu gayawa oga kawai munsamu tamutu shikenam muntaz taji yana neman cire mata wando ta gantsara mashi cizo tasheka da gudu nan suka mara mata baya suma tagaji iya gajiya hartafara danasanin barowarta gida tuntube tayi da katon dutse tafadi kasa aiko yana zuwa yadanneta yatabata haka yasa hannu zai cire wandon sai ihun dayansu yaji koda zai juya basu ba alamunsu yatashi yana lauwali, dauda amma yaji shiru yafara yada fitila yagansu kwance babu rai nan shima yaji abuga mashi wani abu sai kasa nima abin yaban tsoro nafara jada baya saiga yarima nagani yaciccibi muntaz wacce tuni tasuma kafarta da kanta suna fitarda jini sakamakon faduwar da tayi haka yaukota da akwatinta dan tun kuwwar da tayi farko yaji kuma yake biye dasu yana mamakin abinda yakawo macce a dajin nam dayake bukkah biyuce yakaita dakinshi yakwantar yadauko tsumma da ruwa yana goge jinin yasa garin magani duk abinnan dayakeyi baiko kalli fuskarta ba shidai yasan kawai yataimaketane saboda Allah_

**********************************
_yaranda abbah yaturo ko dakyar suka tashi da jan jiki suka koma suka gayawa abba wai aljani yashiga mata fada kuma koda suka baroma kamar bata numfashi tamutu saida yamasu mari biyu biyu yace sakarkarun banza nabaku awa ashirin da hidu ko amace ko a raye ku kawomin ita inba hakaba ranku zaiyi mugun baci dan bakusan irin asarar da zaku jawominba sakarkarun banza ba aljaniba ko uban aljanine ba ruwana kuna jina ko nan kowannensu rikeda kunce sukace yess boss suka fice tsaki yayi yadubi mama yace kinga abinda sakaran danki yajawo mana ko ni anya kuwa najeeb jinana ne kuwa tashi mama tayi tace bangane me kake nufiba idan bajininka bane jinin waye nanfa fada yakaure sujayi kaca kaca kowa rai bace yawuce dakinshi najeeb yana jinsu yashae hawayen bakinciki yace tabbas idan muntaz ta rasu dole sai ya bimata hakkinta indai har bata kirashiba tozai dauki matakin daya dace dasu abbah dama duk wanda yakeda hannu aciki yawuce dakinshi shimq najeeb yarone nutsatstse wankan tarwada ne yanada tsayi ba sosaiba yanada daidai gwargwado duk macce zatasoshi baida makusa duk cikin yayan shikadaine yafita daban_

_yarima bayan yasa mata magani yadawo saman kanta kuwa yasa yasamu kyalle yadaure duk idanshi bakai ga fuskartaba danshi macce bata gabanshi balle wannan jinjirar dako nonon kwarai batada bayan yagama yakomq gefe yana hada wasu magunguna tari tafarayi tana shure shure tana fadin dan Allah kada kalalatamim rayuwa kokarin fadowa takeya yasa hannu duka biyu yatarbota tafada kirjinshi kura mashi ido tayi kamar mai neman wani abu kallon mekike kallona yake mata amma bata daina kallonshiba dayaga abin harda rainin wayo yasa yadirata kan katifar kwara saida tayi kara yaja tsaki yayi waje binshi tayi da ido tanason tuna ina tasanshi komai kama dashi tome yakawota nam sai yanzun take tuna abinda yafaru tace komadai miye wannan daga ganinshi dan wulakanci ne miye kuma na tsaki don yataimakeni bashi zaisa yanemi yamun wulakanciba ji tayi yace ai zaki iya tafiya tunda kinsamu sauki domin nataimaka makine dan naga kina bukatar taimako amma baga ke sam bakisan mutunciba tashi kifita nace yadaka mata tsawa idanunshi har sunyi jah daga taimako zata nemi taraina mashi wayo itakuma kallonshi take tana ayyanawa aranta amma daikam yanada kunne yaakayi yaji abinda tafada tsawanda yadaka matane yadawo da ita hankalinta_

