gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Zafin Rana Complete Hausa Novel by Aishat Alto Chapter 14 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali tace  Naam

"Azeem tace  kiyi hakuri abubuwan dana aikata miki, sannan inaso kisan zaman masarauta bazai taba yiwuwa da hali irin naki ba. "

"Kallanta Binta tai cikin rashin fahimta, Azeema tacigaba  dolene ki san kanki, ki kuma zama mai"

san kanki.

"Bata gane me take nufi ba, Azeema tace  Duk sanda kikaga bazaki dauki abinda ake miki ba ki"

"tuno kalaman nan lokacin zaki fahimta, sannan a kods yaushe ki zama mai amfani da damarki. "

"A hankali Binta tace Nagode Gimbiya, nasan dalilinki na rashin sona wanda ko wanene bazai so"

"wacce ba a san iyayenta bama, sai dai a koda yaushe ina miki godiya a raina nakin korata da kikai, balle harkika barni na auri Yaya, nagode sosai. "

"Jikin Azeema ne ya kara sanyi, ta kalli su Safiya tace  in lokaci yayi ankai Zeena sai ku kaita. "

Tace  to.

********

" Kin zama matar Junaid daga wannan rana, dan haka a koda yaushe ki zama mai kama kai da kuma kula da mijinki, sannan duk sanda kika ga mijinki yayi abinda bai dace ba ki zama mai kokarin nuna masa. Sarki ya kalleta bayan yazo nan a ransa yace  Allah yasa sadaukarwa da"

auranku danai ya biya mun bukatata.

Zeena tai godiya sannan tai sallama suka fito.

"Hajjo zamu wuce, abinda Zeena ke fada kenan a jikin kofar dakin Hajjo."

Hajjo na jinta sai dai haushin abinda ya faru dazu ya hanata fitowa.

Kanwar Hajjo tace  Zeena muje lokaci na wucewa kece Uwar gida ke za a fara kaiwa.

Zeena ta gyara alkyabarta ta sauketa ta rufe fuskarta sannan suka riketa suka hau guda suka fito.

"Mutane sun cika a gun  yan kai Amarya, sai busa ake ana guda tare da kirari."

Haka suka nufi bangaren Junaid.

Bangarenta wanda yasha gyara ta ko ina.

Suka ajiyeta sannan sai datakai wajen awa daya aka kawo Binta nata bangaren dake gefe.

"Junaid na zaune kan salaya yana tilawa, sai daya gama sannan ya rufe qur anin yahau addu oi"

tare da fatan Allah ya bashi damar yin abinda ya dace a koda yaushe.

Yan kai amarya kowa ya watse.

Zeena ta kalli Fure tace  mikon madubi naga fuskata.

"Da sauri Fure ta miko mata, Zeena ta kalli fuskarta ta kara dan gyagyarawa sannan ta maids"

fuskarta ta rufe.

Binta kam sanin Safiya tace mata yau kwanan Zeena ne tunda itace Uwar gida yasa ta sauke

alkyabar ta ta dauro alwala tai salla.

Junaid ne ya kalli Azi wanda ke durkushe yana jiran Junaid ya nufi bangaren Gimbiya.

Junaid ya tashi ganin wannan ne tuni na kusan biyar da Azi ke mai.

"Junaid ya na mikewa Azi yace  Yauwa Yarima, an gaisheka. "

"Junaid bai tankashi ba suka fito, bangaren Binta ya kalla, harya juya sai kuma Azi yaga ya nufi can."

Hankali a tashe Azi yace  Yarima yau kaine xakaje gun Gimbiya Zeena itace uwar gida.

Junaid ya kalleshi yace  na sani.

"Azi yai kasa dakai, bakin kofarta yaje kamar zai shiga sai kuma ya juga suka nufi sashen Zeena."

Fure haryanzu bai iso ba?

Fure tace  haryanzu Gimbiya.

Zeena haushi ya kamata tace  badai gun yarinyar can zaije ba ko?

Da sauri Fure tace inaaaa ai bazai yiwu ba.

Isowar Junaid aka sanar wanda yasa Zeena jin dadi.

Junaid na shigowa suka fita suka bar dakin dukansu.

"Kallanta yai sannan ya karasa cikin dakin, zama yai akan kujera sannan ya gyara kafafunsa ya"

kishingida

Zeena dake zaune taji shiru hakan yasa tadan bude kanta.

Tsananin mamaki ne yasa ta bude baki tana kallansa.........



* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ Š†f[€ ŠfV *

{34}

"Cikin rashin fahimta Zeena ta kalleshi tace ""Ya Junaid?"""

"Idanunsa na rufe bai bude ba yace ""Hmm."""

"""Mekenan?"""

"Ta fada fuska dauke da mamaki, juya baya yai ya fuskanci gefen kujera yace ""inkinyi sallah ki kwanta, ni bacci zanyi."""

"Idanu ta zaro cikin mamaki, sai dai a matsayinta na maje me aji batasan me zata sake cemai ba."

"Gaba daya ta kasa ko mikewa daga inda take, tafi awa daya a haka kafin ta mike cikin takaici tai alwala tai sallah, kusa dashi taje ta zuba mai ido, shikam baccin sa yake sosai zuciya daya, bakinta ne ya shiga rawa cikin takaici ta juya ta kwanta."

"Jin sanyin gari yasa taja bargo, kallansa tai hanayensa a hade, da alama shima sanyin yake ji"

harararsa tai tace kai taji din.

"Ta juya baya, sai dai sam ta kasa bacci, haka ta mike ta dau bargon ta rufamai ta luluba da zanin gadan."

"Da safe bayan yai sallah ya zauna ya kasa yana nazari, tare da kallan Zeena wacce ke bacci."

Zeena kam baccinta ta shara dan sai da rana ta fito.

"Idanu ta bude cikin bacci, mamaki tai da idanunta suka sauka akan Junaid."

"Yana zaune yana kallanta hannayensa a harde, da sauri ta mike zaune tace  Ya Junaid! "

"Idanunsa na kanta yace  ada bayan Jakadiya dake bangaren Marigayi, a cikin bayinshi akwai"

wanda ya bar masarautar nan bayan rasuwarsa?

Kallansa tai cikin mamaki sannan tace  yaya ya daga tashi dai tambayar da ni kaina bansan ta

ba?

"Ki tuno, kin tabaji anyi maganar wani wanda yabar masarautar nan bayan rasuwarsa."

"Kallansa tai kafin tace  ni dai mutum biyu na tabaji, daya Allah yamai rasuwa. "

Dayan fa?

"Tai dan shiru kafin tace  ban sani ba gaskiya, wasu sunce ya rasu wasu sunce yanada rai. "

Su waye sukace ya rasu su waye sukace yana da rai?

"Kallansa tai cikin dan shakka, sannan tai shiru, mikewa yai a hankali yazo inda take kan gado, ya"

"zauna, yace  wanene? "

"Kallansa tai a hankali sannan tace  nadaiji rannan Hajjo na umartan a nemo mata shi, sunanshi Sabisu, shine mai kula da sarki. "

Shiru yai kafin yace  Hajjo ta sameshi?

Kallansa Zeena tai tace  menene Ya Junaid?

Yace  kawai ina san sanin wadanda suka taimaki mahaifina ne.

"Sam bata yadda da wannan zancen ba, yanda ta dago ne yasa yace  menene? "

Shiru tai a ranta tana neman saita kwakwalwarta sannan tace  Bata sameshi ba a iya sanina

kenan.

Mikewa yai sannan yace  nagode.

Har ya juya zai fita tace  idan na samoma shi me zan samu?

"Juyowa yai ya kalleta, itama kallansa takeyi tace  na tabbatar hanya ta sai tafi taka saboda baka"

"dade anan ba, idan na samoma shi ni kuma me zan samu daga gareka? "

Wani rainanen murmushi ya saki yace  me kikeso?

"Shiru tai tare da dan motsa baki, yace  me? Kwana dani? "

"Kallansa tai zuciyar ta tayi matukar kuntata, idanunta ne suka ciciko tace  in naso haka laifi ne?"

Meyasa yaya kake yabamin magana san ranka?

Kallanta yai sai dai baice komai ba ya juya zai fita.

Daurewa tai tace  karka manta zamu gaida Umma karama.

Bai amsa mata ba yai fitarsa.

Cikin takaici ta sa hannu ta cilar da filo din dake bayanta.

Junaid kam yana fita ya kalli Azi yace  Azi ka nemomin wani sanisu a bangaren Marigayi yake.

Gaban Azi ne ya fadi ya kalleshi yace  Sabisu?

Junaid ya tsaya tare da kallan idansa yace kasanshi ne?

Dasauri Azi yace  a a

"Junaid yace  ka nemomin shi sannan inka san inda yake karka fadawa kowa ko shi kansa, ka sanar dani gun. "

Azi yace to.

Bangaren Binta ya nufa.

Tana ta gyara gadan data tashi daga bacci ya shiga.

Jin motsin bude kofar dakin da take ne yasa ta juyo.

Tsayawa yai a jikin kofar cikin wani irin farin ciki yace  Hajiya Binta me kikeyi?

Ya Junaid!

"A hankali ya fara takowa yana zuwa yasa hannu ya rikota, kan gado ya zaunar da ita sannan ya"

kwanta akan cinyarta tare da rufe idanunsa.

"Shiru tai tare da saukar da kanta kasa, sai dai hakan ya kai fuskarta saitin nashi fuskar."

"Shiru tai tana kallan fuskarsa, wani sansanyan murmushi ta saki tana kallan fuskarsa."

Bai bude idanunsa ba sai jitai yace  irin wannan kure kallo? Ko so kike ki gano munina?

"Hannu tasa da sauri ta rufe fuskarta, kansa ya juyar saitin cikinta, yasa hannunsa yasa ya zagayo"

dashi zuwa bayansa.

"A hankali taja wani dan numfashi, ya.  "

Katseta yai da cewa  jina nake kamar a mafarki.

"Wani murmushi ta saki, tare da yin shiru, a hankali dan karamin bacci ya daukeshi, saboda"

farkawar dayai da daddare yana kokarin gano abinda bashida masaniya a kanshi.

"Hannu tasa a kansa tana shafa a hankali, can tace  nice nake ganin komai kamar a mafarki? Ban"

"taba kawo wannan rana ba a tsayin rayuwata, ina mamaki abinda ke faruwa, a da na dauka a"

"matsayin yaya na daukeka, sai dai tun daga sanda kabi bayan Gimbiya nasan zuciyata da biyu ta"

daukeka.

Kaine dai bansan ko haryanzu a matsayin kanwa nake na a gareka.

"Bata taba zata ba sai gani tai ya juyo ya kalleta, hannu yasa ya turata kan gadan tai baya ta"

"kwanta, matsowa yai kusa da ita ta samanta yasa hannu a kan fuskarta yace  kinasan sani? "

"Hannu tasa ta rufe fuskarta, hannu yasa ya zare hannunta yace  shine abinda yake damunki? "

"Shiru tai sai dai tadan daga kai kadan, a hankali ya turo fuskarsa saitin tata, ya sumbaci goshints,"

ya sumbashi idanunta wanda ta lumshe su saboda wani shauki daya zo mata.

"Kan hancinta ya sake sumbata sannan ya saukar da bakinsa kan nata, dan karamin sumba ya fara"

mata sannan ya kalleta tare da kara kai bakinshi cikin nata.

Me takeji?

"Gaba daya jitai komai na jikinta ya kule, sai da ya gama sumbatarta sosai, sannan ya dago ya sa hannu ya dan kishingida ta gefenta ya kalleta yace  Ni tun sanda nasan kaina nasan ina sanki. A hankali ta bude idanunta da gaba daya suka shanye, ta kalleshi, yace  gani ke ba da wannan"

kika dauken ba yasa bantaba nuna miki ba.

"Idanunta ne suke ciciko, tace  Ya Junaid nagode da kakesan wannan wacce batada gatan. "

Yatsansa ya saka akan lebanta sannan ya hade fuska sosai da sosai yace  meye hakan?

"Kallansa tai taga yanda ransa ya baci, mikewa yai ya zauna fuskarsa a hade."

"Tanadaga kwance tasa hannu ta kamo rigarshi, dan jan rigar tai hakan ya sashi yai baya, tace"

 na daina.

Kallanta yai yace  karki sake

Da sauri tace  to.

Jawota yai jikinsa ya rungume.

"Baisan bacci ya daukeshi ba, ganin yanda yake bacci yasa ta zare jikinta a hankali ta fito ta rufe"

kofar.

"Harira ta gani a waje, ta bude mata, Harira ta kalli kuyangun tace  ku shiga da abincin. "

"Nan suka fara shiga da abincin, Binta ta kalleta, Harira tace  Azi yace yarima yana nan ko? "

Binta ta daga kai alamar eh.

Nan suka ajiye suka fita.

*********

Ta gama kwalliya duk da fuskarta kana kallo kasan ba ta farinciki duk kuwa da kasancewar ta

Amarya.

Kallan Fure tai wacce ke gyara mata kanta tace  Ki aika a cema Yarima na shirya.

Fure ta ajiye comb din ta fita.

"Sai dai ba kowa a bangarensa sai bayinsa, nan suka sanar mata yana bangaren Binta."

Mamaki ya kama Fure cikin jin haushi ta nufi bangaren Zeena ta sanar da ita.

Zeena cikin mamaki tace  mene?

Fure tace  ancema wai bacci yake.

Bacin raine karara ya bayyana a fuskar Zeena ta mike a fusace tace kiramin Bintan.

Binta tasa kaya kenan bayan tayi wanka tana jiran Junaid ya tashi suci abinci dan dama tun can

ma tare suke ci.

Harira ce ta shigo da sauri ta kalli Binta.

Binta tace  Harira ashe kina nan.

Ana magana a waje.

"Binta ta fito, ganin Fure yasa tace  ya akai? "

Fure tace kizo.

Ta juya.

Zeena na zaune a falanta Binta ta shiga.

"Kallanta tai cikin tsananin kishi, sannan ta daure bacin ranta tace  dama tambaya zanyi Ya"

Junaid ya farka?

"Binta tai kalleta, Zeena tai murmushi tace  dazu yace zaije gunki ganin ke kadai kika kwana,"

sannan yace bacci yakeji nasan kila yadan kwanta ne.

"Binta tai shiru ta kasa magana, Zeena ta mike da kyar tace  zauna mana, kefa yanzu matar"

"yarima ce, kiyi hakuri nima ba dadi nakeji ba. "

"Tadanyi kasa da murya tace kinsan maza da ranar daren farko, sai ana komawa baccin safe. "

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ Š†f[€ ŠfV *

{35}

"Binta dake kasa tace ""bakomai nan ma ya isa."""

"Yanda tai maganar Gimbiya ta fahimci taji haushi, a ranta tace kiji yanda naji kema, sannan nasan bazai taba cemiki bai kwana dani ba shima."

Wata zuciyarce tace inya fada fa?

"Binta ce ta katseta da cewa ""zan sanar masa."""

Sannan ta nemi izinin tafiya.

"Tana fita Zeena ta kumburo fuska cikin tsananin kishi, maganar daya yaba mata jiya ta tuno, wato daga cemai me zata samu shine zai fada mata haka?"

*****

"Binta kam tana fita ta nufi bangarenta sam ta rasa me yasa take jinta duk ba dadi, a iya saninta dai Zeena matarsa ce yana kuma da hakkin yin duk abinda yaga dama da ita, to menene nata najin haushi?"

"Turo kofar bangarenta tai, mamaki ne ya kamata dataga Junaid a zaune akan kujera."

Kallanta hai yace  Daga ina?

Tace  naje gun Harira ne.

"Hannunsa ya miko mata, a hankali ta karaso ta rike hannunsa, jiti ya jawota ta zauna akan"

"cinyarsa, yace  Binta! "

Naam!

"Ya zuba mata idoyace  yanzu da da fa ba daya bane, kada ki kuskura ki bar wani ya rainaki, ke matar Junaid ce, ko gunsu Harira karki sake zuwa in kina nemanta ki aika tazo. "

"Tace to, yace  ni dai a iya sanina Binta da ko Junaid bai isa takata ya wuce ba amma tunda"

"kikazo nan kin bari kowa ya rainaki, karki kuskura ki cigaba da bari ana rainaki, in ba haka ba nan"

gaba baki isa ki gyara ba.

Dariya tadanyi tace  ko kaine?

Yace  eh ko nine kimin masifa yanda kika saba da in aka bata miki rai. Dariya ta sakeyi sannan tace  Abinci.

Kallan Abincin yai yace  a bangaren Umma karama zamu karya.

Jikinta ne yai sanyi ta daga kai alamar to sannan ta mike daga kan cinyarsa tace  ana jiranka.

Mikewa yai yace  bari na shirya

"Ya fita, da kallo ta bishi sannan ta zauna abakin kujerar daya tashi cikin sanyin jiki."

*********

"Junaid na fita ya wuce ya shirya, sanye yake cikin dakakiyar shadda kalar gajinare hula ya saka"

sannan ya saka takalmi yayi kyau kwarai da gaske. Yana fitowa ya kalli Azi yace  ki kira Binta.

Azi ya kalleshi sai dai ganin yanda ya hade fuska yace  To Rankanya dade.

Nan ya kalli dayan bawan nasa yace  yima Zeenatu magana.

Nan shima ya jiya da sauri.

Junaid ya karasa sa takalminsa sannan ya fito ragowar hadiman na biye dashi.

"Binta dake zaune inda aka barta Azi ya sanar da ita sakon Junaid, cikin jin dadin hakan yasa ta mike da sauri ta shiga daki itama ta zura alkyabarta, kasancewar karta tsaya kwalliya ta bata ran Junaid yasa ta fito."

"Zeena ce tsaye kusa dashi da alama magana sukeyi, kallan Zeena tai taga tasha uban kwalliya."

Dan murmushi ta kakaro sannan ta nufo su.

Agun Zeena da Junaid kuwa kallansa tai tace  bangane Binta muke jira ba?

Wani kallo ya mata yace  batada hakkin zuwa ne?

 Ba haka bane amma ai 

Yace  badai haryanzu a matsayin wacce batada matsayi a gidan nan kike kallanta ba?

"Ranta ne ya baci ta kalleshi, yace  karki manta kishiyarki ce matar Junaid, a ynzu in aka"

"wulakanta matata kamar ni aka wulakanta, kuma ke ma kamar ke aka wulakanta. "

Shiru tai saboda tama rasa me zatace ta ina dan an wulakanta Binta aka wulakantata?

Isowar Binta ne yasa t mata wani banzan kallo.

Junaid wanda haryanzu fuskarsa a hade take yace  muje.

Haka suka taho suka nufi bangaren Azeema.

"Kallan Zeena yai bayan sun dan yi tafiya mai dan tsayi jefi jefi suna daga hannu in an gaishesu,"

yace  ni Shamaki yaushe ya samu mukaminsa?

"Kara matsowa tai kusa dashi hakan yasa Binta tadan ware kadan da su, tace  sanda Abba ya"

hau mulki. Shamakin da fa?

"Tace yayansa ne saukeshi akai, Junaid yace  Galadima fa? "

Tace tunda shine haryanzu kum 

"Baya tai tana neman faduwa, da sauri yasa hannu yariko hannunta."

"Binta ta kalla wacce gaba daya takeji kamar an wareta, wacce ganin Zeena da Junaid a haka ya kara sa taji gaba daya komai ya tsaya mata."

"Wani murmushin wulakanci ta watsama Binta, sannan ta dago."

Junaid yace  Kina Gimbiya bakya ganin hanya. Ya fada yana saketa.

"Gyara tsayuwarta tai tana  yar dariya kadan, tace  tafiyarce bakaga yau wahala takemin ba? "

Cikin rashin fahimtar me take nufi ya maida kanshi kan Binta wacce ita ta fahimci me take san

cewa.

Junaid ne ya matsa kusa da ita yace  Binta!

Kallansa tai sannan tai murmushin yake tace  Naam.

"Muje, naga ne kin tsaya, kai ta daga alamar to."

Haka suka isa bangaren Gimbiya Azeema wacce take ta jiransu. Da hanzari Barira ta karaso tace  sun iso Gimbiya.

Nan ta kara gyara zamanta tasa aka musu iso.

Junaid ne ya fara shiga sai Zeena sannan Binta.

Gaisheta suka fara yi ta amsa.

"Kallan Zeena tai wacce take ta wani iyayi wai ta kasa zama daidai, sannan ta kalli Binta wacce tai"

"shiru, ta kalli Junaid wanda kamar kullum yanzu fuskarsa daf take."

Nan ta kalli abincin da aka jera sosai a gun tace  kuci abinci zan shiga ciki.

"Nan ta mike tai ciki, Zeena ta kalli Fure tace  Fure zubamin. "

"Fure ta taho da sauri, Junaid ya kalleta yace  ku bamu guri. "

"Nan kowa ya fita, cikin mamaki Zeena ta kalleshi, kallanta yai yace  ki zuba da kanki. "

In zuba?

Ta fada tana nuna kanta.

Dauke kai yai daga kanta yace  Binta bismillah.

Yanzu kam bazata kara bari a maidata  yar kallo ba.

"Da sauri ta jawo plate ta zuba mai abinci, sannan ta zuba nata."

"Spoon ya mika mata shima ya dauka, dariya yai yace  naki wayan shine aka cikamin? Itama dariya tai tace  ya kamata kai kaci dayawa dan Allah nasan yunwa kake ji. "

" Ahhhh na manta ashe kina gane in cikina ya rarake, lalai zanyi dabara yanda bazaki dinga"

ganewa ba

Dan Kallan Zeena tai ta gefen ido wacce ta cika ta batse ko abincin ma ta kasa sawa.

Kallan Junaid kawai take dama yana dariya haka?

Binta ce ta kalleta tace  Gimbiya na zuba miki?

"Zeena tai shiru tana nazari kafin tace  basai kin zubamin ba, tunda ya Junaid yace nashi yamai"

yawa bari muci tare.

"Cikin mamaki Junaid ya kalleta, Binta ta zuba mata ido itama."

Junaid ya kalli Binta sannan ya nuna mata plate da idanunsa alamar t zuba nata ya dauke kai.

Cikin kufula ta jawo plate ta zuba.

Safiya wacce sanda sukazo tana hada kayanta taga Azeema ta shigo.

"Kallanta tai tace  Umma ya kika shigo kika barsu, bayan kinsan mata biyu lokaci daya akwai"

hidima?

Azeema ta zauna tare da cewa  hakan ne yasa na taso.

"Safiya tace  ni Binta nakeji, itada bata magana sosai, Zeena nasan haka zataita kunsa mata"

haushi.

"Azeena ta gyara zamanta tace  intaga ana neman kwace mata miji ta kwaci kanta, zama ka"

"fadawa mutum karya bari amai kaza da kaza bata lokaci ne, in taga mijinta na neman yin nisa da"

ita ta mike.

Safiya tai dariya tace  Umma kenan komai naki sai kin hasaso kike aikata shi.

A falo kuwa haka kowa yai shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa.

"Zeena na jin haushin abinda Junaid ke mata, Binta na kishin yanda Zeena da Junaid ke maida ita"

"yar kallo, Junaid kam tunanin Shamaki da Galadima yakeyi, kallan Zeena yai sannan yace  Waziri fa? "

Fuska ta hade tace  shima tun lokacin Marigayi.

Junaid yai shiru yana tunani.

"Binta ce ta zuba ruwa ta ajiye kusa dashi, kallanta yai sannan ya sakar mata murmushi yace"

 Nagode!

Itama murmushin ta maidamai tare da nunamai wata kwanon agun.

Kallan robar yai sannan yace  a a

Tace  kai Ya Junaid!

Yace  Allah karkici kin manta abinda ya saki?

Da sauri tace  na hakura ba sai ka fadaba.

"Zeena ta kalli kwanon dake cike da gwaza, sannan ta haraeta tare da tabe baki."

***********

Sarki ne ya kalli Shamaki yace  ka gano inda Sabisun yake?

"Shamaki ya girgiza kai yace  haryanzu ranka ya dade, amma wai me yasa kake nemanshi"

yanzu?

"Sarki yace  haka kawai nakejin hankalina ya kasa kwanciya, ni gaba daya yaran can gani nake"

kamar kallan mu yake yana nazari akan mu.

Dariya Shamaki yai yace  karka damu Ranka ya dade na tabbatar yanzu da yke danka kuma

sirikinka bazai kawo wannan a ransa bama.

Sarki ya jinjina kai alamar gamsuwa yace  haka nake fata.

******

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ Š†f[€ ŠfV *

{36}

"A bangaren Azeema ya barsu, fitowa yai ya nufi bangaren Hajiya Inna."

Daga baranda ya tsaya yana amsa gaisuwar Jakadiya.

Junaid ya kalli Jakadiyar yace  Jakadiya ina san magana dake.

A tsorace ta kalleshi tace  To Yarima.

Fitowa tai tabi bayansa har bayan ginin Hajiya Inna.

"Su biyu ne agun, ya kalleta yace  Jakadiya shekararki nawa kina aiki anan gidan? "

Dan murmushi tai tace  tun ina Yarinya nake anan.

Junaid ya kalleta yace  meyasa Hajiya Inna batasan Umma?

"Da sauri Jakadiya ta kalleshi, Junaid cikin yanayin maganarsa ta kasaita ya kalleta yace"

" tambayarki nake, dalilin zuwa na da kaina dan karma kiyi tunanin boyemin wani abu ne, zan iya shiga na tambayi Hajiya Innan da kaina. "

"Hankalin Jakadiya ne ya tashi, ta zube a kasa tace  Yarima! "

Junaid yace  menene dalili? Na tabbatar ba akan ta sake aure bane.

Shiru tai sai da Junaid yai gyaran murya alamar bacin rai.

Da sauri tace  Yarima ka gafarceni amma Hajiya In

"tace tun Marigayi nada rai Gimbiya da Sarki suna san juna, tace san mulki ne yasa Gimbiya taki"

auran Sarkin yanzu ta zabi Sarki Zubair.

Junaid ya kalleta yace  dan tana sanshi ta auri yayansa menene na tsanar?

"Jakadiya gabanta ya sake faduwa, hankali a tashe ta kalli Junaid tace  wannan Hajiya Inna ce"

kawai tasan dalilinta.

Ido Junaid ya zuba mata sannan a hankali yabar gun ba tare da yace komai ba.

"Gaba daya kansa ne ya kulle, dan har bibiyu yake gani."

"Dakewa yai harya isa bangarensa, a daki ya zauna yana tunani, in tana sansa kenan Hajiya Inna"

tana zarginsu da kebencewa bayan anyi aure ko me? In haka take zargi kenan shima haihuwarsa

"akwai ayar tambaya? Wani murmushin takaici yai yace  ta yaya? Ai da ba wanda zai kawo maganar aure na da

Please Login or Register in order to submit comment