You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasauke ijiyan zuciya
tace “all this shaye shaye is time zasu dena yarane, last month Khaleel yayi 32yrs
birthday nashi fa, he’s still a child, at the age of 24 nafaramai aure cus I caught
him watching all this videos na banza, I give d’ana freedom yayi anything dayakeso
agaba saisa me and Khaleel share a deep bond sosai I understands him sosai sama da
babanshi, idan lokaci yayi zakiga da kansu zasubar shaye shayen kuruciyane wlh,
kinga Khaleel babu wani abu nashi daban sani ba, I choose the gurls all of them for
him , I’m his everything” gyadama Mom kai tayi tace “wlh zanma Sam auren nan shima”
Kusan 1hour suna juyo ihun Khaleel ko ajikinsu chan suka jishi shiru PA tawuce dan
dauko yarinyar dan baya kwana da kowa agadonshi, knocking tayi gaban kofan batare
data budeba tace “kifito” tashi Zainab tayi daga kasa tana kallon Khaleel dayayi
rub da ciki abinshi, kasanta har zafi yake mata ya kumbura sabida yanda shi babu yi
ahankali a lamarinshi tawuce tafita.
EPISODE 33

JAMA’A KHALEEL IS SO PETTY😂 CUS TELL ME WAT HE DID THERE DAYASA AKA HANA BABAN
YASEER SHIGA DA SHOPPING😂😂

WAIT OO HOW COME HAR PLATE NUMBER YA HADDACE YAKUMA GANE FUSKAN BABAN YASEER???

KUN FARA JIYO WARIN MEKE FARUWA GAME DA THIS BAD BOY KO SAITAI TSAMI ZAKU GANE?😃
[9/22, 6:35 PM] Halima KW: 💫GARGADAN SO💫


✍🏻M SHAKUR



3️⃣
4️⃣
EPISODE 3️⃣4️⃣


REPOST MY TIKTOK FANMILY❤️
https://vm.tiktok.com/ZMhFRaBuC/


Shiga cikin hospital din Baban Yaseer yayi anan reception yaga Baba zaune dasauri
yayi wajenshi adan rude yace “Baba” dasauri Baba yajuyo jin muryan Baban Yaseer
yace “na’am Aliyu harkazo? Ga dakin nan likitoci na ciki cewa sukai na fito, ina
Ni’ima”? Boye komi yayi yace “tana asibiti, nariga na gayamata zatazo da zaran
tasami chance” Baba yace “Allah sarki Ni’ima nasan tashiga cikin tashin hankali”
Baban Yaseer yace “Baba an ina tayi hatsarin”? Tagumi Baba yayi ahankali yace “wlh
bansani ba ko inda motanta yake ma bansani ba ta lafiyanta nake yanzu, kwananta
biyu batada lafiya tun ranan litinin da yamma, yauma cewa tayı bari taje asibitin
su Ni’ima adubata saidai aka kira su Ammi wai me waya tayi hatsari nikuma suka
kirani su Ammin suka sanar dani” anatse Baban Yaseer yace “kada kadamu Baba zan
kira wani Abokina dake aiki da road safety naji idan zan sami any details na
hatsarin da inda motarta yake” Baba yasauke ijiyan zuciya yace “tom shikenan” Baban
Yaseer yadaga wayanshi yakira yadan matsa daga inda Baba yake kusan 20min yayi
sannan yadawo yace “Baba ance motoci biyar ta deba ta hada da trailer amman
Alhamdulillah babu any casualty babu wanda yarasu saidai sunji ciwo, ance wanda
yakawota asibiti yasa agent ne ko PA wani dai nasa yasaka yabiya duka masu motocin
har trailer kudin gyara motan su da kudin zuwa asibiti” Baba yakama baki da mamaki
yace “iyye awannan zamanin abiya kalan kudin nan? Wannan bawan Allah akwai kyan
zuciya da imani dakuma adalci da taimako” Baban Yaseer yace “ba shakka, kowaye
gaskiya yayi kokari Allah sakamai da Alhairi”.


Duk suna zauna awajen dan an hanasu shiga dakinta har around 12 na rana saiga Ammi
tashigo reception din tareda Ramla dake goye da katuwar jaka abayanta dukansu
idanunsu ja, Baba na ganinta yashiga kokarin mikewa hakama Baban Yaseer Ammi ta
taho wajen dasauri Baba yayi wajenta hankalin Ammi atashe tace “ina Hawwan Malam?
Ina Hawwa na? Ina tak….” Sai kuka kaman ba Baba ba yace “ya isa ya isa, gatachan
adaki ance kar adameta kar a shiga saita farka, zauna, Ramla kema zauna” ahankali
Baban Yaseer yace “ina yini Ammi” gyadamai kai tayi tana goge fuskanta da bakin
hijabi tace “lafiya lau Aliyu sannu, bazakaje aiki ba ka zauna anan” adan hankali
yace “bari mugani zuwa ta farka yanzu banda natsuwan yin aiki” ijiyan zuciya Ammi
tasauke wlh har ranta batason zamanshi anan, cikeda hikima tace “to dan Allah
tayani kai Ramla gida ta ijiye kayanmu tadafo wani abu takawo incase Hawwa ta tashi
tanason abinci, Ramla dakin Antyn ku zaki ijiye kayanmu” Dasauri Baba yace “dakin
nata abude yake, kaita Aliyu akwai kazanta adaki zaki iya dumama mata shi Ramla”
hannunshi Baban Yaseer yasa ya karbi jakan dake hannun Ramla yace “muje” binshi
tayi suka fice wajen yarage daga Ammi sai Baba.

Aliyu na ijiye Ramla yajuyo cus bazai iya jiranta tayi wani girki ba ayanda yadamu
din nan tsayawa yayi yay salla yafito yana ciro wayanshi daga aljihu inda yaga
Ni’ima tamai sama da 20 miss calls thank God wayan na silent maida wayan yayi back
yashiga mota yatada.

Shigowa reception din Baba yayi dan yafita yaje masallaci sallan azahar yadawo inda
Ammi take zaune tana kallon gaban dakin da Hawwa tayi yace “likitan dana bari ya
shiga yafito”? Ahankali Ammi tace “a’a baifito ba tukunna Malam gabana sai faduwa
yake sunki fadamana komi har yanzu” shima Baba cikeda damuwa yace “karki damu in
sha Allahu alkhairi zamuji” suna zaune awajen Dr yafito tareda Nurses yakalli su
Baba yace “Alhamdulillah yarku ta farfado” harwani rige rigen tashi tsaye ake
tsakanin Baba da Ammi but Ammi tariga Baba tashi dasauri tace “Dr zan iya ganinta”?
Gyadamusu kai yayi yace “eh zaku iya ganinta amman kafin nan inaso kubini office
inada magana daku” faduwa gaban Baba da Ammi sukayi, gaban Baba nafadi sosai yace
“to Allah yasa lafiya, muje Zainabu” itama Ammi gabanta na faduwa ta gyadamai kai
tabi Baba sukabi bayan Dr. Office din suka shiga suka zazzauna Dr ma ya zauna ganin
yanda suke zazzaro idanu yasa yace “ku kwantar da hankalinku bawai wani abu bane
dalili yasa nakiraku, na farko dai banda ciwukan data samu daga accident din nan
yarku batada lafiya, mun gano tanada Hypertension wato hawan jini” daga Baba har
Ammi atare sukace “hawan jini!”? Gyadamusu kai Dr yayi yace “yes BP yayi high sosai
shinema dalilin dayasa na kiraku tunda nasan kune iyayenta in tambayeku ko akwai
wani tunani da yarku keyi ko akwai takamaiman abinda ke damunta?” Shiru daga Baba
har Ammi sukayi cus they know amsan tambayan Dr, abinda ke damun Hawwa is rashin
aure da yawan tunanin dalilin, Ammi kuma tasan harda fadanta da Ni’ima yahadun mata
but bata taba sanin Hawwa nada hawan jini ba, and she’s sure Hawwa ma batasan
tanada shi ba danda zata gayamata, ganin sunki magana yasa Dr yace “I guess kunsan
abinda kesa yarku damuwa dakuma tunanin datakeyi, banson na shiga family issue
dinku dan haka bazan tambaya ba, amman dai kusani hakkin iyaye ne su kauda duk wata
matsala da damuwa daga jikin yaran su especially idan damuwan yasoma haifar musu da
cuta ajikinsu, arayuwan nan there’s nothing like yarona yayi girma he can take care
of kanshi, naga kasa shekaranta 29 da 10months haka karubuta mana, Baba yaro ko
shekaransa dari yana bukatan iyayensa su kula dashi, ku kula da ita dan Allah, ku
taimakama yarku cus BP ta yayi high sosai, ku bata farin ciki, ku kauda mata
damuwan and support her, BP yatashi yasa tai loosing control kanta tana tuki harta
hada hatsari, hawan jini muguwan cuta ce da tashi daya takan dauki ran mutum, dan
Allah akiyaye, babu maganin dayafi aiki kaman maganin iyaye a rayuwan yaransu,
menene maganin nan danake magana akai? Shine support na iyaye da love da mantar da
yaransu damuwa da bama yaran farin ciki da natsuwa……” Dr yaciga da advising Ammi da
Baba sosai……

Around 1:30 yashigo asibitin parking yayi yasauko yawuce ciki, ganin baiga Baba ko
Ammi wajen ba yasa yayi wajen dakin da Hawwa keciki ya leka ta glass na kofan
idanunta biyu amman idanun sun kankance sosai irin na mara lafiya tana kallon waje
guda tai shiru tana tunani, daga ita sai dogon ringan jikinta ga gyalenta an rataya
wajen bag hanger dake gefen wardrobe na dakin gashin gaban goshinta dukya kwanta
luplup ansa bandage a goshinta hakama hannuwanta duk bandage wani kalan sonta da
bala’in tausayinta ne ya mamayeshi kaman ya shiga ya karbe ciwon daga jikinta,
hannunshi yakai yabude kofan gently yana shiga ciki, ahankali Hawwa ke juyo da
kanta kadan da kadan dan har yanzu kanta na banging saidai ba kaman dazu ba so da
kyar take juya kan kallo kofan dataji an bude tayi tahada idanu da Baban Yaseer
daya shigo yana mata kallon tsantsan so kaman zai hadiyeta, faduwa gaban Hawwa yayi
kaman taga dodo tashiga mikewa tana tashi daga kwance dasauri ya yunkuro zai taho
yace “don’t move Hawwa ina zaki”? Da muryanta da baya fita sosai cikin rashin
lafiya tace “karkazo nan!” Chak ya tsaya daidai tana tashi zaune da kyar idanunta
har layi suke kanta yafara kwankwatsa sabida yanda ta tashi, dafe kanta tayi da
hannunta da drip ke makale tana damtse idanunta cus her head is pounding kaman ana
daka a turmi da kyar tace “kafita Baban Yaseer!” Cus bamata kaunan ganinshi
arayuwanta, kallonta Baban Yaseer yake kaman yau yafara ganinta ahankali yace
“Hawwa nafita kuma why? Nine fa? It’s Aliyu, Kinsan yanda nake cikin damuwa kuwa?”
Ganin yanda yake wani irin kallonta zuwa kirjinta dan andan zage zip na bayan dogon
rigan, tashin datayi yasa gaban rigan ya zazzago sama saman kirjinta na showing, da
sauri tarike gaban rigan da hannu daya dayan hannun takai bayanta taja zip da mugu
karfin hali Hawwa ta sauko da kafafunta daga gadon adan tsorace Baban Hawwa yakara
yunkuro wa zai taho yace “ina zaki Hawwa sit please you’re not well, me kikeso ki
dauka? I can give it to you”hannunta daya akai dayan ta daga ta nunashi tana haki
tace “kafita I don’t want to see you! Stay away from me Baban Yaseer” yana kallonta
gently and softly yace “har abada bazan taba ita staying away from you ba Hawwa”
ganin yacigaba da kallonta yasa Hawwa ta diro daga gadon danta dauki gyalenta
datagani a hanger kawai ta zube akasa babu karfi ajikinta ko digi kaman kafafunta
basa aiki tai wani kara tana kama kanta da duka hannun biyu tace. “Kainaaa
uhnnnnnn”
Dagudu Baban Yaseer yayi wajenta without having a second thought sabida tsabagen
yanda yarude kawai yakai hannunshi yadauki Hawwa dake kasa idanunta a kulle takama
kanta da duka hannuwa biyun jin an dauketa yasa Hawwa tabude idanunta da kyar dan
kadan suka hada ido da Baban Yaseer hawaye masu zafi ne suka fito daga idanunta
cikin muryan da baya fita bamata da karfi sosai tace “Baban Yaseer kaji tausayina
kafita daga rayuwana! Ka ijiyeni! Stop touching me, ka ijiyeni nace” tai maganan
tana lumshe idanu ta rirrike kanta, yanda hawaye ke fita daga idanunta tana magana
kasa kasa kaman yar baby ya kashema Baban Yaseer zuciyan he just wants to kiss her
and hug her so damn tight, kofa yakalla ganin babu kowa dake tahowa yasa ahankali
yashiga sauke fuskanshi zuwa daidai fuskan Hawwa he just love Hawwa and feels like
kissing her baimasan meyake ba, fuskanshi na dab da sauka anata akai mahaukacin
bugokofan dakin dayasa yadago kanshi da gudu Hawwa tabude jajayen idanunta da kyar
suka kalli kofan suna hada idanu da Ni’ima data bugo kofan tana sanye da abaya
idanunta sunyi matsiyacin ja tana kallon Baban Yaseer daya dauki Hawwa ajikinshi
kaman yanda yake daukan su Yaseer da Yasmeen, adaidai lokacin kuma Baba da Ammi na
zuwa wajen duk sukaci tura suka tsaya abayan Ni’ima duk suna kallon Baban Yaseer,
yanda gaban Hawwa yahau bugawa ganin Ni’ima ta dauka kirjinta zai fashene da sauri
ta shiga kokarin kwace kanta batama da karfin motsi abin gwanin ban tausayi tana
kallon Ni’ima Baban Yaseer kuma yariketa gam ajikinshi yana kallon Ni’ima, wani
kalan mosti fuskan Ni’ima yafara tana huci tace “ba kiss zakuyi ba”? Tayi
mahaukacin ihu tana daukan kujeran datagani adakin tayi kansu tace “ka sumbace ta
mana Aliyu…….”

THIS BABAN YASEER IS HE TRYING TO TAKE ADVANTAGE OF HAWWA? CUS WAT WAS THAT DAYAKE
KOKARIN YI PLEASE???

I GET YANA SONTA SOMA MAI ZAFI BUT COMMON SOYAYYA BA HAUKA BANE??

IDAN KENE BABA KO AMMI WHAT WILL YOU DO???
[9/22, 6:35 PM] Halima KW: 💫GARGADAN SO💫


✍🏻M SHAKUR


3️⃣
5️⃣
EPISODE 3️⃣5️⃣


JOIN MY FACEBOOK GROUP

https://www.facebook.com/share/g/MhrpcozubuW3sxg8/?mibextid=K35XfP



Kyakkyawan baccin gagaran Khaleel yayi danko 30 minutes baikaiba ahankali yabude
idanunshi yana juyowa daga rub da cikin dayayi yana kallon saman dakin baimasan
meke damunshi ba, normally yakamata yayi bacci har zuwa 4 na yamma but yakasa
baccin tunanin yarinyar chan kawai yake, kaman her sick spirit na kiransa,
hannunshi yadaga yakalla da Hawwa ta ciza lumshe idanu kawai yayi yabude sannan
yatashi zaune yasauka daga gadon, boxer yacire ya yar awajen yawuce abinsa naked
yafada bathroom yayi wanka yafito yawuce walk in closet dinshi dake kama dawani
exquisite boutique, shiryawa yayi yazaro Balmain monogram print flowing shirt
dakeda kalan black print din kuma white yasaka, yadauko dogon denim wando na Diesel
yasaka daya zauna ajikinshi da kyau dasdas, agogonshi yaciro from drawer na
designers watch dinshi, yacire Furlan Marri yasaka dayama hannunshi kyau, yadan
juya yakalli showglass na takalmansa kaman shago yasa hannu yaciro wani suede flat
takalmi na Birkenstock Boston, sannan yadau turarukanshi yashiga fesawa yadauki
brush yana taje kansa ya shimfada dadduma yayi sallan azahar sannan yamike yabude
kofa yafito yasauka kasa, chan falo yayi yana kallon agogon hannunshi is 1:30 ba
kowa afalo probably Mommy ta kwanta ko tana spa nasu ana mata massage, kofa yawuce
aka budemai yafita wajen black Mercedes Maybach S class dinshi yayi dake kyalli
tsabagen kyau da kudi, da sauri security nashi suka taho wajen yakalli Salman dake
budemai motan yace “when did you come back?” Dasauri yace “not quite long Sir
everything is sorted babu wani matsala motanta I called auto shop sunzo sun dauka
har an fara gyaransa” yatsine fuska yayi kadan baice kome ba ya shiga bayan motan
ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya zauna driver shima na
shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir”
yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi
yanadan shaking kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi
hankalinshi kwance.

*
Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana
sauke Hawwa agadon yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi
zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima completely heart broken Baban Yaseer yabude
hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama rungumeta idan zakayi amman
saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga
wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna
kukeso kuyi ba kuka ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer
yasa ya fizge kujeran daga hannunta yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi
zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi na dauketa da mari
jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata mari
but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace
“kika kara maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi
takalli Baban Yaseer dake tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban
yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu yatashi ahankali yakoma wajen kofa
ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima takalli Ammi
idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata
taba bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa
ni nake tayata bawa diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki
dawani marin, you’re very, very and very stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida
namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada Ammi babu alamun wasa
akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace “Malam Ni’ima
tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi?
Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya
ce, bakar mayya mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan
gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake
hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban Yaseer ke kallonta hakama Baba da
Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person turn monster over
night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko
kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna
Baban Yaseer Ammi tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki
kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan
yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da natsuwa, Hawwa zata iyama
maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!” Rai abace
sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da
muka bata” ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli
Baban Yaseer strictly yace “Aliyu dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da
alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole kace ka gode ba anci
kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai
kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai
facing nashi ganin abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba
yace “kul!”

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from
our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa
novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search
na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment