gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Zafin Rana Complete Hausa Novel by Aishat Alto Chapter 15 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zeena a cikinsu, to menene? "

Sai can bayan Magrib Azi ya shigo yace  Yarima lokacin zuwa bangaren Binta yayi.

"Junaid ya kalleshi sannan ya mike jiki a sanyaye, Azi cikin mamaki ya kalleshi, ya dauka zumudi"

"zai hana Junaid mantawa, meke faruwa?"

*******

"Zagaye take tayi a cikin dakinta, gaba daya hankalinta nakan bangaren Binta dan ta tabbatar"

"Junaid nacan tunda kwananta ne, zama tai a bakin gado ta harari kujerar daya kwanta daren jiya, mikewa tai zumbur ta sa mayafi ta fito falo."

Fure da sauri ta taso tace  Gimbiya lafiya?

Zeena ta kalleta tace  Bangaren Maman Rabi zani.

"Ramlatu? Abinda ya fado ran Fure kenan, tace  Gimbiya me zakiyi acan? "

Wani banzan kallo ta mata tace  mu biyu zamu koma banasan kowa yasan inda muke.

Da sauri Fure tace to.

Fitowa tai ta aiki kuyangin dake waje suka wuf suka fice.

Ramlatu na zaune suna hira Fure ta shigo.

"Zubewa tai ta gaisheta sannan ta mata alama data sallami mutanen dake gun, nan Ramlatu ta sallamesh."

Kallan Fure tai tace  lafiya?

"Gani tai an bude labile kallan mai shigowa tai, mamaki ne ya kamata ganin Zeena."

Da sauri ta mike tsaye tace  Gimbiya?

"Zeena ta karaso ta zauna sannan ta kalleta, sallamar Fure tai sannan ta maida hankalinta kan"

Ramlatu tace  Ramlatu kun samo inda Sabisu yake?

Mamaki karara ne ya bayyana a fuskar Ramlatu tace  Sabisu?

Zeena ta hade fuska tace  kunsamo inda yake?

"Cikin mamaki tace  ai bangane bane, me zaki mai? "

Zeena tace  Zaki fadamin ko sai na fita na nufi bangaren Umma karama na fada mata kin amso

magani?

Hankalin Ramlatu ne ya tashi a tsorace ta kalle Zeena tace  bamu sameshi ba amma munji

labarin yana wani kauye wai Bukul.

Bukul?

Zeena ta tambaya.

Ramlatu tace  eh amma da alama Hajjo ta hakura dan bata sake sawa a nemeshi ba.

Zeena ta kalleta tace  kar wani mai numfashi yasan nazo gunki balle yasan maganar da mukai.

Ta mike ta fito.

Suna isa bangarenta ta kalli Fure tace  da gari yadanyi haske kadan kije bangaren Binta kice

Yarima ina bangarensa ina jiransa.

Kallan mamaki Fure ta mata sai dai batace komai ba sai to.

"A can bangaren Junaid kuwa, bayan sunyi sallah tare ne akan sallaya ta kalleshi cikin kulawa"

ganin yanda yai shiru yana dan nazari.

"Hannu tasa a hankali ta kamo hannunsa, kallanta yai sannan yai murmushi."

 Meke damunka Ya Junaid?

Wani sansanyan murmushi ya sakar mata yace  zuciyata ke sanar dani wani abin wanda kuma

bansan kwakwalwata ta amince dashi.

"Hannunsa tadan murza kadan tace  in har bakasan amincewa dashi ko tsoron tabbatar da abinda kake zargi, ka hakura dashi mana. "

Kai ya girgiza mata alamar a a yace  abu ne da dole sai nayi.

Kai ta daga alamar ta fahimta.

Kallanta yai yace  shiyasa nake neman alfarma.

Alfarma?

"Ta tambayeshi, yace  zaki iya jirana? "

"Kallan mamaki tamai na rashin fahimta, yace  zuciyata gaba daya bata nan gun, sannan ina"

"tsoron abinda zan binciko wanda kila ya shafi tsatsona da rayuwata, zaki jira na gama abinda nake?"

Banasan na shiga hakkin daya daga cikinkin ku.

Gaba daya jikinta ne yai sanyi duk da batasan me yake nufi ba amma tasan tabbas abinda yake

tsoro yanada waya a ransa wanda har yasa yake tunani haka.

"Kai ta daga alamar to hannu yasa ya jawota jikinsa ya rungume, tsoron abinda zuciyarsa take rayamai yakeyi."

"Kwanciya ya fara yi ya jawota jikinsa ya rungume tsam, in har mahaifiyarsa nada wani tabo"

baisan ya zaiyi rayuwarsa ba.

Yanda ya matse binta ne yasa a hankali tace  Yaya!

Kallanta yai sannan ya sassauta rikon yace Yahkuri Binta.

"Murmushi tai ta dago kanta ta kalleshi, ganin yanayinsa ne yasa ta kwanta a kafadarsa cikin"

tausayamai.

A hankali bacci ya dauketa.

Junaid kam kasa bacci yai sai can wajen dayan dare ya samu bacci ya daukeshi.

Yana sallar asuba ya kalli Azi bayan sun fito daga masallaci zai mai magana kenan Hadimin sarki

wanda ke jikinsa ya iso gun da suke.

Junaid ya kalla bayan ya gaisheshi yace  Yarima Mai Martaba yace da rana ka shigo fada.

Junais yace to.

"Yana tafiya ya kalli Azi yace  Azi inaso ka tafi neman Sabisu, karka bari kowa ya san abinda kakeyi. "

Da sauri Azi yace  to Yarima. Daga nan ya fita.

Junaid ya shiga bangaren Binta tana zaune kan sallaya tana wa Junaid addu a da fatan dacewa.

Zama yai a bayanta a hankali yasa kansa akan bayanta.

Murmushi tai bayan ta kammala addu arta a tare suka shafa sannan ta gaisheshi.

Kallanta yai yace  Binta kin tashi lfy? Cikin jin dadi tace  lafiya kalau Ya Junaid.

Murmushi yai yace  Da alama Bintata ta fara dawuwa.

Dariya tai tace  Da ina naje?

Yace  kin bari masarauta ta cinye rabinki.

Dariya ta sakeyi shima yana dariya yace  ba haka bane?

Zatai magana sukaji ana magana.

Cikin mamaki ya kalleta ganin yanzu gari ya waye.

Binta ta fito ta bude kofa.

Fure ta gani cikin mamaki tace  lafiya?

Fure tace  Gimbiya ce tace acema Yarima tanada magana tana bangarensa.

"Tsayawa Binta tai cikin tsananin mamaki, Fure ta juya."

"Binta jiki a sanyaye ta nufi ciki, kallan Junaid tai wanda yace  waye? Wai ya akai bakida hadimai"

ne sai wata guda daya da na gani jiya?

Binta ta kalleshi tace  Gimbiya ce ke jiranka a bangarenka.

"Cikin mamaki ya kalleta, Gimbiya?"

Tace eh.

Yanda tai maganar kana gani kasan taji haushi.

"Shiru yai yana tunani, ta samo wani abin ne? Kamar bazai tashi ba har Binta taji dadi sai taga"

zumbur ya mike.

Kallansa tai da sauri tace  ina zaka yaya?

Yace  bari naje zan dawo.

Mamaki ne ya kamata dako magana bai sake mata ba ya fita.

"Kasa motsi tai a inda take, shiru tai tana tunani, yace bazai kwanta da ita ba bayan jiya ya kwana"

"da Zeena, yanzu kuma ya tafi ya barta? Anya Ya Junaid dinta ne?"

Junaid ne ya nufi bangarensa.

Zeena na zaune a falo ya shiga.

Zama yai daga kujerar dake kallan tata yace  ya akai?

Kallansa tai sannan ta dan lumshe ido tace  magana nakeso muyi.

Kallanta yake baice komai ba.

Tace  na samo inda Sabisu yake.

Kallanta yai da sauri sai kuma yace  taya zaki san inda yake a yini daya?

Tace  Shikenan tunda baka yarda ba.

Ta mike zata fita.

Hannu yasa da sauri ya riko hannunta.

Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba yace  Yana ina?

A hankali ta juyo ta kalleshi tace  Yana Bukul.

"Mikewa yai da sauri, yace  inane Bukul? "

"Tace  bansani ba nima haka kawai akacemin, sai dai yanda nasamoma inda yake nima sai ka amince da abinda nake so. "

"Kallanta yai baice komai ba, tacigaba  Kamin alkawarin bani dama nima. "

Dama?

Ta cigaba  Zuciyara zata hakura da rashin san da kakemin kafin aure amma bazata iya daukar kiyayyarka ba bayan aure.

Kallanga yai baice komai ba.

Shiru suka danyi.

"Cikin jin haushin aikar Azi dayai, ya shiga tunanin abinyi."

Kusa da shi ta kara matsowa tace  Meyasa kake nemanshi wai? Kai Da Hajjo bansan me kuke

nema dashi ba.

Junaid ya kalleta yace  Inaji dole na fita da kaina.

*******

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ Š†f[€ ŠfV *

{37}

"Kallansa tai hankali a tashe tace ""ina zaka?"" Ta fada tare da riko hannunsa."

Kallanta yai ya kura mata ido yana nazari.

"Gani tai ya saki wani dan siririn murmushi wanda ya bata tsoro, tace ""ya akai?"""

"""Ba sai naje da kaina ba, tunda bansan ya yake ba balle inda zan sameshi takamaimai."" Gaba"

"daya batasan me yake nufi ba shi yasa ta kasa cewa komai, hannunsa ya zare cikin nata sannan ya fita."

Kasa tsaidashi tai saboda tana tunanin abinda yake nufi a kanta.

"Junaid na fita hadimansa suka biyo bayanshi, bangaren Azeema ya nufa."

Tana daga kwance ana dan matsa mata kafarta.

"Barirace ta shigo ta sanar da ita isowar Yarima, kallan Barira tai tace ""Junaid?"""

"""Eh Gimbiya."""

"Mikewa zaune tai ta sallamesu, Junaid ne ya shigo ya zauna a kasa."

Sai daya gaisheta ta amsa tare da tambayan kwanan matansa.

Suna lafiya ya fada yana kallanta.

"Kallansa tai tace ""da wani abin ne?"""

"Junaid yace ""matsalarku da Hajiya Inna, bakya tunanin ya kamata ki bata hakuri? Halin rayuwa"

"shi ake dubawa."""

"Kallansa tai tace ""Junaid ko na bata bazata taba hakura ba, ta riga tasa abinda takeso a ranta."""

Abinda takeso? Ya tambayeta.

"Dan zamanta ta gyara tace ""a'a kasan in mutum baya san wani kiris yake jira."""

"""Amma da tana sanki ai."""

"Dan murmushi tai cikin waskewa tace ""hmm "" gani batasan cigaba da zancen yasa yace ""ko"

"kinsan Sabisu?"""

"""Sabisu? Waye hakan?"""

"""Awwwww nagane shi bawan Mahaifinka, ya akai ka sanshi?"""

"Dan kallanta yai yana nazari akanta kafin yace "" naji su Hajjo na nemanshi ne."""

"Hajjo? Tai tambayar cikin mamaki, idanu ta zaro da sauri, sannan ta sauke idanta kasa saboda"

"karya gane, yace ""eh bandai san dalilinsu ba."""

"Yake tai tace ""Allah sarki."""

"Har ya mike yace ""naji yana wani kauye wai Bukul."""

"Mikewa yai ya mata sallama ya fita, yana fitowa Falo ya bi bayan kofar da kallo, yace ""Umma dan"

"dan Allah ko menene karya zama akwai ki a ciki."""

"Tunda ya fito ta kasa ko motsi, meke faruwa?"

"Fitowa yai ya koma bangarensa, bangaren Zeena ya fara shiga sai dai batanan, hakan yasa ya"

wuce bangaren Binta yana nazari.

"Binta na zaune a bakin gado duk abin duniya ya isheta, jin motsin yasa ta fito da sauri."

Tana ganin Junaid ne taji wani dadi ya zo mata wanda har taji idanunta na neman kawo ruwa.

"Mamaki ne ya kamashi, a hankali ya tako inda take, yana karasowa ta rungumeshi."

"""Ya akai?"""

"Tace ""bakomai."""

"Dagota yai a hankali ya zubawa fuskarta ido, a hankali ya sumbaceta, sannan yace ""kinji haushi"

"ne?"""

"Cikin sanyin murya tace ""naji amma kadan"""

"Murmushi yai yace ""wannan karan nayi laifi dafatan baza'a hukuntani ba."""

"Dariya ta dan yi tana neman dan matsawa daga jikinsa ya kara kankameta, tana kallansa tace"

"""bari naga wannan karan wani hukuncin za'ama."""

"Murmushi yai yace ""kenan laifin biyu nai tunda jiya nan na taho da safe kenan kowa namai"

"laifi?"""

"Fuska tadan hade, yace ""zan tafi Binta inada abinda zanyi, nazo ne na fada miki."""

"Jiki a sanyaye ta kalleshi tare da yin murmushin yake tace ""Uhm hmm."""

"A hankalinya zare ta daga jikinsa yace ""kici abinci, sannan zan nemi Harira ta kawo miki hadimai,"

"dan ita ta girma ne amma da ita ta dace dake."""

"Kai Binta ta daga alamar gamsuwa sannan tace ""to Ya Junaid."""

"Sake sumbatar kuncinta yai sannan ya juya ya fita, da kallo ta bishi."

Yana shiga bangarensa yaga Zeena acan.

Tsayawa yai yana kallanta cikin mamaki.

"Tana ganinya shigo ta mike da sauri tace ""Ya Junaid me kake nufi? Wai me kake san ji gun Sabisu?"""

"Kallanta yai yace ""kije ki sanar da Hajjo inda Sabisu yake, da alama itace take nemansa ba ni ba."""

"Kallan mamaki ta masa tace ""bangane ba."""

"Shiru yai yana san mata karin bayani sai dai inya tuna yar Hajjo ce sai yaji bazai iya ba, dan ya"

tabbatar daga tayi subutar baki komai ya wargaje kenan.

"Zeena ce ta kamo hannunsa tace ""menene?"""

"Kallanta yai sannan yai murmushi yace ""bakomai kawai ina ganin ita take nemanshi bani ba."""

Shiru tai tana kallansa ta tabbatar akwai dalilinsa nayin haka.

"Shikenan zan fada mata, kallanta yai a hankali yace ""nagode."""

"Dayake bata taba kawo jin hakan daga gareshi ba shiyasa kalmar ta shigeta dakyau, hannunsa ta"

saki gaba daya jikinta yai sanyi.

"Murmushi ya mata yace ""zaki iya sanar da ita yanzu?"""

"Kai ta daga alamar eh, sannan tace ""nagode Ya Junaid."""

Dame?

Kai ta girgiza alamar ba komai sannan ta fita.

"Tana fita ta tsaya a waje, wani sanshi ne yake kara shigarta da darajashi."

Tana kokarin wucewa sashinta taga Harira a bakin kofar Binta da alama abincin safe suka kawo

mata.

"Binta ce ta bude mata hakan yasa suka hada idanu, su Hari ne suka zube suna gaisheta."

"Binta ce ta gaisheta, tana mamakin meyasa batabi ta can baya ba inda zata shiga bangarenta,"

amma sai data zagayo ta nan?

"Zeena ce ta amsa cikin isa sannan ta wuce, Fure ce ta matso da sauri tace ""Gimbiya kina birgeni"

"wato ki nuna mata daga can kike kenan."""

Wani kallo tama Fure batace komai ba har suka shiga bangarenta.

Junaid kam zama yai a kan kujera tare da hade hannayensa yana fatan samun nasara akan abinda

ya shirya.

Shiru yai yana nazari........

******

"Harira na shiga ta kalli Binta, tace ""Ranki ya dadw inasan magana dake inba damuwa."""

"Binta cikin dariya tace ""lalai Hari muje ciki."""

"Da sauri tace ""a'a nan ma yayi."""

Hadiman sun ajiye abincin sun fita sannan Hari ta kalleta.

"Tace ""Kiyi hakuri da tambayar da zan miki."""

"Binta tace ""Hari ni ki daina min magana haka kimin magana kanki tsaye yanda muka saba."""

"Hari ta kalleta tace ""ba abinda ya faru daren jiya?"""

"Kasancewar ta gane abinda take nufi yasa Binta tace ""eh."""

"Harira tace ""Gimbiya fa?"""

"Binta tace ""bansani ba amma ta kirani tana sanar dani abu ya faru."""

"Harira ta kalleta tace ""Dama tun kafin aure naso na sanar dake amma bansamu dama ba"

kasancewar kuna bangaren Gimbiya sai dai yau naga ya kamata ki sani.

"Kada ki kuskura ki cigaba da sanyin nan da kike neman daurawa kanki, da can kinada sanyi amma abin bai kai haka ba, yanzu ba ke kadai bace agun Yarima, idan har kika cigaba da abinda kikeyi kina zaune wlh Junaid ganinsa ma sai ya gagareki."""

"Cikin mamaki ta kalleta tace ""bangane nida mijina ya gagaren gani ba."""

"""Gidan sarauta kike bayan nan ku biyu ne sannan bayanan matarshi yar sarauta ce jinin mulki,"

"kina tunanin shakuwa da san da yake miki zai dawwama ne?"""

"Binta tace ""Harira Ya Junaid ne fa?"""

"Cikin dan zafi Harira tace ""ba namiji bane? Maza duk inda suke irinsu daya, idan har kika cigaba"

"da wannan halin naki kina zaune sai kin rokama zai ganki, me kike mai anan? Banda ki zauna kullum kina kiransa? Kinsan matsalarsa? Kinsan burinsa? Kinsan abinda ke kasan ransa? Kinsan me yake tunani?"""

"""Taya zansan abinda bai fadamin ba?"""

"Dole a matsayinki na matarsa wacce kuka taso tare sai kin mike kinji menene matsalarsa, na"

"tabbatar shima yanasan sanar dake bayasan saki a damuwa ne."""

"Gaba daya jikin Binta ne yai sanyi, Harira tace ""anjima zan kawo miki hadiman da zasu kula"

"dake."""

Tana kaiwa nan ta mata sallama ta mike.

Shiru Binta tai tana nazarin kallamanta tabbas gaskiya Harira ta sanar da ita.

********

"""Me kike anan? Haryaushe akai auren da zaki fara yawo?"""

Hajjo ta tambayi Zeena dake zaune.

"Zeena ta kalleta tace ""kefa Hajjo dadina dake rashin hakuri, sai kiji ai dame nazo miki ko?"""

Hajjo ta hade fuska tace  menene?

 Sabisu!

Da sauri Hajjo ta kalleta tace  ya ya? Ke a ina ma kika sanshi?

"Ranar ina nan kuke labari da Ramlatu, na samo inda yake. "

Da sauri Hajjo ta matso tace  a ina yake?

 Bukul wani kauye ne.

Kallan mamaki Hajjo ta mata tace  ya akai kika sani?

"Shiru Hajjo tai tana kallanta, Zeena tace  menene? "

 Junaid kikaji yana nemanshi?

Zeena tai shiru badai Junaid abinda yakeso kenan ba? So yake ai zargin yana nemanshi? Kai ta

girgiza sauri ganin abin bai bada ma ana ba.

Kallan Hajjo tai tace  koma menene ni ki fadamin meyasa kike nemanshi?

"Hajjo ta kalleta ta matso tace  Bincike nake san yi, so nake in samo abinda mahaifinki bai isa ya"

hana Zubair mulki ba.

Baki ta tabe tace  wai ke haryanzu Hajjo batun ba Zubair mulki yana nan?

Wata muguwar harara Hajjo ta bata tace  tashi ki tafi gun mijinki da alama nan gaba komai naki

ma gun mijinki zai koma.

Zeena ta mike ba musu ta masa sallama ta fita.

Wani irin haushi ne ya kama Hajjo kafin tai maza tasa a kira mata Zubair dan yazo ya sa a nemo

mata Sabisu.

**********

Junaid ne ya shigo cikin fadar Zagi na mai kiran Lafiya.

Junaid ya shigo sannan ya gaida mai martaba.

Sarki cikin nuna jin dadinsa yace  Matawalle an shigo?

Junaid yace  Eh Ranka ya dade.

Nan su Shamaki da su Waziri da sauransu suka fara gaisheshi.

Junaid ya amsa cikin isa da kasaita irin ta  ya yan sarki.

Sarki yai dan gyaran murya yace  Dama nasa kazo ne saboda a sanar dakai abubuwan da zaka

dingayi a matsayinka ma matawalle.

Junaid yai dan kasa dakai cikin girmamawa yace  to Ranka ya dade.

Galadima ne ya kalli sarki yace  Ranka ya dade naga bai dade da aure ba da nauka za a barshi

ya dan huta zuwa sati biyu.

Junaid kam a ranshi yace ina za a banni na huta ba a san nasamu lokacin bincike?

Haka sukai tattauna sannan suka taso.

*********

"Azeema tayi shiru tanata zagaye a dakinta tana jiran Barira, can Barira ta shigo da sauri, ta yaye"

"mayafinta tace  Gimbiya na sanar ma Gimbiya Safiya, tace ta sanar ma Mijinta yanzu zai wuce. "

Azeema ta jinjina kai cikin gamsuwa.

******

Hajjo ce ta kalli Zubair tace  ka tura kanin nawa?

Yace  eh Hajjo sai danaga tafiyarsa na shigo.

*******

Junaid na kishingide a bangarensa idanunsa a lumshe a hankali naga ya sake yin wani sansanyan

murmushi wanda nace hmmm



******Ayusher ******

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ Š†f[€ ŠfV *

{38}

"Yau kwana biyu kenan da tafiyar Azi, gaba daya Mai Martaba yasa Junaid ya shiga hidima ta ko"

ina.

Yar yanzu ba wacce ya kwana da ita tsakanin Zeena da Binta.

"Yau ya kasance ranar Zeena ne, yana zaune a bangarensa bayan ya kammala abubuwan daya kamata yai, shiru yai yana duba wasu takardu tare da fatan dawowar Azi a wannan rana."

Tun safe yake jiran isowarsa amma haryanzu shiru.

"Kamar da wasa yaji Azi yace ""Yarima nine!"""

"Zamansa ya gyara yamai iso, Azi ya shigo ya zube a gabansa ya fara gaisheshi."

"Junaid ya amsa sannan yace ""ya ya?"""

Azi ya kalleshi ya danyi shiru.

"Junaid yai dan murmushi yace ""bakomai, ko baka sameshi ba akwai masu kawoshi."""

"Kallansa yai cikin mamaki yace ""su wa?"""

"Junaid yace ""inata nemanka ne dan ka samin ido ka dubamin bangaren Gimbiya da bangaren Hajjo, amma yanzu kaje ka huta zuwa dare tukun."""

"Azi yace ""na taho dashi ai."""

Ka taho dashi? Ya tambaya gabansa nadan faduwa kadan.

"Azi yai kasa dakai yace ""Sabisu kanin mahaifina ne shiyasa kana fada nasan inda zan sameshi, yanzun ma dan baiyarda ya taho bane saboda yana tsoron abinda zai faru dashi, sai dana zauna"

na shawo kansa tukunna tuba nake ranka ya dade.

Kallansa Junaid yai yace  Kanin mahaifinka?

Azi yai kasa dakai cikin daukan laifi.

Junaid yace  yana ina yanzu?

"Yana can waje, a boye, bansan meke faruwa ba amma yace  baisan kowa ya ganshi. "

Junaid yace muje na shigo dashi dakaina.

"Fitowa sukai suka je inda Sabisu yake, Sabisu babban mutum ne dan a kalla zai kai shekaru 60,"

Junaid cikin girmamawa ya gaisheshi.

Kallansa yai cikin jin dadin ganin Junaid yace  Yarima! Ashe zan ganka kafin lokaci na yayi?

Junaid ya kamo hannunshi yace  kayi hakuri duk da bansan meke faruwa ba amma nasan dalilin

abinda ya faru ne ka bar masarautar nan.

"Shiru yai tare da sauke kansa kasa, Junaid ya kalli Azi yace  mu shiga. "

"Nan suka shiga Junaid na gaba, su Azi sun ba Sabisu kayan hadimai ya saka, haka suka shigo cikin"

"dari, sunyi sa s suka wuce bangaren Junaid."

"Junaid ne yasa aka kawo mai abinci, sai dayaci sannan ya kalleshi yace  Baba kayi hakuri amma"

na rasa meyasa nake da tambayoyi dayawa akaina game da masarautar nan.

Sabisu ya kalleshi yace  Yarima ya akai ka dawo?

Junaid ya bashi labari a takaici.

Sabisu cikin jinjina kai yace  Alhamdulila da baka dawo ba sai daka mallaki hankalin kanka. Junaid ya kalleshi duk da gabansa na faduwa saboda tsoron abinda zai tono amma yace  Sabisu kasan meyasa mahaifina ya kaini can wani gari? Ba da sanin mahaifiyata ba?

Sabisu yai shiru kafin ya kalleshi yace  Yarima!

"Junaid ya maida jankalinsa kansa yace  ka sanar dani, koma menene zan dauka. "

Ajiyar zuciya yai yace bakomai na sani ba sai dai zan sanar dakai abinda na sani.

Junaid ya tattare hankalinsa kansa cikin danne damuwar dake ransa.

Gimbiya ta dade tana neman haihuwar da namiji sai dai a duk sanda ta haihu cikin rashin sa a sai ta haifi mace.

Sannan abin ya dameta haka ma mai martaba saboda yasan irin san da Gimbiya kema Abdulsalam amma saboda burin zama matar sarki uwar sarki yasa ta ajiye komai ta aureshi.

"Sarki Zubair na tsananin san Gimbiya, haka sukai ta fama amma duk sanda ta haihu sai dai ta haifi mace, daga bayama haihuwar ta tsaya, dan sai datai shekara hudu sannan ta sake samun ciki."

Wannan cikin data samu yazo mata da matsala sabods tasha wahala akansa burin su kawai wannan karan a dace a samu d a namiji.

"Cikin yardar Allah Gimbiya ta haihu ta haifi d anamiji, sai dai abin mamaki da tsoro yaran yazo ba lafiya, tunda aka haifeka bakai kuka ba sannan bakai bayan gida ba, bayan haka yanayin yanda kake numfashinka ba daidai yake fita ba."

"Sai dai wannan rashin lafiya taka Azima ta sa an boyeta, dan inba ni da Mai martaba ba bawanda ya sani a iya sanina kenan."

Sarki yasa an nemo masu magani cikin sirri amma abu yaki yiwuwa.

"Duk an fara cire rai dakai, dan har ta fara hakura akan a sanar da mutane dan da alama bazakai rai ba."

"Kwatsam wata rana Abdulsalam ya ziyarci Mai Martaba, tun daga sanda ya fito daga"

bangarensa 

"Shiru yadanyi tare da dan share kwallarsa, Junaid wanda gaba daya yake jin kalaman Sabisu a"

kwanyar kansa yace  inajinka.

"Sabisu ya cigaba  Tundaga wannan lokaci Sarki ya fara rashin lafiya, sai dai abin mamaki randa ya kwanta rashin lafiya ranar kai kashi, haka dai ya cigaba da daurewa sai dai mu munsan yanda yake jinya, yana jinya kai kuma kana samun sauki, ranar yana tashi daga bacci ya umarci a fara gini a filinsa dake cam wani kauye, tun daga nan kuma lamari sarki ya canza, kullum zaka sameshi shiru yana tunani."

"Ciwon sa baya tashi sai dare, yasha wahala matuka sai dai da safe inka ganshi bazaka gane ba sai dai ramewa dayai."

"Sarki ya hana matansa kwana a bangarensa sai dai adanyi hira sannan su koma. Ka samu lafiya sosai, hankalin kowa ya kwanta banda Sarki dake ta fama."

"Akwai wata rana da ya zauna shi da Shamaki nada bana yanzu ba, tun daga wannan rana Sarki ya canza kwarai da gaske, ya fara janye jikinsa daga kan komai, sai ya zauna yai shiru yana tunani."

"A lokacin kana shekara 7 ciwonsa ya tsananta, har Allah ya dau ransa. "

Shiru Junaid yai gaba daya ya kara sashi a duhu duk da dai ta wani bangaren ya dan warware

"masa wasu abun, kenan shi dan Zubair ne da Gimbiya na gaskiya."

Kallansa yai yace  bakasan me suka tattauna ba?

"Sabisu yace  bansani ba Yarima, sannan sai da mai martaba zai rasu ma Abdulsalam ya kira. "

"Azi, Junaid ya kirashi, da sauri ya shigo yace

Please Login or Register in order to submit comment