ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fushin yi
hakuri banaso kina fada da meela yayarki ce kingani kuma kwadayi bakyau kinji kidaina,
To mama insha Allah nabari daga yau,yawwa er albarka Allah yanunamin aurenki,ai a 360 nabar
palon ina rufe fuska naji kunya amma akasan zuciyata se ameen nake cewa😉,



Allah ya raya mana muhammadu ameen.
[8/19, 8:38 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)

By
SophieG

A very heart touching story 2017.



LAST PAGE



Inaso Ku saurareni dakyau kunga yadda rayuwa ta zame mana inaso Ku dauki rayuwar duniya
abakin aure Ku masu mata kuriqe matayenku da kyau kuriqesu irin riqon dazakuyiwa kanku
yayayenku Ku kasance masu kula da rayuwarsu da tarbiyarsu lubna kekadaice mace kiriqe mijinki
dakyau kikula da tarbiyar yayanki kiyi yadda kikaga inayi sirrin mijinki shine babban abinda zaki
boye lubna kinji labarina kuma kingani da idonki don Allah Ku taimaka Ku kasance masu riqe
amana kuma kusani kune ABIN ALFAHARI NA,

Nan sukayi murna kowa zuciyarsu fess majid dake jikin kofa yashigo yana cewa,

Madalla da samun mata irinki madalla da samun uwar yaya irinki badee'a hakika nima Y'AY'ANA
ABIN ALFAHARI NA ne,

Murmushi sukayi sukace madallah da samun iyaye kamarku muma muna alfahari daku,

Allah yai muku Albarka yasa mugama daduniya lafiya,ameen muka amsa harnima.



ALHAMDULILLAHI

Anan na tattaro alqalamina na ajiye shi sekuma wani lokacin idan Allah yakaimu da rai da lafiya
acikin sabon littafina me suna DUNIYA DA ZAMANI.



Kudan bani lokacinku anan don Allah,



Idan kunlura acikin wannan littafin nawa ina girmama Kalmar HAKURI wasu dayawa suna cewa
babu mace irin badee a duniya Toni anan banace muyi hakuri irin nata bane a'a inaso ne mu
kwatantayin hakuri koda Rabin nata domin akowane kunci to akwai walwala,akowace wahala
akwai sauki,akowane kuka to kucigaba da kallon fuskar me kukan zakuga murmushi ashimfide
domin akowane duhu haske nanan zuwa,

Kufahimci cewa akwai dangana dakauda ido awurin badee da yayanta domin da babu haka
atattare da su da sundaukowa uwarsu rigima yanada kyau mukula da yayanmu,

Akwai sanin darajar yaya da iyaye dakuma en uwa semuriqesu dakyau,

Idan mukayi hakuri zakuga Allah ya kwato muku hakkinku tun anan duniya kamar yanda yafaru
da safara'u semu kiyye mukasance masu fahimta da hakuri.



Masoyana kusani nima inasonku kuma nima INA ALFAHARI daku nagode dakuka bada precious
time Dinku kuka karanta littafina kuma INA fatan Allah yasa kun karu da abinda ke cikinsa,



Mata masu aure da yaya Allah yabaku hakuri da zaman lafiya Allah ya albarkaci yayanda kuka
Haifa dawa yanda zaku Haifa yabaku ikon tarbiyarsu,

Yan mata irinmu Allah yabamu mazaje nagari da zuriya Dayyaba,

Wayanda suka rigamu gidan gaskiya Allah yajikansu mukuma Allah ya kyautata namu karshen
Allah yagafarta mana,



Na sadaukar da wannan shafin ga dukkan marubuta Allah yabiyaku da mafificin alkhairi ameen.

#AnaTAre😍

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment