You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ta miqe zata gudu,
Inkika sake kika shiga bayinnan wallahi sena ranqwasheki uban wa kike kunya anan?tsaf zan
zaneki danni ba wuce duka kuka yi agurina ba maza zoki karba ki shnye ina gani Dan nafara
zargin zubarwa kike,
Lubna tace nikam mama bani idan wannan me dadin ne kuma wannan Dan karamin kofin baze
isheni ba,
Sannu kekuma rasa kunya,tunzuro baki tayi,
Ahankali juwairiyya tazo takarba tazauna tana sha a hankali harta shanye,
Badee na fita juwairiyya tacewa lubna waike baki gaji da waynann abubuwan bane da ake dirka
mana nifa nafara jin yanayi kumama nikam banaso suyi yawa naje ya hallakani a banza,
Wane irin hallakawa sekace baya sonki Nikam wannan kazar ne bazan tabaci ba bakiga ba
akawomana ba?ninace karsu wahalar dakansu wallahi gara wannn kodan dadin sa zaksha,
Juwairiyya tayi dariya kawai Dan ita mamakin lubna take yadda bata iya boye abinda keranta,
Biki kam anshashi har angode Allah ranar Saturday da safe aka Daura aure da dare misalin karfe
Tara aka miqa kowacce dakinta bayan sun sha nasiha lubna kam ita aka kai karshe Dan maqalewa
tai jikin badee tana kuka itafa seyanzu da za akaita tagane tafa bar gidan kenan danhaka taringa
kuka seda majid yazo ya rarrasheta tana rungume jikinsa yakaita mota,
Hmm lubna amarya.
Abdulrahim kam da abduljabbar basu yi wata wataba suka angwance daganan suka kwashi baccin
su me dadi,
Bangaren Mus'ab da lubna kuwa rarrashinta kadai seda suka kai karfe dayan dare kafin suyi
alwala suyi sallah dacin kaza seda yadaukesu awa daya,
Wayyo yaya bacci nakeji,tab..yace wannan karatun dolene yau kibari idan kingama dauka sekiyi
baccin kinji daganan al'amura suka chanja (dama ni bana tsayawa daukar irin wannan rahoton
saboda dalilai danhaka nafito najamusu kofar sedai fatan Allah yabada zuri'a Dayyaba ameen),
Washe gari misalin 10:12 am tafarka dasauri ta tashi zata miqe,
Wayyo Allah na tace takomawa zaune,shikenan yakassarani mama kizo kigani ban iya tafiya tasa
kuka,
Gogan cikin bacci yajyo kukan lubna dasauri yatashi,
My lady ya akayi?sannu kinji,bari na hada miki ruwa namiki wanka,
Banda kuka da shagwaba tana kara narkewa babu abinda take,
Bayan sunyi sallah yace,my lady Kindaina jin zafin?,
Juya fuskarta tai gefe tana jin kunya tace um um,zo induba kose anyi Dinki ne?,
Nikam ka kyaleni jikina duk ciwo yake kuma bacci nakeji,
To ki kwanta bari naje nasiyo miki magani kinji,
Abdulrahim kam yarasa inda ze tsoma kansa Dan dadi ko motsi safna tayi seyace sannu,
Wani Abu dayake ban dariya shine koda naje abduljabbar da juwairiyya kunyar juna suke ji
sunkasa hada ido,
Yaya asama'u ita tai abincin aka kai musu suka ci,
Lubna na zaune a Palo Sega kiran safna awayarta,
Matar yaya,inji lubna
Matar yaya Mara imani,
Yayanki daine bashida imani muryata seda tadaina fita,
Dan bakiga abinda yayanki yaimin bane ke ko tafiya ban iyayi fa,
To uban waye yake iya tafiyan dalla daga chan ni se anjima maganama wuya take min,
Sosae safna tai dariya kafin suyi sallama.
Dana sani na tsaya najiyo ihun Lubna koda shine nayo recording amma nextym video zanyi
Basenasha wahalar typing ba 😉
[8/16, 8:35 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 41
Bayan wata daya da en kwanaki lubna ta soma laulayi duk abinda taci seta Harar yauma zaune
suke itada Mus'ab da yamma ya karbo mata tuwo gun momynsu,
My lady pls tashi kidanci koda loma goma ne kinji,
Nikam kabarni idan naci amai zanyi,ba zakiyi Amai ba kina ci zanmiki alluran daze hanaki Amai,
Dakyar yasamu tadanci yaimata allura yace tadan kwanta kafin yaje masallaci yadawo tasamai
kuka dakyar ya rarrasheta tabarshi yafita gashi ta hana ya fadawa kowa tunjiya ta rikice,
Sallar magrib kadai tayi agurin tafara Amai tanayi tana kuka ahaka tayi kokari ta gyara gurin,
Sallahr isha'i ma azaune tayi saboda jiri take ji tana gamawa sewani aman gabadaya ta gama
galabaita kuka kawai take ahaka Mus'ab ya zo yasameta abokinsa yakira yataimake sa yakawomai
ruwa da magani baze iya fitaba zesaka mata drip din agida,
Mus'ab gara ka kawota asibiti kawai tunda batada lpy sosae bekamata ka ajiye ta gidaba Dan kana
takamar kai likita ne tana bukatar kulawa sosae amma fa shawara ce,
To shikenan Ibrahim gamunan zuwa Dan wallahi ko magana bata iyayi nagode,
Shege Mus'ab sharp shooter haka fa ka yiwa jamila kaikam bakasan dadin amarciba,
Kujimin Dan iska dallah nidai gani nan zuwa banza kawai,
Suna zuwa akayi admitting dinta akaimata komai daya kamata tasamu bacci,
Se washe gari yakira gidansu yafada hankalin badee sosae yatashi tafada wa majid tare sukazo
lubna na bacci majid be jima ba yawuce kafin yamma asibiti en uwa duk sunzo dubiya zuwa
lokacin ta farka amma takicin komai ita tsoro takeji,
Safna,juwairiyya, Rahama da babynta,laila da ramla duk suna dakin badee taje gida tayo wanka,
Safna tace,waikukam bakuda uzuri harkun abinnan?, tayani fada inji juwairiyya duk kwazaban
yayanki dai ba asamu rabo ba,
Ita dai kallonsu kawai take batajin zata biye musu amma Wallahi tanajin sauki duk seta fige su
Dan seta rama,
Se dariya suke suna kiranta me hazaqa aiko taji bazata iya hakuri ba majid na zuwa tasoma
narkewa a jikinsa tanace wa,
Wayyo My man yunwa nakeji,ko inbaki abincine zaki gwada ci ne?,nikam ba zanyi Amai
ba?,insha Allahu bazakiyiba, miqewa yai yadebo tuwo kadan a plate ya leqa toilet ya wanke
hannunsa yadawo yazauna yanajanyota jikinsa,
Su safna anzata abin Na kallo ne kawai sesukaga yafara bata tuwo abaki tanaci tana kukan
shagwaba ahankali suka silale waje suna fita se dariya juwairiyya tace kai amma wallahi lubna er
iskace kukaga yadda tabamu kunya fa,
Safna tace aitayi maganin tsiyar damuke mata,
Seda tai sati daya a asibiti tadanji sauki ta matsa aka sallameta,
Wanka tai taci abinci ta kwanta Dan dare yayi Mus'ab ma wanka yayi suka ya kwanta yana janyota
jikinsa,
Cikin dare yaji kamar lema akasan su dasauri yatashi yakunna wuta,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, jini duk agadon lubna se baccin ta take Tashin ta yashiga yi
tashinta yai daidai da murdawan maranta dasauri taduba jikinta ihu ta kwalla shikenan se suma
jinin kuma kamar ankunna famfo sekara zuba yake kwasar ta kawai yayi sukayi asibiti,
Zama nai akasa na ringa ihu INA gun jin kuka nashiga uku har na hangomu ranar suna munacin
rengem😭🙆🏻,
Kafinma su isa cikin yafita dafe kansa yayi kamar zeyi kuka se Ibrahim ne yai kokarin tsayar mata
da bleeding din tasamu bacci se kusan la'asar ta farka sekuma ciwon Mara haka taringa wahala
kuka kawai take tana juyi tasha injection kamar me amma bawani chanji,
La'ilaha illallahu yarnan haka kike wahala?wannan cikin ya gwada miki boni sannu kinji inji
hajiya se kuka tana kamawa lubna,
Har kusan magrib Abu yakici yakicinyewa,
Ji tayi tagaji da gadon ma kasa takeso ta kwanta batasan lokacin da ta fizge cannula din hannunta
ba ta fado kasa ta kwanta tana kiran mama,
Mama Dan Allah kitaimakeni marata jinake kamar zata fita baba kutaimakeni wallahi mutuwa
zanyi,
Mus'ab ji yayi kuka yazo masa amma yadannne kmata yai yamaidata gadon yasa auduga yana
danne gurin data cire cannula din sbd jini dake fita,
Sannu lubna kidaina wannan ihun kina addua kinji?,
Wayyo Mus'ab kaceci rayuwata incikinnan ne ke min haka Dan Allah kuciremin shi inba hakaba
shine ajalina,
Bashi bane yi hakuri kinji bari Ibrahim yakawo allura insha Allah daga anmiki ita zakiji sauki,
Mus'ab nagaji da alluran nan kuciremin cikinnan don Allah,
Majid ne yashigo yariko hannun ta lubna kiyi shiru kiyi addua ba ihuba kinji kuma kidaina zancen
aciremiki ciki kinji?,
Baba harda kai baka sona?yaushe kabar sona?don Allah kutausaya min bakusan me nakeji ba
wallahi jinake kamar zan mutu,
Abdulrahim dake gefe yaji hawaye Na kokarin zubo masa da sauri yajuya yai waje yana kuka
kamar yaro baze juri ganin er uwarsa hakaba yana jin sonta fiye da tunanin me karatu,
Mama kema kinbar sona?to kice sucire mun cikinnan nasan ke kinaso na,
Na lura lubna bata hayyacinta danhaka dasauri nabar dakin inata kuka kuma nace sena fadawa
mamana😫😩.
[8/17, 6:18 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 42
Shiru ta lafe jikin Mus'ab ahankali bacci ya kwashe ta tana sauke ajiyar zuciya,
Washe gari garau ta tatashi sedai Dan abinda baza arasaba kafin yamma ta wartsake se shagwaba
take zubawa,
Kwana daya ta kara aka sallameta badee ta wuce da ita gida seda tadan kwana biyu gidan badee
tace mijinta yazo yadauketa takoma gidanta suna zuwa Momy tace takoma part dinta seta kara
samun sauki wannan wahala haka aidole tahuta sosae,
Sega lubna tana kasa dakai yanzu kunyar Momy akeji,
Subhuhanallahi yaya meya sami safnar?,ohh harkun dawo gida?OK to insha Allah inanan zuwa
yau idan Abu Zara yadawo,ahh haba aisena zo karma kace a'a akwai ma zancen danake so muyi da
safnar,to shikenan Allah ya inganta mana,
Tab...su safna angama yimin tsiya Ashe ta kwasa,hmm
Aikin ta tacigaba dayi tana goye da baby,
Baban baby kagama cin abincin nan dasauri muje dubo safna wai batajin dadi,
Meyake damunta?kwazabar Ku kedamunta mana ciki ne da ita amma ba serious ne ba ciwon
kawai kasala ne,
Safna dama haka en gdnku suke?kema bakida dangana daga zuwa har kinyi wannan,
Er iska baznji haushi ba ai nasan ramawa kike,
Dariya sukayi daganan suka shiga hira har dare lubna ta koma gida,
After two month lubna ta sake kwasar wani sedai wannan daga bayyanarsa ya fita tasha wahala
kamar wancen Dan haka tana Dawowa gida bayan kwana biyu tana zaune gefen gado Majid na
shirin fita office tace,
Dan Allah nikam yau idan zaka dawo kadawomin da maganin planning mana,
Maganin planning? Waye zesha?yakamata taje asibiti kafin tafara sha,yafada yana yagyara belt
dinsa,
Nice zansha fa kaima kasan yakamata na huta koda shekara dayane?,
Waike meyasa kike Abu kamar bakida hankali?kawai Dan kinsamu miscarriage sau biyu sekice
zakiyi planning? To wallahi ban yadda ba kuma idan kikayi aboye bazan taba yafemiki ba,
Ai dole kace haka tunda bakaine kasha wahalar Dana shaba,
Koma dai menene inkinaso musami matsala dake to ki gwada yin abinda kikace wallahi me rabani
dake se Allah shashancin banza,
Sosae ranta yabaci Dan haka tace, ni wallahi senayi inba haka ba sedai in bar maka gidanka bazan
zauna inna dauki ciki yana wahalar dani kuma inma yafita sena wahala ba kuma ace bazan dauki
mataki ba ai hutawa nace zanyi ba cewa nai bazan kara dauka ba,
Wannan maganar da jahili yaita bazanyi mamaki ba amma kisani kekam kinban mamaki kuma
Dan Allah karki fasa,
To shikenan zakaga jahilci kuwa,
Fuuuu ta fice kayan ta ta hada tabar gidan yadda zuciyarta tazo wuya,
Yana kallonta ta hau adaidaita ransa abace yanufi wurin aiki,
Lubna meye haka daga INa haka kika kwaso kaya?,
Mama Mus'ab ne,meyai miki?,wai Dan nace zanyi planning shine yarufeni da fada kuma yana
fadamin bakaken maganganu,
Lubna shine kikayo yaji?,Tass..ta sauke mata mari kafin tacire sleepers din kafarta tashiga
dukanta,
Ashe bakida hankali,dakika zo nan uban me zanmiki,maza dauki mayafinki kibarmin gida babu
ubanda ze rakaki ni haka kikaga nayi wace kalar wahalar ce ban shaba da bazaki kwaikwaiyo da
halinaba kiyi hakuri billahillazi idan kika kuma yin yaji kikazomin nan sena kusa illataki balle
wannan banzan dalilin naki dabe taka kara ya karya ba,
Lubna da tuni tasoma nose bleeding tabi hanya babu mayafi se dankwali kawai akanta,
Mus'ab jiyai baze iya hakura ba bari yabi bayanta yana kokarin shiga yaci karo da ita zata fito
badee na bayanta da mayafinta ahannu tana kiranta amma ko juyowa bataiba,
Riqeta yai sosae amma dakarfi ta kwace dganan tashiga buga kanta duk inda tasamu dakyar ya
riqeta ya lalubo numbern malam ya kirashi yazo addua yaimata se bacci,
Mus'ab tashi kaje gurin aikinka kaji bayan azahar daidai tafarka sekazo ka kwashe ta Dan bazata
kwanarmin agida ba,
Godiya yai yafita daga gidan yana cewa dole Na kiyaye bacin ran lubna wannan bala'i haka
dabadan nazo ba haka zata fita ana kallemin jikinta,
Koda yadawo daukarta har suka isa gidan ko kallon sa bataiba bata fasa bashi abinci ba haka
tashiga kitchen tadafa abinci me rai da lafiya,
Da dare taje gun momy,lubna lafiya jiya bakizo kin karbi baby ba kuma da safe bakizo ba mun
gaisa nace ko lpy larai ta dubomin tace bakwanan,
Eh Wallahi bacci ya kwasheni jiya se 11 nafarka shiyasa banzo ba kuma d sassafe naje gida
banjima da dawowa ba,
To lafiya daiko,lpy lau fa kawai dai naje ne,
To shikenan babyn nacan tana bacci tagama rigimar Neman ki,
Ai dole tawuni ta kwana bataga uwarta ba bari nadauki abita mutafi nayi missin shagwabarta,
Momy tai dariya kawai tana jin dadin yadda lubna ke kula da baby.
[8/18, 8:59 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 43
Wanka tayi tayiwa baby duk yana zaune amma ko kallonsa batayi ba secin magani take,
Kwanciyarta tayi bayan ta musu addua tashafe jikinsu da ita ganin haka yasashi cire jallabiyar
jikinsa ya hau gadon ahankali yadauke baby yakaita gefe yamaye grubinta jikin lubna jin tadan
matsa baya yasa yagano idonta biyu danhaka yafara laluben kalmomin da ze rarrasheta,
My lady don Allah kiyi hakuri dukda nasan inada gaskiya akan abinda kike shirin yi kiyi hakuri
mu cigaba da rokon Allah insha Allah daga kinkara daukar wani cikin zamu dauki matakin da idan
Allah yataimaka baze fita ba amma don Allah ki fahimceni inason naga Dana ko yata daga gareki
kitaimaka muyiwa babynmu kani ko kanwa kinji,
Allah nagode maka daka azurtani damiji me sanyin hali nice nai masa laifi amma shine yake bani
hakuri Allah ka bamu zaman lafiya dahakuri Allah ka kauda shedan a tsakaninmu,
A hankali tafara kuka tana kara shiga jikinsa,don Allah kayi hakuri kayafe min daga muryata danai
akanka dakuma fita danayi bada izininka ba,
Ohhh nahakura maman baby kinsan banason kuka musamman naki muyi bacci kinji,daganan
nikam nadawo gidan babana na rungume nawa sweetheart din (pillow😩) dakyar nai bacci,
Washe gari yanata sauri ze fita yayi letti sun fito kenan tayo masa rakiya Sega wata mata da
zumbulelen hijab tsayawa sukayi suna kallonta harta karaso kusada su,
Durqusawa tai gabansu tafara rero kuka,Mus'ab don girman Allah kayi hakuri abinda nai maka
kagafarta min don Allah Badon halinaba wallahi rudin shedanne da zuga daga wurin Momy gashi
ta rabani da mijina da yata mafi soyuwa agareni wallahi ba laifina bane,
To da farko dai na yafemiki domin Allah ma munai masa laifi kuma ya gafarta mana amma kisani
tunda nake ba aimin abinda ya batamin rai ya tabo zuciyata irin wannan ba,Dan haka gaskiya
tsakani da Allah bazan iya kara zaman aure dakeba ina rokar miki Allah daya baki wani mijin
Wanda yafini ga yarinya ta nan Allah da ikonsa ya rayamin ita cikin koshin lafiya,
Allah ya isa taringa jerawa Momy aranta kafin daga baya ta share hawaynta,ta miqa hannu ta karbi
baby sosae takejin sonta na ratsata hakika tayi wauta da rashin hankali data yarda ta wofintar da
rayuwar er ta tun tana cikin tsumman goyo,
Don Allah ka yimin alfarma daya inaso adan ringa kaimin yarinyar nan koda na awa dayane
domin na ringa ganin ta,
Dama Waze raba da da mahaifi?zata ringa zuwa ganin ki bakida wannan matsalar,godiya tai musu
kafin tashiga bangaren Momy itama taneme gafararta akan rashin kunyar da taimata,
Anan kuwa tagafar tamata takama gabanta,
Kishiyar Momy wacce itace silar faruwar duk wani mummunan abu agidan tazo tana Neman
gafara ganin yadda Allah yai da ita yasa suka gafarta mata bakinta kadai ke aiki banda shi babu
wani Abu mnajikinta dayakeda amfani,
Da room freshener na ahannu nashiga dakin da safara'u take amma se kamshinsa ya hade da
mummunan warin dake tashi adakin akwance nasameta kan tabarma,
Yo waike kukan ubanme kikewa mutane duk kinbi kin suna daki da azababben wari wannan warin
Allah ya agajeni karya kasheni sbd masifa munyi yawon asibiti har mun gaji amma babu wani ci
gaba duk Dan abinda natara ya kare gurin neman magani wallahi bar ganin ki kwance zan
wanwanka miki mari bakar munafuka,
Mahaifiyarta ke wannan masifan ta miqe a dudduqe takarasa dakinta Dan tuni tamaida safara'u
dakin ajiye shirgi acewaeta bazata juri wannan warinba,
Baban safara'u ne yabiyo se shiga gidan a hankali yajiyo muryarta tanakiransa saboda tausayinta
dayake ji yasashi shiga dakin yana toshe hanci,
Baba don Allah kakiramin su badee'a in roke su gafara ko zan samu sassauci,
Hawayensa ya share yace Allah yasa zasu yafe miki nima tabarma nazo dauka domin su majid din
sunshgo gari yace badee tana tafe itada lubna sunzo ganin gida,
Aidasauri tace kataimakeni ka kiramin su inrokesu ko Allah zesa su yafemin domin na cutar dasu,
Majid kam warinta yagama isarsa kuma bayajin ze iya yafe mata danhaka yajuyard fuskarsa gefe,
Cikin muryar kuka da tsantsan tsoro badee tace nayafemiki safara'u Allah yayaemiki wannan
lalurar majid don Allah kayafe mata bakaga halin da take cikina,
Tunawa yai duk laifin dayaiwa badee batareda ta tsaya wani tuna niba tayafemasa kuma yaiwa
Allah laifuka da dama yana Neman gafarar sa meze hana yafewa wannan matar kila sanadiyar
haka shima Allah yayafe masa,
Babu komai mun yafe miki Allah ubangiji yatakaita wahala,
Yana gama fadar haka yai waje,anan badee tai musu Dan ihsani kuma ta roki inna da ataimakawa
safara'u da wanka lubna kam jikinta duk amace yake kalli wannan matar katuwa ji yadda takoma
batada maraba da kwarangol,
Allah ka gafarta mana zunubanmu wayanda muka aikata da gangan da wayanda bamusan mun
aikata ba
[8/19, 1:38 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 44
Hello yaya abdulrahim ina wuni,
Lafiya lau sisi yajikin ki?,
Naji sauki sosae gashi ma ina shirin zuwa muku wuni yau,
Kin cika yawo kuma gashi lafiyar ma bata isheki ba to yau bama nan,
Kuna ina yaya,tafada muryarta kamar zatayi kuka,
Muna asibiti safna ta sauka dama shinakira nafada miki,
Wani ihu datayi seda tasauke wayar daga kunnensa,
Tsaya mana hajiya,
Yaya me muka samu?,
Baby boy,
Aiko ganinan zuwa dama a shirye nake,
Bata jira ya amsaba ta katse wayar,
My man tashi muje asibiti safna ta sauka munsamu baby boy,
Alhmdllh, amma kidaina wannan tsalle tsallen karki mana wata barnar,
Murmushi kawai tayi tace bari naje Na fadawa Momy kilama zata bimu takaiga jika,
Dariya kawai yayi yabi bayanta,
Bayan ansallamesu abdulrahim yayo gidansa da ita badee takirashi awaya,
Nace kamayarda safna gida acan zatafi samun kulawa lubna tace kayi can gidanka da ita,
Yanzu mama seta koma gida?harfa se bayan kwana arba'in,
To rashin kunya zaka yimin?,kokuma shawarar ka nanema?,
A'a yace murya a sanyaye,to kamaida ita gida zatafi samun kulawa,
Badan ransa yasoba yai yadda badee tace,
Yanzu cikin lubna yana wata hudu kenan,
Yau ake suna kasancewar gidan za ayi suna yasa en uwa zuwa suka tare part din lubna tunda
sassafe zasuyi aiki,
Ta fito zata fada musu ga abinda za ayi Mus'ab yajnyeta daki sunyi jira har sun gaji Dan haka suka
fara gyara kayan miya,
Ke Zainab tunda ke gidan yayanki ne danje ki kwankwasa musu rana keyi fa ga mutane sun fara
zuwa amma ba agama abinci ba,
Zainab diyar kawunsa ce zuwa tai ta kwankwasa kofar lubna na zaune gefen gado da hand dryer
hannunta tana busarda gashinta Mus'ab kuwa yana tsaye yana Daura agogo tsintsiyar hannun sa
tace waye? Zainab ce wai anty juwairiyya tace kifito rana nayi basusan meza afara ba,
Zainab ki shigo bana jinki,itakam tsaye tai jikin kofar taki shiga Mus'ab yagama shirin sa yai mata
sallama ze fita taimasa Allah yakiyaye ,
Kishiga mana Zainab kika tsaya anan,shiga tai duk kunya ta isheta tace,
Yaya lubna aiki fa mukeda kikazo kika zaunan nan tundazu,
Laifin yayanki ne meyasa baki masa fada ba seni zakizo kinawa Turin baki nidalla mikomin
doguwar rigata cikin wardrobe dinnan tafarko daga sama zaki ganta nasa mutafi karku cini gaya
babu miya,
Dariya Zainab tayi tace to kiyi sauri,
Atakaice dai sunan yayi dadi yaro yaci suna abubakar sadeeq Allah yaraya mana,
Ramla ma ta haihu tasamu baby girl sunanta Aisha juwairiyyan abduljabbar ma ba abarta abayaba
seda ta suntulu yarta mace kamar lubna tayi kaki,nan abduljabbar yaiwa badee'a takwara suna
kiranta mami,
Lubna kadai ta rage ta sauke nata Dan har ta koma gida saboda kumburi babu abinda take iyayi se
salla shima dakyar tana numfarfashi har ta gama badee bata bari tai komai kullum tana kwance,
Lubna tana zaune wayar badee na gefenta taga yaya asama'u Na kiranta miqewa tai dakyar tayi
hanyar palon majid da wayar a hannunta,
Majid na zaune kan doguwar kujera badee tayi pillow da kafafuwansa da alama ma bacci take
dasauri lubna ta juya zata fita majid yace,
Daughter zo mana ko jikin ne?,
A'a baba wayar mamace ake kira shine nakawo mata ta ajiye wayar kan center table tafita da
murmushi a fuskar ta,
Se sukan la'asar badee ta farka da sauri ta miqe saune,
Haba majid meyasa kabarni inata bacci haka?gashi nace yau dambu zamuci komai ban shirya ba,
Hmm gadai wayar ki lubna ta kawo yaya asama'u nakira,
Zaro.ido tai tace lubna taganmu a haka?,eh mana amma wayar kawai ta ajiye ta fita,
Aiduk laifinka ne seda nace zanje daki nakwanta kace nai kwanciyata anan yanzu gashi kaja ta
ganmu duk kunya ta kama ni,
Dariya kawai yayi yace ji yadda kikayi da fuska kamar wata yarinya nidai kije ki matsa mata
kafafuwanta naga sun kumbura,
Wallahi haka suke kullum ko jiya seda najira tai bacci nima nayi segumi take duk sanyin dakin
tausayinta nakeji bata taba jin dadin cikiba,
Nima ina tausaya mata ganin kotafiya dakyar take yi amma ai takusa sauke wa Allah dai yasauketa
lpy,
Ameen bari inje indubata,
Washe gari tunda ta tashi sallar asuba take jin abubuwa amma dai ta daure har gari yayi haske,
Dafa gadon tayi zata miqe ta kasa jin yadda bayanta ya riqe tace washhh,dasauri badee ta
taso,lubna ko abinne?,
A'a bayana ne kawai naji yariqe,😳kuma kikace a'a?, ina wayar ki nakira Abdulqadir yakaimu
asibiti,shiru tayi zufa naqaryo mata,pillow badee ta daga tadauko wayar dasauri takira abdulqadir
jikinsa har rawa yake daga masallaci yadawo gida dasauri,
Lubna kiyi kokari ki tashi muje mota mana,
Mama wallahi kodaga nafara bazan iya yiba,to bari nakira abdulqadir Yakama min ke,kusan karo
sukayi tace zoka kamamin wai bazata iya tafiyaba,
Yana zuwa ya sureta se mota se cije baki take tana runtse ido sosae,
Dasauri aka karasa da ita labour room Sega Mus'ab kamar ze tashi sama yashige dakin,
Har karfe goma na safe babu wani labari,ta wahala iya wahala saboda girman babyn se kusan
karfe goma sha biyu ta haifi namiji ni narasa dawa yaron ke kama gashinan babba kamar insace
ingudu.
Rawa naringa yi ina murnar zamusha biki sedai wani Abu Dana tuna yasa jikina yai sanyi😔
[8/19, 8:38 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017.
Second to d last page
Page 45
Baka tafi kabarni ba gashinan ankawo wata tsohuwa secin zalina take,inji lubna dake waya da
Mus'ab,
Metai miki?,yatambayeta da muryar murmushi,
Muna fa zuwa ko zama banyi ba mama tasa tamin wanka daruwa me azabar zafi,
To kiyi hakuri taimakonki take ina baby,
Yanacan hannun mama tana shirya shi shima anmai wanka shima naji se tsala ihu yake,
To kije ki rarrashe shi mana,ta zaro ido tace rufani ka sayani kar kasa mama ta fige ni dama tana
cewa banida kunya,
Dan kinrarrashi danki shine bakida kunya?,eh mana kaibakada labari ne dama ba Dan fari bane
bari inci abinci zan baka labari yunwa nakeji,
To bye luv u,luv u too my man,
Dakin badee suke zazzaune duka matan sa'anninta Sega badee tashigo da baby karbi lubna bashi
nono yaronma yanada dangana tunda yazo duniya benemi abinci ba se bacci yake,
Karbar sa tayi tana kallon su safna kasa kasa itafa akwai matsala yaza'ayima shekara da shekaru
tana boyon Abu yau kawai bainan nasi ace taciro shi kowa yagani hijab ta janyo tasa ta tura babyn
ciki,
Ke meye haka?inji badee,
Mama nikam wallahi banaso suganmin jikina,
Yo naji wani shashncin banza jama'a Ku tayani gani ko a tarihi bantaba jin wannan labarin ba,
Aiko mesu safna zasuyi ba dariyaba,
Ke zaki ciro mamman kibashi yadaina mana kuka kokuwa senazo naciro dakaina?,
Toni ban iyaba,dada kika kunshe cikin hijab mezakiyi?,tana masifa tanuna mata aiko yana
kamawa ta fizge tana ihu,
Wallahi lubna watan cin ubanki ne yakusa kamawa Dan marinki zanyi zaki kamane yadai tsallar
masa a fuska kose yayi kuraje?,
Wallahi mama zafi bakiji ba daya kama,ai kowa da haka ya saba ki kama dalla malama yaro
yunwa yakeji shayarwa yazama wani jidali kuma,
Sudai su riyya se dariya suke,lubna kuwa harda Dan kwallanta ita anganemata jiki kuma gashi
tanajin zafi,
Nikam murna kawai nake yaune suna danhaka nace sena yanki en biki Kure adaka zanyi nadauko
kayan sallana a kasan akwati domin yaune suna,
Inacikin shiri cikin Dan ubansun lace dina sega momma na (Zainab inuwa #antysis) tashigo cikin
shirin ta nace mama wannan wankanfa inazuwa?,
Tare zamuje Dan bazan yadda kije kina tsokanar meela ba kuma gakida Dan iskan kwadayi,duk
inda raina yake seda yabaci dn bazan manta ba bikin jawaheer ma haka taimin seda nasha
ranqwashe ko babbar tusa hanani tayi,
Haka nagama shiri ina ta turin baki harna shiga mota muka tafi ban daina fushi ba Dan nasan ba
zanci rengem ba yau,
Tun gate na hango meela dasauri na dauke kaina araina nace mummuna kawai kamar ba er
gidanmu ba,
Mamaki ne ya cika ni lokacin Dana hango ayarin en gidan Sophie G kowa tadau wanka sunkame
akan kujerun roba se hankadar mutane suke,
Can Na hango su anty billyn Abdul,cute Zara,maman Nana,anty badee social,baby nurse daga gefe
se yagar naman rago suke aiko idona nakansu se hadiyar yawu nake,kyakkyawan rankwashi naji
senaci uban makiyanki bikin nan bazamu jima ba Dan bazaki sani kunya abinda kikeyi ko sultan
bayayi kwadayi kamar mayya,
Nidai se zare ido nake nasan banida gaskiya meela tabiyo gefen mu tace andai ji kunya
kwadayayya kawai,nace wallahi zamu hadu yanzu Dan kinga mamane kinsan bazata bari muyi
fada anan ba,
Biki yai biki se shagali ake mama takasa ta tsare haka naita kumburi ga ankawomana abinci ta
nama anhanani ci dole na dangana atakaice dai banji dadin bikinba,
Gaisawa kawai nayi da en gidan ZBI mama tasani agaba mukayi gida bayan anbiyomu dakayan
bikin anan nema naji sunan yaro Muhammad,
Har mukaje gida bakina kamar zetabo bango,haba sweetheart zokiji banason wannan
Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500