gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Zafin Rana Complete Hausa Novel by Aishat Alto Chapter 3 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsowa"

tace  Fure debo ruwancan ki watsama wancen bawan.

"Fure ba tare da musu ba tai hanyar bakin tulun, totulo ruwa tai ta matso kusa da Junaid dake"

"kallan yarinyar ransa a bace, jiyai an shekamai ruwa ba tare da ya ankara ba."

"Wani irin sheka yai sannan ya kalli jikinsa, sannan ya kalli matar, baki ta dan tabe sannan tace"

 Fure karo.

Nan Fure ta kara tutulo ruwa ta kara shekamai.

"Junaid yasa hannu ya goge fuskarsa idanunsa haryanzu suna kanta, wanda ita kuma tasa a ranta"

sai ya daina kallanta zata daina sawa a zuba mai ruwa.

Alama tama Fure nan Fure ta kara debo ruwa ta sheka masa.

"An debo ruwa na shidan ne, Zubair yace  meye hakan? "

"Juyo tai ta kalleshi wanda ya shigo dan gaishesu, daga bakin kofa ya kalleta, kallansa tai sannan"

"ta kali Junaid, ganin haryanzu ya kafeta da ido ta kalli Fure ta kara mata alama, nan fure ta juye shi"

a jikinsa.

"Ran Zubair ya baci ya wuce ciki, yana shiga ya kalli Hajjo yace  Umma kima Zeena magana. "

"Kallansa tai tare dayimai alama akan yai shiru, Zubair ya kalleta sannan ya kalli waje wanda"

hakan yaba Azeema damar fahimta.

Kallan Zubair tai tace  me autar tai?

Ta fada tana kallan Hajjo.

Nan hajjo tace  kiramin ita.

Yana mikewa Azeema tace  bari naje na mata magana.

"Bata jira amsar Hajjo ba tai gaba, nan sauran mata suka mike, Hajjo kam tana tsoron kar Zeena"

ace abu tai mara kyau yasa ita ma ta mike da sauri.

Suna fita waje ana kara shekama Junaid ruwa.

Cikin mamaki da takaici Hajjo ta kalleta tace  Zeenatu!

"Zeena ta kalleta sannan ta kalli matan dake gun, idanunta ta maida kan Hajjo tace  kalli abinda"

yakemin.

"Nan kowa ya kalleshi, ya tsare Zeenatu da kallo haryanzu idanunshi na kanta."

"Hajjo ranta ya baci ta kalleshi, Ramlatu ta matsa da sauri ta gauramai mari tace  ka dauke"

idanka ko sai munsa an dauke mana su yanzun nan?

Junaid ya dago ya kalli Ramlatu yace  mene?

"Azeema kam idanu kawai ta kuramai, ya yake kama da Junaid dinta?"

Wanene wannan?

Zeenatu ta matso tace  mene kace?

Kallanta yai yace  to fadamin mena miki? Me na miki da zaki aikata min wannan abin?

Yai maganar cikin fushi.

"Baki kowa ya saki, cikin tsananin mamaki, yauce rana ta farko da bawa ya taba magana haka."

*Ayusher.*

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Bakwai

"Ran Zeena ya kai matuka gun baci, kara wanka mai wani marin tai ta kara daga hannu zata sake"

"marinsa, Azeema tace  Zeena. "

"Zeenatu ta dakata amma ta kasa sauke hannunta, Kusa da ita ta karaso ta kalleta sannan ta"

kalleshi tace  me zaisa ki nemi tada hankalinki? Bawa yayi laifi ki bari a hukuntashi amma yin hukunci da kanki ai wahalar da kanki kikeyi. Bafaden nan ta kalla tace  a kulleshi kar a bashi abinci yau.

Da sauri bafaden nan ya fizgi Junaid wanda ya zubawa duka mata ido yana san gane wacece

"mahaifiyarsa, wacce tasa a kamasa ya kalla wacce kuma yafi zargin itace."

"Azeema ta bishi da kallo, har suka fita."

"Zeenatu ta kalleta tace  Ai naso na zaneshi kafin a kulleshi wlh, da dabulala zan zuzubamai. "

"Hajjo ta kifa mata wani kallo sannan ta juya ranta a bace, ganin yanda abu baiyi dadi ba yasa"

kowa ya mata sallama ya tafi.

Azeema suna fitowa Barira ta kalleta kadan tace  Gimbiya me yasa kika taimakeshi?

Azeema tai murmushi tace  kina tunanin taimakonsa nai?

Barira tace  haka dai jikina ya bani Ranki ya dade.

"Azeema tai shiru sai can tace  haka kawai nake kallan Junaid a cikinsa, hakan yasa nake tsoron"

"abinda za amai, sai kuma nai tunanin in na taimakeshi nima za a taimaki nawa indai yanada rai. "

Azeema tai shiru tana tunanin lalai rashin Junaid ne yake damunta wanda gashi har ta fara ganin

kamaninsa a kan wanda ta fara gani yau.

********

Hajjo ta zubawa Zeena wata muguwar harara tace  ni wai dan Allah meke damunki? Wato ke

bazaki taba barina na samu kwanciyar hankali ba ko?

Zeenatu tace  yanzu laifina kike gani kenan Hajjo? Kina ganin bawa yana neman maidani kawar

"wasansa, ta yaya bawa zai mun kallo haka? Wanda ko mutane basu isa su min ba? "

Hajjo cikin takaici tace  ba sai kisa a rufeshi a zaneshi a can ba? Kawo shi nan din na menene?

Akoda yaushe in baki kaskantar dani agaban Azeema ba hankalinki baya kwanciya.

Zeena tace  to ni sam haushi daya dameni ba ina nai wani tunanin haka? Gabans fa yaja ya

tsaya.

 Tashi ki ban guri kuma ki cire hannunki daga yi mai hukunci zansa Zubair yamai abinda ya

cancanta.

Baki ta turo cikin jin haushin abinda Hajjo tace  ai wlh ko an hanata sai ta mai rashin mutunci.

"Mikewa kawai tai ta fita ba tare da tace komai ba, Hajjo ta bita da kallo tare da girgiza kai, dole"

tasamu a aurar da Zeenatu shikedai ne zaisa hankalinta ya kwanta.

*******

"Junaid kam na zaune a inda aka garkameshi, guri ne wanda duk kasa ne a gun, sai itace da aka"

"samu akayi daki daki karami wanda kana iya ganin na ciki, dakunan da ake rufe bayi insunyi laifi."

"Daga can gefe ma wani ne a garkame, kallan Junaid yai yasa dariya yace  me ka aikata kai"

kuma?

"Junaid ya kalleshi ba tare da yce komai ba, saboda mugun sanyin dake shiga cikin jikinsa, ga gari"

da sanyi ga kuma ruwan sanyi na tulu.

"Amma wannan wace irin muguntace, me ya mata? Ransa yakai matuka gun baci, muryar na"

gefensa yaji yace  da alama laifi kai sosai harda ruwa?

"Junaid ko kallansa yanzu baiyi ba, ya runtse idanunsa yanajin wani mugun sanyi na ratsashi."

Yaushe zasu bude mu?

"Abinda ya tambayi bawan kenan, mutumin yasa dariya yace  yaushe? Lalai yaran nan ka"

"rainamin hankali, kanaso kacemin bakasan in aka kulle bawa sai yayi kwana hudu ba? "

"Da sauri junaid ya bude idanunsa ya kalleshi, kwana hudu? Bama awa hudu ba?"

"Binta? Azi? Hari? Abinda ya fado mai kenan, yanzu in Azi yai ta nemansa fa?"

In Binga taga bai dawo ba ya zatai? Hankalinsa ne yakai kololuwa gun tashi.

Ya zaiyi?

"Yana nan a zaune gaba daya hankalinsa ya gama tashi, balle dayaga rana ta fadi."

*******

"Wannan littafin na kudi ne, ga duk mai san siya bai san yanda zaiyi ba ya tuntubi number daya daga cikin marubuta na Haske, mungode."

*******

"Azi sai kara duba hanya yakeyi, sai dai ba alamar Junaid, ganin dare ya fara yi sosai yasa ya koma"

"cikin masarautar cikin tashin hankali, da kuma fatan Allah yasa ba wani abin ne ya sameshi ba."

"Abinka da gida katu, Azi duk ya rasa ina zai zagaya."

"Junaid kam gaba daya hankalin sa ya gama tashi, gashi ba wanda yake a gurin sai dakaru."

Ya ja baya yasa kansa akan itacen nan yana tunani.

Kai!

"Abinda yaji ance kenan, da sauri ya bude ido, yarinyar nan ce ta dazu."

Kallansa tai tamai alama daya matso.

Da kamar kary matso sai dai san ta yafemai ta bari ya fita yasashi matsowa.

Kallansa tai tare da yin wani murmushin mugunta tace  Kana tunanin zamanka anan shine

samun saukinka?

Junaid ya kalleta sannan yace  dan Allah kisa a budeni akwai abubuwa masu amfani daya

kamata nayi yanzun nan.

Baki ta sake tana kallanshi kafin ta saki muguwar dariyar tace  masu amfani?

Kamar me da me kenan?

"Junaid yai shiru tace  ayyya ya za ayi dan wallahi sai kayi kwana goma a cikin nan, aso samuna"

"na ma sai kayi wata, zaka san ni Gimbiya Zeenatu ni ka zubama ido. "

"Ta juya tana neman tafiya, da sauri ya sa kansa a jikin itacem yace  kiyi hakuri ki barni na fita. "

Kallansa ta juyo tai sannan tace sai naga kana zubarda hawaye sannan kukan ma sai kayi na jini

tukun na.

Ta juya ta tafi.

"Junaid ya bita da kallo cikin mugun takaici, bawan nan ya kalleshi yace  wai Gimbiya kama"

laifi?

Junaid bai kalleshi ba ya koma ya zauna.

"Bawan yace  yaro kana ruwa, Allah ne kadai zai ceceka wlh. "

Junaid ya kalleshi yace  da gaske saita bari sai nai kwana goma?

Bawan yasa dariya yace  kai daga wani kauyen kake ne? Yo nasan ko a kauye kake kasan abinda

zai yiwu.

"Junaid yai shiru, Bawan yace  ka nutsu in kayi sa a ta sakeka nan da kwana goma. "

Junaid ya runtse idanunsa cikin tashin hankali.

Ta ko ina Azi ya nemi Junaid har alfijir ya fito bai huta ba.

"Ganin abu yaki yiwuwa kawai ya koma bangaren Mai martaba, dole ya fadamai, to amma yace"

me?

"Yana neman komawa yaji wasu da suka fito zasu nufi massalaci suna cewa, kace jiy yaji jiki?"

"Dayan yai dariya yace  nima sai dare naji labari, ai da badan an hana kashe bayi ba inaji yaran nan da sai ya sheka barza u."

Gaban Azi ne ya fadi ya kallesu da sauri yace  wanene yai laifi?

Hannunsa da ya rike ya ture yace  ina muka sanshi? Muma labari mukaji.

Da gudu Azi ya juya ya nufi indai yake tunanin samunsa.

"Junaid na kishingide ya gaji dajin munsharin dayan, ya mike ya zauna, daga nesa ya hango Azi,"

"cikin tsananin farin ciki, ya ke kallan Azi harya karaso."

Azi idanunsa suka ciciko yace  waye yama wannan wulakanci? Waye wannan. 

"Muryarsa ce ta fara rawa saboda karayar zuciya, Junaid ya kalleshi yace  Azi. "

Kallansa yai yace  tunda nasan inda kake bari na sanarwa Mai martaba.

"Idanu Junaid ya zaro yasa hannu ya jawoshi dan kusa dashi, cikin rada rada yace  karka kuskura,"

ka wuce ka koma gida gun Binta dan nasan tana nan hankalinta a tashe.

Ni zan taho da zarar ta budeni.

Azi ya kalleshi yace  yanzu Yar wali kana cikin wannan hali zan tafi gun Binta? Kayi hakuri

amma bazan iya barinka ba. Shima cikin rada yai maganar.

"Junaid ya kalleshi yace  umarni na baka, ka wuce yanzu ka koma gida, in hankalinka bai kwanta"

ba nan da kwana goma sai kazo mu tafi.

"Azi kam hankalinsa ya tashi, ya kalli Junaid zaiyi magana wannan Bawan yace ah wai har gari ya"

fara wayewa.

Junaid ya kallo Azi yace  ka wuce kafin ya mike zaune.

Azi ya juya yana kamar wanda bashida laka a jikinsa.......

********

"Binta dukunkune cikin dakin Yarima sai kuka kawai takeyi, Hari tayi lalashi harta gaji, daga baya ma zazzabine ya rufeta, amma duk da haka idanunta bai bar zubar da kwalla ba, saboda jikinta ya gama bata gidansu ya koma ya barta anan."

"Cikin kuka tace mahaifinki ma ya cillar dake ko nemanki baya yi, ga Junaid shima ya yada ke. "

Kuka ta kara sakawa.......

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Takwas

"Zaune take a bakin gado ta dafa kanta wanda yake sara mata, tabbas yaran nan kamarsa daya"

"da Junaid ba idanunta bane yake mata gizo, mikewa tai a hankali ta fito falo."

Bari na tsaye tana ba kuyangun umarni yanda zasu gyara gidan.

"Tana ganin Azeema ta fito ta nufi gunta da sauri, Gimbiya lafiya? Da sassafen nan?"

"Azeema ta kalleta tace ""Bari kaini inda yaran nan yake, inada tambaya da zan mai."""

"Bari cikin mamaki tace ""wani yaro?"""

"Azeema ta kalleta, ""yaran jiya?"" Bari ta tambaya."

"Kai kawai ta daga mata, nan suka shiga cikin daki, bari ta yafa mata wani dogon mayafi, suka fito."

"Sum sum sum suke tafiyar saboda basa san wani ya gansu, da yake kuma safiya ce kowa na"

"dakinsa, sai bayi suma kadan daga ciki."

"Azi na jingine da ginin hankalinsa a tashe, yana tunanin gaskiya bazai iya tafiya ya barshi cikin"

wannan halin ba.

"Hango mutane biyu sun nufo gun ne yasa ya boye, wucewa sukai, Bari t leka taga dakarun gun"

"basanan, dan dama Azi dazai shiga ne ya aikesu."

"Ciki suka shiga da sauri, bari ta kalli Junaid sannan taga wani a gefe, gashi a kwance amma da"

"alama idansa a bude yake, bari tace ""kuyi magana bari naje can."""

"Tana fada ta nufi dayan gun da yake, bawan Allah tambaya nake."

"Mikewa yai daga kwancen, ta tare saitin da Azeema take ta fara mai tambayoyin shirme, dayake"

mutum ne mai san magana ya biye mata yanata bata labari.

"Junaid ne ya kalleta, ya ganeta, itace ta dazun nan."

Shiru tai ta zubamai ido wanda harya fara tsarguwa.

"Idanunta sun ciciko suna neman zubar da kwalla, gaba daya jikinta rawa yakeyi, gabanta sai wani"

"irin faduwa yakeyi, a hankali tace  Junaid? "

"Kallanta yai zuciyarsa ta fara harbawa, itace kenan? Abinda yazomin a ransa kenan."

Ganin yanda yai da idanunsa ne yasa tace  Junaid?

"Jikinsa ya kalla, ya tuno abinda ya faru dashi jiya a gabanta, kallanta sannan ya wawaiga ya nuna"

kansa yace  ni?

"Jikinta ne ya saki, ta kalleshi a tsorace tace  Junaid? "

Yace  wai ni?

"Hankalinta ne ta tashi ta kalleshi, idanunta suka zubo da kwalla ba tare data sani ba, shima nashi"

"idanun ne suka fara rauni, daurewa yai ya kalleta yace  wani kike nema Gimbiya? "

Kallansa tai tare da goge hawayen tace  ya sunanka?

"Wali ta fada yana kallanta, kai ra jinjina gaba daya jikinta ya mutu, tai murmushin yake tace  a"

ina kake?

"Shiru yai yana kallanta itama kallansa take tace  ba a nan garin nake ba, zuwa nai, sannan"

inada iyaye da kane.

"Shiru tai tana kara kallansa, tace zaka iya cire rawaninka? Kasan kanka zan gani. "

 kasan kaina?

Tace  eh.

Yace  Me kikesan gani? Yai maganar adan raunane.

"Kallansa tai tace  ina duba zan fadama, sannan bakai kama da bayi ba, ko daga kalamanka. "

"Mikewa yai yace  dan Allah Gimbiya ki yafemin, ku barni sa raina, bansan mena aikata ba, yau"

"na fara zuwa gidan sarauta dan Allah ku taimaka ku barni na fita, iyayena na jirana. "

"Jitai kanta yana kara sarawa, da gaske Junaid ne yake mata gizo a fuskar yaran?"

"Bari ce ta mata alama da tai sauri, hakan yasa ta kalleshi tace  kayi hakuri in na bata maka. "

Harta juya tana neman tafiya yace  wa kike nema?

Juyowa tai ta kalleshi sannan tai murmushi mai tattare da bege tace  d ana.

"Tana fada ta juy, Bari ga kalli mutumin tace  nagode fa zan duba abinda kacemin. "

"Ta juya suka fita, suna barin kofar kuwa dakarun na dawowa."

"Azi dake tsaye yana kallansu sanda suka fito, shiru yai yana tunani, bari yabi umarnin Junaid ya"

"tabbatar zai kula da kansa harya dawo, juyawa yai ya fita."

"Junaid kam tana fita ya runtse idanunsa, gaba daya idanunsa suka kada sosai sukai jaa, dazu"

"yunwa da fitsari sun matseshi amma yanzu sam baima jin yunwar, meyasa kace mata bakai bane? Bayan zata sa a budeka in taji kai waye."

Kai ya girgiza yace sun yadda ni taya zan yarda ta gani a cikin halin tausayi? Bayan ta yarda danta

tana rayuwarta yadda ta saba?

*********

"Azeema na shig dakinta taga Mai Martaba a zaune a dakin, mamaki ne ya kamata dan ba zuwa"

"yake ba sai dai ya aiko taje, yau lafiya?"

Kallanta yai sannan yace  daga ina? Da sassafen nan?

Zama tai kusa dashi tace  jinai banji dadi shine nai yar tafiya.

"Murmushi ya sakar mata sannan ya riko hannunta wanda ya dau sanyi, hannunsa yasa ya rufesh,"

sannan ya fara hura hannun nata yana murzawa.

"Shiru tai ta kuraws kasa ido, sai dayaji hannun yayi dumi sannan ya jawota jikinsa yace"

 Menene?

"Dagowa tai ta kalleshi tace  wani na gani, kamarsu daya da Junaid. "

Kallanta yai jikinsa yai sanyi yace  a ina?

Tace  jiya yayina Zeena laifi.

Bawa ne kenan?

Tace eh

"Da har gabansa ya fadi amma jin haka yasan ba shi bane, balle yasan jiya Azi yazo."

"Kwanciya yai a kan gadon sannan ya kwantar da ita kusa dashi, yace  Zaki ganshi insha Allah. "

"Hawaye ne suka zubo mata, tace  da na dauka gyambon ya tafi, amma yau ganin yaran nan ji"

"nake bazan iya rayuwa ba Junaid ba, Abdulsalam ka taimaka ka nemon Junaid. Kuka ne ya kwace mata."

"Zuciyarsa gaba daya ta gama karyewa, gaskiya zai kaita inda Junaid yake sai ya fada mata tayi"

hakuri ta barshi a can tunda umarnin Sarki Zubair ne.

*******

"Zeena tana zaune gaban abincin da aka jera mata, kallan Fure tai tace  jeki sa a kawon yaran"

nan.

Fure cikin mamaki tace  Gimbiya.

"Zeena ta zabga mata wata harara, da sauri Fure ta fita, tana zuwa ta sanar dasu sakon Gimbiya"

"nan aka bude Junaid, mamaki ne ya kamashi dan yasan wannan yarinyar bazata bude shi ba, ko Ummansa ce? In itace zai bata hakuri y fada mata."

"Fure har ta fara tafiya yace mata yana san shiga kewaye (toilet) ban ta kalli dakawan, sukai"

kewaye dashi.

"Bayan ya gama ne ya tsaya ya kakkade jinkinsa, dan taimama yai yayi sallah a kasa, duk kayan"

"sun baci da kasa,yadan gyara rawanin sa dayai sannan ya fito."

"Fure na gaba yana binta a baya, tsayawa yai cak? Dan yanzu ya ganeta itace mai zubamai ruwa"

"jiya, kenan yarinyar nan ce?"

Fure ta juyo ta kalleshi tace  muje.

Junaid ya hade fuska yabi bayanta.

"Tana zaune haryanzu bata fara cin abincin ba aka shigo dashi, kallansa tai sannan ta fara cin"

abincinta.

"Dayake yunwa yakeji kamshin abinci yasa yunwar ta motsa sosai, Zeena kam cin ahincinta take"

"harta gama sannan ta kalli Fure ta mata alama da a dauke, nan Fure ta sa aka kwashe."

Zeena ta kalleshi tace  fita waje ka tsaya a tsakiyar rana.

"Da sauri ya kalleta, tace me? Bazaka iya ba? Ko kafi karfi?"

Mikewa yai ya fita waje ya tsaya a tsakiyar rana.

"Daga ciki ta wangale kofa tana kallansa, murmushin mugunta tai sannan tace  bani hakuri. "

"Kallanta yai, Binta! Abinda ya fado masa a rai kenan, ya daure yace  yahkuri. "

Dariya tasa tace haka ake bada hakuri? Ka ban hakuri sosai kace Gimbiya Zeenatu ki yafemun

ki taimaka kiyi hakuri.

Kallanta ya sakeyi tace  kafi karfi?

"Shiru yai kawai baice komai ba, iska tadan furzar tace  karkaga laifina. "

"Mikewa tai ta fito waje, ruwa ta debo da kanta ta nufo inda yake, ta daga hannu zata zubamai"

yace  me zai kareki in na fada?

Da sauri ta kalleshi rai bace tace  mene?

A hankali yace  kina matsayin Gimbiya bakya tunanin kina kaskantar da kanki gun daga

hankalinki akan bayi irin mu?

Idanunta ne suka fifito saboda bacin rai a zafafe tace  mene?

Da dan karfi Yace  Gimbiya Zeenatu ki yafemin ki taimaka kiyi hakuri.

"Huci kawai take saboda bacin rai, yace  na fada ki barni na koma gida dan Allah. "

Kallansa ai tace  gida?

Tasa dariya tace  na fasa kulleka ma bawana zaka zama zanga me zakayi.

"Junaid ya kalleta cikin takaici, yanzu wannan kanwarsa ce? Tunda babansu wa da kani ne? Wani"

irin tarbiyya aka bata?

***********

"Hankalin Hari ya tashi saboda zazzafan zazzabin da Binta keyi, sai amai take shekawa ta kasa cin"

"komai, Hari ta rasa ya zatai, ta bata magani ta zauna kusa da ita tana tausarta akan tasan Junaid bazai taba yadda ita ba......."

Nima nace gaskiya. lol

*Ayusher Muhd*

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Tara

Ran Zeena yakai matuka gun baci da taga yanda ya kalleta.

A zuciya ta ciklar da kwanan data debo ruwa tai ciki rai a bace.

Tana shiga ta hau cillar da abubuwan dake cikin fadar tata.

"Tana gamawa, ta wuce ta fito ta kalleshi tace biyoni."

"Junaid bai musa mata ba yabita, bangaren Hajjo tai dashi, tace ya koma ya tsaya cikin rana, ita"

kuma ta shiga ciki.

"Hajjo ta kalleta tace ""kinga damar zuwa?"""

"Zeena ta turo baki tace ""Yanzu na tashi."""

"Hajjo ta tabe baki tace ""kardai ki manta anjima zakije gun Yariman Gobir dan mai martaba jiya ya"

"aiko a fada miki."""

"Kallanta tai tace ""Wai meyasa kuke san sai kun aurar dani dole?"""

"Hajjo ta mata wani kallo tace "" kin girma gundin gundin so kike mu saki a gaba muna kallo kamar"

"kawar mu?"""