**********************************
_get out i said now dasauri tasauko har tana tuntube zata fita yace who d hell do you think zaki barma wannan akwatin jiki na mazari tadauka tana hawaye hartakai kofa tajuyo takalleshi aiki harhada magunguna kawai yakeyi da alama batama dameshiba tari tayi ya dago kai tace dan Allah kayi hakuri wlh bansan inda zanjeba idan nabar nam kuma inajin tsoron dajin nam kataimakamin dan Allah kallon sama da kasa yamata yace zaki fita kosai nataso kin fita tayi tanata kuka wani mugun haushi tabashi yataso dasaura yajata daga ita har akwatin nata yajefar waje kayan ciki suka watse yakulle kofa kuka takeyi sosai tafi minti 30 gurin saiga malan sadiku yadawo da mamaki yake kallonta tana ganinshi tafara jada baya tana dan Allah kada kacutardani basan inazan dosaba ka taimakamin pls tausayi tabashi yace yarinya daga ina kike haka nan tabashi labarin yanda akayi yarima yadaukota yajinjina kai yace oya dauko akwatinki nan mta harhado tabishi yarima yanajin sallamar mallam yazo yakarbi kayanshi yana masu sannu dazuwa kallon mara kunyar yarinyar yayi yawatsa mata harara saida cikinta yayikara ta labe bayan malam dariya malan yayi yace haba yarima kanaso kabata ladarka inakai ina biyema wannan yarinyar bayan sun zauna kan tabarma ne mallan yafiddo da abinchi sukaci dayan cefane dayayo masu yarima dai fuskar nan murtuke sarauta tatashi dama bayason raini_

_malan ne yakalleta yace yasunanki tace fatima amma ana kirana da MUNTAZ... malan yakalli yarima saiya tuna lokacinda yadauko yarima sunandaya fara fada kenam sannan kuma daga baya yace JANNAH... yarima kan ko ajikinshi hakalinshima yana wani gun malan yakalli muntaz yace meyakawoki nam hawaye tagoge tagayamashi komai ba malan ba harda yarima saida idanshi yakawo ruwa amma bai bari sun luraba lallai yarinyarabar tausayice malan yagyara murya yace to yarinya kinga mudai anan cikin dajin muke rayuwa zaki iya zama damu??? daga kai tayi dan tasan kota fita anam batasan inda zatajeba amna tanajin zama da wannan miskilin nan tasaci kallonshi yamaka mata harara ta duke kai tana tunani aranta dawa yake mata kama malan yace zata zauna dakin yarima shikuma yadawo dakin malan danshi malan baima cika zamaba yarima kamar ya hadiye zuciya ua mutu gaskiya yarinyar nam tamaji dadin wlh yayimata kallon zaki gane kuranki tundaga lokacin muntaz ita takeyin abinci taji dadin yan kayanta data dauko idan sukayi dauda tawanke harda na jikinta kala shiddane dakuma kananan kaya sai kayan kwana da hijabaiya da kayan kwalliya dan abinda baa rasaba dai kwananta uku amma gaisuwa kawai ke hadata da yarima_
πŸ’πŸ₯€πŸ₯€ *_MUNTAZ..._* πŸ₯€πŸ₯€πŸ’

*written by MAMAN AHMAD*

*(mardiyya kaoje)*


*DABAZARMU WRITERS ASSOCIATION*


Page 31-35

*Godiya da tarin gaisuwa ga masoyana da littafaina kuna bani kwarin guiwa sosai nagode kwarai da kaunarku gareni*

Zara surbajo
Zainab kaoje
Hauwau jega
Hauwa nijer
Maryam kaoje
My besty maryam ishaq
Da sauransu duk ina gaisuwa da godiya gareku

_bayan sati daya da zuwan muntaz gidan tsakaninta da yarima gaisuwa malan kuwa haka yadauketa kamar yarsa yakanfita zuwa cikin gari yabarta da yarima bayan yayi mashi nasiha da dan Allah yadauketa kamar kanwarshi yace idan malan baya gidan Munta adaki take wuni bata fita ballantana ma tahaduda miskilin can abinda bata saniba yarima kuwa fitarshi yake yaje can cikin daji abinshi baya dawowa sai bacci itaduk aganinta yana gidan yasa batajin tsoron komai abinci kuwa itakadai takeci shibayaci tun tanayi dashi harta daina kwance take gurin karfe shabiyun dare fitsari yatasheta sanye take cikin kayan bacci riga da wando iya guiwarta tafito tayi fitsari tajuya kawai taga mutun yashigo gida kuwa tayi ta haska fitila bata daga takalli komiyeba kawai dai ta haskashi marinda tajine yasata dagowa dasauri rike da kuncinta hawaye na zuba yarima tagani tsaye fuskar nam kamar zaki yace ke mahaukaciyar inace zakizo kina mana ihu kuma dan tsabagen rainin wayo kirika haskani har cikin ido wlh sai nayi jifa dake cikin dajin nam wayasanima ko karya kikeyi yawon iskanci kika fitoyi baki samu saaba sauke idanta tayi tace kayi haku yaya dan Allah tajuya cikin kuka tashiga dakinta wani irin abu yaji huyawa yayi yashige daki_

_kuka muntaz takeyi sosai tadauko hotonda yazame mata kanar ibada tana kallo tana hawaye wata bangare na zuciyarta kuma tana tuna najeeb domin shikadaine wanda takejin dadinsa amma tagudu Tamarshi share hawayenta tayi tace insha zandawo gareka inasonka nima a gurin yarima kuwa a zahirin gaskiya tabashi tausayi amma yarinyar ne tacika rainin wayo yau kan koina baitafiba zaune yake karkashin bishiya itakuma yunwace ta addabeta yasa tafito dan ta dora ko jelof ce doguwar rigace baka tasa tayi rolling da dan kwalinta tashiga kitchen dakayi da langa langa girshi taganshi zaune saida gabanta yagadi amma tadake ko gaidashi batayiba tawuce kitchen takunna dan karamin risho dake ciki tadora abincin nan tayi zaune harta kare yarima kuwa kamshin abincin nata duk yacikq mqshi hanci sai lasar baki yakeyi gashi dama yunwa yakeji sallamar malan ce tasa yasaki murmushi yasan dole dai tazobo musu fitowa tayi takarbi kayan hannun malan tana maahi sannu dazuwa yakalleta yace fatima babu dai wata matsala ko kallon yarima tayi wanda shima yake kallonta wata faduwar gaba taji wanda yanzu yazama mata jiki indai suka hada ido kirjinta zai rika dokawa ne batasan dalili ba amma tabbas tanajin kamar akwai wani kusanci tsakaninsu dashi dabiunshi da wasu abubuwa nashi suna mata kama da yayanta jannu kauda kai tayi tace bakomai abba nan yabata wayarta data basuwa yasa mata chaji dakuma pawer bank da sabon sim card jiki na mazari ta karba saboda murna har hakoranta kana gani ta matsu takira yayanta najeeb dan tasan yana cikin wani hali yanzu bayan taajiye kayan da malan yashigo dasu taje tasamu plate tadebo masu abinci kamar zai fuske amma yakasa nan yafara saka loma yana mamakin yarinya da ita amma ta iya saka loma dakinta tashiga tasaka sabon layinta da kati takira najeeb_

***********************************
_zaune yake kan gadonsa abin duniya sunmai yawa yau kwana takwas da tafiyar muntaz amma bata kirashiba wayarshice tayi ringim bakuwar nomber yagani dasauri yadauka kukanta kawai yaji jikinshi harbari yakeyi yace muntaz kina inane dan Allah kigayamin zanzo yanzun kinji goge hawaye tayi tace yaya basai kazoba I'm safe here nd happy too i have a family here i just want here your voice das All fuskar tausayi yayi yace are u sure baby I'm so worried about you murmushi tayi tace yaya kada kadamu everithing will be all right nisawa yayi yace ok amma batun skull dinki fa daga ido tayi sama tace i will think about it kozan koma ba Turkish ba saidai kanemomin wata ok kawai yace kintafi da atm dinki ehh tace ok zan maidamaki salari dinki aciki insha Allah zanga lawyer dinki saikirika laluririnki amma promiss me bazaki bata rayuwarki ba baby kinji idanma bazaki damubq nizan samo maki gidanda zaki sauna nasamo maki mai aiki ok tace amma yaya ba yanzunba nafison abba yadauka na mutu tukunan zamudai rika magana kada ka yarda wani yasan muna waya haba baby aiba wanra zaiji zanyi kiranki anytime idan nata ehh yaya zaka iya amma kayi a hankali kada agane nan tagayamashi yanda abba yaturo mata yan daba wani mugun rakaivivda kishi yaturnukeshi yace sry baby in Allah yayarda komai zaizo yawuce u will b happy kinji murmushi tayi tace thank you yaya sukayi sallama nan take yatura mata katin 5000 tayi godiya kiranda malan ke mata yasata ajiye wayar ta fito_

_naam abbah gani shine abinda tafada kallonta yayi yana tuna wasu abubuwa dasuka faru dashi shekaru tara dasuka wuce da yarshi bata yarasuba da ba abinda zai haba yace yarshice dan kamarsu daya da matarshi gani abba takara cewa yasa yadawo daga tunanin da yatafi kallonta yayi yave yanason tagayamashi duk wani avu daya faru arayuwarta kila zai iya taimaka mata ta wani bangaren abinda kuwa yasa yayi hakan shine duk yakalli yarinyar yakanji kamar akwai wani boyayyen alamari dayakeson yasani koda kila zarginshi yazama gaskiya zama tayi sosai dayake yarima kwance yake kamar mai bacci yana tunanin wasu abubuwa dan malan yafara bashi maganinda zai tuna koshi waye labarinda tafara basuwa ne yasa yatattara hankalinshi gunsu haka muntaz tafara bada duk wani labari data sani dangane

Please Login or Register in order to submit comment