"Zeena ta hade fuska tana cewa ""ni wlh bana sansa da wani bakinsa kamar na. """

Kallan da Hajjo ta mata ne ya sata tai shiru.

"Hajjo tace ""baki dai dauko yaran nan daga magarkama bako?"""

Kallanta tai a ranta tace ya akai ta sani?

"Hajjo ta kalleta tace ""kinyi ko?"""

"Zeena tace ""ni ki barni da kaina zan koyamai hankali."""

"Hajjo tace ""ai rashin hakurinki nasan bazaki taba iya barinsa a can ba, wannan rashin hakurin"

"bansan ya zakiyi ba in kakai aure."""

Zeena ta juya kai.

Junaid na tsaya cikin rana yunwa kadai ma ta isheshi.

Jin hirar taso da Hajjo bata mata ba yasa ta fito.

"Kallansa tai taga yanda ya dan galabaita tace ""biyoni."""

"Nan Junaid ya bita, duk inda taje bata dadewa take fitowa gashi ko ina sai tasashi tsayuwa cikin"

"rana, tun yana daurewa har yunwa ta fara sa kafafunsa dan rawa, rabanshi da abinci tun a gidansu daren shekaranjiya kafin su taho, to gwara a hanya da suka iso Biram sun dan sai gyada sun ci."

"Zeenatu ta koma bangarenta, tana zama ana hera mata abincin dare."

Daga waje tana kallan yanda Junaid yake daurewa da alama yunwa ta kusa mai ila.

"Kallansa tai sannan ta kalli Fure tace ""zuba abinci ki ba wancan."""

"Fure cikin mamaki tace ""eye?"""

"Zeena ta kalleta, hakan yasa ta yin saurin zubawa, fitowa tai da abincin ta kalleshi tace ""gashi."""

"Junaid ya kalleta sannan ya kalli Zeenatu wacce itama kallansa take, harya kai hannu zai amsa"

"Zeena tace ""Fure? Uban wa yace ki zuba abincina ki ba wa wani bawa?"""

"Fure cikin mamaki ta juyo ta kalli Zeenatu, Kin dawo nan ko sai ranki ya baci?"

"Fure ta juya da sauri, Junaid ya kalleta, yanzu kam ya gane wani salan wulakanci ne yasata sawa"

a kawo mai.

Fure na komawa ta amsa ta ajiye sannan ta fara cin nata.

Lomarta uku aka aiko akan taje Yariman Gobir na jiranta.

Ranta ne ya baci wanda ko abincin ma bata iya cigaba da ci ba.

"Haka Fure ta tayata ta canza mata kaya, ta mata kwalliya, fuskar nan tata a hade bakin ciki da"

takaici duk ya isheta.

"Tana fitowa tsa hannu ta dau gwaibar dake cikin kwano, ganshi tai a tsaye, kallansa tai tace"

 biyoni.

Ta kalli Fure tace ku tsaya na dawo.

Mamaki ya kama Fure tace  amma Gimbiya. 

Zeena tai gaba wanda ya hana Fure kara magana.

"Junaid yabi bayanta yana tafe a baya tana gaba, juyowa tai ta mikamai gwaibar, ansa yai tare da"

cewa  na meye?

Bata kalleshi ba tace  bansan ka mutu min a auramin laifin kasheka.

"Haushi yasa bai bata amsa ba, harta dan cigaba da tafiya sai kuma ta tsaya ta juyo tace  ina"

"tunanin abinda zan maka, dan Allah wannan abinda ke yawo akanka sai na saitashi. Ta juya."

Wani kallo ya mata sannan yace  naji ko menene kimin amma dan Allah ki barni na koma gida

na bar iyalaina cikin wani hali.

Kamar baza tai magana ba sai jiyai tace  iyalai? Aure gareka?

Eh harda yara.

"Baki ta tabe sannan ta cigaba da tafiyarta, Junaid yace  yaushe zaki sallameni? "

" Ban sani ba, sai sanda ladabinka ya dawo? "

Junaid baisan sanda yace  mene? Cikin sautin dayai maganar ne yasata juyowa a fusace tace

 me kace?

"Shiru yai sai kallanta dayai, ranta

Please Login or Register in order to submit comment